Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da damuwa, Shahzain ya ce "Da zarar mun samu danginta sai a miƙata can garesu kawai, ina ga fa wannan ba wani abin ɗaga hankali bane Mom; Boss ka manta da su kawai." Miƙewa ya yi ya bar wajen ba tare da ya ce ƙala ba, Shahzain ma ya bi bayansa. Mommy ta ce "Kai Duniya Allah ka yi mana tsari da dukkan munanan abubuwan cikin wannan Duniyar." Inna ta ce "Amin Ƴata, ni dai na san Wannan miskilin mutumin ba halinsa ba ne kar ki fara ɗarsa wani tunanin daban akansa." murmushin ƙarfin hali Momi ta yi ta ce "Inna duk da abin ya yi ka ma da jirwaye me kamar wanka amma ina ganin Aikin ba na Shahbeer bane sai dai ba mu da tabbas kin san sharrin Zuciya da ruɗin Duniya, bare Kinsan Jini ba ƙarya bane dole iri baya ƙarya ko ta yaya ne sai ya nuna, Mahaifinsu..." Inna ce ta katse ta da cewa "Ya-salam! Dena irin wannan maganar kinsan idan su ka ji abin ba lallai ya yi daɗi ba." Goge hawayen da ke kan fuskarta ta yi gami da cewa "Allah ya yi mana me kyau, amma ina tsoron ranar da yarinyar nan za ta dawo haiyacinta ko kuma ranar da gaskiya za ta baiyana cewa Muktar ɗina ne ya ci zarafin yarinyar mutane." "Ki dena kuka A'i Allah ya san abin da ke ɓoye a cikin lamarin walau gaskiyar ko akasinta, addu'arki itace mafi muhimmanci da tasiri garesu" Inna ta yi maganar cikin sigar rarrashi da kwantar da hankali, gyaɗa kai kawai ta yi, Inna ta ci gaba da lallaɓata har sai da ta tabbatar damuwar ta-ta ta ragu sannan ta nufi kicin. Da sauri Ma'arufa ta miƙe ta na zazzare ido jin motsin shigowar Inna. "A'a jikata kin riga ni zuwa kicin ɗin yau?" gyaɗa kai ta yi kafin ta ce "Ina kwana Inna." "Lafiya lau ya mutan gidan naku?" "Lafiyarsu ƙalau" "To madallah, yau iyayen gidanki ba sa cikin yanayi me daɗi dan haka ki yi taka-tsan-tsan dan kowannensu ji ya ke da baƙar Zuciyarsa irin ta gado, akan tsini su ke dan haka ki kula; ni kar ma mu yi abin da ba sa ra'ayi su ƙi ci inaga ki je ki tambayo min su me su ke so. A ɗan tsorace ta ce "Inna kin ce a kan tsini su ke to idan na je na ƙara ɓata musu rai fa? dan Allah ki je da kanki." "Ba fa za ni ba, kuma yin abin da ba sa so ɗin ya fi tambayo sun haɗari dan haka na bar miki zaɓi. "Zan je" ta ce kafin ta fito daga kicin ɗin cikn sanyin jiki. Sallama ta kai Biyar ta yi amma ko ɗaya ba'a amsa ba hakan ya sa ta danna kai Abin mamakin su na falon amma aka rasa me amsa sallamar, cikin sanɗa ta ƙarasa a sanyaye ta ce "Inna ce ta ce Na tambayeku abincin da ku ke so." wani shegen kallo Shahmeer ya watso mata gami da cewa "Ba ki iya gaida mutane ba kuma??" da sauri ta ce "Ayi haƙuri ina kwana?" ƙwafa ya yi gami da juyar da kansa gefe, Shahzaib ya ce "Sai na ɓarar da ke in ba ki bar wajen nan ba aikin banza ku bar mutane da abin da ke damunsu sai kun kawo maganar abinci, ba za mu ci abincin ba kar ma ta girka." Da sauri ta miƙe jiki na tsuma ta juya da nufin barin gurin muryar Shahbeer ta dakatar da ita, hakan ya sa ta ja numfashi me ƙarfi gami da zazzaro ido.... "Da wace ƙafar za ki bar gidan nan kuma da izinin wa? ki tafi ina ma??" "Ki yi haƙuri Mom gidanmu zan je, ina ta kewar Iyayena da ƙannena su ma na san suna son ganina a kusa da su, ba ni da ja akan hukuncinku amma dan Allah kar hakan ya sa ku shiga haƙƙin rayuwata." ta ƙarasa maganar ta na hawaye. "Ahh lallai Shukriya akwai abin da ki ka taka, amma ba komai ni na wuce kwankwason babarki ma bare ke daidai nake da kowane tsagera, da hankalina fa ba za ki ninke ni ba kin ji ko?, ki tafin ga hanya nan ki ce ina gaisheta indai Maalik ne kuma gidanku ɗin ma gidansu ne zai zo ya sameki har ɗakin uwarki. Daɗin Maganarta ta ƙarshe Shukriya ta ji dan haka ta yi saurin yi mata godiya sannan ta fice, ta na jinta ta na cewa ta tsaya direba ya kaita amma ta yi banza ta gwammace ta je ta nemi napep. Maalik ya na shigowa ba abin da ya fara tambaya sai ita, kansa tsaye ya ce "Mom ban ji wani abu a Zuciyata ba, ina Shukriyata?" Dada ta ce "Shukriya ta gaji da zaman gidan ƙaya ta tattara ta koma gidansu ɗazu, idan ka na son ta dawo sai ka je ka ɗakko kayarka tin da kai ne mijin da za ta aura ai ba me hanaka." "Mom ki na nufin ba ta nan?" "Zan ta mai-maita maka magana ne??" zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Ba na jin daɗin gidan sabi da ba ta nan, Rashinta ya na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ya sa ba na son zaman ƙasar nan, gobe zan tafi nima." "A'a Maalik ka san dai yadda na ke sonka ba na son abin da ba zai maka daɗi ba, ka yi haƙurin jira na kwanakin sati ni kuma a ranar da ta cika satin na yi maka alƙawarin ranar za ta zama matarka, kafin satin kuma za ka iya komawa can gidan da zama ko kuma ka dinga zuwa a duk lokacin da ranka ya so, amma in hakan ya yi maka. "Hakan shine kwanciyar hankalina Mom lallai rana irin ta yau Shukriya ta zamto matata. daga haka ya tashi ya fice daga gidan. ya na fita Dada ta ɗauki waya ta kira Alhaji Ibrahim ta sanar masa hukuncin da ta yanke ranar Asabar me zuwa za'a ɗaura auren, da yake ba ya yi wa yayar tashi musu Allah ya kaimu lokacin kawai ya ce. Abida da Abid sun yi farin cikin ganin yayarsu sosai har dare hira su ke sha har da Mami. sai bayan sun yi sallar isha'i sannan ta wuce ɗakinsu, gyare-gyare ta shiga yi kasancewar ba ta son ganin barkatai ita kuwa Abida ko meye ta hargitso ba za ta maida shi inda ya dace ba rashin Shukriya a gidan ya sa ɗakin ya yi watsa-watsa. Abida ce ta shigo ganin ta na abin da ta saba ya sa ta cewa "Sannu Aunty ba kya rabo da kintse-kintse." murmushin takaici ta yi gami da cewa "Idan na kife ki da mari sai kin dena ganewa, haka ma za ki ce bayan ke ce me ɓatawar?" Dariya Abida ta yi ta ce "Ki yi haƙuri Aunty ni wallahi ba na iya ƙalƙalar nan" "To Allah ko ya kyauta miki kina mace wadda za'a kai gidan miji ki ke wannan halin." "Ba komai tin da ta na da me gyara mata yanzu idan ta je gidan mijin kuma nasan za ta yi dan ƙanwar tawa ba daga nan ba." Muryar Maalik ce ta karaɗe kunnuwanta, a tsaye ta suma ko motsi ta kasa yi sai Zuciyarta da take gudu a ɗari ba ɗaya. Abida kuwa ganin Maalik a bayanta ya sa ta yi saurin ba shi hanyar wucewa gami da gaishe shi, amsawa ya yi cikin sakin fuska, suna gama gaisawa ta fice har da gyara musu labule, abin da ya ƙara ɗaga hankalin Shukriya kenan, "Yanzu ba me tausaya mata ko ya fahimci halin da take ciki? me yasa ba sa guje mata auren wannan me lalatacciyar tarbiyar?'" tambayoyin da Zuciyarta ke yi mata kenan sai dai ba ta da amsarsu. sai da ya kashe hasken ɗakin sannan ya ƙaraso inda ta ke tsaye, kansa tsaye ya janyota jikinsa ya rungume ta gam sauke nannauyar ajiyar Zuciya ya yi kafin ya ce "Me yasa ki ke guduna Shukriyata?" yadda ya yi maganar a wani susuce ya sa ta rintse ido gami da furta "A'uzubillah" a cikin ranta, "Kinsan komai da mahaɗinsa idan ba'a haɗa ba baya ƙarko Shukriya, ko ban faɗa ba nasan kinsan kece mahaɗina, me yasa ki ke gujewa Zuciyar da ta haukace akan sonki? anya kuwa kina da adalci Matatah!!!!?" wasu zafafan hawaye ne suka shiga kelo mata, laƙwas ta yi a jikinsa duk jikinta ya yi sanyi. "Na yi ƙoƙarin hana kaina abin da ba kya so kuma na kiyaye akwai abin da ya rage ne? me na yi miki wanda ya sa ki ka nesanta da ni? tambayoyina gareki su na matuƙar yawa sai dai na san ko kina da amsarsu ba zan samu daga gareki ba, Shukriya gaya min wace irin ƙauna ki ke so na nuna miki?" jin ya fara wuce gona da iri ya sa ta sakin kuka me ƙarfi, "Maalik ba na so, don Allah ka yi haƙuri, ni ban yi jayayya da hukuncin Dada ba na amince zan aureka kuma ta ce nan da sati ne ɗan jiran da za ka yi fa ba wani bane amma ka ke ƙoƙarin yin abin da bai dace ba idan ka jure rashin ganina na kwana bakwai kawai daga nan za ka kwashi lokaci me tsayi a tare da ni. "Amma gani nake yanzu mun fi kusa tinda aure kawai ya rage mana ba na ganin kuskurena. "Hakan ba daidai bane Maalik, tafkeken kuskure ne wanda da yawanmu ba mu fahimci akasin da ke ciki ba, hallau dai aure bai shiga takanina da kai ba ka ga kuskure ne wani abu bayan gaisuwa ya shiga tsakaninmu, ni ba irin wannan tarbiyar aka bani ba Don Allah ka yi haƙuri ka ƙyaleni. numfashi ya ja ya sauke kafin ya janyeta daga jikinsa, cikin raunanniyar murya ya ce "Janye ki daga jikina tamkar zarar ruhi daga gangar jiki haka na ke ji amma na yi don ki na son hakan, Don Allah Shukriya za ki zamo tawa har abada??" tambayar ta zo mata a waskace gefe gudu mugun tausayinsa ya gama lulluɓeta a wani ɓangaren kuma tsananin son Safyan ke gargaɗarta, rasa amsar da za ta bashi ta yi dan haka ta sake fashewa da kuka. "Ki yi haƙuri Shukriya akanki ba na iya sarrafa Zuciyata; zan koma gidanmu Don Allah ki kula min da kanki. bai jira abin da za ta ce ba ya fice daga ɗakin. a gurin ta durƙushe ta sake rero sabon kukan. "Duk abin da ki ka girka shi za su ci Arufa, ba zai yuwu su zauna da yunwa ba" Shahbeer ya yi maganar ba yabo ba fallasa. ganin ta ƙame a wuri ɗaya ne ya sa Shahzain cewa "Jeki mana Aunty Beauty." da sauri ta fice gabanta na faɗuwa akai-akai ƙafafunta har su na harɗewa sabi da sauri. Shahzain ne ya ce "Kun fiye buyagi gaskiya ita fa ba ita ta yi muku laifi ba." Shahmeer ya ce "Ko ba ita ta yi ba ina ruwanta da ƙara ɓatawa mutane rai?" "Allah ya baka haƙuri" Shahzain ya faɗa gami da gyara zamansa. Waya ce a hannun Kamal ya na son kiran Safyan amma tsoro ya na dakatar da shi, ya ɗebi lokaci ya na nazarin lamarin sannan ya yi ta maza ya tura kiran, kira uku ya yi sannan Safyan ya ɗauka. "Safyan Yane?" "Daidai wallahi ya kwana biyun?" "Sai godiya, wani labari na ke son baka amma fa kar ka bari a san ni na faɗa. "Labarin waye?" "Shahbeer. da sauri Safyan ya miƙe tare da mai-maita sunan, "Me ya faru da Shahbeer ɗin?, Me ya sa ba ka son ya sani? tsoronsa ka ke ji?" ya jero masa tambayar a tare. "Hmm Safyan kenan, ba za ka gane illarsa ba har sai ya hanaka rintse idanunka da sunan bacci, kai daga baya ka san shi ni kuma tin muna yara, tare mu ka yi karatu, tare mu ka yi tashen ƙuruciya, tare mu ka yi farkon samartaka 18-19-20 Years ɗinnan, ka ga gashi mun haɗu a 29-30-31, Mugun Shu'umi ne ka je ka tuhumi tarihinsa kai ma za ka ji tsoronsa, shi yasa kar ka bari ya sani gaskiya idan ka san za ka bari a ji ni na faɗa ba zan gaya maka ba. "Yi haƙuri ba zan bari kowa ya ji ba, Ka gaya min, ni fa na ƙagu in ji ko mene. "Dama yau kwana uku kenan ya kawo wata yarinya asibiti ba ta da lafiya....... duk abin da ya sani da wanda ya faru tsakaninsu ya kwashe ya gayawa Safyan. Sosai Safiyan ya ji daɗin labarin dan kuwa bai tsinkayi zancen ba sai yanzu, sabi da farin ciki har kyauta ya ce zai yiwa Kamal, atake ya yanke cewar ya samu wani makamin da zai ƙuntatawa DOUBLE TWO STAR. _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ Jaririyar Elegant. *INDO* [12/9, 1:02 PM] INDO CE: *WATA HANYA* 12 Free buk Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* MOONASH Alƙaluma Shida. Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS. BANI DA HUJJA Maimoon SARƘAƘIYA Shaahd BARRISTER SHAHEEDA Ayush AUREN ƘAUYE Nazlarh ZUMUNCIN ZAMANI Jikar Nashe Cike da farin ciki Safyan ya koma gida, Alhaji Boza ya na sashinsa kai tsaye can ya nufa ya na zuwa ya fara labarta masa abin fa ya faru. ba wata murna ya yi ba sai ma fargaba da ta ƙara ɗarsuwa a cikin Zuciyarsa, wasu tunane-tunane su ka shiga dawo masa, ganin ya yi zugum ya sa Safyan cewa "Daddy fatan dai lafiya na ga ka yi irin wannan shiru haka, murna fa ya kamata ka yi." "Haba Son, barni na jimanta abin da ke damuna mana, ba za ka gane komai ba domin kai yaro ne, amma ba zance komai ba sai dai na ce Allah ya sa hakan silar da zai dinga daraja ni ce. da mamaki sosai a tattare da Safyan ya ce "Ban zata za ka yi sanyi lokaci guda haka ba Dad, wai don Allah me ka ke ɓoye min ka barshi a Zuciyarka haka?" "Safiyanu ranar wanka ba'a ɓoyon cibi dan haka wata ran idan lokacin ya zo za ka sani, ai rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. "To ai shi kenan da ma na san ba lallai na samu amsar ba, ni dai yanzu ko ka na so ko ba ka so sai na tonawa munafiki asiri, ya na fakewa da adalci da temako ya na cin zarafin yara ya na fyaɗe su. girgiza kai Alhaji Boza ya yi cike da jimami ya ce "Ashsha!! abin ba dacewa gaskiya da bai yi hakan ba." "Daddy dama irinsu ai ba su da kama ni dai wallahi kawai ka zuba min ido. "To ni ai baƙon sauƙi ne, zan sa ido in ga yadda za ka yi. daɗin maganar Dad Safyan ya ji sosai miƙewa ya yi ya bar wajen, kai tsaye sashin Mom ya nufa don ya sanar da ita abin da ke faruwa. Inna ce ta ce "Haba ƴata, wannan damuwar ai ta yi yawa da me za mu ji?, ke damuwa Shahbeer damuwa kamar ba ku da tawakkali?" A sanyaye Mommy ta nemi guri ta zauna tareda sauke numfashi sannan tace "tsorona ya kafu akan maudu'i daban daban Inna, amma Allah yafimu sanin abunda hakan yake nufi" Shahzain ya ce "Gaskiya kam Mommy abin ya yi yawa, Don Allah kawai ki ƙaddara komai ya wuce." shiru ta yi ko ƙala ba ta ce musu ba. Shahmeer ya ce "Masoyita don Allah ki kula da Mommy mu za mu shiga ciki, ta rage damuwar nan don Allah." zama Inna tayi kusa da ita ta shiga rarrashinta. Su Shahzain suka wuce sashin su. A zaune suka tarar da Shahbeer yayi tsit ya dafe goshi da alamu ya lula duniyar tunani. Shahzain ne ya dafa kafaɗarsa cike da kulawa ya ce, "Inya duk wannan tunanin ba naka bane ka dena don Allah" Ɗago ido yayi ya kalleshi sannan ya ce "ka ce? tunani ba nawa bane kenan sai kai me ƙwaƙwalwar tunani?" Shahmeer yace, "Haba Shahbeer daga rarrashi kuma sai faɗa? ba na son hakan yasa ka canja fa, amma aganina idan baka damu ba ai ba wani abu bane da zarar ta Samu lafiya zamu mayar da ita wajen iyayenta" Ya ce "a'a!!! lafiyarta ba itace abun damuwa ta ba face makomar mu da kuma ta- ta; Umminmu mukaɗai ta haifa ba ta da ɗiya mace hakan ne yasa ba ku ji zafin da nake ji ba kasancewar an raba yarinyar nan da mutuncinta, ban santa ba, bansan wace manuface tasa duk mutanen da suke garari a Duniya bata faɗa hannun kowa ba sai nawa, amma haka kawai na damu da son sanin abunda ke ɓoye acikin wannan sirrin, ina son sanin waye ya aikata hakan gareta a gefe guda kuwa yanayin bugun zuciyata yana gaya min cewar an shirya hakan ne domin gurɓata farin cikin mu, sanin kanku ne a Duniya kewaye muke da maƙiya masu tarin yawa, kuma ya na da kyau kuyi tunani ba iya ni kaɗai ba Ƙarami, Jariri, Auta, amma tinda bakwa so kuje ku kawo min shayin kanumfari kawai ni kuma zan manta da komai" jikinsu ya yi matuƙar sanyi da jin kalamansa, Shahzaib ne ya ce, "Ka kwantar da hankalinka ɗan uwana ba abin da zai faru da izinin Allah" Bai ce komai ba ya ci gaba da danne dannensa. Miƙewa ya yi gami da cewa "Boss shayin a sa sugar da yawa ko kaɗan?" "Daidai misali" ya bashi amsar ba tare da ya kalli inda ya ke ba. kai tsaye kicin ya nufa cike da tunane-tunane, jin motsi ya sa shi yin sallama, da sauri Ma'arufa ta amsa gami da kame kanta, gaishe shi ta yi ya amsa ba yabo ba fallasa; ta yi mamakin ganin haka sosai kai tsaye ta yarda Auta (Shahzain) ne dan ya fi kowa sakar mata fuska sai Shahbeer shi kuma ba kasafai ya ke murmushi ba sai dai in shi da ƴan-uwansa ne, ba ta bambance su ta fuska ko ta sunayensu amma ta wajen faɗansu da haɗe rai ta na bambance wanda ya fi yi mata mutunci. yadda ta ke mugun kallonsa ya sa shi cewa "Lafiya dai Madam?" a ɗan kunyace ta ce "Lafiya lau yallaɓai, ka yi haƙuri." "Ohh ina ce ba lafiya ba ai, nima Boss ne ya sani dahuwar shayin kanumfari shi ne ki ka ganni a kicin, ko kin iya ki dafa masa?" "A'a Yallaɓai abin manya bai yi daidai da na ƙanana ba ka daure ka yi da kanka. murmushi ya saki gami da cewa "Me yasa?" ya jefo mata tambayar gami da kasheta da idanunsa masu matuƙar sakar mata dafi. ƙasa ta yi da kai ta na kokawar saita numfashinta, wai garin wane rashin hankalin ma ta fara sakin baki wajen yi masa magana?. Dr Malika ce ta fito falo cikin tsararriyar tafiyarta irin ta ƴan-mata ma su ji da kansu, kusa da Momma ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya-kan-ɗaya ta ci gaba da taunar cingam ɗinta ba tare da ta kula kowa ba; Momma ta kalleta ta watsar ta ci gaba da abin da ta ke yi. sai da suka ɗan ɗebi lokaci a haka kafin Dr Malika ta ce "Saukar yaushe Ya Abeer?" "Kin gama yi mana kallon tara ahun??" murmushi ta yi gami da cewa "Ba haka bane Yaa Abeer." ya ce "Na ga kin canja min gaba ɗaya kin yi kozai-kozai, ina fatan dai lafiya." ɓata fuska ta yi gami da kauda kai, ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, har yau ba ta fasa kukan baƙin cikin abin da ya faru ba. Momma ta ce "Abeer ai kafin ka tafi ta na gidan Mommynta ta je takalo faɗa da Shahzaib" Momma ta yi maganar cikin sigar zolaya; ci gaba ta yi da cewa "Ban ga ta na da niyar dawowa ba idan na tambayeta sai ta ce ba yanzu za ta dawo ba sai ranar nan katsam na ganta wujiga-wujiga tin daga lokacin da Shahbeer haɗari ya faru ya buge wata yarinya shi kenan mu ka dena gane kanta, yanzu ma sa'a ka yi ta kulaka, aikin da ta ɗauka yanzu na kuka ne." "Haba ƙanwata garin ya haka? me yasa za ki damu kanki tsautsayi ne fa, ke wallahi kin fiye tarar aradu da ka, ai kowa hakan ta na iya faruwa da shi a bisa rashin sani ya buge mutum idan da ƙarar kwana sai ki ga an mutu to duk haka ake jurewa ba zama ake ana kuka ba. "Ai ba za ka taɓa fahimta ba Yaa Abeer, Momma ma ta kasa fahimtar halin da na tsinci kaina bare kai. "Na kasa gane miki Malee me ki ke nufi ne?, akan Shahbeer ɗin ko kuwa?, ai bai zama lallai sai wani ya fahimci sirrin Zuciyar wani ba in kina so mu gane sai kin sanar da mu abin da ke ɓoye cikin ranki" Abeer ya na gama faɗen haka ya miƙe da nufin barin gurin dan ya san babu lallai ya samu amsar tambayarsa. "Na kamu da Son Shahbeer Yaa Abeer!!, sai gashi an wayi gari da wani banzan labari, Ina da matuƙar kishi hankalina Ba zai iya ɗauka ba, lokacin da na ganshi ya rungumo yarinyar nan ji na yi kamar na yi hauka, lokacin da na ji ance fyaɗe akai mata na ji tsoro kar na je da gasken -gaske Shahbeer ne ya aikata idan kuma sharri akai masa ina cike taf da tsanar wanda ya ke da hannu akai ciki kuwa har da wannan yarinyar, na tsani ganin baƙar fuskarta, don Allah ku bar ni na ci gaba da damuwata dan ba wan da zai min maganinta sai Allah. komawa Abeer ya yi ya zauna da ga shi har Momma su ka zuba mata ido cikin tsananin mamakin kalaman nata. numfashi Momma ta ja gami da cewa "Hmmm!!! tirƙashi, kin iya ɗaukar dala ba gammo Malika, anya kuwa ba ki ɗau Wata Hanya da za ta sa ki haukacewa ba?" Abeer zai yi magana ta ce "Don Allah Momma fatan alkairi ya kamata ku yi min ba wasu alamomi ba, ni dai ina son shi kuma ba zan dena ba." Abeer ya ce "To Allah ya temaka." Momma cewa ta yi "Allah ya yi mana zaɓin alkairi ba zaɓinmu ba." Maalika ta amsa da "Amin" Diri-diri Ma'arufa ta fara yi cikin rawar baki da kyar ta ce "Ba komai kawai hakan ya fi dacewa ne." daga haka ta yi hanyar fita cikin sauri. "Arufa!!!" ya kira sunanta ya na ƙara ware mata idanunsa, tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba ta ce "Na'am yallaɓai." "Ba zan iya yi ni kaɗai ba, za ki ta ya ni???" ta na shirin cewa "A'a" ya katseta da cewa "Ohh za ki taya ni kenan ai na ɗauka za ki tafi ki barni ne, to na gode." "Ya Allah"

Chapter 7 of 30