Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dinga tuna baya." bai ce komai ba ya ja hannun Shahzad su ka koma Sashin Inna. Shukriya da Innan sun sa Halima gaba sai tijara su ke yi, Ma'arufa kuwa sai dai ta yi murmushi idan sun yi abin murmushin in sun tambayeta ta gyaɗa kai ko ta girgiza. su na cikin haka Shahbeer ya yi sallama, Inna ta ce "Madallah da zuwanka Inya, mu na nan mu na faɗa akan fitar da ta yi ta bar gida ko tausayin Mahaifinta ba ta ji ba." Cogewa ya yi ya harɗe Hannayensa a cikin ƙirjinsa cikin ko'in kula ya ce "Ai yanzu ta gane Ba Mutum Ɗaya bane mu Biyar ne, Idan Ramadan ɗin nata zai tafi sai ta bishi." Shukriya ta ce "Aff, faɗa mata dai Yallaɓai Shahbeer, nima haka na ce mata, ni so nake ma ta baka haƙuri wallahi, akanta wane irin iftila'i ne ba ka gani ba? amma haka ta hamɓarar ta shiga gari ya ƙanshin dahuwa." Halima ta share ƙwallar Nadama cikin sanyi ta ce "A bisa kuskure ne, ku yi haƙuri." cikin sauri Shukriya ta ce "Aaaa!!!, tsaya!, ba gaira ba sabar ba za'ayi irin wannan da mu ba, ai da wannan sanyin muryar taki sai kin kalle ƙwayar idonsa sannan za ki faɗa ya gane in ba haka ba kuma ba batun haƙuri, yanzu sai mu haɗa miki kayanki ki bi Ramadan, au YaYa Ramadan." yadda ta fiffiƙe ta yi kicin-kicin da rai kamar gaske ya sa Halima ta tsorata, ba za ta amince da bin Ramadan ba don haka gwara ta bashi haƙurin, idanunta cike da ƙwalla yare-yare ta ɗago ta kalleshi, su na haɗa ido ta yi saurin sunkuyar da kai wani sabon hawayen ya fara tsiyaya, shi ma ya kauda kai kamar bai ganta ba. cikin rawar murya ta ce "Ka yi haƙuri, na gane kuskurena ka yafe mini." "Ai ni ba haƙurin da za ki bani illa kin gaya mini alaƙarki da Ramadan har ya kawo aikin ashsha tsakaninku" ya yi maganar ya na ƙara murtuke fuska. Shukriya ta ce "Shi kenan!!, ai Wallahi Ya Shahbeer daga kanka sai Yaƙin Ƙarshe, shi yasa ka ke burgeni wallahi." ya ɗan murmusa tare da cewa "Godiya na ke Ƙanwata." Halima ta ƙara fashewa da kuka cikin shashsheka ta fara basu labarin. Kan hanyarta ta ɗibar ruwa ya tare ta kamar yadda ya saba cikin sigar lallami da lumana, "Ƴarmakafi ba kya gajiya da aiki ne? da kin dawo daga Islamiyya za ki fara tsalle-tsalle ba kya son zama" Ta yi murmushi kafin ta ce "Ai ba na aiki da yawa, daga ni sai Baba fa, dama ina so in yi maka godiya akan Taliyar da ka Saya mana jiya." ya rausayar da kai ya ce "Haba Halimeme, meye abin godiyar? ba na so gaskiya ki dena, kawo in tayaki ɗaukar ruwan." "A'a barshi, amma banda abin ka ai godiyar ba laifi bace." ya ce "To shi kenan ki gaida Baban." ta gyaɗa kai ba tare da ta yi magana ba. haka ta ƙarasa gida ta na tunaninsa, ya matuƙar shiga ranta sabi da temakon da ya ke yi musu ita da Mahaifinta, sau da yawa idan sun rasa Abin ci shine ya ke temaka musu da ko garin jiƙo ne, bayanshi sai Bello me Kanti da ya ke basu rance idan sun je bara sun samo sai su biya shi. da haka Ramadan ya kafa sansaninsa a Zuciyar Halima har ta yarda da shi ta ɗauke shi a matsayin me gaskiya da Amana; duk wani tantirancin shi a ɓoye ya ke yi ba ya bari ta san asalin halinshi. yau ta na banɗaki Baba ya shiga rera mata kira, ta yi sauri ta fito don ganin abin da ke damunsa, a galabaice ya ce "Halimatu ki je gurin Bello ki karɓo mana garin jiƙo ko na murtala biyu sai ki tawo mana da Sikari." ta ce "To Baba, amma dai na Murtala biyu ai ba zai ishemu ba sai dai huɗu, idan ma mun ƙoshi in anjima sai mu ƙara ci ko?" ya ce "To Ƴar Albarka, amma don Allah ki bi rayuwarki a hankali, kin ga ni nakasashshe ne ba ni da ƙarfin da zan iya sa ido akan motsinki, ki tsoraci Duniya da ababen cikinta, ki guji Mu'amala da Mutanen banza ko da kaɗan ne, kar tsanani ko wani abu ya sa ki banzatar da tarbiyarki kin ji?? lallai ki kiyaye ba kowane ɗan Adam ake bawa yarda ba." ta na murmushi ta ce "Haka ne Baba, zan kula da yardar Allah" har cikin ranta ta yarda da Ramadan shi ya sa ba ta yi ma tunanin sa shi a cikin jerin irin mutanen da Baba ya ke nufi ba. haka ta fice ta na tunanin rayuwarsu tare da tausayin Babanta. Da sallama ta shiga kantin sannan ta ce "Malam Bello Babana ya ce ka bani Gari na Murtala Huɗu har da Sikari. Malam Bello ya ce "To ƴar-makafi, Baban naki ya na lafiya?" "Lafiya lau, ya ce ya na godiya da temaka masa da ka ke yi. Zai yi magana Ramadan ya shigo tare da Sallama, "Ƴar-makafi me za ki saya mana ne?" Shiru ta yi ta na ɗan murmushi, ba ta son gaya masa don kar ya saya musu tasan ba ya gajiya. Malam Bello ya ce "Garin jiƙo za ta saya." "Na ce ki dinga karɓar duk abin da ki ke so idan na zo zan biya. ta ce "A'a gaskya, ranar da Allah ya bamu kuɗi ba sai mu biya da kanmu ba?" ya ce "Dama nemanki na ke yi har zan je gidanku sai na fada, Mamata ce ta ke so ku gaisa shi ne na ke nemanki, zo mu je daga nan sai ki tawo da garin." ta ce "Kaii! ba za ni ba, Baba ya na can ya na jirana gaskiya." "Haba Halima ba cinye ki zan yi ba, ba za ki daɗe ba za ki dawo nima sauri na ke." ta rausayar da kai ta ce "To Amma dai ba nisa ko?" ya ce "E" tasa ta ya yi a gaba don kar ta sille masa. Gidan na talakawa ne dai amma da rufin asirinsu, dama an gaya mata nan ne gidansu ta ƙi yarda ashe da gaske, cike da murnar za ta ga Mamarsa ta ce "Mamarka ita kaɗai ce a gidan?" ya ce "E mana." ta na juyawa ta ci gaba da tafiya har ta shiga zaure ya shaƙa mata wani ƙyalle ta silale a gurin. Waya ya cira ya kira abokinsa ya na zuwa ya kara Mota a ƙofar gidan su ka zura ta ciki, su ka ƙara gaba. Ba ta farka ba sai lokacin da Ramadan ya ke ƙoƙarin keta haddinta, ta fara kokawar ƙwatar kanta sai dai kashsh!! an fi ƙarfinta, daga baya ma sai su ka haɗa mata da duka wahala biyu ta haɗe mata har ta suma, daga nan su ka je kan hanyar Shahbeer su ka ajiyeta don sun san lokacin da zai dawo, su na maƙale a yankin har ya iso ya ɗauketa sannan su ka ci gaba da tafiya ransu fari tatas. Shahbeer ya taɓe baki ya ce "Ashe ɗan Unguwarku ne a da." ta gyaɗa kai, ya ce "Oo Allahu Jalla'wa'azza lallai Ramadan akwai ƙarancin Imani." Shukriya ta ce "Wallahi abin ba daɗi, Allah sarki, amma ai yanzu sai dai tarihi, ki ma godewa Allah." Shahbeer zai yi magana Shahzad ya katse shi da cewa "Baba Aunty Baby ya na yin Kuka." Gabanta ne ya yanke ya faɗi, ta ɗago ta zuba masa idanu, kenan wannan ne ɗan da aka ce Ɗanta ne?, ta yiwa kanta tambayar cike da Nadamar sanin Ramadan da ta yi a rayuwarta, yau an wayi gari ita da ko zancen Aurenta ba'a taɓa yi ba amma ita ce da Ɗa, fashewa ta yi da Kuka bayan ta ƙare masa kallo. ya turo baki ya ce "Ya ƙi denawa Baba." Shukriya ta ce "Za ta dena ka ji?" maida kallonta ta yi kan Halima cikin tausasawa ta ce "Ki yi haƙuri Halima komai ya wuce, kin ga ɗanki ma ba ya son kukan naki, ki yi shiru kar ki tayar masa da hankali." Inna ta ce "To, Allah gamu gareka, wato idan ka ji labarin Duniya sai ka raina kanka, Allah i yafe mana zunubanmu, Ke dai Halima wannan ta wuce sai ki yi ƙoƙari ki gyara gobenki." haka su ka ci gaba da yi mata Nasihu da shawarwari. Shahbeer kuwa tuni ya ja Shahzad su ka koma ɓangaren DR Malika. Alhaji Basiru Boza, Asalin sunansa Basiru Mahaifinsa Mukhtar, haifaffen garin Kano, Mutum ne shi me zafin nema da mugun son kuɗi, ko ta yaya ne komai wahalar aiki ya na yi don ya samu kuɗi, a gefe ɗaya kuma ya na da wata baƙar Aƙida tare da wani mugun buri wanda shine ya illata rayuwarsa, hangen abin da ya fi ƙarfinsa, matsayin na sama dashi, zama me kuɗi na bugawa a Jarida, Me kuɗin da zai gagari kowane me kuɗi a Nigeria, Mutum na farko wanda ya fi kowa Shahara ta fanni daban-daban. Waɗannan burikan ne cike taf a cikin rayuwar Basiru, sai dai cikin ikon Allah ko me ya taɓa wargajewa ya ke yi, babu Albarka a cikin duk irin Sana'ar da ya ke yi, rana ɗaya ya yi mafarkin ya je gurin boka daga nan Nasararsa ta fara, tin da ya yi wannan mafarkin ya ɗau Aniyar nemar inda Boka ya ke, haka ya yi ta bulayin neman bokaye har ya kai ga wani hatsabibin Boka, shi ne ya tsafe shi sannan ya ce masa ya je ya nemi Mata ya yi Aure sa'arsa ta na tattare da Matarsa. a cikin watan Ya nemi budurwa, cikakken wata ɗaya ba'ayi ba ya yi Aure, bayan watanni biyu ya ga ba canji kamar yadda Bokan ya faɗa masa kwana biyar shida ya yi yawa zai fara ganin kuɗi ta ko'ina gashi ba ta faru ba, don haka ya yi shiri ya koma, Boka ya ce masa ba itace matarsa me Arziki ba ya je ya nemi wata. sai da ya yi Mata kala biyar kafin ya Auro Furairatu, itace ta ɗan jima tare da shi sabi da ya na ɗan ganin canji ba kamar da ba, haka ya yi ta lallaɓawa da ita har ta samu Juna Biyu, duk da bai yi murna ba amma ya na tsoron ya yi mata abin da za ta gudu. Mommy, Asalin sunanta, Aisha, Mahaifinta Aminu, Haifaffiyar ƙasar Jigawa yankin Dutse, cikin Dangin Yawa ta taso, cikin gata da kulawar iyayenta, ta na Shekara 19 Wata ranar Laraba da yamma, Allah ya haɗa ta da Alhaji Boza, a Hanyarta ta dawowa daga Makaranta, gaisawa kawai su ka yi daga nan babu abin da ya ƙara haɗasu. tin a Daren ranar hankalinsa ya tashi burinsa gari ya waye ya je gurin Boka, ana yin Assalatu kuwa ya ɗau Hanyar zuwa, Boka ya sanar masa su ne su ke nemansa ya yi maza ya je ya Auro wadda ya haɗu da ita jiya itace Mahaɗin Arzikinsa. cikin murna ya koma kuma ya je har gidansu, da sigar yaudara ya je mata a matsayin me neman temakon ya marai-raice mata ya shimfiɗa zabga zabgan ƙaryayyaki har ya yi Nasara ta hanyar tura tausayinsa cikin ranta. haka ya ci gaba da jan ra'ayinta ya ɗimauta ta, da ya ke akwai Aikin Tsibbu a cikin lamarin bai sha wahalar kafeta ba, sannan ya tsiro da Labarin Aurenta Mahaifinta ya ce ya yarda sai dai YaYan Mahaifin nata ya ce sai dai idan ya mutu sannan za'ayi. da temakon Ƴarsa budurwa da ta ke son Basiru ya ke jajircewa akan Aisha ba za ta Auri Basirun ba, Hannatu itace ke zuga Mahaifin nata. haka akai ta gumurzu da ƙura amma ya ƙi Amincewa ganin haka ya sa sauran ƴan-uwan Mahaifinta su ma su ka ƴi Amincewa. Ita dai nata aikin kuka ne, ba ta ce dole sai ta Aure shi ba amma a yanayin halin da ta ke za'a fahimci ba ƙaramin so ta ke masa ba. Da Babanta ya lura ta shiga mugun hali sai ya yanke hukuncin Aura mata shi, ya sami Basirun ya gaya masa ya turo iyayensa. Asalin Mahaifansa sun gaji da karɓo masa Aure ya na wulaƙantawa don haka su ka ce ba za su je ba, maƙota da ƴan dattawa ya haɗa aka je aka karɓa masa Auren aka yi duk abin da za'ayi cikin kwanaki ƙalilan aka ɗaura Aure. a ranar Ƴan-uwan Mahaifinta su ka yi mata korar kare kaca-kaca, sannan su ka ce in dai ta ƙara zuwa Jigawa ma ba su yafe mata ba kar ta ƙara neman inda su ke babu su babu ita, haka Babanta ya haɗota da ƴan komatsenta ya bita da Nasiha da fatan Alkairi sannan ya ce kar ta ƙara zuwa ɗin sabi da a samu zaman lafiya. haka shine silar rabuwarta da danginta ta dawo gidan Mijinta Kano. Bayan wasu ƴan kwanaki ya fara wulaƙanta Furairatu, duk da Aisha ta na ƙoƙarin nusar da shi amma ya ƙi fahimta, dama dukanau ma ba son su ya ke ba don cikar muradinsa ya ke tare da su, cikin ɗan lokaci ya sallama Furairatu da cikinta na Ramadan, sannan ya dawo kan Aisha, anan ne ta fara ganin tashin hankali da azaba, tsafe-tsafe iri-iri Boka ya ke sa shi yi kuma itace Mahaɗin kowane irin tsafi da zai yi, a kowane irin hali na ƙazantarsa ta tsibbu a haka ya ke kusantarta, har yanka jikinta ya ke yi ya ɗebi jininta, abubuwan Azaba iri-iri na yau daban na gobe daban ga jarabar nemarta a kowane lokaci. dandanan kuwa Komai ya fara haɓaka ta fannin kasuwancinsa sai ya zamana duk abin da ya taɓa ya zama kuɗi kawai....... _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [1/8, 9:24 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 36 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. Yau ta tashi da wani Mugun zazzaɓi da ciwon kai, ko tashi tsaye ta kasa yi sabi da jirin da ya ke ɗibarta. kasancewar baya gidan tin Asbahi ya fice sai da ya dawo ya tarar da ita a kwance, cikin ko'in kula ya ce "Ina Karin Kumallona??" cikin girmama rashin imani irin nashi ta buɗe baki da kyar ta ce "Ba zan iya tashi ba zazzaɓi na ke." "Zazzaɓi?? kuma shine zai hanaki yiwa mutane Abinci?" wasu zafafan hawaye su ka shiga zirarowa ta gefen idonta, cikin rawar baki ta ce "Ka yi haƙuri, Don Allah ka kaini Asibiti." tsaki ya doka ba tare da ya ce komai ba ya fice daga gidan, ta saki wani wahaltaccen kuka tare da Addu'ar Allah ya kawo mata ɗauki. tin da ya fita bai dawo ba sai 12:00Am ya na shigowa ba abin da ya nufa sai ita ba tara da ya damu da halin da ta ke ciki ba. sai da gari ya waye ya ga dai da gaske neman Mutuwa ta ke yi sannan ya kaita Asibiti, anan ne likitoci su ka faɗa masa abin da bai masa daɗi ba cewar ta na da Juna biyu. Tin daga ranar tsangwama da kyara ta shiga tsakaninsu a cewarsa ba dan ta haihu ya Aureta, hankalinsa bai kwanta ba har sai da ya sa Bokansa ya Lashe ɗan cikin nata, ta sha baƙar wahala a lokacin kamar ba za ta rayu ba. bayan shekara ta ƙara samun wani cikin, a wannan karon wahalar har ta ci uban ta Da, abin da ba ya yi duka amma a wannan karon sai ya fara, haka ya ci gaba da azabtar da ita sai da Cikin ya kai wata Huɗu sannan su ka samu Nasarar rabata da shi. daga nan Boka ya tashi tsaye don hanata Ɗaukar cikin amma da yake rabo ya rantse sai ta samu na ƴan huɗu. kuma aka yi sa'a ya zo mata da mugun laulayi, sai dai duk yadda Boka ya buga ya kaɗa akan ya zubar da cikin ya kasa sai dai ta sha wahalar su miƙe tare. Yana zaune kan Sofa sai kumbura ya ke ya na cika da batsewa kamar zai fashe, ta na dai kallonsa ba ta ce komai ba, ganin ba za ta kula shi ya samu dalili ba ya sa shi cewa "Ki shirya gobe zan kai ki Asibiti." gabanta ne ya yanke ya faɗi don kuwa haka siddan ta san ba zai kaita Asibiti don neman lafiya ba, cikin sanyi ta ce "Me za mu yi a Asibiti??" a masife ya ce "Ina ruwanki??, jarababbiya ƴar bala'i wannan cikin naki ƙila maye za ki haifa ko Aljani, ki kalli yadda ki ke shan wahala amma ya ƙi fita, ai kuwa dole ne ya zube don ni ba zan tara ƴa-ƴa ba, ni ba dan ki haihu na Auro ki ba, gwara ki yi mini abin da na ke so kawai in ba haka ba ba za ki gaji da wulaƙanci ba." murmushin takaici ta yi kafin ta ce "Da zan haifi Aljanin ma zan ji daɗi ko dan ya Addabi rayuwarka, Azzalumin banza." ya ce "Oho dai, na faɗa ciki ne sai an zubar." banza ta yi masa ya ƙaraci bala'insa ya yi shiru. Washegari ya ɗibeta riya-riya akai Asibiti, a lokacin ne Allah ya haɗata da Dr Idris. kuka ta dinga yi ta na haɗa shi da Allah akan ya ƙyale mata Ɗanta, da ya lura ta fi Mijin nata gaskiya sai ya temaka mata, sannan ya ce duk randa matsalarta ta tashi ta neme shi, sannan ya bata shawara akan kar ta bari ya san cikin ya na nan. Tin daga wannan ranar DR Idris ya zamto haske a gareta, shine kaɗai me temaka mata ta fannin cikin jikinta. Cikin wannan baƙar wuyar har cikin ya girma, babu irin masifar da Alhaji Boza bai yi ba akan cikin amma dole ya haƙura don Allah ya riga ya rubuta sai sun zo Duniya. Tin safiya ta ke jin ciwon naƙuda sa'i-sa'i ita kaɗai tai ta rarrashin kanta har dare ya yi lokacin abin ya ta'azzara, haka ta dinga kuka ta na roƙonsa akan ya kaita Asibitin amma ya ƙi da ta dame shi ma sai ya bar mata gidan ko fitila babu, haka tai ta majau-jawa cikin wannan mugun halin har gabannin Asbah sannan Allah ya bata ikon Haihuwa; duk wani kicimillinta ita kaɗai ta yi ba ta da matemaki sai Allah, da temakonsa ta gyara kanta ta gyara ƴaƴanta. Wunin ranar cirr ko Abinci ba ta samu na sawa a bakinta ba gashi ko kare bai leƙota ba bare ta sa rai, ta yi kukan har ta gaji ta dena, ta na cikin mawuyacin hali, ƴan-huɗunta kawai ta ke kalla ta ji farin ciki duk da baƙin yanayin da Basiru ya jefata. sai da ya gama abin da zai yi ya koma gidan ya tarar da ita da ƴaƴa huɗu rigis, ya yi mugun mamaki don kuwa bai taɓa zaton hakan ba, lokaci guda muguwar ƙiyayyar yaran ta gama ratsa dukkan sassan jikinsa. haka ta raine su ita kaɗai har su ka yi wayo in banda cin Mutuncin ba abin da ta ke fuskanta daga gareshi. Shahbeer, tin ya na yaro ya ke da halinsa na ko'inkula sai dai kuma a haka ne kamar bai damu da kai ba, amma a gaskiyance duk wani motsi na Ɗan-adam ya na lure da shi kuma ya na fahimtar inda ya dosa, ya na da nutsuwa da mugun wayo amma wayon ba na fitina ba na gane halin da Duniya da mutanen cikinta su ke ciki. Duk wani rashin mutunci da Alhaji Basiru zai tufkawa Mahaifiyarsa ya na ji kuma ya na fahimta sai dai ko uffan ba zai ce ba, su Shahmeer ne ma masu ƙoƙarin yin kuka in sun ga ta na yi. ba ta taɓa tunanin Zai zamo mata garkuwa ba sai wata rana da Alhaji Basiru ya kamata ya yi mata shegen duka, shi kuma da ya tashi ya ɗauko kwalbar turare ya jefe masa kai, ai kuwa ya kama shi ya yi masa dukan tsiya. Tin daga ranar kafin Basirun ya jibgeta zai shiga tsakaninsu ya ce sai dai a dake shi, haka zai ƙaraci Masifarsa ya haƙura. DR Idris ne ya sanya su a Makaranta ta Islamiyya da ta Boka, idan biyu su ka je Islamiyya da safe sai biyu su je Boka da yamma, ya rarraba su ba makaranta ɗaya su ka yi ba, kuma da sun dawo cikin gida ba ƙara fita su ke yi ba, hakan ya sa Mutane su ka kasa bambance ƴan-huɗu ko ƴan-biyu. Shahzaib ya na da Zuciya har ba ya iya tausarta idan ta riga ta yunƙuro. Shahmeer kuwa haƙuri gareshi har ya amince ya yi kuka akan ya ƙwatarwa kansa Ƴanci. Shahzain idan aka ƙular da shi bashi da sauƙi, amma duk ya fi su tsokana. Shahbeer kuwa Duniyar ma ba za'a ce ya damu da ita ba duba da yadda yanayinsa ya ke, kowane irin firgici zai gani ba zai taɓa baiyana rauninsa ko asalin abin da ke cikin Zuciyarsa ba, a zahiri ya na da haƙuri da kauda kai duk abin da akai masa ba zai tanka ba, amma a gaskiyarsa Sai ya ɗau Fansa, kamar Maciji haka ya ke ta wajen a taɓa shi ya rama, ba ya faɗa ko hayaniya a gaban ƴan-uwansa sai ya raka su gida sannan zai koma ya nemi mutum, wannan dalilin ya sa yara su ke shakkarsa; Gashi tin su na yara su ke da maƙiya waɗanda ba sa ƙaunar ganinsu cikin zaman lafya da kwanciyar hankali. Yau ta na zaune ta na yi musu Nasiha akan su tsaya iya matsayinsu kar su yi shishshgi wa mutane, Wata mata ta yi sallama, Mommy ta amsa cikin sakin fuska ta ce "Sannu da zuwa, ga kujera nan don Allah zauna." a fusace matar ta ce ''Ni ba zuwa na yi don mu gaisa ba, Wallahi yaron nan naki sai ya janyo miki

Chapter 24 of 30