Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yasa na ke neman temakonki mu haɗu mu tona musu asiri. Mamakin Maganar Safyan ya gama sumar da Shukriya a tsaye, lamarin ya gama ɗaure mata kai lallai kuwa idan da gaske ne ba abin da zai hana ta rufe ido ta fallasa su tin kafin shirin su ya kai gacci, da kyar ta iya cewa "Da gaske na maganar nan ka tabbata? ko dai bahaguwar fahimta ka yi musu?" "Shukriya na san ba lallai ki yarda kai tsaye ba sabi da abu ne wanda ba zato ba tsammani, ba wanda zai taɓa zaton za su aikata haka duba da yadda su ke da adalci a idon Duniya ashe duk su na yi ne don su tarwatsa Ƙasarmu, Idan ba ki yarda ba Ki binciki Kayan kamfanu-nuwansu waƴanda ki ka lissafa min ɗazu za ki ga akwai abubuwan da su ka fara canjawa, sannan ki bincika a gidansu ma yanzun haka akwai wata yarinya da su ka lalatawa rayuwa kuma ta na gidansu sun maida ita Karuwa Wata ƙanwar abokina ma...; zan turo Ɗan-sandan da ya ke tayani bincike ya kawo miki sauran bayanan sai ya yi miki bayanin da kansa wala-alla ki fi yarda, abin dai ba daɗin faɗe Shukriya, amma idan hakan zai jawo miki matsala ba sai kin temaka mini ba Allah zai yi maganinsu. Ya ƙarasa maganar gami da tattaɓe fuska ya na shirin fashe mata da kuka. Na yarda da Adalcin mutanen nan ɗari-bisa-ɗari, a da su na burgeni sosai ashe Azzalumai ne. tunanin da ta ke kenan a cikin ranta, zuwa yanzu tsananin tausayin Safyan ya kamata ya haƙiƙance wajen tseratar da bayin Alllahn da basu ji ba ba su gani ba, me kuwa zai hana ta temaka masa su yi aikin Alkairi su temaki ƙasarsu daga tarkon azzalumai?. Murmushi ta yi cike da son kwantar masa da hankali ta ce "Kar ka damu, ka turo min bayanin komai ɗin, In Allah ya yarda kamar an yi an gama ne, nima ba zan zuba ido a cutar damu ba zan yi iya bakin ƙoƙarina." Murmushin yaro bai san wuta ba Safyan ya sakar mata gami da cewa "Ki yi haƙuri fa daga haɗuwar mu zan wahalar dake, amma ina ganin idan ra'ayinmu ya zo ɗaya ta nan ɓangaren Soyayyarmu za ta fi ƙayatarwa." Ta yi murmushi gami da cewa "Haka ne kuma, Don Allah idan ba damuwa ina son komawa gida." "Har kin gaji da ganina ne?" ya yi maganar cike da yaudara. girgiza kai ta yi kafin ta ce "A'a ko ɗaya, ba zan iya gajiya da ganinka ba ai." ya murmusa "Mu je in kai ki da kaina. ba ta yi magana ba ta shige mota, shima shiga ya yi sannan ya figeta su ka bar wajen. Ta na fitowa bakin layinsu ta yi karo da Bashir, yau ta sakar masa fuska ba laifi ba su rabu ba sai da ta tabbatar masa da alaƙarsu za ta ci gaba, ya nuna mata matuƙar farin cikinsa da jin hakan, ita kuwa duk hakan bai yi mata ba don ba ta tashi ta ke ba. Ta na yin Sallama a falon gabanta ya yanke ya faɗi jin yadda Malika ta ke kuka tare da faɗin kowace irin magana ce ta zo bakinta akan Shahbeer, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta gaida Mommy, ba ta iya amsawa ba sabi da kuka da ta ke yi ƙasa-ƙasa, maida kallonta ta yi ga Inna gami da gaisheta, duk da ta na kuka amma hakan bai hanata amsawa ba cikin rawar murya irin ta wanda ya ke kan gaɓar kuka. miƙewa Ma'arufa ta yi ta nufi kicin, kasa aikin komai ta yi sabi da raunin da Zuciyarta ta yi sai nemar guri ta yi ta zauna. ciki-ciki Shahzaib ya yi sallama a Falon, bai jira a amsa ba ya shigo ciki, Zuciyarsa tafarfasa ta ke sabi da irin ƙyamar da Mommy ta ke nunawa ɗan-uwansa, bai taɓa zaton abu irin wannan zai ratso cikin rayuwarsu kuma har Mommy ta yarda za su iya aikatawa ba, jin Malika ta na ta surutai ba ƙaramin fusata shi ya yi ba, "Fisabilillahi Mommy Allah ya baki ɗa me kyakkyawar Zuciya irin Shahbeer amma ki ke bin shi da wannan mugun zargin?, ban zaci za ki yi wannan tunanin akan mu ba har ki zauna ana faɗen maganar banza akan ɗan-uwana ki na ji, idan ma Shahbeer ɗin ne ya za ki yi tin da kin haifa ai dole ki rungumi ƙaddararki, Na gaji da wannan lamarin naku gaskiya Mommy in dai ba za ki dinga jansa a jiki kamar da ba mu ma za mu barki da waƴanda ki ke so, dama ai ba tin yau ba an so farraƙamu Allah bai ida nufinsu ba, to yanzu sun yi Nasara tin da har sun iya sa rashin yarda a tsakaninki da ɗan da ya baki ci da sha kuma ya ke kula dake fiye da rayuwarsa ya fi kowa sanin abin da zai ɓata miki rai kuma ya fi kowa gudunsa, yanzu Mommy ta ware miki don Allah ki tarkara ki koma gidansa da zama shine zan san kin yi fushi damu, Halimatu kuma za mu iya riƙeta har Allah ya rabata da abin da ke jikinta. Inna ce ta fashe da kuka ta na cewa "Yanzu ɗannan ka na nufin ni ce na farraƙa ku da Mamanku?,, wallahi Allah ban aikata ba kuma ba ni da niyyar yin hakan Allah kuwa." a tsawace ya ce "Ke wa yake ta taki??? wa ma ya sako ki cikin zancen nan?, ana maganar mutane masu jini a jika ki na tsomo baki salon ki tarwatsa min Zuciya ke baki san in ran mutum ya ɓaci ki yi masa abin da zai ji sanyi ba?" Malika ce ta miƙe tsaye cike da tsiwa da kuma ɓacin rai da raɗaɗin da Zuciyarta ke mata ta ce "Ba da ke ya ke ba Inna, a ganinsa ke ba ki isa ki farraƙasu ba sai dai ni, ni ka ke tunanin zan rabaku da Mahaifiyarku bayan ɗan-uwanka shi ne ya aikata laifin, To wallahi banzan tunaninka bai faɗa maka gaskiya ba, ƙaryar mutum ya ce zan yi haka ai So..." wani fitaccen mari ya sheƙa mata hakan ya dakatar da maganar da ta ke yi ba dan takai ƙarshe ba, cikin fusata da rufewar ido ya zare belt Ya fara Dukanta ta ko'ina. Mommy da Inna ne su ka fara kici-kicin ƙwatarta amma sun kasa don kuwa idan ya hautsine sai ta Allah. Tsawa Shahbeer da ya fito yanzu ya daka masa, ya yi wirgi da belt ɗin gami da shafar kansa, ya fara Zarya a wajen ya na mita "Wallahi da ka barni na farfasa mata jiki tin da ba ta da hankali, mu za ta zo ta yiwa maganar banza anan?. Shahbeer ya ce "Ya isa mana, komai na Duniya fa ɗan haƙuri ne komai ya na da lokacinsa da ya wuce shi kenan wataran sai labari, ka wuce ka koma sashinmu ai da ba ka fito ba da kunnenka bai ji maka abin sa zai ɓata maka rai ba." bai yi magana ba ya wuce. kallon Malika ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Anan za ki kwana ne ko tafiya za ki yi?" wata shegiyar harara ta zuba masa kafin ta yamutsi ɗankwalinta da jaka ta yi hanyar fita. cikin ɗan ɗaga murya yadda za ta ji ya ce "Ke fa Likita ce ki na da buƙatar nutsuwa ko dan Al"ummar da ki ke temakawa, to ina ganin shiga sabgar wani ba taki bace ki manta kawai, me faruwa dai ta faru ba wanda ya isa ya canja abin da Allah ya rubuta akansa ko akan wani, ina so ki dinga tunawa da haka. sai da ta tsaya ta gama saurararsa sannan ta ja tsaki ta fice. "Mammi ki yi haƙuri don Allah ki rage damuwa, ni da ta shafa ku barni na ji da damuwata don Allah. Ko uffan Mommy ba ta ce ba ta nufi sama, ya rakata da ido ya na mamakin irin bahagon tunanin da ta ke akansa, muryar Inna ce ta katse masa tunanin. "Um!!! Sahun Keke ba'a gane gabanka!!!" Murmusawa ya yi kafin ya ce "Da haka dai akai min Laƙabi Inna, amma me fahimta ai ya na ganewa, kin ga Momma ma ta kasa fahimta duk da cewar itace ta haifeni." "Kar ka damu Shahbeer indai kasan da gaskiyarka ai rashin fahmtarta ba zai tauyeka da komai ba, Wataran za ta fahimta ka ji?" ya gyaɗa kai sannan ya wuce sashinsu. Malelekuwa kawai ta ke yi ta rasa ina za ta sa kanta ta iya bacci, tunanin babban lamarin da ta ɗaukarwa kanta kawai ta ke, tabbas ba dan ta na son Safyan ba da ta haƙura da aikin nan sai dai yadda ta lura idan ta ce ba za ta yi ba zai ce ba ta son shi kuma shi ma ya ƙi sonta dalili kenan da ya tsirko da zancen a lokacin da su ke ƙoƙarin fahimtar juna, Soyayyarsa ce ta tilasta mata sakin labarin da ba za ta so ace daga Ma'aikatarsu ya fara fita ba amma ba yadda za ta yi dole ta yi hakan. har washe-gari jinta ta ke kamar an yi mata shegen duka, haka nan ta shirya ta fita aikin, tararwa ta yi Fatima ba ta samu zuwa ba sakamakon Tafiya da ta yi hakan ya ƙara kashe mata jiki sosai, ita kaɗai ta gudanar da aikinta. Kamar yadda Bayanan Safyan su ka nuna da kuma yadda ya bata labari haka ta wallafa tare da bawa mutane tabbaci akan su dakata da amfani da duk wasu abubuwa da su ka Shafi kamfanin DOUBLE TWO STAR musamman abin da ake ci ko ake amfani dashi ta kusa da ci. kafin Azhar Labari ya gama karaɗe mutane da yawa kuma ya yi matuƙar ɗaga musu hankali da rikita tunaninsa, wasu a ciki baƙin cikin Rashin imanin Lalata Ƴa-ƴa mata da sayar dasu ya fi ɗaga musu hankali, wasu kuwa Neman kashe su ta hanyar sanya guba a cikin abin da su ke amfani dashi ya fi ɗaga musu hankali, ko mutum bai ji labarin ba idan wani nasa ya ji sai ya ɗaga waya ya kira ya sanar masa don kula da kai da kiyaye lafiya. Abeer ne ya yi sallama bai jira an amsa ba ya ƙaraso hankali tashe ya ce "Inya, ba ku san abin da ke faruwa ba?" "E ba mu sani ba. miƙa wa Shahmeer wayar ya yi gami da cewa "Duk Social media ta ɗauka abin da ake tattaunawa akansa kenan a yau, wata Yarinya ƴar-jarida HAUWA'U IBRAHIM ita ce ta fara wallafa labarin kuma tare da tabbaci, har da wai ba ku da Uba. Murmusawa Shahbeer ya yi kafin ya ce "Dama nasan don hakan aka shirya haɗuwata da Halimatu, to ba komai dama ai bamu da Uba, amma abin da mutane su ka kasa fahimta kuma su ke ban mamaki akai, ai ba sai ɗan halak Allah ya ke wa arziki ba, sannan shi wanda ba ɗan halak ba ai ba laifinsa bane laifin iyayensa ne To ina ganin bashi da laifi bare har a nuna tsana da kyara gareshi, shima kuma mutum ne kuma ɗa ne kamar kowa bambancin kawai wani da Aure aka haifeshi wani kuma ba da Aure ba, amma duk ɗaya ne ko a gurin Allah bambancinmu wanda ya fi tsoron Allah shine sama da mara tsoron Allah, ni fa hakan bai wani tiƙa ni da ƙasa ba don gaskiya su ka faɗa ba mu da Uba, batun fyaɗe kuma Ai ku ma ba ku da tabbacin ba ni na yi ba tinda har Mahaifiyata ma ta yarda na aikata nima na yarda na aikata ko da a mafarki ne ko a ido biyu yayin da bansan na yi ba, abin da dai ban san da zaman shi ba shine batun cutar da Al'umma da guba a cikin abinci da kuma sayar da ƴaƴan mutane, wai Zubisss!!!!!! kenan. ya ƙarasa maganar ya na dariya. "Ya'akai Zuciyarka ta ƙeƙashe ta bushe haka Shahbeer??" Shahzain ya jefo masa tambayar yayin da idanunsa su ka rikiɗa su ka yi wani kalar ja su ka cicciko da ƙwallah. "Auta idan ka ce komai zai ɓata maka rai wata rana za ka rasa abin da zai ɓata maka ran, kasan komai akwai lokacin da ake buƙatarsa, Waye Mahaifinka Shahzain?? tare da kai mu ka fita ranar da na zo da Halima gidan nan?, a'a, duk ba ka san abin da ya faru ba Sai Allah, Ni dai nasan ko abu makamancin haka ban taɓa aikatawa ba to me zai sa na ɓata raina akan abin da ya damu wani??, na gamu da mutane iri-iri a rayuwa akan gaya mini indai Allah ya ɗagaka zaka samu ƴan-baƙin-ciki da ƴan-hassada da maƙiya, ban yarda ba sai da na fara gani a zahirance, ku barsu su yi abin da su ke ganin za su iya. Shahzaib ya ce "Hmm!!, ZARE Ba'a san kanka ba ba'a san ƙafarka ba, ku bar Shahbeer daga baya zai gaya muku asalin Lamarin." Abeer ya nemi guri ya zauna ba tare da ya ƙara magana ba dan kuwa ya yarda da maganar Shahzaib shi ma ya fahimci Shahbeer wani rikitaccen mutum ne wanda a cikin idanunsa ko akan fuskarsa ko a furucin bakinsa ba za ka taɓa gane abin da Zuciyarsa ta ke kitsa masa ba bare wanda ke lulluɓe a cikinta. Mommy da ke tsaye ta na sauraren su ta fice ta na kuka. shiru gurin ya yi har tsawon wasu mintuna. Shahbeer ne ya katse shirun da cewa "Wacece ita Yarinyar?? lallai a kawo min bayanai akanta, ni yanzu na san dole Hukuma ta kama ni, sauran hukunci ya na hannunku. Shahmeer ya ce "Okay Boss" miƙewa Shahbeer ya yi ya nufi sashin da Inna take don ganin Halimatu dan acan take. su na zaune ita da Inna ta na yi mata sokana ita kuma ta na biye mata, kusa da Inna ya zauna kafin ya ce "Inna sannu fa na gode da bata kulawa." "Ba Komai ɗan-motsin gadon Ummansa." ta yi maganar cikin sigar Zolaya. ci gaba ta yi da cewa "Allah sarki Shaƙuwar nan taku kullum ƙara gaba ta ke yi gashi ba ka san da wace manufa ta ke tare da kai ba." "Ni na sani Inna, yanzu ma na ƙara fahimta, da na yi tunanin ta na da laifi amma yanzu na gane itama ba laifinta bane, Sun riga sun yi abin da su ke son yi kuma sun yi Nasara; Don Allah ki ci gaba da kula min da Halima har zuwa wani ɗan lokaci kar ki bari wani abu ya sameta. "In Allah ya yarda zan kula da ita sosai har ma da temakon wannan ƴa Ma'arufa, Allah ya ɗora ku akan maƙiyanku Jikana. Da Amin ya amsa, zai yi wa Halima magana wayarsa ta fara ƙara, ɗauka ya yi tare da yin shiru, a ɗaya ɓangaren aka yi sallama sannan a ka ci gaba da cewa "Adam Ridwan, Daga Hukumar kare Haƙƙin Ɗan-adam, a bisa wani labari da ke yawo yanzu ka shiga hannun mu, za mu yi bincike a sirrince sabi da Mutunci da Darajarka, don haka mu ka yi saurin shiga lamarin kafin wata hukumar ta shigo har Duniya ta san matakin da ake kai, maganar gaskiya ba mu da Hujja ko Dalilin da za mu ɗora maka laifin sai dai dole ne tsananta bincike akanka don haka za mu killaceka, yanzun haka akwai Jami'inmu ya na ƙofar gidanka, ka biyo shi ku taho salamun alaika ba wata hayaniya." "Okay Thanks. Shahbeer ya faɗa sannan ya katse wayar. ido ya zubawa Halima har na ɗan wani lokaci..... jiki na tsuma da kakkarwa ALHAJI BASIRU BOZA ya tsinkawa SAFYAN wani mugun azababben Mari..... _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO'* [12/16, 10:54 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 17 Free Book Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* MOONASH ELEGANT ONLINE WRITES. Jiki na tsuma da karkarwa Alhaji Basiru Boza ya tsinkawa Safyan wani Mugun azababben mari,,, sai da yaga taurari na azaba sama da ashirin suna giftawa a cikin ganinsa. cikin razani gami da ɓacin rai Mom ta yo kansu ta na cewa "Ka yi hauka ne Alhaji da ka ke yiwa Safyan irin wannan mugun dukan, anya lafiyarka ƙalau kuwa???" a fusace Zuciyarsa na dakan shalugude ya ce "Ni mahaukaci ne mana tin da Duniya ta sa na bi WATA HANYA mara ɓullewa, NA CUCI KAINA, Astagfirullah wa'atubi'ilaika Ya-Allah, Safyan kasan waye Shahbeer a gurina kuwa?? ka san me ka taɓa? me yasa za ka aikata hakan? shi kenan ka gama kassarani ka cuceni yau tawa ta ƙare ba ni babu wata rayuwa me daɗi a doron Duniya." cikin tsananin mamaki Safyan da ya farfaɗo da kyar, ya ce "Ban fahimci me ka ke nufi ba Dad, duk wannan abin da ka ke wai na mene? kai dai ba burinka ka kaisu ƙasa ba kuma nima ai hakan na yi." "Rufe min baki Dan-ubanka Safyan mara hankali, wallahi ka ji jiki Alhaji wannan ai abin kunya ne abin ayi mana Dariya, har da sa hannu ka marar min ɗa sabi da wasu ƴan-iska to lalata goben su yanzu muka fara, sai na yi kaca-kaca da aniyarsu sai na sa sun bar baƙin tarihi a Duniya, wallahi tallahi indai ni haifaffiyar Cikin uwata da ubana ce sai na ɗaiɗaita su, kuma mu zuba ni da kai mu ga wa zai kwashe, yanzu muka fara kuma ba zamu dena ba yanzun hakan ma matakin gaba na tarwatsa su za mu hau, in ya so kai ma ka tarwatse tin da ɗana ya tsaya da ƙafafunsa. Mommy ta na gama maganar ta ja hannun Safyan su ka bar wajen a fusace. "Tsakani na ga Allah ban san ya aikata ba Muktar wallahi ban san haka zai yi ba da na ɗaureshi tin kafin ya ɗaure kansa, nasan karo da kai ba Nasara na yi nadama na saduda, Shi kenan Safyan ka gama illata min rayuwa na shiga uku. cikin fitar haiyaci ya ke maganar, jaɓar ya zauna akan kujera gami da rushewa da wani fitinannen kukan da bai san ma ya na yi ba dan ba'a haiyacin sa ya ke ba. Ido ya Zubawa Halima har na ɗan lokaci sannan ya yunƙura ya tashi gami da cewa "Inna Hukuma za ta yi bincike akaina, kar ku wani ɗaga hankalinku." rarraɓe baki Inna ta yi ta fara kuka ta na cewa, "Dama nasan za'a takan haka, itama A'i tsoron da ta ke kenan shi ya sa ta ke damuwa; ba zai iya zaman rarrashinta ba dan haka ya ɗaga ƙafarsa da nufin ci gaba da tafiya, caraff ya ji Halima ta riƙe hannunsa ƙam,,, cakk!! ya tsaya gami da jan wani dogon numfashi ya kasa sauke shi, hatta idanunsa sai da su ka ƙara girma dan kuwa bazata ta yi masa bai yi tunanin ma za ta kula shi ba har ya fice. miƙewa ta yi ta na riƙe da hannun nasa ta zagayo ta tsaya a gabansa ta na fuskantarsa cike da sokonta da maganarta irin ta ƴan koyo ta ce "Tafi ja ka barni ko?" yadda ta yi masa firi-firi da ido ya bashi damar jefa ƙwayar idonsa cikin ta-ta, lokaci guda ya lula Wata Duniya me cike da tunane-tunane da SARƘAƘIYA iri-iri, gefe guda kuwa wani mugun rauni Zuciyarsa ta yi sabi da tsananin tausayinta da ya yi lulluɓi ga Zuciyar tashi, cikin rawar murya ya ce "Zan Dawo Halimatu!!" noƙe kafaɗa ta yi gami da cewa "um-um Baby Cunana." Wani susutaccen murmushi ne ya suɓuce masa, ya lumshe Oily Eyes ɗinsa cikin tattausar murya ya ce "Baby!!! Zan dawo" sake maƙale kafaɗa ta yi gami da rungume hannunsa a cikin ƙirjinta ta na murmushi irin na shiri-shiri ta ce "Jan je." girgiza kai ya yi "Baby A'a. Shagwaɓewa ta yi kamar za ta yi kuka ta ƙara cewa "A'a Jan je." zai yi magana muryar Mommy ta dakatar dashi "Ka fita sabgar ɗiyar mutane Inya!!!!. a ɗan kunyace ya zame hannunsa ya na ɗan sosa ƙeya ya yi gaba, Halima ta zube a gurin ta saki kuka ta na tirje-tirjen ƙafafu a dole sai ta bishi; da sauri Inna ta yo kanta ta shiga rarrashinta. "MUKHTAR!!" Mommy ta kira sunansa, dakatawa ya yi da tafiyar har ta iso inda ya ke, "Inya, duk abin da ka ga na yi akanka ba dan ba na sonka bane sai dan nima macece: uhm, za ka iya tuna rana irin wannan??" kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ɗan murmusa ya ce "Uhm, ba na jin zan manta da ita Mamma." "Yau ce karo na farko da waccan ranar ta maimaita kanta, yau ma gashi Hukuma ta kamaka, ba na so ta uku ta zo don bana jin za ta yiwa kowa daɗi, Shahbeer nasan ka na da ƙarfi da isar da za ka murza hannunka a shafe babin labarin nan, A'a ba na son hakan Don Allah ka bari gaskiya ta yi aikinta bincike zai nuna, ba na son ka sa koda baki akansu bare ka dafa da hannunka ka barsu su yi aikinsu. ɗan murmushi ya yi a ransa ya ce ''Na riga na kunna wutar kuma ai Mommy." a zahiri kuwa cewa ya yi "Zan yi iya bakin ƙoƙarina dan kawar da kai daga kan lamarin, na yi miki alƙawari Mama." murmushi ta yi gami da cewa "Allah ya tsare." "Ga Halima nan dai, Amanata ce. yanab faɗen haka ya yi gaba. A hanyar fita ya yi karo da Baba, hankali tashe ya ce "Ya'akai haka Shahbeer?, waye ya ke yaɗa banzan labarin nan ne?" "Baba wai sunanta Hauwa'u ni ko saninta ma ban yi ba ashe Celebrity ce ma kowa ya santa. ya yi maganar ya na dariya "Dariya ka ke Inya? ni fa hankali tashe na tawo da na ji Hukuma za ta kamaka, kasan mutane ba imani wasu ƙiris su ke jira su tozarta ka akan abin da ba ka ji ba, ba ka gani ba. lumshe ido ya yi gami da cewa "Ashsh!!sha Baba, kai ka fara kama Aljani to ka yi ma ya-ya dashi? ina ma za ka aje shi.??" Baba ya murmusa gami da cewa "Haka ya ke wannan Ɗan Albarka, zan yi duk yadda zan yi dan na fitar

Chapter 10 of 30