Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ki san wa ki ka zaga. "Kai ɗin Banza? me ka isa ka yi?" "Maza koma cikin gari ki ji me ke faruwa hhhhhhhh. da sauri ta tashi a mugun tsorace ta haɗa da gudu don tafi saurin dawowa gida ta ga me za ta tarar. Sun gama hira kenan shi da iyalinsa ya miƙe da zummar komawa sama, yanke jiki ya yi ya faɗi, su ka yi kansa cikin sauri, Shahbeer ne ya rungumo shi a jikinsa hankali tashe ya ce "Babana meke faruwa?, Shahzain ɗakko Mukullin Mota mu je Asibiti. a wahalce ya fizgo muryarsa da ta cunkushe da kyar ya ce "Zuwanmu Asibiti ba zai hanani Mutuwa ba ƳaƳana, lokacina ya yi dole sai na tafi, ku yafe mini, ku yafe mini don Allah ku yafe mini, sannan ku raini junanku ku riƙe junanku da Iyalinku Amana, ku riƙe Alƙawari kar ku bar Zumuncinku ya tarwatse har bayan-bayanku, kui ta Haɗa ƳaƳanku Auren Zumunci hakan zai temaka wajen Cure Iyalinku guri Ɗaya; ni yanzu tafiya Zanyi, wa'adina ya cika." Tini kowa ya fara kuka amma banda Shahbeer da ya ke jin kamar zaiyi hauka, ga tsananin Tashin hankali da wata muguwar Azaba da Zuciyarsa ta ke yi, "Baba, mu na buƙatarka don Allah kar ka barmu." Duk su huɗun har ma da Mommy Magana su ke yi masa amma ya kasa amsawa, Sa'ad ma ya kasa magana sai kuka me tsananin zafi da taɓa Zuciya. _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [1/18, 6:19 PM] INDO CE: *WATA HANYA* 43 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. Dogon Numfashi ya ja idanunsa suka jujjuye zuwa sama. "Innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un" kalmar da su ke ta maimatawa kenan, Shahbeer tin da ya zuba masa ido ya kasa motsawa har Allah ya yi hukuncinsa, gaba ɗaya ya rasa wace Duniyar ya ke, duk tsananim Rayuwa bai taɓa jin ya na Barar Mutuwa ba sai a wannan lokacin da ya na ji ya na gani ta Ɗauke Mahaifinsa Ɗaya Tilo da ya Mallaka a Duniyar nan. Mommy ce ta dafa kafaɗarsa ya yi saurin Zaro idanunsa da su ke masa Zugi kamar an watsa Attaruhu, Hannu ta sa ta shafe idanun Alhaji Boza suka rufe, ta ƙara fashewa da wani sabon kuka me tsuma Zuciya, cikin Shashsheka ta ce "Mun rasa shi Shahbeer, sh kenan Rayuwar ta zo ƙarshe." "Ki dena kukan nan Umma Don Allah, mu yi masa Addu'a ya fi buƙatarta fiye da komai, Halima ki ɗauki wayata ki kira Ramadan da Safyan; Malika kema ki gayawa Baba, Shahmeer Ku tausayawa Rayuwata Ku dena kuka Don Allah kar ku sa nima na Mutu, ba zan iya Jura ba abin ya yi mini yawa." Yadda ya ke maganar ma kaɗai ya isa tabbatar da irin yanayin azabar da ya ke ciki, tabbas Mutuwar Alhaji Boza ta bala'in girgiza shi, abubuwa da yawa ne su ke dawowa cikin tunaninsa har da wanda ya faru tin ya na ɗan ƙarami, ganin kukan ƴan uwansa kuwa ya fi komai ɗaga masa hankali gani ya ke kamar masifar ba ta ƙare ba. Har aka kammala haɗa shi aka kaishi gidansa na gaskiya ko ɗigon Hawaye babu a idanun Shahbeer sai dai kukan Zuci ko magana da kyar ya ke iya yinta. Mom Safyan Ihu ta fasa lokacin da labarin Mutuwarsa ya risketa, ta tume a ƙasa ta na burburwa da ihu ta na cewa "Shi kenan tawa ta ƙare tsinanne ya mutu ya tafi da komai, Allah ya isa tsakanina da kai Basiru, ba zan yafe maka ba baƙin Azzalumi , ka gama da rayuwata ka cuceni ka tafi da duk abin da na tara, wayyo Allah na shiga uku na lalace." Safyan da ya gama burkicewa ya ce "Ai ba ki lalace ba sai kin je duk inda Dukiyarsa ta je kin ga yadda ta ƙone ƙurmus, in ba ki sani ba duk wata Dukiya ta shi ta zama ƙasa ta ƙone ba ita a Duniya, wallahi kin shiga ukunki Mom, wallahi ke ce ki ka cuce ni ke ki ka ɗora ni a Wata Hanya wallahi ba zan yafe miki ba Duniya da Lahira, baƙin halinki sai ya bi ki, ni ba ni ba ke har Abada, na ji ma na tsani kaina kasancewar ke ki ka haifeni, gidan da mu ke ciki ma ya kama da wuta sabi da ba Dukiyar halak bace, Allah i la'anci lamarin Shirka da tsafe-tsafe." bayan ta gama saurarensa ta yi kururuwa ta yo kansa ta shaƙe shi da ƙarfinta na gaske ta na cewa "Ƙarya ka ke munafuki algungumi kaima sai ka ɗanɗana irin ƙuncin da na ke ji kashe ka zan yi in huta, dama na san sai ka koma son tsinannun Ƴan-uwan nan naka, sai na kashe ku duka!!!!" cikin ƙaraji da daddagewa iya ƙarfinta ta ke maganar. Mutanen da ke gurin ne su ka yo kansu don bashi agaji, sai da aka sa ƙarfi aka yi da gaske sannan aka iya ƙwatarsa bayan ya gama galabaita ta na sakinsa ya faɗi a sume. Baya-Baya ta yi kafin ta yage ɗankwalinta ta ƙwalla kururuwa ta durfafi Mutane ta na cewa "Ƙarya ku ke Ƴaƴan matsiyata kuma sai kun Mutu, abin da Basirun nice na ke Bashi shawara akan abin da zai yi, wallahi ni na sa shi ya ke komai, na ce ya saki Aisha ya ƙi munafiki sai da ya mutu da Aurenta, wallahi ma duk ni na temaka masa ya samu wannan Dukiyar ni ce ma na haɗashi da Bokan da ya yi masa Tsubbun har ya samu kuɗin, amma da yake tsinanne ne kun ga ya na Mutuwa Kuɗin sun zama asara duk sun ƙare wasu ma sun ƙone to yanzu in banda Tsinantaka wane gidan zan kwana?? ai da kun sani kun ƙona shi shima la'ananne." Surutai ta ke jerowa iri-iri ta na yi ta na kaiwa mutanen da su ka taru maƙil cafka, ganin ta tabbata Mahaukaciya ya sa Aka samu jarumai su ka riƙeta akai mata Ƙullin goro sannan aka nemi Masu tallafawa Mahaukata, Safyan kuwa Asibiti aka nufa da shi don bashi temakon gaggawa, bayan an duba shi aka nemi Lambar wani makusancinsa, Lambar Shahbeer aka bayar sannan aka kira shi. Ya na zaune zugudum, idanunsa a buɗe su ke amma a zahirance ba ya ganin komai sai dubu, ga wani mahaukacin ciwon kai da ya rufe shi, yakanji Su Baba da Ƴan-uwan Alhaji Boza su na karɓar gaisuwa amma ba abin da ya ke iya fahimta a ciki; ya na cikin wannan mugun yanayin aka kira shi aka sanar da shi halin da Safyan ya ke ciki; Sunan Allah kawai ya ke ambata ya na ƙara Kaɗaita shi gami da tsarkake izzarsa, ba abin da zai iya yi wanda ya wuce gode masa don kuwa ya fi shi sanin dalilin da ya sa rayuwarsa ta ƙare ba tare da wani cikakken farin ciki ba. Har aka yi Bakwai ba su dawo daidai ba, masu kukan kullum cikin yinsa su ke Shahbeer kuwa sai dai yanayinsa ke gwada ya na yin nashi kukan a Zuci. Yau ta kasance ranar Laraba da Safiya, Ya na zaune duk ya rasa meke masa daɗi, Falon Shiru duk da cewar Shahzad Malika Halima duk su na kusa da shi. Wayarsa ce ta fara tsuwwa, Malika ta miƙo masa gami da cewa "Maman YaYa Ramadan ce." "Innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un" itace kalmar da ya furta sabi da faɗuwar gaba da ta riske shi lokacin da Malika ta faɗa masa me kiran, cikin rawar jiki ya karɓa gami da karawa a kunnensa, kuka ta ke yi sosai ta rasa ma me za ta ce masa, cikin rawar baki ya ce "Shima ya Mutu ko Mama?" sake fashewa ta yi da kuka ta ce "Ya Mutu Shahbeer, shi kenan Dodo ya cinye mini Ɗana. katse kiran ya yi ya aje wayar a gefe, "Subhanallah Alhamdulillah La'ilaha'illallah Allahu'akbar" ya fara maimaitawa gami da rufe fuskarsa da tafukan hannunsa. Tini Halima ta ɓare baki ganin yadda Nutsuwarsa ta bar jikinsa, Shahzad ma taya ta kukan ya farayi bayan ya dawo kusa da Shahbeer ya na matsar ƙwalla ya na kallonsa. Malika ta ce "Nur, Meke Faruwa? Waye ya mutu?" ɗago rinannun idanunsa ya yi ya kallesu daga ita har Shahzad ɗin, lokaci guda Zuciyarsa ta yi rauni, "Ya Ramadan shima ya Rasu Malika yanzu mun dawo sai mu kaɗai mun rasa Mahaifinmu mun rasa YaYanmu." sharrrr!!!! sharrr!!!! hawaye su ka fara bin kumatunsa. Kuka Malika ta fara yi idan ta kalli Shahzad sai ta ji Zuciyarta ta ƙara karaya. Allah Sarki Rayuwa. Share ƙwallar ya ke yi amma sun ƙi dena zubowa domin yanzu ne su ka samu damar kwarara, ya na so ya yi magana ma ya kasa sai dai kukan. Wayarsa ta ɗauka ta kira su Shahmeer ta sanar da su. Duk me imani idan ya ga halin da su ke ciki zai tausaya musu ba kaɗan ba. Safyan ya ji sauƙi har an sallame shi daga Asibiti Shahbeer ya dawo da shi gida, Mom Safyan kuwa ta na ƙarƙashin kulawar Asibitin Mahaukata domin kuwa haukan nata ba kaɗan bane ƙara girmama ya ke yi, gashi ba ta iya zama kawai sai ta daki Mutum ga surutai ba na misali ba, mafi yawancin tsiyar da su ka yi daga ita har Alhaji Boza shi ta ke faɗe. Bayan Shekara Huɗu da watanni. Malika Ƴaƴanta Biyu Mace da Namiji, Aisha ana kiranta INAYA da Idris ana kiransa Aslam. Halima Namiji ta haifa Basiru ASLAN. Ɓangaren Shahmeer da Fatima, ƳaƳansu Biyu Mace da Namiji RAIHANAT da RAMADAN. Shahzaib da Ma'arufa Ɗansu Ɗaya watansa Tara da Haihuwa MUHAMMAD RISLAN. Shahzain da Shukriya Ƴaƴansu biyu na Biyun watansa Uku, Rayan da Rohan. "Baba!! Baba!!!!" kira Inaya ta ke ƙwala masa cikin kauɗi da zaƙin Muryarta, ba tare da ya kalle su ba ya ce "Menene?" "Aslan ne ya dake ni." ya ce "Dama nasan sai shi ai, Shahzad tashi ka sasanta su sannan ku tarkata ku je ku taya Mommy Hira." Aslan ya ce "Baba ƙarya ta ce." "Ba zan iya yarda ƙarya ta ke ba Aslan, tin da mu ka zauna anan ban ji ko tarin Aslam ba duk da shi yaro ne amma ku kun fi kowa ƙiriniya a gidan nan. "Sugar me iyali" Malika da take bayansu ta faɗa ta na dariya. Taɓe baki ya yi kafin ya ce "Ya ki ka ce? wai a hakan ma sauran iyalin ba su shigo ba. ta ce "Allah ya shirya mana su kawai amma akwai lafiyar tsalle-tsalle, ga surutu, ina ga dai wanda za su yo halinka a yanzu dai Rislan Shahzad sai Aslam, su ne ba su fiye magana ba amma banda su Inaya." "Lafiyar kenan ai. Ƙarasowa ta yi ta zauna kusa da shi kafin ta ce "Sa'ad da Abeer..." katse ta ya yi da cewa "Su na son Aure ko?, Ɗaya a Sharaɗa Ɗaya a Yahya Gusau, ki ce su zo su same ni da kansu." "Wow, Noor komai ka sani kenan akan ƴan-uwanka, hakan nan ya na matuƙar burgeni, zan so Shahzad ya kasance me kula da ƙannensa har haka ko ma fin hakan." murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. su na barin sashin su Inaya su ka arta da gudu wai su gurin Umma Za su je.. Shukriya ta na fitowa daga kicin su ka shigo su na tsalle-tsalle, "Inaya ki temaka mini ku nutsu yanzu na gama zane Rayan." zaro ido ta yi gami da cewa "Duka???" "Eh mana duka, na gaji ne su barni in ji da Yaron cikina." Baya ta yi ta ƙwalla ƙara ta na cewa "Rayan ku zo mu gudu wajen Ammi." Shukriya ta rintse ido gami da cewa "Alhamdulillahi, ni dai na godewa Allah da ya bani Magajiya, rawar kanta sai kace Ni YaYa Ma'arufa dai ta huta da ta samu Magajin YaYa Shahbeer." kafin ta gama maida yadda akai ɗin tini sun bar sashin nata sai ɓangaren Fatima. "Ga uwar gaiya nan, me Karaga da Iko kenan" ta faɗa ta na murmushi da ta ji motsinsu. Shahmeer ya ce "Ahh akwai Iko kam sai dai akwai rawar kai mu kuma ba haka mu ke ba, ina ga dai ku na fitinannun da ku na yara." "Tab nima Saliha ce ba ni da fitina ko ta sile ɗaya." ya ce "Ai na gani a Jarida." dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba, ko ta kansu su Inaya ba su bi ba su na tarar da Ramadan da Raihanat shi kenan su ka ƙara yawa firita ta ƙaru, Fatima ta ce "Ƴan Albarka ku tsaya ku ji." Inaya ta ce "Ammi ta na magana, ku yi shiru ku zazzauna." shirun su ka yi duk su ka zauna kamar yadda Inaya ta ce musu. Fatima ta ce "A duk lokacin da ku ka kasance cikin farin ciki ba wai tsalle-tsalle za ku yi ba, ku maida hankali wajen yiwa Annabi Muhammad Sallallahu'alaihiwasallam Salat,i, komai dare komai rana kar ku gajiya, sannan ku dinga Istigfari Ɗan-adam yakan aikata kuskure ba ma tare da ya san ya yi ba, don haka ina so ko dage da neman gafarar Allah." Su ka ce "To". cikin sa'a kuwa su ka nutsu kamar ba su ba kowa sai muimui ya ke yi da baki. Ma'arufa ta na cikin neman wanda zai ɗauke mata Rislan Allah ya jefo Shahzad ta liƙa masa shi ya kaishi gurin ƴan-uwansa. yau Mommy da Inna su na zaune suna hira Abeer da Sa'ad su ka yi sallama. bayan sun gaisa Mommy ta ce "Ashe abin ya zo shine ba'a gaya mini ba sai Inya ko?" da sauri su ka yi ƙas da kai cike da kunya, Abeer ne ya ce "Mommy ba ƙin gaya miki mu ka yi ba kinsan sai ya Amince sannan idan bai so ba dole za mu haƙura shi yasa mu ka fi son fara jin ta bakinsa. "Nima zolayarku na ke, Allah i tabbatar da Alkairi. su ka amsa da Amin sannan su ka nufi sashin Shahbeer. _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [1/19, 11:00 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 44-45-END Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. Shafi na Ƙarshe. Da sallama su ka shiga Malika ta amsa kafin ta ce "Sannunku tagwayen sarari." Abeer ya ce "Kar ki mana iyayi, ina YaYa Shahbeer?" Sa'ad ya ce "Dan Ƙanwarka ce fa ba ya na nufin ka girmeta ba yanzu Auntynka ce ko ba dan YaYa Shahbeer ba yanzu ta haifa ta zama Uwa, ato." Daidai lokacin Halima ta ƙaraso wajen ta na cewa " Na hau bayanka na yi ɗare-ɗare Ƙanina." Abeer ya ce "Ku fa Mata akwai ƙarfin hali wallahi, wai ƴar Jaririyar nan ce ta ke ce maka ƙaninta amma ka yarda." Sa'ad ya ce "Ai YaYata ce ko ba ka so kai ma YaYarka ce." Malika ta ce "Daɗina da kai faɗen gaskiya, Allah ya baka Masoyiyarka, kai kuma Ya Abeer Allah ya sa Ya ce sai nan da shekara tara za ka yi Auren." "Gwafar Uba!!" ya faɗa gami da sakin baki ya na kallonta, ganin hakan bai wadatar da shi ba ya sa ya ɗauki Filo ya jefa mata ya na cewa "Ku ji Yarinya da Mugunta?" "In ka kwantar da hankalinka kwana nawa ne maye ya yi Amarya ya cinye Abarsa!" Shahbeer da ya ƙaraso ya faɗa ba tare da ya kallesu ba. da sauri su ka daidaita nutauwarsu kafin Sa'ad ya ce "Wato, Sannu da fitowa dai YaYa." Abeer ya ce "Sannu YaYa an fito lafiya." murmusawa ya yi gami da cewa "Yaran nan an yi shakiyyai, Lafiya lau to ku zauna idan kun gama Zolayar yayyen naku." zaman su ka yi kafin Abeer ya ce "Anya kuwa YaYa ba ka da Aljanu??" da sauri Malika ta ce "Af, ashe ka raina, ba ka san ance kowa ya na da ɗari ba ɗaya ba??" Sa'ad ya ce "Banda abin ki ai waɗannan ba masu tashi bane, amma dai akwai Aljanu a cikin lamarin Mijin nan naku." Abeer ya ce "Gaya musu dai, gaskiya ce dole ne mu faɗeta ko ba kya Sallah sai Idi Shekara-shekara kenan." Halima ta ce "Maganar da ta kawo ku za ku yi ko kuma Lissafin Taurarin kwaɗin za ku ci gaba da yi??" Shahbeer ya ce "Oh Ƴar Budurwa da ba ki tanka musu ba su gama surutun, a lokacin da za su samu lokacina ni kuma ba ni da nasu kinsan ni Mutum ne me komai akan lokacinsa." da sauri Abeer ya ce ''Haba YaYa daga wasa?, maganar gaskiya dai za ka jita a bakin Sa'ad ni dai nauyinku na ke ji." Malika ta ce "Nauyi kuma? ashe dai mun zama manya kai jama'a?, yau dai ana jin kunyata." harararta ya yi gami da cewa ke a suwa?" Sa'ad ya ce "Ku yi haƙuri da batun nan sai an gama wannan, YaYa ka saurareshi zai gaya maka." Abeer ya ce "A'a O'o ban yi Alƙawari ba, ka fini iya bada labari ." Sa'ad ya ce "YaYa ka san dai bani da surutu ai, don Allah ka faɗa musu Abeer." Abeer zai yi magana Shahbeer ya dakatar da shi da cewa "Ka tabbatar ba shirma za ka faɗa ba." haɗiye waccan maganar ya yi sannan ya ce "Maganar gaskiya YaYa wata Yarinya ce ta ce Sai Ni." Halima ta ce "Ta ce sai kai ko kuma ka ce sai ita??" Sa'ad ya ce "Iskancin fa? Ni wallahi cewa ma ta yi na fito." Malika da Halima su ka tuntsire da dariya, Shahbeer kuwa murmushi kawai ya ke yi, miƙewa ya yi sannan ya ce "Zan yi Magana da DR." daga haka ya fice. rungume juna su ka yi cike da farin ciki da murna. Malika ta ce "Oh Allah me iko duk farin cikin ne haka?" Halima ta ce "Ta ya za su zauna da murfi aka?" Abeer ya ce "Kun ji ƴar gari, gaskiya dole ma ta ce miki Aunty!" Hira su ka ci gaba da yi su na zolayar juna. Kowa ya tattara a Falon Mommy ana Hira, wayarta ce ta yi ƙara ta ɗauka gami da sallama, Maalik ya ce "Mommy dama kiranki na yi in sanar miki Zakiyya ta Haihu lafiya lau." "Ma sha Allahu, Allah i raya kan sunna, Mace ko Namiji?" "Macece a gayawa sauran Ƴan uwa. "To shi kenan Allah i raya Allah i sa Ɗayyiba ce." ya amsa da Amin. Mommy ta ce "Kun ji Allah ya nufi Zakiya da Haihuwa, Ɗiya mace. Abeer ya ce "Wai tin da ta Haifi Namijin nan ya rasu ba ta ƙara ba ko? Allah sarki." Mommy ta ce "Eh Allah ya yi macen ce ta farko." Shahbeer ya ce "To Allah i raya." "Safyan Ƙannenka sun ɗakko maka magana, Su na neman Aure don haka ko ba ka shirya ba kai ma zan haɗa da kai, idan ba ka da wata zan yi maka Auren Haɗi" Shahbeer ya faɗa gami da kashe Safyan da idanunsa. Gyaɗa kai ya yi cikin sanyi ya ce "Na gode YaYa, Duk zaɓin da ka yi mini na Amince" Shukriya ta ce "Amma ba za ka bashi damar nema ba sai ka yi masa Auren haɗi?." "Na riga na yanke hakan za'ayi kawai sai haƙuri. Shahzain ya ce "Wai ganin su Inaya bai sa ki girma ba?, ya ci yanzu kin gane idan Inya ya yi magana ba a Musantata." Shahzaib ya ce "Ai ba za ta dena ba, karambani dai." Fatima ta ce "To ni dai duk ba wannan ba, yaushe ne za'ayi bikin?" Ma'arufa ta ce "Ke fa akwai son shagali, to an fasa Bikin." cikin sauri Abeer ya ɗora hannu aka gami da cewa "Innalillahi, Aunty Ma'arufa wannan maganar taki sai ta tsaida numfashina fa." dariya su ka yi kafin Shahmeer ya ce "Yaron nan fa ya fini sangarcewa ta fannin soyayya." da sauri Inna ta ce "A'a ai ba wanda zai kai Mijina iya soyayya, kowa ya biyo bayansa." Shukriya ta ce "Anya kuwa ? gaskiya ni dai nawa ya fi naki Inna." Mommy ta murmusa kafin ta ce "Asalin Masoyi a gidan nan shine Ɗana na farko, Babu wanda ya kai shi kuma ba wanda zai kamo shi, shine cikakken Masoyi me sadaukar da farin cikinsa akan wanda ya ke so." Ƙasa ya yi da kai ba tare da ya ce komai ba. Shahzain ya ce "Gaskiya ne Mama, wallahi kin gama magana." Inna ta ce "Nima na yarda, ni Nawa Mijin ma da ya je ya yi mini kishiya?" Dariya su ka yi kowa ya fara tofa Albarkacin bakinsa cikin nishaɗi ba tare da wata damuwa ba. Bayan Bikin su Abeer. Sa'ad da Safyan a kusa da Babban gida su ka tare da Matansu, daga cikin gidan su Shahbeer akwai hanyar da za ta sadaka da gidan su Safyan, Abeer kuma a gefen Unguwarsu gidansa ya ke, makeke kuma haɗaɗɗe Shahbeer ya yi masa kyautarsa. Safyan Firdausi Ƙanwar Ma'arufa aka Aura masa. Bayan wani lokaci. Halima ta ƙara Haifar Ɗiya Mace, wadda ta ci sunan Mahaifiyarta Maryam ana kiranta Amira. Fatima kuma Tsohon ciki gareta. Babu wani abin baƙin ciki a rayuwarsu kullum sai farin ciki kamar ba abin da ya faru, ko a cikin yaran duk ba bambanci kowa na kowa ne ba me nuna fifiko tsakanin wani da wani hakan ya sa su ke matuƙar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kowannensu ya na ƙoƙarin nunawa Matarsa soyayya Musamman Shahbeer ya na ƙoƙari sosai

Chapter 29 of 30