Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗauki kira na biyu da ya shigo. "Barka da wannan lokaci Baban Junior Mukhtar, Prince Shahzad, ina tayaka baƙin cikin da jimamin rashin lafiyar matarka tare da jajanta maka akan rashin Ɗanta da ka yi, Ramadan YaYan Ƴan-huɗu." Shahbeer ya ce "Ohh, Amma ai ban tambayi kowaye ba ko?, na kuma gode da jajanta mini sannan nima ina jajanta maka kasan-cewar Abin da ya shafi Shahbeer ya shafi Ramadan domin Uba ɗaya ne ya kawo mu Duniya, bansani ba ko taka za ta fi tawa kyau amma ina ji maka tsoron ranar da abin zai juyo kanka, bare ka haɗa da zalumci da rashin tsoron Allah, Ashsha lamarin fa ya munana domin kuwa Ba na jin ƙarshenka zai yi kyau." Dariya ya yi kafin ta ce "Na fa gode nima, wai ya akai ban ji saƙonka ba har yanzu ina ta jiran abin da ka ce za ka mini a sansanina, ohh na tuna ashe fa rashin Lafiyar Hasiya ne ya sha maka kai, Yau ina ga Ma'arufa Zuciyar Shahzaib tare da Shahzad sun je unguwa ko?? to ko dai mu haɗu a hanya in ga Ɗana?" Sai a lokacin Shahbeer ya tuna Ma'arufa ta je gidansu tare da Shahzad...... _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [1/6, 10:20 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 34 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. Shahbeer ya ce "Idan kaga za ka iya sai ka gwada amma fa dole ne ka yi ladabi." "Babbar dama ce wannan ka bani ƙanina don haka na gode" ya yi maganar ya na dariya. Shahbeer bai ce komai ba ya katse wayar. Ramadan ya yi dariya sannan ya miƙe cikin takun gadara ya fice cike da jin daɗin damar da ya samu. Ma'arufa su na cikin hirarsu Yaro ya ya yi sallama ya ce "Wai Ma'arufa ta kawo Shahzad inji Shahbeer." Umma ta ce "Gata nan zuwa." Ma'arufa ta ce "Oo, hankalinsa dai bai kwanta da fitarmu ba har yanzu shine sai ya biyoni ya karɓi Shahzad." Firdausi ta ce "Ai da gaskiyarsa, ki tashi kar ya gaji da jira." ta tashi ta zura Hijab sannan ta kama hannun Shahzad da su ke wasa shi da Usman. ba tare da ta yi tunanin komai ba ta fita, har wajen Motarsa ta ƙarasa sannan ta tsaya. Fitowa ya yi daga Motar fuskarsa ba Annuri, a dake ya ce "Shiga Mota mu je ko ki bani ɗan na tafi da shi." a tsorace ta ce '"Kai kuma waye? akan me zan baka Yaro?" "Dalili ki ke son ji? Shahzaib bai gaya miki ya na da YaYa ba?, Shahzad Ɗana ne don haka ki ban kayana. cikin ƙarfin hali ta ce "Ba zan bayar ba, ai YaYa Shahbeer bai ce in bawa kowa ba." "Kar ki sa na gwada rashin imanina akanki don kuwa ban yi niyar sakoki cikin lamurana ba amma in kin matsa za ki gane Kowaye Ramadan, zan iya illata rayuwarki sannan in ɗauke yaron zai fi sauƙi ki bani shi ko kuma ki bini, in hakan bai miki ba kuma zan sa ƙarfina in ƙwata kuma abin ba zai yi kyau ba. Nazari ta yi kafin ta yanke hukuncin binsa don ba za ta iya bashi Shahzad ba kuma ta na tsoron ya aikata abin da bakinsa ya ke furtawa. . Maman Ramadan, Ta na zaune a ɗan madaidaicin falonta ta naɗe ƙafa ta na taunar kayan marmari, jin ana buga ƙofa ya sa ta yi tsaki ta yatsine fuska, "Ke!! je ki ga waye ya ke neman damun mutane?" Ta yi maganar ta na kallon ƴar-aikinta. Ƴar-aikin ta tashi ta fita zuwa wajen Get, ta na buɗewa ta yi ido huɗu da su Zagarido, Kacau ya ce "Mama ta na nan??" "Ta na nan suwaye ku??" "Ki ce mata yaran Oga Ramadan ne ta fito, ya ce a ɗauketa akaita Gidansa na Nasarawa sabi da tsaro." ƴar-aikin ta ce "To" Komawa ta yi ta sanar mata. Cikin rawar jiki ta tashi ta shirya ta sha ado kamar za ta je Dinner, sai da ta korawa Ƴer-aikin ta-ta Kashedi na kula da gidan da ajiyar da ke cikinsa sannan ta fito ta na taku na ƙasaita, a dole ɗanta ya yi kuɗi shi yasa ta ke jin kanta kamar Sarauniya. Ta na fitowa su Kacau su ka kwashi gaisuwa sannan su ka yi mata Jagora zuwa wajen Mota. Dakatawa ta yi cikin farin ciki ta ce "Wannan jibgegiyar Motar ma ta Ɗana ce?" Zagarido ya ce "Ai Oga Ramadan ya wuce nan ma, sai ma mun je gidan za ki ga yadda ya tsaru kamar a ƙasar waje, ai yanzu fa yayin Oga Ramadan ake yi, ba ki ji har gidajen Radio zancensa ake ba?" ta ƙara sakin murmushi na farin ciki, kanta ya ƙara girma da faɗi ta ji kamar ta yi daidai da Sarauniyar Duniya, cike da gaiya ta ce ''Ai duk wanda ke son ganin bayanmu sai dai mu ga nashi wallahi, ga arziki nan Ɗana ya yi mun wuce wulaƙanci wallahi." Zagarido ya ce "Ai na ƙagara ki je gidan Mama, ki yi sauri mu na cinye lokaci anan.'' ta ce "Haka ne Yaro, buɗe motar." buɗe mata gidan baya ya yi ta shige ta na surutai na habaici, su Kacau kuma su ka shige gaba ɗaya direba ɗaya ɗan zaman banza. hankalinta ya lula wajen tunanin Daular da ɗanta ya jefata gaba ɗaya nutsuwarta ba ta kusa, Sai da su ka bar unguwar sosai tafiyar ta nisa sannan ta lura akwai Mutum a kusa da ita, da mamaki ta ce "A'a?? a cikin Bayin ma har da masu zama a gefen Sarakai??" ta yi maganar ta na ƙare masa kallo, kasancewar ya yi irin Cover da su ke yi in za su fita ba ta gane kowaye ba, cikin nuna ƙyama ta ce "Wai kai direba ba ka jina ne?? akan me za ku zo da wani ku sa shi a kusa da ni?? an gaya muku ni daidai na ke da ku?? maza tsaya ya fita daga motar, naga jin kansa ma ya yi yawa wai waye shi????" Kacau ya ce "Ki yi haƙuri Mama, tambayar dai da ita ki ka yi tin farko, wani Bawan Allah ne, ai shine me Motar gidan da za mu je ma nasu ne." ta ce "Me?? wannan dai ba Ramadan bane." latse wayar da ke hannunsa ya yi kafin ya zare gilashi da Hankicif ɗin, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Gafarceni Mama Furairatu ban gabatar da kaina ba tin farko, Mukhtar, Shahbeer, YaYan su Shahmeer Ɗan A'i da Boza baban Shahzad ƙanin Ramadan Maƙiyinki, duk yadda ki ka ɗaukeni daidai ne ni me binki ne sau da ƙafa." A take alamar tsoro da Razani su ka baiyana akan Fuskarta, cikin rawar baki ta ce "Mem..me..mene?? ka na nufin sace ni ka yi dan ya karɓi Ɗansa?????" "Gyara kalaminki Uwar Ramadan, Ɗan Shahbeer ne ba nashi bane, kuma taɓa Ahalina gaskiya akwai haɗari, don ma kinsan Jini ba ƙarya bane amma da wani ne Ramadan ba shakka da na hukuntashi akan laifuka da dama musamman Keta Haddin Matata Halimatu, kuma ni ba sace ki na yi ba gida zan kai ki don ku gana ke da wadda ki ka tsana, har ki ka raini Ɗanki akan turbar ƙiyayyarta da Ƴaƴanta bayan ma mu ba mu san da ku ba." Zuwa yanzu ta gama kaiwa gejin tsoro ga wani bala'in kwarjini da ya ke mata, duk jikinta ya hau tsuma kamar an tarfa ɓarawo. Shahbeer ya ce "Har farin ciki ki ke yi sabi da ɗanki ya tara miki Dukiya ta hanyar Sata ta hanyar Haram, kaico, Abokan Adawar taki ba ɓarayi bane guminsu su ke ci, burinki ɗanki ya ɗaukaka ya zama ya yi kankankan da DOUBLE TWO STAR, maganar gaskiya kin ɗauki Duniyar da zafi Madam." Wani mugun yawu ta haɗiye ta ƙara gyara zama ta tsuke jikinta ganin ba ta da niyar yin magana ya sa ya ja bakinsa ya tsuke. Har su ka isa ba wanda ya ƙara magana a Motar, bayan sun tsaya su Kacau su ka buɗe musu murfinta, Binsa kawai ta ke yi duk a sassaɓule, ta na tafiya ta na ƙarewa gidan kallo, ko ba'a faɗa ba itama kanta ta san ta raina kanta da duk wani arziki da ta ke jin ɗanta ya na da shi. Su Mommy su na zaune a Falo su na hira Shahbeer ya yi sallama Maman Ramadan ta na biye da shi, da sauri Mommy ta miƙe idonta akanta, itama ta zuba mata ido su ka shiga kallon kallo, Maman Ramadan tunaninta ɗaya tayaya A'i ta ke zauna a cikin irin wannan Daular bayan ta daɗe ta na bin duk wasu matakai dan ta tarwatsa farin cikinta sannan ta yaya wadda ta tsana za ta kasance ta Alfarma haka?. Juyawa Mommy ta yi za ta bar gurin Shahbeer ya dakatar da ita da cewa "Mommy ki tsaya ku gaisa, kafin Ramadan ya zo ya maida ita." tsayawar ta yi ba tare da ta zauna ba, fuskarta babu walwala ta ce "Sannu." "Hmm, sannu Aisha, waɗannan kuma fa? nasan dai Maza gareki ba mata ba" ta yi maganar ta na kallon su Malika. Shahbeer ya ce "Wannan Malika kenan Matata ce, Waccan kuma Shukriya Matar Shahzain, ku gaisheta Malika." gaisheta su ka yi ta amsa ta na ƙara binsu da kallo. Mommy ta ce "Inya, Auta, ku ɗan bamu guri, Shahbeer lokacin shan maganin Malika ya yi." ya ce "To Mamma." temakawa Malika ya yi ta miƙe ya rungumeta ta gefensa cike da kulawa ya ce "Ki dinga tafiya a hankali." ta yi murmushi gami da cewa "To" Shahzain ma Kama hannun Shukriya ya yi su ka nufi Sashin Inna domin hira. Mamar Ramadan ta ce "Me ki ke son gaya mini kuma??" "Tambayarki na ke son yi a bisa dalilinki na tsanata ni da iyalina. keɓe baki ta yi tare da yiwa Mommy Kallo me kama da Harara ta ce "Ai komai a zahirance ya ke, ke Muguwa ce mara imani da tausayi, kin zo kin tarar da ni a gidana kin kore ni kinsa Miji ya tozarta ni, haka ki ka sa Basiru ya koreni Da cikin Ramadan daga nan bai ƙara bibiyarmu ya ji a halin da mu ke ba, bai sani ba na haihu lafiya ko akasin haka, baisan cinmu ba baisan shanmu ba haka muka ƙare kalangu-guwarmu, ai ba zan taɓa yafe miki ba Azzaluma, na tsaneki." Mommy ta jinjina kai kafin ta ce "A cikin Duhu, rashin sani na kewaye da ke shi ya sa ki ke irin wannan tunanin, ni ba irin Zuciyarki gareni ba da har zan zaɓi in wulaƙanta ki, da za ki saurari nawa labarin ke da kanki sai kin ce naki shafar mai ne." Sai da ya gama yanga sannan ya ɗauki kiran Shahbeer Ɗin, ya na dariya ya ce "Ƙanina na ji baka nemi Ɗan naka ba ko ba Kati a wayarka??" ya ɗan murmusa kafin ya ce "Ina tare da Kakar yaron nemansa na me zan yi?, na ga ka na da idanu da yawa, ba'a gaya maka cewa na Ɗauki gyatimarka ba?, Na san duk wani kwari da lungun da za ka je ka ɓoye Abin da ka ɗauka daga gareni, amma ni idan na so ɓatar da Ƙaniyarka ko labarinta ba za ka ƙara ji ba sai dai tarihi kuma a hakan ta na raye kawai ɓoyeta na yi, ya kamata ka dakatar da wannan shiriritar ka gane Inda ka ke sa gaba, Yanzu ka zaɓi Halima da Shahzad da Ma'arufa a bakacin Furairatu??" Bai yarda Mamarsa ta na hannun Shahbeer ba don haka ya yi saurin katse kiran ya shiga kiram ƴar-aikinta. wayar ta na shiga aka ɗauka ga mamakinsa sai ya ji murya irin ta Shahbeer, cikin sakin fuska Shahmeer ya ce "Ba yarinyar bace mun zo mun ɗauki Halima ita kuma yarinyar mun sallameta dama mu ne mu ka turo ta don ta gane mana sirrin gidan naku, Ita kuma Mama Furaira ai inaga ta na gidan Mommy." katse kiran ya yi cike da takaici, ji ya ke kamar ya yi hauka sabi da tsabar takaici da baƙin ciki, da sauri ya kira Shahbeer ya na ɗauka ya ce "Zan dawo maka da su kar ka ɓatar mini da Mamata, Bani da kowa sai ita." "Ka na da kowa Ramadan sai dai ba ka ɗauki kowa ɗin amatsayin kowa ba shi yasa ka ke ganin ba ka da su, Kamar yadda ka taso ba ka san daɗin Mahaifinka ba mu ma a hakan mu ka rayu amma duk da haka mu na da kowa, damu da kai duk ba marayu bane Mahaifinmu ya na nan haka iyayenmu Mata, mu na da Ƙanne uku a gurin Mamar Safyan sannan mu huɗunnan ma ƙannenka ne mu kuma mu na da YaYa, sannan mu biyu mu na da Mata wanda kai tsaye za ka ce Matan ƙannenka ne, kuma ka na da Allah shine ma ya raya ka har ila i yanzu, ka ga kuwa idan ka ce ba ka da kowa ka butulcewa Allah, ya kamata ka yi karatun ta nutsu Ramadan, Idan ka shirya sai ka kawo mini su." ya na kaiwa nan ya katse kiran, Ramadan ya ji kamar ya fashe da kuka amma ya kasa. Zakiyya, shigowa Maalik ya yi ɗakin ya durƙusa a gabanta Zuciyarsa fes ganin yadda ta galabaita ya sa shi farin ciki, kwanceta ya yi kafin ya ce "Za ki koma gidanku ne?" girgiza kai ta yi ta ce "A'a ba zan koma ba ko me za ka yi mini ka yi amma ni ba zan sa ka sakeni ba sai dai in ka yi niyya." maganarta ba ta yi masa daɗi ba sam, ya taɓe baki ya ce "Ba zan sake ki ba kuwa har sai kin gama ɗanɗana irin azabata." cikin kuka ta ce "Na Amince da komai, amma don Allah ka ban abin ci in ci ga ƙishirwa ma ina ji." "Ai itace za ta kashe ki don kuwa ba ki aje bawa a gidan nan wanda zai kawo miki Ruwa da Abinci ba" ya faɗa tare da tashi ya nufi hanyar fita, kulle ƙofar ya yi sannan ya ci gaba da tafiya. Mamar Ramadan ta ce "Ban gane ba, shashantar da ni ki ke son yi??" Mommy ta ce "A'a, ina ga ni zan koma ɓangarena idan Ramadan ɗin ya zo sai a nemo ni." ta na kaiwa nan ta ci gaba da tafiya. kamar an dasata haka ta zauna ta yi kasaƙe ta na tunani akan magan-ganun Mommy, ta kasa gane inda su ka dosa kwata-kwata; ta na nan ta na tunani Ƴan-aiki guda biyu su ka zo su ka zauna a gurin don sa ido akanta, hakan ya sa ko sha'awar tashi daga inda take ba ta yi ba. Su Shahmeer su ka yi sallama tare da Halima cikin sauri ta tashi ta na cewa "Ku uban wa ya baku wannan Ƴar??" ko kallon kirki ba su yi mata ba su ka wuce ciki. komawa ta yi ta zauna ta ɗinke bakinta. Zakiyya sai da ta tabbatar ya tafi sannnn ta sa hannu ta ɗakko wayarsa da ya ajiye lokacin da zai kwanceta kuma ya manta ya tafi. Lambar Mom Safyan ta saka sannan ta tura kira, ta na ɗauka ta fara gaya mata abin da Maalik ya ke mata, Ashar ta kutuntuma kafin ta ci gaba da cewa "Ai duk abin da ki ka samu a kusa da ke ki ki ɗauka ki buga masa ko Mutuwa ya yi ma ba ruwanmu, Idan ma wuƙa ki ka samu ki daidaici inda za ki yi masa illa ki soka masa ita........" ba tare da ta gama faɗen abinda za ta faɗa ba Alhaji Boza ya fizge wayar, ya na sharar ƙwalla ya ce "Ƴata ni Mahaifinki ne kuma ina sonki ina son in ga Gobenki ta yi kyau, koda ni ba zan samu Rahmar Allah ba ina me kwaɗayin ku Iyalina ku samu, ni tawa ta zo ƙarshe ku kuma Yara ne, Zakiyya ina so in baki Umarni a matsayina na Mahaifinki, ko da na Mutu ki ɗauki su Shahbeer da Sa'ad a matsayin iyayenki, ki yi biyayya ga duk hukuncin da su ka yanke akanki don na yi imani ba za su cutar da ke ba, ba na so kema ki yi kuskuren da na aikata, na bi WATA HANYA wadda ba ta ɓullewa Hanyar da ta kaini ga halaka, kuskurena ne sanadin rarrabewar kawunanku amma ku ba maƙiyan juna bane, Zakiyya ki yi biyayya ga Mijinki ki yi haƙuri da fushinsa wata rana sai labari, yanzu ya na cikin fushin rashin wadda ya ke so ne idan ki ka yi haƙuri komai zai wuce, sannan idan ki ka shiga wata damuwa kar ki ƙara neman Mahaifiyarki ko Safyan, ki nemi iyayenki wato su Shahbeer su ne za su baki shawara me kyau shawarar da ba za ta hallakar da ke ba kamar yadda nima na hallaka, Ina so ki fita daga cikin Tafiyar Mahaifiyarki ki koma kan Hanyar Gaskiya itace HANYA ƊAYA wadda za ta inganta rayuwarki, Na faɗa miki ne domin ina kwaɗayin Farin cikinki ba wai dan ina ƙinki ba." ya ƙarasa maganar ya na kuka. Jikinta ya yi bala'in Sanyi musamman da ta ji Babanta ya na kuka karirisss, ƙara fashewa ta yi da kukan ta na cewa "Daddy ka dena kuka, na yi maka Alƙawarin zan yi aiki da maganarka, in Allah ya yarda na dena goyon bayan rashin gaskiya, zan kasance Ƴa tagari zan yi ƙoƙari sosai don na gyara rayuwata, su ma su Ya Safyan ina fatan su shiryu su gane gaskiya." ya ce "Ƴata kin ga dai ƙarshen rashin gaskiya da rashin tsoron Allah, ƙarshe dai kin ga yadda rayuwa ta bi da ni, ni na banzatar da su Shahbeer gashi yanzu na zo ina sonsu amma sun yi mini tazara, gashi waɗanda na ɗauka a matsayin mafisoyuwa a gareni yanzu kuɗi sun fini muhimmanci a gurinsu, Allah ya tsareku da faɗawa halaka ƴaƴana." ta ce "Amin Dad, in Allah ya yarda nima ba zan bi wannan kuskuren nasu ba, na fahimci komai Daddy." ya ce "Allah ya yi miki Albarka." ta amsa da "Amin" sannan ta katse wayar ta ajiye masa ta ci gaba da kuka, ta yarda kuskuren da ta aikata a baya ne ya ke bibiyarta shi yasa Allah ya haɗata da Maalik ya ke gasata. Har su Ramadan su ka iso ta na nan a zaune tare da ƴan tsaronta.......... _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO"* [1/7, 10:52 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 35 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. Ta na ganinsa ta miƙe da sauri ta ce "Ya akai ka bari su ka satoni? ka ga da sun cutar da ni fa shi kenan ba labarina." Ma'arufa ta ce "Kun yi musu gurguwar Fahimta ne amma babu ƙudurin cutar da wani a cikin tsarinsu." Wani mugun kallo Ramadan ya zuba mata ba tare da ya ce komai ba, Mamar Ramadan ta ce "Ke dallacan, rufewa Mutane baki, dan kin samu kanki har shine za ki yiwa mutane iya yi? Tin kafin ki zo Duniya na san waceca Aisha kuma ba dalilin da zai sa na yafe mata." Muryar Mommy ce ta katse mata maganar "Ko da ba ki yafe mini ba ni bani da damuwa don na yarda ban yi miki komai ba; Ramadan ashe zan ganka? ikon Allah gaba-ɗaya sai ku ka biyo Mahaifinku banda haka ai da cewa zai yi ba Ƴaƴansa bane." kallonta ya yi ya kauda kai cike da tsanarta. Mom Ramadan ta ce "E, ai dama ba ki so ya zo Duniya ba bare ki ganshi, kuma gashi ya zo kin ganshi sai ki mutu." Mommy ta murmusa kafin ta ce "Haba Maman Ramadan ina jin zafi idan ki na jifana da irin maganar nan, tamkar ƙazafi ki kai mini fa domin kuwa ni ba haka na ke ba, ba na so na ji kina faɗa mini abin da ban aikata ba." "Ai dole ki ce ba ki aikata ba tinda kin gama cutata dama..." Shahbeer ne ya katse ta da cewa "Tin da ya kawo mini Shahzad sai ku tashi ku ci hanya tin kafin ku fara ɓata mini rai." Mommy ta ce "Kafin su tafi ya na da kyau su ji Tarihin rayuwarmu da Alhaji Boza." ya ce "Ohh, zan bar gurin don ba zan iya saurara ba. Mommy ta ce "Na fi murna da hakan don ba na so ka

Chapter 23 of 30