ta ƙaraso ta na cewa "Kai barka Hajiya Sannu da dawowa, kin dawo akan lokaci dama ƴa-ƴanki na buƙatarki, ke dai sannu ai kin sha hanya."
Mommy ta ce "Ai na sani dama dan-dai sun ƙi faɗa ne, Sannu da aiki Inna na sameku lafiya?"
zama ta yi ta na cewa "Lafiya lau"
surutu Inna ta fara zubowa Mommy har da wanda ba'a tambayeta ba.
cikin tafiya me kama da sanɗa ta shigo falon ganin su Shahbeer ba sa nan ya sa ta sauke ajiyar Zuciya, cikin sanyin jiki ta gaida Mommy, amsawa ta yi cikin sakin fuska, Inna ta ce "Kin gama ne??"
"e na gama ki zo ki duba"
Inna ta ce "Ko ke fa, je ki ina zuwa.
maida kallonta ta yi kan Mommy gami da cewa "Yarinyar nan ta na da hankali shi yasa ma Ɗanki ya ce in dinga koya mata girki."
Mommy ta ce "Ai na ji daɗin hakan dan kuwa ba kowa ne su ke yarda da shi ba kin ga kuwa in ana haka ai akwai matsala."
Inna ta yi dariya gami da cewa "bari dai in dubo mata dan tafiya za ta yi gidansu."
Da sallama Inna ta shiga kicin ɗin, Ma'arufa ta na zaune ta na jiran zuwanta, da sauri ta miƙe ta na cewa "Inna tafiya zan yi za ki sa su Atika su kai musu??"
"ke Ƴar nan rufa ni ko saya ni, sashin su idan ba ni ba sai uwarsu dan haka ke da aka sa ke za ki kai da kanki, maza-maza har-haɗa ki ɗauka ai kin gama me wuyar Allah ya yi miki Albarka.
Kamar za ta yi kuka ta kinkima fuskarta sam ba annuri, Mahaifiyarta da ƙanwarta su na can ba lallai in sun ci abincin ba amma ita ta na nan tana bautar girkawa wasu,
jin ta yi karo da mutum ne ya sa ta yi saurin zaro ido ta yi baya gami da cewa "Subhanalllah!!"
cikin haɗe fuska ya ce "Tunanin uban me ki ke da zaki juye min abinci aka??"
baki na rawa ta ce "ka..k.ka yi haƙuri ban kula bane."
"Ohh ki na ƴar ƙarama da ke amma kin iya sa kai a uku, ki na tafiya ki na tunani ke da ko gama sanin rayuwa ba ki yi ba"
Shahbeer ne ya dakatar da shi da cewa "Ya isa mana Jariri (Shahmeer) abin ai duk bai kai haka zafi ba, Beauty Kalar kyau ƙaraso ki aje musu."
da sauri ta raɓe ta kusa dashi ta wuce dan kuwa abin da take jira kenan ta ajiye ta gudu.
da ido ya rakata har ta ajiye ta juyo sannan ya basar, cikin ko in kula ya ce "Ki dinga kama kanki Do Allah ki dena karo da maza, yanzu da ba ni ne ba f...."
shegiyar hararar da Shahbeer ya watso masa ce ta sa ya yi saurin gimtse bakinsa.
Ma'arufa ta na fita hanyar gidansu ta kama, har ta isa jikinta bai dena gaya mata ba daɗi ba dan kuwa yau ba ƙaramin razani Zuciyarta ta shiga ba.
Yau da wuri Ma'arufa ta gama aikin da za ta yi ta tafi gida.
misalin ƙarfe 09:12,
zaune suke su na hira, jefi jefi Shahbeer ya ke saka baki dan shi ba me son cece-kuce da yawan surutu bane.
wayar Shahmeer ce ta fara tsuwwa ganin Inna ce ya sa shi saurin miƙewa ya na cewa "Masoyiyata ce ta korani ku yi min shiru dallah."
Shahzain ya ce "Ka jiƙe indai sai mun yi shiru za ka amsa kiran wannan Tsohuwar."
ƴar dariya ya yi gami da ɗaga wayar ya kara a kunne.
Tattaɓe baki ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Masoyi ka kira min ƴan-sanda an yi min sata, kuma indai aka gano ɓarawon sai na karya masa ƙafa."
Dariya abin ya bawa Shahmeer dan haka ya dara kafin ya ce "Amma Baby a gidan nan akai miki sata? kuma me aka sata?"
"Wallahi a kitchen na ajiye dubu biyar shine yanzu na zo ɗauka ban gani ba.
"Kin duba da kyau kuwa? ƙara dubawa idan ba ki gansu ba to.
"Wallahi ɗannan na duba sosai amma ban gansu ba, ni dai ka kira min ƴan-sanda idan kuma ba za ka kira min ba sai in gayawa Inya"
"A'a abin bai yi zafin haka ba Inna bari zan baki kuɗin amma ba sai an kira ƴan-sanda akan dubu biyar ba, ki yi haƙuri.
ta ce "To amma idan ɓarawon ya ƙara zuwa fa?"
ya ce "Ba ma zai ƙara ba In Sha Allah."
katse wayar ya yi cike da mamaki, duk yawan ƴan-aikin gidan bai taɓa jin an ajiye abu an rasa ba, to kuwa waye ɓarawon a yanzu?.
Shahzain ne ya ce "Lafiya kuwa na ji ana zancen ƴan-sanda?"
dariya ya yi gami da cewa "Rikicin Inna ne fa dubu biyar ɗinta ce ta ɓata shi ne za'a kira ƴan-sanda sabi da ba su da aikin yi."
dariya su ka yi Shahzaib ya ce "Allah ya shirya Inna, inaga fa ita ce ta manta inda ta ajiye."
Shahmeer ya ce "Wallahi ta ce a kicin ta ajiye kuma ta duba babu, gaskiya dai nima abin ya ɗauren kai."
Shahzain zai yi magana Shahbeer ya dakatar dashi da cewa "Ba ku da wani abin yi ne wanda ya wuce mai-maita zance ɗaya?.
Shahzain ya ce "Akwai mana."
"Okay" kawai ya ce ba tare da ya ƙara magana ba.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/2, 6:24 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
7
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
MOONASH Alƙaluma Shida.
Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS.
BANI DA HUJJA
Maimoon
SARƘAƘIYA
Shaahd
BARRISTER SHAHEEDA
Ayush
AUREN ƘAUYE
Nazlarh
WATA HANYA
Indo
ZUMUNCIN ZAMANI
Jikar Nashe
Da sallama Ma'arufa ta shiga gidansu jin ba'a amsa ba ya sa ta wuce ɗaki, hijab ta cire ta ajiye sannan ta fito tsakar gida, dai-dai Lokacin Umma ta fito daga banɗaki riƙe da buta a hannunta, ganin Ma'arufa ya sa ta saki fuska gami da cewa "Sannunki da dawowa ƴar albarka, yanzu na gama begenki Allah dai ya sa kin tawo mana da abin da zai temake mu."
cikin ƙarfin hali Ma'arufa ta gaida Umma, amsawa ta yi sannan ta ci gaba da cewa "Na ga kin dawo da wuri yau lafiya?"
"Umma lafiya lau, ina Fiddausi da Usman ne??"
"Sun fita Shi Usman ma bansan inda ya yi ba ita kuma Fiddau ƙila ta na maƙota.
cike da takaici Ma'arufa ta ce "Hakan fa ba dai-dai ba ne Umma, yanzu fisabilillahi Usman ba kowa ne ma ya san akwaishi a gidan nan ba sabi da tsabar gantalin shi koda-yaushe ba ya gida, Umma ba mu san inda ya ke zuwa ba idan ya fita ita kanta Fiddausin ba mu da tabbacin inda take zuwa."
"Amma Banda abinki Ma'arufa ai Usman namiji ne kuma idan ya fita ƴar hamsin da ɗari yakan kawo mana mu toshe wata kafar.
"Haba Umma?, sabi da Allah akan ƴar ɗari da kobo sai mu taru mu lalace wannan rayuwa ce?, ni na fita su sun fita kema ba ƙaunar zaman gidan nan ki ke ba duk me yasa hakan?"
"Amma ai kema ki na buƙatar matemaki tin da Allah ya sa shi namiji ne ai zama bai kama shi ba.
"Ƙaramin yaro ne fa Umma, to ni indai akaina ne kar wanda ya ƙara fita su tsaya su yi karatu su ilmantu da ilmin Addini ya fi wannan gantalin nasu, ni a gantale su a gantale ai abin sai ya yi yawa, zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen samar mana abin da za mu ci sauran ƙyale-ƙyalen duniya kuma duk ba namu bane dan haka Umma kar ki bari mu lalace mu duka.
Umma ta numfasa cike da tausayin ƴarta-ta ta ce "Shi kenan Ma'arufa zan yi ƙoƙarin hana su fita kema Allah ya rabaki da lalacewar ki ma dena faɗenta a bakinki."
share ƙwalla Ma'arufa ta yi aranta ta ce "Lalacewa kuwa ai na gama yinta tin da akan neman rufa mana asiri zan iya ɗaukar abin da wani ya ajiye ba haƙƙina ba."
Umma ce ta katse mata tunanin da cewa "Da Ƴar naira Ɗari-da-hamsin ɗin da Usman ya kawo ya siyo mana Garin Kwaki da Sugar muka rage zafi."
Ma'arufa ta ce "Yau na samu kuɗi zan je na Biya Garo me kanti kuɗinsa sai na siyo mana wani abin."
cikin fara'a Umma ta ce "To Alhamdulillahi, Hajiyar ce ta baki?"
gyaɗa kai kawai Ma'arufa ta yi gami da nufar hanyar soro ta na jin Umma ta na zazzagawa Hajiya Albarka.
cikin doguwar riga Abaya Maroon wadda ta sha adon dutsina baja-baja Shukriya ta shirya sannan ta fito Parking Space inda Maalik ke tsaye ya na jiran fitowarta, fuska a haɗe ta ce "Gani na fito sai mu je ko?"
Hajiya Dada ce ta dakatar da su da cewa "Allah ya yiwa wannan haɗin albarka, Shukriya idan na ganku tare da Maalik ba ƙaramin daɗi nake ji ba, haka kawai duk yawan matan duniya da ke kaɗai na fi ganin dacewa da santalelen ɗana ƙannensa biyu shi kaɗai ne namijin da nake da dan haka na ke son ganin farin cikinsa."
murmushin yaƙe ya fi kuka ciwo Shukriya ta yi gami da yin ƙasa da kai.
Maalik kuwa har cikin ransa ya ke jin daɗin ƙaunar da Dada ke nunawa Shukriyar da ya gama mutuwa akan sonta idan ya tuna cewa ba dan Dadan ta na sonta ba da ya shiga matsala sai ya ji farin ciki ya lulluɓeshi.
Addu'a Dada ke yi musu har suka fice daga gidan.
shiru motar babu me cewa ƙala ganin sai tufka da warwara yake yi akan ti-ti tafiya ta ƙi ƙarewa ya sa Ta ce "Maalik ina ka ke son zuwa ne?? ka sani fa har ga Allah tsoron kaidinka nake ji."
sosai maganar ta daki Zuciyarsa dan kuwa ba son wasa ya ke mata ba ita kuwa ɗaukar abin take kamar labari ko tatsuniya ko kuma son Zuciyar Mahaifiyarsa, dannewa ya yi kamar bai damu Ba cike da miskilanci ya ce "Ban taɓa jin wannan takurawar ba, ni da Matata ne fa amma sai an tuhumeni? da wani ne ya yi min haka da na nuna masa zahiri amma ba yadda na iya tin da an fi ƙarfina."
a ƙufule Ta ce "Zan buɗe murfin motar in faɗa wallahi in dai ba ka gaya min gaskiya ba."
da sauri ya ce "Ashshah!! me yasa ba za ki yarda da ni ba wai?, Zan je na haɗu da abokina ne a gidan gonarsu dan Allah ki yi shiru ba zan iya cutar da ke ba Shukriya."
banza ta yi masa ta ci gaba da kalle-kalle, sai da suka isa sannan ya ce fito mun zo.
fitowa ta yi ba tare da ta kalli inda ya ke ba.
tin daga nesa take kallon abokin nasa Zuciyarta na bugawa da sauri da sauri..
"Lamarin Malika ya fara firgita ni Jama'a koda-yaushe ƙara lalacewa ta ke yi idan fa ba'ayi mata da gaske ba nan gaba fin haka ma yi za tai, ba ta da kunya yanda ka san ɓeran masar"
Shahzaib ne ya yi maganar ya na kallon ƴan-uwansa cike da son jin ta bakinsu.
"Addu'a itace makamin Shahzaib duk wannan rigimar ba za ta shirya mutum ba"
Shahbeer ya faɗa gami da miƙewa da nufin zuwa babban Falo, ganin ya yi hanyar fita ya sa suka bi bayansa.
A falon Mommy da Inna su na cikin hira su ka ji sallama, haɗa baki su ka yi wajen amsawa, Sa'ad ya ƙara faɗaɗa fara'arsa gami da cewa "Sannunku da gida Mommy."
cikin sakin fuska ta ce "Sa'adu kai ne a gidan namu? shigo mana?"
ƙarasowa ya yi ya zauna a inda ta nuna masa sannan ya gaishe su, bayan sun gaisa ya ce " Su Ya-Ya Shahbeer ba sa nan?, Mommy don Allah ki yi haƙuri ni wall...."
cikin sauri ta dakatar da shi da cewa "Ina sonka sabi da ka na son Ƴa-ƴana Sa'ad, ba dalilin da zai sa na kalle ka da laifin da na san ba kaine ka aikata ba."
murmushi ya yi gami da cewa "Na gode Mommy, amma fa har yanzu sun kasa yarda da ni ni ba halinmu ɗaya da Daddy ba ina so su yafe min amma sun kasa fahimtata."
rausayar da kai ta yi ta ce "Ba'a iya yi musu dole Sa'ad amma da na sa sun dena banzatar da kai, amma komai ya yi farko zai yi ƙarshe.
muryar Shahmeer ce ta daki dodon kunnensu, "Wane ɗan-iskan ne ya ce ka zo gidan nan?? ba na rabaka da bibiyarmu da tsohuwar maitar nan taka ba?"
Shahzain ya ce "Mommy me yasa ki ke mana haka don Allah?, ki ga fa yadda ki ka ba shi gurin zama a gidanmu."
Cikin ƙunci da damuwa Sa'ad ya ce "Allah ya huci Zuciyarku..."
a fusace Shahzaib ya yi kansa wasu shegun zafafan maruka ya yarfa masa guda uku kyawawa, "Maza ka bar gidannan tin da ba na gadon gidanku bane"
Shahzaib ya faɗa ya na huci gami da nunawa Sa'ad Hanya.
cikin sauri ya fice har ya na shirin faɗuwa, ya na shiga mota ya cewa direba su tafi gida, ɗora kai ya yi a jikin kujerar direba ya fashe da wani irin kuka me tsuma zuciyar me sauraronsa.
Ido rufe suka shiga zazzaga masifa a gurin tare da jan kunne ga Inna da Mommy akan kar su ƙara bawa wani wanda ya shafi Alhaji Basiru Boza ko da shimfiɗar fuska bare ta tabarma, da kyar Mommy da Innan su ka lallaɓasu tare da cewa ba za su ƙara ba.
tin da Mommy ta shige ɗakinta ba ta ƙara fitowa ba har washe-gari.
su ma su Beer ba wanda ya ƙara nemanta ranar da takaici su ka kwana.
Tin sassafe su ka ji ana bubbugar ƙofar bedroom ɗin ba su yi niyar buɗewa ba sai da su ka ji abin ba na ƙare bane.
tozali ya yi da Malika ta zuba masa tsayayyun idanunta wanda su ka ji kwalli rabaɗau kamar a cikinsu aka tisa kwallin, sanye take cikin riga da wando sai ɗan ƙaramin mayafi da ta zizara daga kanta zuwa kan kafaɗa.
cike da gadara ta ce "Yau ba ranar bacci bace a fito a rakani zan yi lelewa a ti-ti."
a zafafe Shahzaib ya zabga mata wani lafiyayyen tafi wanda ya ɗauke ji da ganinta na wani lokaci, cikin tsabar zafin Zuciya ya ce "Har kin isa ina bacci ki zo ki buga min ƙofa a matsayinki na wa????"
fashewa ta yi da kukan azaba ta na cewa "Allah ya isa ban yafe ba azzalumi me baƙin halin gado kawai, kuma wannan cin zarafin da kake min ka sani bashi ne wata rana sai na rama."
"Ni ne mugun naki?? a gurin ubanwa na yi gadon baƙin hali???"
ya faɗa tare da nuna ƙirjinsa da ɗan yatsansa, cikin ƙarfin hali da tsiwa irin ta-ta ta ce "Kai ka fi ma mugu mugunta muma Allah ya isa."
ya ɗaga hannu zai ƙara mata Shahbeer ya daka masa tsawa "Ka fara hauka ne Zaib? duk Azancinka a matsayinka na namiji ba yadda za ka iya tafi da yarinya ƙarama sai ta wannan hanyar?"
Tsaki ya buga gami da banka ƙofar ya dawo cikin ɗakin ya na cewa "Kasani ba na son raini Amma ita ba ta da wanda ta raina sai ni sai na ɓarar mata da haƙora sai na ga da abin da za ta dinga yiwa mutane Rashin kunyar."
Tsaki Shahbeer ya yi gami da cewa "Jariri (Shahmeer) do Allah je ka rarrashi yarinyar can, ka fiye Saurin hannu Zaib."
Miƙewa Shahmeer ya yi yana turo baki gaba da alama shi ma bai so rarrashin ba, a durƙushe ya sameta a bakin ƙofa tana ta ɓarza kuka kamar wadda aka yiwa wahayinsa, durƙusawa ya yi saitinta cikin tattausar murya ya ce "Malee,,," ba ta bashi damar ƙarasa faɗen abin da yake son faɗe ba ta tsinka masa mari da iya ƙarfinta.
cikin zafin nama ya yi gefa da fuskarsa gami da rintse idanunsa da ƙarfi, marin ya shige shi sosai da sosai dan kuwa ba zato ba tsammani kawai sai zafinsa ya ji, atake inda ta mareshin ya yi raɗau da shatin yatsunta zara-zara duka biyar ɗin ba wanda bai fito ba, idanunsa da suka cicciko da ƙwalla ya zuba mata ya na binta da wani fitinannen kallo wanda ta kasa gane me yake nufi.
wani mugun kwarjini ta ga ya yi mata wanda ya sa kukanta tsayawa cakkk ta na bin ƙwayar idonsa da kallo lokaci guda hankalinta ya fara barin jikinta.
Adadin kusanto inda suke da Safyan ya ke yi adadin ƙaruwar bugun Zuciyar Shukriya, wani dogon tunani Zuciyarta ta tafi yi sai da Maalik ya ce "Shukriya wannan shine Safyan Boza abokina kenan."
sai lokacin ta lura ashe har ya zo inda suke, sai da ta yi da gaske sannan ta saita nutsuwarta suka gaisa.
Maalik ya ce "Ƙanwata ce, haɗin Ammina kenan."
Safyan ya yi dariya gami da cewa "Ya yi kya mu je mu zauna ko?"
Kallon tawo mu tafi Maalik ya bi ta da shi ta yi saurin girgiza kai gami da cewa "A'ah, ku je kawai ni ka buɗe min mota zan zauna a ciki."
mamakin yadda ta rikice lokaci ɗaya ya hana shi yi mata musu.
tin da ta shiga motar ba abin da take kallo sai Safyan, yanayin motsa bakinsa da ƙifta idanunsa murmushinsa dariyarsa ba abin da ba ya burgeta, hankali da mutsuwarta da tunaninta gaba ɗaya sun gama salwanta akanshi lokaci guda, idan ya yi murmushi ba ta sanin lokacin da nata murmushin yake baiyana, "Masha Allah, Tubarakalla" su kaɗai take iya mai-maitawa a bakinta gaba ɗaya ta ma manta a inda take.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/4, 10:13 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
8
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
MOONASH Alƙaluma Shida.
Daga Ƙungiyar ELEGANT ONLINE WRITERS.
BANI DA HUJJA
Maimoon
SARƘAƘIYA
Shaahd
BARRISTER SHAHEEDA
Ayush
AUREN ƘAUYE
Nazlarh
ZUMUNCIN ZAMANI
Jikar Nashe
WATA HANYA
Indo
Maalik ne ya katse mata tunanin da cewa "Tunanin me ki ke haka?."
Sai a lokacin ta farga da dawowarsa, cikin ko in kula ta ce "Ba Komai."
bai ce mata komai ba ya figi motar da gudu dan kuwa shi ba ma'abocin tuƙin mota a hankali bane.
tsalle Auta (Shahzain) ya yi ya diro daga kan gado a matuƙar fusace, "Kam bala'i!! Jariri idan ba ka karya min ƙafar yarinyar nan ba da kaina zan karyata"
Shahzain ya yi maganar cikin jin zafin marin da Malika ta shararawa ɗan-uwansa.
Shahbeer ya ce "Zain ka fara hauka ne??"
a masife ya ce "Marinsa fa ta yi dan taga ana sauraronta shine za ta raina mutane ko sa'an wasanta ne??, Sai na ragargajeta in ga uban da zai tsaya mata."
Ya ƙarasa maganar gami da miƙewa zai nufi inda suke a durƙushe har lokacin kallon mage da ɓera su ke yi wa juna.
Cikin tsawa Shahbeer ya ce "Zain idan ka ɗaga ƙafarka daga gurin nan sai na tafaka, masu saurin manta halacci kawai"
ya yi maganar cikin ɓacin rai, zafi biyu ya haɗe masa ga raɗaɗin marin ɗan-uwansa ga takaicin hauragiyar da Su Zaib su ke yi, asali ma bai ga abin ɗaga hannu da Zaib ya yi ya mareta ba in da bai yi hakan na da abin bai kai haka ba.
Dawowa baya Shahzain ya yi ya zaune ya jingina da jikin gado gami da zabga tagumi ransa na wata irin tuya.
Cikin dakakkiyar murya Shahmeer ya ce " "Sata a gidan ɓarawo rance ne Malee!!!, za ki biya a inda daga ni sai ke ba me tsawatarwa anan ne za ki san wa ki ka mara."
daga haka ya miƙe daga gurin, kai tsaye sashin mahaifiyarsa ya nufa dan kuwa a wannan ƙadamin ita kaɗai ce za ta iya rarrashinsa in aka cire Shahbeer shi kuma a tafashe yake banda zafi ba abin da zai ƙara masa.
Saƙol Maleeka ta tashi cikin sanyin jiki, kukan ma ta dena sabi da wani abu me kama da Al'ajabi da yake yawo a cikin kowane sassa na jikinta har cikin tsakiyar Zuciyarta, ba ta nufi gurin Mommy ba dan kuwa ta san can Shahmeer ya nufa ɗakinta ta wuce sai da ta kulle ƙofa sannan ta samu nutsuwa, zama ta yi ta fara tunanin abin da ya faru gaba ɗaya lamarin gizo ya ke mata, Shahmeer ɗin ta mara? Shahzaib ne? ko kuwa Auta (Shahzain) ne? ko haka nan sai ta nutsu take iya banbance su yau kuma sun yi abin da tunaninta ya yi rikicewar da ko Shahbeer ɗin ba lallai ta iya ganewa ba, haka kawai take jin tamkar ba da Shahmeer ta ketawa wannan marin ba.
tunanin abin ya ƙi barinta ta rasa inda za ta sa kanta ta ji sauƙi ba shiri ta shirya ta fice daga gidan ta nufi Asibiti don duba Patient's ɗinta.
Sai da Mommy ta yi ƙoƙarin gaske sannan ta samu Ya kwantar da hankalinsa.
Su Shahzaib kuwa tin da Shahbeer ya yi magana ko uffan ba su ƙara cewa akan lamarin ba.
Shukriya, sagaraftu take ta faman yi a ɗakin ta kasa ko zama bare kwanciyar da bacci zai ɗauketa, tunanin Safyan da kuma makomar tunanin nata kawai ta ke yi, idan ya kasance abin da ta ke ji aranta har Zucyarta take ƙissima mata haka ne kenan wace irin aradu ta tarowa kanta?
ta san tsaurin Hajiya Dada ko za ta mutu ba za ta bari ayi jana'izarta ba tare da an ɗaura mata aure da Maalik ba tin da har ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 30