ƙasa-ƙasa da kai.
Shahmeer ne ya amsa gami da cewa "Ƙaraso Beauty Kalar kyau."
ƙarasowar ta yi ta durƙusa sannan ta ce "Hajiya ta na kiranku."
Shahzain ne ya haɗe rai a dake ya ce "Ke? Hajiya ma ki ke kiran Mommyn tamu?, daga yau da sunan da mu ke kiranta za ki dinga kiranta."
da sauri ta gyaɗa kai gami da cewa "To Yallaɓai."
Shahmeer ya ce "Me ke faruwa ne??"
"Dama Halime ce ta ke neman YaYa Shahbeer kuma kuka ta ke ta yi ta ƙi cin abinci wai sai dai su ci tare."
"Kam bala'i!"
Shahzain ya faɗa gami da zaro ido.
Shahzaib ya ce "Dallah ɓame bakinka Malam."
Shiru Shahzain ya yi, Shahmeer ya ce "Ki ce muna zuwa Beauty."
tashi ta yi da sauri ta yi hanyar komawa sashin Mommy.
"Shaƙuwa mugun tarko inaga fa Shaƙuwa ta fi So haɗari"
Shahzain ya faɗa ya na jinjina al'amarin.
Shahmeer ya ce "A'a, So ya fi shaƙuwa haɗari don ya fi ta illa, kuma shi Shahbeer duka ya haɗa."
"Allah ya taƙaita to" Shahzaib ya faɗa gami da miƙewa.
Kusa da Inna su ka sameta ta na kukanta tsakani ga Allah ita dai Inya ɗinta.
Mommy ta ce "Don Allah ku lallaɓa yarinyar nan, ba na so naga koke-koken nan."
Shahzaib ya ce "Amma Mommy kin san dai ta na gane Shahbeer akanmu anya kuwa za ta yarda?."
Shahmeer ya ce "Ni bari in Jaraba."
kusa da ita ya zauna ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ce " Baby kukan me ki ke? ai na dawo"
Ƙura masa ido ta yi na ɗan lokaci sannan ta ce "Inna ce!!"
"Ohh Inna ce ko?, ƙyaleta ba za mu da ita ba, maza ki ci abincinki."
buɗe baki ta yi gami da turo masa plat ɗin, "Wayyo!!" ya faɗa ya na shirin zaro ido Shahzaib ya dakatar dashi da cewa "Kana bari ku ka haɗa Ido wallahi tuburewa za ta yi don za ta gane ba Inya bane."
da sauri ya yi ƙasa da idonsa ya rausayar da kai sannan ya fara bata abincin a baki.
09:40PM
Alhaji Boza, Tagumi ya zuba da hanna-yensa duka biyu, ba shakka Rayuwa ta yi masa tutsun Jaki, tunani ne kala-kala ya ke yi, kamar an tsikare shi ya miƙe ya zari mukullin motarsa.
Gidan DR Idris (Wato, Baba) Ya nufa cikin sa'a kuwa ya same shi a gidan, ko gaisawa bai bari sun yi ba ya ce "Dr Don Allah ya za'ayi ɗana ya kuɓuta?"
Baba ya ce "A'a Boza Ɗanka ko ɗana?? ƴaƴanka Uku ai, ni kuma Shida.
"Ban gane nufinka ba, ka sami dai A'i matata ce.
"E, na sani amma ƴaƴan ai ba naka bane, ka faɗi sunansa sak!! ka dena wani ce masa ɗanka.
wani ƙullutun baƙin ciki ne ya tsayawa Alhaji Boza a maƙoshi, ya kasa gane inda DR ya dosa da maganar ba ƴaƴansa bane, idan haka ne to shi ina nashi ƴaƴan??. Dr ne ya katse shi da cewa "Kar ka damu Zuwa gobe in Allah ya yarda komai ya yi daidai, bincike ne kuma indai an yi shi da nutsuwa da gaskiya zai nuna gaskiya, to Alhamdulillahi ta nan ɓangaren ba'a samu matsala ba bincike ya tafi yadda ake so kuma ya nuna a cikin abubuwan da aka ce ya na aikatawa ba ko ɗaya da ya yi, yanzun haka ma in sha Allahu zuwa gobe zai yi free, amma fa Kabar Baya Ba Zani Yallaɓai Boza domin kuwa dole sai an Tuhumi Safyan akan sharrin da ya yi wa ƴaƴana.
Alhaji Boza ya ce "Alhamdulillahi, Alhamdulillahi na yi farin ciki mara misali, Allah ka ƙara kiyaye min ɗana daga dukkan wani sharri, ni Safyan ba ruwana da abin da za'ayi masa shi ya jawowa kansa."
"Okay To in sha Allahu gobe ya na gida.
"Ai kuwa zan je gidan nasu.
"Wannan ba ta shafe ni ba"
Dr ya faɗa gami da miƙewa.
Wayar Shahzain ce ta yi ƙara ya ɗauka gami da cewa "Kacau!!"
"Sai da kai Autan Oga, barka da Dare, dama Yarinyar nan Shukriya me rawar kai na ji ta ƙaryata kanta kuma ta bada labarin Mahaifinku har da muryarka na ji ka na cewa Alhaji Basiru Boza Mahaifinka ne, da gaske take ko mu haura kanta??"
Sororo Ya yi, ya rasa ma ta cewa tunann yadda akai ma ta samu muryar tashi har ta ɗora ya ke yi sai yanzu ya tuna ƴar-Jarida ce za ta yi iya yinta don ta naɗa, wani mugun takaici ne ya lulluɓe shi da kyar ya ce "Bayan haka me ta ce?"
"Wai ƙaninku ne Safyan kuma shi ne ya bata labarin har da wani Ɗan-sanda kuma ta na da Hujja a rubuce da suka bata, sannan Mamanku ma ta na da Aure har yanzu kuma bayan shekara huɗu da Aurensu aka sameku, wannan duk a bakinka na ji, gaskiya dai ba ta faɗi wani abu mara daɗi ba kawai ta ƙaryata kanta ne ta faɗi gaskiya dama ƙila kuɗi ya biyata.
"Okay ku ƙyaleta, amma Ku je inda ta ke ku maida ita gida dan Safyan bashi da Gado me karaga zai iya illatata jin ta fallasa shi.
"An gama Autan Jagayya.
daga haka ya katse kiran.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
...................................
ZANNUWAN GADO SAYE KO SARI.
Don ƙarin bayani da ganin style ku shiga wannan lambar,
👉🏽 09079885632
sai na ji ku
*INDO*
[12/19, 11:18 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
19
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Dafe goshi ya yi gami da cewa "Ohh ni Jikan Fulani."
"A gidan Ubanwa ka zama jikan Fulanin?"
Shahzaib ya wurga masa tambayar gami da kashe shi da wata muguwar harara.
Dariya Shahmeer ya shiga tuntsurawa gami da cewa "Kara kai da shishshigi ba kwarjini."
Shahzain ya murmusa kafin ya ce "Ba wani kara kai, ai naga da Hausawan da Fulanin duk ɗaya muke."
"Ba ni da wata alaƙa dasu, Asalin Bahaushe ne ni ka ji!"
Shahzaib ya faɗa ya na dariya, Shahzain ya ce "Nima wahala ce ta sa ni na furta ka ji!, Yarinyar nan ce ta ke neman sa ni a tsilla-tsilla, ta sa Alhaji Boza zai ji daɗin bacci yau kuma ta sa kanta a gonar Safyan."
Dogon Tsaki Shahzaib ya ja kafin ya ce "Akan hakan ka ke neman ɗaga hankalinka?? abin da ya shafi ɗan-iska da ƴar- iska har wani tayar maka da hankali zai yi? i junansu ne fa."
"Ba haka bane Ƙarami, Ba iskanci bane sharrin Zuciya ne da rashin sanin gaskiya, amma banga alamun iskanci a tattare da ita ba.
Shahmeer ya ce "Gaskiya kam, daɗina da Ƙarami kwaran-kwatsam ya ke sakin magana duk wadda ta zo kan harshen sa ko gatsa ta ba ya yi bare ya tauna."
Tsaki ya kuma yi sannan ya ce "Kai da ka san Doka kenan."
Shahzain ya ce "Kai ma ka santa ba ka amfani da ita ne."
Shahmeer ya ce "Ya isheni dallah ban son hayaniya ku yi mini shiru zan kira Masoyiyata."
"Kai baje maganarta dalla mu yi magana akan abin da ya shafe mu"
Shahzain ya faɗa gami da janyo Laptop ɗin da ke ajiye a kusa da Shahzaib.
ci gaba su ka yi da tattaunawa akan lamuransu.
Hajiya Dada rai ɓace ta yi sallama, Idon Shukriya kamar su faɗo sabi da tsoro da razani duk ta zazzare su, shi kenan tawa ta ƙare, ta faɗa a can ƙasan Zuciyarta.
Mami ta amsa sallamar cikin sakin fuska gami da yi mata marhaba, Ko zama ba ta yi ba ta fara da cewa ''Kin iya aiki Shukriya ai kin yi ƙoƙari, wato wannan shine burin naki da ki ke son cikawa har ki ka kori Maalik daga Ƙasar shi ta haihuwa ko??."
"Allah ya baki haƙuri Dada wallahi nima ba son raina kena..."
"Rufe mini baki do Allah"
Hajiya Dada ta faɗa cikin tsawa gami da kawo mata hamɓara, "In banda rashin Tunani irin naki meye haɗinki da abokin miji?? gashi nan ya kunyata ki a idon Jama'a ɗan aikin naki ma babu.
Mami ta ce "Ƙwarai kuwa, ai mun yi baƙin ciki da wannan sakaci nata, Dogara da ƙafafunka ai ya fi da wani mutum ko wani abn amma kin ga yanzu ba aikin, sai ta zauna a gida ta na haɗa kafaɗa dani."
Dada ta ce "Wannan haka ya ke, ai haka ta nema kuma ta samu, ni dai ba komai ne ya kawo ni gidan nan ba dan ke na zo don in jaddada miki gami da ja miki kunne akan kar tsautsayi ya sa ki so wani ɗa ko ki bashi dama ya so ki bayan ɗana ko waye ƙaryarsa ƙaryar Uwarsa indai ina raye Sai Na Aurawa ɗana ke, ki goge komai daga cikin tunaninki ki sa wannan, kar ki bari ma tunanin wata Duniya ya zautar da ke."
Ƙasa ta yi da kai kamar tsohuwar munafuka, Hankalin Dada ya na barin kanta ta tashi ta gudu ɗaki.
Abeer ne ya kalli Shahbeer wanda ba su daɗe da dawowa gidan ba shi da Baba, ya na murmushi ya ce "Na ga Suffar gaskiya da Alkairi YaYa Shahbeer, idan ka na kyautatawa mutane kai ma sai Allah ya kyautata maka."
Murmushi kawai Shahbeer ya yi, Baba ya ce "Gaskiya ne wannan, Allah ya ƙara tsarkake zukatanmu."
Mommy ta amsa da "Amin''
Sallama Alhaji Basiru Boza da Sa'ad su ka yi, Baba ne ya amsa ba yabo ba fallasa.
Shahzaib ya ce "A'ah ?gaiyato mana jama'a ka yi ne Baba?"
"A'a Yaro, sai dai in shi ya gaiyaci kansa ko kuma Hajiya Aisha ta gaiyato shi."
Da sauri Mommy ta ce "A'a ba ni na gaiyato shi ba."
tin da suka shigo Shahbeer ya zuba musu wani mugun kallo na ƙiyayya har su ka ƙaraso, miƙewa ya yi gami da ɗaukar Ricky Karensa ya saɓa shi a kafaɗa ya na shafa shi, Bin bayansa su ka yi su duka, gurin ya rage daga Baba sai Alhaji Boza da Sa'ad da Mommy.
ƙoƙarin zama ya fara yi Mommy ta dakatar dashi da cewa "Kar ka zauna min a gida."
"Me yasa Aishatu?"
ya faɗa gami da miƙewa ya fasa zaman.
Ba ta yi magana ba sai kuka da ta fashe dashi, ta miƙe za ta koma sashinta, cikin sauri ya dakatar da ita da cewa "Aisha Don Allah ki fahimceni, ni..."
"Ba abin da za ka faɗa mini face ƙarya da Kalmomin yaudara, Zalumcin naka har kan ƴaƴanka ya ma wuca kan wasu daban, anya kuwa kai mutum ne ba Dabba ba?"
Baba ne ya miƙe gami da cewa Sa'ad mu je Gurin Su Shameer, binsa ya yi suka rankaya.
"Ko me na aikata musu ba zan iya binsu da wannan mummunan sharrin ba, Safyan ne shi da Mahaifiyarsa."
sassauta Murya ta yi cikin kuka ta ce "Ya zama Dole Ƴaƴana su dinga ganin Iftila'i kala-kala domin ka riga ka gada musu wahala, indai jininka ya na zagayawa a jikinsu Dole ne kusakuran da ka aikata su dinga bibiyarsu, ina jin tsoron faruwar wani abin bayan wannan."
Wasu zafafan hawaye ne suka wanke masa fuska, cikin sanyi ya ce "Tabbas Ƴaƴana ne kuma ko meye ya faru da su Laifin nawa ne, Ki yi haƙuri Aisha..."
"Da bani da haƙuri ai da ba mu Haifi ƴaƴa tare ba, don Allah ka ƙyale ni in ringumi ƴaƴana tare da ƙaddararsu kar ka sake shigowa rayuwata ka ƙaro min wata wahalar ba zan iya jura ba, ka tafi Don Allah."
"Shi kenan Zan tafi, amma ba zan dena neman yafiyarki gami da baki haƙuri ba.
"Wannan duk abin da ya shafeka ne.
daga haka ta nufi sashinta cikin sauri.
suluf-suluf ya fice daga gidan Zuciyarsa sam ba daɗi ya so ganin ƴaƴansa amma hakan ba zai yuwu ba dan kuwa ya san ba yadda za'ayi su saurare shi, tabbas ramin ƙarya ƙurarre ne gashi yanzu ya ƙure masa, zai yi ƙoƙarin janye jikinsa daga garesu har zuwa nan gaba tin da ba sa so.
da wannan tunanin ya shiga motarsa hango Sa'ad ya yi ya na tafe ya na kuka, da sauri ya fito ya na tambayarsa ya akai , sai da ya shiga mota sannan ya ce "Daddy ka cuci rayuwar ƴaƴanka, ba ka haɗu ba Daddy, kowane Uba ƙoƙari ya ke ya haɗe kan zuri'arsa amma kai farraƙemu ka ke."
"Me su ka yi maka?"
"Ka san dai bai wuce su ci mini mutunci ba, kuma hakan su ka yi, sun jaddada mini cewar sun tsanemu daga ni har kai har abin da ya shafeka, ka ga ai ba ka da riba, Allah ka dagar damu akan tafarkin gaskiya, Daddy lokacin da nake Ƙoƙarin fahimtar da kai kuskurenka tsanata ka yi, yanzu kuma ka gane a lokacin da hakan ba amfani gareka, dama ba dan Allah ka dawo garesu ba sai dan ka na son ka zama uwa uba a harkar Siyasa."
Alhaji Boza Bai yi magana ba ya bawa motarsa wuta.
Tsaki Shahbeer ya tafka kafin ya ce "Yaudarar banza da wofi kawai."
Shahmeer ya ce "Ai kuwa fa, duk mugun abu ne a Zukatansu gaba ɗaya ba mutanen kirki bane dashi da ƴaƴan nasa, aikin banza, ni wallahi ko sunansa ba na son ji, idan kuma ya cika takura mana sai na targaɗa rayuwarsa wallahi."
Shahzaib ya ce "Ni na ma gaji da ji, don Allah ku yi shiru."
Baba ya ce "Gaskiya ne shiru zai fi Alkairi akan irin magan-ganun nan."
Abeer ya ce "Gwara dai a jawo wata hirar.
ci gaba su ka yi da wata Hirar Inna ta shigo su ka ci gaba da fafatawa.
"Ma'arufa!!" Umma ta kira sunanta, ta amsa gami da cewa "Gani nan zuwa Umma."
fitowa ta yi ta zauna kusa da Umman gami da cewa "Gani"
"Yauwa game da labarin da aka yaɗa ɗinnan, wai kuma da gaske ne??"
"To ke Umma meye naki a ciki?"
"A'a wai kinsan ance tambaya mabuɗin ilimi.
"To ƙarya ne, kar ku fara yarda ma da abin da baku tabbatar ba, wani abin camfe-camfe ne, wani kuma sharri, wani Zato, amma kuskure ne ku yarda da irin wannan dan kuna ɗaure mutum ba tare da ya yi muku laifin komai ba kuma Alhaki ku ke ɗauka.
"To Mun Dena Ma'arufa; Man-shafawar-mu ya ƙare ki sayo mana irin Cream ɗinnan me gyara fata kin ji?"
''Gyaɗa kai ta yi a ranta tana tunanin wai ita Umma ba ta damuwa da inda nake samun kuɗi ita dai burinta na yi musu komai.
"Tunanin me ki ke ne? ; na ma manta Jiya Bashir ya zo bakya nan.
"In ya ƙara Zuwa ki leƙa ki ce masa ya raka Zuwa gaba idan zai iya jirana ba yanzu za ku Aurar da ni ba.
"A'a me yasa za'ayi hakan Ma'arufa?"
"Sabi da ba ku shirya ba, sai da kuɗi fa ake Aurar da ƴaƴa ko da maza ne bare mace, Don Allah ki bashi haƙuri ki ce ya ƙara jira sai nan gaba, yanzu ba mu ajiye ba bamu ba wani ajiya ba sai dai in ba za ki yi mini komai ba haka za ki Aurar da ni.
"Gaskiya ki ka faɗa kuma Wallahi, in sha Allahu zan Bashi haƙuri, nasan indai ya na sonki to zai haƙura.
gyaɗa kai kawai Ma'arufa ta yi ba tare da ta ce komai ba.
ya na shiga Ɗaki wayarsa ta fara tsuwwa, ɗauka ya yi ba tare da ya duba ba ya kara a kunne gami da sallama.
Ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta ce "Na yi maka laifi ne Shahbeer Ɗina."
idanunsa ne su ka ƙara girma jin yadda ta kira sunansa har da wani haɗawa da nata, dannewa ya yi ya ce "Dr Dr Ya Mom, kwana da yawa."
"Ba na jin ka na nema na ko da ta hanyar cigiya ne, in laifi na yi maka Allah ya huci Zuciyarka YaYa Shahbeer, ba na so ka yi Fushi dani in ba ka haƙura ba ma na yarda ka yi min hukunci amma don Allah kar ka banzatar dani.
ta ƙarasa maganar cikin tattausar Murya; "Ko kaɗan ba ki yi mini Laifi ba Malika, Na ga kwana biyu ba ki zo mana ba ko lafiya??"
"Wata ƴar damuwa ce ke damuna amma in Allah yarda za ta yaye wataran sai labari.
"Allah i yarda, do Allah ki gaishe mini da Mom za mu zo ma gaisheta in sha Allah.
"To zan gaya mata.
daga haka ya katse kiran ya yi wurgi da wayar zuwa kan gado.
Bayan wani lokaci.
A kowane ɓangaren za'a iya cewa ba abin da ya sauya haka rayuwar ta ke cuɗawa.
"Tunanin me ka ke Inya?"
Mommy ce ta yi masa tambayar gami da tsare shi ido.
"Mommy watan Haihuwar Halima ya kama."
Baki ta saki ta na kallonsa har na ɗan wani lokaci kafin ta yi murmushin takaici ta ce "Ka na tsoratani da irin wannan Ɗabi'un naka, meye naka a cikin Lamarin Haihuwarta?"
Inna ta ce "Ai tausayi ma wani Abu ne, haba A'i, ya kamata ki dinga saƙa Alkairi a Zuciyarki, ni wallahi ban sanki da haka ba."
Lumshe Ido ta yi ta buɗe sannan ta ce "Inya ka na son Halima Ko??"
da sauri ya ɗago Brown Oily Eyes ɗinsa ya zuba mata kafin ya ce "Mommy amma ba wannan shafin na taɓa ba ai."
"Ka taɓa shafin mana tin da ka taɓa abin da ya shafeta, ka ce dai abar zancen kawai.
Inna ta ce "To abarshi mana tinda ba labarin shiga Aljanna bane?"
"Ai an barshi."
Shahbeer ya bata amsa.
Malika ce ta yi sallama, ta ƙaraso a kasalance. Mommy ce ta ce "A'a yanzu muke ganinku?"
Murmushin ƙarfin hali ta yi gami da gaishe da Mommyn, ko kallon inda ta ke Shahbeer bai yi ba sai ma tashi da ya yi ya bata guri.
Da ido ta raka shi Zuciyarta sam ba daɗi, gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, yanzu magana ma sai an tona ta ke yinta, Damuwa ta kafa sansani a cikin rayuwarta, tausayin kanta ne ya kamata ta yi ƙasa da kai cikin Raunin Zuciya.
Inna ce ta ce "Fisabilillahi Wannan Ɗa anyi mara mutunci, amma ya na ganin mutum ko ya tsaya a gaisa?, ki ga yadda Malika ta yi hankali abin ta kamar ba ita ba."
Danne Damuwarta ta yi cikin sakin fuska ta ce "Ba komai Inna ai ba gurinsa na zo ba, dan bai saurare ni ba ba ji."
Mommy ta ce "Ai mutunci ya fi kuɗi, gaisuwa ai ba faɗa bace."
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
01:00AM
Juye-juye ta ke a gadon ta kasa bacci, tin Inna tana lallaɓata akan ta yi har ta gaji ta kwantar da kunnuwanta, zuwa wannan lokacin ta fara jin sautin kukanta ƙasa-ƙasa, da sauri ta tashi ta na faɗin "Oo, ni Ƴar Mutanen Asali, Halimatu me ke damunki??, lafiya ki ke kuka??"
ba ta yi magana ba sai ma ƙara ƙarfi da kukan nata ya yi.
ganin ta na riƙe ciki ya sa Inna faɗin "Lahaula-walaƙuwata-illabillahil'aliyyul'azim, A daren nan Sadiyayye ni kam yau na ga ta kaina.
waya ta ɗakko ta kira Shahbeer ta sanar masa abin da ke faruwa, hankali tashe ya diro daga kan gado ya nufi sashin Innan.
Inna kuwa ta na katse kiransa ta kira Mommy ta sanar mata, kusan tare su ka iso, Mommy ta ce "Mukhtar, Ka je ka yi mata Addu'a ka ji?, In Allah ya yarda za ta haihu lafiya."
gyaɗa kai yanyi ba dan ya so ba ya koma sashinsu.
Addu'a ya yi mata sosai sai bayan ya yi sallar Asbahi bacci me cike da mafarkai iri-iri ya yi awon gaba dashi.
sai 09:28am ya farka ya ga duk ba sa ɗakin da alama sun dire sun yi gaba, agogo ya kalla hakan ya sa ya yi saurin tashi ya na yamutsa sumar kansa, dan lalacewa wai ni ne da bacci har Tara?, ya yi wa kansa tambayar, Zuciyarsa ce ta yi wata muguwar bugawa da ya tuno halin da Halima ke ciki, da sauri ya nufi Banɗaki ya watsa ruwa ya na fitowa ya ɗauki kayan da su Shahmeer su ka ware masa ya zura, ko mai bai shafa ba ya fita ya nufi sashin Mommy.
a Falo ya samesu Su na ɗan taɓa hira sai dai ba walwala a tattare da su, tin daga nan ya ji ya fara tsinkewa, "Inna, Ina kwana, ina Mama ta ke? ya jikin Halima?"
duk a lokaci ɗaya ya zubo mata tambayoyin, Inna ta ce "Halima ta sauka lafiya, Ta haifi Ɗa Namiji me kama da kai."
"Da ni??????????"
ya jefo mata tambayar cikin yanayin kaɗuwa.
Shahmeer ya ce "Ko shakka Babu damu ya ke kama yaron nan Shahbeer."
Daidai Lokacin Malika da Mommy su ka ƙaraso wajen da yaron a hannun Mommy kai tsaye inda ya ke ta nufa ta miƙa masa shi gami da cewa "Yaron Jinin Boza ne."
a matuƙar firgice ya karɓeshi ya rungume gami da zuba masa idanu, Shi kuwa ɗan-jariri kamar ance buɗe ido ya waro su akan Shahbeer, baki buɗe ya ke kallonsa musamman ƙwayar idonsa wadda ita tafi komai ɗaukar hankalin me kallon fuskar yaron. Dalilin da ya sa aka fi gane shi a cikin ƴan uwansa Duk su huɗun babu me irin ƙwayar idonsa, tashi ta banbanta da ta kowannensu, sai kuma yanayin salihancinsa amma babban dalilin kenan, yau kuma gashi ya yi tozali da Jaririn da ya ɗakko kalarsa sakk!! shi kansa sai ya ji ya fara tsoron kansa; ko Mahaukaci idan ya kalleshi ya kalli Jaririn zai ce sun yi kama ta Asali ma ba kaɗan ba.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 30