ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[1/12, 6:46 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
38
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Suna nan tsaye har ya fito riƙe da hannun Zakiyya sai ƙasa take da kai don kuwa tsoron Maalik ta ke ji.
Shahbeer ya ce "Yanzu ina buƙatar kwanciyar hankali, akanka kuma ba zan kasa bacci ba don haka shiga tsakaninka da ƙanwata ya zama dole, duk wata Alaƙa ma da za ta haɗamu da kai na janyeta, ka je ka rayu mu ma ka barmu mu rayu cikin farin ciki, Na barku lafiya." daga haka ya yi hanyar fita, "Ya Shahbeer idan fa ka ce kowace Alaƙa ka na nufin har Aurena da Shahzain ka janye" ta yi maganar cikin ɗaga murya, ba tare da ya juyo ba ya ce "Hakan nake nufi" bai saurari abin da ta ke cewa ba ya fice.
Riƙe ƙugu ta yu a masife ta ce "Kan uban nan, Maalik zalumcin naka har ya kai ka raba ni da Aurena??, waye kai da ba za ka haƙura da Abin da Allah ya ƙaddara maka ba?, ai kuwa za ka gane kurenka, sai na yanka-ka a gidan nan sai ka yi me dalilin." abin Duniya ya gama rikice masa, har wata muguwar zufa ta wahala ya ke yi, cikin rawar baki ya ce "Ki fahimce ni Shukriya nima ban san hakan za ta faru ba, ko abu ɗaya ban yi don na cutar da ke ba wallahi son da na ke miki ya fi gaban nan, kuma na riga na haƙura Dada ce ta ƙi haƙura banda ina ba ta haƙuri da tuni ta yi abin da za mu zo mu ji kunya, ashe ma Mommyn Ƴar-uwarta ce." ya na juyowa ya ga babu Shukriya a gurin, da sauri ya yi cikin gidan ya na ƙwala mata kira, ta firo daga kicin a haukace hannunta riƙe da wata lafiyayyar wuƙa, rufe ido ta yi kamar sabuwar mahaukaciya ta yo kansa ta na cewa 'Tin da ka shiga tsakanina da Mijina sai na yanka-ka ba zan haƙura ba nima sai na shiga tsakaninka da rayuwarka." a tsorace ya ce "Haba Shukriya, don Allah ki fahimce ni mana."
ganin za ta yarfa masa yanka ya sa ya fara zille mata, duk yadda ya so ƙwatar wuƙar ya kasa don kuwa ta tubure Ba abin da ta ke kira masa sai yanka kuma farmakarsa ta ke yi da gaske indai ta samu dama yanka shin za ta yi; zuwa yanzu ya yarda Aljanu gareta ko ciwon hauka, sai da ya gama gajiya ya galabaita sannan Allah ya bashi damar shigewa ɗaki ya kulle, numfarfashi ya dinga yi bayan ya huta sannan dubarar kiran Dada ta zo masa, ya kirata ya sanar mata abin da ya ke faruwa kuma ta ce gata nan zuwa.
Shukriya ta na zaune da wuƙarta a ƙofar ɗakin Dada ta yi sallama, saɗaf-saɗaf ta shigo a ɗan tsorace.
Shukriya ta ce "Yauwa Ammi kin ganshi ya raba ni da Aurena ko, ki zo ki yi masa magana ko in yanka shi.''
jiki na tsuma Dada ta ce "Yi haƙuri ƴata Shukriya, ai kinsan Maalik yaro ne akwai ƙuruciya a tare da shi, shi yasa ma ya yi miki haka, ajiye wuƙar kin ji ƴata, ai ba zai kuma ba kuskure ne ki yi haƙuri."
"Dama ai ke ki ke koya masa, sai na yanka ku duka."
ta faɗa tare da yunƙurawa ta miƙe, kan Dada ta yi ta na cewa "Sai na yanka ku, ba zan ƙyale ku ba, ni sai na yanka." Addu'o'i Dada ta shiga jerowa jikinta na kakkarwa, da sauri Maalik ya buɗe ƙofar cikin ɗaga murya ya ce "Shukriya kar ki taɓa Ta don Allah, ni ki yi min ko me za ki yi mini."
Da sauri Dada ta ce "Ni na fi sonka akaina, ba na son na rasaka gwara ni ta hukunta ni."
zamewa ta yi ta faɗi sulululu cikin nutsuwa har ta taɓa ƙasa.
Dada ta nisa Maalik ya sauke ajiyar Zuciya. "Ammi kin ga ko? rashin haƙurinki ne ya jawo mana, ba dan ina da sauran kwana ba ai da tuni yarinyar nan ta kashe ni.
"Ai sai mu godewa Allah, Aljanun nata sun tafi, mu yi sauri mu kaita gidansu kafin Aljanun su dawo.
"Ammi wai wacece A'i ashe dama Mahaifiyarsu Ɗan-wa da Ɗan-ƙani ku ke ban sani ba??"
cikin mugun mamaki ta ce "Ɗan-wa da Ɗan-ƙani??? ni da Babar tasu?? A'i??"
"E, ƴar Baba Aminu Aisha, wato ke kin ma manta da ita bayan ke da Baba Habibu ku ka rabata da jin ɗumin danginta har ma da iyayenta.
hannu ta ɗora akai ta fara maimata Innalillahi, ya yi mata shiru har ta gama sannan ta ce "Na shiga Tara, ka na nufin A'in gidanmu ce Mahaifiyar Yaran nan huɗu??, Subhanallah, Allah me iko, wannan shi ake kira Ishara, Allah ya haɗa mata Masarautarta anan cikin iyalinta hankali kwance duk da cewar ina ganin na rabata da wani sashi na rayuwarta, Subhanallah, Allah ka yafe mini, son Zuciya ya na kaimu ya na baro mu, a lokacin da Zuciya ta raya mana abu sai mu aikata ba tare da tunanin me kyau ne ko akasin haka ba, Yanzu Aisha za ta yafe mini kuwa anya??"
Maalik ya ce "Zancen gaskiya ya baiyana kenan, dama ai biri ya yi kama da Mutum, ai ba halinku ɗaya ba da dai ke ce na san ba za ki yafe mata ba sabi da mugunta amma tinda ita kyakkyawar Zuciya gareta za ta yafe miki."
"Ba komai ko me ka faɗa Maalik, da ban yi ba da ba za ka ce ba, dole ma ta tashi tsaye ta Aurawa ɗanta Shukriya ko dan haɗa zumunci tsakaninmu, ta yi daidai wallahi, gaskiya na yi abin kunya, tir da irin wannan baƙin hali na mugunta, abin ba kyau ni dai na yi nadama na tuba Allah ya ganar da masu irin halina su dena su tuba, Ni dai in Allah ya yarda ba zan ƙara zalumtar kowa ba."
"To Allah i sa, ni dai mu kai yarinyar nan gidansu kar Aljanunta su dawo.
Dada ta ce "Ɗebo ruwa ka ji?" ɗebowa ya yi ya kawo ta yayyafa mata, ta tashi a firgice sai kuma Atishawa.
Maalik ya koma daga bayan Dada sannan ya ce "Shukriya? tashi mu je gida."
tashi ta yi ba gardama, su ka yi gaba ta na biye da su har su ka isa mota, Maganar Duniya sun yi mata amma shiru har su ka isa gidansu.
Anan ɗin ma jimamin abin aka zauna yi tare da Alhaji Ibrahim har ma da Mamin Shukriya, Sun yi mamaki sosai da Dada ta gaya musu kowacece Aisha.
Motar shiru kowa da tunanin da ya ke yi, Zakiyya ce ta katse shirun da cewa "Ya Shahbeer shi kenan na rabu da Maalik?, ni fa Yanzu ina son shi wallahi." ta yi maganar cikin sanyi.
Murmushi ya yi gami da cewa "Haba mana Ƙanwata, shi ɗin banza uwarsa ma ta ganmu ta ƙyasa bare shi, bar Ɗan-iska zai zo ya sameki."
ta murmusa gami da cewa "To."
ba wata hira su ka yi ba har su ka je gida.
Tin daga ranar Maalik bai ji ɗuriyar Zakiyya ba haka ita ma ba ta ji ɗuriyarsa ba.
yanzu ba shi da tunani sai nata, idan ya tuna azabar da ya sau gana mata sai ya ji haushin kansa ya kama shi, gaba ɗaya hankalinsa ya gama karkata zuwa kanta neman ta hanyar da zai samu sasanci kawai ya ke yi amma ya rasa wanda zai tara da maganar.
Ma'arufa, suna zaune su na hira Tare da Su Umma Abban ta ya yi sallama, cikin mamaki su ka tashi tsaye su na kallon hanyar shigowa gidan, ganin shi ɗin ne da gaske ya sa farin ciki ya lulluɓe su, da sauri ta ƙarasa wajensa ta karɓi jakarsa cike da murna da farin ciki ta ke masa sannu da zuwa.
Cikin farin ciki su ka janyo shi ciki Usman ya na cewa "Abba ka kalli gidan da mu ka dawo bayan ka tafi."
ya yi murmushin takaici kafin ya ce "Haka ne Usman, gida ya yi kyau sai dai na san duk da haka farin cikinku bai cika ba tinda ba na nan.
Umma ta ce " Zauna dai yanzu ba shine lokacin hirar nan ba, tinda dai Allah ya dawo da kai lafiya shi kenan, amma ina fatan ba za ka ƙara tafiya ka barmu ba."
ya ce "In sha Allahu ba zan ƙara barinku ba."
bayan sun zauna ko huta bai yi ba Usman ya fara binsa da tambayoyi, sai da Ma'arufa ta hanashi sannan ya haƙura.
Fitowa ya yi cikin sanyi ya zauna kusa da Daddynsa, Dada ta ce "Wai kai me yake damunka ne?"
da sauri ya ce "Ni dai Daddy a maida Shukriyar can a dawo mini da Matata."
Daddy ya ɗan murmusa kafin ya ce "Daga baya kenan, ashe za ka dawo ka nemeta, to ni gaskiya ban san me zan ce maka ba don ba na son harkar ƙaranta, ka sa mun karɓa maka Auren ƴar Mutane ka zo ka wulaƙantata yanzu kuma idan mu ka dawo maka da ita ba mu san halin da za ka jefata ba, bugu da ƙari ma Mahaifiyarka ba ta sonta ina ganin gwara ku sauwaƙe mata kawai."
cikin sauri ya tari numfashinsa da cewa "Ina ba zai yuwu ba wallahi, ni in saki Matata? wallahi sai dai in koma gidansu in tare indai ba su dawo mini da ita ba, ni zan bata haƙuri kawai nasan za ta haƙura, don Allah Daddy ka temaka mini."
Daddy ya ce "Ai ita yarinyar ladabi take ga duk abin da yayyenta su ka ce, indai ta haƙura Shahbeer bai haƙura ba ai anyi ta banza, ya riga ya kafa mini sharuɗa akan dawowar Matarka muddin mun bi su za mu sameta"
"Don Allah Dad wane sharaɗi ne? wallahi zan iya ko menene, hankalina ya gama tashi tausayinta na ke matuƙar ji sabi da na wahalar da ita, ina so ta yafe mini Daddy ka faɗa mini."
"Ka riga ka rantse akan za ka iya ko mene akanta ko??, to Sharaɗinsa shine ko a ciki ko a waje kar ka ƙara danganta ƙanwarsa da wata, ina nufin..."
da sauri ya katse shi da cewa "Daddy na dena wallahi a yanzu ma ka gaya masa na dena, tin daga ranar da tabar gidana in ba ita ba ba na tunanin kowace mace, wallahi na dena kuma ba zan ƙara ba ita kaɗai ta ishe ni rayuwa."
"To Alhamdulillahi, na ji daɗi kuwa da ka dena don aikin Haram ba abin yi bane."
Dada ta ce "Ku na ta maganarku kun yi mini banza kun ma manta da ni a gurin ko? yanzu Maalik ba ni da amfani kenan duk irin gatan da nake nuna maka."
Daddy ya ce ''Maganar Aure ake yi ke kuma macece ina ganin ba sai an sako ki a ciki ba, yanzu komai ya wuce Maalik in Allah ya kaimu gobe za mu je sai mu ji ya za'ayi."
Dada ta jinjina kai, Duniya kenan, duk goyon bayansa da ta ke yi akan ya yi abin da ransa ke so yanzu gashi ta tashi a sansoriyo sabi da ba hanyar kirki ta ɗora shi ba. jikinta ne ya ƙara yin sanyi ta ƙara yin dana sani akan irin halayenta na son Zuciya.
Murmushin farin ciki ya yi gami da cewa "Yauwa haka na ke son ji Na gode Daddy."
"Ba godiyar kawai nake buƙata ba, ka kula da mutunci da kimar ƴar mutane sannan ka kula da haƙƙinta, ka zamo me Adalci gareta..."
Nasihu ya ci gaba da yi masa gami da nusar da shi akan rayuwar Duniya.
Gabanta ne ya yanke ya faɗi jin ƙarar shigowar saƙo a wayarta, har cikin ranta ba ta son Dubawa amma ba za ta iya jurewa ba duk da kalaman su na bala'in tsorata.
a hankali ta ɗauki wayar ta buɗe ta saki murmushi ganin saƙon ne dai tunaninta ya bata daidai.
sai da ta sauke ajiyar Zuciya kafin ta fara karantawa.
"Assalamu Alaikum
Ina faran farin ciki da walwala a tare da ke, Barka da wannan lokaci, ina miƙo gaisuwa da ban girma ga Sarauniyar kyawawan Mata, ba iya kyawun fuska ba kyakkyawar Zuciyarki da kyawun halayenki sun fi komai sa ni Alfahari su ke sa in ji tamkar ni ne Autan Maza, sai dai ina cikin damuwa kasancewar har Yanzu Kin kasa Amincewa da Soyayya gashi na riga na kamu da Sonki ba tsumi ba dubara, ki tausayawa Zuciyar da ta riga ta mallaka kanta gareki, na riga na zamo miki tamkar bawa ina fatan ki zamto mini Adalar Sarauniya; Bayan haka ina son in ce Ba na son ganinki cikin kaɗaici, ki dena yawan tunane-tunane sannan ki na kaɗaita kanki, a yanzu ma haka babu kowa a kusa dake sabi da kin fi son kaɗaicewa."
Rungume wayar ta yi tare da share ƙwallah gami da murmushi, cikin rawar Murya ta ce "Kowa da kalar Ƙaddararsa ni kuma Allah ya jarrabeni da Son Aljani, Ba zan iya banzatar da Soyayyarka ba domin nima na kamu, ko da ba jinsinmu ɗaya ba ina fatan in rayu tare da kai har ƙarshen rayuwata."
Murmusawa ta yi kafin ta fara rubuta masa amsa "Don Allah waye kai? ka nuna mini kanka ko da sau ɗaya ne."
"Lokaci! shi zai nuna....
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*Ku yi Share pls domin masu bibiya su samu, ba ni da cikakken lokacin yi😊*
*Indo*
[1/13, 10:22 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
39
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
"Lokaci shi zai nuna ba ni ba."
Murmushi ta yi tare da cewa "Allah ya kawo mini wannan lokacin."
ta ƙara maimaita karanta saƙon, Kira ta tura wa lambar a karo na ba Adadi don kuwa kullum a ba ta kira ba ta kira Sau goma shabiyar amma ba ta tafiya. Yau ma hakan ce ta kasance, sanin daga haka maganar tasu ta ƙare ya sa ta ajiye wayar a gefe, cikin ranta ta na Addu'ar samun mafita daga wannan tarkon so da ta faɗa.
"Abbanmu wai ya akai ka dawo??"
Usman ne ya jefawa Abban nasu tambaya, idanu su ka zuba masa don jin amsar da zai basu don kuwa su na da buƙatar jinta.
ya ce "Usman da wuri haka? ka na da son tambaye-tambaye."
Fiddausi ta ce "Abba kwananka uku da dawowa fa, ya kamata mu ji labarin rayuwarka da ba ka yi tare da mu ba."
Ma'arufa ta ce "Haka ne kuma Abba."
gyara zama ya yi kafin ya fara cewa "Cigiyata akai ta yi har na tsawon lokaci, sai yanzu Allah ya yi za a gano ni, sannan akai mini Albishir na komawa gida cikin iyalaina, bansan ko suwaye su ba amma na riƙe da DOUBLE TWO STAR su ne wanda su ka sa a nemo ni kuma su ka nusar da ni abin da na kasa hankalta da shi duk da cewar na fisu shekaru; ban yi tunanin halin da za ku shiga idan ba na nan ba kawai na barku ba kulawa ban san ya ku ka kwana ba bare ya ku ka tashi; wannan Babban Ƙalu-bale ne garemu mu Iyaye hakan za ta iya jawowa yaranmu faɗawa hallaka ta kowace irin hanya, Shaye-shaye ko sace-sace da biye-biye da abubuwa masu tarin yawa waɗanda su ke abin gudu ne; Duk ba na wannan tunanin sai yanzu da Allah ya yi zan gane ta silar su, Bansan meye Alaƙata da su ba amma sun ce mini akwai babbar Alaƙa a tsakaninmu, Yanzu rayuwa me kyau na ke son ginawa tare da ku, ina fatan za ku yafe mini a bisa kuskurena."
Murmusawa Ma'arufa ta yi gami da cewa "Abba na ji daɗi sosai, yanzu za mu yi farin ciki ko da yaushe mu ma gidanmu ya zama gida."
Usman ya ce "Wallahi kam, dama a Unguwar da mu ka taso cewa ake yi gidanmu ba Uba."
Abba ya ce "Ku na da Uba Usman, sai dai bai kula da haƙƙinku ba shi yasa kowa ma zai ce haka."
Umma ta ce "Mun godewa Allah kuma mu na ƙara gode masa, To Alaƙar da ke tsakanin kai da D2Star su na son Ƴarka ne, Ma'arufa ɗaya daga cikinsu ke sonta, kuma ni a ɓangarena na amince da hakan ina fatan kai ma za ka Amince."
"Alhamdulillahi" ya faɗa kafin ya ci gaba da cewa "Ai Iyaye ba mu da burin da ya wuce mu ɗauki Amanar da Allah ya bamu mu damƙata a hannun Mijinta na yi farin ciki da hakan, indai har ta Amince nima na Amince don kuwa ko ba'a faɗa ba na san su na da kyakkyawar Mu'amala ba na jin ƴarmu za ta tozarta idan har mun ba su ita, Yanzu abin da ya rage mini tinda na bar yawace-yawacen nan zan koma in rungumi dangina duk da cewar ba su da yawa kuma iyayenmu dun mutu amma na san su na da iyali, Yayyena Biyu da kuma Ƙanwata, Zumuncin namu ya fi komai muhimmanci a yanzu don haka za mu samu lokaci mu je musu Ziyara."
Firdausi ta ce "Abba dangin naka da ko ƙwayar hatsi ba wanda ya ke bamu da ba ka nan??"
"Duk da ba su temaka muku ba, ba zan kalli hakan ba ku ma ba na so ku kallesu da hakan, kuma ko ma menene halina ne ya jawo muku, ni Mahaifinku na watsar da ku ina ga su? ko da sun yi ma za su gaji su bari, Ina so ku girmama su ku ƙaunace su fiye ma da yadda ku ke ƙaunata."
Ma'arufa ta ce "In Allah ya yarda hakan za mu yi Abba, Allah ya ƙara Zumunci da Aminta tsakaninmu."
su ka amsa da "Amin" Abba ya ce "Ɗiya me hankali Allah i yiwa rayuwarki da zuri'unki Albarka."
su ka ƙara amsawa da Amin.
Shukriya, Shahzain, Shahbeer, Inna, Shahmeer, Malika, Shahzad, Ma'arufa, Zakiyya, Shahzaib, Sa'ad, Abeer, Mommy.
Suna zaune su na hira cikin walwala da nishaɗi, Wayar Shahbeer ce ta yi ƙara ya ɗauka, cike da ladabi ya gaishe shi, bayan ya amsa ya ce "Shahbeer Mahaifin Maalik ke magana."
''Na gane ya su Maalik ɗin?"
"Su na lafiya, dama maganar Zakiyya ce ke tafe da ni, Ina neman Alfarma ku bamu damar yin Maslaha don dawo da ita ɗakin Mijinta, Maalik ya hankalta kuma ya ɗauki sharruɗanka In Allah ya yarda ba zai ƙara gwada kuskuren ba, na yi magana da Alhaji Ibrahim akan Shukriya ya ce in nemeka in gaya maka cewa itama za mu dawo da ita sannan za mu dawo da Zakiyya cikinmu kuma in sha Allahu za mu riƙe Amana; ina fatan Amincewarka a duk lokacin da ka Amince ka sa mana lokaci za mu zo.
"Ya yi kyau na yi farin ciki da hakan domin kuwa Maslaha ta na da matuƙar daɗi da kuma amfani ga Al'uma, to a nawa ɓangaren ko yanzu idan kun shirya ku zo sai mu ƙarasa maganar.
"To Madallah, Allah ya bar zumunci.
Shahbeer ya amsa da "Amin"
da haka su ka yi sallama ya kalli Shukriya ya na dariya ya ce "Tarkonmu ya yi babban kamu Ƙanwata, sai ki shirya Auta ya mayar da ke gida Yanzu iyayen Maalik sun shirya dawo da ke su karɓi Zakiyya." kwashewa ta yi da dariya ta na cewa "Ban biyar Mutumina!!!"
hannu ya bata su ka tafa su na dariya ta ci gaba da cewa "Shi ya sa fa na ce daga kanka sai Yaƙin Ƙarshe Ya Shahbeer."
Abeer ya ce "Shukriya, Ya Shahbeer fa Sirikinki ne ki ke tafawa da shi."
"Waye ya ce maka Sirikina ne?"
ta faɗa ta na turo baki gaba.
Shah beer ya ce "Abeer ai idan ta yi wani juyin Abokai muke zama."
Mommy ta ce "Shiri-ritarku ai ta na da Afki, ni bansan da yaushe ka zama magananne ba Inya."
Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya miƙe ya nufi sashinsu.
Shahzain ya ce "To Mrs Gigi idan ba ki shirya ba na tashi fita gaba zan yi."
ta ce "A'a me ya yi zafi ido zai ci wuta? bari in tashi."
Shahzaib ya ce "Abban su Ma'arufa ya dawo Mommy."
ta murmusa gami da cewa "Na yi farin ciki, ka samu Babanku ka sanar da shi sai ya je su gaisa ko?"
ya gyaɗa kai.
Shahmeer ya miƙe ƙafa gami da cewa "Malee ko Ma'arufa a samu ɗaya ta kawo min abin sawa a baki."
Inna ta taɓe baki kafin ta ce "Duk da dai ina da kishi amma na ji har yanzu ba kai mini zancen kishiya ba, ya kamata ka ƙara Aure."
"Kina rikita-rikita" ya faɗa gami da gyara kwanciya.
Inna ta ce "Allah ya yi maka magani to."
Mommy ta ce "Amin dai Innata."
Sa'ad ya ce "Inna kar fa ayi miki kishiyar fa ki kasa zaune ki kasa tsaye."
harararsa ta yi ta ce "Sai in jefeka da filon nan Ja'iri, ance maka ina tsoron kishiya ne?"
ya yi dariya gami da cewa "Ai nasan ko da me
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 30