Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da kai ba zan barka cikin wannan duhuwar ba, zan san yadda zan yi na baiyana gaskiyar. "Ai ita gaskiya ba ta damu da a baiyana ta ba ita ce ta ke baiyana kanta, bari in fita kar su ga kamar ba zan zo bane. Har wajen motar Baba ya raka shi ya na yi ya na tausar shi. Shahzaib ne ya miƙe gami da cewa "Ba na jin ƙaramar yarinya kamar wannan za ta iya saƙa wannan mugun sharrin, akwai wata a ƙasa dai," Shahmeer ya share ƙwalla kafin ya ce "Nima ba na jin itace ta yi da kanta, gaskiya wani ne ya sa ta." Rai ɓace Shahzain ya ce "Ku bar ta ni zan ji da ɓangarenta za ta yi min bayanin uban da ya sa ta, ko kuma na hana ubanta zaman Kano wallahi." Shahzaib ya ɗan murmusa kafin ya ce "Ya yi, na damƙa lamarin a hannunka; Jariri (Shahmeer) wai kukan na menene sai ka ce wani ƙaramin yaro sabi da Allah?." Sai a lokacin Abeer ya yi magana, "Ka san shi ba ya son tashin hankali. "Shi yasa su ka sangarce, kuna abu kamar Mata, kuma Inya ne ya lalata ku da hakan, duk wata gwagwar-maya da zai yi ba ya sako ku a ciki, to yanzu dai ya zama dole su Salame a bar soyayya da Inna a san abin yi." Abeer ya yi dariya, Shahmeer ya ce "Ni Salame kai Salamatu ba, ni wallahi lamarin Duniya tsoro ya ke bani. Abeer ya ce "Gaskiya kuwa ka na gani a iya yau duk an kulle kamfanu-nuwanku har ma da waɗanda su ke mu'amala daku ta shafesu. murmushin takaici Shahzaib ya yi, ya ce "Wato kai Duniya ce ta ke baka tsoro ko?, shi yasa dai shi ya ke sayar da rayuwarsa domin taku amma duk baku sani ba." Shahzain ya ce "Ni kam da barin maganar nan ku ka yi Zaib. "Okay Bari in je kicin. Zaib ya faɗa sannan ya fice daga falon. Hankalinta ya gaza kwanciya, ta kira Wayar Safyan shiru bai ɗauka ba daga baya ma in ta kira ba ta shiga, Mami da Abba duk sun ce babu ruwansu a cikin lamarin ko me ya biyo baya ita ta janyo wa kanta, tsoro da razani gami da nadama su yi mata taron dangi, har ta yi wata muguwar ramewa ta yi zuru-zuru ga wani mugun ciwo da kanta ya ke yi, jikinta ya ɗau zafi kuma ba zazzaɓi ta ke ba, kowa na gidan ya ƙi saurararta ba wanda ya goyi bayan abin da ta aikata. a daddafe ta kai washe-gari; ba abin a ya canja ta koma kamar mujiya a cikin gidan, ji ta yi azabar ta yi mata yawa dan haka ta shirya ta nufi gidansu Fatima, a cewarta tun da ƙawarta ce za ta zauna ta fahimceta. da kyar ta ƙarasa gidansu Fatima wujiga-wujiga, Sallama ta yi a Falon cikin sa'a Fatima ta amsa, da sauri ta ƙarasa ta na cewa "Kin dawo Fatima gaskiya na ji daɗi, nasan ke za ki fahimce ni." miƙewa Fatima ta yi cikin fushi za ta bar wajen, da sauri Shukriya ta ce "Fatima don Allah ki tsaya mu yi magana kar ki yi fushi dani." a fasace ta juyo ta ɗauketa da wani zazzafan mari, "Kin bani kunya Shukriya, yanzu shi kenan kin kassara kanki babu me ƙara yi miki kallon daraja, me yasa ki ka aikata haka??, kallonki muke a matsayin Ƴar-jarida me hankali da dogon nazari ashe duk ba haka bane, mene ya gusar da hankalinki ki ka yi abin da za ki zo kina nadama??" fashewa ta yi da kuka ta na cewa "Soyayya ce Fatima, wallahi ban san taya na amince ba, ya faɗa mini gaskiyar lamarin ni kuma naga ba sai na ƙara bincike ba tinda gaskiya ne." dogon tsaki Fatima ta doka kafin ta ce, "Kuskure ne ki ɗauki rahoto irin wannan kuma daga bakin wani ba tare da kin yi bincike kin gane gaskiyar ba ki je ki faɗawa Al'umma, kar fa ki manta da yawansu su na dogaro ne da abin da mu ka faɗa musu, akan me za ki tabbatar musu da abin da hankali ba zai iya ɗauka ba??" "Wallahi Bala'in So ne ya jefa ni cikin wannan tarkon...." "Rufe min baki, So hauka ne?? fisabilillahi daga ganin mutum ba ki san halin sa ba sai ki yarda da wannan ƙaryar da ƙazafi dan ki na son shi?? anya kuwa kin yi wa kanki adalci??, ai ko da suna aikatawa bai kamata a ji a bakin ki ba, ki bar mutum da Allah mana wataran fa sai labari, Azzalumai nawa ne su ka shuɗe kuma Allah ne ya karya su ba wani ba" Cikin shashshekar kuka ta ce "Nima sai yanzu na gane ba hurumina bane, Na yi ganganci, wallahi da kyar na iso gidan nan kar ki ga yadda wasu mutane su ka dinga razana ni ina ciki Napep saura ƙiris su haɗa mana haɗari, su kai ta jifana da lemon tsami har gefen bakina su ka fasa min, kuma banga fuskar ko ɗaya a cikin su ba" Fatima ta ce "Ai ke ki ka jawowa kanki, dole komai ma za ki gani, yanzu dai ki zauna a gidan nan zuwa wani lokaci, kar ki fita su yi miki wani abun." gyara zama ta yi, ta haɗe kai da guiwa ta na sauke ajiyar Zuciya akai-akai. Abeer, Shahzain, Shahzaib, Shahmeer, Baba, Maleeka, Motar su ce ta tsaya a harabar madai-daicin gidan, dukkansu fuskarsu ɗauke take da damuwa me tarin yawa. Jami'ai guda biyu ne su ka ƙaraso bayan sun gyarawa tasu motar parking. Baba ya ce "To, ta ina za mu ganshi?" Jami'in ya ce "Zai fito yanzu." gyara tsayuwa su ka yi suna jiran zuwan sa. tare da wasu Jami'an aka fito dashi, sai ƙasa-ƙasa ya ke da ido. Cikin tausayawa Baba ya ce "Shahbeer ina fatan ka na lafiya." Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Muna lafiya Baba?." Shahzaib ne ya rungume shi gami da cewa "YaYa muna ta kewa." murmushi ya yi, ya ce "Kar ka wani ɗima kanka da ƙasa Ƙarami." kamar daga sama su ka ji Muryar Alhaji Basiru Boza. "Alhamdulillahi, na ji daɗin ganinka a kusa Shahbeer. Kallon sheƙeƙe Shahbeer ya yi masa, hakan bai dameshi ba ya ƙaraso, kai hannu ya yi zai taɓa shi, ya yi saurin kauce cike da nuna ƙyama. Boza ya ce "Don Allah ka yi haƙuri Mukhtar bansan hakan za ta faru ba d......" a tsawa ya ce "Kar ka faɗa min komai malam, wace jarabar ka zo mini da ita kuma?" "Haba ɗana wace irin jar...." a Zuciye Ya cafki kwalar rigarsa cike da gargaɗi ya ce "Kar ka kuma, kar ka ƙara kirana da ɗanka hakan ya na Ƙona min Zuciya, ni ba ɗanka bane ba ɗan kowa bane ni Shege ne, a yawon ta zubar aka sameni kamar yadda ɗanka ya faɗa." ya na kaiwa nan ya hankaɗa shi gami da cewa "Ba na son ganinka, ba haɗi tsakanin shege da Uban wasu." Wani Shigaggen Mari Alhaji Boza ya watsawa Shahbeer cikin Tsawa da tsananin Zuciya ya ce "Kulll!!!!! Kull!!!! Mukhatar kar ka ƙara kiran kanka shege dan ba shege bane kai kana da uba." A fusace Shahzaib ya ce "Wallahi zan haɗa ma jikinka in ba ka bar wajen nan ba." cikin ɗaga murya BOZA ya ce "KO KUNA SO KO BAKWA SO NI MAHAIFINKU NE, ba abin da zai canja Ni Babanka ne Shahbeer." "Ba zai yuwu ba!!!!!, babu yadda za'ayi ka zama mahaifina Basiru Kar ka ƙara furta hakan gareni don abin da zan yi zai yi maka ciwo, A'isha ta haifa kuma sun girma, Sai ka gwammace akan ƙaya ka ke da zama don ka faɗa Komar Shahbeer, ko da nake yaro ba na ɗaukar wargi bare yanzu na girma, da ka sani ka kasheni tin kafin na fara hanaka rintsa idanunka, ƙazami dattijon banza." daga haka ya juya a fusace ya koma cikin gidan, masu tsaronsa su ka rufa masa baya. Alhaji Basiru kamar zai haukace ya fara hanƙoron bin Shahbeer ana rirriƙeshi sai Surutai ya ke yi, su Shahzaib kuwa kamar ba su san dashi a gurin ba sun yi masa banza, ransu cike fal da farin cikin wankin babban bargon da Shahbeer ya yi masa. da ƙyar ma'aikatan da Abeer da Baba su ka taitayeshi su ka yi waje dashi har cikin motarsa su ka tura shi su ka kulle. Baba ya ce "Ku zo mu wuce." Shahzain ya ce "Zan kira a zo a ɗauke ni, ba gida na yi ba." "Okay. Baba ya faɗa sannan ya shige mota. Fatima ce ta dafa kafaɗarta, a firgice ta zame jiki na rawa ta na zazzare ido. Fatima ta ce "Ni ce nutsu, yanzu aka sanar min za'ayi tattaunawa da ke a gidan TV don jin kan lamarin, sai ki kasance cikin shiri kuma kisan yadda za ki fitar da kanki. Fashewa ta yi da wani sabon kukan tana cewa "Wayyo na shiga Uku na lalace. Fatima ta ce "Ki nutsu, wannan koke-koken ba zai miki maganin komai ba." Wayarta ce ta yi ƙara Fatima ta miƙa mata, sabuwar lambace , da ba za ta ɗauka sai kuma ta yi tunanin ko Safyan ne ɗauka ta yi ta kara a kunne gami da sallama cikin rawar murya. "Shukriya!!!" ta ji an kira sunanta Muryar kamar ta Safyan, wani daɗi ne ya ratsata ta yi saurin cewa "Na'am, ina ta nemanka ba na samunka ina ka shige ne??" "Ki fito ina ƙofar gida ina jiranki za mu yi magana. daga haka ya katse, cikin farinciki ta ce "Safyan ne bari in yi sauri in je." "Kin tabbatar shi ne??. "Wallahi muryarsa na ji shine ma." da gudu ta tsallla ba tare da ta jira amsar Fatima ba. Fatima ta bita da kallon tausayawa, ba dan ƙawarta ce ta a mutu tare ba da ba abin da zai hana ta zuba mata ido don ganin gudun ruwanta amma ba yadda za ta yi dole ta ɗorata a hanya. gidan Baya ta buɗe ta faɗa ba tare da ta tsaya dubawa ba. A tsiyace ya ja motar har sai da ƙura ta tashi. jin suna ta zuba wuta bai ce komai ba gashi ya na ta zuba mugun gudu ta fara tsorata, cikin sanyi ta ce "Safyan!" "SAFYAN BASIRU BOZA, Ba shi Bane, Sunana AMINULLAH BASIRU BOZA, (SHAHZAIN)." yadda ya yi maganar a kausashe ya sa ta ji Zuciyarta ta yi wata muguwar bugawa, danda nan jikinta ya fara rawa sabi da razani. Gat ɗin wani makeken gida ya sa kan motar, ko gyara Parking bai yi ba ya fito, zagayowa ya yi ya ja hannunta ƙiiiii ya yi ciki da ita. Falo ne me girman gaske ya sha ado iri-iri ga kukan fankoki da AC Ko ihu ta yi babu me jin motsinta. kuka ta saki ta na roƙonsa akan ya barta ta tafi amma ya yi banza, sai da ya dangana da wani tafkeken Bedroom sannan ya wurgata kan haɗaɗɗen gadon dake ɗakin. ba ta gama firgicewa ba sai da ta ga ya tuɓe rigarsa har singlet ɗin ya dawo daga shi sai fatar jikinsa. wani ƙwaƙƙwaran ihu ta zunduma har sai da ya toshe kunnuwansa, ya na buɗe su kuwa ya yo kanta kamar Mayunwacin Zaki. sabi da tsabar tsoro da firgici har duhu ta ke gani, gimtse idanunta ta yi ta rintse su da ƙarfin gaske ta na jiran abin da zai yi matan ya biyo baya. jin shiru ba ta mutu ba ya sa ta ƙyallaro ido ai kuwa su ka yi muguwar arangama da nasa, ƙara ƙanƙame jikinta ta yi ta na zazzare masa idon. a kausashe ya ce "Kin yiwa ɗan uwana sharrin fyaɗe kin ce mu shegu ne, to meye aikin shege idan ba shegantaka ba? kuma ta kanki zan fara yau ba me cetonki, na tsani a ce na yi abin da ban aikata ba dan haka zan aikata sai a samu Hujjar kama mu. girgiza kai kawai ta ke yi ta na so ta yi magana amma maƙoshinta Ya yi bushewar da muryarta ma ba za ta fito ba. "Kin san waye ya baki labaran da ki ka watsa?? Kin san waye Basiru Boza?? kin shiga rikicin Dangi sabi da rawar kai da rashin hankali irin naki, kin yaɗa labaran da Za su tarwatsa rayuwarki....... _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [12/17, 8:36 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 18 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. ...Shi Safyan ɗin Ƙanina ne, Mahaifinsa Mahaifina ne, Mahaukaciyar banza da wofi." yamutsa sumarsa ya yi gami da furzar da wata zazzafar iska, sassautawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Kin zagi kima da darajar Mahaifiyar da ta tsaya tsayin daka ta raini ƴa-ƴa huɗu a lokaci ɗaya kuma ta iya basu ingantacciyar tarbiya, tabbas da Mommyn mu Ba ta kirki bace ba abin da zai hana na yi miki abin da bakinki ya furta, amma ba haka ta koyar damu ba, in baki sani ba to har yau ba zaman zawarci ta ke ba akwai igiyoyin Aure har Uku na Basiru Boza akanta, mu ne mu ka hana ta saurararshi sabi da bai cancanci hakan ba, Ba ma amfani da sunansa sabi da bai amsa sunansa Uba ba bawai dan ba mu da shi bane, Mommy har gobe Matar Aure ce hallau kuma bayan shekaru huɗu da Aurensu aka same mu bare ko ki ce kafin ne; Banziya kawai." wani marayan wahaltaccen kuka ta saki, cikin shaƙaƙƙiyar muryarta ta ce "Don Allah ka yafe min ka yi haƙuri, sharrin Zuciya ne wallahi Son da nake masa ne ya sa na yarda dashi." Murmushin takaici da baƙin ciki ya yi gami da cewa "Ai So ba hauka bane Hauwa'u, sai yanzu na tabbatar ba ki cika mace ba, duk macen da za ta iya rafka wannan haukan naki akan So to ba mace bace, Mama ta haifi ƴaƴanta Na halak amma ana kiransu Shegu, me ya fi wannan ciwo a rayuwa?; idan ki ka ji tarihinmu sai kin raina kanki yarinya, dan dai iya mu ne mu ka san meke gudana a cikin Ahalinmu kuma ba ma buƙatar ƴan-jarida, shima Safyan ɗin naki bai san su waye mu ba kawai a matsayin Ƴan-uba ya ke kallonmu bai san mu ne iyayen nasa ba ma; ba na faɗa ne dan ki janye kalamanki ba a'a ina so ki kiyaye gaba ne kar ki ƙara kwatanta irin haka. ya na gama faɗen haka ya sauka daga kan gadon ya figi rigarsa. cikin kuka ta ce "Don Allah kar ka tafi ka barni anan, ko hanyar fita ban sani ba bare hanyar gidanmu, Don Allah ku yi haƙuri ba zan kuma ba." "Ai ba hayata ki ka ɗakko ba bare ki ce sai na yi abin da ki ke so. "Don Allah ka yi haƙuri ka tafi dani zan mutu a gidan nan wallahi ba zan iya fita ba." " Kuma kin-ki-marki zan yi ko ba ki da ƙafafu ne??" "A'a ina da su. ta faɗa gami da yunƙurawa a galabaice, kafin ta dire ƙafafunta a ƙasa su tsaya tini ya fice tsangal-tsangal ta bi bayansa, har da gudu-gudu ta ke haɗawa amma ta kasa cimmasa sai dai ƙyalli ƙyallinsa ta ke gani sai ta yi inda ta ga ya bi, da haka su ka fito inda ya ajiye mota ta na zuwa ta zube a gurin ta na tarin azaba. ganin zai shige mota bai ko kalleta ba ya sa ta ware muryarta da ta ke fita da kyar, ta ce "Yallaɓai Don Allah ka tausaya min kar ka barni a gurin nan ban san ina nake ba." "a tunaninki dan tsautsayi ya sa na sako ki a motata ɗazu yanzu ma zan iya haɗa numfashi da ke ne??, ba zan iya ba don haka ki nemi Ɗan-sahu ki hau. Ƙara wangale baki ta yi ta ci gaba da ɓarza kuka ta na cewa "Na tuba na yi Nadama wallahi, na rantse da Allahn da ya busa mini rai ba zan kuma ba, ko me ka ce in yi ma zan yi maka, ni wallahi ko baiwarka ka maidani na yarda, Don Allah ka temaka ka maidani gidan iyayena, Na dena son Safyan ɗin Wallahi kai na ke So ba na son mara gaskiya. "kehhhh!!!!!" ya daka mata wata muguwar tsawa, Wata Shegiyar firgita ta yi numfashinta da kukan da ta ke yi su ka tsaya lokaci guda; a hankali sautin Dariyarsa ya karaɗe kunnuwanta, tin ya na yi a hankali har ya fara yi da ƙarfi harda bugun mota, sai da ya yi ta ishe shi sannan ya ce "Baiwar Allah, dama mawuyacin abu ne idanunmu su gauraya da na yarinya ba ta Kamu da So ba, to kin shiga KOMAR WAHALA Yarinya." Sakato ta yi ta na kallonsa sai a lokacin ta fara marowa har ta tuna da kwaɓar da ta yi, kamar ƙasa ta tsage ta shige haka ta ji sabi da wani irin takaicin da haushin kanta da ta ke ji gashi ya yi mata ƙuril da idanunsa, Kwarjininsa ya sa ta kasa ko motsin kirki sai Zuciyarta da ta ke wani mugun tsalle. "Jiranki zan zauna yi ne??" da sauri ta miƙe, da jan ƙafa ta ƙarasa wajen motar ta buɗe ta faɗa, ajiyar Zuciya ta sauke sai yanzu ta ɗan ji daɗi da ta ganta a mota, da ya ƙi tafiya da ita da gawarta kawai za'a zo a tarar, a cewarta, ganin bai shigo motar ba ya tsaya amsa kira ya sa ta zaro ta-ta ƴar wayar da ta yi ɗamara da ita a ƙugu ta na ɗaukar duk surutan da su ke yi, tin daga lokacin da ta lura ba Safyan ɗin bane ta shirya tsaf kuma ta yi sa'a bai gani ba kuma bai yi tunanin za ta ɗauka ɗin ba, ganin ya na shirin dawowa ya sa ta yi saurin ɓoyewa ta yi muzu-muzu da ita alamar rashin gaskiya. bai ce mata cikal ba ya ja motar. har ƙofar gidan da ya ɗauketa ya maida ita duk da ta ce gidansu za ta je amma ya ce ba ta isa ya kaita ba. ta na shiga ta samu Fatima a tsaye ta na zarya ta kasa zama tunanin halin da Shukriya ta ke ciki kawai take. Umman su Fatima ta ce "Allah ya sa dai lafiya Shukriya , ga ƙawarki nan ta kasa zama." murmushin yaƙe ta yi gami da cewa "Umma lafiya lau, ina wuni?" ba ta jira Umman ta amsa ba ta fara jan hannun Fatima ta na cewa zo ki temaka mini Don Allah, binta ta yi suka shiga ɗaki. sai da ta goggoge fuskarta sannan ta sauke ajiyar Zuciya idanunta da su ka yi tulu-tulu ta zubawa Fatima sannan ta ce "Na sha baƙar wuya kamar ba zan rayu ba, wallahi na zata sai na mutu bayan ya rabani da mutuncina ashe ba haka abin ya ke ba." "To wai ba Safyan ɗin bane? ko kuwa??" "Ina kuwa Safyan? Aminu yace sunansa, na yi recording don Allah ki tayani mu tace shi sai mu ɗora, wallahi zancen banza Safyan ya gaya mini, kai na shiga tara ni Hauwa Kulu, ni dai yau na yi Nadamar kasan-cewata ƴar-jarida, ashe-ashe Da Double Two Star ɗin da Safyan ɗin ma Babansu ɗaya, kai wannan masifa Duniya ta yi min zafi Subhanallahi, na tafka hauka Fatima, shi kenan na bar wa kaina baƙin tabo. Fatima ta ce "Su sun fiku hankali da dogon Nazari in banda haka da Azzaluman ne ai da yanzu sai buzunki, to ki dena damun kanki In sha Allahi ba abin da zai faru da ke sai Alkairi, amma Fisabilillahi akwai ki da wauta, kin tsallake wanda ya ke sonki da gaskiya kin kama wanda zai zurma ki a wahala, shine fa amfanin ka nutsu ka fahimci wace hanya Allah ya ɗoraka kar ka fanɗare ka ce a dole sai ka yi abin da ka ke ganim ya fi maka, Dan kin So shi ai ba dole ne sai kin same shi ba, da kin yarda kin Auri Maalik da yanzu ya na nan ya na kulawa da ke kamar ransa, yanzu kuma sai ki ce Kin bar Safyan wannan ɗan-uwan nasa ki ke so ko??" ƙasa ta yi da kai gabanta na faɗuwa Fatima ta tuna mata abu mafi girma da ya addabi Zuciyarta musamman in ta tuna kalaman da ya faɗa bayan ta yi ta-ta taɓargazar, ta kasa bambance asalin yadda ta ke bare ta gane kanta. Fatima ta yi murmushin takaici "Allah i yaye miki wannan masifar Shukriya, wallahi ba dan ke ƙawata bace faɗa miki gaskiya ya zama dole da na zuba miki ido, wace irin raguwar Zuciya gareki haka??" "Ban sani ba Fatima mi dai ki yi haƙuri, wallahi ya tsorata ni sosai ki barni na gama dawowa daidai in ya so duk yadda za ki yi dani sai ki yi, ni ce da laifi dan haka ki hukunta ni. "Okay, sai ki ƙoƙarta" Fatima ta faɗa gami da karɓar wayar hannunta. "Allah sarki yarinyar nan, irin masu banzar Zuciyar nan ne" Shahzain ya faɗa ya na rausayar da kai. Shahmeer ya ce "Fitar da ni mana." "Me saurin Kamuwa da Son Mutum da kuma saurin tsige shi daga rayuwarta. Ya ƙarasa maganar ya na dariya, Shahzaib ya ce "Allah me halitta a yadda ya so, akwai irin ta da yawa a Duniya ba wuya an so ka ba wuya an dena sonka, akwai kuma wanda idan ya So abu ya yarda ya rabu da kowa akan ya rasa abin, ni kuma da irin wannan Son gwara ma ba ni da shaukin Son gaba ɗaya." Shahzain ya ce "Tab, ta na gwagwagwa, har na tausaya mata." "Nima tausayin nata na ke wallahi, da haka Safyan ya yaudareta yanzu ka ga aikin nata ma in ba sa'a ba ta rasa shi kenan." Shahzaib ya ce "Can ta waɗaɗe, tin da ba hankali ne da ita ba, gobe sai ta ƙara biyewa so ta tafka hauka." Dariya Shahzain ya yi, ya ce "Ta ce ba za ta kuma ba ai." "Kaiya dai, yanzu ka gama cewa banzar Zuciya gareta, na tabbata idan ka ce ta ce wani abun sai ta faɗa." Shahzain ya ce "Da gudu har da tuntuɓe ma kuwa." Dariya su ka yi Shahzaib ya ce "Molankar banza da wofi." Shahmeer ya ce "Oo Jama'a, Allah i yaye mata, wannan ta cancanta a tausaya mata." Shahzaib zai yi magana Ma'arufa ta yi sallama ta na

Chapter 11 of 30