zauna a gefensa jiki na rawa ta ce "Ɗan nan, ji na yi ka na wasu ƴan magan-ganu masu firgitarwa, ka na nufin idan ta samu lafiya rabuwa za ta yi da kai ta dena kula ka??, to wane laifi ka yi mata??, gaya min gaskiya, ka ga nan ni kaɗai ce ba me jinmu kuma na yi maka Alƙawarin ba zan bari kowa ya sani ba, a ganina idan ba kaine ka yi mata laifi ba ai ba za ta gujeka ba ko? Ko dai kaine Baban ɗannan da gaske?"
Murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce "Ni ne Inna, Halima tawa ce Shahzad kuma ɗana ne, ko kin gayawa Momma ma itama ta sani, Ki ga dai yadda Ɗa ya yi kama da Babansa sak.
Hawaye Inna ta fara yi ta na cewa "Inya, ban zata za ka yi haka ba sam, na kasa yarda kaine ka aikata ashe kaine ɗin, gaskiya ka bani Kunya, ko dan ku dama a jininku ba ku san martabar Mace Ba.
"Haka ne Inna, Alhaki kuikuyo ne Dole ne Alhakin da Alhaji Boza ya ɗauka ya bibiye mu, amma ki yi haƙuri Inna ba zan ƙara ba.
goge ƙwallar ta shiga yi gami da cewa "Allah sarki ai na san ba halinka bane Muntari, Ina fata dai ita ce farko ita ce ƙarshe."
"In Allah ya yarda.
"To ka yi min Alƙawari.
"Inna na yi miki Alƙawari ba zan ƙara ba.
ta ce "To ɗannan, Allah ya yi maka Albarka, Ƴar nan Ƙawar Shahzain ta tafi ta ce in ƙara gaisheku."
"Ba ƙawarsa bace.
"O'oo, ba ƙawarsa bace to mecece? na ga kamar ta fi sanin shi.
Murmusawa ya yi kafin ya ce "Allah sarki Ƴan-uwana, Shahzain da Ita Yarinyar duka su na son junansu, shi Sakaran Ƙanin nawa ma bai san ya na sonta ba."
washe baki Inna ta yi gami da cewa "Laa, ai kuwa shi ya sa naga sai kallonta ya ke ashe ashe sonta ya ke yi, kai Alhamdulillahi, ai gwara ku yi Aure sai kun fi martaba da kima, idan ba ni da Ummarku ba fa ba ƴa mace a gidan nan kaga kuwa mu na buƙatar ƙari, ka san gida da mata shine gida.
"Kar ki damu Inna in sha Allah za mu yi, amma dai banda ni don ba zan Auri Halima ba har sai ta samu lafiya.
''Kai Da'alla can, sai mu zauna jiranta kenan?, to Allah ya bata lafiyar su kuma ya sanya musu Albarka.
"Amin" ya amsa gami da zamewa daga riƙon da Halima ta yi masa ya sauka, Falo ya nufa rungume da Shahzad, ya na zuwa ya tarar da Mommy da Alhaji Boza su biyu, takaici ne ya lulluɓe shi ya sassauke rumfar Ido ko bin ta kansu bai ba ya raɓe zai wuce sashinsu.
"Shahbeer Ɗana"
Alhaji Boza ne ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunansa da haka.
Da sauri ya miƙe ya nufi inda ya ke tsaye cike da fargabar irin watsiyar da Shahbeer zai yi masa.
gyaran Murya ya yi sannan ya ce "Ka na lafiya?, Bani Jikana mu gaisa."
"Ba zan iya yin hakan ba, Ɗana ne ni nake da iko dashi kuma ban amince ya shigo hannunka ba, bayan na gaya maka kar ka ƙara dawowa gidanmu kar ka ƙara neman inda mu ke me.."
katse shi ya yi da cewa "Shahbeer gidan nan gida na ne dalili kuwa shine Matata ta Sunna ta na cikin shi da Ƴaƴana Maza har su huɗu yanzu gashi har da Jikana, nan Family House ɗina ne."
cikin ɓacin rai ya ce "Mommy ki gaya masa ba gaskiya ya faɗa ba hakan ba zai yuwu ba sam mu ba ƴaƴanka bane, Don Allah Mommy ki gaya masa ba shi da kowa a gidan nan."
wasu zafafan hawaye ne su ka biyo bayan maganar tashi, cikin sauri Alhaji Boza ya sa Hankicif ɗin hannunsa ya fara goge masa ƙwallar, cikin raunanniyar Murya ya ce "Shahbeer kai fa Sarki ne, kuma ba ka Kuka, ba zan iya bari hawayenka su zube a ƙasa kuma a gabana ba, ka temaki Rayuwata ka dena kuka.
"Ina, kai Mushriki ne, maganarka ba abar yarda bace ba abin da bakinka zai furta in yarda da shi sai dai in cewa ka yi Allah Ɗaya ne.
Durƙusawa ya yi kan guiwoyinsa Kafin ya ce "Na yarda kai ne silar zuwanmu Duniya ka yi haƙuri kar ka sa na yi abin da Tsinuwar Allah za ta tabbata akaina , ba na son ganinka, idan na ganka Zuciyata tafasa ta ke ta na ƙuna, Ba zan iya jura ba tabbas ba dan na yarda Kaine Mahaifina ba da ba abin da zai hana ni yi maka abin da na ke yiwa duk wanda ya shiga gonata, ba zan iya kiranka da Baba ba har Abada, don Allah ka temaka ka ƙauracewa ganina ka fita daga rayuwarmu kar ka gurɓata Rayuwar Ƴan-uwana kamar yadda ka gurɓata tawa rayuwar."
wani Mugun sanyi jikin Alhaji Boza ya yi ya kasa cewa komai ya na kallo Shahbeer ya tashi ya ƙara gaba.
"Ga dai abin da baƙar Zuciyarka ta jawo nan Basir.
Muryar Mommy ce ta katse masa tunanin da ya ke yi, takowa ta yi ta zo inda ya ke, idanunta sun kaɗa sun yi jajir alamun ɓacin rai. "Lallai babu wani Alfanu a cikin rashin gaskiya da rashin tsoron Allah Basir, ni na kasa dena Sonka har yau amma sabi da Alhaki kuikuyo ne ƴaƴan cikinka basu da maƙiyi a Duniya tamkar kai, maganar gaskiya Basir ka cutar dani ba kaɗan ba, da ba ka kasance me son Zuciya da son Duniya ba
da za mu kasance ne Ahali ɗaya cikakke kuma mutuntacce, amma ka tarwatsa mu sabi da son rai, gashi wasu abubuwa wanda su ka banbanta da halayen Ƴaƴana ya na ta faruwa a cikinsu, ni kaina na kasa yafe maka, kuma ba zan iya hakan ba har sai lokacin da Babban ɗana kuma Jigona ya Amince mana mu yafe maka.
ta na kaiwa nan ta juya zuwa Sashinta.
Hanyar waje Alhaji Boza ya nufa ya na tafiya ya na haɗa hanya, Addu'a ya ke yi duk wadda ta faɗo bakinsa, motarsa ya shiga ya bata wuta ba tare da yasan ina ma zai dosa ba, ya tabbata idan ya komawa Hajiya Habiba matarsa cikin wannan yanayin gashin ƙuma za ta yi masa.
Zaune su ke suna ƴar hira kaɗan-kaɗan, Shahmeer ya ce "Inya, Wakilin da mu ka tura Zuwa Katsina Ya sauka Lafiya, yanzu su na kan tattaunawa ne."
"Ya yi.
Shahbeer ya faɗa cikin yanayin ko in kula.
Shahzain ya ce "Ni fa So nake in ɗan yi Tafiya YaYa, kwana biyu ba mu fita ba."
Shahbeer ya ce "Ouh, dama ina son Magana da kai."
Da sauri ya gyara zama ya yi tsilla-tsilla da ido gami da cewa "Allah ya sa ba laifi na yi ba."
"Ba laifi ka yi ba, Ka na Son Shukriya don haka ka je ku shawota, idan ka shirya zan nema maka Aurenta.
Zamewa ya yi daga kan kujerar ya zube a ƙasa gami da cewa "Waye ya faɗa maka?"
Dariya Sosai Shahmeer ya ke yi, "Ba sai an faɗa ba ai indai Boss ne ya san kowane kalar takunmu, kai dai yanzu an baka Izini ka dena noƙe-noƙe ka taro Soyayya kanka tsaye.
ya ci gaba da dariyarsa, murmushi kawai Shahzaib ya ke yi dan kuwa ba shi da ta cewa don ba ya so Allura ta tono masa garma.
Shahbeer ya ce "Eh Jariri ya faɗa, na baka Izini Shahzain Kuma na yi maka Alƙawarin indai ta na sonka zan Aura maka ita da Amincewarta da ta iyayenta, Ina son ganin Farin cikinka don haka ba na buƙatar ka zauna ɓata mini lokaci."
ƙasa ya yi da kai ya na murmushi ya ce "Na gode sosai Ɗan-uwana.
Shahmeer ya ce "Autan Mommy baki har tsakiyar kai, Allah ya biya Na Shukriya."
"Jariri (Shahmeer) ba na son Ɗanyen kai, rufe min baki ko na sa A ɗaura maka Aure da wata a satin nan wallahi.
Shahzaib ya ce "Ga Malikarsa kuma dama.
shiru su ka yi da zancen don sun san halin kayansu, motsin kirki wanda bai yi masa ba su ka yi zai iya aiwatar da abin da ya faɗa shi ba shakka ya ke ba.
Yau ta kasance ranar Sati ɗaya da Zuwan Shahzad Duniya, Hajiya Zainab Maman su Malika da Hajja Asma'u Aminiyar Mommy Su kaɗai ne baƙi a gidan su ka sha wuninsu su ka koma gida Yaro ya ci sunan Babansa kamar yadda Shahbeer ya yi masa huɗuba MUKHTAR (SHAHZAD).
"Oo Yaro Ɗan gatan Abbansa, ku ga bajinta kamar ranar Aure.
Mommy ta yi Dariya gami da cewa "Ya na son abin da ya ke so haka ya ke ƙin duk abin da ya ƙi, Ina nufin Ɗana Muktar ba naki ba Inna."
Inna ta ce "Ai gaskiya akwai ƙauna tsakaninsa da ɗansa, shi ba irin Babansa bane."
Mommy ta ce "Ba na son ki taso mini maganarsa Inna Don Allah yi tafiyarki zan kwanta na huta."
"To Ƴar nan.
kafin ta yunƙura ta miƙe Wayar Mommy ta yi ƙara miƙo mata ta yi gami da cewa "Hajja Zainab ce ke nemanki."
karɓa ta yi ta kara a kunne bayan sun gama magana ta yi shiru ta na tunani, miƙewa ta yi ta nufi sashin Inna dan kuwa yanzu ta isa komawa.
Cike da kokonto ta ce "Inna kin ji Hajja Zainab ta ce ta rasa sarƙarta me tsada a Gidan nan, kuma nima na tabbatar anan ta ɓata dan kuwa lokacin da muke Hirar akan Style ɗin Sarƙoƙin da muke Sayarwa ana zancen ta ciro ta ta nuna mana sai kuma ta ajiye akan center table daga nan ba mu kuma ganinta ba an sace.
Ido warwaje Inna ke kallon Mommy har ta gama faɗe sannan ta ce "Wallahi Allah ban iya ɗaukar abin wani ba Aisha, amma bari in kira Masoyina ya kira min ƴan-sanda ayi bincike.
"Inna, na san ba za ki ɗauka ba amma kinsan ba ni da uwa kamarki ke zan faɗawa abin da ya dameni.
Inna ta ce "E haka ne, tawo mu je wajen Shahbeer mu sanar masa."
Rungumo Shahzad ta yi sannan su ka nufi Sashin Su Shahbeer.
Shiru su ka yi har Inna ta gama sanar musu abin da ya faru yanzu har ma da wanda ya daɗe ya na faruwa don ta na ganin Sata iri-iri amma ba ta tayar da zancen don Mommy ta ce mata duk wanda ya ɗauka ya na da buƙata ne.
Kowa Shiru ya yi su na Nazari, Inna ta ƙara cewa "Maganar Gaskiya Inya duk da ban san wane irin kallo za ka yi wa maganata ba amma Zan faɗi gaskiyata Ma'arufa ce ta ke ɗauke-ɗauken nan.
"Me?????"
Shahzaib ya faɗa cikin kaɗuwa.
Ko Gezau ba Alamar yi a tattare da Shahbeer sai idanunsa da ya ke rarraba su akan kowa; wanda ya san shi sanin gaske ne zai iya banbamce kallon ya na nufin Nazartar yanayin kowa da ke gurin.
Inna ta ce "Dama na ji shakkar faɗe sabi da gudun ɓacin rai, magana ta gaskiya ba yau ta fara Sata a gidan na ba, ban ƙara tayar da zancen ba Sabi da Mamarku ta hanani amma ta na ɗauke-ɗauke gaskiya.
miƙewa Shahzaib ya yi ya fara kai kawo a gurin, ransa in ya kai Dubu ya gama ɓaci, cikin hargagi ya ce "Lallai ma Yarinyar nan, sai na..."
tsawa Shahbeer ya doka masa hakan ya sa ya fasa faɗen abin da ya ke son faɗe.
Wani Rantsatstsen Mari Shahbeer ya zabgawa Shahzaib, gefe ya yi da fuskarsa ko ɗago idanunsa bai ba.
Cike da takaici Shahbeer ya ce "Ko me ta yi kaine ka jawo, Yarinyar da ka ke da Muradin Ƙare Rayuwarka tare da ita amma ka kasa yi mata Hidimar da sai ka barta ta na Sace-Sace?? ka fara hauka ne Ƙarami??"
"Ka yi Haƙuri YaYa, ba ka bani Izini bane shi yasa."
"Ba ka taɓa gaya min ka na sonta ba ni da kaina na fahimta, Zurfin ciki hauka ne?? Akan me za ka bar Rayuwarta a ɗaiɗaice haka?, Ka ɓata min rai, gashi yanzu abin nata ya wuce gida ta fara taɓa na Mutane ta na neman Tozarta mu abanza, to ka sani daga yau kulawa da ita ya dawo ƙarƙashinka duk abin da na ke yi Dominta nima na dena, kuma duk laifinta laifinka ne duk abin da ya faru da ita kai zan Hukunta.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/22, 12:18 PM] INDO CE: *WATA HANYA*
22
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Mommy ta ce "Saurin yanke hukunci haka Inya, yarinyar da take sata ka amince ɗan-uwanka ya Aura??"
"Ba laifi bane hakan, ki yi fatan ta shiryu kawai Mum, kuma laifin nashi ne ma idan da ya kula da ita ai da ba ta faɗa irin wannan halin ba, kuma na riga na yanke hukunci Shahzain ma na Zaɓa masa Yarinyar da ta zo miki ranar nan, Shukriya, ban damu da komai ba kawai ina son yi wa Ƴan-uwana abin da ransu ya ke so, Yi haƙuri Mama ba na son ki ce komai akai face fatan Alkairi.
jinjina kai ta yi kafin ta ce "Allah i sanya Albarka, ina farin ciki kasancewarka tsayayye akansu, Nima na Amince da abin da ka yarda dashi.
Murmushi ya yi gami da cewa "Godiya na ke Mammy.
Inna ta ce "Ni ai farin ciki ya ƙi barina bacci, wallahi kullum Addu'a ta kenan ku samu mata na gari ku yi Aure."
Shahmeer ya ce "Ai kuwa Inna, ni da ke dai mun Cale shekarunmu kusan Talatin da takwas da yin Aure."
dariya ta yi gami da cewa "Hee! Allah abin Godiya, ga kuma Ɗa mun samu a sadaka."
Kallo me kama da Harara Shahbeer ya yi mata gami da cewa "Waye ya ce miki ɗan sadaka ne??"
"Ai ɗan da ba kai ka yi gumin Haihuwarsa ba kuma ka same shi ai a gurinka ɗan Sadaka ne, kai dai da ya ke kaine Babansa kai ka san Zafin kayanka.
Momy ta ce "Zancen ya isheni haka Inna, ba kasafai na ke son Hirar Yaron nan ba don tarihinsa ba me kyau bane.
ta na gama faɗen haka ta yi hanyar fita. Shahbeer ya rakata da ido, ya ji ciwon maganarta sosai amma ba yadda zai yi don ta fi shi gaskiya .
Shahzaib Zuciyarsa na tiriri ya ke Tuƙa Motar har ya isa ƙofar gidansu Ma'arufa, ya na tsikara Parking ya fito ya na zazzara ido don samun ɗan aike zuwa cikin gidan, kamar da wasa ya hangi mutuane a kan tabarma a ƙofar gidan, ƙara saurin bugawa Zuciyarsa ta yi lokacin da ya lura Mutum biyu ne a wajen kuma da alamu Mace da Namiji ne, hankalinsa ya ƙi kwanciya don haka ya ƙarasa wajen gami da yin sallama.
Bashir ne ya Amsa gami da miƙewa Zumbur..
Gabanta ya shiga faɗuwa ganinsa tsidim ba tsammani, cikin rawar baki ta ce "In,ina,ina-wuni."
"Kam Bala'i"
ya faɗa lokacin da muryarta ta tabbatar masa cewa itace, kunna hasken wayarsa ya yi ya haskasu duka su biyun sun yi fiƙi-fiƙi kamar manyan munafukai.
cikin Ƙunar Rai da tafasar Zuciya Ya kifa mata wani kyakkyawan Mari, kamar kunnenta zai cire sabi da tsabar azabar da ta ratsa shi, idonta guda ɗaya na ɓangaren inda ya mara ya fara tsiyayo da hawaye. komawa ya yi kan Bashir cikin sigar gargaɗi ya ce "Daga yau na haneka da tinkararta, ba kai ba ita don ita ba Kara zube ta ke ba."
Bashir ya ce "Na
Fahimta Sir."
A tsawace ya ce "Wuce ki shiga mota!!!."
Maƙalewa ta yi ta fara baya-baya da nufin faɗawa cikin gida, A Zuciye ya ce "Wallahi Tallahi Ba na Rantsuwar banza idan ki ka bari na sa ki a motar da kaina ke da gidanku har gaban Abada ."
hankali tashe ta fara kuka ta na bashi haƙuri, wata ƙwaƙƙwarar mangara ya kai mata ta tsallake da gudu ba ta san lokacin da ta yi landin a cikin motar ba.
Lokacin da ya tashi motar zai tafi ya yi daidai da fitowar Umma da Fiddausi, kafin su yi wani yunƙuri Tini ya ɗageta sai ƙurar da ya tayar a wajen, Bashir su ka hanga a can gefe ya yi Tsili-tsili su ka fara tambayarsa ba'asi.
Cikin sanyi ya ce "DOUBLE TWO STAR Ɗaya daga cikinsu ne ya zo ya ɗauketa, Amma in Allah ya yarda ba abin da zai faru ko kwantar da hankalinku."
Umma ta ce "Yau an shige su, me ta yi musu ni ƴar nan da za'a biyota har gida a ɗauka kusan ƙarfe goman dare?"
Bashir ya ce "Allah masani, amma ku kwantar da hankalinku, ku koma cikin gidan ni zan ji da sauran komai da yardar Allah."
Komawar su ka yi, Umma sai salate-salate ta ke yi.
Fiddausi ta ce "Umma kar ki damu Don Allah, ki dena surutan nan, ba ki sani ba ko lokacin zubar hawayenmu ne ya ƙare, ta yuwu Alkairi ne ke tinkaro mu, mu yi mata Addu'a mu nema mata kariyar Allah a duk inda ta shiga.
Umma ta ce "To Fiddausi Allah ya tsare mana ita."
"Amin" Fiddausi ta amsa.
Lelewa ya dinga yi da ita a Titi har na tsawon lokaci sannan ya tsayar da Motar, zagayowa ya yi gidan baya ya zauna gami da rufe murfin Motar ya kunna hasken wayarsa ya haska ta gami da zuba mata ido, ta manne a jikin ɗayan Murfin Motar sai Kuka ta ke da Alama a matuƙar firgice take.
dogon tsaki ya ja kafin ya ce "Me yasa za ki aikata mini haka Ma'arufa?, kinsan me ki ka yi kuwa?"
"Don Allah ka yi ha..."
da sauri ya ce "Ba xan iya haƙura ba don ba ki nemi na haƙura ɗin ba, me yasa za ki dinga sata ba za ki tambayeni abin da ki ke So ba??, kinsan wacece ke a gidanmu kuwa, kinsan wane matsayi gareki a gurina?, shi kanshi YaYana ya na martabaki amma sai gashi kin zo kin bamu kunya, hakan tamkar wulaƙanta mu ne a idon Duniya, me yasa ki ka ɗauki Sarƙar Baƙuwar Mommy??, me yasa ki ka kasa yi mini Adalci Ma'arufa, ki na so ki ɓata min sunan Zuri'ata ko??"
zuwa yanzu magan-ganunsa sun fara bata mamaki da tsoro, to ita meye haɗinta da zuri'arsa? ta jefawa kanta tambaya, kamar ya san abin da ta ke tunani ya ce "Ba ki san cewa ke ce Za ki Haifa mininƳaƴa ba bayan mun yi Aure, so ki ke a dinga ce musu ƴaƴan ɓarauniya??, Kin sa na sha kuka na sha Mari a gurin YaYana ya ce laifina ne, na ji zafi sosai Zuciyata ta ƙonu na yi tsaki sau ba adadi, ji na yi kamar in na ganki na rufeki da Duka amma ba zan iya hakan ba don ba na so na illata Zuciyata, Don Allah Ma'arufa ki tausaya mini ki dena ɗaga ido ki kalli abin wani har ya baki sha'awa, ni zan yi miki komai da ki ke so kar ki yi shiru ki tambaye ni ko menene,; yanzu faɗa mini in da Sarƙar take.
cikin Kuka ta ce "Allah ya baku haƙuri, ta na cikin jakata da na dawo ban cirota ba, ina son irinta ne shi ya sa na ɗauka, don Allah Rankayadaɗe ka dena yi min irin wannan labaran hankalina ba zai iya ɗauka ba, Zan dena zuwa gidanku ma sabi da kar na ƙara yin abin da na yi gwara in zauna a gidanmu, Don Allah ka bawa Mommy da Ƴan-uwanka haƙuri, in Allah ya yarda ba zan ƙara ba, zan ce Saurayina ya turo manyanshi mu yi Aure kawai inaga hakan zai sa na samu nutsuwa."
"Mee??? batun Aure da wani ki ke yi bayan gani a zaune? So ki ke na zauce ne Arufa da me zan ji?, Ba na so, kar ki ƙara faɗen sunan wani ko a bayan idona, kar ki sa na hukunta wanda ba shi ya yi mini laifi ba, ya kamata ki fahimceni a koda yaushe ƙara shiga raina ki ke, ƙaunarki ta yi tasiri a rayuwata, nasan za ki yi tunanin ina yi miki rashin Mutunci ko?, Hmm ba ki taɓa tsaya ko na minti ɗaya kun yi magana da Shahzain ko Shahmeer ba duk Ni ne amma kar ki tuhumeni akan dalilin da ya sa na ke yin hakan, nima kaina ban san me zan ce miki ba.
Tsayawa kukan nata ya yi sai ido da ta ke zazzarewa gabanta na faɗuwa akai-akai, ko a mafarki ba ta taɓa tunanin a cikinsu akwai wanda zai ji ta burge shi ba bare ma ya Ƙauna ce ta, lamarin nasa ba ƙaramin Tsoro ya bata ba har ta fara tunanin ko dai gamo ta yi da Aljani?
"Yau a gidanmu za ki kwana daga yau har bayan Aurenmu ma a gidanmu za ki dinga kwana, gwara in dinga jin motsinki a kusa dani, hankalina ba zai kwanta ba tin da na ganki da wancan Soloɓiyon Yaron kuma a daren nan kusan Goma, na ji haushi sosai fa kawai ina tsoron na zaneki ne Shahbeer ya rama miki, don Allah na roƙe ki kar ki bari Ƙaunarki ta illata ni.
tafukan hannunta duka biyun ta sa ta rufe fuskarta don kar ma ta ƙara ganinsa, Addu'o'i kawai ta ke jerowa ta ko'ina fatanta ɗaya idan mafarki ta ke ta yi gaggawar Farkawa.
fita ya yi ya zagaya mazauninsa na direba ya nufi gida da ita, har ya isa ta na nan cikin Duniyar Tunane-tunane "Zo mu shiga ciki.
firgigit ta yi a tsorace ta rintse ido ganin ta ƙara yin tozali da shi.
hannunta ya riƙo gami da cewa "Ki yarda dani Arufa, ba zan iya cutar da kowa ba bare ke da ki ka kasance wani Jigo nawa, Don Allah ki samu nutsuwa ki biyo ni.
ba yadda za ta yi wanda ya wuce ta bishi ɗin don haka ta fito daga motar, hannunta na cikin nashi ya fara janta zuwa ciki.
babu kowa a Falo hakan ya bashi damar wucewa sashin Inna ba tare da ɓata lokaci ba, wani ɗaki da ke gefen na Inna ya rakata, ƴan maidai-daitan Setin kayan Gado ne a ɗakin ba wasu tarkace masu yawa.
"Ki yi baccinki cikin kwanciyar Hankali ba abin da zai same ki, ɗakin kusa da ke Inna da Halima Har da Yarimanmu duk su na ciki in kuma in raka ki gurinta to?"
girgiza kai ta yi a sanyaye.
ya lumshe ido gami da sauke ƴar Ajiyar Zuciya, gaba ɗaya suffarta abar tausayi ce ba ta da wani kazar-kazar ko rawar kai komai nata saɗaf-saɗaf ga alamun hankali da nutsuwa a tattare da ita.
Murmushi ya yi gami da cewa "Ki yi Addu'a kafin ki yi bacci, amma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 30