idan aka shiga tsakaninmu.
ɗan murmushi ya yi gami da dukan kafaɗar Shahzain ya ce "Kai fa Ƙanina ne Shahzain, Ɗan-uwana, ba amfanin rayuwata idan ba zan iya cika Muradinka ba, zan yi magana da Baba, Gobe in sha Allah za mu je mu samu Mahaifin yarinyar, indai ya amince to ko ta wane hali ne sai ta zamto matarka."
Murmushin farin ciki ne ya sulluɓe masa, ya rungume Shahbeer cike da soyayya irin ta jini ya ce "Na gode sosai YaYa."
"Allah shine abin godiya ka ji!"
Shahbeer ya faɗa ya na murmushi.
Ma'arufa ta na zaune a cikin Lambu da ke bayan gidan wanda aka ƙawata shi da shuke-shuke da abubuwa na burgewa, iska gami da sanyi-sanyi ne su ke tashi a hanka a hankali. jefi jefi takan sauke ajiyar Zuciya ba abin da ta ke tunawa sai rayuwarsu ta baya da kuma Mahaifinta wanda a yanzu ba ta san wace Duniyar ya shiga ba.
"Beauty!"
Muryar Shahzaib ce ta katse mata tunanin da sauri ta miƙe ta na waige -waige don ganin ta inda ya ɓullo. murmushi ya yi gami da cewa "Shine ki ka tawo nan ba ki ce in raka ki ba ko?, tunanin me ki ke yi don nasan in ki ka kaɗaice banda tunani ba abin da za ki yi."
Murmusawa ta yi gami da girgiza kai ta ce "A'a, ba tunani na ke yi ba, yanayin iskar gurin ce ta ke burgeni.
ta na kaiwa nan ta juya da nufin barin gurin ya yi saurin dakatar da ita da cewa "Bani Labarin Mahaifinki!"
tsam ta yi na ɗan wani lokaci sannan ta nisa, cike da takaicin irin halin Baban nata ta ce "Me yasa ba za ka nemi wani labarin ba sai wanda zai ɓata maka rai?"
"Duk yawan abin da Mahaifinki ya yi miki ba lallai ya kai ga namu Mahaifin ba, Duk da cewar Yanayin labarin ya yi kamance-ceniya, ki faɗa mini kar ki yi tunanin ɓoye mini domin ni mijinki ne.
jinjina kai ta yi cikin sanyi ta ce "Ka zauna."
"Umhm" ya faɗa gami da jan kujera ya zauna.
itama zaman ta yi sannan ta fara da cewa "Babana Asalinsa ɗan nan garin ne amma ba mazaunin gida bane a tafiye- tafiye zuwa wasu garuruwan ya ke samun duk abin da zai ci damu ya tufatar da mu, da farko idan ya tafi baya wuce sati Ɗaya zuwa biyu koda bai zo ba zai yo mana aike idan akai wata to fa zai zo sannan zai kawo mana kayan abin ci, daga bisani sai ya zamana idan ya tafi ba ya waiwayenmu, yakan yi shekara Ɗaya ko shekara da rabi bai zo gida ba kuma aiken da zai yi mana bai fi sau ɗaya ba a tsayin wannan lokacin, bayan nan ya kai shekaru uku bai zo ba kuma bai aiko kowa ba bai san halin da mu ke ciki, bai san me mu ka ci mu ka rayu ba hallau bai san ya mu ka kwana ya mu ka tashi ba, mu ma ba mu san inda ya ke ba, bayan shekara uku da wasu watanni ya zo da daddare washegari tin kafin mu tashi daga bacci mu ƙara ganinsa ya yi tafiyarsa, shekararsa Biyar bai ƙara waiwa-yenmu ba hakan ya jefa rayuwarmu cikin ƙunci ga rashi wata rana ba mu da abin da za mu ci sai dai mu kwana da yunwa ba mu da shi ba mu da me bamu, daga nan wata da ta ke nemawa Mutane gidan aiki sai ta nema min nima a cikin wannan ƙarnin ne na koyi sa hannu in ɗauki abin da ba nawa ba duk dan in samu in kaiwa Ummata da ƙannena abin da za su ci, idan an bani kuɗina na aiki a lokaci guda mu ke ƙarar dashi sabi da a gidanmu ruwan da za mu sha ma wahala ya ke mana, ranar da Babana ya zo aka gaya mini ya zo in zo mu gaisa a lokacin kuma sai ka hanani zuwa yanzun haka kenan ni na kusa cika shekaru shida rabon da in sa shi a idanuna, ko wace irin lalacewa mu ka yi Babanmu shine silarta."
ta ƙarasa maganar ta na kuka mara sauti.
Numfashi ya ja gami da cewa "Bansan me ya sa waɗansu mutanen su ke banzatar da iyalnsu ba, ba sa tunanin hakan haramun ne kuma illace babba garesu da iyalin nasu, ba na son ganin kukan ki Arufa ki dena, komai ya wuce shi ma Zan sa a nemo shi in sha Allahu."
"Ba lallai a ganshi ba domin ba mu ne a gabanshi ba, shiga Duniya da yawon cikinta shi ne abin da ya sa gaba, a matsayina na ƴarsa ya kasa yin jira na ƴan mintuna domin na ganshi bayan shekarun da ya ɗiba ba ya nan, ka barshi ya rayu a yadda ya zaɓawa kansa."
"Tinda haka ki ka ce na barshi amma lokacin nemansa zai zo a lokacin zan nemeshi, yanzu dai ki kwantar da hankalinki ki samu nutsuwa.
"Nutsuwa a gurina ta zama wajibi tin da ina da gwanin da zai sama mini ita.
Murmusawa ya yi gami da cewa "Za ki sa na yi Dariyar da ban shirya ba, Mu ma wata rana za ki ji tarihin wancan me baƙin halin Alhaji Boza, yauwa Yau za mu je gurin Mahaifin Shukriya domin nemawa Shahzain Aurenta ki taya mu Addu'ar kar a yi rikici don in sun ƙi Amincewa za su tunzura Zuciyar YaYanmu shi kuma akwai iya yiwa Mutum Zarra.
"Allah i bada Sa'a, ai in sha Allahu ma ba za su ƙi ba.
"To Allah ya sa, amma dai yaushe ne mu ma za mu yi Aure???"
zaro ido ta yi gami da cewa "Me???"
ya ce "Yadda ki ka ji."
dariya ta yi gami da cewa "Ba yanzu ba ni dai na fi ganewa Zama kusa da Mommy kuma ka ga ina taya YaYa Shahbeer kula da Shahzad tin da ni ya na yarda da ni.
"Ouhh yaron namu ai wayo gareshi bansan ma taya ya ke gane mu ba duk da cewar kamarmu ɗaya da Shahbeer amma wai ya gane Babansa mu sai ya ƙi yarda damu, to amma ba komai tin da ya na yarda da Maman Ƙannensa.
"Wacece?"
"Kyakkyawar Tauraruwar da ke kusa dani.
Murmushi ta yi gami da miƙewa ta ce " bari in je gurin Inna na san yanzu ta fara girki."
"To masu Aljanun girke-girke da ke da Innan duk ba kwa gajiya.
Murmushi ta yi ba tare da ta yi magana ba, ya bi bayanta su ka nufi cikin gida.
Bayan an yi Sallar isha'i Su Shahbeer su ka sauka a gidan su Shukriya, Faran-faran Abbanta ya karɓesu cikin mutunci da mutuntawa.
Bayan sun gama gaggaisawa DR ya ce "To Alhamdulillahi Alhaji Ibrahim idan ba damuwa muna neman Alfarma ne a gurinka Allah i sa za mu samu."
Abban Shukriya ya ce "Allah ya bani ikon iyawa idan har zan iya, ina saurarenka DR."
"Wato da Ɗan wajena ina nufin Aminullah Shahzain da kuma Ɗiyarka Allah ya haɗa su akan wani fanni da ya shafi rayuwarsu kuma sun fahimci juna hallau sun ƙaunaci Junansu, to akan hakan mu ka zo nema masa Aurenta Alfarma ce mu ke nema don Allah a daure a yi mana.
shiru ya yi ya na Nazari sannan ya ce "To Gaskiya YaYata ta na son yin haɗin zumunci tsakanin Shukriya da Maalik Ɗanta kuma gaskiya ba ma gujewa umarninta ko abin da ta ke so hakan matsala ne a garemu.
Dr zai yi magana Shahbeer ya ce "Ba haka tsarin da Allah ya ce abi ya ke ba, don kai ne Mahaifinta ka na da iko da ita ba dole sai ra'ayinka za ka bi wajen haɗata da Abokin rayuwarta kuma ba tare da Amincewa ko son ranta ba, kar ka yi tunani akan YaYarka ka yi tunani akan rayuwar ƴarka da gobenta da kuma makomarta, ina so ka yi tunani sannan ka shawarci ƴarka da Mahaifiyarta nasan za su faɗa maka abin da in ni na faɗa za ka ɗauka ƙarya na yi ko kuma son Zuciyata ne, ni ina son Abin da ƴan-uwana su ke so Don Allah kar ka yi abin da za ka sa na yi Aiki da Ƙarfin da na ke dashi wajen ƙwatarwa Ƙanina Ƴarka a matsayin Matarsa.
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/27/2022, 12:28 PM] INDO CE: *WATA HANYA*
26
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Da sauri Shahzaib ya ce "Ahh sanyi mana Boss, na san ma Abba zai Amince don kuwa Iyaye akwai tausayi da jinƙan ƳaƳansu.
Abba ya ce "Ƙwarai kuwa, wannan haka ya ke, To Dr Idris In Sha Allahu duk hukuncn da na yanke za ka ji na nemeka.
Dr ya yi murmushi cikin nuna farin ciki ya ce "Alhamdulillah, Madalla da Kulawa Alhaji Ibrahim, Haƙiƙa mu na ƙara miƙo dubban Godiyarmu gareka a bisa karramawa da Mutuntawa kuma in Allah ya yarda za ka same mu da cikakkiyar gaskiya da riƙon Amana ba za mu taɓa bari ɗiyarmu ta wulaƙanta ba, Allah i saka da Alkairi ya ƙaro Zumunci a tsakaninmu.
Abban Shukriya ya amsa da "Amin" da haka su ka yi sallama su ka rabu lafiya.
Dariyar Shahmeer ce ta dawo dashi daga Duniyar tunanin da ya lula, ya saki baki gami da cewa "Meye???"
"To hanga rufe bakin tukunna"
Shahmeer ya faɗa ya na ƙoƙarin dakatar da dariyar tashi.
Shahzain ya ce "Ba na son Ɓelesi in za ka gayan gaskiya ka faɗa."
"Na ga ka zuba tagumi ne tin da su ka tafi ko motsin kirki ba ka son yi.
rausayar da kai ya yi tare da cewa "Uhm, ya ci gaba da cewa "Ina cikin Fargaba ne, ba na son abin da zai yi katanga tsakanina da Shukriya wallahi sonta na ke da dukan Rayuwata, ji nake kamar idan na rasa ta zan iya haukacewa."
Jikin Shahmeer ya yi sanyi lokaci guda, ba abin da ya fara faɗo masa sai Malika, yarinyar da tin ta na rarrafe ta gama shiga Zuciyarsa kuma ya kamu da tsananin Sonta amna da ya ke SO Wawa ne ita da ta tashi sai ta kamu da Son Ɗan-uwansa, murmushi ya yi cike da dauriya ya ce "Hukuncin Allah shi ne Hukuncin Gaske Auta, ba ka ga yadda Tawa Ƙaddarar ta zo mini ba? ni na Sota ita Ta So Ɗan-uwana amma haka nan na daure na yi haƙuri Domin Farin cikinta, Gaskiya ka bani kunya da na ji ka ce haka ai haƙuri Ya na da Tasiri akan ko menene ya ke neman Addabarka."
"Dole ne na yi fargaba amma dai bai kamata na ce haka ba, Na Fahimta sosai Jariri sannan ina Addu'a da neman temakon Allah.
"Yauwa Ɗan-Autanmu; ni jikina ma ya na bani ba wata matsala, ka kwantar da hankalinka kamar an gama ne In sha Allah.
Mommy ce ta yi Sallama Tana riƙe da Shahzad sai da ta ƙaraso inda su ke Sannan ta ce "Ga Ɗanku, abin ya yi mana yawa Itama Ma'arufa ta gaji, ku ku riƙe shi yanzu.
Shahmeer ne ya miƙa masa hannu gami da cewa "Zo nan Ɗan Albarka."
tattaɓe baki ya yi Zai ƙara fashewa da wani kukan. Shahzain ya ce "To tawo gurina mu yi wasa ko?"
sai da ya ƙare masa kallo kamar ba zai je ba sai kuma ya yarda.
Mommy ta ce "Yaro sai wayo kamar Ɗan Dila?"
Shahmeer ya na Dariya ya ce "Lallai kam, ai haka ɗin ya fi, idan ba shi da wayo kuma ki ce bakya son Sokon Miji.
Gaba ta yi ta na murmushi gami da cewa "Ai kuwa ya takurawa Masu Rainonsa don yaro me Ɗafa ya fi takura.
Bayanin abin da su Dr su ka zo masa dashi ya yiwa Mami, cikin fara'a ta ce "Alhamduɗillahi, To maganar gaskiya Dama inaso in sanar da kai hakan nima domin kuwa ina ankare da Shukriya gaskiya ta na son yaron sosai, Ya kamata a matsayinmu na iyayenta mu fito mu yi mata Adalci, ka ga Hadiza fa Hajiya Dada ce ta yi mata irin wannan haɗin, to ya na da kyau akan Shukriya dai mu zama iyayen Asali kar mu cutar da rayuwarta, ni dai ba na goyon bayan ta Auri Maalik sai dai ya haƙura kuma ni a shirye nake da duk abin da Dada za ta ce, ni dai Fatana ka yiwa ƴarka Adalci kar ka biyewa Son Zuciyarku."
Abban Ya ce "Nima na yi wannan Nazarin sai dai ba na son abu me zama tashin hankali; Dr Idris Babban Mutum ne ana ganin mutuncinsa sosai nima ina ganin Mutuncinsa to ina ganin tin da Aurenta da Maalik ba abu ne wanda ya zama Dole ba kawai zan Amince musu in ya so ni sai in ɗauki laifin da kaina, In Allah ya yarda zan gaya musu na Amince."
Mami ta ce "Na yi Farin Ciki da wannan Sabon tunanin da ka yi, Allah i kaɗe dukkan fituntunun da ke ɓoye a ciki.
"Amin"
_______________
Dukansu sun yi matuƙar Farin Ciki da Amincewar Abban Shukriya musamman cikin Sauƙi ba tare da ansha muguwar wahala ba.
Yau. Ba su daɗe da shigowa gidan ba ko gama hutawa ba su yi ba Ma'arufa ta zo ta sanar musu sun yi baƙuwa Hajiya Dada.
Da sauri Shahzain ya kalli Shahbeer tare da cewa "Me ta zo yi kuma??"
Shahbeer ya ce "Sai ta faɗa za mu ji ai, ku barni da ita kar wanda ya ce zai yi mata magana."
Maida kallonsa ya yi ga Ma'arufa ya ce "Ki shigo da ita sashinmu.''
Shahzaib ya ce "Wannan Mace Anyi fitinanna; amma ai ba za ta hana abin da Allah ya rubuta ya faru ba.
Shahmeer ne ya miƙe ya na cewa "Ni idan kun gama sai a nemeni ba zan zauna ba."
tashi su ka yi dukansu su ka fice.
Sallama Dada ta yi sai kumburi take ta na huci, ya amsa cikin fara'a ya yi marhabin da ita.
akan Kujera ta zauna shi kuma ya zauna kan carpet.
"Kaine waye ma??"
Dada ta yi masa tambayar a yatsine.
"Ko gaisawa ba mu yi ba fa; Ni ne Shahbeer"
"Ai ba gaisawar ce a gabana ba ni, dama Shahbeer ɗin na ke nema sabi da shine tsageran, na zo akan Maganar Yarinyar da Ɗana ya ke so, Yadda ka ke son abin da ƴan-uwanka su ke so haka nima na ke matuƙar Son abin da Ɗana ya ke so, Ƴa kuma mu ne iyayenta mu ke da Iko da ita wata barazana taka da kurari ba zai sa mu baku ita ba, ka sa a ranka na riga na Aurar da ita ga Ɗana, ku cire tsammani kawai wannan shi ya kawo ni.
Murmusawa ya yi kafin ya ce "Na kasa zama a kan Kujera sabi da in baki girmanki, Haba ke fa Uwa ce kar ki zamto me son kai mana, Itama Mahaifiyarta ai ta na sonta kuma ta na son abin da take so kenan tauye musu nasu haƙƙin shine Cikarki Uwa??, ni ba wannan a tsarina, Kuma na riga na rubuta a Kundin Tarihina indai da rai da Rabo Shukriya ta Shahzain ce"
"Ni kuma indai ina raye Ba Namijin da zai Auri Shukiya in ba Maalik ba, ko me za'ayi ba zan taɓa canja ra'ayina ba sai in na mutu za'ayi.
"Ai kuwa Za ki Mutu Domin rabo kisa ya ke, ba wai ni na faɗa ba haka na ji Manya na cewa, hallau kuma wani ba ya cin rabon wani ko da ya ci sai ya yi amansa, kar ki ce za ki yi ƙoƙarin katange Shahzain akan Shukriya ki bari Lokaci ya nuna ita ɗin Rabon waye tsakanin shi da Maalik, indai ba ki yi hakan ba ni kuma zan nuna tawa Isar don ni Namiji ne uba nake a gurin kowace mace, za ki wayi gari ki ji sanarwar Aurenta da Ƙanina, Ina fatan ki kula Umma Dada, ina martabaki Sosai.
Da kyar ta numfasa cike da jin zafin maganar Shahbeer harda za ta mutu, jinjina kai ta yi gami da cewa "Danƙari Maƙari, Wato Magan-ganun banzan nan ni ka ke gayawa su, ba ka san wacece ni ba ko??, Ba ka san ni ke da iko da Yarinyar ba?? Idan na ɓoyeta fa wallahi ba ka isa ka ƙara ganinta ba daga kai har Mara Kunyan ƙanin naka.
"Kenan Ɗan naki ba Jarumi bane??"
ya yi mata tambayar ya na dariya.
"Ɗana Jarumi ne cikakke ma kuwa"
ta bashi amsa a fusace.
ya ce "To ki fita daga sabgar kawai ki bar Jarumai a cikin Fagen, Indai har Maalik ya yi Nasarar kayar da Shahzain Na Rantse da Ubangijin da ya shirya mini Ƙashin haƙarƙarina Da kaina zan bawa Maalik Gudummawa wajen Aurenta, Ki Ɗauka cewa gasa ce tsakanin ni da ke za mu ga wanda ya fi Zarra ba wai ƙarfa-ƙarfa da shiga hurumin Yara ba ko na iyayen ƴaƴa ba.
"Za ka gani kuwa, ni Zarra a jinina ta ke gadarta na yi wallahi, ba yadda za'ayi ka nuna min ita ƙarya ka ke YARO, Na bar su kuma za ka ga yadda Ɗana zai yi cali-cali ya yi Fatali da Ɗan-uwanka don ni ban haifi lusari ba daga nan har Shekara Biyar ina jiran wannan ranar, sai Ɗana ya nuna maka bambancin da ke tsakanin Shege da Me Uba.
Ta yi maganar ta na huci ba tare da ta jira amsar shi ba ta gyara jakarta ta nufi Hanyar fita.
Dariya ya yi Sosai kafin ya ce "Iskar Banza da Wofi, gashi har na sauya miki tunani duk wannan fuffukar, kuskuren da ki ka yi kuma shine na Amincewa da Gasa tsakanina da ke, ba lallai ki kai Labari ba."
Tashi ya yi ya nufi Babban Falo ya yi kicin kicin da rai kamar ba shi ba.
Mommy ta ce "Shahbeer Me ya faru naga ta fita ta na tiriri."
"Mama kin san in mutum ya tunzura musamman irinsu masu shegen jin kannan abin akwai daɗin Kalla, Ban ma zaci cikin sauƙi zan shawo kan Matsalar ba; yanzu ka na da sauran Lokaci Shahzain.
Mommy ta ce "Na ji daɗi Allah ya sa ba wayo ta yi maka ba."
Shahzain ya ce ''Haba dai wayo dai?? ai tin da ta faɗa Tarkon Me Dabai-bayi shii kenan ta gama yawo.
Shahmeer ya na shirin yin magana Malika ta yi Sallama, Mommy ce kawai ta ke fara'a gami da yi mata sannu da Zuwa, Shahmeer kuwa ƙasa ya yi da kai ya lumshe idanunsa sabi da wani irin ciwo da ya taso masa tin daga Zuciya.
Takaicin ganinta ya sa Shahbeer ya ƙara sauke rumfar Ido.
ta ƙaraso Kanta a ƙasa kamar tsohuwar Munafuka, gaba ɗaya sai ta ji ta tsargu tausayin kanta ya kamata, gefen Mommy ta zauna gami da gaisheta ta amsa cikin sakin fuska, da kyar ta iya miƙo musu tasu gaisuwar Shahmeer ya yi da gaske ya amsa tare da miƙewa, Tsaki me dogon sauti Shahbeer ya murza sannan ya Nufi Sashin Inna don gano Bugun numfashinsa, duk watsewa su ka yi daga gurin kamar sun ga baƙar sa'a, kasa jurewa ta yi ta fara zubda ƙwallah a ɓoye don kar Mommy ta lura.
Mommy ta ce "Ina son na yi magana da Dr to Allah bai yi ba har yau, in Allah ya so ma da kaina zan zo ba sai ya wahalar da kanshi ba, ranar da za ki tafi sai mu tafi tare.
kai ta gyaɗa cikin sarƙaƙƙiyar Murya ta ce "Yau zan tafi ba zan ma daɗe ba."
"Me yasa Malika?"
"Am..am... ban tawo da niyar kwana ba dama Mommy.
"To shi kenan Ni in na samu lokaci ɗin zan zo".
ta gyaɗa kai ba tare da ta yi magana ba.
Ya Maalik ya na jiranki a Mota.
Abid ya faɗa ba tare da ya jira cewarta ba ya fice.
Wani mugun baƙin ciki ne ya turnuƙeta, ai fa shi kenan ya dawo na shiga tara, ta faɗa a cikin Zuciyarta.
Kwanciya ta yi ba tare da niyar tashi ta je ɗin ba, ta na jin wayarta ta na kuka ta san Maalik ne don haka ta yi banza da ita. ta ɗebi lokaci me tsayi a kwance har ta fara bacci-bacci Abida ta zo ta tasheta "Wannan ai rashin mutunci ne Anti Shukriya, Fisabilillahi haka ake rayuwa kin ajiye mutum ko tunaninsa ba kya yi?, Ba ki ce masa ba za ki zo ba, ba ki ce masa za ki zo ba kin barshi sai jiranki ya ke yi.
"Ke ba na son Guyaba Dallah Malama.
"Alllah ya baki haƙuri amma gaskiya ki dinga Adalci.
ta na kaiwa nan ta fice daga ɗakin.
wayarta ta janyo ta duba lokaci 09:01pm tsaki ta ja kafin ta ce in banda iskanci a daren nan zai zo ya ce wani sai na fita. Hijab ta zura ko gyara shi ba ta yi ba ta fice cike da baƙin ciki da takaici.
baya ta shiga ta yi damfamfan sai tsaki ta ke rafkawa ba ta ce masa ci kanka ba Shi ma ya yi mata banza har ta gaji ta buga tagumi ta fara gyangyaɗin Dole.
Fitowa ya yi ya zagayo bayan ba tare da ta ankara ba sai jin muryarsa ta yi a kusa da ita ta yi firgigit ta tsorata.
"Ba haɗiye ki zan yi ba kwantar da hankalinki.
tsaki ta yi ta bashi wata kyakkyawar harara kafin ta ce "Ai za ka iya tin da ka zama maye, jarababbe kawai na ce ba na sonka amma dan Masifa da baƙin naci da ƙarfin hali irin na Gado ka ƙi rabuwa da ni."
"Ba zan iya rabuwa da ke cikin sauƙi haka ba, mafi sauƙi ki kasheni sannan ki Auri wani yanzun ma kin riga kin yi wa rayuwata illah da ki ka fara son wani ki ka banzatar da ni, Ke fa ba irin Mata barkatai ɗinnan bace samun kamarki sai wanda ya dace.
"Wasu ƴan zantukanka na banza na yaudara, ba zan yarda dasu ba, ka ga ni dare ya yi zan koma cikin gida.
"Fita mana ko yatsa ban ɗora akanki ba bare ki ce riƙe ki na yi.
Buɗe murfin Motar ta yi ta ji garam alamar a kulle ya ke, a Masife ta ce "To ka buɗe mini mana."
"Hakan ne dai ba zan iya ba, ya kamata ki zauna ki fahimceni Don Allah kar ki bari Sonki ya lalata mini rayuwa, na ji Hajiya ta ce Abba ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 30