Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [12/20, 9:42 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 20 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. "Subhanallah' walhamdulillah, wa la'ilaha'illallah" shine abin da Shahbeer ya furta bayan ya gama ƙarewa yaron kallo. anya kuwa ni ba wani mutum ne wanda ban san kaina ba? ya yi wa Zuciyarsa tambayar. Muryar Mommy ce ta katse masa tunanin "Shahbeer ka ga ranar da nake gudu, na ji matuƙar tsoron haka ta faru sai gashi kuma ta tabbata, karɓar ƙaddara me kyau da mara kyau ita ce ta dace da kowannen ɗan-adam me tawakkali ban da haka da bansan wane irin tashin hankali zan shiga ba, tabbas iri baya ƙarya yanzu kai ma ka shaida. baki na rawa ya ce "Mama kenan Ɗana ne???, kenan ni ne na aikata kema kin shaida Umma???" "Hatsabi-bancinka ya fi komai razanani Inya, ka manta ko kai waye ne?, ka manta Yaron da ya gagari kowane sa'a??, Ba zan iya yarda cewa ba Ɗanka bane Shahbeer, idan kuma ba naka bane ka nema min ubansa a tsakanin Kai da ƴan-uwanka su uku da kuma ƙannenka guda biyu da Mahaifinka, cikinku dole akwai Mahaifinsa" "A'a Mama, ba na jin Mahaifina ya taɓa aikata Zina duk rashin mutuncinsa, kuma ina da tabbbaci akan cewa Ƴan-uwana ba Mazinata, bane, ban ƙi ba Safyan kuma ba zan ɗora masa laifi ba dan ba ni da tabbacin shine ko ba shi bane. Kallon Ɗan-jariri ya yi cikin lokaci guda ya ji ƙaunar Yaron ta gama shiga Kowane saƙo da lungu na Zuciyarsa, fuskarsa ɗauke da Murmushi ya ce "Ni ne Mahaifinka Ɗana, Ba na so ka kira wani da wannan sunan in ba ni ba, Amma Don Allah kar ka kwaso irin Halaye da Ɗabi'una, Ina sonka Mukhtar Takwarana." Ci ke da Mamaki Malika ta ce "Shahbeer ka san me bakinka ya ke furtawa kuwa??." "Ɗan da ba abin da ya zubar daga Babansa kin ga ai ya cancanta na kira shi da Sunana. Mommy ta ce "Suna ne me daraja sunanka, kar ka zubar da Mutuncin sa ta wannan Hanyar" "Ba dan Tsirarun Mutane a ka yi sunan ba Ummi, ki barni in kira shi da sunan da nake so, nima ba'a son raina na kasance Muktar ba don haka ba komai ne ake so a samu ba. "Shi kenan, Abin da ya shafeku ne wannan, da kai da Babanka da Kakanka me irin sunan naka. Daga haka ta bar wajen. sake rungume Takwaransa ya yi cike da kulawa. matsowa kusa da shi Malika ta yi idanunta sun cicciko da ƙwalla, cikin Sanyi ta ce "Zan zamo Uwa gareshi indai ka bani damar hakan, Allah ya sa mini son Yaron ji nake ina ma zai zamo Ɗana na kaina, na so ni ce silar Zuwansa Duniya ba Halima ba. "Kin fara Haukacewa ne Malika??" Shahmeer ne ya yi mata tambayar cikin fushi da ɓacin rai. "A'a ban haukace ba, amma ban sani ba ko kallon haukan za ka yi mini, hakan ba zai dameni ba domin in ka gaɗa to da hakan na yi maka kama. "Zan iya kulawa dashi Malika, na gode da kulawarki da kuma Ƙaunarki gareshi. Ya na gama faɗen haka ya nufi sashinsu. Inna ta ce "Allah ya raya mana shi ita kuma Halima Allah ya bata lafiya." Shahmeer ya ce "Abin akwai ɗaure kai, ya kamata mu binciki Safyan da shi da Sa'ad ɗinnan me zubin Salihai." "Ya yi, nima na yi wannan tunanin, idan kuwa ba su bane to tabbas Ya tabbata Ɗanmu ne" Shahzaib ne ya yi maganar cike da kokonto. Da haka suka bar maganar. Safyan ne da Mom ɗinsa su ke zaune su na tattauna, "Mom wallahi kin san ba dan babban Abokina ne Maalik ba da tuni na yi wa Yarinyar nan abin da ba zai mata daɗi ba." "Abotar taku ta banza da wofi, ceto martabarka ai ya fi Abotar taku, gashi yanzu ta sanadin abin da ku ka yi kai da ita Alhaji ya fara nuna mana iyakarmu akan ƴa-ƴan da ba'a da tabbacin ta halak ya same su." "Waye ya sani Musu?, nima wallahi abin ya na ci min tuwo a ƙwarya yanzu Sa'ad shine ɗan gaban goshi, kuma kinsan wani tashin hankali?? Wallahi Double Two Star sun yi Nasarar Rusa Dukiyar Alhaji yanzu ba wani abu nashi da ya ke motsawa, don haka zan yi ƙoƙari sosai dan na ceto martabar Dukiya da Sunan Dad. "Daɗina da kai ɗan Albarka ne, ka yi komai kar ka raga musu ka ji?" ya ce "To Mom." Abida ce ta kalli Shukriya ta kauda kai kafin ta ce "Ya Maalik ya na bala'in sonki Aunty Shukriya, amma me yasa ba za ki so shi ba?" "Ba na ra'ayinsa, kinsan ba'a yi wa So Dole ko a tilasta shi, sabi da haka ki ƙyakeni. "To kin ce ya baki lokaci kuma ya baki, har yanzu lokacin bai yi ba??, ba na so ki taso hayaniya fa. "Da haka zan dinga jan lokaci har Na kai gacci, Ɗabi'unsa munana ne haɗa alaƙa dashi wahala ce. "Amma a ganina Jansa a jikinki zai fi tin da ya na sonki. "Ke Yarinya ce Abida ba za ki gane ba, ni fa Akwai wanda na ke mafarkinsa kullum, shi na ke so kuma In Allah ya nufa shi zan Aura, sai dai ina tsoron Jarabar Hajiya Dada. "Ai Dole ta yi Jaraba tinda nema ki ke ki maida ita ƙaramar yarinya. ''Kin ga in haka za ki ca ki yi mini shiru, ba na son rainin hankali. "To na yi shirun, amma dai gaskiya na ke faɗa miki, ko da yaushe hankalinsa ya na kanki, ba ki da Imani ma. hannu ta ɗaga mata gami da cewa "Dakata Malama, ina ruwana don hankalinsa ya na kaina? na ce ba na so dole ne?, aikin banza duk kin ɓata mini rai." "Amma ai ya gama yi miki komai, da bai shiga lamarinki ba da ki ka tarkatowa kanki tsiya ai da yanzu wannan Mahaukacin Safyan ɗin ya yi gutsi-gutsi da ke, yanzu kin samu kanki shi ya sa ki ke da bakin magana. "Ohh Allah na, ya kamata ki fahimce ni, na san kusan kowace maganata a barkwanci ku ka ɗauke ta, to wallahi ba wasa na ke ba ba kuma shirmena bane ni akwai wanda na ke so kuma kullum sai na yi mafarkinsa. Tausayinta ne ya fara kama Abida, cikin sanyi ta ce "To Aunty ai Allah shine ke yaye kowace irin damuwa, sai ki ta addu'a Allah ya zaɓa miki mafi Alkairi da dacewa dake." "Yauwa haka na ke son ji, nifa yau unguwa zan je. "Allah ya tsare, ni dai ba raka ki zan yi ba. "Nima ban gaiyaceki ba ai. tashi ta yi ta nufi ma'ajiyar kayanta domin Duba wanda za ta sa ta fita dashi don kuwa so take ta ƙurewa kyau gudu. Zazzafar Iska Shahmeer ya furzar kafin ya ce "duk binciken da mu ka yi ya nuna Ba ruwan Safyan a cikin lamarinnan haka Babanshi, wai me hakan ya ke nufi ne?" Shahzaib ya ce "Allah ne ya sani." Shahbeer ya ce "Kar ku ƙara wahalar da kanku akan maganar nan, ta riga ta wuce Ɗana ne, ku faɗawa wanda ranku ke so." Shahzain ya ce "Takaici na ke ji idan ka na faɗen haka Inya." "Komai ai kamawa ta ke yi, abin da ya ke a Zahiri shi na ke faɗa, ba amfanin mu zauna ɓata rai da lokacinmu akan abin da ya riga ya faru mu maida hankali a wajen gyara gaba. jinjina kai Shahzaib ya yi kafin ya ce "In Allah ya yarda ta wuce Inya, yauwa dama ina so in ce maka ka je nemawa Auta Aure." Murmushi ya yi gami da cewa "Aure dai?" "E mana, har yanzu bai dena begen yarinyar nan me dattin ƙwaƙwalwa ba." "Wai da gaske ne Autana?" Shahzain ya ce "Ko shakka babu ƙarya ya zumbiɗa mini." Shahmeer ya yi Dariya gami da cewa "Wallahi na ɗauka ko shakka babu da gaske ne, ashe sanyin guri Ƙarami ya ji." "Ni ba na ƙarya kun sani, Do Allah wani ya je ya ce Inna ta haɗo mini Shayin Soɓo." "Nima zan sha amma fa ba za ni ba." Shahmeer ya faɗa gami da gyara kwanciya akan kujera. Auta ma cewa ya yi "Idan ka je kofi Uku za ka yi mana Ƙarami." "Je ka da kanka daga nan ka duba mini Ya Halima ta ke." kai kawai ya gyaɗa cike da tausayin ɗan uwan nasa, Har mamakin yadda soyayyar mace ke neman sauya masa rayuwa ya ke, ga wani abu me dabaibayi a gefe guda. da ƴan tunane-tunane ya ƙarasa babban Falo Inna da Ma'arufa ne kawai a zaune su na hira, bai zauna ba ya ce "Inna Shayi." "To Ƙarami bari in tashi." "Aaaaa!!! tsaya tsaya, ina wannan ta ke Beauty Kalar kyau?" sai da ta jinjinawa ƙarfin rashin mutuncinsa, ya na kallonta amma ya ke tambayar inda ta ke sabi da rashin mutunci. Cikin yanayinta na sanyi-sanyi ta ce "Gani nan." "Ohh To, ai ina zattawa ba ta ga nan ne, Inna ta biyo ni ta tayani dafawa." ido ta zuba masa bayan ya yi gaba, ji wani yare da ya yi kuma a hakan Hausa ce, "Zancen yaren za ki yi ko za ki taya shi aikin??" da sauri ta miƙe ta na cewa "A'a Inna me ya kai ni? yanzun nan zan tafi. ya na tsaye jikin bango ya harɗe hannuwansa a bayansa, idanunsa a lumshe a hankali sautin karatun Alƙur'ani mai girma ya ke fita daga bakinsa, kasa yi masa magana ta yi sai ta ja ta tsaya ta na jiran gamawarsa, a hankali tunaninta ya fara sauyawa daga na jiran nashi sabi da kallon da ta ke masa ya sa Zuciyarta ta fara saƙa mata abubuwa iri-iri akanshi, ta iya cewa tin da take ba ta taɓa zama ta yi masa kallo na tsanaki ba, a cewarta ya fiye jaraba. ji ya yi shirun ya yi yawa gashi ya na jin kaifin Idanu kamar ana kallonsa, buɗe ido ya yi ai kuwa su ka karaf!! da sauri ta sunkuyar da kai ta nufi hanyar fita. murmushi ya saki kafin ya ce "Ya kamata a dinga neman izinin mutum kafin a dinga kallonsa ko dan gudun katari." ƙara sauri ta yi za ta fice "Ma'arufa!!" ya kira sunanta, tsayawa ta yi cakk cike da zullumi, "Zo ki ɗakko mini Soɓo. ba dan ta na so ba ta dawo, ta na ɗakko masa ta koma gefe ta tsaya kanta a ƙasa kamar munafukar da aka yiwa ƙawanya, ji ta yi ƴar ƙaramar wayarta da ta saya ta yi Motsi, ta tabbatar kowaye ya kira ta bai wuce Umma ba dan haka ta ce "Rar, Rankayadaɗe zan ɗan je wajen Inna." da kai ya amsa mata, ta yi saurin ficewa daga kicin ɗin, har kiran ya katse sai ga wani ya ƙara shigowa ɗagawa ta yi gami da sallama, Umma ta ce "Ma'arufa Babanki ya zo ki yi sauri ki dawo ku gaisa kafin ya ƙara tafiya, don idan ya tafi ba mu san lokacin da za mu ƙara ganinsa ba." murmushi me tafe da hawaye ta yi gami da cewa "Na yi farin ciki sosai Umma, don Allah ki gaishe mini dashi kafin in zo, yanzun nan zan tawo." "To sai kin zo. soke wayar ta yi a ƙugunta ta koma kicin cikin sauri, jikina na rawa ta ce "Ka yi haƙuri Yallaɓai zan tafi gida yanzun nan uzuri ya kamani." "A'a, ba za ki tafi ba Tuwon Dawa na ke so in na gama shayin." kamar za ta fashe da kuka ta ce "Ka yi haƙuri ka barni na tafi, na san Inna za ta yi maka, idan ban je ba..." katse ta ya yi da cewa "Idan ba ki je ba Za a tashi Duniya ne??, o'o? yau na taɓa na ji, ga abin da na ce ina so ke kuma ga wanda ki ke so, dolenki ki tsaya ki yi mini kafin ki tafi ko kuma ki bani ƙwaƙƙwaran dalilin da ya sa za ki tafi, idan kuma ba dalili to fa ba za ki je ko'ina ba." In ce masa Babanmu ne ya zo?? kai A'a, hakan kamar tozarci ne garemu, nasan zai mini wasu tambayoyin akan hakan kuma faɗa masa sirrinmu ba amfani, tunanin da ta yi kenan dan haka ta ce "Don Allah ni dai ina son zuwa, zan ma dawo ka temaka mini." "Ba ki da aikin yi ne, in za ki fara aiki ki fara in kin gama kya tafi. hanyar fita ya nufa ya na cewa "Idan Shayin ya yi ki kawo mana duka fulas ɗin, sannan kar ki min ɗanyen Tuwo. daga haka ya fice ko waiwayenta bai ƙara yi ba. fashewa ta yi da kuka me cike da takaici, sauri sauri ta dinga yi don ta gama ta tafi, shekara biyar kenan bata sanya Babanta a idanunta ba yau kuma ya zo ana neman yi mata sanadin da zai ƙara guduwa ba tare da sun haɗu ba. duk da saurin da ta yi ta na zuwa Fiddausi ta ce "Ai ya riga ya tafi, wai dama wucewa ya zo yi." "Innalillahi, yanzu Baba ƙara komawa ya yi?" Umma ta share ƙwallah kafin ta ce "Ya koma, ai ba shi da imani da tausayi, wai duk wannan shekarun da ya yi bai san cinmu ba bai san shanmu ba wai masara kwano Uku ya sayo mana, haka ya ƙara ɗaukar jiki ya tafi, biyar ɗin da za mu yi cefane bai bayar ba sai ka ce ɗanyar Masarar za mu ci." zama Ma'arufa ta yi gami da cewa "Wasshh, ai duk wannan mugun azzalumin mutumin ne ya sa ban ga Baban ba, wannan wace irin jaraba ce?, wallahi da ina nan ba zan bar shi ya tafiya ba." Umma ta ce "Ga Usman nan ga Fiddausi, idan bai ji kukana ba ai ya ji na ƴaƴansa, to duk irin kukan da mu kai masa akan kar ya tafin sai ya watsar ya yi gaba, dan mutum Mafatauci ne ai ba haka Allah ya ce ayi ba, gaskiya ya na zalumtarmu, ba dole ƴaƴan mutum su lalace ba fisabilillahi? da mu ka ce ya jira ki zo ku gaisa ma ƙi ya yi, hakan Adalci ne? " "Umma ku ƙyaleshi, Allah ya ganar dashi gaskiya, Addu'ar da zanyi masa kenan. Fiddausi ta ce "Amin, amma ya riga ya saba ba yadda za mu yi. Ma'arufa ta ce "Allah zai kawo mana mafita. tashi ta yi ta wuce ɗaki can ƙurya sannan ta fashe da kuka, ba wanda ta fi jin haushi akan tafiyar da Babanta ya yi sama da Shahzaib, kamar kar ta ƙara komawa gidan nasu haka ta ji sai dai ba yadda za ta yi can ne rufin asirinta, da ɗan abin da ta ke samowa gashi ta fara canja musu rayuwarsu itama har waya ta saya, ta daɗe ta na kukan kafin bacci me cike da gajiya ya yi awon gaba da ita. Inna ce ta shigo da sallama bayan sun amsa ta ce "Wata kyakkyawar yarinya me fara'a ta zo nemanku. kusan a tare su ka ce "Mu??" "Ƙwarai kuwa ta fi riƙe sunan mutum biyu amma ba zan faɗi ko suwaye ba. Shahzain ya ce "To gaskiya sai dai in Shahzaib ko Jariri (Shahmeer)." Inna ta ce "Ku dai ku zo mana, ni fa me shigo muku da ita nan ce in kun ƙi zuwa." sanin za ta aikata ya sa su ka miƙe Inna ce ta yi musu jagora har zuwa Babban Falo su na tafiya ta na musu Nasiha akan kar su yi wa yarinyar rashin mutunci su karɓeta hannu bibbiyu, To kawai su ke ce mata har su ka ƙarasa ta na jaddada musu. ta na ganinsu ta miƙe tsaye zumbur gami da faɗin "Wow Ma sha Allah, wallahi sai yau na taɓa ganin ƴan huɗu ido da ido kuma manya ma, gaskiya ni ƴar baiwa ce, sannunku Yallaɓai Shahzain." Kamar soko haka ya saki baki ya na kallonta, ganin yadda ta ke maganar kamar za ta tashi sama sabi da rawar kai ya sa ya ƙara sarawa girman gigi da rawar kanta, gefe guda kuwa mamakin zuwanta a wannan lokacin ya ke yi bayan watanni kusan Twakas da haɗuwarsu da rabuwarsu. Jariri ne ya ɗan taɓa shi gami da cewa "Idon Boss fa ya na kanka." da sauri ya yi ƙasa da kai Zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri. murmushi Shahbeer ya saki gami da cewa "Ƴar-jarida Hauwa'u Ibrahim, yau Ziyarar bazata muka samu?" da sauri ta ce "A'a Yallaɓai ba ƴar-jarida ba, ka manta cewa an koreni daga aiki? ai har yanzu zaman banza na ke yi, ga yawan mafarkai akan ƴan-huɗu wata rana sai in ji dama nima na haifi ƴan-huɗunnan." Duk yawan Dauriyar Shahbeer sai da dariya ta sulluɓe masa. Shahzain kuwa dafe kai ya yi gami da cije gefen leɓensa, bai yi tunanin irin wannan katoɓarar daga gareta kuma a tsakiyar Babban Falonsu ba ga su ga Mahaifiyarsu. Shahbeer ya ce "Ƙanne na Shahmeer Shahzaib Da Autana Shahzain su na yi miki barka da zuwa, Ki zauna sai mu gaisa ko?" Zaman ta yi ta harɗe ƙafa sannan ta ce "Yallaɓai Ka ce Ƙannenka su zauna." da hannu ya yi musu alamar su zauna, su ka zauna ba tare da sun yi magana ba kowannensu jinjina da ban girma ya ke ga Lamarin Shukriya ba ma kamar Shahzain da ta gama Ɗaure masa kai. "Woow ya yi, Yallaɓai na ga ko magana ba ka yi ba da iya hannu ka sa su ka zauna." "Ya isa Shukriya, ko gaisawa ba mu yi ba fa. "Au na manta ina wuninka, Shahmeer Shazaib ShahAuta Ina wuninku?" Amsawa su ka yi amma banda Shahzain da ya ke binta da kallo me kama da Harara. Mommy ce ta ce "Shukriya Ki na da Surutu da yawa gashi kuma Inya ɗina ba mai son hayaniya bane?" Dariya ta yi gami da cewa "Allah sarki, to Mommy ya koma Bedroom ShahAuta zai tayani Hira ko Auta??" Murmushi Mommy ta saki dan kuwa... _________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ *INDO* [12/21, 11:23 AM] INDO CE: *WATA HANYA* 21 Ayeesha Abdulkareem *(Indo ce..)* ELEGANT ONLINE WRITERS. ....Don kuwa ta fahimci duk cikinsu Auta ne kawai ya fi Burge Shukriyan. Shahzaib ya ce "Ban san menene dalilin zuwanki gidanmu a wannan lokacin ba, ko dai labarin namu ki ka ƙara zuwa za ki ɗiba??" da sauri ta ce "A'a rufa ni ka sayani, ai na watsar da Al'amuran nan, kawai cewa na yi bari in zo mu gaisa." kafin Shahzaib ya yi magana Shahzain ya ce "Ai kun gaisa sai ki tashi ki san na yi." "Au kora ta ka ke yi??, to ai ba da ƙafarka na zo ba. Shahmeer ya ce "Ohh idan kuma ya maida ke da ƙafar tashi fa." Za ta yi magana Shahbeer ya katse ta da cewa "Maalika Kawo mata abin sawa a baki mana." tin da su ka fito Sai lokacin ta ɗago kai ta kallesu, ganin yadda ya yi maganar ba tara da ya kalli inda ta ke ba wani takaici ya turnuƙeta gashi tin da Yayi Alaragab da Shukriya ya ke ta Murmushi amma ita ya ƙi sauraronta ko kallo ba ta ishe shi ba. Shukriya ta ce "A'a Kwantar da hankalinki ba abin da na ke so wallahi ba zan ci komai ba." "Don Allah ki tashi ki tafi na gaji da ganinki, haba wannan ai ƙaddara ce" Shahzain ne ya yi maganar a Masife. sakin baki ta yi gami da cewa "Laa, Allah ya yi ka da saurin Fusata kai kam." Shahbeer ya ce "Ina me baki haƙuri Shukriya, Don Allah ki bamu damar komawa Sashinmu. ta ce "Ai ba sai ka nemi izinina ba yallaɓai." "Okay" ya faɗa gami da miƙewa, Su Shahmeer sashin su su ka koma shi kuma Ya nufi sashin Inna, So ya ke ya ga motsin ɗan Jaririnsa, can ya hangoshi kan gado a ɗan Nesa da Halima, ya sha kwalliya cikin haɗaɗɗun kayan Jarirai Farare tass, Fuskarsa ta ɗau Farar Hoda da Kwalli har da fashin goshi, irin ɗan zanen da ake yi wa yara maza a tsakanin girarsu, da Alama Inna ce ta yi masa kwalliyar, baccinsu su ke cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali ba abin da ke damunsu. hannunsa harɗe a ƙirjinsa ya coge ya na kallon Yaron tamkar Tauraro ɗaya a Sama; ya ɗauki Lokaci a tsaye kafin ya ƙarasa kusa dashi, cike da ƙauna ya sa hannu ya shafi gefen fuskarsa gami da Cewa "Mukhtar (SHAHZAD), bai kamata Inna ta bar ka anan kai kaɗai ba" zama ya yi a gefen gadon sannan ya ɗakko Jaririn Wanda ya yi masa laƙabi da Shahzad (Prince) rungume shi ya yi ya na ƙara zuba masa idanu. ya yi nisa a cikin Tunanin ya ji siririyar Muryarta ta na kiran sunansa kamar yadda ta saba "Baba!!" ɗago idanunsa ya yi Hakan ya bawa Hawayen da suka cika idanun nasa taf damar zubowa, numfashi ya ja ya sauke kafin ya ce "Halima Kin tashi?" ido ta zuba musu su duka biyun ta daɗe a haka sannan ta ce "Baba mene wannan?" Kallon Shahzad ya yi ya kalleta murmushi ya suɓuce masa, "Ɗanmu ne ni da ke, Mutum ne ba wani abu ba cewa za ki yi Waye wannan, shi Jariri ne bai iya magana ba kin ga ke kin iya. "Ka cauke ci. ya ce "Kamar ya kenan? ki na nufin kar in ɗauke shi? bacci ya ke fa." langaɓar da kai ta yi a shagwaɓe ta ce "Um-um ba na con ci." Waro mata ido ya yi gami da cewa "Me???, ba kya son Shahzad? amma a hakan Inna ta yar min dashi a kusa dake salon ki tashi ka shaƙe min shi ko ki jefo shi daga sama?, ki canja tunani gaskiya, ni kin cika min kunne ma do Allah kar ki tayar min da yaro daga bacci. ganin ya haɗe rai ya sa ta fara Dariya ta na cewa "Je yi faɗa je yi faɗa. murmushi ya yi ya ce "Wato kema har kin gane banida sauƙi kenan. Inna ce ta shigo da sallama, "Oo, Allah kenan me tsara abin sa yadda ya so, kalle ku a haka kamar gaske gwanin sha'awa, wallahi ka yi ƙoƙari ka Aure yarinyar nan, dik da naga Ummanku ba ƙaunarta ta ke Sosai ba. Dariya ya yi gami da cewa "Inna ke waye ya tambaye ki?" "Ai ka san Allah gaskiya na faɗa, kuma ita gaskiya ko ba'a tambayeka ba in ka faɗa ba laifi, wallahi a hakanku kamar ma'aurata. "Inna Zan Aureta mu riƙe ɗanmu tare mana, amma idan ta dawo hankalinta ba kya tunanin abin da zai faru? na san ba za ta ƙara yarda ta haɗa hanya dani ba. da sauri Inna ta

Chapter 13 of 30