dan Da Ƙarfin Addu'a ba da yanzu ya zame min taɓin hankali domin ya riga ya fara gushewa.
Shahzaib ya ce "Allah ya yi kariya a gareka Shahbeer, Don Allah a duk lokacin da ka ji irin wannan tunanin ya dawo maka kai ta A'uziya don shaiɗan ne ya ke ƙoƙari yi maka gangi."
Da murmushi akan fuskarsa ya ce "To Shahzaib, Bari in je in Dafa mana Shayin."
Shahmeer ya ce "Ni dai na Soɓo na ke so."
"To" kawai ya ce ya ci gaba da tafiya.
a Falo ya tarar da Inna da Mommy suna Hira ya yi sannu musu sannan ya nufi hanyar kicin. "Amma Inya da Aurenka ka ke neman hanyar kicin??"
Mommy ta yi masa tambayar tare da tsare shi da ido.
"Oh Mamma, Ina Muradin yi da kaina ne kawai.
Inna ta ce "Ƙyale shi, Kar ki ɗorawa kanki Wahala, jeka Ɗannan."
ba tare da ya yi magana ba ya shige.
Inna ta kalli Mommy cikin muryar raɗa ta ce "Bar ni da shi Ai zuwa zan yi in ce ta fito ta yiwa Mijinta girki, in ya so sai su yi tare ko ya bar mata ta yi."
Mommy ta ce "A'a ki ƙyaleta ta huta."
tashi ta yi ta na cewa "Idan na barta ai ba za ta dinga yi masa ba mu za ta barwa aiki.
kafin Mommy ta yi wani yunƙurin Inna ta yi nisa.
ya na aikin ya na tunane-tunane, kamar daga sama ya ji sallamarta, bai ɗauka ita ce ba dan bai yi tunanin ganinta, ko sallamar bai amsa ba bare ta san ya san da zuwanta.
cikin sanyi ta ƙaraso can gefe da shi ta tsaya, ta gaida shi cikin ɗari-ɗari.
Ido ya zuba mata na ɗan wani lokaci kafin ya ce "Lafiya, me ki ka zo nema a kicin kuma yanzu?"
kanta na ƙasa ta ce "Shayi Inna ta ce in dafa maka."
ohh Inna aikin manya ta yi mini kenan, ta ce a barni na yi yanzu ta turo mini wata, tunanin da ya ke kenan a cikin ransa kafin ya juya mata baya ya ce "Zan iya da kaina.
"Ka bari in yi maka Don Allah, meye amfanina idan ba zan dafa abu ka ci ba?"
"Malika kar ki bari raina ya ɓaci, ko murya ba na son ɗagawa mace ba na son ki yi mini abin da zan ɓata miki rai.
Wasu zafafan hawaye ne su ka fara rige-rigen sakkowa kan kumatunta, cikin rawar murya ta ce "Allah ko me za ka yi mini zan jure don na san akan gaskiyata na ke, a matsayina na Matarka Dole abin da ya shafi wannan ɓangarena ne."
Ko cikal bai ce mata ba ya ci gaba da abin da ya ke yi.
"Aunty Ma'arufa ke yaushe za'ayi bikinki da YaYa Shahzaib?"
Usman ne ya jefo mata tambayar cike da son jin gaskiya.
Da sauri ta ce "Kai ku ji Ɗa Don Allah, ni Allan-musuru ce da za ka yi mini irin tambayar nan?"
Fiddausi ta ce "Wallahi nima da tambayarki zan yi sai ya riga ni.
tsaki ta yi kafin ta ce "To ba yanzu ba, sai lokacin da za'ayi na Ya Shahzain da Ya Shahmeer, nasan shima Ya Shahbeer zai Auri Halima kun ga sai ayi lokaci Ɗaya, amma fa ba kwanan nan ba."
Fiddausi ta ce "Gaskiya ya kamata ayi mu sha biki."
Usman ya ce "Wallahi kuwa."
murmushin takaici ta yi gami da cewa "Ba ku san meye damuwar ba ku kam, Mu da Babanmu ba ya nan gashi duk danginsa ba me nemanmu duk ba mu san su ba, ba mu san inda su ke da zama ba taya Aure zai yuwu? waye ma zai Ɗaura mana Auren??, Dole sai lokacin da ya waiwayemu ko da nan da shekaru goma ne idan ba zai iya jirana ba sai dai ya Auri wata ni kuma in zauna jiran Babana"
Ta ƙarasa maganar ta na kuka.
Fiddausi ta ce "Kuma gaskiya ki ka faɗa, Amma ki kwantar da hankalinki In Allah Ya Yarda ba zai watsar da ke ba shi ma zai jira Baban namu.
Umma ce ta shigo ɗakin ta na cewa "Ai Allah ya na duba da kyakkyawar Zuciyarki Ma'arufa in Allah ya Yarda ba za ki taɓe ba, Ba iya jaje za mu zauna yi ba sai mui ta Addu'a Allah i baiyana mana shi.
Su ka amsa da ''To, Amin"
Duk suna zaune a Falo su na Hira, jefi-jefi Shahbeer ya ke saka Baki, Alhaji Boza ne ya yi Sallama. Inna ta Amsa tare da yi masa maraba shigo.
da kyar da kyar ya ke iya takawa domin kuwa ji ya ke ƙafafunsa su na neman gaza ɗaukarsa.
tin kafin ya zauna duk su ka tashi da nufin barin gurin, ya dakatar da su da cewa "Shahbeer ina son yin magana da ku ne.
"Da mu dai?"
Ya ce "Hajiya A'i ki temaka mini ki sa baki su tsaya su saureni."
Mommy ta ce "Shahbeer, ya kamata ku tsaya ku saurari Mahaifinku."
"Mama wallahi har cikin raina ba na jin daɗi in ki ka ce Mahaifinmu, Babu batu na gaskiya da tsoron Allah a kan harshensa, ko me zai faɗa mana Gaibu ne kawai"
Shahbeer ne ya yi maganar cikin tsananin damuwa, raunin sa ya gama baiyana akan fuskarsa, hakan ya ƙara taɓa Zuciyar Alhaji Boza sosai, tabbas rashin Imani da Tsoron Allah babban Ƙalu-bale ne ga me su, ya bi Duniya ya zaɓeta akan Lahira gashi yanzu Ta yi masa Juyin-Juya Hali.
Ya na hawaye ya ce "Tabbas Ku ƴaƴana ne, amma ban cancanta ku kira ni da Baba ba, amma Don Allah Don sonku da Annabi Muhammad, Sallallahu'alaihi'wasallam, ku yi haƙuri ku yafe mini ku jiƙaina sannan ku saurareni Ƴaƴana, haƙiƙa ba ni da kamarku duk Duniyar nan, Tsakanina Ga Allah na ke faɗa ba son Zuciya bane ko Ƙarya, wallahi tallahi ku ne sittira ta duk abin da na ke dashi Dukiya ko Wani abu duk na banza ne, ku kaɗai ne ƙashin bayana, ku ne abu mafi muhimmanci da daraja a gareni Allah ya mallaka mini."
Girgiza kai Shahbeer ya yi ya ce "Duk sai yanzu ka san da haka? sai wani abin ya taso maka sannan za ka neme mu?"
"A'a ba haka bane, dan dai kun ce in ƙyaleku ne amma da ba abin da zai sa na barku a wannan ƙadamin, amma yanzu dole ta sa na ƙara dawowa don na kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali, burina in sanar da ku halin da na ke ciki ni da ɗan-uwanku Sa'ad, ni tawa ta ƙare , ko da rai ya yi halinsa Don Allah kar ku guji wannan yaron, Ya na sonku tsakani ga Allah sannan ya na da kyakkyawar Zuciya bai yi irin halayenmu ni da Mahaifiyarsa ba, sau da yawa yakan zaɓeku akanmu, lokacin da ya ke gaya mana gaskiya gani mu ke kamar maƙiyinmu ne amma yanzu na gane Gaskiyar kuma na yi riƙo da ita daga nan har na koma ga Allah, Yanzu ya na cikin wani hali na rayuwa ko Mutuwa sabi da zazzaɓi ya hana shi zaman lafiya kuma zazzaɓin ya samo asali ne daga kusa-kuraina, Su ne su ke bibiyarsa, Nima yanzu gashi na kamu da ciwon Zuciya Ban sani ba ko zan ga gobe ko zan ƙara ganin wata shekarar, ni dai fatana ko da na Mutu ku riƙi Sa'ad Amana kamar yadda ya ke sonku tsakaninsa da mahaliccinsa shi ma ku so shi Ba dan ni ba Don Allah."
Jikinsu ya yi matuƙar sanyi musamman Shahbeer da ya ji halin da Sa'ad ya ke ciki, haka kawai ya ke ƙaunar Sa'ad sosai abin da ya ke hana su saureren shi tsoron gamaiya da Halin Baban nasu da yaudararsa sun san zai iya turo wani cikinsu sannan ya illata su.
Shiru ne ya biyo baya har na wani lokaci sannan Shahbeer ya ce "Allah ya bashi lafiya."
Daga haka ya juya da nufin wacewa sashinsu Mommy ta tsayar dashi da cewa "Malika ba ta da Lafiya, ka je ka duba ta."
karyar da kai ya yi kamar zai yi kuka ya ce "Mama ba..." saurin ɗaga masa hannu ta yi Dole ya yi shiru ya nufi ɓangaren nata.
A hanya ya ci karo da ita ta na ƙoƙarin komawa cikin ɗaki.
"Ya jikin?"
ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.
Murmushin takaici ta yi tare da cewa "Na ji sauƙi tinda gani na fito da Falo zan je sai kuma na ji Kuna magana da Baba, Ina maka tsoron ka ƙara wani kuskuren Ya Shahbeer ya kamata ku fuskanci Mahaifinku, wannan ƙazamar ƙiyayyar Allah ya hanemu da ita a matsayinmu na Musulmai, Domin rayuwa ta yi kyau ana buƙatar Farantawa iyaye, duk da bansan me ya yi muku ba amma abin ya yi tsauri da yawa, idan mutum ya tuba har ya nemi yafiya yafe masa ko da ba da gaske ya ke ba sai ka barshi da halinshi kai kuma Allah zai kareka daga kaidinsa, Don Allah Ya Shahbeer."
Hawayen da ya ke ta dannewa ne su ka samu damar silalowa, "Malika Da na ƙi Mahaifina amma yanzu Ina son shi sai dai ina tsoron munanan halayensa, muna tsoron mu yarda dashi mu ja shi a jiki ya ƙara cutar damu, a sanin da na yi masa DA baya abin sa don Allah sai don WATA MANUFA, da yawan wasu kuskuren ba namu bane na Mahaifinmu ne ya ke ta bibiyar rayuwarmu, Sa'ad ya faɗa mawuyacin hali sabi da shi, rayuwarmu ta canja sabi da shi, tin daga kan wanzuwar Shahzad a Duniya har wasu ƙananun abubuwa duk laifin ba namu bane na shi ne, Ba mu yi Sa'ar Uba ba sam."
ya ƙarasa maganar ya na kuka har da shashsheka..
Za ta iya cewa tin da ta zo Duniya ba ta taɓa ganin hawayensa ba bare kuka kashirɓan, jikinta ya yi matuƙar sanyi, da kyar ta yi ta maza ta riƙo hannunsa ta ce "Mu je ka zauna ka huta, ya kamata ka dinga samun nutsuwa."
bai ce komai ba ya bi ta ta ja shi ɗakin a bakin gado ta zaunar dashi sannan ta ɗakko masa gorar ruwan sanyi ta miƙo masa tare da cewa "Ka sha Ruwa za ka ji sanyi-sanyi."
Karɓa ya yi gami da cewa "Na gode Malika."
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[1/1, 10:05 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
29
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Shiru ne ya biyo baya kafin Malika ta katse shirun da cewa "Na ji Ɗazu ka yi Magana akan Shahzad, meye kuskuren Baba a ciki kuma?, Koda yaushe gaskiyar lamarin ta na yi mana Jirwaye ne mun kasa gane a inda take."
Nazari ya ɗan yi kafin ya ce "Ki bar labarin kawai, ba za ki gane ba."
"Ta yaya zan gane bayan ba ka ganar da ni ba?"
"Ko da na ganar da ke mawuyaci ne ki fahimta; duk abin da Zuciyarki ta raya miki akaina da kuma wanda ki ka yarda dashi kawai ki Ɗauka hakanne gaskiyar.
ya na kaiwa nan ya miƙe ya nufi hanyar fita ya na cewa "Ki maida hankali wajen shan magani, Allah i yaye."
da "Amin" ta amsa tare da bin bayansa da Kallo.
Haka rayuwa ta ci gaba da Tafiya rayuwa ta na garawa Duniya ta na juyawa yanayi ya na canjawa.
Sa'ad ya samu sauƙi sai dai ba a ce ya warke ba, Zazzaɓin yakan zo a lokacin da ya so kuma ya tafi a lokacin da ya so. Addu'a itace ta samar masa da sauƙin da ya samu.
Mom Safyan da Safyan , ta Dukiyar Alhaji Boza su ke yi duk sun karɓe komai daga gareshi, kama daga kan kasuwancinsa har abin da ya mallaka a Cewar Mom Safyan shi ya gaza kuma rayuwa sai da kuɗi don haka dole su tattala kuma su tsaya su nema.
Shahmeer Bayan Tafiyar Lokaci damuwarsa ta kau ya dawo kamar yadda yake Da tini ya manta da anyi zamanin, Yanzu tsinkar furensu kawai su ke yi Shi da Inna.
Shahzain ba abin da ya canja a nashi ɓangaren sai ƙarin Matsaltsalu musamman daga ɓangaren Maalik.
Shahbeer Duk fushin da ya ke ya sakko sabi da ganin ɗan-uwansa ya dawo sak, sai dai abubuwa da dama su na damunshi, su ke jaza masa tunane-tunane da ƴan zazzaɓe-zazzaɓe, Kullum Mommy da Inna har ma da Baban Halima cikin nasiha su ke akan Tsakanunsu da Malika, yadda ya ke nuna Mata halin ko in kula ya na matuƙar damunsu, da rarrashi da Nasihu su ka samu komai ya dai-daita.
a Ɓangaren Malika kuwa lokacin wuya ya wuce sai daɗi, ada ta sha wahala kafin Allah ya dai-daita tsakaninta da shi, yanzu kam daidai gwargwado yakan bata kulawa amma duk da haka mafi yawancin lokacinsa ya na ga Shahzad da Halima, ya fi basu lokacinsa fiye da kowa.
Shahzaib da Ma'arufa ba abin da ya ke damunsu sai ciwon So, kullu-yaumin cikin Soyayya su ke Kamar Tantabaru.
Shahzad ya girma ya yi Wayo da ya ke me azanci ne sosai, Shekararsa Biyu amma kamar ya fi haka sabi da wayonsa da Surutu ga Dubara kamar ba Yaro ba.
Shahbeer ne zaune ya na danne-danne a Laptop duk ya gama maida hankalinsa akan binciken da ya ke yi. Sautin Muryar Shahzad ce ta dawo dashi nutsuwarsa, "Baba!! Baba!!! Baba!!!"
Shahbeer ya ce "Na'am meke faruwa?"
Dariya ya yi tare da cewa "Zo"
Shima Shahbeer ya yi Dariya tare da cewa "Ai har yanzu ban ganka ba, ka na ina?"
"Gani!"
miƙewa Shahbeer ya yi ya na dube-dube don ganin ta inda ya ɓullo, Motsinsa ya gani a bayan labule hakan ya tabbatar masa a can ya laɓe, ya yi Murmushi tare da cewa "Ai kuwa na ji Kamar su Baba Auta za su je unguwa anya ba su shirya ba?"
Da sauri ya fito ya na ƙyalƙyala Dariya tare da cewa "Iya bayan labule Baba."
Shahbeer ya yi dariya tare da buɗa masa hannu alamar ya tawo, ya lumshe ido gami da cewa "Na ganshi ai shi yasa na yi masa wayo."
Da gudu ya tawo ya ɗafe jikin Shahbeer ya na dariya Ɗaga shi ya yi zuwa kan kafaɗarsa ya nufi Falon su Shahmeer.
Shiru Falon ba abin da ake ji sai ƙarar TV duk sun yi fakare su na Kallon Ball ta gama ɗaukar musu daɗi.
a tsakiyarsu ya dire Shahzad ya ce "Ga shi nan ya taya ku hira, ina aiki ya je zai dameni gwara ku aikin banza ku ke."
Ko tari Shahzaib bai yi ba Shahmeer kuwa gyara zama ya yi tare da cewa "bari sai angama Wasa."
Shahzain ya yi dariya tare da cewa "Miƙo shi nan, amma sai na ɗaure masa baki tukunna za mu daidaita don surutunsa ma kaɗai ya isa yasa a cimu Wasa."
Sai lokacin Shahzaib ya ce ''Gashi Arufa ba ta nan, amma Kai shi gurin Mommy ko Inna wallahi yanzu sai ya ƙara mana zafi Nasan ma Dariya zai yi mana idan aka tashi muna ciki."
Shahbeer ya ce "Gwara da Allah bai ɗora mini jarabar Sports ɗinnan ba, da yanzu nima ina nan ana nuna mini fari ina a'a baƙi ne duk sabi da kun Bada hankali akan TV, ba za ku gaji da Hawan jini ba kuwa."
Shahzaib ya ce "Kai dai ja Ƴar-bainunka ku yi gaba."
hanyar fita ya yi ya na cewa "To ya na iya tinda kun ƙi karɓa."
Mutsu-mutsu Shahzad ya fara yi ya na cewa "Baba aje shi."
''To in na aje shi ina zai je?"
"Momyy"
"Oh, to bari in kai shi da kaina.
sauya tafiyar ya yi zuwa ɓangaren Mommy, ta na murmushi ta ce "Wato bai yi bacci ba."
"Matarsa ba ta yi ba ina shi ina yi, ni kam aiki nake gashi nan ya tayaki kwana"
Ta ce "To amma fa in ya mini ɓarna sakin da ba sasanci zan yi masa.
Shahbeer ya ce "Ba zai yi ba in sha Allah, ko Shahzad?"
bai yi magana ba sai murmushi kawai ya ke zubawa.
Shahbeer ya dire shi sannan ya yi musu sallama ya koma ɓangarensu.
Maalik ne zaune kusa da Hajiya Dada Ya yi kicin kicin da rai.
Hajiya Dada ta taɓe baki kafin ta ce "Ba komai Maalik, ba dai ni na haifeka ba? kuma YaYa nake a gurin Ibrahim? to kamar na Aura maka Shukriya ne, sai yanzu na yi dana-sanin Amincewa da yaudarar yaron nan a matsayin Gasar gwajin Gwani, ashe ya karkatar mini da hankali ne ban sani ba sai yanzu na fahimta, gashi anyi shekara biyu ana ta ja-in-ja to zan kawo ƙarshen lamarin, da ƙarfina zan Aura maka ita tinda Ibrahim Son Ƴarsa ya rufe masa ido nima ina son nawa, yau ɗinnan zan kira shi ya zo mu tsaida Rana."
Naseera da ke gefensu ta ce "Gaskiya Ammi ba'a Auren Dole a zamanin nan, ku bar Aunty Shukriya ta zaɓi wanda ranta ya so tin da ba ku ne za ku zauna da shi ba."
Dada ta jinjina kai ta riƙe haɓa gami da cewa "Iyee??!!! lallai Naseera kin isa, wato kece ma za ki gaya mana abin da ya kamata mu yi ko??, to ki rufe mini baki, kar ki ƙara shiga zancen nan tin da dai kema ba kya son ɗan-uwanki, in banda ƙuruciya har kin fi son ita ta samu abin da ta ke so Ɗan-uwanki kuma ya rasa??"
Naseera ta ce "A'a Ammi wallahi ba in nufin haka ba, idan ki ka ce ba na son YaYana gaskiya kin mini wata fahimtar daban, Amma tinda itama Ƴarki ce ai ya kamata ku yi mata Adalci, kuma YaYar ta ma fa kece ki ka yi mata Auren haɗi don Allah ita ki barta ta Auri wanda ta ke so, in ya so Shi Ya Maalik ki Aura masa Abida ai itama ta girma ta isa Auren."
Dada ta yi salati ta sanar da Ubangiji kafin ta ce "Maalik ka na jinta ko??"
Maalik ya gyara zama kafin ya ce "Ƙyaleta Ammi, ƙuruciya ce ta ke Damunta, Idan An Ɗaura Auren tasa na saketa tinda itace Uwata, tsagerar banza kin zo ki na shiga maganar Manyanki.''
Nasira ta ce "Ba maganar girma ai wannan ta shafi kowa ba iya ku kaɗai ba."
Dada ta ce "Wallahi Zan sa Maalik ya yi miki duka in ba ki rufe mini baki ba, ki ma tashi ki ba mu guri, tashi maza."
Miƙewa ta yi gami da cewa "Allah ya zaɓa mafi Alkairi amma a ganina tilastawa ƴar mutane b shine ado ba."
Maalik ya ce "Je ki dai, mun ji ba ma buƙatar ƙara ji."
ba ta ce komai ba ta yi tafiyarta.
Dada ta ci gaba da tsarawa Maalik yadda komai zai kasance da yadda za'ayi biki.
Shahbeer, Shahmeer, Shahzaib, Shahzain,
Suna zaune tare da Baban Halima ya na basu labarai na Rayuwa.
Shiru Shahbeer ya yi ya na tunani, ya gama yin nisa a ciki, har Baban Halima ya lura baya cikin Nutsuwarsa, cikin Kamala ya tambaye shi abin da ke damunshi, ya ɗan numfasa kafin ya ce "Baba Tunanin Halima na ke yi."
cike da mamaki Baban Halima ya ce "Mukthar Halima dai tawa??"
ya ce "Eh ita."
"To ta Mutu ne Mukhtari?"
girgiza kai ya yi tare da cewa "Ta na raye Baba."
zai ci gaba da magana Shahzaib ya kwaɓe shi da cewa "Shahbeer mene haka? kar fa...."
dakatar da shi ya yi da cewa "Haƙuri za ka yi Shahzaib dole in faɗa masa gaskiya. ci gaba ya yi da cewa "Baba don Allah ka yafe mini a bisa ɓoye maka gaskiya da nayi, Halima ta na gidanmu ta na tare da mu, abin da ya sa na kasa dawo maka da ita sabi da halin da ta tsinci kanta a ciki, na yi tunanin kafin yanzu za ta dawo haiyacinta ashe ba haka bane, gashi an shekara an kuma ba ta dawo daidai ba, ta riga ta manta rayuwarta ta baya Mu kawai ta sani sabi da mu ta fara gani bayan ta dawo wannan sabuwar rayuwar, bayaan hakan kuma Anyi mata Fyaɗe yanzu haka ɗanta ya nan ya girma Sunansa Shahzad, Baba Shi ɗin Ɗana ne"
Shiru ne ya biyo bayan magamar tashi dukansu jikinsu ya yi bala'in sanyi, yadda Shahbeer ya ke magana ma kaɗai ya isa tsinkawa duk wani mutum me tausayi Zuciya, Sai da aka ɗan ɗebi lokaci sannan Baban Halima ya samu damar fara Kuka.
Shahbeer ya zame daga kan Sofa ya dire guiwoyinsa a ƙasa, cikin rawar murya ya ce "Baba na shiga haƙƙinku na zalumce ku, ku yafe mini ku yi mini Afwa, idan har ba za ku iya yafe mini ba Baba a shirye nake da na karɓi kowane hukunci ku ka yanke mini, Nima Mutum ne kamar kowa Baba za ka iya hukuntani."
Share Ƙwalla Baban Halima ya fara yi kafin ya ce "Haƙiƙa Ɗan nan kowane ɗan Adam da irin tashi Ƙaddarar, Da ka dawo mini da Halimata tin lokacin da haka ta faru da zan karɓeta a yadda ta ke ko da kuwa ta fi haka muni, Ba zan iya juya mata baya ba don wata ƙaddara ta sameta, haka-zalika kai ma, ina Me jan kunnenka akan kar ka Ƙara aikata zunubi ko kaɗan bare irin wannan, ka tubarwa Allah ka ci gaba da neman yafiyarsa shi Allah me karɓar tuba ne, ya na tausayawa duk wanda ya yi Imani, ni kam na yafe maka Mukhtari, ka dawo mini da Halima in ganta."
Cikin shashshekar Kuka Shahbeer ya ce "Ina matuƙar Son Halima Baba ina tsoron duk abin da zai rabani da ita, hakan ne ya sa kullum na kasa gaya maka har tsawon wannan lokacin, gashi nasan ba za ta ganeka ba hakan zai ƙara tada hankalinka."
Baban Halima ya jinjina kai kafin ya ce "Ina Abin wuyanta?"
Nazari ya ɗan yi, sai a lokacin ya tuna da wani Zobe guda biyu da ya samu a tare da ita kuma suna nan ya na ta ajiyarsu har da canja musu chain. "Ya na nan na Ajiye"
ya bashi amsa cike da ƙaguwa da son jin abin da zai ƙara faɗe.
Baban Halima ya ce "A ɗakko su a maida mata a wuyanta in Allah ya yarda za ta tuna da komai, ko ba ta tuna duka ba za ta tuna da Babanta, Da ka sanar dani tin-tuni da na faɗa maka haka, Allah ya ƙara tsarkake zukatanmu Mukhtar, Ka ci gaba da neman Yafiyar Allah, tabbas na ji ba daɗi amma ba yadda zan yi da Ƙaddara, mutum ba ya iya sauya tashi bare ta wani."
Shahbeer ya ce "Ina Ƙara bada
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 30