kafin na tafi ina so ki yi min Alƙawarin ba za ki ƙara ɗaukar abin da ba naki ba.
ƙasa ta yi da kai wasu sababbbin hawayen suka fara sintiri akan fuskarta, cikin sanyin muryarta ta ce ''Ba zan kuma ba na dena, na yi maka Alƙawari amma don Allah ka barni na tafi gidanmu kar ka rabani da su, ba su da kowa sai ni kaɗai ni ce na ke temaka musu ta kowane ɓangare, don Allah ka barni in tafi."
"Za ki tafi amma ba yanzu ba, ke dai ki yi baccinki kuma na gode da Alƙawarin da ki ka yi mini, Allah ya baki ikon cikawa.
ya na kaiwa nan ya fice daga ɗakin.
Washe-gari
cikin Sauri-sauri DR Idris ya fito da shirinsa na zuwa Asibiti, miƙewa Momy ta yi gami da cewa "Ina son yin magana da kai Dr."
"Okay, faɗi.
"Ka na tsaye ina tsaye ai ba za mu fahimci juna ba.
ba tare da ya ce komai ba ya zauna ya na sauraron abin da za ta ce.
"Ka nemawa Ƴarka Farin cikinta tin kafin ciwon damuwa ya kasheta, Ta na Son Shahbeer ta ƙi saurarar kowa sabi da shi amma a banza, na tabbatar ya san ta na son shi amma ko Alama bai nuna mata ba yi ya ke tamkar baisan ta na yi ba, to maganar gaskiya ka yi musu Halacci a rayuwa yanzu karo na farko ka nemi wannan alfarmar a gurinsu na san ba za su ƙi yi maka ba.
"Me ki ke so na yi kenan? kin san dai ba zan amince da yi masa abin da ba ya so ba.
"Na san hakan, amma ka jaraba neman Alfarmarsu idan ba haka ba ƴarka za ta lalace a tsaye yanzun ma ta zama kamar ba ita ba, ka duba ka ga yadda ya ke bala'in ƙaunar Ɗan da Halimatu ta haifa amma ya kasa nunawa wadda ta ke son shi ƙauna, gaskiya ba zan iya jura ba idan ba za ka iya ba ni zan yi masa maganar da kaina don ina son ƴata nima kuma ina son farin cikinta, indai ba son kai da son Zuciya a tattare da su ba za su ƙi amincewa ba.
Jinjina kai Dr ya yi gami da cewa "Na ji zan yi maganar da Hajiya A'i.
"To ai hakan ya fi, gwara a san matakin ɗauka.
da haka suka bar maganar.
Tin da ta tashi daga bacci ta shiga banɗaki ta fito ta zauna a can ƙuryar gado ta haɗe kai da guiwa sai tunani ta ke yi, abin da ya faru jiya ne ya ke mata yawo a cikin tunaninta yanzu dai ta gane gaske ne ba mafarki ba, tsoro gami da nadamar satar ta-ta sun gama lulliɓeta.
Inna ce ta yi sallama ta ci gaba da cewa "Ke da ki ka tashi sai ki zauna ba za ki fita ba?, Nan fa Gidanku ne gwara ma ki saki jikinki, Yanzu ma ki je Mommy da Shahbeer su na nemanki."
Rasss gabanta ya yanke ya faɗi, wani sabon tsoron ne ya ƙara yanko mata dandanan jikinta ya fara ɗaukar zafi..........
(Saura ku Raina ku ce ba yawa🙄 )
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/26, 8:36 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
23
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Inna ta rausayar da kai Gami da Cewa "Allah Sarki, Allah ya kare ki da sharrin Son Zuciya ƴarnan, don in ki ka saba da shi har Abada da haka za ki ɗore, kin yi kuskuren fara tunanin nemawa kai mafita ta hanyar Sata, Sata Haramunce ba kyau, Allah ba ya son mai sata Amma ke kin zaɓawa kanki ita, ba ki san Hukuncin da Allah ya ce a yiwa duk wanda ya ɗauki abin wani ba?, ki na da ilmi fa na san kin san ba kyau kawai sharrin Zuciya ne, to ki ta tuba ki na neman yafiyar Allah da neman tsari da aikata Sata kin ji Jikata, ki kwantar da hankalinki karin kumallo za ki yi ba laifi ki ka yi ba, sarƙar ma tini an dawo da ita."
Gyaɗa kai ta yi kafin ta lallaɓo ta sauko daga kan gadon jiki a saɓule ta bi bayan Inna su ka nufi Falo.
ya na zaune sai haɗe rai ya ke yi ya na muimui da baki, Shahbeer kuwa ya yi masa banza kamar bai ganshi Ba shi kuwa shariyar da ya ke masa ɗin ƙara ƙona masa rai ta ke yi, amma ya fi ganin laifin Ma'arufa akan kowa.
ko da su ka ƙaraso bai ɗaga ido ya kalli inda su ke ba daga ita har Innan.
Shahbeer ne ya ce "Wasan Ɓuya kuma za mu koma yi Arufa?"
ƙara lakurewa ta yi a bayan Inna cike da kunya.
Inna ta zame gami da cewa "Ai kunya ba ta kama ki ba tin da zaman cikinmu ya Aureki.
"Zo ki zauna kusa da ni Ƴata"
Mommy ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi.
Inna ta ce ''To ƙetara Ni dai ina daga nan kusa da Babyna."
Shahmeer ya murmusa kafin ya ce "Dama Ina nan ai kina kusa da ni, in an ganni za'a ganki kinsan tif da taya ne mu."
Shahzain ya yi dariya gami da cewa "Ah rai da Rayuwa ku ke ba Tif da Taya ba."
Cikin sanyinta ta ƙarasa kusa da Mommy kanta a ƙasa sim-sim, gaba ɗaya ji take ta tsani kanta haushin kanta ta ke ji sosai kamar ta mutu dan baƙin ciki, yau kam Allah ya nuna mata ranar jin Kunya ƙiri-ƙiri.
hannunta Mommy ta riƙo gami da cewa "Zauna kin ji, komai ya wuce Allah i kyauta gaba, na san ma ba zai ƙara faruwa ba in sha Allah."
kusa da ƙafafun Mommyn ta durƙusa gami da gaisheta, ta amsa cikin sakin fuska gami da tambayarta ya ta kwana.
Hawaye ne su ka fara wasan tsere akan fuskarta cikin rawar Murya ta ce "Don Allah ki yi haƙuri ba zan ƙara ba."
kafin Mommy ta ce komai Shahzaib da baƙin ciki ya ke neman kaiwa Barzahu ya ce "Ki ka ƙara ba mutane haƙuri sai na targaɗa ki, Tsabagen iskanci idan an tambaye ki damuwarki ki ƙi faɗe amma kin zo ki na ɗauke-ɗauke sannan ki zo ki na wani bawa mutane haƙuri, sa'a ki ka ci ban zubar miki da haƙora ba da sai ki bada haƙurin da Hujja."
Inna ta ce "O'o Ni Hadiza Ka fiye masifa Ƙarami, Budurwar taka ma sai ka yi mata?"
"To in ban yi mata ba a matsayina na Mijinta waye zai yi mata?, ko so ki ke na bari Duniya ta koyar da ita?"
Shahbeer ya ce "Wai mu za ka zauna yiwa tijara anan, ka fi kowa Zuciya ne?? ka sake na ƙara jin bakinka sai na kikkifa maka tafi, Ai na gaya maka laifinka ne ba na wani ba."
Dogon tsaki ya buga gami da miƙewa ya sa ƙafa ya yi fatali daTray ɗin kofina da ke gefensa, fuuuu ya nufi sashin su kamar me shirin yin dambe da iska.
Ido Shahbeer ya zuba masa dandanan hannunsa ya hau kakkarwa idanunsa su ka fara canja kala.
ganin haka ya sa Mommy ta yi saurin cewa "A'a Inya, ka yi haƙuri Don Allah."
"Dan bashi da kunya har ni zan yi masa magana ya yi min tsaki??, Wai kenan ba za'a yi masa faɗa ko a faɗa masa gaskiya ba??, ko ya fi ni Zuciyar ne ya ke ganin? ba na son Bugajin banza da wofi shi da bai san bin abu ta maslaha ba."
Mommy ta ce "Ka yi haƙuri dai na ce maka, ka san abin da ciwo ne, ko kaine ace matarka ta na haka ai ba za ka ji daɗi ba, dole abin zai yi masa zafi bare kuma ka na ta share shi ai dole hankalinsa ya gaza ɗauka."
Inna ta ce "Gaskiya ne kuwa ka yi haƙuri ai manya ba sa fushi, Allah zai gyara mana ka ji?"
banza ya yi da al'amarin.
Ma'arufa kuwa ta na gefen Mommy ta haɗe kai da guiwa ta na kuka, tin da ta ke a gidan ba ta taɓa jin saɓani ko da makaman-cin haka a tsakaninsu ba sai ta sanadinta.
da kyar Mommy ta lallaɓata ta yi karin Kumallon sannan ta yi mata nasihu sosai kuma ta ce mata ta je ta bashi haƙuri.
Shukriya ce zaune ta yi tagumi ta lula Duniyar tunani, wayarta ce ta yi ƙara alamar shigowar Saƙo, kamar ba za ta duba ba sai kuma ta duba, ga mamakinta sai ta ga baƙuwar lamba "Yau za ki yi baƙo" haka kawai aka rubuta, ta maimaita ya kai sau biyar kafin ta maida martani "Waye?"
"Mu haɗu a gidan su Fatima Aminiyarki, Idon ki zai gane miki ko waye, Misalin Ƙarfe 04:15 ba daɗi ba ragi za ki ga na zo in Allah ya yarda."
"Ina jin Tsoro gaskiya, ka faɗa min kowaye ko kuma na sanarwa ƴan sanda.
Alamar Dariya ya saka tare da, "Ba buƙatar Hukuma a tsakaninmu, ki yarda da Allah kawai ba abin da zai same ki domin ni ma me baki Kariya ne, Tamkar Inuwa haka na ke son zamtowa a gareki.
Kafin ta maida martani kira ya shigo wayar, da sauri ta ɗaga ganin lambar Fatima, "Ke Aminiya ashe-ashe ban sani ba??, me ya kamata mu tanadarwa baƙon namu ne?"
a ɗan tsorace ta ce "Baƙo kuma Fatima anya ba ki fara cin kai ba."
"A'a yayan cin kan na yi, ki ji min rashin mutunci, ke fa dama wallahi shirginki ya fi ƙarfinki, in banda rashin mutunci ki turo min Text ɗin za ki yi baƙo a gidanmu ɗin sannan ki ce min ba ki sani ba, yanzu fa ba shirin Bandariya mu ke yi a Radio ba ki dawo haiyacinki."
zuwa yanzu Lamarin ya gama ɗaure mata kai, Idan ta fahimta daidai wanda ya gaya mata za ta yi baƙo shi ne ya gayawa Fatima haka.
"Kin yi shiru ko dai kin fara kwancewa ne?"
numfashi ta ja kafin ta ce "Zan zo, Amma ba sai na zaɓi abin da za ki yi masa ba komai ma ki ka yi daidai ne.
"To shi kenan amma ya naga kamar bakya farin ciki?"
Dariyar yaƙe ta yi gami da cewa "Ina farin ciki, to ai ban san kowaye baƙon bane shi yasa, gashi ba na jin daɗi yau.
"Ohh aikuwa faka za ki yi ki tashi tsaye mu fitar kunyar baƙonmu.
"Ke can da yawarki.
Shukriya ta faɗa gami da katse kiran.
tunani ta tafi yi, Waye wannan?? shi kuma me ya ke so a gurina? meye haɗina dashi? me zai ce min? ko Safyan ne??
ko kuma Maalik?? Ko dai Abbana ne ya haɗa ni da wani daban?.
haka ta yi ta tufka da warwara, Mami ce tsaye akanta ta na ta yi mata magana amma shiru har sai da ta gaji ta ɗaka mata duka, ta yi firgifit gami da cewa "Waye kai???"
Mami ta ce "Oh Allah sarkin Baiwa Zaman banza ma bai yi ba, ƴar-kan-uba kin sa an rabaki da aikinki kin zo sai damuwa ki ke yi, kin sani yanayinki na nishaɗi ne irin zaman nan zai iya illata ki amma ki ka rintse ido ki ka tafka kwakyara, da tuni ki na gurin aikinki amma yanzi ga ki a gida, tunanin ma me ki ke yi?? har da firgita kuma waye ma ki ke tambayata?"
Ɗan sosa ƙeya ta yi gami da cewa "Amm... kin san tunani ma fitar da mutum ya ke daga haiyacinsa; yauwa wai Maalik ya dawo ne?"
Mami ta ce "A'a amma dai ya kusa."
To kenan ba Maalik ɗin bane? ta tambayi kanta, "Yauwa Mami zan je gidansu Fatima yau.
"Allah ya tsare ki ce ina gaida Maman taku, amma ba na son sakarci da rawar kan nan naki, ki dinga nutsuwa idan kin fita.
"To Mami Na gode.
ta faɗa cikin fara'a.
3Seater 2seater 1seater ne kaɗai a ɗan madaidaicin ɗakin sai sauran kayan ƙayatarwa na ado da aka yi.
kanta na ƙasa ta yi sallama a ɗakin, ya na daga can kan 3seater a kwance ya na Kallo, ganin ba shi da niyar amsawa ya sa ta ƙara matsawa sannan ta ce "Ance ka yi haƙuri."
Ɗago kai ya yi ya ƙare mata kallo sannan ya maida kansa ya ci gaba da abin da ya ke yi.
ci gaba ta yi da kuka dama ba wai dan ta gaji bane ko ta gama ya sa ta yi shiru dan dai Mommy ta ce ta yin ne, ita kuwa a Duniya irin banzatarwar da ya ke mata ta na mugun ƙuntata mata.
a ƙufule ya ce "Wai ke bakya rabo da kuka ne sai ka ce wara tinkiya?, kuma ba na ce kar ki ƙara bari na ji haƙurin nan a bakinki ba?"
cikin shashsheka ta ce "Ai Mommy ce ta ce in ce haka."
Ta so bashi dariya amma sai ya fuske ya ƙara sautin TV dan karma ya dinga jin sautin kukan nata.
tsaiwa ta ci gaba da yi har sai da tafara gajiya ta ga ba zai kulata ba ta ƙarasa kusa da kujerar da ya ke kai ta durƙusa, ta ɗan ɗaga murya daidai yadda ta san zai ji ta, ta ce "Don Allah ka yafe min ba zan ƙara ba na tuba wallahi."
lumsassun idanunsa ya buɗe ya juye su akanta, ido cikin ido su ka yi kafin ta yi saurin yin ƙasa da nata.
ya ɗan murmusa gami da cewa "Ba ni da damuwa da hakan don ni ba me amfani bane bai kamata a ban haƙuri ko a nemi yafiyata ba tinda bakya Sona Arufa."
da sauri ta wararo masa idanu gami da cewa "A'a.
"Ya a'a??a zahirance kin nuna ba kya ƙaunata sam, ni ma na san ba lallai ki so ni ba don ban cancanta ba.
girgiza kai ta yi gami da cewa "A'a Ina Sonk..."
kasa ƙarasawa ta yi Da ta tuna da wa ta ke tare da kuma irin katoɓarar da ta ke neman yi, gashi ya kafeta da na Mujiya.
Wani Lallausan murmushi ya yi gami da cewa "Da gaske? wai ki na sona?, shi kenan nima na zama Autan Maza?"
sakin baki ta yi sototo kamar wata sabuwar sokuwa ga ƴan guntayen hawayenta a fuska.
"Ki gazgata min Yadda ko Duniya zan iya tinkara in faɗa musu na fi kowane namiji Sa'ar Mata, da gaske kema ki na sona ko dai tilastawa Zuciyarki za ki yi?"
girgiza kai ta yi kanta a ƙasa murya can ƙasa ta ce "Na fi tunaninka fiye da kowa.
zumbur ya tashi zaune ya ƙara sassauta murya "Kenan dai da gaske ni ɗan Sa'a ne, Matata ta gaya mini ta na sona, bari in hanzarta in gayawa Boss"
da sauri ta miƙe ta nufi hanyar fita ta na cewa "Don Allah ka rufan asiri da wasa nake."
ya murmusa sannan ya koma ya kwanta ya ci gaba da tunaninta ya na murmushi.
Ba ita kaɗai ba ita kanta Fatima ta ƙagara ta ga baƙon nasu, sun kasa zaman kirki sai kaiwa da komowa su ke yi akai-akai su ke duba waya ko za su ga saƙon shi ya shigo.
04:15pm ya turo cewar ya zo.
Fatima ta ce Shukriya ta fara fita Shukriya ta ce Fatima ta fara fita, haka su kai ta turereniya har sai da Umman su Fatima ta gaji ta ce su je su duka.
da wata haɗaɗɗiyar Baƙar Mota su ka yi tozali a ƙofar gida Shukriya ta yi saurin komawa ta laɓe ta na cewa "Ke Fatima mu rufawa kanmu Asiri mu koma gida kar a sace mu a banza, ga wata mota kamar ba ta mutum Ba ko hanyar da za'a sha iska inaga babu baƙiƙirin da ita"
Fatima ta na shirin yin baya ta ga ya fito daga motar, cikin Baƙaƙen kaya ƙananu rigar me ɗan ƙaramin hannu sai wandon jeans, P-Cap da kuma rufaffiyar fuska da baƙin hankicif da baƙin gilashi.
"Na shiga uku na watse, Shukriya leƙo ki gani"
Fatima ta faɗa cikin kaɗuwa.
Shukriya ta leƙa jikinta na kakkarwa maƙurar tsorata ta gama tsoracewa, ganin ya yo kansu gadan-gadan ya sa ta cewa "Wayyo Allah Gamu gareka mun janyo ɗan Boko haram gidanmu."
ta kasa guduwa ko motsawa ta kasa yi kuma ta kasa janye idanunta daga kanshi.
da Fatima ta lura Shukriya ta fara Firewa sai ta shiga gaba-gaba dan kuwa ta fi ta Jarumta.
sai da ta kusa suma jin sallamarsa a kusa da ita, ta ja wani sarƙaƙƙen dogon numfashi.
Fatima ta haɗiye yawun da ya yi mata ƙullutu a maƙoshi cikin ƙarfin hali ta ce "Wa'alaikassalam, Waye kai??"
Ɗaga mata hannu ya yi gami da keɓeta ya wuce gaban Shukriya.
diff..diff..difff... Zuciyarta ke bugawa, cikin rawar baki ta ce "Waye kai?? don Allah kar ka cutar dani ban yi maka laifin komai ba."
"Ba na fatan ki yi mini laifi har bayan raina, magana ɗaya ce ta kawoni gareki.
ya ƙarasa maganar gami da cire glass da hankicif ɗin, nan take farar fuskarsa ta baiyana, ya kasheta da Kaifafan idanunsa. "INA SONKI Shukriyata, itace kawai maganar da zan faɗa miki ina fatan kema za ki So ni ko da kwantan-kwacin yadda na ke sonki ne.
Maganar ta zo mata a bazata matuƙa, lokaci guda wani sassanyan farin ciki ya lulluɓeta, sai a lokacin ta samu damar sauke ajiyar Zuciya ta ƙara jan lafiyayyen numfashi;
Murmushi me haɗe da hawaye ne ya suɓuce mata, kamar za ta yi kuka ta ce "Ka tsorata ni Shahzain."
ya yi lallausan murmushi kafin ya ce "Tuba nake, ban so Tsorata Sarauniyar Mata ba."
Kukan ne ya kufce mata ba tare da ta shirya ba "Ni dai ka dena tsokanata ba na so"
ta yi maganar cikin wata shagwa-ɓaɓɓiyar murya.
gyara tsayuwarsa ya yi kafin ya ce "Ko da zan tsokane ki ba zan tsokane ki ta wannan hanyar ba, So indai na gaskiya ne ba maganar wasa a cikinsa, ki dena kuka yanzu ba lokacinsa bane, ki yarda dani, ban iya irin surutun nan da yawa ba ne ban san ta yadda zan yi miki bayani ba, abin da na riƙe kawai shine ina matuƙar Sonki Shukri"
Farin ciki ne ya ƙara sakko mata ta ko'ina, kukan nata ya koma haɗe da murmushi, kasa cewa komai ta yi sai dai kallonsa ta ke, ji take kamar ta yi tsalle ta rungumeshi sai dai ba ta da damar hakan, juyawa ta yi da gudu-gudu ta koma cikin gida..........
..
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*INDO*
[12/26, 8:37 AM] INDO CE: *WATA HANYA*
24 Free Book
Ayeesha Abdulkareem
*(Indo ce..)*
ELEGANT ONLINE WRITERS.
Fatima Da ke tsaye a gefe sun barta kamar shanya ta rufe bakinta da ta saki tin lokacin da ta gane kowaye, cike da farin cikin Samun soyayyar ƙawarta-ta ta ce "Ka yi mana bazata Yallaɓai Shahzain."
ɗan murmusawa ya yi gami da cewa "Na ji tsoro ne kar na gaya mata ni ne ta ce ba ta nan ko ta ce kar na zo"
Ta murmusa kafin ta ce "Ba za ta yi haka ba ma nasani Yallaɓai."
"Ohh Fatima yanzu ni Abokinki ne fa ki dena kirana da yallaɓai ɗinnan, Shahzain, ko ki ce Auta.
ta ce "To ba komai, amma ka tsaya a nan mu ƙarasa ciki mana, na ga ma ba ku gama magana ba ta shiga ciki.
ya ce "Na ji tsoro kuma, ina cikin fargaba kar ta ƙi Sona."
Fatima ta ce "Ba za ta ƙi sonka ba in Allah ya yarda, don Allah ka shiga ciki dai."
"Okay.
gaba ta yi ya na biye da ita, kai tsaye Falon saukar baƙi ta raka shi sannan ta wuce cikin gida.
kasa zama ya yi ganin Shukriya a zaune ta na kuka, ya tsira mata ido har tsawon wani lokaci sannan ya taka zuwa inda ta ke, durƙusawa ya yi akan guiwarsa kafin ya fara magana a marai-raice "Me yasa ki ke kuka Shukri?, na yi shishahigi wa rayuwarki ko?, na rasa yadda zan yi ne Domin Sonki ya riga ya kaini matakin da ba zan iya jurar rashin ki ba, Ki yi haƙuri."
goge ƙwallar ta shiga yi ta na murmushi "Ban san wane irin farin ciki zan nuna ba da na samu soyayyarka Na gode Zain, Na gode da ba ka bari Sonka ya kasheni ba, amma na san Hajiya Dada ba za ta bari na Aureka ba shi yasa na ke kuka wa kaina.
"Wacece ita???"
ya jefo mata tambayar gami da kafeta da idanu Zuciyarsa na wani irin tsalle.
_______________________
Kai-kawo ya ke yi a barandar samansu ya na ta faman rarrashin Shahzad .
Inna ce ta yi sallama Halima na maƙale a bayanta sai zazzare ido ta ke yi ta san ta yi laifi.
ko kallonsu bai yi ba, Inna ta ce "Baban Shahzad Ka fito ka ci Abinci.
Idanu ya watso mata fuskar nan a murtuke, a dake ya ce "Ni zan wani ci Abinci yanzu bayan ki na kallo kula nake da Ɗana? ki ce mata ba zan ci ba.
"O'o ni Jikar Hajara"
Inna ta faɗa gami da riƙe haɓa, ta ci gaba da cewa "Wai shi ma ɗannan da Mita har yanzu kukan ya ke yi? gashi kuma sai ya ce dole sai a hannunka kawai zai yi shiru."
"Inna ba dole ya yi kuka ba Mahaifiyarsa ta ƙi karɓarsa don cin zali har da dukansa.
"To
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 30