ba a wannan lokacin, ya na da matan aure guda biyu da yara masu yawa, ina gama gaishe su muka fita muka tafi gidan Addah Ummu, murnar da na yi na ganin ta ba kad'an bane, domin kuwa ta haifi Ahmad dama ban samu zuwa suna ba,hakan se ya sanyaya min zuciya ta,a kan Ahmad na fara d'aukan jarirai saboda ina matuqar jin tsoron tab'a su motsin su a hannu na firgita ni yake, se gashi na d'auki yaron na riqe kamar ba zan ajiye shi ba, Addah Ummu ta ji dad'in gani na itama sosai, muka zauna muka sha hira na ci abinci a gidan ta na yi nak sannan muka mata sallama muka shiga gidan Sarki dan gaishe su, daga nan muka yi ta shiga da fita zuwa dangin Babana na jiki da kuma dangin Yah Maheer d'in.
A matuqar gajiye muka dawo gida ranar ana daf da kiran magariba, bayan na gaishe da mutan gidan tare da isar da saqon gaisuwar mutanen da muka je wajen su,se na cire takalmi na na dakko slifa na da na zo da shi dan sakawa a tsakar gida, hijabi na na cire na yafa a igiya sannan na d'auki buta na zaga bayan gida, ina fitowa na d'aura alwala na ja hijabi na na d'auki jakata da na yasar a tsakar gidan na shige d'aki, Ummeeta na can sashen su itama a gajiye.
Sallahr magriba na gabatar sannan na jingina da kujera ina fidda numfashin wahala, tinda uwata ta haife ni ban tab'a tafiyar qasa irin wannan ba, ko ina na jiki na ciwo yake min, gashi wanda zan zubawa shagwab'ar baya nan, ko ina ya tafi oho? Tinda na fita sau biyu ya kira ni, rashin samun wanda zan yi wa kukan na gaji da rashin samun Yah Maheer a gida se ya had'u ya haifar min da fushi mara dalili, Allah Allah nake ya dawo ya tadda kalar fushin da nake shi na bari na da ya yi na gaji.
Wani irin tuwo me rai da motsi aka ajiye a gabana ga dakakken yajin daddawa da ya sha maggi har da farin maggi mutumi na, ga man shanu an zuba masa, qamshin tuwon nan ne ya sa na ji duk wata masifa da fushi da na kinkima wa kaina na gaira babu dalili ya zagwanye, jan kwanon na yi na yi bismillah na hau danna tuwon nan a ciki na ba qaqqautawa,bayan gidan Addah Ummu duk inda muka je aka bani abinci bana ci kunya nake ji, in ko ruwa aka bani gidan be min ba se na tsoma baki na a ciki na yi kamar sha nake na dire kofi ko kwanon,in kuma gidan ya min sai na sha na qoshi, shine dalilin da ya sa na dawo da muguwar yunwa a tumbi na marata kuma fal fitsari .
Ina tsaka da cin tuwo aka kawo wutar lantarki wadda tinda na je ba a kawo ba, gashi dama muna cikin watan maulud ne an kusa mauludi,dan haka dama tinda muka je kad'e kad'en waqoqi na tashi sama sama saboda rashin wuta, ai kuwa ihun yara da matasa ne ya karad'e garin, ni kaina se na ji ni ina ta murna saboda wutar lantarkin da aka kawo, kafin kace me garin ya kacame da kad'e kad'e da waqe waqen yabon Annabi yanda ka san a cikin gidan aka kunna, nan da nan kuwa kaina da ke matashin ciwo ya dauki babban ciwo, a hankali na ci gaba da danna tuwon nan har na qoshi, tashi na yi na fita domin wanke hannu, Zainab na gani qanwa ga Yah Maheer 'ya a wajen Mama, kiran ta na yi na nuna mata robar wanka na ce dan Allah ta zuba min ruwa a ciki, na watsa, babu b'ata lokaci kuwa ta d'auka ta wuce bakin rijiya, kafin in gama shirin wanka in fito ta cika min robar ta kai min, godiya na masa ina tsokanar ta da cewar,
"Kin fanshi yayan ki, na gode"
Wanka na na yo ina mamakin yanda ake qure kid'a a ko ina ba tare da tinanin maybe akwai marasa lafiya, ko wanda suke karanta qur'ani a wannan lokacin ko sallah, ko bacci da dai sauran ire-iren wadannan uzirin da ba su son hayaniya,da so samu na ne da sun rage kid'an tinda nima ina sauraran kid'a amma qarar ta yi yawa, haka na gama wanka na na fito na yi alwala sannan na wanke baki na na koma d'aki,sallah na yi sannan na yi shirin bacci dan yanda nake ji na in ban bacci da wuri ba kai na zai iya tsage min gida biyu, tinda na saba baccin rana amma ban yi ba, na kuma saba da in yi zamana ina hutawa ta to ga yawo nan na sha na gaji.
Yau da wuri na shimfid'a qaramar katifa irin ta 'yan boarding school na yi kwanciya ta, Umma ta yi ta yi na hau gado na qi,rashin sabo da kwanciyar qasa ya qara shiga list d'in damuwa ta a wannan daren.
Ina nan kwance ido ya min jawur da nauyi kamar 'yar maye, ga bacci ya qi zuwa Yah Maheer ya dawo, ina jin shi ya na ta min magana tare da shafa qafata bayan ya zauna a tabarmar da Umma ke zaune ta na jan carbi, na yi shiru kamar me baccin gaske, haka ya gaji ya tashi ya tafi d'akin Baba, Yah Maheer gaba d'aya shi baya sauraron kid'a baya son kid'a saboda ciwon kai yake saka shi, wanda a wannan lokacin jin shi kawai nake dan ba wai na yarda bane, dan haka shima yanda na kwana ba bacci shima haka ya kwana ba bacci da kuma ciwon kai me tsanani.
Washegari haka muka tashi ni da shi babu lafiya, su kuwa mutanen garin mu shirye-shirye Maulidin su suke yi abun su ba abinda ya shafe su da wata MAHREEN da Maheer d'in ta.
*************************
Washegari ziyarar a gidan Goggon su Yah Maheer ta fara, inda muka je tin wajen qarfe sha d'aya na safiya, dan kuwa an ce in dai za a je gidan ta to tafi so a je da wuri kuma a jima mata, ba wai ana zuwa a tafi ba, sanin cewar za mu je ne ya sa muka tarar da ana ta hidimar yin abinci ita da yaran ta, gida ne gidan malamai da sanin ya kamata, dan haka yaran ta kan su a nutse suke qaramar cikin su zata yi sa'ata ko ta girme ni ma, komai a nutse suke yin shi da kamala da mutuntawa, haka muka nutsu muma muka saje da mutanen gidan ni da Ummeeta, a taqaice dai bayan mun gaishe ta da mutanen gidan har da mijin ta wanda shi ne waliyyin Yah Maheer, nan muka ci muka sha muka qoshi har na samu baccin da ban yi ba a daren ranar, sai da azahar ta yi na farka muka yi sallah sannan muka tafi,bayan mun fito ne na ke mamaki anya wannan baiwar Allah zata yi maganar da aka ce ta yi akammu na cewar in ba zamu zo ba mu yi zamammu ya cinye ni? Duba da yanda ta tarbe mu cikin nishad'i da qauna da soyayya.
Kad'a kafad'a ta na yi na kyab'e baki na alamar 'Oho koma dai menene na ci wake da shinkafa da mai da yaji'
Haka muka ci gaba da ziyara har gidan qanwar Yah Maheer Ruqayyah wadda suke Mahaifiya d'aya (Allah ya musu rahama) ba tare da na san alaqar da ke tsakanin su ba a wannan lokacin,daga nan muka je gidan 'yar Dada wadda suke unguwa d'aya da Ruqayyan.
A hanyar mu ta dawowa ne muka je gidan Dada wadda ta nuna ita sam wannan zuwa be mata ba sai na je na musamman na yini mata, sannan ta san na je, hakuri na bata tare da alqawarin sake komawa kafin mu tafi.
Washegari kuwa Yah maheer da kan shi ya ce mu huta yawon ya min yawa kar in zo ina zazzab'i, ai kuwa na ji dad'in hakan se kawai na shiga sashen matan yayan shi muka sha hira, sun yi matuqar mamaki da suka ga na sake ana hira da ni, ga dariya ina ta basu suna karb'ewa, duk wani shirin mauludin da za a yi a washegari da ni aka yi, duk da cewa ni gidammu ba a maulud shima Yah Maheer baya yi, amma hakan be hana ni shiga an yi da ni ba, girke girke kam an sha shi na alfarma, dan kuwa ko ba komai mun ci kaji sosai, ranar Maulidin kuwa haka aka dinga yin abubuwa na qayatarwa, duk inda ka juya idanun ka ganin mutane zakai cikin farin ciki sanye cikin sabon kaya.
Makarantu da qungiyoyi haka suka dinga wucewa saman titi kowacce qungiya da jagororin ta da kuma irin qasidar da suke rerawa ko suka kunna suke taka rawa.
Tin ina kallon na marmari har na gaji na koma cikin gida na zauna ina hutawa, Yah Maheer ne ya min waya ya na sanar da ni in shirya da dare zai kaini gidan abokan shi, amsa masa na yi da "To" sannan na tashi na hau duba kayan da ya kamata in saka da daren, wani material mara nauyi na dauka kalar ja,sai farin Hijabi, dan ni na fi son fara yin shiri tin kafin lokacin abu ya yi, saboda bana so ya zo yana jira na ina tinanin kayan ma da zan saka.
Yamma na yi na sake yin wanka, nan da nan aka samin suna sarkin wanka, dariya kawai na yi na shige daki na shirya na yi sallar magrib sannan na zauna na tsara simple makeover da ya fito da fuska ta da kyau, turare na fesa da wuri saboda ya d'an bi iska kafin lokacin tafiyar mu ya yi, ina nan zaune aka kira sallar Isha'i ko abinci na qi ci dan kar na b'ata kwalliya ta, sallah na tada ina jin haushin jiran shi da ya sa ni yi, kuma ya san bana son jira.
Ina raka'ar qarshe ya shigo hannun shi d'auke da ledar fruits ya miqa wa yara ya ce gashi a raba, se leda me dauke da ayaba, ya ajiye a gefe na, ina idar da sallah ya nuna min ledar, nan da nan na ji na dena jin haushin shi dan kuwa na hango ayabar, ina zira hannu na na ji har da mutuniya ta wato chocolate, murmushi na kashe shi da shi wanda ya sanya shi sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta,
"Kin biya wannan service d'in madam"
Baki na tura cike da shagwab'a na ce,
"Ni na fad'a maka bana son madam se kace wata qedara"
Dariya ya bushe da shi kamar yanda ya saba a duk sanda na ce masa bana son a kira ni da madam.
"Wai ni Young Lady baki san ma'anar madam d'in bane ko me?"
"Na sani mana, kalma ce da ake amfani da ita wajen girmama mata, madadin a kira sunan mace gatsal ba girmamawa se a ce mata madam, uhmmm ni dai gaskiya bana so, arna na ke ji ana cewa madam tin tasowa ta, kuma na ce ka dena bari abokan ka suna cewa 'Ya madam'"
"Tom an dena daga yau inshaa Allahu maza ki gama ci mu tafi,"
"Yanzu dare be yi ba?"
"Beyi ba kam in dai anan garin ne, yau fa ranar maulidi kar ki manta, wa ki ke tsammanin zai bacci qarfe tara bata rufa ba? Gobe nake so mu tafi da yamma" halin shi kenan da bana so fad'an abu a qurarren lokaci.
Ji na yi ban ji dad'in tafiyar da ya ce za mu yi ba gobe,dan ban gama ganin Addah Ummuna ba, dik da cewa in zamu fita ko mai rintsi se na leqa gidan ta, tinda gidan ta a kan hanya yake, ganin yanda raina ya sosu ne ya sanya shi karb'e b'awon ayabar da na riqe ina tara kwalla a ido na ya ce,
"Kin ga gobe monday ya kamata na koma ranar Wednesday akwai abinda zan yi, kin san ina neman aiki to akwai wani abu mai mahimmanci da ya kamata na koma na yi"
"Allah ya kaimu da rai da lafiya"
Shine abinda na fad'a na dan saki raina na sanya hijabi na muka yi wa mutanen gidan sallama muka fita.
Kamar yanda na sanar da ku garin Liman Katagum ba dai ni'ima ba, musamman da dare, sai fitar nan ta zame min fitar masoya, dan se na manta ma wai ziyara za mu je, haka Yah Maheer ya riqe hannu na a nashi muka yi tattaki har zuwa gidan abokin shi wanda yake takwarana, matar shi na da tsohon ciki a lokacin rasa inda Amina zata sanya ni ta yi dan farin ciki (Allah ya mata rahama) lemon kwalba da soyayyan nama ta kawo, ko bata matsa min ba na yi niyyar ci amma da na ga irin mutanen nan ce ita masu takura wa mutum akan ya ci abu sai na dinga noqewa ina nuna jin kunya ta,da kyar na dauki nama na fara ci, cikin raina ina jin dad'in tarbar da aka mana.
Daga nan muka fita muka ci gaba da zaga gidajen abokan shi, bamu dawo gidan ba sai goma da rabi, muna zuwa qofar gidan su muka ga wajen shiru ba mutane sosai, nan muka samu waje muka zauna qasan bishiya muna shan iska muna hira, ganin dare na yi ne ya sa Yah Maheer miqa min hannu da niyyar d'aga ni mu shiga sai ga Baffa Zubairu qanin mahaifin Yah Maheer ya dawo zai shiga gida, a matuqar kunyace na fizge hannu na na afka cikin gida, shi kuwa Baffa ya yi kamar ma be ga me muke yi ba.
Washegari kuwa kamar an yi sanarwar za mu koma, (wanda ban sani ba ashe duk gidan da muka je ni da Ummeeta sai da shima ya je gaishe su, daga nan yake sanar da su zamu koma ranar monday) tsaraba aka dinga kawo mana su kuka ne,su daddawa ne yaji ne da sauran su.
Tinda na je gidan su Yah Maheer na tadda wata qaramar qanwar shi mai suna Suwaidatu wadda take shiru shiru, bata yawan magana se kukan shagwaba, yarinyar na so na, ta na zuwa inda nake ta tsaya ta na shan kunu a cikin fidar roba har in yi ta mamaki duba da cewa a qalla za ta kai shekara takwas zuwa tara,Suwaidatu 'ya ce a wajen Mama wadda ba laifi ta fi sauran yaran Mama hasken fata, ko da zamu tafi yarinya ta dinga kuka zata bi mu, an yi an yi ta yi shiru ta qi, dan haka sai Baba ya kira mu, ya sa aka shirya ta da kayan ta, ya damqa wa Yah Maheer ita ya ce gata ya bamu ita,nan da nan ba tare da damuwar komai ba muka yi masa godiya muka kamo hanya sai garin Bauchi.
A ranar da muka dawo ko hutawa ban tsaya yi ba na hau gyara waje, ban zauna ba se da na yi wanka na yi sallar la'asar sannan Addah ta kawo mana abinci muka ci ni da Suwaidatu se na d'ora wa Yah Maheer taliya da mai da yaji, tinda muka iso Suwaidatu ta kyalla ido ta ga ba mutanen gidan su se ta hau b'ata rai, sannan ga Yah Maheer kamar wanda yake jira mu dawo ya jani zuwa d'aki muka barta a nan parlour bayan na kunna mata TV na tafi se kawai ta hau kuka,kuka ta dinga yi kamar irin na qananan yaran da aka yi kiminashin d'in su aka kai dokar daji aka yar, ban tashi sanin meke faruwa ba sai da muka fito da misalin shida da rabi na yamma, ta yi kuka har zazzab'i ya sauka a jikin ta ta yi bacci a wajen.................
Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 12:
Ko da na fito daga d'aki na kafin na tafi watsa ruwa se da na leqa ta, ganin cewa bacci take kawai se na wuce ba tare da yin kwakkwaran motsin da zai farkar da ita ba, wanka muka yi baki d'aya sannan muka shirya cikin kaya marasa nauyi, muka koma parlour na sa mana abun sallah kamar yanda muka saba ya ja mu sallah.
Bayan mun idar mun yi azkar ne ya janyo mana qur'anin mu babba mai fad'i a saman TV stand dan ya fi ni kusa da shi ya yi min nuni da in je gare shi yanda muka saba yin karatun a tare ina cikin jikin shi, alamu na yi masa da kaina alamar Ah ah, yanzu ba mu kad'ai bane dole yawan zama a manne da junan mu ya ragu,tashi na yi na je d'aki na dakko wani qur'anin na zauna a inda na yi sallah nesa da shi, na bud'e surar da muka tsaya, muka fara rera karatun qur'anin mu cikin nutsuwa.
Tashin muryoyin mu ne ya tashi Suwaidatu a bacci, cike da kyab'e baki irin na wanda suke son yin kukan nan, bayan mun kai qarshen aya na ce mata,
"Kin tashi? Je ki yi alwala ki sallah se ki zo ki ci abinci in yaso da kin yi isha'i se ki koma baccin ki ko?"
Gani na yi ta kasa tashi, sai na ajiye qur'anin na je gare ta, ina tab'a jikin ta na ji ya d'auki wani irin zafi zauuuu, tausayin ta ne ya kama ni, da sauri na hau neman maganin saukar da zazzabi, a saman cinya ta na dora ta na balli maganin Yah Maheer ya miqo min ruwa na bata a baki, cikin yunqurin yin amai ta dinga qoqarin shanyewa, a haka har Allah ya taimake mu bata dawo da shi ba, ta na nan zaune a saman cinya ta kai ba dankwali da rigar da zani na wani yellow d'in material a jikin ta na yi feeding din ta abinci da kyar ta iya cin shi,abu daya ne ya sake damu na, zama na da na dan yi da ita da yayun ta na kula suna son shan kunu, ni kuma gashi banda shi, dan za a dama kunu tin da safe a babban bokiti a ajiye a kowanne lokaci mutum ya so sha zuwa zai yi ya kamfata ya sha har cikin dare shan kunu suke, sannan ina tunanin na yi qanqanta a kula da ita tinda nima dika dika nawa nake? Yanzu gashi bani da kunun bata gasu da son kunun tsiya.
Dan bana manta zuwan Yayan ta da suke d'aki d'aya,Yah Maheer ya girme shi, ita kuma shine babba a d'akin su, mai suna Isma'il ya zo shi da Abubakar, zuwan shi na farko da na basu abinci suka ci ana hira se da ya tambaye ni ko ina da kunu? Zuwan shi na biyu ma haka, sannan akwai wani zuwa da ya yi still bayan ya kammala cin abinci se ya samu doguwar kujera ya hakimce ya miqe qafafu ya yi zaman shi ya na ta tilawar qur'ani domin Isma'il is claming Ustaz a koda yaushe,hadari ya taso sosai, a zaton mu zai tafi can gidan kawun su ne inda ake riqon shi tinda hadari ya taso goma na dare ya yi, ya kuma ci abincin da ya kan zo ci da dare, Yah Maheer na matuqar so mu je mu kwanta amma ya yi zaman shi, sannan shi be ce anan zai kwana ba, kuma be ce tafiya zai ba gashi har ruwan sama mai qarfi a wannan lokacin ya fara sauka,ji yayi garin ya yi sanyi ya yi ni'ima, sai ya juyo ya kalle ni ni da Yah Maheer da ya kasa jurewa se da ya ja ni zuwa jikin shi, cikin muryar shi ta ustazai ya ce,
'Wato ainihin Amarya kyan wannan ruwan da ake yi mutum ya samu shayi me zafi ko kunun da aka dama me zafi, ya na zaune yana korawa,'
A hankali Yah Maheer ya ce,
"Kai kenan da ka ke gwauro,ni kuwa ina da plans,"
Dariya na yi kawai dan ban sani ba ko Isma'il ya ji ko be ji ba,ni dai da kalmar "gaskiya ne" na bishi da ita, tada ita na yi daga cinya ta na zaunar da ita gefe, a raina ina ayyana,
'Anya yarinyar nan me maqon gida zata yarda ta zauna da mu kuwa?'
Gashin kan ta na sake kallo a karo na ba adadi na sake ayyana.
'Lallai ina da aiki a gabana, ga yarinya me kyau masha Allah amma duk rashin gyara ya sa ta dafe"
A haka muka kwana ranar cikin jimamin zazzab'in da Suwaidatu ke yi, da safe kuwa bayan na gama yi mana abun karyawa sai na dora ruwa mai zafi na mata wanka na wanke mata kan ta da na tsefe shi tsaff, sannan na taje shi na mata oiling,na yanke mata farce se ga shi zazzab'in ya sauka, ta dawo normal, a ranar se da Yah Maheer ya je ya siyo kunu dan kuwa na matsa masa na ce tinda bamu da geron yin kunu dole a nemo mata kunu dan ta fi son shi.
Ai kuwa ta yi farin ciki da hakan dik da bata wani sake sosai ta nuna ba, amma daga yanayin walwalar ta da ya sauya da yanda ta fara fara'a na gane cewar ta yi murna sosai da hakan.
Kwanan mu uku da ita a na hud'u sai ga Maman ta ta zo d'auke da wata qaramar yarinyar mai suna Sa'a, yarinyar marainiya ce ta dakko ta saboda tana da alaqa da iyayen ta, ta ce ta biyo ne a gaisa, Suwaidatu ta yi murna sosai, kuma ita kan ta Maman ta yi murna dan ganin yanda ta yi tsaf da ita a 'yan kwanakin,domin kuwa dik da ban wani iya kitso ba sosai a wancan lokacin a haka na samu na gyara mata cinyayyen kan ta da ko kitson azziqi bai kamuwa a yi da shi.
Sanda Mama za ta tafi sai da Suwaidatu ta yi kuka ta lallashe ta, ta ce in tana kuka ko ta shigo garin ba zata biyo a gaisa ba, dan haka ta yi hakuri ta dena kuka, 'yar tsarabar da ta zo mana da shi ta bani sannan ta tafi.
A hankali Suwaidatu ta fara sabawa dani, sannan ta rage kwalaficin gida,Yayan ta kuwa da take kira da Yaya, yana ci gaba da zuwa akai akai, tinda ya maida gidan wajen cin abincin daren shi, ta bangare d'aya kuma Abubakar ya tattaro shima ya dawo nan waje na da zama, ya yi wa kan shi d'aki a garejin gidan wanda yake da qofa ta cikin parlour, tabarma ta me kyau me flour da kyalli da ado da iyayen mu ke sai mana a duk sanda aka wa d'aya daga cikin mu aure ita ya d'auka ya tafi da ita ba tare da izini na ba ya ke kwana akai, ban tab'a cewa dan me ba, saboda a lokacin na d'auki 'yan uwan Yah Maheer 'yan uwa na ne, ko ba komai dikkan mu muna da alaqar zumunci a tsakanin mu.
Sannan a lokacin ni dai kawai shimfid'a tabarmar nake ba dan na san cewa an yi ta ne purposely saboda cin abinci bane, dan haka ban wani san amfanin ta ba da kyau.
Satin Suwaidatu uku a gidan mu zuwan Isma'il ya qaru a gidan sosai watarana har kwana yake, a hankali ya fara zuwa da jaka ya na kwana d'aya zuwa biyu se ya tafi, Yayan shi kuma be masa magana ba, be ji dalilin da ya sa yake haka ba, tinda asali a gidan d'an uwan Maman su yake da zama a cikin garin.
Watarana ya zo da wata baqar jaka da daddare zai shige d'akin da Abubakar ya yi wa kan shi masauki, sai na kalle shi ina tinanin,
'dika dika watana uku fa amma na ga alamar bayin Allahn nan nan suke son su dawo da zama, ko gama more zaman auren ban yi ba, ga aiki banda hutu safe da rana da dare,gashi ba wanda ke min bayani se dai kawai na ga anzo an zauna, idan Abubakar ya zauna saboda dama ba a cikin garin bauchi yake da zama ba shi Isma'il ne ya ke yawan kawo shi bayan ya na zaune a gidan Kawun
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 30