Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dama can ke ba me wasa da ibadar ki bace Allah ya muku albarka, Allah ya kai ku lafiya ya baku zuri'a mai albarka, ki kara hakuri akan rashin haihuwa domin dama Allah ya ce a cikin Alqur'ani mai girma, 'Audhu billahi minasshaid'anirrajeem, Lillahi mulkussamawati wal'ardhi yakhluqu ma yasha'u, Yahabu liman yasha'u inasan wa Yahabu liman yasha'uzzukra, au yuzawwujihum zukranan wa inasan, wa yaj'alu man yasha'u aqima, innahu aleemun qadeer.' a takaice dai kamar yanda na sha faɗa maki Allah ne me azurta bawa da yara wasu ya basu mata zallah, wasu maza zallah wasu kuma ya haɗa masu mazan da mata, wasu ya bar su aqima,wanda ba su haihuwa, ki sa a ran ki duk yanda Allah ya yi ki shi ne daidai, shi ne kuma mafi alkhairi a gare ki," "Inshaa Allahu Baba na gode, da yardar Allah zan yi dukkan abubuwan da ka lissafa min, kuma nima na sha faɗa maka ka dena damuwa akan rashin haihuwa ta, ni da kai na nake addu'a idan yara alkhairi ne a rayuwa ta da addini na da miji na Allah ya bani masu albarka idan babu alkhairi Allah ya qara mana hakuri da juriya, idan shi alkhairi ne a wajen shi ko ba da ni ba Allah ya bashi masu albarka, baba lokaci na tafiya kar na rasa motar farko" Maganganu na sun shige shi sosai saboda ina ganin hawaye kwance a saman fuskar shi, a duk sanda za mu yi magana irin haka to tabbas za mu saka juna kuka, shi ya na fara nashi nan take ni kuma ina nan ina nawa a duk sanda na tuna maganganun shi, sallama na masa na kama hanyar komawa cikin gida. Nan take ina tafiya na hau hasashen kalar hakurin da zan qara yi a rayuwa ta da kalar kauda kan da zan ci gaba da yi a rayuwa ta akan duk wani abu da zai bata rai na ko ya dasan baqin ciki. Tunawa da na baro hawaye na zuba a idon Baba sai ya sa jiki na sanyi, na miqe na yi wa mutanen gidan sallama na aika Sa'id ya sanar da Baba na gama shirya wa, Baba ya dauki makullin mota ya ce na je waje gashi nan zuwa. Ban san me ya tsaya yi ba har muka fitar da kayan mu wajen mota muna jiran shi, se daga baya Baban ya zo, da shi da Mama suka kai ni tasha, Baba ya ce gaba za a kama min ni ɗaya ba zai yu a samu a baya mu matsu ba,ko kuma ya biya mana kuɗin mutum uku a bar mana baya, haka kuwa akai nan take ya biya mana kuɗin mutum uku muka shige baya mu na daga masu hannu suka tafi, Mama na ta jaddada min na riqe addu'a na roqi Allah duk abinda nake so a halin tafiya Allah zai amsa ko ba jima ko ba dad'e,ina kuka muka rabu da iyaye na suka tafi, mu na nan zaune a tasha har kusan takwas na safe kafin motar ta cika mu kama hanyar Kebbi. Tafiyar awanni bakwai ce ta kai mu garin na Kebbi, inda mu ka tarar da Yah Maheer da abokin shi na jiran mu a tasha, kayan mu suka dauka su ka sanya a bayan motar abokin shi sannan mu ka nufi gidan da muke zama, mu na zuwa na ga gidan ya sha gyara daidai iyawar namijin da be saba aiki ba,dariya na yi na wuce wanka na yi wanka da ruwan tap me dumi, ina fitowa na ga ya dakko mana holandia me strawberry, ruwa da abinci, zama mukai ina ci ina mamakin a ina ya samu abinci haka har da nama na san be iya girki ba, ko ashana da kyar yake kunna wa ya sa mana maganin sauro. Murmushi ya yi ya ce, "Ki adana tambayoyin ki se kun huta zan baki labari" "To ai hikenan Allah ya kai mu mu huta din" Nan na hau bashi labarin bikin Ameenah qawar shi, dan duk qanne na sun fi yin wasa da tsokanar juna daga ita sai Auta Jiddah,bayan mun gama da cin abinci ne na shiga daki dan na sauya kaya na, ina shiga kamar tare muke da shi ya rungume ni sosai ya na sauke ajiyar zuciya tare da faɗin, "Alhamdulillahi na gode wa Allah da ya dawo min da fitilar gida na lafiya" "Hummmm ai kai dai ka ga bone Husband, wai ko kunya baka ji ba ka kira Mama ka na ce mata gidan ya maka duhu na dawo, habaa ai a zato na ba zaka iya faɗa wa mama wannan maganar ba" Kama baki ya yi ya na mamaki na, "Me na yi to? Gulma ko sata da na baki kunya?" A hankali ya kama hannaye na da nake qoqarin jan rigar da na sanya qasa, ya kalli cikin idanuwa na ya ce, "Ki na nufin abinda na faɗa ba gaskiya bane? Kin kuwa san yanda ki ke a rayuwa ta? Ba zaki gane ba, amma yau zan sanar da ke wani sirri da ke zuciya ta, wanda ban taɓa faɗa maki ba, Baby na ke ce farin cikin rayuwa ta, mutane na ce wa ke/kai ne farin cikin rai na a baki, ni ina faɗa maki ne har cikin rai na,ke kadai ke bani nishad'i da cikakken farin ciki, to kin ga kuwa rashin ki dole rayuwa ta ta zama cikin duhu, in shiga qunci shi ne ma'anar gidan ya min duhu" Ba qaramin tasiri maganganun shi suka yi a zuciya ta ba, na yarda da kalaman shi, na yarda da abinda ya ce duba da yanda ya rame' ya yi duhu, ya yi aski amma gaba ɗaya fuskar shi ta zurma Suwaidatu ta riga ta san in mun shiga daki ta bar mu mu kebe ba tare da ta shiga ta dame mu ba, wannan dalilin ne ya sanya mu sake jiki da junan mu har sai da aka kira la'asar sannan muka fito,wanka mu ka yi sannan ya ja mu Sallah tunda ya makara ba lallai ya samu sallah a masallaci ba. A nan parlour mu ka ci gaba da hira har bacci ya damu Suwaidatu ta shiga daki ta bar mu zaune a parlour, ashe rabon mu sha wahala ne ya hana mu bin ta mu kwanta baki daya.......... *Assalamualaikum mutanen kwarai masu albarka, kar ku manta ku fara shirin siyan part two na wannan Novel da zarar an kammala part one din shi...Thank you for all ur support and love....Allah ya bar mu tare har aljannah* 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 32: *Mai so a sanya ta a group ɗin MAHREEN2 paid book ta min magana ta wannan No 09031416423* Qofar parlourn gidan( Kamar ) soundproof ce saboda in aka rufe qofar wanda ke ciki baya jin me ake yi a parlour, sannan wanda ke parlour ba ya jin me ake a ciki. Mun riga da mun rufe qofar gidan baki ɗaya daga gate ɗin gidan har qofar shiga parlourn, sanda Suwaidatu zata tafi cikin gidan ta rufe qofar key ya na jikin qofa ta waje, we became trapped a cikin parlour no any other way out, mu na nan zaune ba tare da mun san me ke faruwa ba, mu na ta cin soyayyar mu da tsinken tsire hankali kwance mu a dole an bamu waje. Sauro ne ya dame ni na tashi ina mita na ce, "Gaskiya sauron nan kun sha na Allah ya isan ya yi yawa haba, duk jiki na cizon sauro ne so suke su kada ni qasa, tashi mu koma d'aki Please na gaji da zaman nan yanzun nan za su dauke wuta na san 12am ya kusa" Yi ya yi kamar be ji ni ba, cike da shagwaba na zube a jikin shi ina roqon ya tashi mu shiga ciki, a hankali ya buɗe ido ya na kallo na sannan ya ce, "To d'aga ni, in dai ki na so mu tafi ki d'aga ni na miqe tsaye da qafafu na ba ki na ikirarin ke mai qarfi bace? Qiwar tashi nake ji" "Ohhhhhh za ku wa ka sha mamaki, ni sai in ɗauke ka ma, ina zuwa" Tashi na yi tsaye na dinga qoqarin d'aga shi ya zauna ma da duwawun shi na kasa, yaraf na sake kwantawa a jikin shi ina kukan shagwaba ina roqon shi ya tashi mu tafi, amma ya qi, ba mu yi aune ba sai gani mu ka yi an ɗauke wuta, cikin jin haushi na ce, "Great ! Burin ka ya cika ai sun ɗauke wutar wayoyin mu na cikin d'aki ba abun haska wa," Buɗe idon shi ya yi da ya ke a kulle tun dazu ya kalli hasken farin wata da ya ratso labulayen parlourn ya shigo, sannan ya maida kallon shi gare ni ya ce, "To ba ga shi Allah ya bamu haske mai sanyaya zuciya ba, kalli fa ki gani kalar fatar ki ce kawai bana gani saboda na fiki haske" "Mafarki kenan na faɗa maka na Fika haske da ina yarinya, ka tambayi mama ka ji" Dariya ya yi sosai sannan ya ce, "To ni kin ganni ne da ina yaro, ke ma kin san na fi haka haske ko ba a faɗa maki.ba ko?" "To na Ji, ni dai tashi mu tafi" Kamar wanda aka yi wa allurar qarfi haka ya miqe, ya kama hannu na na kwace na koma bayan shi na d'ale ina buga qafa ta a jikin shi kamar me buga machine na ce, "Yauwaa mu je, laaa mun manta bamu kashe AC ba" Komawa ya yi da ni a bayan shi ya kashe AC, sannan muka nufi hanyar fita ina tsokanar shi na ce, "Mijin 'yar lukuta, kai yanzu ko nauyi na baka ji ko?" "Wa yaga Yar paper, Ke ki ke ganin kan ki da girma ni har yanzu kamar Maijiddah(Autar mu kenan) nake ganin ki" "Tabdijam sauke Ni to bana son goyon" Riqe qafafu na ya yi gam, ya ce, "Baki isa ba ai, har d'aki se kin je a haka yarinya ni na gayyace ki goyo?" Door handle ya kama zai murd'a dan ya buɗe mu shiga cikin gida sai ya ji wajen ya riqe ya qi bud'uwa, sauke ni ya yi ya ci gaba da qoqarin buɗewa,qofa ta ce ba sai ka buɗe ni in gani ba? Duk wani qoqari ya yi amma shiru, can muka gane fa mun rufe kammu ko in ce Suwaidatu ta rufe mu bata sani ba,gashi kuma in ba an buɗe mu ta baya ba ba zai yu mu iya fita ba, Suwaidatu muka ware murya mu ka dinga kira amma shiru, da alama ta na shiga bacci ya ɗauke ta, kuma baccin ma me nauyi, domin kuwa kiran sunan ta muka dinga yi tare da buga qofa, nan da nan na ji numfashi na na min wahalar fita hankali na ya tashi, what if Wani abu ya faru fa? Something like gobara ko wani abu dai makamancin wannan ya za mu yi? Nan da nan na fara hango gobarar da mu ka yi ido na sai fitowa ya ke ina neman iskar da zan shaqa, Yah Maheer na ganin haka sai ya tafi da gudu ya janye glass din wajen ya buɗe windows se ga iska ta fara shigowa, bakin window na je na tsaya ina shaqar iska ina kiran sunayen Allah duk wanda ya zo baki na,cikin rai na kuma ina addu'ar Allah ya kawo mana mafita dan ni fitsari ma nake ji, juya wa na yi da niyyar na sanar da Yah Maheer Ina jin fitsari sai na ga ya na sintiri a zato na halin da nake ciki ne ya sanya shi sintiri baki ya buɗe ya ce, "Fitsari nake ji Baby na, gashi qofa ta rufu ba hanyar fita" "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, nima fitsari nake ji" Nan da nan hawaye ya fara sauka a ido na, danasanin zaman mu ba mu tafi dikan mu ba ne ya baibaye ni,wani ɓangaren na zuciya ta ina jin haushin shi duk shi ya ja mana kuka na fara sosai, dan sai na ji kamar ana matse min mara ta, se na ji ma kamar ban taɓa jin fitsari kamar na wannan ranar ba tunda nake a duniya. Kallon parlourn mu ka hau yi ni da shi mu na neman mafita, bakin qofa na sake zuwa na dinga kwala wa yarinyar nan kira amma inaaa shiru da dukkan alamu da ta shiga ciki ta rufe qofar dakin ma, tunda in abude ne za ta ji dukan qofa ko da bata Ji magana ba, ji na yi fitsari na son ya zubo min na tafi da gudu na ɗauki dustbin irin na 'yan gayun nan na roba me kamar bokiti na tsugunna akai na hau tsula fitsari ina gamawa se na ji kamar an zare min wata qaya a mara ta, ganin haka Yah Maheer ya hau min faɗa, "Ya zaki ki bata wa mutane abu fisabillahi, a fa parlour ake ajiye wa kin kuma yi fitsari a ciki" Ni ma cikin faɗa da kuka na ce masa, "Do you have any other way da ya kamata na yi fitsari Mr. Right? Kai komai se an bi qa'ida in zaka zo ka yi anan ka zo ka yi in ba za kai ba ni ba ruwa na" Na maida dustbin can bakin qofar shiga parlour na koma doguwar kujera na zauna cikin fushi, ya san hali na abu kadan ke sa wa na hasala kuma ya san shima be kamata ya min faɗa a wannan lokacin ba, duba da halin da muka samu kammu a ciki, ko ba komai gwanda da na yi anan akan na bari ya kubuce min a qasa ga Centre carpet, in ya gangara kai fa? Ya na so ya bani hakuri ya na tunani, dan ya san yanda na hasala din nan sake botsare masa zan yi gashi ya na fama da nashi fistarin. Cikin duhun na ji qarar ruwa na zuba, kafin na gane me ke faruwa se na ji dariyar Yah Maheer qasa qasa, nan take na gane ashe ya yi amai ya lashe ne, haba me zan yi banda dariya, cikin dariya na ce, "Ahhhhh su Mr. Perfect an gama faɗan, na ce an gama faɗan? Ai ni ce kai bari zan yi se gobe in an buɗe qofa se na je na yi a toilet nan ne ya fi dacewa na yi fitsari" Dariya ya dinga yi ina taya shi,se dai abun haushi ba ruwan tsarki, mu na tsaka da dariya na ce, "To yanzu yanda mu ka gamji zogale dazu Allah ya raba cikin mu da birkicewa ka san dai ni in zafi ya yi zafi ciki na na rikicewa ko?" "Allah ma ya kiyaye," Anan nake bashi labarin yanda tun ina qarama bana manta yanda Mama ke tashi cikin zafi ta yi ta min firfita saboda bana son zafi Sam, in zafi ya kad'a ni ina yawan yin amai ko na yi zawo, har girma na Mama na qoqarin yi min firfita in dai ba wuta mu na zaune tare, har watarana se na ce ta bari. Sauro da zafi sun rutsa mu, ga kujeru ba su da daɗin kwanciya yanayin shape din su bai tafi a miqe ba, sannan tun da muka je gidan dama na hana kwanciya akai, kar mu bata musu daga abun azziqi. Gashi ni bana iya kwanciyar qasa gefen ciki na na dama sai ya hau ciwo, rasa inda zan saka raina na yi, tun ina kuka har na gaji da kuka. Motsi na dinga ji cikin duhun, sannan na ji Yah Maheer shiru ya bar kusa da ni, cikin iko na Allah se ga hasken waya ya bayyana a hannun shi, tsalle na daka na je gaban shi ina murna, "Ina ka samu wayar ka? Ya akai ka san ta na nan? Akwai kati ciki? Kira mana Suwaidatu" "Yi a hankali Hajajju, ina zaune kawai na tuna mun yi waya da su Ummah kin manta ne? Wayar ki na daki Allah Ubangiji ya sa baki barta a silent din nan ba" Sosa kai na na yi dan kuwa na san zai wahala ba ta silent, ina yawan saka waya ta a silent saboda qarar shigar messages, dan haka se na ce masa, "Ka kira kar mu yi loosing hope wataqila Allah ya sa ta ga hasken wayar ta dauka se mu ce ta bude mu" Kira ya hau yi shiru ba ta dauka ba, be gaji ba haka ya dinga gwada wa from time to time har Allah ya sa bacci ya ɗauke ni ina kwance qasan carpet. Bamu muka farka ba sai da qarar buɗe qofar parlour ta tashe mu, lokacin gari ya waye tangararau, kallon Yah Maheer na yi da ke miqar da hannun shi da ya min pillow da shi, a guje na wuce su na faɗa banɗaki, saboda yanda na ji kamar an turo min bahaya nan take. Se da na yi wanka na yi alwala sannan na fito na koma parlour na dauke dustbin na je na zubar da fitsari na aje bakin tap na kunna ruwa ya dinga zuba, dan na yi aniyar dirzar shi kwarai. Kafin na gama Yah Maheer ya yi alwala ina shiga na tarar ya na saka kaya ni ma kayan na saka mu ka tada sallah. Bayan mun idar ne na shiga kitchen dan yi mana girkin safe, na ɗora ruwan zafi zan fito daga kitchen qefen ciki na ya riqe,kamar an soka min wani mashi a jiki ba a zare ba, a gigice na hau kiran sunan Allah, numfashi na da suka ji ne ya ja hankalin su suka yi waje na da gudu,da kyar na iya nuna musu inda ke min ciwo. Abun hawa Yah Maheer ya fita ya samo, kan ya dawo na saka doguwar riga da hijabi, mu ka wuce asibiti. Se da Yah Maheer ya gama duk wani abu da ya kamata a yi kafin a duba mara lafiya kafin likita ya hau duba ni, Wanda ya ke gynocologists ne likitan,duk wasu gwaje gwaje da scanning da komai an yi min, tun qarfe takwas da rabi muke asibitin har biyu da rabi ba mu koma gida ba, na gaji na jigata matuqa. Jini ne kawai ke zuba min duk da an siyo pad na saka ya b'ata pad din ya b'ata Kaya na,tunawa na yi lafiya muka shigo daga sa hannu a duba lafiyar mahaifa ta jini ya ɓalle, se na sake fashe wa da kuka akan wanda nake yi, a zuciya ta ina ayyana shikenan sun fasa min mahaifa. Likita ne ya samu waje ya zauna bayan ya karbi result ɗin ultrasound da aka yi min ya na duba wa, jinjina kai ya dinga yi sannan daga baya ya hau rubuce rubuce a saman wanda ya yi tun zuwa na, abinda ke qara bani tsoro kenan, duba da a qalla an yi amfani da takarda ta kai hudu. "Allah ka shiga lamura na, shike nan duk zuwan da zan yi se an cika takardu ni wai ba a ganin wani sauqi a tattare da ni ne?" "Madam ki kwantar da hankalin ki, matsalar ki inshaa Allahu Mai warkewa ce, saboda akwai matsalar hormonal imbalance da ke damun ki, sannan kuma....matso matso nan ku gani,domin abu biyu zan sanar da ku yau game da lalurar ki" Matsawa mu kai daga ni har Yah Maheer mu ka leqa wata blank takarda dake gaban Dr. Nan da nan ya hau zane, i am a science student so na san zanen mahaifa ne wannan, nan da nan na gane akwai matsala a zanen da ya yi mana. "Yauwa kun ga nan, haka zanen mahaifa yake a cikin kowacce mace, se dai taki an samu matsala, wadda inshaa Allahu ba za mu iya cewa matsala bace completely tunda za a iya samun maganin ta, kin ga dai wannan ovary ɗin taki tafi wannan girma ko? Ta dama ta fi ta hagu ko?" Daga masa kai na yi ina jin cewa ohhhh shi yasa nake jin ciwo kenan a wajen "Yauwaa to dalilin jin ciwon ki kuma ya haɗa da over weight, Wanda if I could remember na faɗa maki ki rage qiba times without numbers, Ina ga zuwan ki huɗu nan ina ce maki ki rage qiba, ki yi watching diet din ki ko ba ai haka ba?" "An yi amma Dr. Ina qoqari, weigh din ne baya raguwa size ɗina ne kawai ke raguwa ya zan yi? Na ce ka rubuta min magani amma ka ce is not a good idea gwanda na rage da kai na, ya zan yi?" Kuka nake sosai har da majina saboda tsananin tausayin kaina,dan ma Allah ya sa ciwon da nake ji ya ragu sosai saboda pain killer da na sha bayan na sha Nutrimilk da biscuit. "Madam ki yi hakuri ki dena kukan saboda kar ki yi ciwon kai, matsalar in baki rage qiba ba nauyin ki ya dinga pressing ovary ɗin ki, shi ke sa ki bleading musamman in kin yi tafiya me nisa, ko kin yi aiki me yawa, shi ke sa ka ki riqewar qafa da baya in kina tafiya ki kasa gaba ki kasa baya ki dinga jin sharp pain a abdomen din ki, so I strongly suggest that you reduce your weight ,ok?" "Inshaa Allahu za mu qoqarta Dr. Za ta rage, to yanzu menene abu na gaba da ka ke so ka mana bayani akai?" "Yauwaa abu na gaba ina so na sanar da ke kar ki d'aga hankalin ki Allah shi ke bada haihuwa sanda ya so kuma ya bawa wanda ya so, kin ga wannan mahaifa taki da ta fi girma za ki iya daukan ciki da ita fa, har cikin 'yan biyu ko iya abinda Allah ya nufa su zauna a ciki, so is not a problem, matsalar shine wannan jinin da kuma wannan ciwon, ki dage ki rage nauyin naki komai zai daidaita" Zama ya yi ya rubuta mana duk abubuwan da ya kamata ina ci, da wanda be kamata ina ci ba, sannan ya rubuta min magani, godiya muka masa sannan mu ka tafi gida. Kafin mu isa an kira la'asar a qofar gida yah Maheer tsaya dan ya wuce masallaci ni kuma.na shiga gida, cikin sauri Suwaidatu ta zo waje na ta na jera min sannu, ina shiga gidan na ga ta gyara shi sosai, ta dafa abinci, shinkafa da miya, se a sannan na tuna da yunwar da nake ji. Tabbas yawan zama da yunwa ne ya jawo min ulcer, Dan zaman mu a gidan nan mun wahala da yunwa, mun fahimci yanda marasa shi suke kwana in basu ci ba, mun wa'azantu da ayar Allah matuqa gaya. Se da muka jira Yah Maheer ya dawo sannan mu ka ci abincin, dama haka muke in abinci bai da yawa sosai to haduwa muke mu ci sai a tashi kowa ya qoshi,amma in aka raba sai kowa ya ci ya na neman qari. Bayan ya dawo mun ci abinci mun sha ruwa na kora magani na, se na ji tausayin Yah Maheer na shiga ta a hankali, duk kudin da na dawo da shi ya qare a wajen neman lafiya da cin abincin mu, sannan shima na hannun shi ya qare ga wata be yi nisan da za a saka ran za a samu wani abu ba. Hawaye ne masu mugun zafi ke sauka daga ido na, da sauri ya Kalle ni,ya dawo kusa da ni, sannan ya sa hannu ya na share min,cikin Muryar lallashi ya ce, "Kar ki damu baby na you will be fine inshaa Allahu kin ji? Allah ya baki lafiya baby na" "Ameeen, ka yi hakuri,gaba ɗaya yawan rashin lafiyar da nake yau da gobe ya sa baka aje komai ba da zaka mora a rayuwa, i am so sorry" "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, wannan maganar daga ina kuma? Ke ki ke wannan furucin? Ke da na sani yarinya mai tawakkali mai sanin ya kamata? To lallai yau kin ban mamaki, kin manta Allah shi ne ke azurta wa shi ke barin bawa cikin babu? Me zan tara? Wa zan tara wa kuma? Dama ke zan tara wa in ma tarin ne, to ba gwanda ki ci ba ki more? Duk da ba ta haka nake so ki mori abinda na mallaka ba, amma Kar ki manta yawan ciwo da ki ke alkhairi ne, ba a jarabtar bawan da Allah baya so da jinya domin jinya kankarewar zunubi ne, ki yi saurin cire tunanin nan a ran ki tun kafin mu bata kin ji ko?" "Eh na ji, ka

Chapter 26 of 30