Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da wata riga fara mara hannu guda, hannu dayan kuma guntu ne ko damtse na be rufe ba, sai makeken tambarin heart a jiki wanda aka rubuta I LOVE YOU a qasan heart d'in rigar ga zauna a saman qirji na sa kyau ta qara bayyanar da su, sai na d'aura wani zani na materil me kama da skirt irin me fad'in nan sosai ta qasa ta sama ya kama mutum,Baba ne ya siyo mana ni da su Addah Ummu inda daf da biki na ya qaro min da wata riga da yake kiran ta rigar amare, dan kuwa sak irin ta amare ce amma purple. Kai na a gyare yake na tsaga tsakiyar shi na kwantar da shi ya yi kyau sosai, ina ta rubuce rubuce a wani d'an qaramin littafi na, domin Allah ya zuba min son yin rubutu,tin a da can, haka nan zan qirqiri magana mai ma'ana na rubuta na ajiye a littafi, ina tsaka da rubutun na ji muryoyi na tashi a tsakar gida ana ta hayaniya sosai, tashi na yi na jawo hijabi na da ke saman qofar d'aki na a koda yaushe saboda baqi na zira na idasa fita,mata na gani sama da biyar suna tambayar nan ne gidan D'an azumi?Maimunah ta ce ba nan bane, dan ba da haka ta san sunan shi ba, wata dattijuwa ta kafe ta ce nan ne, saboda nan aka musu kwatance,ko da na leqa sai qanwar Yah Maheer da ni ban san ta a fuska ba amma na san ta a waya ta ce, "Goggo nan ne, ga ma Mahreen d'in can, kama suke da Ummu" (Ta san Addah Ummu tinda ta kan je kano gidan Kawun su) Baki na washe alamar na san su tinda sun nuna sun san ni suma, shiga suka yi na wuce gaba muka je parlour, suka zazzauna, na zauna a qasa a gefen kujera na hau gaishe su, anan ne na ji wata ta na ta tsokana ta da 'yar qauye se na gane akwai wasa a tsakanin mu, ni dai ban tanka ba ina dai ta murmushi, da sauri na je na deb'o musu abinci,dama na dafa shinkafa da miya da kifi na had'a musu da kayan gara da ruwan sha na ya ka musu lemon da ya rage bamu sha ba, se na basu waje dan su ci na koma d'aki. Ina kwance ina ci gaba da rubutu na qanwar shi ta shigo saboda ta na fama da tsananin ciwon kai, nan take sanar da ni ita ce Abidah da muke waya sanda ina gida,hira muka dinga yi kamar dama mun san juna,har Yah Maheer ya dawo, suka hau hira, ta na masa magana akan matsalar ta, ya na nuna ba wani aljanu dan dai ya kwantar mata da hankali ta dena sa damuwa a ranta, se bayan ya fita ne ta yi murmushi ta ce, "Kin san Ustazai shi se ya nuna ba wani aljanu ko sihiri in kama addu'o'i in yarda komai ya same ni daga Allah ne" "Allah sarki, ai maganar shi gaskiya ne ke dai ki ta addu'a Allah ya baki lafiya" "Hummm Ameen to, wato kin bi bayan mijin ki ko?" Dariya na yi cike da jin kunya na sauka a gado zan maida hijabi na se ta ga shigar da ke jiki na, salati ta saka se da ta tsorata ni, sannan ta ce, "Lallai ana nan ana rikita d'an uwa na" Da sauri na fice a d'akin ina dariya, a raina ina ayyana 'A shigar qananan kaya na me ki ka gani baiwar Allah?' Ko da na shiga na ga sun ci abincin amma ita cousin d'in shi Ramatu bata ci ba, ashe ita da Abidahn ba su cin kifi ne, ita Ramatu haka take, ita kuma Abidah saboda cikin da ke jikin ta ne a lokacin, se na ji babu dad'i nan take na ce zan dafa masu wani abun ko da taliya ne, suka qi amincewa suka ce tafiya ma za su yi za su koma can garin mu wato Liman katagum driver da ya kawo su na jiran su, dan haka har bakin.qofar gidan na raka su bayan na debar masu kayan gara na hada da plates dan na ga mafitan sun kusan qarewa shi yasa ban basu ba suna da yawa. Bayan tafiyar su muka koma ciki yana qara yi min bayanin su, ashe mutanen gidan su ne da qanwar baban shi da suke uwa d'aya uba d'aya da baban shi,hamdala na dinga yi da na dora hijabi a saman riga ta basu ga komai ba. Mu na shiga na cire hijabi na na rataye idanu Yah Maheer ya qura min kamar be tab'a ganin abinda ya burge shi a duniya ba sama da ni, da sauri na dau littafi na da nake rubutu a ciki zan fita ya kuwa sa qafa ya tokare qofar ya rufe........ Nima na zare hannu na a rubuta sirrin masoyan.... Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all. 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 10: Watan mu uku mu na tsikarar amarcin mu da tsinke ba tare da wata matsala ko damuwa ta gifta mana ba,Yah Maheer ya yi nasarar wayar min da kai ta hanyar nuna min cewar Ustazai su ne gidan soyayya kulawa qauna da tarairaya,ya yi qoqari ya kafa kan shi a jaririyar zuciya ta ta yanda bayan qima daraja da kirkin shi da nake gani akwai wani lamari mai girma da ni kaina ba zan iya bayyana shi ba ko na yi bayani akan shi game da abinda nake ji akan Yah Maheer, a hankali na fara mantawa da komai da kowa da ke cikin zuciya ta, na maida hankali wajen biyayyar aure. Ba tare da mun sani ba ashe ran Goggon shi wato qanwa ga mahaifin shi ya b'aci sosai akammu, ta na ta fad'a akan bamu je garin mu ba,labarin ya riske mu ta wajen qanin shi inda ya ce mana, Goggo fa ta ce, "In ba ya raina mutane ba ace har yanzu wata uku kenan da yin bikin su amma be ga damar ya d'auki matar shi ya kawo ta garin nan ba ya nuna ta a dangi, wanda itama dangin ta ne ko ba komai ta san mutane tinda ba a nan ta tashi ba, to ai shikenan, in ya ga dama ya kawo ta, in be gadama ba ya riqe ta a can ya cinye" Sanda muka ji labarin nan dariya kawai Yah Maheer ya yi, dan shi be cika announcing abu ba in zai aikata se dai kawai a ga ya yi, kwana uku da yin haka ya same ni ina zaune ina kallon wa'azin shaikh ja'afar Mahmoud Adam (Allah ya masa rahama) wanda Baban mu ya ke bamu in an yi mana aure, (tare da wa'azin Shaikh Bn Uthman Kano na Tara Na Ma'aurata) suna na ya kira wanda ya sauya min tin ina watanni biyu da zuwa gidan, wato "Baby Na" "Na'am Husband?" "Ki shirya inshaa Allahu gobe juma'a za mu je gida LK (Liman katagum)" "Allah ya kaimu, amma da ka sani ka sanar da ni da wuri," "Kar ki damu kawai ki shirya gobe za mu tafi" "Allah ya kaimu" Ba b'ata lokaci na shiga shiri, na had'a mana kayammu a akwati guda, hatta da wanda za mu saka na ajiye mana da takalmi da komai da za mu buqata, duk na had'a, dan ni ina da wani hali bana yin abu a makare, ina fara shirin yin abu kafin lokacin abun a koda yaushe, saboda bana son jira, ba kuma na so a jira ni. Washegari kuwa kamar yanda ya yi alqawari muka samu adaidaita sahu ya kai mu tashar zuwa qauyen mu, baya ya kama mana gaba d'aya, dan haka mutum biyu kawai aka jira suka shiga gaba mota ta tashi sai LK. Da yake ranar kasuwar mararraba ne mun sha wahalar cunkoson hanya kafin muka samu muka isa da yammar ranar, jiki na sanye da wata koriyar atampa wadda ta qara bayyana haske da kyawun da na qara, nan da nan gida ya d'auki murnar yara da manya ga Yah Maheer da Aunty Mahreen, murnar da har gobe idan na je yaran nan na yi saboda qauna ce Allah ya sanya a tsakanin mu ta musamman (Ummeeta da dikkan yaran gidan ku Allah ya yi maku albarka) Sai da na fara gaishe da Mahifin Yah Maheer wanda ya kasa b'oye farin cikin gani na, ya tambayi lafiya ta, ya tambaye ni ko ina waya da mutanen gida suna lafiya ko? Na tabbatar masa da komai da kowa lafiya qlou, sannan na shiga d'akin Ummaa muka gaisa wadda ita na sani a matsayin mahaifiyar shi, wanda a wannan lokacin ban san takamaimai cikakken tarin asalinah mahaifiyar shi da ta haife shi ba,ina ka saka ina ka aje aka shiga yi da mu, abinci kala kala,saboda dama duk ranar juma'a sun fi yin girki na musamman saboda suna bawa ranar girma da daraja. Sai na ji ciki na ma ya cushe na kasa cin abincin sosai,saboda ganin yawan shi, bayan na kammala cin abinci na yi sallahr la'asar na huta ne Umman su ta sake shigowa ta zauna fuskar ta d'auke da mad'aukakin murmushi wanda ni a ranar na fara ganin ta, ita kuma ta jima da sani na,gaisuwa ta sake dasawa a tsakanin mu sabuwa, (abinda na kula mutanen garin mu na girmama gaisuwa) ni d'in ma sake duqar da kaina na yi na gaishe ta, Mama ma ta shigo, (matar Baban Yah Maheer) muka sake gaisawa,tin a wannan lokacin na fuskanci wani yanayi a fuskar Maman, wanda ba zan iya nuna yatsa na akai ba, dan kuwa muryar ta da fuskar ta a sake suke a gare ni amma haka kawai zuciya ta bata nutsu da gaisuwar da muka yi wa juna ba kamar akwai fake caring da take nuna min ban dai gama ganewa ba, tsarabar da na zo masu da shi da yaran su na miqe na bud'e akwati na na dakko na bawa Umma, murna ta yi ta kalli kishiyar ta ta ta ce, "Lami gashi a raba" Tsinke ta danna a baki ta hau sakace sannan ta miqe qafafu tare da tura d'ankwalin ta bayan kan ta ta na sosa kan nata can ta maida hannun tsakiyar cinyoyin ta ta ce, "Ah ah yaya raba dai" Ganin yanda ta yi maganar se na ji jiki na ya yi sanyi, ita kuwa Umma fuskar ta dauke da yaqe ta ajiye leda gaban ta, ta bud'e ta hau rabo. Sashe shida ne a cikin babban gidan na su Yah Maheer amma se na ga ta yi kaso takwas,kowa ya samu Omo sabulu da biscuits da sweet, yaran da ke tsaye basu tafi ba Umma ta dinga kira ta na basu, suka karb'a suka tafi kaiwa kowanne sashe a gidan, sauran kason ta had'e su waje d'aya ta ce a zo a kai wa gidajen da ya kamata a sanar da su matar Maheer ta zo. Ranar haka na kai magariba ina ganin gata da kulawar dangin miji kuma dangi na, murna da farin ciki duk ya cika zuciya ta,na gaza boye farin ciki na, amma sai dai ina da wani hali, wato rashin sakewa da mutane da farkon had'uwa, sai na gama sanin halin kowa sannan zan fito da nawa na addabi jama'a, wannan dalilin ne ya sa bana dariya sai dai murmushi bana kuma Uhmmm bana um-um,komai aka yi da ido nake bin kowa ina karantar kowa. Bayan magariba ina zaune ni d'aya a d'aki yara biyu suka shiga, Hafsat da Safiyya suka sanar da ni iyayen su na can na jira na a ci abincin dare,sannan kuma mu yi hira. Tashi na yi na gyara riga ta sosai a jiki na na sanya hijabi na bi bayan su, duhun dare ya fara dan haka sai na kunna fitilar jikin waya ta ina haska mana hanya har muka shiga sashen babban yayan su na gidan wanda yake da mata biyu a wannan lokacin, yara na gani da yawa da kuma sauran matan qannen Yah Maheer Aeesha da Maryam (Allah ya mata rahama) Maryam mace ce mai tsananin fara'a da tsokana, dan haka sai na samu kaina da qaunar ta cikin raina. Sai Yaya wato Maman Ummee da amaryar ta Halima da suke kira da Umman Muheebbah,mata ne masu barkwanci da son mutane tare da girmama baqo, mata ne da in har zan bayyana dikkan mutunci da soyayyar da suka nuna min to fa se mu qare page din nan kaf ban gama ba. Aysha matar qanin Yah Maheer kuma ta b'angaren mahaifiyar shi a matsayin Innar shi take, macece mai fara'a ta nuna min qauna kwarai, hira akai ta yi ana abun dariya bayan mun kammala cin abinci ni dai daga murmushi se murmushi ba na jefa baki na a maganar su,cikin zuciya ta kuwa har na hango ni na sake a cikin su ba qaramin dariya za a sha ba, domin kuwa da alama kallon 'yar birni suke min se kace su d'in qauyawa ne, ita Yaya wato Maman Ummee a koda yaushe qoqari take ta jefa min kalmar turanci in muna magana, se a yi shewa a tafa jin Yaya ta yi turanci, ni kuma dariya kamar na yi yaya amma haka zan guntse ta in maye gurbin ta da murmushi. Ban bar wajen su ba sai qarfe goma na dare da Baban Ummee ya dawo muka gaisa na yi musu sallama, da fari suka ce na yi zama na ai nan se a kai sha d'aya ma ko sama da haka ana hira musamman in an yi baqi, na nuna masu bacci nake ji, nan kuwa qasan raina ina so na zame ne na je wajen Yah Maheer da ke ta zabga min saqonni kala kala na ya yi kewa ta in je mu gaisa mana, ai kuwa miqewar nan da zan yi sai jin sallamar shi na yi, ashe tare suke da Baban Ummee suna hira a waje, murmushi na yi a raina ina ayyana, 'Ohhh Yah Maheer ba ko kunya, da kana tare da Yayan naka ka ke min wad'annan messages, Ustaz kam a ido gashi nan tsaf' "Kallon kuma fa? Ai tinda kin zo gida yanzu kin barshi ya huta ko?" In ji Umman Muheebbah da ke tsokana ta, Maman Ummee da muke kira da Yaya kuwa ta ce, "Yo ai shine ya wani kafe ta da ido ba zai iya hakuri ba se da ya biyo sahun ta" Nan suka shiga gaisawa da juna cikin mutuntawa da nuna tsantsar shaquwa da qaunar da ke tsakanin su, tin a nan na fahimci yanda matan yayan nashi ke son shi kuma suke wasa da dariya da junan su cikin nishad'i, ba su yi aune ba na zame jiki na na koma d'akin Umma wadda har ta gyara min gado ita ta sakko qasa wai anan za ta kwanta, ai kuwa na ce sam ba zai yuwu ba, se dai ni na kwanta a qasa ita ta hau gado. Ja in ja muka hau yi da ita, qarshe ta yi rantsuwa ba za ta hau gado ba ni zan kwanta a kai, ba haka na so ba dole na je na yi alwala na yi sallar isha'i na yi addu'o'i na sannan na sauya kaya na na kwanta, nan fa bacci ya ce sam be san zance ba, saboda ban watsa ruwa da na saba ba tin ina gidan mu. Juyi na dinga yi gadon na motsi, gani ba kad'an ba,kawai se na ji hawaye na zubo min saboda zafi nake ji sosai. Kamar Yah Maheer ya karanci menene damuwa ta, suna hira sama sama da Baban shi a d'akin Baban se ya fito ya kira ni, na amsa murya a shaqe irin ta masu kuka, ko da na fita sai na ji kamar na je gare shi ya rungume ni kamar yanda ya saba min in ina kuka, a hankali ya min rad'a ya na tambaya ta menene matsalar, cikin shagwab'a da kukan da nake yi na ce masa, "Ina so na yi wanka ne, ni zafi nake ji, kuma na kasa bacci" "To ki yi hakuri mu je na ja maki ruwa ki watsa" Ji na yi gidan ya d'auki shiruuuu alamu ne na ko kowa ya yi bacci ,ko kuma sauraren mu ake yi, ni dai ba ruwa na, ko ma meke faruwa ni dai zafi nake ji ba zan iya bacci a haka ba,gaba ya yi na bi shi a baya, ya jawo min ruwa ya cika min babbar muta ya miqa min,a tare muka shiga bayin nasu mai matuqar girma da tsafta irin bayin nan na qauye mai bud'add'en sama, ya na tsaye a bakin qofa na yi addu'a na qarasa shiga na yi wanka na na sake alwala na fito fuskata d'auke da murmushi, shima murmushin ya mayar min sannan ya rungume ni ya na fad'a min sai da safe, nima sai da safe na yi masa sannan ya d'auki butar ya d'ebi ruwa a rijiya shima ya shige bayi. Ban san sanda ya fito ba ma saboda bacci ya yi awon gaba da ni ina kwantawa. Da asuba kowa ke tashi sallah a gidan sab'anin wasu gidajen da se rana ta fito sannan za a yi sallahr asuba suna mantawa da cewa in rana ta fito ba sallar asuba suka yi ba se dai su nemi wani suna su bata amma ba asuba ba kam,muna idar da sallah na ga Mama ta shiga kitchen ta kunna wuta,nan da nan ta dora dumamen tuwo aka dora ruwan kunu(koko) ni kuma ganin haka tinda garin ya dan waye se na d'auki tsintsiya na share tsakar gidan tass wanke wanke sau biyu suke yi ashe watarana uku ma, dan haka ba tare da na sani ba na dai ga an tara wanke wanke a bayan d'akunan su kawai se na ja ruwa a rijiya na fara wankewa, nan fa qanwar Yah Maheer mai suna Nafeesah wadda 'ya ce a wajen Mama ta fito ta taya ni muka wanke, Zainab kuwa ta wanke band'aki sai ga gida ya yi tarrr da shi. Duk abinnan da ake idanun Baba ya na kai na, kuma fuskar shi ta bayyana farin cikin da yake ciki dan be boyuwa a wannan lokaci,se da na gama sannan na cire takalmi na a yashin da ke malale a tsakar gidan na hau saman simintin da ke gaban d'akunan gidan na tsugunna a qofar d'akin Baba wanda labule ya rufe shi me shara shara, shi ya na hango kowa, amma kai na waje ba za ka gan shi ba, ina durqushe a wajen na yi sallama ya amsa,na gaida shi, ya amsa tare da yi min sannu da aiki da sanya albarka, Yah Maheer ne ya yi gyaran murya, ban san sanda murmushi ya kwace mim ba, wato ya na sanar da ni he is awake fa shima, dan haka na d'aga murna na ce, "Ina kwana Yayah" "Lafiya qlou kin tashi lafiya?" "Lafiya qlou alhamdulillah" Shiru muka yi na tashi na shiga sauran sashen na gaishe su sannan na koma d'akin Umma na d'auki waya ta, message d'in Yah Maheer na gani, hannu na sa na latsa wajen na fara karantawa. *Allah ya yi maki albarka My Baby,zan baki tukuicin aikin da ki ka yi na musamman, amma se mun je gida, za ki ci masa a siyo ? Dan na san yanda ki ke son masa* Murmushi na yi sannan na aika masa da amsa nima kamar haka. *Ameen ya Allah tare da kai Babyn Baba, ka gudu ka buya a bayan Baba ka ke yi min irin wannan maganar ko? Eh zan ci masa please a sa quli da yawa* Da alama ya gama karantawa ne,se ya fito ko kallon inda nake be yi ba ya kwala wa Zainab kira ta je da sauri, kud'i ya zaro d'ari biyar ya bata, ya ce ta d'auki kwano me kyau a siyo masa ta d'ari uku, d'anwake na d'ari biyu. Da sauri kuwa ta karb'a ta yi kitchen ta samu kwanuka ta fice daga gidan, d'aki ya koma bayan ya saci kallo na, ni kuma na yi saurin Kawar da kai na gefe na yi kamar ban gan shi ba. Ba jimawa Mama ta kawo min dumamen tuwon masara miyar kuka, ga kunu (koko) Baba kuma ya ce a kawo min ruwan zafi, ya dakko gwangwanayen madara peak da millo ya miqo min,gwangwnain millo d'in ko bud'e wa ba a yi ba sabo ne, se robar butter me dauke da sugar a ciki, se na rasa ma me zan ci ne a ciki ga masa na hanya, kamar Baba ya karanci me nake nazari akai sai ya ce, "Ki had'a shayi me kyau ki sha da farko komai se ya biyo baya," Murmushi na yi sannan na ce masa, "Na fi son koko, Baba, bari na sha kokon kawai" "To ki zuba madarar a ciki zai fi riqe ciki" Ban sake masa musu ba tinda harka ta ce dama wato had'in kwad'ayi, nan da nan kuwa na loda madara abuna a cikin kunun na hau sha, ban gama sha ba Zainab ta dawo, se abun ya bani mamaki ganin masar da yawa, qin karba na yi na ce ta kai a debar masu, suma suka qi karba wai na ci na rage, qarshe dai da kaina na d'akko kwano na debar masu har Umma na cewa ashe dai bani da cin abinci? Dan ta kula tinda na zo tsakura nake kawai, ko dai akwai abinda nake so ne na musamman? Na ce mata ah ah haka cin abinci na yake dama, d'anwake kuwa Yah Maheer aka kai wa suka ci shi da Baban shi suna hira abun su kamar wasu abokan juna. Da misalin qarfe sha biyu na rana na yi wanka na gama shiri na ci ado na burgewa na fito hannu na dauke da jaka ta baqa ina gyara sanya takalmi na sau ciki a qafata, Ummee da zata raka ni gidajen 'yan uwa ta sha gayun ta itama, haka nan Allah ya dora min son yarinyar tin a wancan lokacin har a yanzu, saboda kula da na yi itama ta na so na kuma ta na da hankali,ita ce babbar 'yar Yayan Yah Maheer, ji na yi ana mata lissafin gidaje wajen guda ashirin, nan da nan hankali na ya tashi, dan kuwa da alama duk a qafa za mu yi yawon nan, zare ido na fara, nan take Yah Maheer ya fito ya na min dariya ya ce, "Umma ina ga a bar zuwa bakin rafi sai gobe su yi masu fita ta musamman suma" "Eh ka kawo shawara kuma, to Ummee kin dai ji ko? Ku na fita yanzu da gidan Gurama za ku fara sannan gidan......." Haka Umma ta sake jero lissafi har a wannan lokacin ban ji kwanciyar hankali ba, sai kawai a raina na ayyana, 'Na shiga uku, dama an ce fa garin nan kusan dika 'yan uwa ne, does that means sai na je dika gidajen da ke cikin garin nan' Kamar wanda ya karanci damuwa ta,Yah Maheer ya zo ze gifta ta gefe na a hankali ya ce, "Se fa kin je kafff gidajen da ke cikin garin nan an gaisa dan su ga matar d'an su" Da sauri na kalle shi idanu na na son su zubda ruwa, shima cikin dariyar wasa ya ce, "Ke wasa nake maki, ku je se kun dawo Allah ya kiyaye nima zan d'an fita anjima" "Allah ya dawo da kai lafiya" shine abinda na ce kawai. Fita muka yi na wuce sashen sauran matan gidan ana ta kallo na kowa ka gani fuskar shi d'auke da fara'a, har muka fita gaishe gaishen dangi........... Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all. 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 11: Gidan Gurama shine gidan da muka fara shiga kamar yanda aka umarce mu,gida ne na fulani dan kuwa ka na shiga za ka ga hakan saboda mutanen gidan suna da hasken fata da qaramin jiki irin na fulani, sai da mu ka dinga bi sashe-sashe muna gaishe da mutanen gidan har sashen kawun shi wanda yake qani ne ga mahaifiyar Yah Maheer ba tare da na san alaqar da ke tsakanin su

Chapter 8 of 30