ba har se aikin maganin ya qare a jiki na.
Ganin haka ne ya sa na sawaqe wa kai na wahala, gashi ba zan iya ce mata kar ta bani ba se ta ga na raina qoqarin ta, tunda akwai wadda ta taɓa sanar da ni cewar a garin Kebbi mace ta nuna ta na son ki da alkhairi shine ta baki tsarabar maganin mata, a haka dai maganar bani maganin mata ta tashi ba a ban lallen da ruwan ba se aka bani gumba da madara na sha cikin iko na Allah sai ban zubar da jini ba, amma fa haka nan Yah Maheer da kan shi ya ɗauke wuta, za mu kwana waje ɗaya yanda muka saba maqale da juna amma ba zai nemi komai a waje na ba har safiya ta waye, haka da safen ma za mu koma baccin safe kamar yanda muka saba amma haka za mu tashi ba abinda ya gitta, gajiya na yi da wahala na cire rai akan komai na sa wa raina se maganin ya bar aiki jiki na komai zai koma mana normal, tunda ni kaina se na ji ba zan iya fara miqa kai na da kai na ba se ya nema.
Rayuwar mu muka ci gaba da gudanar wa kamar wasu 'yan uwan juna na jiki, zama muke mu sha hira duk ta san mutanen gidan mu a baki na wanda dama zai wahala ka zauna da ni baka san Mama...Baba...Innata...da yaran gidan mu ba gaba dayan su, saboda su ne rayuwa ta, yanda kuwa Yah Maheer ke kula da ni be taɓa damun Naman Abdurraheem ba dan ban taɓa gani ba a fuskar ta ko a maganar ta, duk watarana ta kan tsokane ni in ta ga ya min wani abu takan ce, 'Uhmm ka ga masoya/ mu ma dai Allah ya sa mu na da masoyan' wata rana kuma in ya yi wani abu da ya burge ta sai dai ta hau yaba masa, ba dai ta kushe ba, ta ce na roqi Allah ya sa ita da mijin ta su koma kamar yanda muke, murmushi na kan yi na janyo wata hirar a bar maganar mu.
Mu na nan zumuncin mu na ta qara qarfi da Maman Abdurraheem, zaman lafiya na ta wanzuwa tsakani na da Yah Maheer, sai dai kun san a koda yaushe ba a rasa sabani irin na harshe da haqori, to muma mu na samun wannan lokaci zuwa lokaci,watarana mu na zaune ana hirar gida da ni da Yah Maheer sai na ce,
"Kaiiii amma ban taɓa zuwa gidan da ya yi bala'in yi min dad'i ba sama da wanda mu ka yi d'innan ba hayaniya,ba takura ba tashin hankali,zallan zumunci aka sha aka dawo,komai cikin sauqi gwanin sha'awa"
Wata kalma Yah Maheer ya jefe ni da ita da ta sanya ni hantsilawa daga kujerar da nake zaune na kifa qasan carpet ba shiri tare da sauke masa idanu na da ke cike da tsantsan mamakin kalaman shi.
"Me ka ce? Me ka kira ni da shi?"
Cikin nuna rashin danasanin kalaman shi ya maimaita abinda ya ce,
"Cewa na yi dole ki ce wancan zuwan ya maki dad'i mana tunda kin haɗa munafurci kin taho"
Ji na yi kamar ya buga min guduma akai na, tsabar yanda na ji kalmar munafurcin ta dake ni, mutumin da banza ko wani sunan zagi be taɓa haɗa ni da shi ba ke faɗin na haɗa munafurci, to wanne munafurcin na haɗa, nan da nan na ji ido na ya taru da hawaye, Suwaidatu da ke zaune a gefen mu sai ta hau raba ido a tsakanin mu, zama na yi da kyau ina fuskantar shi na ce,
"Wanne irin munafurci na haɗa ni kuwa har da ban sani ba tsahon lokacin nan da muka ɗauka da dawowar mu, ashe na haɗa munafurci shine ba ka taɓa faɗa min ba? Ba dan an dakko maganar gida ba kenan haka za ka dinga min kallon munafuka ba zaka sanar da ni komai ba ko?"
Nan take idon shi ya nuna nadamar abinda ya faɗa amma bakin shi ya kasa qaryata kalaman shi, zama na gyara na ce se ya sanar da ni munafurcin da na haɗa, nan ya fara zayyano min wani zancen qarya da aka tuqa shi aka ce ni Mahreen ni na faɗa kuma ni na hada komai, ashe bayan tafiya ta Bauchi daga liman Katagum har gaban manya aka zauna aka tattauna, direct a gaban mutane Yah Maheer bai kare ni ba saboda kar a ga ya bi baya na sai ya furta musu cewa 'Ashe Mahreen ita ce munafukar da ta haɗa komai ta tafi' nan take Kabeer ya ce 'Kai ma ka san ba zata taɓa aikata hakan ba a dai sake bincike'.
Wani irin duhu na ji ya mamayen ido na tsabar hawayen da ke zuba min ba na gani sosai kwata kwata, nan take na zauna na zayyane masa duk abinda ya faru iyakar gaskiya ta,alamun gamsuwa da kwanciyar hankali ne suka bayyana a saman fuskar Yah Maheer wanda ya bani mamaki matuqa, kenan da ban masa bayani ba ya yarda ni munafuka ce har ya iya furta hakan a gaban mutane? A duniya be taɓa min abinda ya qona min rai irin wannan ba, wani irin haushin shi da ban taɓa ji bane ya mamaye zuciya ta.
Nan take mu na zaune ya sa waya ya kira Kabeer ya bashi labarin kaff da na bashi, ina Jiyo sanda kabeer ya ce masa,
'Ai na faɗa maka ba zata taɓa yin abinda aka ce ta yi ba, habaa kowa fa da kalar tarbiyyar shi, kuma mun san halin kowa, kowa da abinda in aka ce maka ya aikata to fa ba makawa ya aikata ɗin in kuma aka ce maka be aikata ba to fa be aikata ba'
"Hakane, Allah ya sa mu dace ya haɗa kan iyalan mu, Allah ya shiryar mana da su"
"Ameeen ya Allah"
Sallama suka yi da junan su, sannan Yah Maheer ya miqe ya na so ya kama ni dan ya bani hakuri, wani irin kallo na watsa masa da ban san ma zan iya yi masa irin kallon ba har abada, jikin shi ne ya yi mugun sanyi, ya durqusa gaba na ya na so ya kamo hannu na, kuka na fashe da shi sosai, zuciya ta na quna matuqa.
Ina son da yake min?
Ina kulawar da yake bani?
Ina qaunar da ke tsakanin mu?
Ina aminci da yardar da ke tsakanin mu?
Ta ya za a yi abu bana nan iya tsahon wannan lokacin ya kasa sanar da ni?
Ta ya za a yi abu bana nan ya kasa tsaya min har ya kira ni da munafuka a gaban mutane?
Me yasa ba zai bada shaida akai na ba tunda ya san ba hali na bane ba zan taba iya bata zumuncin da ke tsakanin mu ba se dai na gyara.
Miqewa na yi na shige daki na barshi duqe a wajen,ya rasa ma abun faɗa dan ya san na riga na yi mummunan fushi da shi.
Allah Allah nake ya fita Masallaci na siyo katin waya na kira Habibah na ji dalilin da ya sa ta min haka,ina nan zaune na ji ya na faɗin,
"A tashi a yi sallah, se na dawo"
Banza na yi da shi, tunda dama ai da hankali na ba se an fadan na je na yi sallah ba, na san daidai, murguda baki na yi da na ji ya fita, da sauri na yi zillo na sakko daga gado na fita parlour riqe da ɗari biyar a hannu na, Suwaidatu da ta yi alwala na ba wa na ce ta siyo min katin waya na MTN na duka kuma ta yi sauri kar ta jima.
Ai kuwa ta na karba bata jima ba ta dawo, ina nan zaune daga ni sai vest dina me kyau kalar pink da gajeren wandon ta na daure gashi na da ribom kalar pink se pink dankunne qarami da na sanya,ina ta kad'a qafa ina tuna kalar cin mutuncin da Habibah da Mommy matar Abubakar suka yi min, dan wannan cin mutunci ne ya taba mutunci na abinda suka min.
Ina karba na loda a waya ta, ya na gama shiga na nemo lambar Habibah na kira, cikin Sa'a kuwa ta hau ringing ba jimawa ta dauka, ashe an sa ni a handsfree ne ban sani ba, nan na fara tuna mata abubuwan da suka faru na ce me ya sa ta juya magana kai na? Dariya ta yi ta hau yi min maganar banza wadda har yanzu ban gama gane inda ta dosa ba wanda na ɗauki hakan a matsayin shirme da sambatun kare kai.
Muryar Mommy na ji matar Abubakar da Abubakar ɗin kan shi su na dariya nan take Mommy ta daga murya ta min magana, murmushi na yi bayan na gane inda suka dosa, kawai se na kashe waya ta, raina na qara ɓaci ina jin haushi matuqa akan abinda suka min, wato na yarda da su dukan su, kuma a zato na duka daya muke, kullum Mommy ta kawo min sukar Habibah zan hana na ce ta dena saboda kar zumunci ya rabu, ita ma Habibah koda yaushe se ta yi complain akan Mommy da Abubakar, ban tsaya na zama 'yar tsakiya munafuka ba a tsakanin su na yi qoqarin nuna wa kowa kuskuren shi da yanda ya kamata ya gyara ashe ban kyauta ba, shawarar kuma da na bawa Habibah akan kuɗin takalmin ta nan ma da ta ce Isma'il ya cinye shima na yi laifi, kad'a kai na yi tare da share kwallar baqin ciki da ke zuba min a kumatu na sannan na ce,
"Wato su nan su na nuna cewa su 'yan daki ɗaya ne ni da Yah Maheer mu ne bare, duk kalar qiyayyar da suke nuna wa juna ina qoqarin haɗa kan su se suka ware ni suka haɗa min munafurci? To da kyau gwanda da aka yi haka, Allah ya bamu rai da lafiya"
Da kyar na tashi na je na yi alwala na yi sallah, ina sujjadar qarshe ina addu'a tare da kuka a cikin sallah ta akan Allah Ubangiji ya bayyana gaskiya ta ya saka min qazafin da su ka min Yah Maheer ne ya shigo ya ganni ina sallah ina kuka, hankalin shi ba qaramin tashi ya yi ba, saboda shi fa duk abinda za a kai shi qara wajen Allah baya so, nan take ya zauna a gefe na, ina idar da Sallah ya rungume ni ya na bani hakuri, cikin fushi na fizge kai na na ce,
"So ka ke in yi halin nawa na munafurci na ce maka na yafe maka bayan a zuciya ta ba haka bane? Dan Allah ka kyale ni ni"
"Ba zan kyale ki ba Baby na har se kin yafe min, ban fad'i haka ba sai dan bana so su ga kamar na bi bayan ki ne ba tare da an yi binciken gaskiya ba, amma dan Allah ki bar maganar komai ya wuce"
"A wajen ka ba? Yanda suka bata min rai suka yi qoqarin bata suna na ba zan yafe ba,"
"Dan Allah ki yafe ki yi hakuri haba baby na ke fa ba kyau fushi"
Ganin ya na so ya maida abun wasa ne ya sa na kalle shi kallo na ba fa wasa ake ba anan malam, jan bakin shi ya yi ya tsuke amma yinin ranar ba inda ya sake zuwa, daga masallaci se gida ya na faman ban hakuri, ni kuma ina sake hawa dokin zuciya dan gani nake komai ya ce min ma sake raina min hankali yake ni ce munafuka duk qoqarin da nake na daidaita zumunci a tsakanin matan shine na zama munafukar shi, zai kuwa ga aikin munafukai.
Ina cikin wannan fushin ne Uncle Inuwa ya tashi zai yi tafiya, sai Maryam ta roqi azziqin mu ara mata Suwaidatu ta koma wajen ta da zama, ba bata lokaci muka tattara Suwaidatu da kayan ta ta koma wajen Maryam, ni kuma na ci gaba da fushi na, Yah Maheer ya san me ke saurin saukar da fushi na, nan take kuwa ya dinga bani cin hanci chocolates da Apple green din, se ya ciko baqar leda da su ya kawo min ya ajiye ni kuwa dake ban huce ba se na buɗe da ya fita se na dauki ɗaya ɗaya yanda ba zai gane ba a gani na kenan, se na cinye, da ya dawo na ci gaba da fushi abu na.
Wata ranar juma'a se ya kawo chocolates da Apple da chewing gum da biscuits, ya ajiye a fridge ya fita, ya na fita na ja leda na hau ci ina jin dad'i har qoqon zuciya ta ina addu'ar Allah ya kai mu aljannah mu ci na can mu ji ya yake, dariya na ji ta na tashi a baya na,dan kuwa ta qofar kitchen ya shigo parlourn, bata rai na yi baki cike da Apple, na qi na ci gaba da taunawa abunka da me kumatu sutum sutum se suka qara hayewa sama, cikin dariya da hawaye Yah Maheer ya ce,
"Baby na ba Kya fushiiiiii"
Wata iriyar dariya ce ta kama ni ban san sanda na kece da dariya ba, a hankali ina dariya na cinye na baki na na sake kaftar wani, nan da nan aka shirya aka hau hira, ya so na bashi ko da Apple ne na hana, na ce punishment ɗin kira na munafuka ne, ya ce,
"Kashhhh ba Kya mantuwa, to na gode da aka yafe min na horu iya horuwa diba fa ki ga har ramewa na yi"
Daga nan salon namu ya sauya ya koma na masoyan asali, komawar Suwaidatu gidan Maryam ya bamu damar cin amarcin da bamu ci ba a baya, daga ni sai shi,haka muka dinga ririta juna mu na faranta wa junan mu, wasanni ba kalar wanda ba ma yi, goyo kuwa na sha shi kamar zan balla masa baya, in ya qi goya ni se na taso da laifin da ya min, na ce biya na b'acin ran da ya saka min zai yi, ya kan ce,
"Ohhh ni Maheer na shiga uku kamar ni ma ba a min laifi na ke hakuri na kau da kai amma ni an kasa min uziri"
Ina jin shi zan banza da shi se dai ya goya ni ɗin, gani da shegen nauyi amma se ya na kira na da 'yar paper, Wai saboda shi baya jin nauyin nawa, shi yake benefiting da goyon nawa a cewar shi.
Wata rana mu na zaune mu na shan iska da Yah Maheer a parlour sai ga su Suwaidatu an taso su daga makarantar islamiyya ita da su Ameerah sun biyo dan a gaisa anan ne take bani labarin wani gida a baya da mu an yi gobara, matar na da jariri sabuwar haihuwa, nan take na ji hankali na ya tashi, ta na bani labari ita da su Ameerah da suka biyo ta dake unguwar da suka koma ya fi kusa da gidan Maryam ɗin Uncle Inuwa, nan take suka hau bani labari su na dariyar matar yanda ta rud'e, ina jin haka na tsawatar musu ina cewa,
"Ku dena dariya ba kyau, ba wanda ya wuce Allah ya jarabce shi da gobara Allah ya kiyaye mu, ku zo maza ku tafi magariba na gabatowa, a je a yi alwala kafin a fita, kar a manta a yi addu'a kafin a fita kuma a hanya kan a isa gida a na tafe ana azkar kun ji ko?"
"To aunty"
Alwala suka yi ina tsaye ina kallon su ina musu gyara a inda suka yi kure har suka gama suka tafi.
Wannan tsarin alwala in Za a fita daga gida daff da magariba tsarin Mama ne, takan ce,
'Ku yi alwala in ta kama dole se kun fita daff magariba saboda a lokacin shaidanun aljanu ke fitowa cin kasuwar su, gudun kar ka hadu da mugayen se ka yi alwala ka nemi tsarin Allah daga gare su'
Ni kuma se na ɗora da yin azkar a duk sanda na fita magariba ta taho ina tafe ina yi har na isa inda zani, in da yara nake tafe nan ma haka muke yi gaba ɗaya.
******************************
Ranar 5th January shekara ta 2012 rana ce da Adda Ummuna ta haifi 'yan biyu rana ce da ba zan taɓa manta ta a rayuwa ta ba, domin rana ce da ta tara min abubuwa da yawa na farin ciki da baqin ciki.
Bana manta wa da safe na je gidan Maman Ameenah karbar garwashin wuta domin na yi hayaqin habbatussauda da ke cikin magungunan Islamic da Yah Maheer ya siyo min nake sha, ina gidan Mama ta yo min waya tare da yi min albishir da haihuwar da Addah Ummu ta yi na yara biyu mace da namiji, tun a gidan na ke ta murna ina sanar da su abun farin cikin da ya same ni, taya ni murna suka dinga yi na dawo gida na sanar da Maman Abdurraheem wadda ta yi shiri tsaf zata fita unguwa ita da mijin ta da yaron su, fatan alkhairi suka yi mana da sanya albarka suka fita suka bar ni ina ta murna, na kira Addah Ummuna mun gaisa na mata barka tare da sanya albarka, se na zauna ina yi wa Yah Maheer kukan ina so in je in ga yaran, hakuri ya dinga bani ya na nuna min zuwa gida a wannan lokacin ba zai yiwu ba, amma na qara hakuri akwai lokacin da za mu je ɗin, murna ta bata boyu ba har mu ka yi sallahr azahar, mu na nan zaune cikin zafi ba wuta mu na hirar haihuwar Addah Ummu tare da jiran NEPA su kawo wutar 3 o'clock.
Dika-dika Sati ɗaya kenan da yin wata gobara a bayan layin mu, dake in sanyi ya zo haka ake yawan yin gobara a garin Kebbi musamman a unguwar,nan take na ji hankali na ya tashi, da misalin qarfe biyu da arba'in da wasu 'yan mintina Suwaidatu ta zo an aike ta Siyan kayan Miya ta biyo take bamu labarin gobarar, jiki na duk ya mace,daga baya muka koma yi mata faɗan qazanta duk ta dafe alamun bata wanka, Maryam dai ba qazama bace balle na ce ko a can ta ga ana rashin wanka, tunawa da kafiya da taurin kai irin na Suwaidatu ne ya sa na hau yi mata faɗa sosai saboda ta gyara ta dena zama ba wanka daga qarshe nake mata albishir da haihuwar 'yan biyu da Addah Ummuna ta yi mace da namiji, murna ta taya ni sannan ta musu addu'a ina ta jin dad'i a raina.
Kamar wadda aka yi wa wahayi ina zaune kawai se na kalli kai na, kamar kullum baqar shimi ce a jiki na me siririn hannu da guntun wandon jeans,tashi na yi na shiga daki na dakko wata doguwar riga ta armless na sanya na daura zanin atampa ta me adon flower purple da milk sannan na kalli qofa na ga hijabi na na nan saqale kamar kullum, zama na da abinda be fi minti huɗu ba mu ka ji an buɗe gate ɗin gidan namu da qarfi an shigo ana ihun.
"Malam Maheer gobara ! malam Maheer gobaraaaaa !! Ku na ina Gobaraaaaa !!!"
A guje mu ka fita har mu na rige-rige da ni da Yah Maheer da Suwaidatu wajen fita daga parlour....................
*Assalamualaikum mutanen kwarai masu albarka...kamar yanda na nemi shawarar ku wasun ku sun amsa ni da karrama wa da mutuntawa, dan haka inshaa Allahu za mu raba novel din Mahreen kashi biyu, da zarar kashi ɗaya ya qare wanda yake kyauta ne, kashi na biyu zai fara shi kuma zai zo maku ne a matsayin paid book da yardar Allah sai dai ni ba zan karbi kuɗi ba se bayan na kammala gaba ɗaya saboda halin yau,ba zan iya typing kullum ba, kuma ba zan yi alqawarin ga time da zan na posting ba duba da yanayin wasu uzururruka da nake da su,duk mai son ta shiga group din paid book ta min magana ta PC sai na saka ta a duk sanda na gama part one sai a fara part two d'in bayan na kammala dika sai a yi payment, bana son haqqin jama'a a kai na tunda Allah kaɗai ya san gawar fari shi kuwa bashi masifa ne in ba a sauke maka shi ba sanda ba ka a duniya...dan haka se na kammala za a yi payment,wataqila in na tuna 'yan kuɗaɗen na maida hankali na gama da wuri😂😂 kar ku ga Lehi na wa ya qi kudd'i??😂 Allah ya sa mu dace da rabon alkhairi.*
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 30:
Mu na fita mu ka ga wani bawan Allah wanda ni ban san shi ba amma Yah Maheer ya san shi ya na mana nuni da maqotan mu, wato gidan Maman Abdurraheem ya kama da wuta, ginin mu a Manne yake da juna,hankali tashe mu ka nufi qofar sashen nata, gani muka yi qofar a rufe take, of course dole qofa ta zama a rufe mana tunda ba sa gida? Ta baya muka zagaya a gigice ni da Suwaidatu hankali na tashe na bude windown ta na kitchen wani hucin zafi ne ya buge ni se na hango wuta na tashi a ciki amma bata mamaye ko ina ba, tunanin zura Suwaidatu ta window ne ya zo min a rai na in ta shiga ta kashe ta fito, dan da zan iya shiga ni zan Shi na kashe na fito, wata zuciyar nan take ta hane ni da yin wannan aikin gangancin, cikin jimamin abinda zan yi muka ji Yah Maheer na kira na, a rude na koma sashen mu, ashe wuta ta bi ta silin ta shiga sashen mu, kafin ka ce me gidan mu ya cika da matasa da maqota da mata, Yah Maheer na qoqarin fitar da akwatin da credentials din mu ke ciki wasu matasa na qoqarin fidda kayan mu, amma wutar nan bata bada damar daukan kaya ba, ta na gama wa da gidan mu har ta faɗa gidan Hauwa'u da wata baiwar Allah da ake kira Maman Khadeejah wadda ta shigo dan taimaka mana, wuta ke ci ba tsaya wa ba qaqqautawa ina tsaye a tsakiyar parlour na ina jin yanda tiririn wutar ke duka na amma gaba ɗaya hankali na baya jiki na,ni ba tunani nake ba ban kuma san me ke faruwa ba a kewaye da ni, cannn nesa da saurare na na Ji ana faɗin,
"Ke ki fita daga wajen nan, ki gaggauta fita wutar ta ci saman wajen da yawa fa kar ya fado akan ta"
Yah Maheer da ya zaci ina waje ne ya kalli inda nake tsaye cikin parlour na da ke ci da wuta, wurgi ya yi da akwatin hannun sa ya isa gaba na ya na min magana, ganin bana gane komai sai hawaye da ke zubar min ne ya sa shi kama ni ya rungume ya fitar da ni daga cikin wajen,can jikin katangar gidan ya tsayar da ni ya na duba jiki na ko zai ga wani alamun quna be gani ba, komawa wajen akwatin takardun mu yayi ya dauka ya kai gaba na ya ajiye sannan ya janyo fridge d'ina gaba na da TV na se ya koma suka ci gaba da fidda abinda ya samu, duk abin nan da ake Yah Maheer na komai a guje ya na neman layin Ahmad mijin Maman Abdurraheem dan ya sanar da su abinda ke faruwa amma ba ta shiga.
Hankalin shi tashe ya roqi wani a wajen ya ce ya kira masa maqocin mu saboda su san halin da ake ciki saboda su zo su bude wajen a samu ko ba yawa a fidda masu wani abun.
Ana haka Hauwa'u da mijin ta suka iso bayan gidan su ya gama qonewa qurmus,ga ta da ciki, kuka ta dinga yi itama, ni kuwa ina nan inda Yah Maheer ya aje ni tsugunne ina tsiyayar da hawaye ina tasbihi ga Ubangijin da ya halicci wuta, sannan ina neman tsari daga azabar ta.
Wuta ce jajazur sakamakon kusan komai nawa na parlour red ne, komai ma lasar shi take a wajen abun gwanin ban tsoro, ba abinda nake tunawa se qiyama, na yi istighfari ban san adadi ba saboda tsoron Allah da na ji ya shigo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 30