Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
min waqa ta tin ta yarinta, kusan duk haka take mana) Ganin ba fa zai min maganar shekarun da na qara ba kawai se na tafi gidan Maman Aminu, nai zama na, anan ne Amina ta kai ni gidan wata mata da ke unguwar, bayan mun gaisa ne take tambayar ina ne gidana na yi mata kwatance, bata gane ba, Amina ta ce mata, ni matar Malam Maheer ce ai, gidan mu daya da Maman Ameerah, mamaki ne ya kama ta, ta ce, "Auuu dama da gaske da mutane a gidan bayan ita Maman Ameerah? Ai na sha zuwa da dare in na ga haske sai in ce mata anan matar Malam Maheer take sai ta ce ah ah,ba kowa su kadai ne a gidan,ashe qarya ne, ai ko inshaa Allahu duk na zo zan zo a gaisa," Haka muka ci gaba da hira sama sama daga baya na koma gida, bayan na koma ne wata 'yar ajin mu ta zo me suna Asma'u wasagu take sanar da ni randa na tafi fa Mr. Joseph sa wa ya yi a taimaka min wajen yin map reading saboda an sanar da shi banda lafiya ne ya sa na tafi, hamdala na dinga yi ga Allah ina sakewa, sannan na ce in yana da rabon musulunta Allah ya sa ya musulunta. Bayan tafiyar ta da 'yan mintina ne na ji waya ta ta yi qara alamun saqo ya shiga ciki, ɗauka na yi dan in ga wanda ya tura saqon, sunan Yah Maheer ne ya bayyana cikin tura baki kamar ya na gani na na buɗe, kalaman da na karanta se da suka sanya ni zubar da hawaye, addu'o'in da ya min sun raunata zuciya ta sosai, ina tsaka da kukan farin ciki wani message din ya shigo, katin waya ne na dari biyar,kafin in kwashe in loda a waya ta ya kira ni. "Hayyakillah ya habibty" Wani irin farin ciki ne ya kama ni har da tsalle na, "Wato ashe kyale ni ka yi ko ka na sane ka qi kula ni, ni ma to Yau ba zan kula ka ba" "Tooo da wa nake magana yanzu?" "Da dodo" "Dan Allah ya yi hakuri kar ya firgita ni, babyna na kusan dawowa me ki ka dafa ne yunwa na ke ji" "Ni ba abinda na dafa yanzu dai nake so na yi girkin saboda na san se bayan Isha'i za ka dawo tunda yau ka na da 4-6 lecture" "Hakane to kin san yanda za ai ki yi girkin kaɗan tunda kin ga zafi ne kar ya kwana ya lalace" "Inshaa Allahu haka zan yi se ka dawo, Allah ya bada Sa'a, Allah kai ma ya yi maka dukkan abinda ka roqa min a wajen shi har ma da qari" "Ameeen mar'atussalihaaa se na dawo" Bayan ya kashe waya ne na ji wani kwarin guiwa, ban ɗora girki ba kuwa se da shida na yamma ta yi dan na san se bayan magrib zai dawo, shinkafa da fa dika na yi ta sha zogale gidan Maman Aminu na samo ga albasa se qamshi take,da busasshen kifi na yi amfani dan ni na fi son in dai dafa duka zan na sa kifi na fi ci sosai. Kankana na wanke na yanka na cire wa kwallaye na yanka ta qanana, na zuba madara da sugar dan kuwa ita kaɗai nake da a wannan lokacin, sai ruwan da ba wani sanyi sosai, ina girki ina gyaran gida da jiki na, dan haka sai kammala komai da na yi ya yi daidai da bugawar agogo qarfe takwas na dare, ina Yah Maheer ya tsaya? Me ya sa be dawo da wuri ba? Daurin dankwali na da na kafa na taɓa dan so nake na burge shi saboda addu'o'in da ya min da kalaman qaunar da ya zuba min amma fa fisabillahi na takura, na jima rabon da na saka atampa gashi ba wuta mu za a kawo wa da sha biyun dare yau. Ai kuwa ina nan zaune har tara ta yi na ɗora hannu na zan tuge dankwalin se muka ji qarar buɗe gate, murgud'a baki na yi na ce, "Haaaa Allah ya temake ka da se dai ka zo ka ga wannan cinyayyen gashin nawa da quraje suka cinye" Sallamar shi ya yi cikin sanyin shi sannan ya shiga parlour,miqe wa na yi da sauri ganin ledoji a hannun shi,karba zan yi ya girgiza mun kai alamar in barshi, se da mu ka yi sannu da zuwan mu da muka saba na musamman sannan na ja baya ya wuce ni zuwa bed room din mu nan take na taka na bishi. A gado ya baje ya na maida numfashi, da alamun gajiya da yunwa a tattare da shi sosai, cikin tausaya wa na hau matsa masa qafafun shi sannan na ce, "Sannu Yah Maheer ɗina, ka gaji ko? Mu je na taya ka wanka, se ka ci abinci, ko kuma abincin zaka fara ci?" Idanun shi lumshe ya ce, "Bari na fara wankan,dan in na ci abinci ba zan iya ba bacci zan yi na san" Wanka na tafi na taya shi bayan na rufe qofar da zata sada mutum da parlour da banɗaki saboda kar Suwaidatu ta gani. Mu na fitowa na haɗa masa abinci, nan take ya ce, "Ba ki duba abinda na kawo ba ko?" Ni dai na ji qamshin abubuwan kwad'ai tunda na san ina da kwad'ai ba se an fadan ba ma, jan ledojin na hau yi kayan kwalama ne kuwa sosai a ciki da kuma gasassun kaji biyu manya se lemon exotic da qananan cup cakes,tsalle na yi na d'ale shi ina ta murna sannan na hau yi masa godiya da addu'a, se da na gama murna ta sannan ya ce, "Kar fa ki ga na siyo wadannan abubuwa ki zaci ina supporting wai bikin zagayowar ranar haihuwa,ah ah na miki ne dan kyautatawa, dan kar ki saba da wai duk ranar zagayowar haihuwar ki sai na ce maki happy birthday Shi yasa na jinkirta ban maki ba, so ki sa a ran ki ko da BD ko babu in ina da shi zan kyautata maki kuma zan maki addu'a sannan in banda shi za mu ci gaba da hakuri da rayuwa kin ji ko?" Kai na daga na yi masa godiya, Suwaidatu ta yi bacci dan haka aje mata nata na yi na ce gobe sun haɗu, gajiya na yi da daurin dankwalin kai na se na Kalle shi nace, "Ka ga kwalliya ta?" "Eh Masha Allah kin yi kyau duk da cewa ke ɗin kyakkyawa ce ko ba wanka ba guga" Dariya mu ka yi a tare sannan na ce, "Ka ga daurin dankwali na ya yi kyau?" "Sosai ma ai in ki ka kafa gwaggwaro sai mutum ya zaci kun haɗa dangi da yarabawa nan kuwa tsabar kwarewa ce kawai" Dariya muka dinga yi sosai saboda yanda yake maganar na san ya san me nake shirin yi,ai kuwa tuni na sa hannu na tuje daurin na ce, "Washhh Allah na na gaji, yau na yi qoqari na jima da daurin nan a ka" "Ni da na san cire wa za ki yi, shi yasa ki ke ta wannan shan kwanar" Haka muka kwana cikin farin ciki, sai na ji duk wasu ciwukan da nake ji sun min sauqi saboda farin cikin da Yah Maheer ke bani, hamdala na dinga yi ina gode wa Allah mai kowa me komai wanda yake yaye wa mutum baqin ciki ta hanyoyi da dama, idan ya jarabce ka da rashin wani abun ta wani ɓangaren sai ya jarabce ka da samu ta wani bangaren, ko ya yalwata maka ya sanya ka farin ciki ta wani fannin, dan haka na tabbatar da cewa Allah ya jarabce ni da ciwo tun ina qarama ta, se ya bani iyaye na gari masu tausayi na da 'yan uwa masu qauna ta, bayan na girma na fita daga qarqashin kulawar su se ya haɗa ki da miji na gari mai tsananin so na da qauna ta tare da kulawa da ni,shi din 4 in 1 ne, shi ne uwa ta uba na kuma 'yan uwa na da ke nesa da ni sannan kuma miji na. Duk irin gwagwarmayar da nake sha ta rayuwa mutane da dama ba su hango wannan illa gatan da nake samu wajen Yah Maheer shi ke tsone masu ido, shi kawai ake so a dakushe min ko ta wacce hanya ba tare da ni na sani ba, domin ban taɓa kwana da kowa da mugun nufi ba a rai na, sannan ban taɓa tashi da kowa da mugun nufi ba a raina. *************************** Bayan sati biyu muna zaune da dare tsakanin magariba da isha'i, daren ranar anata kod'a zafi Maman Ameerah da iyalan ta na tsakar gida su na shan iska, ni kuma da nawa iyalan mu na qunshe a cikin gida mu na shan zafi saboda ba ma so mu fita gaba ɗaya a cakud'e abun be yi tsari ba dan na san da mijin ta ya dawo anan zai kwanta,Yah Maheer kuwa ba zai bari mu zauna ga mu ga su ba se ya ce in aka kawo wuta fa? Shi baya so, ina zaune se na ji yo muryoyin mutane a tsakar gida alamun an yi baqi, ina nan zaune shiruuu ina ta aikin firfita a raina ina fatan su kawo wuta dan mu ne da wutar sha biyu na dare, zuwa a asuba,gashi Yah Maheer na masallaci be dawo ba, sallama na ji an yi min a qofar parlour na, jinkiri na ɗan yi kafin na tashi zaune na amsa, mayafin da nake daurawa na gyara saboda ni bana daura zanin atampa se dai mayafai da na mayar zani dan sun fi fitar da shape me kyau a jikin mace, ba za ka zauna ka yi kamar wani ɗan qauye ba. A bakin qofa muka haɗu na tsaya ina mamakin ganin su............ *Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful* 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 26: "Ah bismillah Ku ne ke tafe, ku shigo" "Wallahi mu ne, ai cewa na yi yau dai se na shigo mun gaisa," "Ina yini, ya yara, ya zafin nan na garin ku?" Cikin murmushi matar ta amsa min da , "Lahiya qalou alhamdulillahi, zahi gashi nan ko wallah mun gode wa Allah" Hira mu ka ɗan taɓa kaɗan a matsayin mu na waɗan da ba su saba da juna ba, sannan ta min bayanin ita ce matar wane da ke can layin mazan mu na gaisawar mutunci ta jima ta na so ta shigo sai yau Allah ya nufa, godiya na yi mata sosai sannan da suka tashi tafiya na raka su har wajen shimfid'ar su Maman Ameerah,anan hirar ta tsaya suka tafi ni ma na gaishe su na koma ciki, washegari sai ta dinga d'akko maganar matar ni Kuma na qi bata dama, saboda ba shi da wani amfani se dai na sanya ta ta yi qarya ni kuma banda wannan lokacin sauraron qaryar ta ta ina fama da kai na. Haka rayuwa ta ci gaba duk wani wanda nake tare da shi Maman Ameerah ke tare da shi sai ta san yanda ta yi ta hure masa kunne akai na,ana haka sai ɗaya daga cikin abokan Yah Maheer da suka samu aiki a garin Kebbin tare ya yi aure, sanda zai kawo amaryar ba laifi mu ne muka je tarbar su, Amaryar shi fara sol da ita kamar ka taɓa ta jini ya fito,da zuwan amarya sai Maman Ameerah ta dinga qoqarin jan ta a jiki, ni kuma cikin ikon Allah Allah ya riga ya haɗa jinin mu da amaryar, dan haka duk wani qoqari da yunkurin shiga tsakanin mu be samu ba a wajen ta, se ya zamana na tsira da qawa guda ɗaya a cikin unguwar tamu duk da dai akwai ɗan nisa tsakanin mu, amma ko ba komai ni ma na samu mai zuwa min da wanda zan je wa. Ana haka amarya ta samu ciki, a duniya ina tsananin tausayin masu ciki, yin daga kan Addah maqociya ta ta Bauchi na fara tausaya musu saboda shi ne cikin da na gani tin ya na qarami har ranar haihuwar shi ina tare da ita, dan haka na ga matsananciyar wahalar da mata ke sha,wannan dalilin ne ya sa na ke tausaya wa masu ciki ainun,hakan shi ne ya yi dalilin da ya sa bana rabo da zuwa gidan amaryar saboda cikin nata mai tsananin laulayi ne, wani sa'in ko tsayuwa bata iya wa da kyau sai jiri ya dinga diban ba, abinci ko wanne iri ne aka kawo sai ta qi ci, fruits ne ya zama abokin ta, duk da cewa su din ma ba kowanne iri ba. Haka zan bar gida na bayan na gama abinci na gyara komai zan je gidan amarya na yi mata girki na gyara mata abinda ya kamata in matsa Mata ta dan samu abinda ta ci, watarana duk qoqari na haka zata kasa cin abincin saboda ba zata iya ba bata so,akwai sanda tsabar tausayin ta sai da na yi mata kuka da na dawo gida,tsoron ciki da goyo da raino baki daya sai ya kama ni, nake ganin ba zan iya ba, kullum addu'a ta sai ta karkata akan Allah ya zaba min abinda ya fi zama alkhairi a rayuwa ta da addini na da rayuwar Yah Maheer miji na. Ana haka aka samu hutun sallah, mu ka rankaya mu ka yi gida, kamar koda yaushe in za mu gida mun yi ɗinkin sallahr mu mun yi qunshi kitso da duk wata kwalliya da ake yi domin murnar bikin sallah, Amarya ta fara cin abinci duk da ba sosai bane amma ta fi da. Sai da mu ka fara sauka a Kano mu ka huta sannan mu ka wuce Bauchin Yakubu,direct gidan Kabeer muka sauka mu ka huta sannan muka wuce LK. Wannan zuwan ya min dad'i sosai saboda kusan kowa da kowa ya zo sallah gida, qannen Yah Maheer mata biyu da ke aure a Bauchi sun zo, cousins ɗin shi da suke aure a wani wajen duk sun zo ga matan qannen shi da yayan shi, gida dai ya cika maqil abun gwanin ban sha'awa. Ranar sallah haka mu ka dunguma dukan mu yawon sallah, Ni, sadeeyah, Habibah, Zaituna, Bilkisu,Ladhifatu, da Umaimah (Matar cousin ɗin Yah Maheer ce kuma ita ma cousin ɗin shi ce auren zumunci aka yi musu bayan Maryam ta bar gidan aka aure ta) duk inda mu ka je se an bamu barka da sallah dan haka jaka guda mu ka ware ake zuba kuɗin barka da sallah, Memuna ita ce qarama a cikin mu dan haka ita ke riqe da kuɗin, mu na tafe mu na hira cike da matsanancin nishad'i, duk inda muka gilma mun zama kamar wasu taurari, kaf gidajen gwaggunayen su sai da mu ka je daga nan muka je gidan Babbar yayar su Yah Maheer wato Dada, anan aka yi mana goten tsaki da ya ji gyad'a, mommyn Abubakar na dauke da cikin Yaron su na biyu, ta zage ta sha gwaten nan sosai, ni kuwa da dama can ba ya burge ni se na dinga tsince gyadar da aka zuba a ciki ina cinyewa, mu na gamawa mu ka.musu sallama mu ka nufi gidan Goggon Hauwa'u (Itama yayar su Yah Maheer ce cousin ɗin shi ce) anan ma gwaten aka mana a bokiti qarami aka ce za a kai mana gida tunda yawon ziyara muke yanzu. Har gidan su Maryam se da muka je wato tsohuwar matar qanin Yah Maheer, mace mai kirki da mutunci da barkwanci lokacin ta na gidan ita ce ta sanya ma kowa suna a cikin mu, sunayen bishiyoyi da shi take mana amfani siriri se ta samu sunan da ya dace da shi baqi ta samu sunan icen da ya dace da shi ni da nake da jiki se ta samu sunan icen da ya dace da ni haka ita da take doguwa se da ta yi wa kan ta suna, Maryam ta iya zaurance ni kuma ban iya ba haka za su yi ta yi su na tsokana ta ana dariya a hankali in suka yi se ta fassara min har na fara gane me suke faɗa Maryam bata da girman kai ba ta da mugun hali ko hayaniya qaddarar rabuwa ta gitta tsakanin su dan haka se mu ka kai mata ziyara gidan su, (Allah ya jiqan ta ya mata rahama) mu na fita muka je gidan Rasheedah 'yar Babbar yayar su Yah Maheer wato Dada Jummai, ta ji daɗin zuwan mu sosai, ta dinga hidima da mu, dama ni duk zuwan da zan yi ya zame min kamar ibada se na je na gaishe ta, dake gidan ta da gidan qanwar Yah Maheer da suke Mama ɗaya ba nisa sosai, bayan mun fito na yi iya qoqarin da zan yi dan mu je gidan qanwar Yah Maheer ɗin haka aka doje aka qi zuwa, abun be min dad'i a rai ba, cikin rai na na ce, 'Da ace su masu kuɗi ne komai nisan alaqa se an kai mata ziyara ba komai, na dawo daga baya mu gaisa har gidan Ladidi zan je inshaa Allahu.' Daga nan gidan wata mata muka je da ake zargin ta na maita, mu na zuwa mu ka gaishe ta muka yi mata barka da sallah, ido ta kafe ni da shi, ta ce, "Waccan ɗin wacece?" Nan da nan na ji gaba na ya fad'i, cikin dakewa na ce, "Goggo baki gane ni ba? Kullum na zo fa se na shigo gaishe ki" "Ni ban gane ba, kin san abun da yawa," Memuna ce ta ce, "Goggo matar Ɗan azumi ce fa" "Wanne Ɗan azumin?" "Ɗan azumin Fendi mana" "Allah sarki," Idanun baiwar Allahn nan a kaina ta qi ɗauke wa, nan da nan se na fara addu'a a a cikin raina, miqewa kowa ya yi dan mu tafi wani ɓangaren dan gidan qato ne, babban gida ma ake ce masa saboda girman sa kuma duka mutanen gidan dangi ɗaya ne. Duk sun saka takalmin su wasu sun yi gaba dan sun kula kuɗin Barka da sallah za ta bayar babu kuma me son karba, duk saurin da nake na saka takalmi na sau ciki se da aka gudu aka banni dan haka a hannu na ta damqa kuɗin ina ah ah Ina ah ah, se da ta bani dole, ina gama sanya takalmi na na same su a qofar gida dariya suka dinga yi min, cikin tura baki na ce, "Ban taɓa tsanar sanya takalmi sau ciki ba se yau" Dariya suka bushe da ita, mu ka tafi na miqa musu kudin kowa ya ce ba za a hada shi da sauran da muka samo ba, a haka muka kama hanyar gidan qanwar Mahaifin Yah Maheer wato Goggo Ladi (wadda suka dauko Ni da ina amarya). Me gyad'a aka gani irin ta soyu ɗin nan, nan da nan aka kira ta aka ce a zo a kashe kudin da waccan Goggon ta bamu kar a haɗa da sauran, nan take na ce ni dai ba zan ci abu da wannan kuɗin ba su bani wani na siya gyadar da shi, ai kuwa haka akai kowa ya ci gyad'a da kuɗin nan Ni kuma na siya da wasu, muka tafi ana ta hira ana jin dad'i. Se bayan la'asar mu ka bar gidan Goggon tamu, mu na tafe ana hira can Habibah ta hango wani gida da bishiyar zogale, se cewa ta yi, "Wallahi kamar mu je mu ce a sammana gobe mu yi dambu" Tsokanar ta aka fara ko dai akwai ɗan Baba ne, cike da nishad'i muka gama ziyarar mu muka koma gida, a dakin Mama aka baje wasu kuma suka shige dakin Ummah ni kuma na wuce daki na na cire sarqa ta da ta dame ni,na cire ɗan kunnen na ajiye sannan na kwanta a gado ina jin yanda qafafu na suke min tsananin ciwo, a hankali na furta. "Allah dan girman zumuncin da muka sada yau Allah ka sa kar ciwon qafata ya motsa" Ina nan kwance ido lumshe aka aiko yaro na zo a raba kuɗi, kamar in ce in an raba a aiko min, se na ga akwai wanda suka girme ni be kamata na qi zuwa ba, tunda ba laifi gidan nan kowa na girmama na sama da shi. Da kyar na miqe na tafi na same su ana ta hira, miqo min kuɗin Bilkisu ta yi ta ce, "Aunty Mahreen gashi tunda ke ce matar babban yaya ki raba mana kuɗin" Dariya na yi na qi karba na ce. "Ban iya rabo ba, ni lissafi ma wuya yake min shi yasa ko makaranta bana cin maths," Dariya aka yi sannan Bilkisu ta raba mana,ko ba komai an bani girma na na matar babban yaya karba kowa ya yi ana hamdala dan kuwa mun samu kudi ba laifi. Da dare wanda suke aure a cikin garin suka koma gidajen su wanda za su kwana anan kowa ya yi wajen baccin shi ni da Ummeeta dama tunda na je tare muke kwana, muma mu ka wuce daki na mu ka kwanta, tunda na fara rashin lafiyar da Yah Maheer ya yi tafiya na ga wata mace a gefen gado na nake matsalar rashin bacci da dare,wanda ya bi ni har yanzu, watarana na samu baccin kamar ba zan tashi ba, lokuta da dama kuma haka zan zauna kowa na bacci ido na biyu se da safe nake samun bacci, watarana da safe ma ba zan samu ba se na jera kwanaki ban bacci isasshe ba. Yau na samu nasarar samun bacci mai daɗin gaske ya kwashe ni bayan na yi addu'ar bacci, ina tsaka da bacci kawai se na fara mafarki, wanda ya fi kama da gaske, wato ina nufin kamar a farke nake ganin abinda nake gani, jiki na ya dauki wani irin zafin da se da gadon da nake kai ya ɗauki zafi kamar wuta, zafin jiki na shi ne sanadiyyar farkawar Ummeeta daga baccin da take, ta kai hannu ta na tashi na, cikin hamdala da zumudi tare da jin daɗin tashi na daga wannan mummunan mafarkin ko kuma mummunan abinda nake ganin na buɗe ido ina qarewa dakin kallo. Tin ina kwancen ido na a rufe nake so na yi ayatul kursiyyu na kasa se na kamo ta kufce se na fara ta zille, qulhuwallahu ahad na samu na kai da kyar da sid'in goshi ina zuba zufa kamar wadda ta yi gudu ko aka kara a bakin wuta, wayata na ja yo na kunna karatun qur'ani Fatiha na direwa baqara ta dauka. Wani irin bacci na ji ina ji me masifar dad'i wanda tunda uwa ta ta haife ni ban taɓa jin irin wannan baccin ba a rayuwa ta, mamakin baccin be gama saki na ba baccin ya yi nasarar cin galaba akai na, nan take na hau bacci, the same abinda na gani a bacci na da farko shi na sake gani wato fuskar matar da muka je gidan ta da aka ce ta na maita, ga fuskar ta ga tawa sauran kaɗan ta haɗe fuskar mu waje ɗaya, cikin hukuncin Allah Allah ya bani iko na farka da qarfi a firgice baki na na karanta can qarshen ayatul kursiyyu wanda ban san sanda na fara ta ba. Ummeeta ce ta farka ta ke yi min sannu,cikin wata iriyar murya na ce mata kama ni na je na yi alwala, a hankali ta kama ni ta ce, "Kaiiiii Aunty jikin ki zafi zauuu" Ni kai na zafin ya bani mamaki, domin ba irin zafi ne na zazzaɓi ko wani ciwon ba, zafi nake ji kamar ina gaban murhu ko an manna min garwashin wuta, a haka muka fita tsakar gida, Baba na gani a tsakar gidan ya na alwala ya na gani na se ya bi ni da kallo da alama akwai abinda ya ke ayyana wa,bayi na shiga na kama ruwa sannan na dawo na yi alwala,tambaya ta ya yi lafiya? Nan take na kora masa bayanin abinda na gani da abinda ke faruwa ban boye masa ba, "Allah ya kyauta, kin yi daidai yi alwala ki yi nafila Allah ya baki lafiya" "Ameeen" na iya cewa na miqe da kyar na shiga d'akin, zama na yi Ummeeta ta haye

Chapter 21 of 30