matsayin gidan mu,muna hira nake sanar da su zan kwashi kaya na ne mu kai can gidan, Mama ta ce ,
"To gasu can a drum ɗin can duka tarkacen kwanna ne, (duka tarkacen kwanika ne) Saudee (Maman Abdurraheem)ma ta zaka (ta zo) ta ɗebi kayan ta, har da kujerar nan 'yar doguwa da abun suyar nan baqi"
Saboda bana iya duqawa sosai sakamakon ciwon baya da nake yawan yi Yah Maheer ya sa aka min kujeru guda biyu na zama na nusamman kamar stool haka.
"Ah ah ai wadannan kaya na ne Mama,"
"Ah to dai haka mun ka ce, wad'anga kaya awa naki,(waɗannan kayan kamar naki) tacce nata na, mu ko bamu hana mata dauka, aka rasa abinda ya fi su ma? Ki yi hankuri Allah shi maida maki da alkhairi"
Mamaki ne ya kama ni, Maman Abdurraheem ko a da ta fi ni kaya, ta fi ni abubuwa sosai, ni dai ban taɓa d'aga kai na kalli abinda na sama na ke da shi ba balle ya dame ni,na fi kallon wanda ke qasa na shi yasa alhamdulillahi ba alfahari ba ban damu da abinda wani ke da shi ba, kai na na sani me nake da shi ya min kyau ko zan qoshi idan na ci, da na samu wadannan cikar burin shikenan.
Ban tashi mamaki ba sai da Ameenah ta dinga nuna min abubuwa ta na cewa akwai kaza irin wannan ta dauka da shi,haka dai na hakura na danne zuciya ta for the sake of zaman mutunci da muka yi a baya ba zan magana ba na bar mata Allah ya sa mu dace. (Ba tare da na san ta na can ta qulla min mugun abu ba a idon mutane)
Katifa ta tun ta aure aka nuna min duk ta ji jiki kamar ta shekara goma, a raina ina ayyana in Allah ya hore mana zan sauya mata riga, se drum dina qarami wanda kwanuka na ke ciki da risho da sauran tarkace dai wasu ma dole na hakura da su dan wuta ta ci su sun yi baqi,wasu kuma duk da baqin nasu tunda banda wanda suka fi su haka na killace su na ce a bari daga baya zan zo na ɗauka,akwai wasu takardu na da aka kai wani gida a lokacin gobarar har yau ban san wanne gida bane kuma ba su neme ni ba, duk da dama ana gobarar ina gefe ina kuka ina ganin wasu su na kwasar ganima mu kuma mu na cikin baqin cikin rashi da mukai na dukiya su suna farin ciki banza ta fadi,bamu bar gidan ba sai yamma.
Ba tare da na sani ba Yah Maheer ya je ya kwashe kayan duka ya kai can sabon gidan da za mu zauna, ya saka mana sabuwar ledar d'aki,babban carpet ɗina kam na riga da na rasa shi, sai wanda Mama ta bani wani ash colour me nauyi sosai, ya sa an wanke shi an malala a parlourn farko, da dare ina nan ina ta mugun tarin da ya kama ni sakamakon AC da na sha Yah Maheer ya shigo ya ce,
"Tohhh kayan ku dai duk a haɗe suke ko?"
"Eh ai dake ba wasu kaya bane sosai komai ya na nan a haɗe yaushe za mu tafi?"
"Yanzu,"
Bata fuska na yi, shi matsalar shi ba zai sanar da mutum abu akan lokaci ba sai lokaci ya qure sannan,
"Wai dan Allah sau nawa zan faɗa maka ka dinga sanar da ni abu kafin lokaci, ka san ni ba na son komai a qurarren lokaci me ya sa ka ke haka dan Allah, yanzu in akwai abinda zan yi fa?"
"Se ki yi shi yanzu, ke wai dan Allah me ya sa tunda kin san hali na haka nake ba za ki dinga kyale ni ba?"
"Ba zan kyale ka ba ɗin, bana son wannan halin bana so, ina nuna maka illar sa ne saboda kar watarana ka rasa abu me amfani a rayuwa saboda yin abu ba a kan lokaci ba"
Dariya ya yi saboda ganin yanda na yi serious ina magana cikin ɓacin rai, riqo hannaye na biyu ya yi ya na dariya ya ce,
"To tunda makara ta ta zame min alkhairi ai ni jam in ji Fulani,ko kin manta yanda na bar maza su na ta rububin ki kowa na so ya ɗauke ki ya kai gidan shi ya killace ya na more rayuwar shi amma na lallabo na lallabo na dauuuuke ki? Ba wannan ba ma ai dai kin san in dai abu na da amfani da mahimmanci bana wasa haka, dan na san na isa da ke ne ya sa nake faɗa maki abu a qurarren lokaci, kuma na san ba zaki bani kunya ba a duk abinda na ce ki yi ko da sauran second ɗaya ne,bayan haka amarya ai da dare ake kai ta dakin mijin ta ya fi sirri"
Murguda masa baki na yi na kwace hannu na na shige daki na ɗakko jakar Suwaidatu da ke zaune a parlour ba na jin ma ta san da tafiyar, buɗe parlour na yi na kira ta ina ta zumbura baki, na ce ta fitar da jakar ta waje yau zamu koma can Alieru quarters, murmushi na ga ta na yi, ta karbi jakar ta fitar, ni kuma na dauki akwatin mu da yar jakar kayan mu Yah Maheer na gani na fito da su ya yi sauri ya karba, hijabi na na ɗakko na saka, sannan na tattara soson wankan mu da sabulu na ɗauki na wanke-wanke da tsintsiyoyin mu, sai towel da muka mayar tsumma, na zuba su cikin dustbin da na siyo tun zuwanmu na saka makwashin shara a ciki, murmushi na yi na ce,
"Allah sarki da wadannan kawai muka zo wasu ma anan muka siya, to mun gode Allah, gida salamu alaikummmm se wataranaaaa"
Yah Maheer ne da ya shigo ya ji me nake faɗa sai ya yi dariya ya kalli bathroom ya ce,
"Ni kuma I will miss youuuu saboda ba laifi an darji qauna a cikin ka"
Dukan shi na yi muka fashe da dariya muka kulle ko ina sannan mu ka tafi waje, qanin Bashar ne Abdulmajeed ya zo ya karbi makulli muka musu godiya mu ka tafi, ta waya na kira Rasheedah na mata godiya sosai da fatan alkhairi saboda su na Abuja ba sa gari.
Ko da mu ka isa sabon gidan da za mu zauna sai na ga unguwar ba laifi akwai mutane gidajen a kurkusa suke,kowa ya ja gate ya b'ame qofar shi, sai masallaci da ke a tsakiyar unguwar da ka doso shi za ka fara gani.
Da Bismillah na sa qafata ta dama na shiga, duhu dindum ba wuta an dauke,ina shiga sai na ga gidan an sauya masa gini ba kamar sauran yake ba, da ka shiga tsakar gidan parlour ne se kitchen da ke kallon parlour da banɗaki a tsakiyar su.
Se ka qara gaba a nan ne asalin ginin da gwamnati ta yi ɗin yake, parlour kitchen and toilet, se daki guda ɗaya, a parlourn farko Yah Maheer ya malala carpet ya sa fridge da TV da DVD din se ya zamana komai ash colour ne a wajen da Black, labulaye na dama sun jima da cinyewa tun a gobara har da sabbin da nake da su, be fi guda uku bane na tsira da su a akwati, dan haka se na qudurta gobe zan saka labule daya a qofar can one bedroom din kuma na saka a window tunda na ga bayan mu wani ginin ne duk gidan mutum daya ne, filin da gidajen ke da su ne ya sa ake iya qara wasu ginin a ciki, shi yasa windown na dakin namu direct cikin gidan wasu ya shiga, na ce daya labulen na sa a qofar shiga.
A daren ranar duk mun manta bamu ci abinci ba cikin daren yunwa kamar mu yi kuka gashi duk ya kashe kudin shi wajen gyara mana inda zamu dawo, indomie ya siyo da dari biyar da ta rage masa,ina gani na fashe masa da kukan shagwaba na ce,
"To da wanne rishon za mu yi girki?"
"Ah baki buɗe kitchen ba? Ai na karbo kayan gidan Mama dukan su har rishon da tukwane na ga tukwanen ma biyu kawai suka rage duk kwarin su, ai a zato na wannan ko wutar me aka yi ba za su ci wuta ba saboda kwarin su,"
"An kwashe mana su duka Maman Abdurraheem ce wai ta dauki wasu abubuwan nawa...Ni ba wannan ba ina kananzir to?"
Shiru ya yi ya na sosa qeya,
"Kai se ka dinga abu ba shawara, yanzu da ka faɗan abu zaka siyo se na ce maka siyo mana bread ko da pure water ne se mu ci yanzu ya za mu yi da indomie?"
"A jiqa ta a ruwa irin na 'yan makaranta"
"Auu wasa ma ka dauki abun ko, to ni wallahi yunwa nake ji"
Na zauna a qasa dabar ina masa kuka har da qaqalo hawaye na, shi kuma ya durqusa ya dauki indomie da na zubar a qasa ya dauko wani dogon cooler irin wanda ake saka abun siyarwa dan ya riqe sanyin nan, ya wanke ya juye indomie din duka a ciki ya debi ruwan sanyi ya sheqa mata, zai saka maggin ta na riqe hannun shi na ce,
"Ai an bari ta jiqu ko ?"
"Ai na zaci ba zaki magana ba tabarar zaki ta yi"
"Eh din tabarar zan ta yi"
"Kin san Allah in Ina magana ki na cewa eh din? In ki na cewa eh din? Ki ka qara cewa eh din ki ga Ni, qara mana? Haaaaa yarinya yau da kin ga kiran eh din me zai ja maki"
Zuciya ta fal tsoro dan da gaske yake bani warning, amma dake bakin nawa se a hankali se na miqe na gyara zama na ta yanda da an ce kyat zan sheqa da gudu na buɗe baki zan magana wani mugun tari ya sarqe ni, tun ina yi sama sama har abu ya zamana zama ma ya gagare ni, na kwanta na tashi, na koma na sake kwantawa, na miqe tsaye,Yah Maheer kuwa sai ya rikice ya na ta faman jera min sannu, Suwaidatu da ke daki ma sannu ta dinga jero min ko amsa wa bana iya yi.
Nan da nan ido na suka fito suka yi jawur kai na ya hau ciwo qirji na da mara ta suka dauki ciwo,qarfin yanda nake ta tarin ne ya sanya jini fara zubar min, kuka na sanya ina tausayin kai na ni kenan da na yi aiki me tsanani ko na ɗauki abu me nauyi ko na kwanta na jima kwance sai jini ya zuba min.
Yah Maheer ya zaci kukan azabar tarin da nake ne ya kama ni, nan take na kama hannun shi na sa a gaba na ya dangwalo jini,
"Subhanallahi sannu baby na, zauna ina zuwa na samo maki abinda za ki saka"
D'aki ya shiga ya ɗakko min abubuwan da nake tare jinin da su,ya ninka min dan ya san ya nake abubuwa na, ya sa min a pant sannan na dafa shi ya saka min pant din na qarasa gyara zaman towel ɗin a jiki na.
Katifa ya yada mana a parlour saboda parlour na cikin ba koma ko kujera 'yar tsugunno babu se leda me kyau da ya saka min, kusan duk inda na yi amfani da leda irin ta nake yi.
Nan fa na kwanta ina maida numfashi dan bana son na yi nishin da zai tado min da tari, Yah Maheer waje ya je ya wanke hannun shi da jini ya taɓa, sannan ya dawo ya kwanta a gefe na, ya na min sannu, murmushi na yi da na tuna rashin kunyar da na fara gashi nan one time Allah ya sa ni a silent.
Kamar ya san me nake wa murmushi shima se ya yi murmushi ya ce,
"Allah na yafe mata, ba ta taɓa min abinda raina ya shiga qunci ko damuwa da ɓacin rai ba, idan ma ta min na manta kuma na yafe mata, na yafe mata abinda ta min a baya, da wanda ta min yanzu da wanda za ta min a gaba"
Hawayen farin ciki ne suka zuba a ido na duk da cikin barkwanci ya faɗa na ji dad'i sosai, mu na nan zaune ciki na na kukan yunwa ya ji sanda cikin ya hau kuka se ya duqa ya kasa kunne a cikin sanan ya ce,
"Yunwar Mahreen ki qara hakuri indomie ta jiku"
Wani haushi ne ya kama ni, ni fa ban taɓa cin kiqaqqiyar indomie ba, na riga na sa a rai na ba za ta yi dad'i ba, ina nan ina bata rai na ji saukar numfashin Yah maheer a hannu na alamar ya yi bacci, Suwaidatu ce ta shiga banɗaki ta yi fitsari ta min sai da safe, na ce ta zo ta ɗebi indomien a haka ta ci.
D'iba ta yi ta tafi dakin ta cinye, ni kuma tunda na yi loma ɗaya na ji ba zata shiga ba se na kyale, haka na kwana da yunwa washe gari ina tashi na hau shara da goge goge, ina yi ina hutawa, tari ya matsa min sosai in na fara har shid'ewa nake, a cikin kwana ɗaya na rame abinda ban taɓa yi ba kenan wato rama komai ciwo komai wahala da babu ba na ramewa, tari wasa wasa ya kai ni kwana biyu ina fama, a haka na shiga maqota gidan Maman Raudhah aka gaisa, wadda take a bayan gidan da nake ciki sunan ta Saratu ta na da yara da fari ban san ta na da kishiya ba ,sai daga baya na san su biyu ne ɗayar ta na can garin su karb'a karb'a za su dinga yi, in wannan ta yi watanni sai wannan ta yi watanni.
Ban cika sati biyu ba Allah ya haɗa jini na da Maman Aysha, wata baiwar Allah 'yar garin Zuru, Maman Aysha ta kula da yanda tari ya matsa min abincin kirki bana iya ci watarana in na fara har amai nake yi, dan haka ko na ci abincin ma dawo da shi nake,ina kwance daga ni sai farar shimi da dogon skirt baqi, kai na ya sha gyara na daure shi, duk da bana qamshin turare ba mai jin wari a jiki na, na yi tsaf da ni gidan mu ma tsaf da shi, Suwaidatu na makaranta ita da Yah Maheer, tunani nake in sun dawo me zan basu ba komai na ci a gidan, ni kai na yunwa nake ji, ko dai Mama zan kira in sanar da ita halin da muke ciki sai a taimaka mana?
Kada'a kai na nayi da sauri na furta,
"Inaaa iyaye na na ganin mutuncin Yah Maheer, 'Yan uwa na na ganin mutuncin shi saboda su na ganin yanda yake kula da lamura na, roqon abinda za mu ci zai iya zubar masa da mutuncin shi a ga ya gaza, bari na qara hakuri Allah ya kawo mana mafita"
Ina nan zaune ina shafa ciki na ina ci gaba da tunanin mafita sai na ji sallama, amsawa na yi a hankali ina tsoron daga murya tari ya sarqe ni, ina fita sai na ga Maman Asyha hannun ta riqe da qaton jug se wani flask na abinci a dayan hannun, gaishe ta na yi sannan na mata jagora mu ka shiga parlour muka zauna a qasa, domin kula da na yi matar ba ta kyamatar babu na shi yasa nake kai ta parlour na na can ciki, wanda na ga yan gayu ne masu d'aga kai se na aje su a na can wajen basu ga na ciki ba balle su raina arziqi na.
Miqa min jug ta yi ta ce,
"Maman Suwaidatu ga kunu irin namu na mutanen Zuru, ki ɗakko cup ki sha tun da zafin shi zai maki maganin tarin nan inshaa Allahu,watarana in ki na tari har gidan mu fa ana ji, Allah ya baki lafiya"
Kwalla ce na ji ta taru a ido na, ba dangin iya ba na baba Allah ya haɗa ni da matar da ta ke tausaya min, tunda na zo dama cup din kunu ko jug haka zata kawo min da kan ta tun ina kwana ɗaya da zuwa unguwar,yau kuma gashi har da kwano wanda da na buda dan naman kai ne akai romon shi da daddawar batso su na cewa miyar miyar chiwende (sorry in ban faɗa daidai ba mutanen Zuru)ta zubo min, miya ce da ke magunguna kala kala in ji mutanen garin masu jego na ci haka ma ko ba jego ana ci har maganin mata suka ce ta na yi, godiya na mata sosai se na aje naman kan na dauko cup na hau shan kunun, wallahi a lokacin nan ko ba ta saka magani a cikin kunun nan ba ya tafiyar min da wani kaso mafi tsoka daga ciwon qirjin da na ke ji, ya kuma yi min maganin yunwa (Allah ya saka maki da alkhairi ya kula da marayun 'ya'yan ki ba zan taba manta alkhairin ki ba gare ni)
Bayan ta tafi ne na ajiye kunun ma su Yah Maheer in sun dawo suma su sha, ai kuwa da ya dawo sai ya dawo da shinkafa, ya auno mana irin 'yar Hausan nan, da wake da mai da maggi sai yaji, murna na yi sosai na samu na kunna risho na dora girki, kafin na gama na ɗakko masu kunun suka sha.
Kafin na gama dafa shinkafa na wanke wake na surfa na jiqa, shinkafa na yi na zuba waken a tukunya da ruwa ya dahu na juye miyar nan da Maman Aysha ta kawo min,se na daka barkonon na qara a miyar na bari ta qara dahuwa ruwan ya tsotse muka ci da shinkafar.
Haka muke ta rayuwa har Allah ya hore wa Yah Maheer ya qara siyo mana katifa muka saka a parlourn shigowa se muka bar wa Suwaidatu nan ya zama dakin ta, tunda dama duk kame kame ake in dare ya yi.
A hankali muka dinga siyan abubuwan da muka rasa, zama da yunwa ya ragu sosai a gidan dan kuwa Allah ya buda mana hanyoyin samu, ashe zuwan mu har an yaɗa gulmar bani da kayan daki, akwai wata 'yar uwar Maman Raudhah ta taba zuwa can gida na kafin mu yi gobara, ana hira take sanar da su dan na yi gobara ne amma ina da kaza ina da kaza a baya yanzu ne dai babu,jin haka masu yi min gani gani se aka dena ake mutunci,sanda na ji labari na sha mamaki na ce wato duniyar nan yanzu se kana da shi ake yi da kai, in baka da shi ba me yi da kai, na ce to ni dama rayuwa ta bana son shige shige da hayaniya, rayuwa ta daga ni sai miji na da qanwar mu ta fiye min alkhairi kowa ya zauna a gidan shi, se na fara taka tsantsan da mutane, duk wadda na ga ta na min gani gani bata sake gani na ko a kan layi.
Mu na da wata uku a gidan Saratu ta tafi garin su inda amaryar ta kuma zata karbe ta ta dawo, dawowar Goggo Bilki gidan ba qaramin jin dad'i bane a waje na, Goggo Bilki itama 'yar lukuta ce kamata, muna zaman mutunci matuqa mun zama kamar yaya da qanwa, yanda Yah Maheer ke qoqari wajen kula da ni haka itama mijin su ke qoqari wajen kula da su baki daya,mun shaqu ta yanda ta na iya zuwa sashena mu wuni hira, nima ina zuwa nata wajen mu wuni hira, hatta da islamiyyar dare tare muke zuwa.
Kwatsam watarana muna zaune da Yah Maheer mu na hira, aka yi masa waya daga gida Baban su ba lafiya, a daren ya sanar da ni shi fa gobe zai wuce Bauchi da yardar Allah, kamar wasa na fara roqon shi akan za mu bi shi tunda Suwaidatu ta yi hutu, gaba ɗaya na manta da kuɗin mota buri na kawai mu je gida tare, gidan zai mana shiru ga Goggo bata nan Uwar gidan ta bata dawo ba, se na ji gidan ya mana girma sosai tsoro ya kama ni, tun ina roqon shi da lalama na fara masifa na koma roqo da lallashi, shi kuma a zaton shi ina sane da kuɗin mota amma nake masa bore,kuka na fara ina jin kamar ba za mu iya zama mu kadai ba ya nan ba, tunda bai taba tafiya ba mu ba, kuka nake kamar wadda aka ce wa in ya tafi ba zai dawo ba, sallar isha'i na yi alwala na tada, ina sallah ina kuka, cikin mamaki bayan na idar Yah Maheer ya ce,
"Yanzu baby na dan na ce ba zani da ku gida ba shine ki ke kai qara ta wajen Allah ki na sallah ki na kuka? Kin manta da kuɗin mota ne bani da kuɗin da za mu tafi duka, sannan ba hutu za mu ba fa Baba ne ba shi da lafiya zan je na gan shi,dan girman Allah ki yi hakuri ki dena kukan nan ya isa haka"
Rungume ni ya yi ya na lallashi, a hankali na dena kukan da qarfi se hawaye, Suwaidatu na gefe ta na qunshe dariya ashe dama ta gama faɗin duk kukana ta san ba inda za shi da mu, ai kuwa se na huce akan ta na miqe na hau ta da duka, dariya ta dinga yi ta gudu daki.
Ina kuka ina hada masa kayan shi, tun abun ya na bashi mamaki da ganin kar Allah ya yi fushi da shi akan bata min da ya yi tunda ya sani kamar yanda miji ke da haqqi akan matar shi haka mata ke da haqqi akan mijin ta, (auren me aiki da ilimin addini wallahi akwai dad'i da fa'ida sosai) daga qarshe dai shima dawowa ya yi ya na dariya,ya ce,
"Ni fa na kula ba wai b'ata maki rai na yi ba shagwaba ce kawai ta motsa, zo nan"
Zuge jakar da na hada masa kayan tafiyar sa na yi na ajiye masa kayan da zai saka washe gari, a saman akwati da hular da zai saka, sannan na je kiran da yake min.............
*Jama'ar Allah....anan na kawo qarshen MAHREEN part 1, mai buqatar jin yanda MAHREEN PART 2 zai kasance ta min magana ta wannan No 09031416423 a kan farashi mai sauqi dari biyar kacal #500 only*
*Shin me yake shiga tsakanin masoyan guda biyu har su rabu na tsahon shekaru biyu?*
*Ki na so ki san babban rikicin da ya faru a garin Bauchi tsakanin Mahreen da faccalar/kishiyar sauri ta?*
*MAHREEN na haihuwa kuwa?*
*Ta yaya akai Maheer ya samu damar danqarawa Masoyiyar shi kishiya? Shin ko dai soyayyar ta qare ne?*
*Ya zaman MAHREEN da kishiya zai kaya, anya zata iya zama ta zuba ido ta na ganin Yah Maheer ɗin ta da wata?*
*Shin wace baquwa Mahreen ta yi da ta so fidda ta a gidan ta ita ta zauna da Yah Maheer ita kadai?*
*Shin kishiyar MAHREEN na haihuwa? Ku biyo ni Dan jin matsalar haihuwar MAHREEN da Maheer ɗin ta daga wajen wa ya samo asali*
*Rashin lafiyar MAHREEN jinya ce ta asibiti ko sihiri ne, ko kuma shaidanun aljanu ta haɗu da su suke wahal da ita?*
*Makaranta na san akwai tambayoyi da yawa da ku ke son jin amsar su, wanda ni HAERMEEBRAERH ce kaɗai ke da amsar su, ku biyo ni Dan jin yanda labarin rayuwar MAHREEN zai kasance....kar ku bari a baki labari....kar ku bari ku jira na sibaren na bayyaye🤣*
*Whatsapp me on this digits 09031416423 domin shiga paid group a dama da ku*🩷
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 30