ya na fad'in in barshi ya gode.
Nan take komai ya dinga dawo min a cikin kwakwalwata a hankali, Murmushi na yi na gyara kwanciya ta na lumshe idanu na, tare da kawar da dik Wani tinanin shi da na fara,domin na San shi mutum ne mai Kamala da kamun kai kallon shi baya nufin Wani abu na daban a gare ni, ba tare da na San cewa ya jima da kamuwa da soyayya ta ba.
Kamar yanda ya Saba tafiya da asuba hakan ce ta faru wannan karon ma, abokin shi dan wani gari ne da ake Kira da Gumi, dan haka ya na da buqatar zuwa tasha da wuri Dan ya samu mota kar ya rasa mota, shi kuwa a l bayan an idar da sallah ya yi wa Baba sallama ya ce a gaishe da mutanen gidan ya wuce abun shi.
*******************************
Komawar Yah Maheer bauchi bai hana shi yawan tinani na ba, sai ma qaruwa da tunani na ya yi a zuciyar shi,duk abinda yake Ina nan maqale a ran shi, ya sha gwada ture tunani na a ran shi amma sai ya tina da addu'o'in da yake akai na, da tashin daren da yake, da yawan azumi da ya dora wa Kan shi duk dan ya yi addu'a akan Allah ya mallaka mashi ni.
Gefe d'aya kuma ya na nan ya na fafutukar neman aiki komai qanqantar shi tinda yanzu ko auren zai yi ai se da kud'i.
Shirin dawowa Kano ya yi da manufa biyu a wannan karon,na farko dan ya had'a medical report a Aminu Kano Teaching hospital na tafiya qasar Turkiyya sakamakon wani sponsorship da ya samu ya cike form din shi, na biyu kuma domin ya bayyana dad'add'iyar soyayyar da ke ran shi,ya yi sallar dare da neman zab'in Allah mafi alkhairi a cikin abu biyun nan, dan haka da kwarin guiwar shi ya taho da yaqinin cewa Allah zai masa zab'i mafi alkhairi kuma ko me Allah ya zab'ar masa zai gode masa ya karb'a hannu bibbiyu.
A ranar da Yah Maheer ya zo Kano daga bauchi direct asibiti ya wuce ya je ya gabatar da duk wani abu da ya kamata ya yi, be kammala ba sai yamma, gabanin sallar la'asar, babu b'ata lokaci ya nemi abun hawa ya kawo shi har gidan mu ya sallame shi ya shigo,bakin shi dauke da sallama ya sanya qafafun shi cikin zauren gidan mu, ya na sanye da shadda ruwan shanshanbale, da hular shi da ta shiga da kayan jikin shi.
D'auke nake da tukunyar da na gama kwashe abincin dare zan kai wajen wanke wanke dan na jiqa ta ya shiga, ina sanye da atampa kalar green riga da skirt wanda na dinka ta da hannu na, ba qaramin kyau kayan suke yi min ba, dan kuwa in na saka ina jin kai na kamar wata babbar budurwa sai na yi ta yanga a ciki, duba da cewa ba a cika dinka mana kaya da skirt d'in ba sai dai zani ko doguwar riga, ko ba komai ma ni ban cika son sanya manyan kaya ba ma.
Ina dago kai na mu ka yi arba da juna, murmushi na sakar masa wanda a nan take Yah Maheer ya karkata akalar addu'ar shi zuwa
'Ya Allah ka mallaka min wannan baiwa taka idan alkhairi ce a rayuwa ta da addini na, ya Allah ka san yanda na ke son ta na ke jin ta a rai na, Allah na miqa dikkan ragamar buqatu na a hannun ka'
"Sannu da zuwa Yah Maheer bismillah Baba ya na nan"
Kamar wanda ya farka daga nannauyan bacci haka ya kalle ni, sannan ya sakar min murmushin da ya sanya gefen kuncin shi lotsawa, ban b'ata lokaci ba kuwa wajen cewa,
"Laaa dama kaima ka na da beauty point irin na mata?"
Dariya na qunshe, na qarasa zuba ruwa a tukunyar na yi gaba ya na biye da ni,sautin murmushin shi na jiyo a baya na sannan ya furta,
"Ki na so ne?"
Tsayawa na yi na juya muna fuskantar juna na wani tsuke dan qaramin baki na da a kullum shi ke rikita duk wata gab'a ta jikin Yah Maheer ba tare da na san da hakan ba, motse baki na da na yi ne ya ba wa gefen kunci na damar lotsawa nima,amma ba wani sosai bane kamar na shi, na ce masa,
"Ka gani nima ina da shi"
Idanun shi ya lunshe sannan ya yi saurin kewaye ni ya shige parlour, zaune ya tarar da Mama da Baba su na hirar su sama sama, hannun Mama riqe da carbi kamar ko da yaushe,
"Maraba da mutanen bauchi qaya, yanzu ka ke tafe? "
"Eh mama barkan ku da yamma, da fatan na same ku lafiya, Barka da Yamma Baba da fatan na same ku lafiya" ba yanda su Baba ba su ba akan ya zauna a saman kujera amma ya qi, ya samu waje tsakiyar su ya zauna a qasa.
"Lafiya qlou alhamdulillah Maheer, ya mutanen gida? Ya D'an uwana ina fatan ya na lafiya?"
"Ya na lafiya qlou alhamdulillah ya ce na gaishe ku sosai,..."
Barin wajen na yi na koma kitchen na deb'o masa sauran abincin rana da ya rage, domin girkin dare na gama a wannan lokacin, ina can zuba masa abinci ya sanar da su Mama dik abinda ya kawo shi asibitin Aminu Kano,albarka suka sanya masa tare da yi masa fatan alkhairi,ina shiga na ga ya deb'o takardun shi ya na miqa wa su Mama da Baba, a zato na sakamakon shi ya karbo na makaranta tinda ban san kan ya abubuwan makarantar yake ba a wannan lokacin, ba bata lokaci nima na zura kaina ina leqa takardun nashi, duk da bana fahimtar komai a ciki, amma hakan be hana ni leqawa ba, wani kallo mama ta bini da shi da ya sa na yi saurin sosa wuya na bar wajen, duk abin nan da ake yi idon Yah Maheer na kai na shi kuma Baba idanun shi na kan na Yah Maheer, wanda baya cewa komai sai rarraba idanun nashi a tsakanin mu, fuskar shi dauke da wani yanayin da ba zan iya nuna yatsa na ce gashi ba, iyaka dai na san murmushi ya bayyana a saman fuskar Baban.
Daki na koma na zauna ina harkokin gaba na, har Yah Maheer ya gama cin abincin shi Baba ya fita ya koma sashen shi, suka ci gaba da hira da mama, kamar Yaya da qanin ta ko Uwa da d'anta na fari.
Tinda abun nan ya faru Yah Maheer ya tafi gidan kawun shi da ke a nan garin kanon, a gefe daya ya na ci gaba da addu'ar zabin alkhairi da ci gaba da cuku-cukun tafiya qasar Turkiyya, ana haka ne tafiyar tashi ta samu tsaiko, ba tare da na san dalilin fasa tafiyar ba, na ji Baba ya na sanar da Mama cewar Maheer fa be samu wannan tafiya ba, sai dai a masa fatan alkhairi da dacen nasara.
Ganin haka ne ya sa Yah Maheer tabbatar wa da kan shi Allah ya zaba masa Mahreen ne a matsayin abokiyar rayuwar shi shi ne dalilin da ya sa be samu tafiyar ba, dan haka ba zai yi westing opportunity din shi ba ba tare da ya zo ya bayyana abinda ke ran shi ba, idan har aka amince masa aka bashi ni, to fa zumunci da kano ya qara qulluwa kenan, idan kuma aka ce ba za a bashi ni ba, zai tattara takardun shi da komatsan shi tsaf ya koma bauchi ba zai sake waiwayar Kano ba sai idan Allah ne ya qaddara zai dawo d'in, wannan shine dalilin da ya sa ya dawo daga gidan Uncle d'in shi da yammar ranar da na yi wanki a maqotan mu ya bayyana wa Baba soyayyar da yake min, abu ne da dama Baba ya riga ya jima da harbo jirgin shi kuma shima ya yi na'am da hakan a zuciyar shi ba tare da ya sanar wa da Yah Maheer d'in ba, jira kawai yake ya gama b'oye b'oyen nashi sai shi kuma ya amsa masa da ya bashi ni, tinda ya na da qualities din da kowanne uba zai so ya ba da auren 'yar shi ga irin mutum kamar shi, dan haka sai ya amince ya kuma yi masa qarin bayani akan ya jima da gano ya na so na shi ne dalilin da ya sa ya ke cewa ya min mijin aure, saboda gida bata qoshi ba ba za a baiwa dawa ba.
Wannan shine taqaitaccen tarihin Mahreen...........
Kamar yanda dangin Yah Maheer suka sanar za su zo kawo lefe da sadaki hakan ce ta faru, a cikin satin da suka sanar a cikin satin suka kawo lefe akwati hud'u,wanda aka shaqe shi da kaya a cikin su, mata ne guda uku sai maza uku,sun tarar da ni na fito daga wanka ba jimawa kaya na kawai na sanya, ban kai ga shafa mai ba suka iso, Addah Ummu na can na girkin tarbar su ni kuma na shimfid'a masu tabarma suka zauna na kawo masu ruwan sha da abubuwan motsa baki, Goggon Yah Maheer da Innar shi sai yaba tsarin halittata suke suna kumawa, a cewar su ya d'akko yarinya kyakkyawa ga hankali da kunya.se dai daga gani 'yar lukuta za a yi nan gaba na qara girma in ji Goggon shi (Allah ya jiqan ta da rahama)
"Alhamdulillah D'an azumi ya yi dacen mata, ga ta da yawan fara'a masha Allahu" cewar Goggon shi.
"Ki na ganin shi shiru shiru d'annema ya iya zab'e," in ji Innar shi wadda take da sanyin magana da sanyin hali irin na Yah Maheer sak.
Qanwar shi da ke shayarwa a lokacin ce ta bi ni parlour muka zauna ta na ta ja na da hira, ni kuma na kasa sakewa da ita, a haka Addah Ummu da Mama suka kira ni, na tafi kitchen na same su ruwa da abinci suka bani na tafi kai wa Baffanin shi da babban abokin shi da ya rako su, ji na yi gaba d'aya na kasa shiga parlourn saboda kunya, na jima tsaye Baba na ce min in shiga amma na qi, dariya suka yi suna jinjina yawan kunya ta da yarinta ta, ba tare da na ga sanda aka taso ba sai ganin Yayan shi na yi ya bud'e labule ya karbi farantin da ke hannu na, ya na dariya ya shige ciki, a wajen na dan bud'e labulen kadan na leqa kaina na gaishe su, amsawa suka yi cike da kulawa, kamar daga sama na ji Baba na ce wa,
"She is just 15 years old, i think she is going to be 16 this coming December 11th inshaa Allah"
Wayyooo me yasa Baba ya min haka, hirar su suka ci gaba wadda ta bani tabbacin cewa ita suke yi kafin na zo, kasa komawa gidan mu na yi saboda bana so na had'u da qanwar shi da ke min hira, kunyar ta nake ji itama, maqotan mu na fad'a, na sanar da Aunty Maryam me ke faruwa a gidan, suka had'u ita da mijin ta suna tsokana ta, qarshe ta bani lemon gwangwani ta zauna muna hira, mijin ta kuwa ya fita daga gidan, ba bata lokaci na hau kora lemon dan kuwa ina buqatar abu mai sanyi da zai kwantar min da abubuwan da ke taso min a zuciya da raina.
Ba su wani jima ba suka kama hanya suka tafi, ba tare da na sake zuwa mun had'u da su ba, nan fa Mama ta yi waya ta sanar da duk wanda ya kamata ya san cewa an kawo lefe na da kud'in aure na dubu ashirin, kafin kace me gidan mu ya zama ana ta shige da fice dan ganin lefen da aka kawo min.
Su Adda Ummu da Adda Firdous sai murna suke za mu yi aure a gari d'aya, ni dai abun mamaki yake bani wai yau ni ake maganar aure na,kuma da Yah Maheer? Ban san a wanne hali nake ciki ba a wannan lokacin, daga qarshe sai na tabbatar wa da raina addu'ar da Baba ya ce na yi ce Allah ya karb'a ya zamana shi ne mijin da zan aura, duk wasu mazan da suka jima suna neman aure na ya kada su daga zuwan shi, duk wasu mazan da suke cike da buri da yaqinin za su samu aure na har suka yi ginin da za su sanya ni ciki, ya rusa masu wannan ginin ba tare da ya sanya qarfi ko dagiya ba, ya miqa lamuran shi ga Allah dan ya bashi ni, kuma ya mallaka masa ni cikin sauqi.
Watanni uku bayan kawo lefe na kowa ya sakankance tare da bikin su Addah Ummu za a had'a namu sai magana ta sha banban, gaba d'aya sai na birkice wa Baba a gefe, na nuna masa ni fa ina so na kammala secondary school kafin na yi aure, na dame shi ba tare da kowa ya sani ba, ganin haka ne ya sanya shi roqon a jinkirta biki na dik da ban san uzirin da ya bayar ba a wancan lokacin, hakan ne ya sa aka janye maganar had'a biki na da na yayu na aka maida hankali a hidimar bikin su su biyu.
Yah Maheer ya shiga matsanancin damuwa inda har sai da ya yi 'yar qaramar jinya, domin kuwa ranar daurin auren su Addah Firdaus da ya zo dik ya rame ya fad'a hasken shi ya ragu, ga qarin haushin ya zo bikin da abokan shi dan su ganni ni kuma ina ta kukan banza an taru ana lallashi na, haushin shi duk ya qare akan yanda ake ta kallo na ina kuka, ko magana baya son bud'e baki ya yi, mama ta zaci ya na jimanta rashin had'a auren mu da na su Addah Ummu ne da ba a yi ba ya sanya shi shiga baqin ciki, ta dinga lallashin shi ta na fad'in,
"Haba Yayana (Yana da sunan yayan ta da suke uwa d'aya uba d'aya) ka yi hakuri inshaa Allahu nan ba da jimawa ba kuma za a zo a yi naku".
Haka ya dinga yak'e ya na nuna mata ba komai, ni kuma a b'angare guda an samu an jani parlourn dake waje.
Abinda ya kawo rikici da kuka na kuwa shin, an kawo motocin daukan amare mutane sun samu sun shisshiga nima na samu wata bus na hakimce, ina zaune sai ga Yaya Babba ya zo da Ummee wato matar shi, gata da tsohon ciki a wancan lokacin ina zaune Yaya Babba ya ce,
"Ah Mahreen har an samu waje? To sakko ki gani, in na shiga Ummee ta shiga sai kema ki shiga, kin ga saboda halin da take ciki ba za a barta a bakin qofa ba ko?"
Gaba d'aya kaina ya toshe ban yi dogon nazari ba na sauka, ina sauka kuwa suka haye mota sai ya zamana ba wani waje da ya yi saura da zan zauna, raina ya yi bala'in baci, amma se na danne na ce zan duba wata motar Yaya babba na ta min dariya, dammu a gidan mu yayun mu sun dauke mu kamar abokan su ne,akwai wasa da dariya da barkwanci tsakanin mu sosai, dan haka sai na tafi duba wata motar ban samu ba, ina cikin sulking cikin baqin ciki Yaya Sahabee ya kira ni riqe da buta wai na deb'o masa ruwa, ina karb'ar butar na fara takawa, a wannan lokacin Yah Maheer ya tinkaro ni da abokan shi, kafin su qaraso na durqusa a tsakiyar wajen na fashe da kukan baqin cikin da aka cusa min, nan take goggoni na da yayu na mata suka yo kaina ana bani hakuri,wanda suka san me ya faru se suka fara narrating abinda ya faru, Baffana da ke bi wa Baban mu da Baba ne suka taso suka zo wajen, Baba ya ce,
"Hadiza ku shigar da ita ciki,ki yi hakuri yau ko motata ce se na bayar an kai ki Bauchi dena kuka"
Haka Yah Maheer ya tsaya sororooo ya na kallon yanda na ke kuka kamar wata qaramar yarinya, domin kuwa Baby autar mu ma da ta ga ina wannan kuka tsayawa ta yi da nata ta na kallo na.
Haka Yah Maheer suka tafi a ranar da abokan shi basu samu yi min magana ba,danni ko sanin ya kawo abokan shi ban yi ba,kuma ganin shi be sa na ma ji ina son na tsaya kula shi ba balle ya ja min na rasa motar zuwa kai amare, ina zaune Yah Kabeeru ya shigo ya ce,
"To akoke kuka ya qare, leqa ki ga motocin can guda uku, ki zab'i duk wadda ta yi miki, a ciki zaki je garin bauchi,"
Cikin share hawayen da ya qi tsayawa a ido na na leqa,ido biyu muka yi da wata mota fara me kyau qarama, sai ta bani sha'awa, nan take na ce ta yi min, ba b'ata lokaci ya ja hannu na muka fita, na dakko qaramar jakar kayana na shige mota sai garin Bauchin yakubu garin su Yah Maheer..........
Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.
💅 *MAHREEN* 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 5:
A gidan Baffan mu aka ajiye amare, dan haka a nan aka ajiye ni tare da Yah Kabeeru nan gidan yake zaune da iyalan shi, kowa ya yi mamakin gani na, murmushi na dinga yi ina musu kallon ba kun taho kun bar ni ba? To gani se yaya?
Murnar gani na aka d'auki yi aka hau tambaya ta ya akai na zo? Na basu labari da yanda driver ke zuqa gudu kamar ba rayukan mutane a cikin motar, can muka baro motoci da yawa ba su iso ba, dan kuwa Motar da Addah Ummu ke ciki ma na riga ta zuwa, bamu wuce can asalin garin mu ba inda nan ne za a ajiye Addah Ummu sai da suka iso Baffan mu ya musu nasiha sannan aka dauki hanya.
Tafiyar minti arba'in da biyar ce ta sada mu da garin, inda na isa a motar uncle d'in Yah Maheer, ina ta bud'a hanci da ganin ni ma wata had'add'iyar baquwa ce ta musamman a wajen, garin Liman Katagum gari ne mai cike da ni'ima da kwanciyar hankali a wancan lokacin, ga tsafta da kyau a idanun mai kallo, wata iriyar iska ce mai sanyi ke kad'awa da dare wadda ke sanya mutum jin shauqin soyayya ko da ba ka da saurayi ko budurwa sai ka hau imagining ka na da su, yanayi ne da yake ratsa dikkan gab'ob'in jiki da ruhi, hakan ce ta sanya na fita qofar gidan Addah Ummu ina shaqar qamshin bread da ke tasowa daga wajen gidan, ina fita sai na ga ashe gidan bread d'in a kusa yake da su, murmushi na yi a raina na ce,
'Su Addah Ummu an zo gida, za a wa brodi cin Allah tsine uwar me qarya'
Cousins d'ina ne su ka fito suma dan su ga gari da kyau, dik da cewa babu wutar lantarki a lokacin amma akwai hasken farin wata sosai, ta yanda mutum zai iya ganin duhu ko hasken suturar d'an uwan shi, tare da cousins d'ina muka fara tattaki dan ganin ya garin yake, mu na tafe mu na hira cike da nisha'di, can gidan kuma an kai mana abinci manyan yayun mu da Goggonayen mu duk sun ci har an fara aikin gyara gidan amarya.
Bamu dawo ba sai da muka gaji dan kammu sannan muka dawo, ina zaune na gama cin abinci riqe da waya ta qarama wadda Yah Maheer ne ya sai min ita, ina ta latsawa, kira na gani ya shigo da wata Number da ban sani ba, a hankali na amsa wayar na kara a kunne na kamar me tsoron kar a sace ta ta wayar, sallamar da na ji ce ta sanya ni ajiyar zuciya mai qarfi,
'Ina Mansoor ga samu wannan Number tawa?' daga can b'angaren shi na ji ya amsa tambayar da ban furta a labb'ana ba.
'Kar ki damu na samu Number ne a wajen Ikleema' (Qanwar shi)
"Allah sarki ya kk?"
"Lafiya qlou tafiya ba sanarwa"
"A yi min afuwa, na san ka san ana biki a gidan mu, kuma dole zani kai amare, shi yasa ban sanar da kai ba,"
'Kar ki damu,da fatan kun isa lafiya?'
"Lafiya qlou alhamdulillah, ka san rabo na da garin nan kuwa?"
'Ah ah sai kin sanar da ni'
"Tin dawowa ta daga gidan Addah Babba"
Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce,
'Lallai an jima, tin ki na 'yar tatsitsiyar ki, gashi yanzu kin girma'
Tura baki na yi cike da shagwab'a ta da take jan hankalin masoya na ba tare da na san tasirin da take da shi a wajen su ba,
"Me ka ke nufi? Ka na nufin dai har yanzu ni yarinya ce, ka san dai na san body language din ka da duk wani amo da ke cikin muryar ka ko?"
Cikin jin dad'in furuci na ya sake kashe murya ya ce,
'Da gaske?'
"Sosai ma"
Kamar daga sama na ji muryar Aunty Meenah ta na cewa,
"Allah sarki Babana bawan Allah, an sa shi a kwana da wannan shagwab'ar, na san ya na can ya rikice ya rasa inda zai saka kan shi"
Da hannu na mata alamar ta yi shiru dan ba Baban nata bane, (Yah Maheer) murmushi ta yi ta zauna a gefe na itama ta na shan iska.
Ganin haka ne ya sa mu ka yi sallama da Mansoor ba dan mun so ba, hira muka dinga yi da ita, ta na sanar da ni d'azu bayan tafiyar mu shan iska yaran gidan su Yah Maheer sun zo gani na,suna roqon dan Allah gobe na je gidan su, murmushi na yi kawai, dan ko giyar wake na sha ba zan iya zuwa gidan su ba, to in je in ce na je wajen wa? Ban ma san gidan su ba tinda ban tab'a zuwa ba, zuwa na garin ma kwata kwata sau d'aya sau d'ayan ma ba wai na je gidan su bane, sannan time d'in be fara zuwa gidan mu ba, kallon Aunty Meenah na yi na ce,
"Su dai yi hakuri, me suke ci na baka na zuba? Indai wannan 'yar lukutar ce za su gan ta har sai sun gaji"
Dariya ta yi, ta na min surutun yanda nake yi wa jiki na tsiyar qiba,
"Ba za a kira ki da 'yar lukuta ba ai ke you are just chubby, masha Allah ina son irin jikin ki"
"Hahhhaaaa Aunty Meenah ba wani wayo fa, d'an lukuti d'an lukuti ne, siriri siriri ne,ba wani chubby duk salo ne na kar a kira me qiba da Fat"
Dariya ta yi ta na ta biye wa shirme na,har dare ya yi sosai muka shige gida dan mu kwanta.
A dakin matar Yayan mijin Addah Ummu za mu kwana, wanda dikka 'yan uwa muke na kusa ma kuwa, ina tsaka da d'aura zani Yayan mu ya shiga wato yayan mijin Addah Ummu,ya na gani na ya hau tasbihi ga Allah, a d'an rikice na juya na kalle shi, saboda a wannan lokacin a tsorace nake bamu jima da jin kukan mage ba, ni kuma a duniya ina tsoron ta sosai, a zato na ya ga magen ne shi ya sanya shi wannan tasbihin, yanda na riki ce ne ya sake sanya shi samun waje ya zauna,
"Ikon Allah, dama gidan Baffa Muhammadun akwai kalar wannan shine nima ban je ba?"
Wata ajiyar zuciya na sauke mai qarfi da ke nuna kwanciyar hankalin da na samu jin cewa ba mage bace.
Matar shi Aunty Khadeejah mai kirki dariya ta dinga yi, ko kad'an ban ga alamun b'acin rai ba a fuskar ta, duba da yanda Yayan namu ke ta yabo na da nuna maitar shi akai na, cikin murmushi ta ce,
"Ai se ka yi hakuri tinda dai Yah Maheer d'in Tafare ya riga ka,ba dan ma iko na Allah ba ai da tini yanzu ita ma ta na d'akin ta, to Allah be nufa za a had'a bikin ba,"
"Ke ki bari dan manzo, wai ki na nufin Yah Maheer shiru shirun nan har ya san ya zab'i mace kamar wannan?"
"To kai ma ka yaba balle shi da yake a nutse"
B'ata rai ya yi sosai har sai da itama ta sha jinin jikin ta,
"Ki na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 30