ba tare da na sani ba, ina shiga sai akai shiru ta miqe ta ce tafiya zata yi ga wannan ta kawo mana, ina bud'a ledar na ga kuka, daddawa, quli, da tasoyu, (gyad'a me gishiri) godiya muka hau yi mata sannan ta tafi.
Ashe tsugunno bata qare min ba, dan kuwa gulmar Safiyanu ba anan ta tsaya ba har gidan Yayar Baban Hauwa'u da ta riqe ta kafin ni sai da ya je ya guntsa mata Hauwa'unta na can na shan wahala.
Itama ta niqi gari ta zo bauchi amma se bata zo wajena ba, ta yi zaman ta gidan qanin ta, sai da weekend ya yi Hauwa'u ta je ganin gida, sai ta tarar da goggon ta ta zo, Goggon ta dik ta duba komai da ya kamata ta duba bata ga wahala a tattare da 'yar ta ba, dan haka Hauwa'u na ninke kayan ta da ta je da su ta kalli Goggon ta ta ce mata,
"Goggo kin ga wannan kayan Aunty Mahreen ce ta bani su fa,har da wannan da wannan"
Gyara zama Goggon ta tayi ta kalle ta sosai sannan ta ce,
"Ni kam "yar Goggo (haka suke kiran ta) da gaske ne kuna shan wahala a wajen matar Maheer?"
"Goggo me ki ka gani?"
"Zuwa aka yi aka sanar da ni abinda ke faruwa shi yasa na kasa nutsuwa na ce se na zo na gan ki, se kuma na ke ta ganin sab'anin abunda aka sanar da ni"
"Lallai kam duk wanda ya ce maki ina shan wahala qarya yake, ki duba fa ki ga abubuwan da ta bani, ga girki yanzu da na iya,"
"Ance a parlour kuke kwana a qasa"
"To Goggo in bamu kwana a parlour ba d'aki zata shigar damu tinda d'akin d'aya ne? Kuma Goggo sabon bedsheet d'in ta me tsadar me laushi shi ta bamu muke kwana akai fa,wai ke Goggo wa ma ya fad'a maki wannan qaryar ne?"
Nan take ta sanar da Hauwa'u cewar Safiyanu ne ya je har gida ya sanar da ita, shine ta zo ta gani da idon ta, nan fa Hauwa'u ta zauna ta dinga sanar da ita yanda muke zaune da yanda na riqe su, tabbas idan suka min laifi ina zane su tasssss, sannan ina musu fad'a sosai in ta kama, amma baya hana in yi wasa da su, dan ina jin kaina da kad'an na fi su, hatta da 'yar carafke yi muke a parlour ko tsakar gida, har da 'yar gala gala muke zanawa da gawayi a tsakar gida mu yi.
Bayan Hauwa'u ta gama weekend d'in ta ta dawo take sanar da ni abinda ya faru, nan take Suwaidatu ma ta ce ai Safiyanu ne ya ce wa Mama tana shan wahala shi yasa ta zo ta gani, na yi ta kukan baqin ciki a ranar , na tuna yanda na tarbe shi da girmamawa da karramawa da kulawa, na tuna ko had'uwa ma da yaran beyi ba, me na masa na yi min sharri?
Tin daga ranar se Maman Suwaidatu ta qara qaimi wajen zuwa akai akai, har na shiga makarantar Wayar makafi dan ci gaba da Secondary school d'ina da ban qarasa ba, inda na had'u da mata nagartattu masu so na,a nan na had'u da qawata me abun dariya me suna 'yar Malam, (alkhairin Allah ya kai maki)
Ina nan ina zuwa makaranta ni da yaran cikin nasara ba wata damuwa,dake qarfe tara ake shiga makarantar dan haka kafin na fita sai na yi abincin safe da na rana, na gyara waje, wanke wanke ne kawai bana yi shima kuma watarana kan na dawo Maimunah ta min, watarana ma har girkin kafin na dawo ta d'ora min, idan ban bar abinda zan dafa a waje ba zata tabbatar ta gama nata abincin saboda na ci idan na dawo se na mana namu.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya da dad'i da ba dad'i halayyar Isma'il na damu na, saboda kullum da sabon salon takalata fad'a da yake fitarwa, gashi idan sun min abu gaba d'ayan su har Abubakar d'in sai su yi sauri su sanar da Yah Maheer, saboda gani suke ko ina sanar da shi abubuwan da suke min dake shi ba me magana bane ya kyale su ne kawai ya na kallon su da abun,ni kuwa ba su san ban iya kan qara baz na fi qaunar duk wanda ya min abu ko wanene na tsayawa kai na, in sun sanar da shi shi kuma baya sanar da ni nan take,sai dai in muna kwance muna hira da dare sai ya ce,
'Baby na ni kuwa me ya had'a ki da wane? Na ga baku jituwa kamar da?'
'Wani abu aka ce maka na yi?'
'Ah ah tambaya ce kawai nake maki'
Anan zan zayyana masa komai ba tare da na yi ragi ko qari ba, ko da kuwa na banka rashin kunya to zan fad'a tinda ni aka fara tab'a wa sannan na maida martani, anan Yah Maheer ze sanar da ni dama sun fad'a masa ya na so ya ji daga baki na ne, watarana ya ce yanda na fad'a masa haka suka fad'a ko a samu sab'anin magana wanda daga wajen su ne dan kawai su kare kan su, haka zai ta bani hakuri ya na min nasiha, tare da tabbatar min dika rayuwar wani d'an lokaci ne qayyadadde dan haka na qara hakuri watarana sai labari, haka zan hakura na dole ba dan na so ba musamman in sun min qarya, dan na tsani a min qarya a rayuwa.
Bangaren Abubakar kuwa zaman mu muke lafiya ba tare da wata matsala ba, wanda ni ban sani ba ashe ta qarqashin qasa Abubakar shima na nan na zagi na a duk inda ya zauna ko ya samu dama, dake yana da wayo kuma baya so na ji se ya yi gulma ta ya san yanda ya danne kar na sani, ina zaune da su da zuciya d'aya ba tare da wani mugun nufi ba,a hankali na sanya wa zuciyata cewar duk abinda Isma'il yake mun zan na d'aukar shi kamar irin samun sab'anin nan da ake in zama ya kama ka da wani ba dan komai ba sai dan samun nutsuwar raina da kuma cire qiyayyar kowa a raina.
A hankali halayyar su ta fara min yawa ta yanda ba a wuce sati d'aya ba tare da mun samu sab'ani da su ba, har ta kai ta kawo shima Abubakar da ke b'oye qiyayya ta a ran shi ya fara bayyana min wasu halayen da ba su yi min dad'i sam a raina.
A hankali na zama masifaffiyar qarfi da yaji dan ni ban yarda ni da gidan aure na ba wasu su takura min har na rame ko na shiga damuwa da tashin hankali ba,sai ya zamana mun koma rayuwar kana yi min in mayar maka da me zafi.
Haka ne ya janyo watarana da rana bayan na dawo daga makaranta kwatsam sai na zuba wa kowa abinci na shiga wanka, ina fitowa daga wanka na yanke shawarar zan kwanta na huta, ban kammala sanya kaya na ba se ga Mama ta sallama ta zo, parlour ta wuce kai tsaye Suwaidatu da Isma'il da ke d'akin su sai suka fito akai ta hira, se da na gama shiryawa sannan na je, ga ba abinci na Hauwa'u ne kawai ya rage ita ba a lokacin take dawowa ba kowa na riga ta tashi daga makaranta.
Ruwan sha na kai wa Maman muka gaisa na tashi na basu waje kamar yanda na saba, na shiga d'aki na yi shimfid'a a qasa saboda zafin da ake,na yada pillow na sa a qasa na kwanta, ban jima da kwantawa ba na ji alamun tafiya da sand'a ana dosowa qofar d'aki na, shiruuuu na yi na luma kaina cikin pillow ina sauraren wanene me yi min sand'a, a hankali na bud'e ido na ta yanda zan dinga ganin me tahowa ba tare da ya yi zargin ido na biyu ba, ai kuwa ba a jima ba sai na ga inuwar mutum a saman kaina..............
Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 14
Qafafun Suwaidatu na gani daf da inda na sanya pillow, a hankali na ke bud'e ido na yanda ba zata gane idon nawa biyu ba, kallo na ta yi na d'an wasu daqiqu kad'an sai ta juya ta koma parlour cikin sand'a, da ganin haka sai na ji jiki na ya yi mugun sanyi, na kasa yarda da abinda na gani.
Menene ma'anar yi min sand'a?
Me za a aikata min?
Me ke faruwa?
Wad'annan tambayoyin na dinga jerowa kaina, tashi na yi a hankali nima na zauna yanda ba za su ji ni ba, na kai kunne na wajen prlour dan na ji me za su tattauna akai na, ji na yi murya qasa qasa Suwaidatu na sanar da su cewar bacci nake, da jin haka suka d'auki cin nama na.
Ina zuba musu abinci kad'an,
Ina wa Isma'il fad'a kamar ni ce gaba da shi,
Ina hana shi tab'a abubuwa sai in ta masa gori akai, sauran abubuwan da ban san sanda aka yi su ba.
Ita kuma Suwaidatu sai cewa ta yi ai bana wasa da ita sai dai na ja Hauwa'u d'aki mu yi ta hira, ko in Yah Maheer na nan mu bar ta a waje mu shige d'aki.(Yaran da har 'yar carafke muke yi da yar burum burum da sauran wasanni na yara)
Shawarwarin yanda za ta dinga kula da kan ta da kuma abinda za ta dinga yi min idan haka ta sake faruwa a tsakani na da su ta basu, sannan ta musu sallama ta tashi zata tafi, na so matuqa a wannan lokacin na je na tinkare su da maganar amma na danne na ci gaba da baccin qarya na har ta fita, abun na raina ya na b'ata mim rai na kasa cire maganganun su a raina har dare.
Yah Maheer ya tafi qauyen da ya samu aiki dan ganin yanayin wajen dan haka a daren haka na kwana cikin baqin ciki ban samu mai kwantar min da hankali ba.
Washegari da sassafe na yi wanki na shanya a igiya na hau yin sauran ayyuka na raina a matuqar b'ace wanda ya sanya Suwaidatu fara shan jinin jikin ta, domin kuwa hatta da murmushi kasa yi mata na yi, saboda qaryar da ta min, ban tab'a banbanta ta ita da Hauwa'u ba, iyaka watarana ina kiran Hauwa'u d'aki dan ta taya ni gyaran d'akin da ita Suwaidatu ba zata iya ba, kuma ba dan komai nake hakan ba sai dan Suwaidatu ta yi qarama ba zata iya ba, sannan ko ba komai Hauwa'u na da wayon ta zata koyi wasu abubuwan, barin ta kuma da muke yi mu shiga daki ni da Yah Maheer banga dalilin da zai sa na shiga d'aki da ita ba a wannan shekarun da ta kai shekara goma ba,to menene laifi a cikin hakan har da za a yi gulma akai?
A haka cikin tunani da b'acin rai na kammala aiki na har girkin rana sannan na shirya dan tafiya makaranta ina fita na ci karo da Isma'il na wanki a tsakar gida, nan da nan baqin cikin abinda suka yi ya taso min na kalle shi na kalli igiyar da na yi shanya se na ga ba rabin kayan da na shanya, sauran kuma da ke kai an matse su waje d'aya,cikin b'acin ran da na jima ya na nuqurqusa ta na ce,
"Kai Isma'il uban wa ya ce ka kwashe min kaya a igiya ka cukurkud'a min wannan?"
Da tsananin mamaki ya miqe tsaye ya na kallo na, ci gaba da karkad'a qafa ta na yi na harare shi na bud'e qofa na wuce makaranta raina na ci gaba da b'aci, ina zuwa makaranta Mommy (principal) ta ce ba makaranta, nan da nan kuwa na hau haramar komawa gida, a lokacin nan akwai wata 'yar ajin mu Maman Zaid ta kalle ni ta ce yau dai baki yi fara'ar da ki ka saba yi ba a koda yaushe, yaqe kawai na mata na ce ina zuwa, da sauri na koma gida ina addu'ar Allah ya sa Isma'il be fita ba, ina shiga gidan kuwa na tadda shi ya na ci gaba da wankin shi amma rantsi da alama baqiqairin yake shima saboda abinda na masa kafin na fita, ina shiga har zan wuce na shige cikin gidan na dawo baya na kalle shi na ce,
"Ammmmm....Yauwaaa ka fad'a wa Maman ku in ta qara zuwa ku ka yi gulmata a parlour na abun ba zai mana kyau ni da ita ba,ta yi na farko na kyale ta yi na biyu na kyale amma duk randa ta yi gangancin yin na uku wallahi rai sai ya yi bala'in b'aci saboda shi babba kama girman sa yake, in ko yaqi yaro ba zai ji kunyar bi ta kai ya take ya murje da qafar shi ba" (na yi alamar takewa da murjewa da qafan)
Bud'ar bakin shi sai ya hau fad'in,
"Waye ya yi gulmar ki?su waje sukai gulmar taki?"
"Su sun san kan su, in ba an raina min hankali ba ina qoqarin zama da ku amma ku wani abun ku ke hangowa dan ku b'ata min rai? Me na yi maku ne mara kyau a rayuwa? Ba fa ku sanni ba a da balle ku ce na jima ina maku wani mugun abu da kuka tsane ni, haka kawai ina fama da rayuwa ku zo ku takura min?"
Haka na shige ciki ina ci gaba da mita, cikin sauri ya gama wankin ya bar gidan, Maimunah kuwa bayan mun had'u na ke sanar da ita ai ba makaranta yau shi yasa na dawo da wuri
" Allah sarki gaskiya mana na ga har kin dawo, uhmmm Aunty Mahreen ni kam ki na bani mamaki na yanda baki d'aukan raini a wajen qannen mijin ki, kuma ban tab'a ji kun samu sab'ani da mijin ki akan hakan ba, ko dai be san meke faruwa bane?"
"Ya sani, tunda suna fad'a masa, iyaka ya tambaye ni, idan na fad'a masa gaskiya ba dad'i ba qari to se ya bani hakuri inda na yi kure ya gyara min, inda suka yi kure ban san ya yake handling d'in su ba, shi dai kullum fatan shi mu zauna lafiya."
"Allah sarki, dama gashi shiru shiru ba ruwan shi shi kam,Allah ya kyauta ya daidaita zaman ku,"
"Ameeen ya Allah, ni bani da burin da ya wuce na zauna da su lafiya, ban yi complain ba a zaman su saboda na san mu 'yan dangi ne muna da yawa a zuri'ar mu, dole haka zata faru amma me ya sa ba za a zauna lafiya ba?"
"Hummm haka wasu suke fa, ke dai Allah ya kyauta d'in kawai,"
Jin shigowar shi muka yi bakin shi d'auke da sallama ciki ciki, ya wuce mu dif dif dif, ni kuwa ko a jiki na qarshe gidan ya zo ya bari da alama wajen aiki zai tafi duba da yanayin shigar shi.
Washegari kuwa ni har na manta me ya faru, saboda ni bana riqo, kuma duk yanda za mu yi fad'a da mutum anjima ko washegari in na gan shi se na masa magana, haka ce ta faru tsakani na da Isma'il da safen bayan na gama yi mana abun karyawa na gaishe shi na ci gaba da b'ata rai nima tinda na ga irin amsawar da ya mun.
Ina nan goye da yarinyar maqotammu wasu ustazai da ke kawo mana ita raino idan maman ta zata je makaranta, ya zo ya sake wuce ni kamar zai taka mana shimfid'ar da na mana, janyewa na yi domin nima na san ta yi kan hanya da yawa, abincin shi ya d'auka ya shige d'aki,ba jimawa na ga ya fito, ba tare da na sani ba ashe ya hango Yah Maheer ya sauka a machine ya nufo gida ne, ina nan zaune na ji sallamar shi cikin zumud'i da qaguwa na juya muka had'a ido, murmushi muka sakar wa junan mu, cikin raina ina tsaki na ce,
'Ba dan wannan qaton ba da tini yanzu mun rungume junan mu tinda su Addah ma ba su nan,'
Jakar hannun shi na karba, shi kuma ya na ta bin fuskata da kallo,
"Dama yau zaka dawo shine baka fad'a min baaaa?"
"A yi hakuri Babyna, kin san ban tafi da niyyar kwana ba amma na ce maki in ban kammala samun abinda nake nema ba na accommodation dole zan kwana in yaso sati na sama sai na fara zuwa daidai yanda muka tsara ko?"
"Allah ya so ka na yi abinci, bari na sa maka ruwan wanka in ka yi se ka wuce masallaci ko?"
"Eh na kuwa gode,"
Kamar daga sama muka ji muryar shi,
"Malam Maheer ina son magana da kai"
Shi ya fi qarfin ya kira shi da yaya, dan kuwa be tab'a ba se dai ya ce Malam,ganin ze b'ata wa miji na rai daga dawowar shi ne ya sa na yi saurin cewa,
"Dan Allah ka adana maganar ka har ya huta"
Kallo na Yah Maheer ya yi ya ga yanda raina ya b'aci nan da nan, nan take ya gane akwai matsala, dan haka be bani damar yin yanda na so ba, sai ya ce wa Isma'il.
"Bismillah mu je parlour"
Sannan ya kalle ni cikin lallashi ya ce,
"Just give us 5minutes yanzu zaki ga na dawo ok?"
Gyad'a masa kai kawai na yi, sannan na wuce na kai masa ruwan wanka na kai abinci d'aki, na nad'e shimfid'ar da na mana ni da yarinyar, ina tsaka da fesa turare na na ji an bud'e qofa Yah Maheer ya leqa kan shi sannan ya ce,
"Baby na dan Allah d'an zo mana,"
Ya fita ba tare da ya jira amsata ba, bin bayan shi na yi, na shiga parlour, na same su zaune a kujera kowa na zaune jugummm, cikin muryar shi me sauqi da laushi da rashin son hayaniya da tashin hankali ya ce,
"Babyna garin ya ki ka zagi mahaifiyar shi? Me ya faru?"
Babban abinda ke burge ni da Yah Maheer kenan, baya yanke hukunci sai ya ji ta bakin kowanne bangare domin hakan shi ne adalci kuma shi ne ya fi dacewa gudun kar wani ya yi qarya a take haqqin wani.
Nan take na zayyano masa tin daga ranar da suka fara magana ta a parlour da ta zo, har abinda ya faru a jiyan.
Kad'a kai Yah Maheer ya yi ya kalli Isma'il ya na jiran ya ji ko zai musanta me na ce, ya jima kafin ya yi magana cikin son kare kai, ya ce,
"Na rantse da girman Allah mu ba mu yi maganar ta ba,"
Wani irin kallo na masa na girman ka ya gama fad'uwa a ido na in har za ka yi abu ka ce ba kai ba, to yanzu zan ji ka fita a rai na, nan take Yah Maheer ya had'a mu ya mana nasiha sosai, wadda gaba d'aya akan zaman lafiya ne da riqo da zumunci sannan ya gargad'e ni da kar in sake zagin mahaifiyar shi, domin shi ma mahaifiyar shi ce, ko me zai faru kar na sake zagin kowa na zo na sanar da shi zai dau mataki, sannan daga qarshe ya bamu hakuri baki d'aya tare da nuna mana duniyar nan ba ta da tsaho ba ta da girman da muke ganin ta na da shi, komai nata qalilan ne, mu yi taka tsantsan da duniyar dan kuwa ba matabbata bace.
A haka muka tashi baki d'aya, Isma'il ya shige d'akin shi ni kuma na wuce namu, Yah Maheer ya shige wanka, ana haka Maman Humairah maqociyar mu ta dawo na bata Sumayyah muka yi sallama na koma ciki.
Masallaci Isma'il ya jira Yah Maheer suka wuce a tare, ina nan zaune ina tunanin qaryar da Isma'il d'in ya yi, wai ba su yi magana ta ba bayan na ji da kunnuwa na ba fad'an akai ba balle na ce qarya akai,
"Allah ya kyauta"
Shine abinda na fad'a na wuce na sake yin wanka na yo alwala na shirya cikin kayan da na san Yah Maheer na mutuwar so, dan dole ne na wanke masa b'acin ran da aka dasa masa daga dawowar shi, turaruka na feshe jiki na da su na zumbula qaton hijabi na har qasa na yi sallah, ina nan zaune na ji dawowar su har Abubakar da su Suwaidatu.
Abincin shi ya roqi na kai masa parlour ya na so su yi hira da 'yan uwan shi, har cikin raina ban ji komai na b'acin rai ba tinda ya saba ce min bari ya je su yi hira, dan haka can na mayar masa suka zauna kowa na cin nashi ana hira har da Isma'il d'in domin ya rage nashi kafin ya fita dan haka sai ya dakko ya qarasa.
Ina nan zaune aka kawo wuta na kunna kallo ina yi ina nishad'i na nima da TV, a haka har na kula gaba d'aya wajen ya yi shiru, sakamakon shagala da kallo na da Yah Maheer ya yi, su kuma 'yan hirar tashi sai suka shagala da kallon mu baki d'aya, ni kuma hankali na be kawo kan su ba baki d'aya sai da na ji shirun ya yi yawa sannan na kalli inda suke zaune, ido na gani a kaina, wanda ya sani murmusawa har sai da hushirya ta ta bayyana, da sauri na miqe na bar wajen na shige d'aki na.
Ko minti biyar ban yi ba na ji sallamar Yah Maheer ya shigo, sabuwar gaisuwa muka dasa da hirar yaushe gamo kamar wadanda suka yi shekaru biyu basu had'u ba.
*********************************
Shirye shiryen tafiyar Yah Maheer qauyen Bura ya tashi gadan gadan, ya sai duk wasu abubuwan da zai buqata a matsayin shi na wanda zai na zama a can sai qarshen sati ya dawo, ranar da zai tafi da kuka muka rabu, shi ya na kwalla ni ina kuka wiwi kamar wata qaramar yarinyar da iyayen ta za su yi tafiya su barta, da kyar na lallashi kaina na koma gida bayan na raka shi har bakin titi.
Niqabi na da hijabi na na cire na ajiye ba tare da na ninke su ba, na fad'a saman gado na hau rera sabon kuka, wayata ce ta yi qara na miqa hannu na d'auka saboda na gane ringtone d'in, ina jin sallamar shi na sake fashewa da kuka, da kyar Yah Maheer ya lallashe ni na yi hakuri na rungumi qaddara, na tabbata ba dan zaman qannen shi ba a lokacin nan tare za mu tafi,dan haka hakuri na ba wa kaina na fita parlour muka hau hira da Abubakar jefi jefi.
Ban tashi sanin me ake cewa kewa ba sai da dare ya yi, na kasa bacci Hauwa'u da Suwaidatu na ce su dawo cikin d'aki su kwanta saboda ina jin tsoro, ko tafiyar da ya yi ma haka muka yi.
Har qarfe sha biyu na dare ido na biyu, ga wayata ba cajin da zan kunna haske, yaran nan kuma sun bata torch light, ba ni da wani hanyar da zan samu haske, se dai na danna wayar na ga waje in ta dauke na sake dannawa.
Ina nan zaune na jingina da allon gado na ji wani bacci me mugun dad'i ya sace ni, ban fi minti biyar ba na farka a tsananin firgice sakamakon wani mummunan mafarki da na yi wanda na kasa tuna shi bayan na farka d'in,wayata na haska da d'an hasken nata da ba shi da yawa, gaba na ne ya yanke ya fad'i qirji na ya buga, nan da nan gumi ya hau tsattsafo min, da sauri na fara ja da baya ina kwaranyar da ruwan hawaye daga idanu na dika biyun, duba na na sake kaiwa inda na ga mace na zaune a bedside table d'in daki na,ta sha lullub'i da mayafin atampa me duhu.
A zato na gizo kawai take min saboda a tsorace nake,na kashe wayar na sake kunnawa sannan na sake haska inda na ga mace na zaune d'in, ta na nan zaune kamar yanda na barta, salati na sanya sannan na hau karanto ayoyin ruqya da na sani a baki na, ina fara karantawa hasken wayata ya dauke, na yi sauri na sake kunnawa, ina kai dubana wajen se
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 30