yi hakuri dan Allah Allah ya jiqan Momcyn mu ya yi maka albarka, Allah ya ja mana da ran Baba ya qara masa lafiya..I love you da yawa Yah Maheeruuu naaaaa"
Ina faɗa ina jan kumatun shi guda ɗaya, da fari mamaki na ya yi dan duk tsahon zaman mu a da ban cika furta masa kalmar I love You baki da baki ba sai dai a rubuce ko in ya faɗa min na ce masa Me too, shine kullum baya fashi rana bata fitowa ta koma ba tare da ya furta kalmar I love you Baby Na ba,Wani qayataccen murmushin jin dad'i ya yi sannan ya kwace kumatun shi a hannu na ya saita hannu na kamar zai sumbata se kawai na ji ya kafta min cizo a yatsa ya wuce daki ya na dariya, alqawarin ramawa na yi kamar ko da yaushe in irin haka ta faru daga murya ya yi ya ce,
"Yaushe ne dama ake shafar ki ko da tissue ne baki ce zaki rama ba ke?"
"Babu rana" na mayar masa da amsa nima.
****************************
Kwana na biyar ina jinyar gefen ciki na kafin ya yi sauqi, daga baya jinin ma ya ɗauke ya dena zuba.
Qoqarin rage qiba na fara yi, dan kuwa yanzu shi ne a gaba na,tunani na yi na ga in ba shinkafa ba se garin masara in an auno wataran sune kawai abincin da muke ci, to mu me ma muke ci da zai qara min qiba a wannan halin dai da muke ciki na a dai ji qundu ya samu hatsi,(Na manta shinkafa da garin masarar carbohydrates ne)da ne na tara qiba kwarai saboda ko ba komai muna cin mai kyau mu shan mai kyau kuma mu ba wa wasu ma, amma yanzu? Yanzu se dai mu ci duk abinda ya zo hanyar mu.
********************************
Wata ranar juma'a na tashi da sassafe na yi wanka na yi alwala na yi sallah, domin ni da asuba nake wanka na in da hali na yi kwalliya sosai, in kuma 'yan kwalliyar ba sa kusa na sha gayu na ba tare da na shafa komai a fuska ta ba, yau ma qananan kaya na saka dogon skirt sky blue da ratsin pink se qaramar shimi me siririn hannu sky blue, duk inda na yi idon Yah Maheer a kai na, ni kuwa a rai na ina ta murna ko ba komai kowacce mace burin ta bai wuce ta ga wanda ta yi kwalliya domin shi ya yaba ba, Yah Maheer bayan yabawa da baki, zai yaba a aikace sannan zai yaba da bina da kallo da murmushi da kalaman qauna, lokuta da dama na kan yi zaton kawai zuzuta ni yake amma ban kai yanda yake tunani ba.
Suna kammala cin abinci mu ka yi sallamar mu kamar yanda muka saba kullum se ya dauki Suwaidatu a machine suka tafi makaranta, se da ya ajiye ta sannan ya wuce nashi makarantar inda ɗalibai ke jiran shi.
Ina nan zaune ina huce gajiyar aikin da na yi, har bacci ya fara d'iba na na miqe zumbur na hau Shara da gyare gyaren gida, a zuciya ta har mamakin yanda na ke ta gyara gidan nake yi se ka ce wata mai tsammanin baquwa ko baqi na musamman, haka dai na kammala na samu waje na zauna ina huta wa can na d'akko comb na hau tsefe kai na, ina cikin tsifa na yi guda uku na ji ana buga gate, murmushi na yi na ce,
'Tooo da alama hasashe na ya zama gaske baqi na yi'..........
Zuwa gobe ko jibi mun ji su waye bakin.
*Mutanen kwarai Assalamu alaikum...ku yi hakuri da rashin ji na da ba ku yi ba jiya, ina ga har da shekaran jiya ma ko? Banda lafiya ne ya sa amma na ji sauqi sosai Alhamdulillahi yau...kun ga dalilin da ya sa bana so na karbi kudi sai na kammala novel saboda halin yau...ku zo ku bada kudi ku ji ni shiruuu ace na jima..Ni kuma bana so a jira ni...Dan haka ku taimaka ku fahimce ni na gode. Mu na daff da kammala part one inshaa Allahu, duk mai so a sanya ta group na kuɗi ta min message a WhatsApp ta wannan No 09031416423*
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL FIFUL WHATSAPP ME ON THIS DIGITS 09031416423 IF YOU WANT TO BE IN MAHREEN PAID BOOK GROUP....THE PAYMENT WILL BE AFTER I FINISH THE WHOLE NOVEL THANK YOU*
PAGE 33:
Ido biyu mu ka yi da Rasheedah wato matar mai gidan da muke ciki, cikin farin ciki da sakin fuska na tarbe ta mu ka shiga cikin gidan ina yi mata sannu da zuwa, har dakin da aka sauke mu na shiga da ita, muka baje anan mu ka hau gaisawa.
Rasheedah na ɗaya daga cikin mutanen da suke so su ga yau ace nima na riqe d'a ko 'ya na kai na,dan haka ta na qoqari sosai wajen bani shawarwarin da suka dace,wannan ne dalilin da ya sa bayan mun gaisa ta d'akko maganar haihuwa,ta ke sanar da ni wani method da ake yi na IVF wato In Vitro Fertilisation, nan take ta hau yi min bayanin yanda ake yin shi, ina ji sai na ji hankali na ya tashi tsoro ya cika zuciya ta, amma ko a fuska ban.nuna mata hakan ba, ina ci gaba da tsifa ta mu na ta hirar, can qasan zuciya ta ina tunanin me zan kawo mata,bamu da komai sai ruwan pampo, se wake da shinkafa da na dafa kuma kaɗan ne ba yawa,haka dai na miqe na je na debo ruwan sha da abincin na kawo, muka ci gaba da hira,cikin hirar ta take sanar da ni cewar ta na dauke da ciki, murna na fara yi ina yi mata addu'a ita da abinda ke cikin ta, haihuwa ta biyu kenan za ta yi da izinin Allah, nan take take nuna min da zata samu hutu tabbas da hakan zata fi so, ni kuwa Se na hau yi mata nasiha da nuna mata ta gode wa Allah ta kuma rungumi kyautar da ya musu hannu bibbiyu, ni ai na ishe ta misali, gashi shekarun aure na sun fi nata kuma ban haihu ba,godiya ta yi wa Allah ta miqe ta ce za ta shiga toilet.
Tashi nima na yi na bi bayan ta muka fita, dake toilet din daf yake da dakin da muke se ta shiga, daga yanda ta fito na gane she was pleased with yanda nake kula da wajen, tunda dama tun da ta shigo na kula ta na ta murmushi.
Freezer din su ta buɗe ta gani ni Kuma Ina biye ina bata labarin karbar naman kan da aka yi, muke dariyar ban san ma'anar langab'u ba,nan take nake sake bata hakurin b'ata freezer din da na yi wajen wanke wa,ta nuna babu komai,mu na ta tafiya se gamu har kitchen, ta ce za ta d'au ki oven qarami, to ni shangai furar daka ban ma san da zaman shi a gidan ba, ina biye da ita ta d'akko shi,se a sannan na san da zaman shi.
Gani ta yi kamar da risho muke amfani nan take ta nuna rashin jin daɗin ta, ta ce,
"Mi da baku anfani da gas cooker? Kuma haɗe yake da electric fa, naga baku anhwani (amfani) da abubuwa da yawa mi halan?"
Murmushi na yi mata na hau magana cikin barkwanci na da mutane ke yawan faɗin ina da shi, na ce,
"Yo ni ina na iya amfani da kayan nan? Kedai banni da rishon da shi na saba, Allah ya saka maku da alkhairi abinda ku kai mana,Allah ya biya ku ya rufa asiri duniya da lahira,"
"Ameeen, amma wallahi da kun yi amfani da komai, na ga ba TV ina TV? Ki na zaune ke kaɗai"
"Ai bamu tarar da TV ba, da alama ba TV a parlour ko an daga ta"
"Ohhh aikin....(ta kama suna) ne, shi ne ya tattara har da TV,"
"Babu komai wallahi, dan Allah ki ma bar wannan maganar ai mu Alhamdulillahi ba abinda za mu ce sai godiya"
A parlour muka tsaya ta yi min sallama na koma na ɗauki hijabi na na raka ta har bakin mota ta shiga ta ajiye oven ɗin ta sannan ta sake jaddada min mu yi tunani akan IVF din nan, an yi wa mutane da dama kuma ana dacewa.
Godiya na yi mata sosai sannan na koma gida ina tunanin maganganun ta, na hanga na hango ba ta yanda zan iya yarda a min wannan abun, se na ga kamar za a wahala matuqa, ni kuwa bana son wahalar da wajen nan, irin yanda nake da shegen tsoro ba zan iya ba, ko da Wasa ban yi wa Yah Maheer maganar ba, fatan alkhairi na yi mata saboda yanda take so na da alkhairi ,ya na da yawa shi da Suwaidatu su ka ci abinci mu ka hau hira sama sama.
Yah Maheer ya Kula ina yawan tunani, tunda ya tambaye ni sau ɗaya me ke damu na, se kawai na ga lokaci ya yi na in fita daga gidan na je kitso dan in ba haka ba to fa daga tambaye tambayen nan zan karya magana ta zan sanar da shi komai, dan ni ko laifi na yi se na fada masa hankali na ke kwanciya.
Kitso na tafi cikin unguwar gidan su Fateema, ana min kitso ina tunanin anya ba za mu gwada ba? Wataqila mu dace tunda an ce ana dacewa a haihu lafiya.
Sanda ta gama min kitson ma ban sani ba saboda na tafi yawon tunani hankali na baya wajen kwata kwata.
Magana ta min dan na san cewa an fa gama kitson, wannan na miqe na bada kuɗin kitso na musu sallama na kamo hanya na yo gida, ko da na zo Yah Maheer ya fita Masallaci dan yin sallar la'asar, hira mu ka fara da Suwaidatu can na d'akko carpet ɗin da aka malala a tsakanin parlour kitchen da sauran dakuna, qofa na bude na fitar da shi na baza a tsakar gida na hau wankin shi, se da na wanke tasss na shanya sannan na hau aikin cire yana duk da ba bu wani yanar sosai dan ina qoqari matuqa wajen cire ta akai akai, duk aikin nan da nake tiqa wai dan duk na manta maganar IVF ne, dan ji nake wata zuciyar na fizga ta akan ko za mu gwada ne?
Kwana uku tsakani na kasa faɗa wa kowa kuma na kasa dena tunanin abun, Yah Maheer ya gaji da bin kai na na faɗa masa me ke damu na, qarshe da kai na na zauna na yi wa kai na karatun ta nutsu, cikin rai na na ke faɗin,
'Wai me ke damun ki ne Mahreen? Ki nutsu kar ki sanya wa kan ki wani ciwon saboda tunani, duk abinda Allah ya yi nufin zai faru da bawa, bawan nan be isa ya wuce qaddarar shi ba, sai dai addu'a na sauya wasu abubuwan, dan haka ki ci gaba da addu'a akan zabin alkhairi daga wajen mai bayarwa Allah, ina ki ka bar halayyar ki ta roqon Allah kuma ki saddaqar ki sakankance ki kwantar da hankalin ki dan kin san matsalar ki ta je inda za a yi maki maganin ta? Dan Allah ki manta da komai ki yi facing rayuwar ki ta gaba'
Ina gama wannan tunanin na sanya waya na kira Ameenah na ce yaushe za ta zo? Sanar da ni ta yi ko yaushe nake son ganin ta zata zo, nan take na ce dan Allah ta zo ko gobe ko jibi, alqawarin zuwa gobe ta min, aiko na ji dad'i sosai, domin ta jima ta na min alqawarin duk sanda za ta zo zata zo da garin dankwake mu yi danwake, dama na kwana biyu ban yi wa Yah Maheer favorite food ɗin shi ba wato dankwaken saboda ba flour,this is my chance da zan masa danwaken in ta kawo garin.
Washegari kuwa muka tashi da murnar Ameenah za ta zo, dan kuwa weekend ne Suwaidatu na gida, Yah Maheer na da lecture safe da yamma, ya kuma tafi tun takwas saura dan shi mutum ne da baya so ace wai sai ɗalibai sun jira shi, ya na iya zuwa ya zauna na minti talatin ya na jiran daliban shi ba tare da ya damu ba, fashi kuwa ba halin shi bane se in ya zama dole.
Mu na nan zaune ina ta zuba ido in ga ta ina Ameenah za ta fito ne shirun ya yi yawa, ga yunwa muna ji, bana so na dafa abinci ta zo a sake yin danwake a matsayin mu na waɗanda ke lallaba rayuwa zai zama an yi barna.
Da misalin sha biyu na rana Ameenah ta zo bana mantawa, sai ga ta da garin danwake irin haɗin gidan nan me kyau da dad'i da kan ta ta haɗa ta tankad'e, ko da ta zo sai ta ce za ta yi mana da kan ta, ruwa na je zan d'ora ta ce kar na damu za ta yi komai da kan ta, miya ta ɗora mana miyar gyad'a domin da shi ta ce za a yi, duk ta zo da komai, ta na girki ta na karatun Hausa novel.
Ameenah ba irin girkin mu na 'yan zamani take yi ba, duk da cewa na girme ta a shekaru amma zama da Mama ya sa ta iya girki irin na gargajiya,ko tuwo ta yi maka sai ka san ka ci tuwon da ya dahu da kyau ba irin tuwon mutanen mu na yanzu ba tafashi tuqa, tun ina jin yunwa har yunwar ta tafi ba a gama ba, kukan shagwab'a na fara yi wa Ameenah ina buga qafa daga inda nake a zaune ina faɗin,
"Ni yunwa nake jiiii Ameenah, yunwaaaaa, Allah zan faɗa wa Yah Maheer in ce qanwar shi ta bar ni da yunwa,"
"Ke dai qara hankuri gama wa akai yanzun ga,"
Waya ta na zaro Yah Maheer na ɗauka na sanya masa kukan shagwaba na fara kai masa qarar Ameenah, murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce,
"Rabu da Ameenah Zan hukunta ta da kai na, ki ce ta yi sauri ta gama ta baki abinci ki ci, ki qara hakuri kin ji banda rikici"
D'aga masa kai na yi kamar ya na gani na, Ameenah kuwa ta na kitchen ta na min dariya, shi kan shi dariyar ya yi kafin ya kashe wayar, kuma da alama ya na cikin ɗaliban shi na yi masa wannan kiran, gashi a lokacin ya na amfani da wata Nokia ne in kana magana da wani ana jiyo maganar mutum kamar an bude speaker.
Mu na nan zaune d'an wake ya kammala amma Miya bata yi ba saboda ta na so ta yi dad'i sosai, danwake Ni be dame ni ba hasali ma da in na ci amai nake, zama da Yah Maheer ne ya sa ni fara cin d'anwake, dan haka ina zaune ina jira se na ga why not Na je na yi wanka na shirya kafin Yah Maheer ya dawo, dan kuwa a lokacin nan Ni ko turare bani da shi, to ana ta ciki wa yake ta turare? Alimun da lemon tsami Na duk sun qare shi yasa a rana se na yi wanka sama da uku, da na ji hammata ta ta sauya zan shiga wanka in kuwa ba a kawo ruwa ba zan diba a buta na shiga bayi na wanke hammata ta da ruwa na yi tsarki sosai gaba da baya bana so a ji wari a jiki na ko kaɗan, ina da tsananin kula saboda kar na zauna a ji wari a jiki na,dan haka wanka na tafi na bar Ameenah da girki a kitchen.
Ko da na fito na shirya cikin wasu riga da wando masu kyau wanda na siya a gwanjo dan mu ɗan qara kayan zaman gida, zama mu ka yi mu ka ci namu ina ta santi sosai.
Yah Maheer be dawo ba sai yamma, Ni kuma na hana Ameenah tafiya saboda bani da kuɗin da zan bata ta yi na machine, a tunani na in ya dawo ko bai da kuɗi shima sai ya kai ta a machine, ai kuwa haka akai, da ya dawo na masa magana akan ya bata na machine se ya ce ba kuɗi, nan take kuwa na ce,
"To Aunty Ameenah se ki shirya Yayan ki ya maida ki gida saboda magariba tayi ba kin tafi ke daya ba"
Ai kuwa ba musu mu ka yi sallama suka fita mu ka koma ciki Ni da Suwaidatu.
Kwana biyu da zuwan Ameenah qawata da mu ka yi BICE tare ta min waya ta na sanar da ni za su kawo min ziyara ita da qawayen ta, za su zo daga makarantar poly inda Yah Maheer ke koyarwa, ciki ashe har da ɗaliban shi, ban sani ba, bayan mun gama gyara gidan na dafa taliya da manja da yaji, sannan na sanya shadda ta wadda Baban Ameenah ya bani, Yakubu ya zuba basirar shi wajen yi min fitted gown da shaddar ba a yi aiki ba sai aka saka mata wani yadi silver colour a qugun ta da hannayen ta,sai riga ta fito ta yi kyau, Masha Allah hips dina sun cika da qirji na dam a cikin ta, ga dankwalin kayan babba ina son na ga dankwali babba nan da nan na gyara jiki na na kafa daurin ture ka ga tsiya, daurin da na fi yi kenan ni dama.
Ina nan zaune har a azahar kamar ba za su zo ba sai ga su sun zo, fita na yi na buɗe musu gate, wata Ummee a cikin su na faɗin,
"Da kun ce min gidan Yah Bashar za a je wa zai wahala haka? Nan hwa gidan Yaya ta ne Rasheedah"
Cikin gidan muka shiga abun ka da yan makaranta na zubo abinci aka zauna aka ci har da ni aka sha hira anan ne nake basu labarin wata Fateema dalibar Yah Maheer ce da muka rubuta NABTEB da ita ta na ta yabon Yah Maheer ba tare da ta san ni matar shi bace har ta na faɗin wallahi matar shi ta yi dacen miji ba ruwan shi da kallon Mata ko son mata, ko lecture ya gama da ya zauna cikin mutane ya gwammaci ya je masallaci ko qasan bishiya na masallacin ya yi zaman shi, watarana in suka je wucewa da qawayen ta da ke son shi sai su ce,
'Baba ina wuni' (Yaran Kebbi na da qoqarin kiran wanda suka girme su da Mama ko Baba, Kuma akwai su da gaisuwa qalilan ne za ka hadu da su ba su gaishe ka ba) shi kuma sai ya ce masu
'Lahiya lau ya karatu? A dage a yi karatu fa,'
A wannan lokacin Hafsat ke sanar da ita ni ce matar shi fa, Fateema ta rud'e, Ni kuma na ce anyaaa ba kawai faɗa take ba ko shi ma ya na da budurwa?
'Haram..wallahi Aunty ba ruwa nai shi da ko kallon mutane ba ba ya yi?'
Cikin rai na wani irin dad'i ya mamaye Ni, dan haka yau ma da ana hira su na yabon shi sai na ji girman shi da qimar shi ta qaru sosai a ido na kuma na ji na qara son shi a rai na,
se wajen la'asar sannan suka min sallama suka tafi.
Bayan sun tafi nake sanar da shi wadanda suka zo wajena ranar ya jinjina kai kawai ba tare da ya bani amsa ba, shiru na yi ina mamakin rashin bani amsar da be yi ba, daga baya na kad'a kafad'a ta na yi parlour na bar shi a d'akin.
********************************
Ba tare da na sani ba Yah Maheer ashe ya na nan ya na ta nema mana gida domin mu tashi, saboda zuwan su Rasheedah daga Abuja wajen biyu kenan ban sani ba sai dai su sauka gidan iyayen su,shi kuma baya jin daɗin hakan se ya ke ganin mun takura su matuqa tunda mutum ya na da gidan shi da zai sauka kuma a ce ya koma gidan iyayen shi ai abun be yi ba.
Watarana bayan ya tafi makaranta ina zaune a gida se na ji kewar shi ta kama ni, na ce bari na kira mu gaisa, ai kuwa ba bata lokaci na sa waya na kira shi, ya na can ya fito daga lecture ana ta hira a ofishin su, ya na ganin kira na ya miqe ya bar wajen, nan da nan kuwa su ka hau yi masa tsiya, su na faɗin,
'Gaskiya Malam Maheer ka riga ka auru, matar ka ta gama aure ka, ji yanda ka ke rawar jiki dan ta kira ka, gaskiya za mu so mu ga wannan lucky woman ɗin da ta yi sa'ar miji kamar ka,'
Budar bakin shi se cewa ya yi,
'Ni Maheer ni ne na yi sa'ar matar aure alhamdulillahi '
Ihu suka sanya kamar wasu qananan yara,shi kuma ya na gama faɗan haka ya fito waje muka hau gaisawa, cikin jin dad'i na ke tambayar shi me ke faruwa ne, se yake sanar da ni cewar,
"Ai gaba ɗaya gani suke ni mijin tace ne se abinda ki ka ce, kin san wai cewa suke tsoron ki nake ji shi yasa in ana hirar mata bana maganar ki ina ganin kamar za ki san na yi maganar ki ki hana ni abinci,"
Dariya sosai na dinga yi, daga baya na ce masa,
"To da mijin meye in ba mijin ta ce ɗin ba?"
"Ah ah ni mijin kan ta ce ne ai kar ki manta kafin ki ce ki na son abu in Ina da hali na aikata"
Shiru na yi ina jin daɗin hirar tamu, a hankali na ce,
"Tabbas ni shaida ce,Allah ya maka albarka Yayana miji na"
"Ameen mata ta qanwa ta"
Daga haka muka yi sallama ya koma office, nan fa suka sanya shi a gaba da tsokana sannan wani abokin shi ya nace ya ce wallahi sai ya kai shi gidan shi ya ganni, Yah Maheer ya sanar da shi cewa yanzu ma su shirya su tafi, ba sai gobe ba,ga wayar shi nan a aljihun shi ya gani ba zai sanar da ni za su je ba, in suka je zai ga abinda ya sa na zama daban a cikin mata.
Ihu suka sake sanya wa, abokin nashi kuwa ba kunya ya sa shi a gaba suka taho su uku a motar abokin.
Ina nan na gyara gidan na dafa wake da shinkafa as usual tinda shi kadai gare mu, kuma muna son shi sosai ba kadan ba ma kuwa, dan ni zan iya jera kwanaki ina ci be ginshen ba.
Na jera komai a parlour inda muke cin abinci ina jiran dawowar Yah Maheer sannan mu haɗu mu ci, ranar har da arziqin sanya lettuce aka samu ga yajin ya sha maggi da garlic se man gyada da na soya da garlic din saboda banda albasa, qamshin se ya yi dad'i sosai ya cika gidan kamar na dafa wani gagarumin abinci me shegen dad'i na yan gayu.
Wanka na shiga na kira Suwaidatu ta debi ruwa a jug da cups ta kai parlour ni kuma ina fitowa na sanya wando na dan qarami da yar qaramar rigar da ko cibiya ta bata gama rufewa ba, na yi parking gashi na, ba turare ba hoda balle kwalli amma alhamdulillah ba wanda zai kalle ni ya kushe dan kuwa na san yanda zan kula da kai na ko bani da komai na gyara.
Allah ya sa Yah Maheer ne a gaba, abokan shi na baya, domin kuwa na miqe zan shiga cikin gida har na kai bakin qofar shiga cikin gidan ya buɗe parlour ya shigo, ya na ganin kayan da ke ji na ya ga na juya zan je gare shi da gudu na, cikin sauri ya ce,
"Malam ku shigo Bismillah"
Da sauri na juya na afka cikin gida na rufe qofar ina maida numfashi,can kuma dariya ta kwace min,tunawa da yanda hankalin Yah Maheer ya tashi dan ganin za a gane masa babyn shi ba wadatattun kaya.
Hijabi na na dakko har qasa tun ina Bauchi ya dinka min su guda huɗu manya, shi kaɗai ne gobara bata ci ba a sauran hijaban, shi din ma se da ta huda shi kadan amma.
Sallama ya yi, sannan ya buɗe qofar ya leqa kan shi ya sake yin sallama ya sanar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 30