sa?'
Zama ya yi a kujera ya na b'ata rai, na kalle shi ban ce komai ba na zubo masa abinci, dauka ya yi ya fara ci, sai ya ji waken be dahu ba sosai, se ya ajiye ya hau bani labari,
"Wannan abincin anya zai shiga kuwa? Ciki na ba wuya ya lalace dan matar kawu na ma rannan da ciki na ya lalace bayan na ci abincin ta sai da na sha kanwa, shine na dinga wato ainihin haka na dinga tusa da muguwar gyatsa sannan na ji sauqi, kwata kwata haka suke abinci ba tsari"
'Ohhh a fakaice dai ana sanar dani bata iya abinci ba, amma ai a qalla ta temake ka da kanwa ya ustaz kuma an yi tusoshi da gyatsa an sace ciki,kuma da ai shekara da shekaru wajen ta dai ka ke anan ka ke cin abincin me yasa yanzu ka ke aibata ta?'
Bayan na gama ayyana haka a raina a zahiri sai na ce,
"Nima abinda ya sa waken be dahu ba kananzir ne ya qare kuma dare ya yi ka ga har yanzu be dawo ba ba me siyo min kawai se na zuba shinkafa haka suka dahu tare"
"Allah sarki bari na tsince waken na bar maki abun ki"
Har cikin raina a wannan lokacin ban ji komai ba, hasali ma sauraren shi na dinga yi ina jin yanda yake ta maganar matar kawun shi ni kuma ina hasaso me yake nufi da qoqarin yin fad'a da su.
Ina nan zaune Yah Maheer be dawo ba saboda aiki da yake yi a wannan lokacin da wani shahararren kamfanin gidan bread da ke garin, kowa ya san bread din a wannan gari saboda yanda ya shahara, gaskiya da amanar Yah Maheer ne ya sa mamallakin gidan bread din ya dauke shi aiki a matsayin me kula da kudin shi a wannan kamfani, ta yanda baya tashi dawowa gida har sai dika branches d'in gidan bredin sun kai masa kud'ad'e ya qididdige su yanda ya kamata.
Watarana ma mai gidan bread d'in da kan shi yake dawo da Yah Maheer har gida ya ce a bani hakuri,watarana ya sa a yi baking min bread kamar cake a kawo min, Yah Maheer na jin dad'in aiki da bawan Allahn nan, haka shima bawan Allahn na jin dad'in aiki da Ya Maheer.
Ina nan zaune ina jin saukar munsharin Isma'il da ya gaji da bani labarin gidan kawun shi bacci ya dauke shi na ji tsayuwar machine, alamu ne na yau Yah Maheer da kan shi ya dawo ba kawo shi suka yi ba, tashi na yi na bud'e masa qofar parlour ya shiga na karb'i ledar hannun shi da ya shiga da ita, na ajiye sannan ya kalli inda Isma'il yake kwance ya ce,
"Ya Ustaz ana shan bacci ne haka"
Farka wa ya yi suka gaisa da yayan nashi sannan Yah Maheer ya wuce d'aki.
Dariya na yi nima na wuce na kai masa ruwan wanka, kafin in dawo ya yi shirin yin wankan, na fito daga band'aki kenan muka ci karo da Yah Maheer a hanya, riqe hannu na ya yi ya ce in zo in taya shi, cikin zaro ido da toshe baki na kalle shi na ce,
"Ka na ganin gidan ya qara yawa, sannan gamu kusa da d'akin Maimunah, kawai ka je ka yi"
"Gashi nan na rufe qofar ba wanda zai gani please"
Kafin in gama tunanin shin in yarda ne ko in qi amincewa ne kawai ya ja hannu na mun shige bandakin tare, bamu jima da fara wanka ba muka jiyo ana bud'e qofar da zata sada mutum da tsakar gidan, qamewa na yi kamar wadda ke tsoron za a kama ta tana aikata ba daidai ba, Yah Maheer kuwa ci gaba ya yi da abinda yake yi ko a jikin shi.
Ji muka yi ana motsi alamun akwai me son shiga bandakin, duk da ya ji cewa akwai motsi a band'akin be sa ya bar wajen ba, d'an qaramin dutsen da ke wajen ya samu ya zauna ya na jirammu, bayan mun gama ne na dinga zumbura baki, ina ayyana cewa Yah Maheer ne ya ja min jin kunyar koma waye a tsakar gidan yake jirammu, da be dage se na shiga ba da ba a ganni zan fito daga bandakin tare da shi ba, a dole dole na bi Yah Maheer da ke min dariya muka fito, da ido Isma'il ya bi mu, sannan ya shige bandakin, ji na yi kamar qasa ta bud'e na shige dan kunya, parlour na je na kai masa abincin shi muna shiga, na gyara wa Suwaidatu shimfid'ar ta sannan na yi sauri na fito dan na koma d'aki bana so mu had'u da Isma'il kunyar shi nake ji sosai,ina fitowa ya na ajiye buta wuff na yi na afka d'aki na, inda na tadda Yah Maheer na sanya kayan shi, haushi duk ya ishe ni, se zumbura baki nake, na kalle shi zan yi qorafi ya yi murmushi ya fita ya barni tsaye.
Se da ya gama cin abincin shi suka tab'a hira da Isma'il sannan ya dawo, anan ya ke jin wai yayi fad'a ne da gidan kawun shi yana so ya dawo nan da zama, na so in ce ya daidaita su mana ai be kamata daga yin fad'a su rabu ba,sai na dai yi shiru saboda bana so Yah Maheer ya ga kamar bana son qannen shi su zauna a gidan, ta wani b'angaren kuma ina hasaso yanda zamana da wad'anda suka girme ni zai kasance, domin kuwa daga Abubakar har Isma'il sun girme ni i was only 16-17 dan se December zan cika 17 din ma, saura wata biyu kenan na cika 17 a wannan lokacin, ga Suwaidatu.
Shirun da na yi sai ya sa Yah Maheer shiga damuwa, hakuri ya bani tare da nuna min mahimmancin zumunci da kuma cewar shi ba zai iya cewa kar su zauna ba, hasali ma dole na fahimci cewar 'yan uwan shi a ko ina yake kuma a kowanne hali yake in suka buqaci zama da shi ko suka buqace shi zai tsaya masu, wannan mahimmancin da ya basu sai ya sa min nima qaunar su a raina na ji cewar zan iya zama da su ai dama nima gidammu gidan jama'a ne.
A cikin sati biyu Isma'il ya zama d'an gida har ya na so ya fi Abubakar sakewa da gidan, tinda shi Abubakar dama kowa ya san baya magana sosai, dan akwai lokutan da in ina hira da baqi da su ka zo daga liman katagum na ce Abubakar ya ce kaza sai dai a barni in ta dariya ta ni kad'ai dan kuwa kallon maqaryaciya ake min sun san baya magana.
Suwaidatu kuwa makaranta Yah Maheer ya saka ta mai suna Zaid Bn Thabit da yamma kuma in an taso ta je islamiyyar da ke unguwar tamu ta wayar makafi.
Kullum da safe Yah Maheer ne ke kai ta ya dawo da ita in lokacin tashi ya yi a haka har ya samu aiki a Polytechnic da ke garin bauchi,dik da cewar ba an dauke shi bane gaba d'aya amma ya fi babu, ba jimawa Yah Maheer ya bud'e wa Abubakar shago, sai aka raba gareji gida biyu, ya zamana rabi d'akin Abubakar da Isma'il rabi kuma shago,sai ya zamanto d'an matsin rayuwar da muka shiga sakamakon zuwan su baki d'aya cikin lokacin da bamu zata ba kuma bamu tsara ba se ya warware, a qalla ko ba komai muna samu mu ci mu sha cikin rashin takura.
A hankali na fara ganin sauye sauyen halayya daga wajen Isma'il wadda ni ban ji ba kuma banga zan iya dauka ba..........
Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 13:
Garin Bauchi shine tushen Baba zama ya kawo Kakammu garin kano har aka haifi su Baban, shima da ya tashi sai ya yi aure anan garin kanon, a hankali sai ga wata kwarya-kwaryar zuri'a ta tashi.
Sai ya kasance mu dake tasowa ba musan komai na al'adun mutanen Bauchi ba,mun san dai Bauchi garin masa ne,se dai tinda iyayen namu suka tabbatar da za su aurar da yaran su a can sai aka fara sanar da mu dikkan wasu abubuwan masu mahimmanci da ya kamata mu sani.
Na farko an nuna mana kar mu na gaishe da mutane a tsaye, domin mutanen bauchi na so a girmama su sosai, na daga cikin girmamawar in zaka gaida babba sai ka durqusa har can qasa, ba a son mata su na yawan saka kaya wanda zai bayyana tsiraicin su, wannan dalilin ne ya sa mutanen bauchi har yanzu suka riqe d'abi'ar d'aura zani da sa babban hijabi, bana mantawa da girma na an kusan aure na sai da Mama ta dinga koya min yanda zan d'aura zani, da ta ga har a wannan lokacin na kasa se aka d'inka min dogayen riguna da zani 3pieces.
An koya mana kwanon miji daban yake dole a killace shi a tsaftace shi na musamman, cokalin miji daban, takalmin miji da butar miji daban, wajen zaman miji ana gyarawa a tsaftace a sa turare, ballantana uwa uba d'akin da miji zai kwanta, an koya mana abubuwa da dama saboda kar mu shiga dangi mu zama daban.
Isma'il ya fara da tab'a duk wani abu da na killace na ce wannan na miji na ne, to inshaa Allahu shi kuma wannan abun shi zai zama abun tab'awar shi, da fari in ya d'auki abu sai dai in yi murmushi in kyale shi a zato na bai gama gane abubuwan da na ware ba, hakan da nake yi sai ya bashi damar yin abinda ya ga dama, har ta kai ya kai ni maqura na kasa jurewa sai da na tanka.
Wataranar juma'a ina kitchen na gama abinci na raba Suwaidatu ta kai wa Isma'il da Abubakar nasu,mu kuma muna zaune a kitchen d'in ni da Suwaidatu da Hauwa'u 'yar gidan qanwar Yah Maheer da ta dawo gidan da zama saboda ya fi kusa da makarantar da take zuwa, mun saka tabarma saboda girman kitchen d'in ya sa mu na iya zama a ciki mu ci abinci, sai ga Isma'il nan ya shigo.
"Ahhh abinci ake ci,"
"Eh, an kai muku naku ko?"
"Eh an kai amarya uwar gida daga kan ki wallahi an rufe qofa, cokali na zo na dauka wannan ai ba inda zai kai mutum, tinda na saba da manyan nan yanzu bana son amfani da wannan"
Waje yaran suka fita dan wanke hannu, kafin ya kai hannun shi zai d'auki cokalin da nake wa Yah Maheer amfani da shi na dakatar da shi,
"Dakata Isma'il,kar fa ka ga ina shiru ka dinga min abinda ka ga dama, wannan cokalin ka sani sarai na Yayan ku ne, amma saboda dai dole sai na yi magana an ga laifi na shine ka ke d'auka, to gaskiya daga yau kar ka sake d'aukan kayan miji na, tinda akwai wasu se ka d'auka ka yi amfani da shi da can ba da irin wannan d'in ka saba cin abincin ba"
Baki ya saki ya na kallo na, daga baya ya yi kamar be ji me na sanar da shi ba, ya ajiye cokalin hannun sa ya d'auki wanda nake wa Yah Maheer amfani da shi,ba tare da na b'ata lokaci ba kuwa na fizge na mayar na kalle shi ido cikin ido na ce,
"Da za a kawo ni ban san zan zauna da kai ba, dan haka kayan miji na kayan shi ne kar ka sake tabawa, plates d'in shi cokalin shi ba abun amfanin ka bane, ko ku a gida kuna amfani da kayan Baban ku ne?"
Fad'in haka da na yi sai ya yi mugun bashi mamaki, abun har ya kai haka? Har zan iya fad'a masa haka? Ya na gani na yarinya, gani da yawan fara'a ashe na iya fad'a? Ko d'aya cokalin be d'auka ba ya kama hanyar waje inda su Hauwa'u suka tafi wanke hannu, ya wanke hannun shi ya zo ze wuce, mu kuwa har mun fara cin abincin mu, se muryar shi na jiyo ya na fad'in.
"Allah ya bamu yatsu biyar mu sa mu tsaida sunnah" ni kuwa na d'aga murya yanda zai ji ni na ce,
"Ai ya kamata a fara tsaida ita sunnar ne tin fari ba sai an nemi magana ba wajen aikata bidi'a"
Mamaki na ya qara kama shi, kawai sai ya kad'a kai ya shige parlour, ina jiyo shi yana hira da Abubakar, ban san dai akan me suke magana ba, mu kuwa muka ci abincin mu muka tashi.
Isma'il be daddara ba ya fito zai maida plate kitchen tsabar neman magana, ga takalmin shi nan amma se ya jawo na Yah Maheer da nake kaiwa gefe na ajiye in ya fita, ya tura qatuwar qafar shi zai saka, cikin sauri na isa gaban shi na janye takalman na ce,
"Wai kai me ke damun ka ne? Ko rashin kunyar taka ta kai ka dinga ganin kan ku d'aya da miji na ne? Kar ka qara tab'a kayan shi na fada maka, ba tarbiyyar da aka mana ba kenan a gida yaro ya na saka kayan manya"
"Ni kenan bani da tarbiyya ba a min tarbiyya ba a gida?"
"Wannan kuma kai ka fad'a, amma kar a qara saka takalmin miji na"
"Sannu me miji, muma dai Allah ya aurar da mu"
"Ameeen ya Allah"
Sai ya maida abinda ya faru wasa, ya ajiye plate ya koma d'aki.
Bayan kwana biyu muna zaune da Maimunah a tsakar gida kowa na aikin da yake gaban shi yara na makaranta, se ga Ismail ya dawo daga wajen aiki, bayan ya mana sallama se ya shige ciki,mu ka ci gaba da aikin mu da hirar mu,se ga Isma'il da butar da Yah Maheer ke amfani da ita zai wuce mu ya shiga bayan gida, ban bata lokaci ba wajen amshe butar na ajiye gefe na ba tare da na ce masa komai ba,kallo na ya yi cikin jin haushi dan da alama a matse yake da koma menene ya koro shi gida, ni kuma na ci gaba da aiki na ban kula shi ba, k'wafa ya yi ya koma ya dakko butar su ya shige band'aki, muna zaune sai tusoshi muka ji suna fita da qarfin tsiya, nan fa muka dinga kokawar rugawa cikin d'akunan mu saboda kar ya ji dariyar mu, a guje na shiga parlour na na dinga zuba dariya, har da hawaye, se dariya zata tsaya se qarar tusa ta qara karad'e gidan, ina zaune a haka na jiyo motsin shi zai shigo parlourn kifa kaina na yi a hannun kujera ina kallon waje ta window fuskata ta yi jawur saboda dariyar da na sha ga kuma wata na neman kwace min, kallo na ya yi ya kad'a kai ya shige d'akin su ya rufe qofar da qarfi, wata mahaukaciyar dariya ce ta kwace min na kuwa bud'e murya na dinga dariya kamar zan yi yaya, bud'e qofar ya yi ya kalle ni kamar ze yi magana se kuma ya fasa, ya dau takalmin shi ya bar gidan, ni da Maimunah me za mu yi banda dariya, ranar haka muka wuni da mun tuna sai mun yi dariya.
A kwana a tashi sai ya fito da d'abi'ar kwashe min ruwa a drum, ba ya tashi wanka har sai an d'auke ruwan pampo, se idan ni ko yaran mun tara ruwa daga pampo sannan zai zo ya kwashe wanda aka tara ya ce zai wanka, ni kuma haka ne ba zan lamunta ba, duk randa ya bari aka d'auke ruwa be d'iba ba to fa ba zan bari ya kwashe wanda aka tara ba, domin kuwa idan ya kwashe zuwa yamma muka zo amfani da shi se fa yaran sun fita rijiya a waje sun samo ruwa, hakan da nake yi na rashin bari a taka ni se ya jawo min tsana wajen Isma'il.
Watarana mun gama tara ruwa ya na d'aki be fito ba har aka d'auke na pampo, na kuwa ce ba zai d'iba a drum ba, dan ko mu bamu gama d'iba ba aka d'auke ruwan, nan da nan ran shi ya b'aci ya hau bambamin masifa, na masa banza na ce ba dai zai d'iba ba, maimunah ce ta fito ta ce,
"Isma'il ka deb'i ruwan drum d'ina dama muna so mu kwashe a zuba wani"
Nan fa ya d'auki bokiti ya hau kwasan ruwan drum d'in Maimuna,tare da fad'in,
"Ke dai Allah ya tsunduma ki a aljannah ya sa oga ba zai maki kishiya ba, Allah ya maki albarka"
Ni kuma na ce,
"Ameeen in da gaske ka ke, in ma ka fad'a ne dan na ji haushi to ban ji ba, domin kuwa kullum ta Allah se miji na ya samin albarka ya min addu'a,kuma na ga aljannar nan dai ba kai za ka kira ni ka ce zo ki shiga ba balle ka hana ni, dan haka ka gama dad'in bakin ka kai ka sani"
Dariya ya yi ya d'auki bokitin shi ya wuce.
Haka rayuwa ta ci gaba da shurawa abubuwa da yawa na ta faruwa ciki har da sake ziyarar liman katagum da muka yi,da samun aikin Yah Maheer a wata sakandire da ke wani qauye mai suna Bura, bai fara zuwa ba a wannan lokacin saboda wasu abubuwa da yake so ya kammala kafin ya tafi d'in.
*****************************
Watarana ina zaune ina wanke wanke, gefe kuma na d'ora girki, gida kuwa na share shi qal ga qamshin turaren wuta ya na ta tashi, sanye nake da qananan kaya kamar kullum, sai na saka wani hijabi na kalar coffee me yadin roba, na shagala wajen wanke wanke na ji ana kwankwasa gida, sai na tashi na leqa ta 'yar bulin da ke jikin qofar shiga gidan, wani matashi na gani wanda na tabbatar da na tab'a ganin shi amma na manta a ina na tab'a ganin shi, bud'e qofar na yi na amsa sallamar shi,
"Barka da rana Aunty, Yayah ya na gida kuwa?"
Daga jin haka sai na fad'ad'a fara'a ta, nan take na tuna inda na tab'a ganin shi, qani ne ga Yah Maheer, d'an gidan qanin Baban Yah Maheer ne, hanya na bashi ya shiga ciki, na masa jagora har parlour sannan na shiga d'aki na d'aura zani saman dogon wandon da na saka.
Bayan na fito na shiga kitchen na duba abincin da na d'ora se na ga ya dahu, dafadukan shinkafa da waken da ya ji alayyahu da kifi na yi a ranar,ban koma wajen Safiyanu ba sai da na had'a masa abinci da abun sha sannan na kai masa, ina zaune mu na ta hira, na sake da shi kamar dama can na san shi dan kawai kar su ga banda sakin fuska,(tinda sun tab'a cewa fuska ta kamar ta shanu take da ina amarya se daga baya suka gane ashe ina da fara'a) maimunah ta ji ni shiru ban koma na ci gaba da wanke wanke ba ga rana ta kwalle, se ta doka sallama na amsa na fita,kallo na ta yi sannan ta yi qasa da murya ta ce,
"Ke Mahreen ki je ki qarasa wanke wanken ki mana, ga rana ta kwalle, ba fa haka ake yi ba, tinda kin kai masa abinci da ruwa sai ki je ki d'an qarasa aikin ki kafin nan ya gama cin abincin sai ki koma"
Dariya na yi sannan na shagwab'e fuska na ce,
"Yaayah Maimunah ranaaahh ni gaskiya bana so na shiga rana yanzu"
Qasan raina ina ganin rashin dacewar na tafi na bar baqo shi kad'ai, sannan na san a yanda Maimuna ke ji da ni zata taya ni wanke wanken, aikuwa kyale ni ta yi ta fice tsakar gida, ina ganin haka na sa dariya har da toshe baki, na tabbata wanke wanken zata qarasa min.
Ina komawa parlour kuwa na jiyo ta fara wanke wanken, murmushi na yi ina jin son matar har cikin raina.
Hira muka ci gaba da yi da Safiyanu ya na bani labarin mutanen Liman katagum,ina bashi labarin kanawa,a haka muka gama hirar mu ya tafi ba tare da ya had'u da kowa ba.
Bahaushe ya ce wai rashin sani ya fi dare duhu, a iya tunani na na qure gudu wajen kyautatawa Safiyanu, dan haka banga abinda na aikata masa ba na yi min sharri,ba tare da na sani ba Safiyanu ya tafi Liman Katagum a ranar, be tashi qulla min munafurci ba sai da yamma, manyan iyaye mata na gidan sun had'u ana cin abinci a bangaren su Yah Maheer ciki har da Maman suwaidatu da Isma'il da kuma Kakar Hauwa'u da nake riqo sai mahaifiyar shi.
Gefen su ya samu ya ja qaramin turmi ya zauna akai ya rafka uban tagumi tare da sauke ajiyar zuciya a jejjere,Maman su Suwaidatu ce ta kalle shi tace,
"Baffa Safiyanu lafiya ka zo ka sa mu a gaba ka zabga tagumi kamar raqumin ka ya b'ace a sahara?"
"Hummm ai Mama abinda na gani gwanda b'acewar raqumi a sahara da shi,"
Nan take kowa ta bashi hankalin ta, shi kuwa ya ci gaba da magana,
"Daga Bauchi nake wajen neman aikin polio d'innan da na ce maku ina nema, se na biya na je gidan Yah Maheer, wallahi su Suwaidatu da Hauwa'u su na shan wahala, kun ga a inda suke kwana kuwa? A dandaryar qasa suke kwana kai abun fa se wanda ya gani"
Allah ya zuba wa Mama son 'ya'ya,duk da halayya ce ta iyaye amma nata ya fita daban, nan take hankalin ta ya tashi ta ce bauchi zata, da kyar aka taushe ta akan ta bari se da safe ta zo.
Haka kuwa aka yi, ba tare da na san me ke faruwa ba, da sassafe na gama yi mana abun karyawa wanda ya kasance fanken da ake sanyawa nama da attaruhu da albasa se maggi da dan sugar kad'an na dafa baqin shayi kowa ya ci ya sha har ya ragu,se na deb'i wake na je tsakar gida dan na gyara da rana ina so na yi mana shinkafa da wake.
Na gama gyara wake na bushe zan shiga cikin gida Suwaidatu da ke tsaye saman d'an dutsen tsakar gidan ta daka tsalle ta d'ale baya na, ga hannu na da plate d'in wake, gashi ta shaqe wuyana da sunan na goya ta, ina tsaka da kokawar kwace kaina a hannun ta na ce,
"Kin san Allah in baki sake ni ba zan zane ki, kin shaqen wuya fa"
Ba zato ba tsammani muka ga an bud'e qofa sai ga Mama ta bayyana bakin ta dauke da sallama fuskar ta ba yabo ba fallasa, da sauri Suwaidatu ta saki wuyana ta ruga da gudu wajen Maman ta, ta na fad'in,
"Maamaaa Oyoyo ! Mama oyoyooo !!"
Da sauri nima na isa wajen ta ina mata sannu da zuwa cike da girmamawa, a haka na raka ta muka shiga cikin gidan har parlour, ban zauna ba sai da na deb'o mata fanken nan da na yi na had'o mata baqin shayi itama, sannan na zauna muka hau gaisawa, kallon mu kawai take da ni da Suwaidatu ta na so ta ga irin wahalar da 'yar ta ke sha, bata gani ba, ga yarinya nan tsaf,gashin ta ya sha kitso, domin hannu na ya karb'e ta nan da nan gashin ta ya cika ya yi tsaho saboda kula da shi da nake akai akai.
Ga ta nan fess dik da a lokacin ma ba mu yi wanka ba dikammu,babu wani alamun damuwa ko wahala a tattare da ita, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce mana,
"Ina Yayan nasu ko ya fita aiki?"( Idan tace Yayan su Isma'il take nufi ba Yab Maheer ba dan shi da sunan shi take kiran shi kai tsaye bayan ya girme wa Isma'il da shekaru masu nisa, sannan dika yaran ta suna cewa Isma'il Yayammu, shi kuma Yah Maheer Yaya Maheer kamar shi ne qasa da Isma'il d'in)
"Ah ah ya na ciki, be d'au murya ba bari ta kirawo shi"
Kiran shi Suwaidatu ta yi bayan ya fito sun gaisa se na tafi d'aki na basu waje.
Isma'il be b'ata lokaci ba wajen qaryara Safiyanu se ya qara da cewar,
"Ni ne ma dai muke d'an takun saqa da ita, amma ba komai komai zai wuce watarana,"
Haka dai suka dinga magana ta a parlour na a cikin gidan aure na,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 30