Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful* 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 20: "Ahh Nafeesah ke ce ki ke tafe? Bismillah shigo ciki" "Wallahi Aunty ni ce ke tafe da yamma, na zo na ɗebe miki kewa dan ke yanzu gwauruwa ce," Dariya muka yi a tare, muka shige parlour muka zauna, ruwa na buɗe fridge na dakko mata na ajiye, sannan muka fara gaisawa tare da taɓa hira. Bamu tashi ba sai da aka kira magariba, muka yi alwala muka yi sallah, sai na duba abincin mu na ga ba zai isa ba mu ci da daren, wake na dafa na qara a shinkafar sannan na zuba wa kowa, mu kuma na haɗa mana baki ɗaya muka zauna muka ci ana ci gaba da hira, da dare ya yi muka sake dunguma daki na muka kwanta,kafin bacci ma hira Nafeesatu tai ta yi min game da auren ta da ya gabato,har daga qarshe ta ce, "Ni fa aunty zuwa na yi ki koya min yanda zan yi girke girke masu dad'i da yanda zan kula da gida na" "Ikon Allah ni ɗin me na iya da zan koyar?" "Ke kuwa ki ka iya Aunty dan Allah ki koya min abubuwa masu amfani,ni fa ko kunna risho da haɗa shi ban iya ba" "Aiki ja kenan, to shi kenan Allah ya kaimu ya bani ikon koya maki abun alkhairi" Haka muka kwana da safe na yi mana wainar flour da na sanya wa kayan haɗi sosai har da lawashin albasa, muka ci muka kora da baqin shayi, bayan mun gama ne muna zaune na dinga koya mata abinci kala kala da yanda zata kula da gidan ta, da sauran duk abinda na sani dai wanda be gagara ba, da rana da za mu yi girki kuwa se na kwance risho gaba daya na nuna mata yanda ake haɗa shi, sannan na sake kwance wa na ce ta haɗa, ta kuwa haɗa shi daidai yanda ya kamata, bata wani jima ba kwanan ta uku ta tafi ta koma LK. Kafin Yah Maheer ya dawo aka yi auren Nafeesah inda aka ajiye ta anan garin Liman Katagum,mijin ta ma ɗan uwa ne dan haka auren dangi suma suka yi. ***************************** Zaɓe ya gabato, rikicin siyasa da na qabilanci na ta wakana a kowacce jaha, a wannan shekarar ta 2011 ne Baba Buhari ya qara fitowa neman takarar shugaban qasar Nigeria inda yawancin mutanen Arewa suka fito qwan su da kwarkwatar su suna so ya zama shugaban qasa tare da wasu qalilan daga kudu,ta wani bangaren kuma sam sam Baba Buharin be yi musu ba ba sa qaunar mulkin shi saboda tarihin shi da suka samu wajen iyayen su, mutanen kudancin Nigeria kuwa wasun su na qin shi ne saboda qabilanci b'angaranci da wariya saboda addini da ba d'aya ba. A wannan lokaci garin Bauchi na ɗaya daga cikin garuruwan da aka dinga samun rikici har ta kai wasu sun rasa gidajen su da 'yan uwan su. Mu kuma da muke gida mu na zaune cikin tashin hankali da taraddadin abubuwan da ke ta faruwa, a lokacin Yaron Maimunah ya fara zama sosai, mazaje na qofar gida ana ta tattauna halin da qasa ke ciki, wata 'yar ajin su Hauwa'u ce ta wuce dauke da qullin kaya akan ta tana kuka, tausayin ta duk ya kama mu Hauwa'u ta je ta same ta ta mata magana tare da jajanta mata abinda ya faru da su gidan su an qona dole su bar wajen. Suwaidatu kuka Hauwa'u Kuka, Hauwa'u fad'i take dan Allah in ara Mata waya ta kira Baban ta ta ji ina yake, fatan ta Allah ya sa baya shago, (Chemist ɗin shi). Ni kuwa da wauta yanayin yanda duk suka rud'e suka rikice sai ya dinga bani dariya na dinga dariya ina tsokanar su, Maimunah kuka take ta na tambayar ko ya 'yan uwan ta suke? In ta kalli d'an ta sai ta ce, "Hummm yaro ka zo duniya a lokacin da ake rikici a cikin ta," Suwaidatu ce ta Kalle ni ta ce, "Aunty ni Kashi nake ji, kamar na gudawa nake ji" "To je ki yi mana, ga Hauwa'u nan ta raka ki," Har sun ɗauki hanyar fita daga parlour na ce, "In fa akai harbi daga nesa se ki ga ya huda gini ya afko wa mutum" Ban gama rufe baki ba yaran nan suka runtumo a guje suka dawo ciki suna iface iface, me zan yi ni kuma banda dariya? Masha Allah Allah ya yi wa Suwaidatu manyan ido, se ga idanun nan sun qara girma ta na ta rarraba su cike da matsanancin tsoro, ni kuma Se ci gaba da sheqa dariya nake kamar na samu comedy me kyau,haka na dinga tintsira dariya ina kumawa, da kyar na lallaba su suka je ta yi kashi, suna dawowa kuwa muka ji qara kamar abu ya fashe, Kamar bomb, sannan muka ji qarar motocin sojoji tinda an saka dokar hana fita amma mazaje ke waje, gudu matasa da magidanta suka saka ji ka Ke rudududu kowa ya kama gidan da ke kusa da shi ko ba naku bane kawai a afka a tsira da rayuwa. Mijin Maimunah mutum ne me qiba sosai, shi kuwa Abubakar siriri ne sosai ga kuma tsaho, ana yo korar nan mijin Maimunah ya shigo rikica rikica ya afka d'akin su, Abubakar kuwa duk tsahon hanyar qofar gidan zuwa parlour na bai gani ba dan be fi taku uku ya yi wa wajen ba ya afka d'akin shi ya danno qofar ya maida wani tsohon turmi da yake sakawa ya rufe qofar,tsabar dariyar da nake ni kuwa a wannan lokacin har kwarewa nake, Maimunah kuka ta saka ta na kiran mun shiga uku yau za ai yaqi kowa ze mutu. Muna tsaka da hayaniya muka ji qarar harbi tauuuu nan fa parlour ya sake rikicewa, cikin dariya na ce, "Ni fa ina gani a American movies da an yi harbi irin haka kwanta wa ake saboda kar ka na tsaye...." Kafin in qarasa magana ta Maimunah da yaran sun baje a tsakiyar parlour, baka ganin komai sai yanda mazaunan ta ke rawa, dariya kamar ba zan sha numfashi ba haka na dinga yin ta, ce wa take, "Miqo min ɗa na, ni gidanmu Zan tafi ba zan zauna anan ba, ko mutuwa zan yi gwara na mutu cikin 'yan uwa na" Cikin dariya na ce, "Ah ah gwanda dai ki mutu a d'akin mijin ki, ni fa na ga Baban Aslam ya shigo d'azu, kuma kamar ba shi kaɗai na ga ya shigo ba," Ta na jin na ce na ga mijin ta ya shigo ta miqe tsaye ta ɗauki yaron ta ta wuce dakin ta, ni kuma da ban da cikakken hankali haka na fita tsakar gida dan jiki na ya bani akwai wanda ya yi gudun ceton rai ya afko gidan, duba banɗaki na yi ban ga kowa ba, na fita na duba tsakar gidan da kyau ba kowa, dabarar in duba kitchen ɗin Maimunah ce ta fadi'o min, da sand'a na isa gaban kitchen ɗin nata me duhu saboda kunna icce ko ina kunkuniya ta fito, ina tura qofar na ga idanu jajawur na kallo na fuskar nan baqa ta saje da kitchen ɗin ai se na yi baya a mugun tsorace na koma parlour ina ihu, fitowar Maimunah da mijin ta ta yi daidai da fitowar Yaya Sani daga kitchen ɗin Maimunahn ,nan fa Mijin Maimunah ya hau dariya Yah Sani ya leqa waje ya ga ba kowa ya runtuma da gudu zuwa gidan su, a sannan na gane wanene kuma me ya faru,madadin tsoron da ya kama ni se na ci gaba da sheqa dariya . Yaya Sani wani mutum ne a unguwar mu dan ba yaro bane kuma ba a ce masa saurayi ba, siririn mutum ne ga shi baqiqqirin sannan in yana magana se mutum ya rantse mace ce ke magana, dama can ya na bani dariya se ga shi a kitchen ya yi tsamo tsamo ya na neman mafaka. Su Hauwa'u tunda suka samu suka gudu d'aki na ba su sake fitowa ba ni kuwa 'yar tafasa bala'i Ina nan jikin window ina ganin yanda matasa da ke riqe da mugayen makamai ke ta wucewa ana iface iface, ba tare da na san cewa Abubakar na ganin yanda na hakimce ina kallon su ba, na ji qarar zare sakatar d'akin shi da janye turmin da ya danne qofar da shi, cikin sanda da magana qasa qasa, ya min nuni da hannu,ya ce, "Rufeee,rufeee labulen nan kar su gano ki su shigo, yanzu nake ji a labarai an rufe ko ina ba shiga ba fita saboda ana ta fad'ace-fad'ace a garuruwa,dan haka ba shiga ba fita yanzu" Habaaa me zan yi banda dariya, gaba ɗaya tsoro ya fita a raina, dariya kawai abubuwan da suke yi yake bani, ban tashi kuka wiwi ba sai da waya ta ta Yi ringing na dakko ina share hawayen dariyar da na yi, se na ga sunan da na sanya wa Yah Maheer ya bayyana a saman waya ta, cikin daidaita nutsuwa ta na dauka na yi sallama, ina so in tambaye shi ya ta wajejen nasu dan na kira shi bata shiga ba se na bari na ce ko matsalar network ne ya sa ta qi shiga, kafin in yi magana na ji Muryar shi cikin hayaniya ya na cewa, "Baby Na muna nan dawowa muna hanya ma yanzu haka, gashi ana ta rikici a garin da muke a sanya mu a addu'a,Allah ya kare mu da dukkan Musulmi, amma inshaa Allahu nan da wasu 'yan awanni za mu iso gida" Ai ina jin haka se na fashe da kuka ina faɗin, "Ka wa Allah husband ku kwana a Kano, ku je gidan mu ku kwana kar ku biyo hanyar nan ana ta fad'ace-fad'ace haka" Be gama jin me nake faɗa ba saboda yanke wa da network Ke yi ya kashe waya, ni kuma wannan lokaci ne fa watan tashin hankali na ya tsaya, na dinga kuka ina addu'a har da d'aura alwala na yi sallah na yi addu'a sannan na zauna karatun Kur'ani,hanci na se majina ya ke fidda wa ido ya min luhu luhu. Nan take na gano wautar da na tafka,nan take na gano kuskuren da na yi a baya, da can ana ta rikicin ban damu da na yi wa 'yan uwa musulmi addu'a ba tinda iyaye na sun tsira 'yan uwa na sun tsira ina tunanin miji na ya tsira se da na ji miji na ya dakko hanyar da ake rikici sannan ne hankali na zai tashi? Istighfari na hau yi ina salatin Annabi, ban tashi ba se da lokacin azahar ya yi, na yi sallar sannan na ci gaba da zama ina addu'a. Ina nan zaune Yah Maheer ya dawo,qarar tsayuwar motar kawai muka ji, sai kwankwaso qofar parlour da aka yi ta baya, ai tinda na leqa na ga shi ne na buɗe na nufe shi a guje na rungume ina murna, "Ya na ga kun dawo da wuri?" "Dama mun kwana a hanya na so na baki surprise ne se dai ki ganni kawai, shine fa wannan rikicin ya barke" "Alhamdulillahi... Alhamdulillahi.... Alhamdulillahi, Allah ya qara tsare wa ya bawa dukkan bayin shi da ke cikin tashin hankali kariya" "Ameeen, na same ku lafiya? Ina yaran suke?" "Su na d'aki na, Abubakar na ciki" Ina cewa Abubakar na ciki na tuna da abinda ya yi nan da nan na ji dariya ta kwace min,ina tsaka da dariya ya sake zare sakatar ya fito, nan fa Yah Maheer ya hau dariya qasa qasa shima,hannu suka miqa wa juna suka yi sallama suka gaisa, Yah Maheer ne ya ce, "Kai ran ka ya dad'e ya akai haka ne?kai da na tafi na bar wa amana shi ne ka gudu d'aki ka buya me ke faruwa ne?" Cikin dariya na ba wa Yah Maheer labarin abubuwan da suka faru,muka yi ta dariya, bayan mun shiga d'aki ne ya Kalle ni ya ce, "To ke Hajiya baki bani labarin me ya sa ki kuka ba?" Na manta shafff ko Mai qanqantar kukan da na yi sai Yah Maheer ya gane, dariya na sake yi sannan na kwanta a jikin shi na ce, "Ba kai ne baaa, kawai ana tsakiyar wannan tashin hankalin ka kama ka wani dawo, da wani abu ya same ka fa?" "To ba gani baaaa na dawo lafiya?" Wasa da dariyar mu muka ci gaba da yi, can ya tuna be yi azahar ba lokacin sallah ya wuce tashi ya yi ya tafi suka yi jam'i da Abubakar a parlour, a sannan na fara tunanin ɗora abincin da za a ci, dan da duk an firgita an manta da wani abinci. Bayan an kammala zabe Goodluck Jonathan ya ci zaben shugaban qasa abubuwa sun lafa muka tattara muka yi wa mutanen Bauchi sallama za mu koma Kebbi da zama, Hauwa'u ta koma gidan su Abubakar ya yi aure anan garin Bauchin, se ya zamana gidan ya dawo se Maimunah ita ɗaya da mijin ta da yaron su da kuma wani cikin da ke jikin ta, mun yi kuka sosai na rabuwa da juna ni da Maimunah, dan irin zaman mutuncin da muka yi da ita, zama ne irin na yaya da qanwar ta, ba zan ce ba a samu sabani ba, amma zaman lafiyar mu ya zarta 80% dan haka zaman lafiya kawai muke tunawa a wannan lokacin, har motar mu ta daga muna kuka, se da muka fita daga cikin gari muka yi nisa sannan na hakura na dena kukan da nake. A Kano muka tsaya muka ci abinci a gidan mu muka yi wanka ni da Suwaidatu Yah maheer ma haka, Mama ta so mu kwana kafin mu ci gaba da tafiyar amma ya ce wucewa za mu yi dan na musamman ya samo driver masanin gari,haka muka ɗauki hanya da azahar mu ka wuce dan zuwa garin Kebbi da zama. Tin ana tafiya ina ganin yanzu ne, ah ah anjima zamu isa, ah ah Mun kusa, inaaa tafiya ta qi qarewa, na yi kuka na gode Allah a hanya, Suwaidatu kuwa ta yi bacci ta farka ya fi sau nawa se ta ga muna nan muna cin kwalta dai ba a isa ba. Hakuri Yah Maheer ya dinga bani ya na nuna min ai an kusa, cikin hawaye na ce masa, "Ni dai na gaji wallahi" "Ki qara hakuri nan da Isha'i za mu isa inshaa Allahu" "Husband Amma dai daga Kebbi nan Nigeria ta qare ko?" Driver ne ya yi 'yar dariya saboda tinda muka fara magana jimmu kawai yake be ce komai ba,Yah Maheer ma murmushin ya yi dan shi kan shi a gajiye yake, babu wanda be gaji ba a tafiyar nan. Kamar yanda ya ce min kuwa haka muka isa bayan Isha'i da kaɗan muka shiga cikin garin, gidan da muke a farkon gari yake dan haka bamu wani wahala ba a gaban gida mai baqin gate motar mu ta tsaya, unguwar shiru ga duhu da alama ba wutar lantarki, Quarters ne unguwar dan haka gidajen da dama iri ɗaya ne, sai dai wasu sun katange kan su sun saka gate wasu kuma su na nan yanda aka gina shi ba su yi katanga ba. Ko da muka shiga sai na ga tsakar gidan wawakeke mai mugun girma daga can ciki gidajen biyu suke a haɗe da juna, wata mata ce wadda ita ce maqociya ta doguwa ta fito daga nata gidan sai qananan yaran ta guda uku, da mijin ta su na yi mana maraba, gaban gidan nasu kuma tabarma ce a shimfide da alama zaune suke a wajen suna shan iska, dan kuwa tunda uwata ta haife ni ban taɓa jin gari mai zafin Kebbi ba. Kayan mu aka shigar nawa bangaren,bayan mun gaisa da matar da ta kira kan ta da Maman Ameerah sai na bi bayan Yah Maheer suwaidatu ma ta biyo baya na muka shiga namu sashen, ko da muka shiga sai na ga wajen an shinfid'a carpet ja gaba ɗaya gidan, ko ina dai ya yi kyau gwanin sha'awa, kitchen na duba na gan shi ɗan ququt ba zai yu yanda nake da qiba ba na shige shi gaba ɗaya na, gyad'a kai na na yi a rai na na ce, 'Tabdijam akwai aiki' Wata iriyar zufa nake yi kamar an watsa min ruwa, nan da nan na shiga na buɗe akwati na na ɗauki towel da kayan wanka, na ɗebi ruwa a drum ɗin da na gani na shiga banɗaki ko da na shiga sai na ga wajen ɗan ququt shima, da kyar na wuce sink na hau toilet na yi fitsari ina gamawa na yi flushing na sakad'a jiki na na bar wajen na shiga wajen wanka, ina wanka ina zufa dan kuwa ruwan ma kan shi zafi ne da shi,amma dai na tabbata in na yi zan rage daud'a. Ina kammala wanka na daura towel ɗina na hau qoqarin buɗe qofar banɗaki qofa tace ba sai ki buɗe na gani ba? Tin ina ganin abun abun wasa ne ba sai gani ina zufa ba kamar na shiga kogi, hawaye na ji sun fara zubo min tsabar tashin hankali, ga Suwaidatu na can waje wajen baiwar Allahn nan maqociyar mu, Yah Maheer na can wajen mai gidan ta da driver su na cin abinci, na jijjiga qofa na kwankwasa na yi kira ba wanda ya ji ni gani jiqe cikin zufa ina neman agajin gaggawa, ji na yi numfashi na na barazanar ɗauke wa tsabar shiga tashin hankali da rashin kwakkwarar iska, damuwa ta haɗu ta min yawa, hasken fitila na hango ta qasan qofar bayin ya na haskoni ya na ɗauke wa, wani irin tsoro ne mai girma ya shige ni, a rai na na ce, 'Na shiga uku an kawo mu gidan mutuwa' Wani marayan kuka na saki a hankali ina kiran sunan Allah a zuciya ta, tare da fatan Allah ya kawo Yah Maheer ya zo ya buɗe min wannan shegiyar qofar da ta qi bud'uwa........... *Mutanen azziqi a kai wa MAHREEN agaji a tolasss* 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 21: Suwaidatu ce ta shigo ina ciki ban san me ya shigo da ita ba, ina jin muryar ta sai na ji wani kwari ya zo min na daga murya na ce ta je ta nemo taimako qofar ta rufe na kasa fitowa, ai kuwa cikin qanqanin lokaci ta fita sai gata da Maman Ameerah sun taho, nan fa suka dinga kiciniyar buɗe qofa, tun ta na yi a hankali har se da ta dakko wuqa, qarshe dai da kyar aka samu qofa ta buɗe, ko da na fito daga banɗakin gaba daya na jiqe jagabbb da gumi kamar ba wanka na yi ba, numfashi na dinga fitar wa a wahale ido na duk ya kakkafe, banda salati ba abinda nake yi a cikin raina, Maman Ameerah ta ce, "Ai na zata malam ya sanar da ku qofar na da matsala se dai ban san abun ya kai haka ba, na yi mamakin irin wannan rufewar da ta yi" Kallon ta na yi a karkace yaushe ma muka zauna da Malam ɗin a daddafe na zagaya na mata godiya da fatan alkhairi na shiga d'aki, kwanta wa na yi a ƙatuwar katifar da ke dakin wanda nan ne Suwaidatu zata dinga kwana, ji na yi ba wata iska da ke shiga ta, kwalin da aka sako tukwane na na yage suka kuwa zubo ta gefen inda na yage din, na hau firfita ba ji ba gani, a hankali hankali na ya fara dawowa jiki na, na ji bacci na mamayata, to amma ban yi sallah ba, dole na miqe na je na yi alwala na yi sallah, ina idarwa na nemi baccin na rasa se kawai na shirya na ɗauki jug ɗin da aka zuba min ruwan sha da ban sha ba lokacin da muka zo sannan na yi hanyar waje, ina fita na isa saman tabarmar da Maman Ameerah ke zaune da yara, na sake gaishe ta sannan na buɗe jug zan sha ruwa, ina kai wa na ji wani tiririn zafi ya daki fuska ta, nan da nan na janye shi na sanya hannu na, mamakin zafin da ruwan ke da shi ne ya kama ni na kalli Maman Ameerah na ce taɓa ki ji,a ɗan tsorace da ni ta Ke Se ta qi sanya hannu, daga baya na kula irin mutanen nan ne marasa saurin yadda da mutane, murmushi na yi na ce, "Kin Ji zafi kuwa ruwan nan kamar an kara a wuta, lallai garin nan da zafi sosai" Sannan ne ta dan yi murmushi ta ce, "Ayiii haka garin yake ai se ma da rana" Nan da nan na ji gaba na ya fad'i cikin sauri nace, "Auuu a hakan da ake gasuwa da rana ya fi?" "Sosai ma" "To Allah ya sauqaqe mana ya sassauta mana zafin nan, wannan ai se kitse na ya d'ige tsaff" Dariya ta yi, sannan ta miqo min abinci, karba na yi na mata godiya sannan na ce suwaidatu ta je ta yi alwala ta yi sallah. Tashi ta yi ta tafi,Nima ina gama cin abincin na yi mata sallama na koma ciki, Yah Maheer na ganin mun shige ciki shima ya biyo bayan mu, ko da muka shiga se yake sanar da ni qofa fa bata da kyau sosai mu yi a hankali,ya manta be faɗa mana ba, cikin jin haushin shi na ce, "Eh ai da na maqale na mace a ciki da ka huta tinda baka faɗa ba tun da wuri se da na shiga na jiyo qamshin lahira sannan za ka faɗa" "Subhanallahi Babyna me ya faru?" Banza na masa na shige dakin mu na karkade gadon sannan na buɗe akwati na zaro zanin gado na saka na haye abuna na hau addu'ar bacci, ina gamawa na fara shafawa na kwanta, Yah Maheer ashe na can Suwaidatu na bashi labarin me ya faru, ina jin sanda ya buɗe qofa ya shiga ya cire kaya ya daura towel din shi da na tarar a dakin tinda shi dama kayan shi na nan ciki. Se da ya je ya yi wanka ya gyara jikin shi sannan ya hawo gadon, ina jin shi amma na yi kamar bacci nake yi, dan ya bani haushi da na mutu a cikin banɗakin fa? Kwanta wa ya yi a jiki na ya na shafa kai na, ya ji shiru ko motsa wa ban ba, hakan se ya bashi tabbacin bacci na yi,dan kuwa baccin gasken ne ya yi gaba da ni, ban sake sanin me ya faru ba sai washegari da asuba. A saman sallaya na tadda shi kamar ko da yaushe, ya na wahala na riga shi tashi, kullum in na tashi zan gan shi ya na ibada,ko na bi bayan shi ko na je na yi uzuri na na kwanta. Sallama na masa kamar yanda muka saba ya amsa ni sannan na wuce na shiga banɗaki na wangale qofar da kyau a raina ina ayyana kowa ya ji a jikin shi tinda abun naka haka ne, ban rufe qofar nan ba se da na yi wanka na gama duk uzuri na sannan na ja daidai yanda ba zata rufe dika ba na fito na tada sallah. Karatun qur'ani muka yi bayan na idar har suwaidatu sannan na miqe na je na dafa mana indomie da kwai da baqin shayi, muka haɗu gaba ɗaya muka ci muka qoshi, bacci na so komawa Yah Maheer ya hau bani hakuri, "Baby na fushin ya isa haka mana,ai ban san zaki shiga ba, na so zuwa na sanar da ku matsalar qofar na manta,a yi hakuri a yi min murmushi in ga hushiryar nan manaaa" Ɗan murmushi na yi amma na qi buɗe hushiryar, already mun yi developing wata dabi'a ni da shi, duk fushin da d'ayan mu yake da mun karanta qur'ani tare kafin mu gama a yi addu'a kowa ya hakura, mun maida karanta qur'ani a tare hanyar warware fushin mu,duk da dai watarana ni nakan ci gaba da fushi na, amma ba koda yaushe bane hakan ke faruwa. Suwaidatu ce ta tashi ta kwashe kwanukan ta kai can baya inda ake wanke wanke,ina hango ta ta fita gaba ɗaya ta na kallon yanayin wajen,Yah Maheer kuwa na ganin ta fita ya ja ni d'aki Wai zai bani hakuri, to ba laifi dan kuwa na hakura ɗin gaba ɗaya an

Chapter 16 of 30