Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tafi ni da Suwaidatu, muna tashi motar bayan mu ma ta kusan cika ashe su Isma'il sun shige ta, dan haka gaba d'ayan mu sai muka isa kusan a tare, Yara kuwa aka hau murna kamar yanda suka saba wannan karon murnar ta zama biyu ga amarya ga Zaituna da tsohon ciki, haka muka tsaya sashen Yayan su Yah Maheer muka gaggaisa a tsaitsaye da su Maman Ummeeta sama sama, sannan muka shige sashen mu, muna shiga gidan Ummah da Mama suka taso su na mana lale maraba, sauran qannen Yah Maheer ma na yi mana maraba lale, gani na yi Ummah ta kama akwatin Habibah suka wuce suka yi d'akin Umman Mama ma ta ja na Zaituna suka yi d'aki Sai gani tsaye a tsakar gida zuruuu ba me Jan nawa akwatin Ina tsaye Ina tunanin shin me ya faru ne haka Sai ga Baba ya fito daga d'akin Shi babu riga saboda zafi da yake Ji, ya kama akwati na zai shigar min da Shi d'akin Ummah da sauri na kama na riqe na ce, "Habaa Baba ka bari Zan Iya ja ba komai, na gode" Suwaidatu na gani ta fito daga d'akin su bayan ta ajiye ta ta jakar, jiki ba kwari na ja akwati na na Kai d'aki a sannan ne Ummah ta hau min sannu da zuwa, na amsa mata Kamar ba abinda ya faru,cikin Ikon Allah kuma Sai na Ji bana jin zafin abinda ta yi d'azun,nan fa aka hau hidima da mu,hirace ta daban ta kuma musamman ke gudana tsakanin ta da Habibah ana jefa wa da ni sama sama, ko kuma in sanya kaina a ciki ko da ba a saka ni ba. A haka muka kwana washegari muka yi wanka muka shirya dan zuwa ziyara, har gidan Addah Ummuna sai da muka je, mun sha yawo sosai na ziyara har sai da qafafun mu suka gaji Libus. Ko da muka dawo gida da yamma lisss mun gaji, na shiga banɗaki na watsa ruwa na yi alwala, a inda na bar su suna hira da Ummah nan na same ta, dan haka se na musu sallama na wuce ciki na shirya sannan na tada sallah, Zaitunah na daki ita da su Suwaidatu suna tasu hirar Mama na kai wa Baba tuwon shi na dare. Kafin na idar Habibah ta je ta yi alwala itama ta zo ta tada sallah,Ummah kuma ta fita tsakar gida dan su ci abinci da Mama se aka bar mu mu biyu a d'aki, hira muke ta zabgawa kamar wasu dad'add'un qawaye, muna tsaka da hira Kabeer ya kira ta, ta kuwa kashe murya ta amsa sallamar shi, yanayin yanda take amsa wayar se ya bani kunya da sauri na kalli hanyar d'akin Baba wanda bamu da nisa da shi, da hannu na yi mata nuni da ta yi a hankali kar ya ji ta, domin shi mutum ne da baya maraba da irin wad'annan abubuwan, na kula yanayin yanda muke jin nauyin juna ni da Yah Maheer a cikin gidan ya na burge Baban, tinda a fili yanayin soyayyar mu, shaquwa, da kulawar mu yake amma bama bayyana wa ta yanda za a ga rashin kunyar mu. Zaqewar da ta yi se ya dinga sa ni jin kunya, amma ita ko a jikin ta dan na kula ta d'au hakan a wayewa, da na dame ta da yi mata nuni da ta yi a hankali se ta fita bayan d'akuna wanda se da na yi danasanin damun ta akan tai a hankali da na yi, domin kuwa kamar a gaban kowa take yin magana, cikin b'acin rai kuwa Baba ya buga tsaki ya yi maganganu wanda ban ji me ya fad'a ba, kunya sai ta baibaye ni na Ji kamar da ni ake, Ko da ta gama ta dawo se ta hau bani labarin wayar tasu, na so na sanar da ita yanda Baba be ji dad'in yanda take waya ba se na kasa na ja baki na na yi shiru. A haka muna hira da Habibahn Yah Maheer ya kira ni,na amsa wayata cikin kulawa kar na yi abinda zai sake sanya Baba yin fad'a, ko ya yi tsaki kamar yanda ya yi d'azun, ba mu wani jima ba muka yi sallama da juna na yi sallar isha'i na yi shirin kwanciya, na riga na gama bajewa a gado zan kwanta na bar space inda Habibah zata kwanta itama tunda zai ishe mu, sai jin Ummah na yi ta ce, "Mahreen na ce ga shimfid'a se ki kwanta ni bari na yada tabarma a tsakar gida ke kuma Habibah se ki hau gadon" Da sauri Habibah ta ce, "Ahh Ummah ta yi kwanciyar ta ni zan kwanta anan ɗin, babu komai" Ina jin su suna ja in ja takaici ya hana ni magana, ni dai da fari Ummah ta san bana son kwanciyar qasa, ciwon jiki take saka ni, tunawa na yi da farkon zuwa na garin yanda aka bar min gadon na kwanta har se da washegari da kaina na yada katifa qasa na kwanta, tun daga nan da ta gane kwanciyar qasa ciwon jiki take saka ni nake kwana a gado in na zo shine yau ake so na dawo qasa bayan gadon ze ishe mu ba sai na sauka ba, jin Habibah ta ce za ta kwanta a qasan ne ya sa na dena tura baki, dan na qudurta ba zan kwanta a qasa ba ko me za a ce. Ina nan kwance bacci ya garere ni sakamakon wani irin tari da ya dame ni, tin Ina Yi a hankali har abu ya ci tura na tashi zaune na dinga yin shi,kanzil ba wanda ya ce mun, haka na yi ta tari har baccin wahala ya ɗauke ni. Ashe ina can yawon bacci cikin dare ciwon Baba ya tashi ban sani ba, da asuba bayan na yi sallah na gaishe da Ummah se na bi lafiyar gado zan koma bacci, dan dama haka muke yi, se gari ya waye muke sake gaishe ta a kuma gaida Baba da Mama da mutanen sauran sashen. Gaba d'ayan su sun zaci na koma bacci, cikin qasa da murya sai Ummah ta ce wa Habibah, "Ki yi sauri ki je ki gaishe da Baban su jiya jikin shi ya tashi be ji dad'i ba akan shi muka kwana" Cikin jimanta lamarin Habibah ta ce "Subhanallahi me ya same shi? " "Yi sauri ki je ki gaishe shi kafin ta tashi ki dawo" Habibah na sanye cikin dogon hijabin ta ruwan coffee bana taɓa mantawa ta miqe ta nufi d'akin Baba,durqusawa ta yi ta ce, "Assalamu alaikum" A hankali Baba ya amsa mata sallamar ta, sannan ta sake cewa, "Ya jikin Baba? Ashe jiya baka ji dad'i ba? Allah ya qara lafiya, ai ban sani ba se daz......" "Tashi ki ban waje, na ce da sauqi......." Ban sake kasa kunne dan jin qarashen maganar Baba ba tsabar dariya da nake ta yi daga nan inda nake a kwance, gashi bana so su san dariya nake tinda su a tunanin su bacci nake, cikin jimami Habibah ta dawo ta zauna a kujera, ita da Ummahn suna sake jimanta maganar rashin lafiyan Baba, na san za a rina tinda ba yau nake da Baba ba, na riga na sani in dai ya yi rashin lafiya baya son hayaniya,tin Ina dariyar su har baccin gaske ya ɗauke ni. Se da na shaqi bacci na son raina sannan na farka, na je na yi brush na wanke fuska ta sannan na ajiye brush dina a jaka ta a lokacin Habibah bacci take bata farka ba, dan haka se na sa hijabi na na je qofar dakin Baba na durqusa na gaishe shi ya amsa cikin sakewar fuska tare da tambaya ta ya jiki na dan ya ji ina ta tari da alama mura ke son kama ni,godiya na masa da kulawar shi a gare ni sannan na miqe na je na sake gaida Ummah da Mama, nan take Ummah ta ce, "Ki jira Habibah ta farka se ku shiga cikin gida ku yi gaisuwa tare" Murmushi na yi na ce mata "Toh Ummah " Shara na fara yi kafin ta farka har na gama ta na bacci,ina tsaka da wanke wanke ta farka, ni ban san ta farka ba se da ta yi brush ta shiga ta ajiye brush ɗin ta fito, sai na ga Ummah na nuna mata hanyar tafiya sashen Baffanin Yah Maheer dan ta je ta yi gaisuwa,sai na yi kamar ban gani ba, Zaituna ce ta fito matar Isma'il da runtumemen cikin ta ta zauna a kusa da inda ake wanke wanke ta dinga kwakule kasar ginin wajen ta na sha, saboda daɗin ta take ji, a haka muna zaune ina kallon ikon Allah Habibah zata je gaisuwar ba da ni ba ko kuwa yaya? Ina kallon ta kuwa ta yi gaba zuwa gaishe gaishe, ni kuma na yi kamar ban gani ba na qarasa wanke wanken na tashi na wanke jiki na, ta na dawowa muka haɗu muka gaisa da junan mu sannan ta wuce daki na tafi tawa gaisuwar. Kwana biyu tsakani aka yi bikin qaramar sallah cike da nishad'i da annashuwa washegarin sallah Isma'il ya ɗauki matar shi suka koma bauchi, ni da Habiba kuwa mu na nan tukunna bamu tafi ba, dangi ana ta kawo mana kayayyakin qauye, su kuka, albasa, yaji, daddawa, kubewa, kayan miya danye da busasshe sai citta da kayan kamshi da sauran su, duk wata albasa da kayan miya da aka kawo sai a baza su su sha iska dan kar su lalace kafin mu tashi tafiya. Bayan sallah da kwana uku kuwa Abubakar ya zo ganin gida shima mu kuma muna shirin komawa da yamma, nan fa aka jawo kayayyakin da aka bamu aka hau rabo, tin da na ga yanda ake rabon be min ba se na ɗauki littafin addu'o'i na na hau karanta wa, Suwaidatu na can an gama haɗa mata kayan ta ta na ta kuka bata so ta koma, duk sai na yi ta jin rai na babu dad'i, ina nan zaune ina tunanin shin me ke saka yarinyar nan kuka ne haka duk sanda muka zo za mu koma Bauchi kamar wadda ake yi wa wani mugun abun se na ga Ummah ta kwashi kayan miya me yawa ta zuba a na gaban Habibah suka kalli juna akai murmushi,ni ɗin ma murmushin na yi a raina ina ayyana cewar, 'Ohhh ni Mahreen Ina ganin duniya yau, mu da muke mu biyar shine ake karawa mutum biyu,Allah ya kyauta' Ta na gama rabawa se cewa ta yi, "Mahreen ɗauki naki" Cikin nuna halin ban damu da abinda kuke aikatawa ba duk da na gani na ce, "Ahhh ba komai Ummah a daukar mana kowanne" Ai kuwa nan da nan aka kwashe wa Habiba kayan miyan gaban ta a kwali, busassun kayan miya kamar su kuka kub'ewa da sauran su aka mata ledar su daban suma, duk ina zaune ina kallon ikon Allah, hadari ne ya taso sosai, ga zafi ana ta zubawa, cikin sauri ta d'ebi nata ta tafi, mu kuma Yah Maheer ya yi waya ya ce mu jira in Abubakar ya gama gaishe da mutanen gida gobe da safe mu dawo tare, ba haka na so ba, dan kuwa raina b'ace yake da abubuwan da aka yi min, haka na danne ba dan na so ba, Baba ya kula da duk abinda ya ke faruwa, dan haka sai ya dinga min hira sama sama, na kuwa ji daɗin hakan sosai, cikin wata hikima ta Ubangiji ina yada fitila gefen kujera zan d'auki tabarma sai na ga kwalin da aka totsarawa Habibah kayan miya da yawa a ciki a gabana ta manta da shi saboda sauri. Abubakar ne ya dauka ya kalla ya yi dariya sannan ya ce, "Ba rabo ba" Umma na jin haka ta hau salati ta na nuna baqin cikin manta kwalin da akai, nan da nan Baba ya ce a fitar da kayan miyan a baza su kafin gobe sai a kai musu, haka kuwa aka yi, aka baza su gefen namu da dama tunda aka ce ga kason mu ban kwashe ba se da Yah Maheer ya ce zamu sake kwana sannan na baza shi. Qarshe dai har da muka koma Bauchi kayan miyan rabon mu ya koma dan kuwa bata je ta ɗauka ba. Haka na dinga ganin banbanci ina mamakin me zai sa a banbanta tsakani na da ita tunda dukan mu d'aya muke, har se da watarana na samu cikakken bayani da tarihin Yah Maheer a bakin shi. *Wanene Yah Maheer?* Shine Babban d'a a maza a wajen Malam Mahmuda da kuma Malama Zainab, mahaifiyar Yah Maheer ta rasu a wajen haihuwar qanwar shi Ruqayyah wannan shi ne dalilin da ya sa riqon shi ya dawo wajen Ummah, ita ya sani a matsayin mahaifiyar shi, ta yi masa riqo riqo irin na amana, ta yanda bata banbanta shi da yaran da ta haifa ba, kowa ita ya sani a matsayin mahaifiyar shi. Mahaifin Yah Maheer na matuqar son shi da qaunar shi, ta yanda duk wani abu da ya danganci shi ya na ɗaukar shi da mahimmanci, a nan na gano cewa ko da Baba na so na na musamman to soyayyar Yah Maheer ta shafe ni. Yah Maheer ya bani labarin gidan Gurama da nake zuwa gaishe su in mun je Liman Katagum nan ne gidan su Mahaifiyar shi, kakanni shi na wajen mahaifiya sun rasu sai qanin mahaifiyar shi da suke uwa ɗaya uba ɗaya da kuma qannen ta da suke uba ɗaya kawai se cousins ɗin mahaifiyar tashi ne suka rage a gidan. Ko da na gama jin wannan tarihi kafff sai kawai zuciya ta ta ba wa Ummah uzuri akan abinda ta yi a matsayin murna da farin cikin ganin surukar ta ta ɓangaren Kabeer, sannan na tuna baya nima fa lokacin zuwa na ta yi min wannan tarbar wadda ta sa ban taɓa ɗaukar ta a wani matsayin da ya wuce mahaifiya ga Yah Maheer ba. Dan haka sai na danne abinda ya faru na binne shi a raina ban sanar da shi komai ba, muka ci gaba da murnar dawowa ta gida lafiya. Ana haka wataranar Laraba Yah Maheer be koma aiki ba muka karbi baquncin qanwar Yah Maheer wato Sadiya (Allah Ubangiji ya gafarta maki ya yafe maki dukkan kurakuran ki ya raya abinda ki ka bari), Abida ta zo da tsohon ciki a jikin ta a wancan lokacin, haihuwa ko yau ko gobe, cikin sauri na dora ruwan yin ɗan wake dan na ji labarin itama ta na son shi kamar Yah Maheer, ina can kitchen Ina kwab'in ɗan wake na bar ta da yayun ta su yi hirar zumunci. Ban koma ba se da na kammala ɗan wake na yi miyar attaruhu da yaji albasa da kifi, na tsame taliyar da na dafa saboda su a Bauchi sukan haɗa taliyar da ɗan wake, ta wani ɓangaren na dafa taliyar ne saboda ni, dan bana cin ɗan wake sosai se dai sama sama. Se da na ajiye wa Yah Maheer nashi da duk abinda ya kamata sannan Suwaidatu ta kai wa Abubakar nashi ta ɗauki nata sannan na dakko mana namu ni da Abidah. Bismillah mu ka yi muka fara cin abincin, bana manta wa tsabar yanda abincin ya mata dad'i se da yawu ya zuba a bakin ta duk da ta cika bakin ta da ɗan wake, tsokanar ta na dinga yi ta na kare kan ta da cewar, "Ba dole na zubo da yawu ba tunda kin iya girki, da baki iya ba se na kawo wa Yayah wata ya qara da ita" Haka muka gama cin abinci cikin raha da barkwanci suka gama hira da 'yan uwan ta sannan Abubakar ya dakko machine ya gyara daidai yanda za ta iya hawa, kallon fuskar Abubakar na yi na ga yanda ya bata rai, sai na ji wani irin yanayi ya shige ni wanda na kasa tantance shi, haka Abidah ta hau machine ɗin nan ya tuqa ta suka tafi. A zato na gidan ta zai maida ta se dai ban sani ba a she ba gida suka nufa ba wani wajen suka wuce............ *Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful* 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 18: Gidan Kabeer suka je inda suka tarar da wata cousin ɗin su Abubakar ɗin ta je itama ziyara, nan fa aka haɗu aka dinga yi da ni, Habibah kuwa ta dafa shinkafa da miya da nama zuqu zuqu, ta d'ebo masu, su na ci suna min qafi kala kala,wai ni MAHREEN ce ban iya abinci ba banda kwab'a ba abinda na iya, Abidah ce ta kai lomar shinkafa bakin ta sai cewa ta yi, "Yanzu ma fa da na je taliya ta dafa tsabar ba a san kan girki ba wai ta watsa su karas da kabeji da green beans a ciki, girki ba daɗi ba komai Salam" Abubakar kuwa bud'ar bakin shi sai cewa ya yi, "Ai se ma ta yi tuwo, haka za ka ji shi kataf ba bu dad'i,miya kamar ruwa ga baqar rowa, a wani ɗan qaramin kwano take zuba mana, kamar ita ke nemo hatsin" "Ai gaskiya Yaya Babba na hakuri, ko dake an ce so hana ganin laifi, shi baya ganin laifin ta sam " "Ni nake da wannan matar ai waje road zan ce mata,ba zan d'auki nonsense ba" Hira ta yi hira, Habibah na ta jin su ta na nad'ewa ta na saka su a aji kala kala,dan kuwa ita da wayon ta kuma dama a shirye ta zo. Qazafi kala kala haka suka yi min suka tashi ya maida ta gida, (har a wajen Allah na yafe Allah ya yafe mana dukkan kurakuran mu baki ɗaya ya jiqan wanda suka gabace mu) Abubakar be dawo gidan ba se dare, ina nan na ajiye masa ragowar ɗan wake da taliya saboda ban sake yin wani girki ba shi ne dai. Makaranta kar ku manta Yah Maheer a wannan lokacin qaramin ma'aikaci ne mai ɗaukan dubu ashirin a wata, ga shi ya na ciyar da mutane har biyar watarana sama da haka tunda a kullum se an yi baqi, abu ne me tsananin wahala mu kwana mu tashi ba a yi baqi ba,ya ilahi ina ake so ya samo kuɗin da zai yi wadaqa da facaka da kuɗi? Ina nan ina ci gaba da kyautata wa kowa zato ba tare da na san ana gefe in an haɗu ana zagi na ba, Allah ya hore min fuska me yawan fara'a da hannu mai kyauta daidai qarfi na, duk abinda mutum ya ga ban bashi ba to fa tabbas bani da shi kuma Yah Maheer ba shi da shi, to dole na hakura tunda ba a kyauta da babu. Ana haka matar Isma'il ta haihu, ta haifi 'yarta mace, kyakkyawa mai kama da iyayen ta, Habibah ce ta biyo min muka je har gida muka musu barka da sanya albarka, a lokacin Habibah na ɗauke da cikin Yaron su na fari, tin a wajen wasu ke min addu'a wadda se daga baya na fahimci har da baqar magana. "To kema Allah ya baki rabon in kuna so dan yanzu wasu da kan su suke hana kan su haihuwar" A lokacin nan wayo na da hankali na be bani wai baqar magana ake faɗa min ba duba da cewa wasu ma ni ban san su ba ya akai su suka sanni? Haka muka yini musu muka koma gidajen mu. Ba a jima da haifar Amaturrahman ba Abidah ta haihu yaron ta namiji,nan ma ban bata lokaci ba wajen dibar jiki muka je gidan nata barka,anan ne nake jin za a yi suna, bayan mun tafi bamu sake komawa ba sai ranar suna,duk wani abu da za a yi haka aka dinga maida ni baya ina ji ina gani be dame ni ba a wancan lokacin dan ban ma fahimci wai ana sane ake min abu dan raina ya ɓaci ba, akwai yarinta sosai da kuma rashin ɗaukar abubuwa da mahimmanci idan ban gane inda suka dosa ba. Bayan gama suna da sati biyu Yah Maheer ya zo min da albishir ɗin samun aikin shi a Kebbi state, shine dalilin da ya sa na ga ba ya zama sosai a watannin nan, dik da ban taɓa zuwa garin Kebbi ba amma ya bani labarin garin a takaice,se na samu kaina da yin murna sosai da farin cikin za mu koma can da zama, haka kawai na ji na gaji da garin Bauchi,Yah Maheer da ya ga murna ta ta yi yawa sai ya tsaya kawai ya na kallon yanda nake ta tsallen murna ina rawa, da na gaji kuma na haye gadon na faɗa jikin shi na kwanta ruf da ciki muna fuskantar juna,hannu na na sanya cikin gemun shi ina tajewa a hankali idanun mu na sarqafe da na juna na lankwashe murya irin yanda yake so na ce, "Yaushe za mu tafi to? Kaa bar ni se ihun murna nake baka ce komai baaa" Murmushi ya yi sannan ya sanya yatsan shi manuni ya na kewaye lips ɗi na da ya ke masifar so ya ce, "Baby na na barki ne ki yi murnar ki sannan in sanar da ke tsarin tafiyar, ai kin ga be kamata ki na tsaka da farin ciki ba na katse miki shi ko?" Ji na yi hankali na ya tashi da jin yace zai katse min farin ciki, da sauri na sake mannewa a jikin shi na ce, "Ni fa ban gane ba? Me ka ke nufi?" "Ina nufin ba tare da ku zan koma ba kai tsaye, har sai na je na ga yanda wajen yake in yaso se na dawo na ɗauke ku mu tafi dika" Ji na yi hawaye sun fara bin kunci na,raina na tafarfasa me yake nufi? Ya na nufin zai iya tafiya wani garin me nisa ya barni? Ina jin fa ya na faɗin in aka tashi daga Bauchi tin safe se an kai goman dare ko sama da haka kan a isa garin, me yasa ba zai je da ni ba? Kwantar da kaina ya yi a qirjin shi ya sumbaci goshi na sannan ya hau jijjiga jikin shi ya na lallashi na, "Habaa young lady? Kukan me ki ke kuma? Ke da zan tafi na bar ki ki zama shugabar gidan duk wanda ya yi ba daidai ba ki hukunta shi, ko ki bari in na dawo ki sanar da ni,dan Allah ki dena kuka bana so, ba fa yanzu bane tafiyar ma se next month ne fa" Cikin kukan da na sake rikicewa da shi na ce, "Lallai ma Yah Maheer ɗin nan jibi ne fa next month ɗin " "Eh mana kin ga kuwa ai da saura, next month fa, month fa aka ce ba week ba" Kawai sai na ji wani irin ɓacin rai ya kama ni, saboda hakan ba abun wasa bane, abu ne me mahimmanci a waje na amma yake wasa da shi. "Yaushe ya zama next month bayan jibi jibin nan za ku tafi, kai yanzu baka ji komai ba za ka tafi ka barni?" "Baby na da ace zan iya buɗe maki zuciya ta ki ga irin kewar ki da na fara tin a ranar da na fara neman aikin da sai kin tausaya min,ba yanda za mu yi ne tafiyar nan inshaa Allahu alkhairi ce inganta rayuwar mu zata yi nan gaba, na yi zaton ma za ki lallashe ni tinda ni ne zan je inda babu ke babu kowaaaa a dangi daga ni sai mutanen da ban sani ba, ban taɓa ganin su ba, ban san ya halayya da dabi'un su ya yake ba, Baby na dan Allah ki yi hakuri ki dena kukan haka ya isa" Sauka na ɗan yi daga jikin shi sannan na daki qirjin shi, cikin shagwaba na ce, "To ba kukan tausayin ka nake yi ba yanzu,ai ni ban san kai kaɗai za ka tafi ba, amma kar ka damu ka na da Allah, Allah ya kare ka ya biya buqatu na alkhairi, Allah ya sa ka je lafiya ka dawo ka tadda mu lafiya" "Yauwaa My love ko ke fa a dena kukan banzaaaa" Cakulkuli ya fara min muna ta dariya, lokacin sallar azahar ne ya yi,

Chapter 14 of 30