Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sulhunta an fahimci juna. Da misalin goma na safiyar ranar ya gama shiri tsaf zai wuce makarantar da yake koyarwa wato Waziri Umaru Federal Polytechnic, kallon shi na yi na kuma sannan na ce, "Wai ka na nufin dama haka ka ke shan gaye ka shiga makarantar?" "Kaiii jama'a! Wanne gayen kuma, ina gayen yake anan? kema dai Baby na akwai neman tsokana ki ga Ustaz da gemun shi da komai ki wani ce gaye" (mijin ki ko bai da kyau yabi abun ki sannan ki nuna ki na kishin sa zai ji dad'i a ran shi) Nan da nan fa na hau faɗa ina cewa gaskiya ni ba zan yarda ba, ya za a yi ya wani sha gayu ya fita? Qarshe har da kukan shagwab'a ta da ya zame min jiki, ya kuwa hau lallashi na ya na ce min zan sa shi makara fa, da kyar na kyale shi ya qarasa shirin shi . Ai kuwa na ce se fa na masa hoto zai fita, dake Yah Maheer mutum ne da baya son hoto kwata kwata se ya qi amincewa,dena dariya na yi na hau murtuke fuska na ce ya tsaya na masa hoto, jakar shi ya ɗauka ya hau rufe fuska zai fice,faɗa na fara sosai ina nuna rashin jin dad'i na akan yanda baya son ya yi hoto, ai hoto ana yin shi ne ko dan tarihi, ko kuma in ya fita na dinga gani ina jin dad'i har ya dawo, nan fa aka hau rikici shi sam ba za a masa hoto ba, ganin yana makara ni kuma ban san Ah ah ba, ya sa na mugun shan mur na bata rai na ce, "Tsaya in maka hoto lokaci na tafiya, in Kuma ba haka ba za mu yi ta tsayuwa ne anan ko na bi ka makarantar se ka zab'a" Ya san hali na sarai zan iya aikata daya daga abinda na lissafa dan haka sai ya tsaya na yi masa hoton wanda har yanzu yana nan aje a wayoyin mu. Ina gama yi masaa hoton muka yi sallamar mu kamar yanda muka saba (abun sirri ne) sannan na raka shi har kusa da gate ɗin gidan sannan na dawo, a hanyar komawa part dina na ga Maman Ameerah ta fito da daurin qirji ta zubar da ruwa kadan a wata roba, gaishe ta na yi sannan na wuce, kallo ta bi ni da shi ni kuma na yi kamar ban gan ta ba, na shige gida na. Maman Ameerah irin dogayen matan nan ne, ba za a kira ta da baqa ba, amma ba fara bace sosai za mu yi haske ɗaya da ita,mace ce mai magana cikin taqama da isa da izza wanda tin a daren da muka zo na kula amma ban maida hankali akai ba saboda ba shi ne gaba na ba,daga baya nake jin labari wajen Addah Babba cewar ta san mijin ta a Bauchi, dan haka se na ɗauki girma na bata a cikin zuciya ta, domin dama ba sa'ata bace da gani ta girmen sosai, tinda ni har a lokacin ina da sauran watanni hud'u kafin na cika shekara sha takwas. Da fari zaman mu muke lafiya ba wata matsala har Yah Maheer ya samo mana makarantar BICE (BASAURA INSTITUTE OF COMPREHENSIVE EDUCATION) ni ina secondary section suwaidatu na a primary section, direct SS3 aka saka ni su na first term a lokacin, da fari na fara jin kamar ba zan iya makarantar ba saboda tsaurin da na gani akwai, se daga baya na gane tsaurin alkhairi ne a wajen ɗaliban saboda in aka bar su sakaka rashin ji za su zuba ba na wasa ba,a hankali ɗaliban suka gano ni matar aure ce, nan fa suka fara bani girman da na dinga ganin ma ya min yawa ai. Karatu ake a BICE ba na wasa ba, wanda ni a matakin da nake a kuma yanda ban samu wani good background ba na ilimin boko sai na ke shan wahala, musamman bangaren da ya shafi calculation,bangaren English da Biology kawai nake samun salama a makarantar,a haka dai akai ta tafiya ana daburawa watarana na gane watarana bana gane me ake yi kwata -kwata. A gida kuma Yah Maheer na iya qoqarin shi dan ganin na iya duk abinda ake koyar mana musamman calculation ɗin amma inaaa bana ganewa, da ya fara zan gane da ya gama ya tafi ya tafi da abun shi se in Ji kamar an min yasa a Kai na. Bangaren suwaidatu kuwa da alama ta na jin daɗin makarantar tinda ko a Bauchi private school ta ke yi dama,ni ce dai ban samu karatu kamar yanda ta samu ba, daga islamiyya na koma primary na boko kuma ban fara daga aji daya ba datsa na yi ban kai aji shida ba na rubuta jarabawa na samu JSS 1 a day Science, Ina JSS 1 na qone a qafa na koma Army day, Ina SS 1 akai min aure,ban yi SS2 ba kuma duk wani karatun sakandire na SS 2 ya fi tattare abubuwa masu mahimmanci dan SS 3 ɗin se ya zamana kamar revision ake musu se in ta gyad'a kai ban gane komai ba. A haka dai rayuwar ta ci gaba da dad'i da ba dad'i, da wuya da sauqi sauqi, har muka gama first term, muka samu hutu a lokacin ne Yah Maheer ya mana alqawarin in sallah ta zo aka samu hutun sallah za mu je ganin gida, murna muka dinga yi tini muka manta da nisan hanyar muka hau hango gida. Jarabawa ta matso dan haka sai muka maida hankali sosai ni da Suwaidatu wajen yin karatu, na fi gane karatu da asuba, dan haka da dare nake jotting abinda zan karanta da asuba ina idar da sallah zan taba karatun qur'ani ko shafi ɗaya ne se na yi addu'a sannan na hau karatu na na boko, a haka zan ta yi har gari ya dan yi haske sannan na shiga kitchen da takarda ta a hannu, ina aiki ina karatu, da na gama shirya wa Bashar zai zo me machine din da Yah Maheer ya Sama mana dan kai mu makaranta. A haka muke har muka yi jarabawa guda uku,a hankali na kula da yanda maqocin mu ke da shegen kallo, idan ya fara baya jin ya dauke idon shi sai ya bar wajen ko ni na bar wajen ko kuma ya samu kujera ya dasa ya zauna daidai inda zai na facing din mu, duk girman gidan nan ba zai samu inda zai zauna ba tare da ya Kalle mu ba tinda mu ne a qarshe dole a gaban gidan mu za mu yi shimfid'a mu zauna,ga zafi kamar ana feshin wuta ban saba ba har a wannan lokacin, (ba a sabo da zafi) rasa inda zan saka kaina nake yi,har dai wasu quraje masu mugun zafi da tada hankali suka hau fito min a cikin kai na da jiki na, su ba ruwa suke ba ba kuma qaiqayi suke ba, haka za su yi jawurr su na kyalli, ko maqiyi na ba zan taɓa yi wa fatan shiga wannan wahalar da na fuskanta ba a wancan lokacin, nan take na gane qananan qurajen da ke fito min ashe a fuska in Zan fita nafila ne, (wasu quraje nake yi a fuska ta da zarar na ayyana zan fita yau ko zan fita anjima, nan da nan sai su fito su batan fuska, da na dawo daga inda naje zan neme su na rasa,bana ma tuna su, se daga baya zan hau tunanin yaushe qurajen nan suka warke ne? In kuwa zan shekara a gida ko daidai da digon kwalli ba zan yi qurajen ba) Wahala se ta qaru akai na, bama bacci ni da Yah Maheer gamsasshe saboda azabar qurajen nan,ga constant ciwon cikin da nake yi wanda ya zame min jiki duk a dalilin rashin yin al'ada daidai , rasa ina zan aje kaina nake in Ji dad'i, in kwanta, in tashi,in zauna, in yi yawo, duk bana samun sauqi, sai da ya zamana in Zan tafi makaranta daga ni Se Yar qaramar shimi ta ciki kai ba dankwali haka zan je na rubuta jarabawa na dawo gida. Qurajen nan ba su tafi ba sai da na gama jarabawa duka, aka mana hutu sai kawai na wayi gari babu ko da d'igo ɗaya na tawada daga qurajen jiki na ya dawo normal, ban kawo komai a kan haka ba sai na ɗora wa exam laifin da kuma zafin rana da nake shiga da zafin gari. Mun samu hutu kuma alhamdulillahi ya yi daidai da haihuwar Sadiya qanwar Yah Maheer murna sai ta baibaye raina,har nake sanar da Maman Ameerah maqociya ta fatan Allah ya raya ta yi min sannan na ce, "Wataqila kafin mu dawo kema cikin ki ya girma,Allah ya raba ku lafiya" Cikin isa da taqamar ta ta ce, "Ehhhhhh" Da na ga kamar bata son hirar se na qirqiri faɗin ina da aiki bari na tafi,budar bakin ta se cewa ta yi, "Za dai a je a maqalewa bawan Allah tinda ya na gida, wai ku ba kwa gajiya da yin abu ɗaya ne? Na ga alama watarana sai na sallama na miqo wa Uncle Malam madarar peak dan ya samu kuzari habaaa" A lokacin nan wata iriyar kunya ce ta kama ni,saboda ni dai ban sa wa kowa ido ba, dan haka ban yi tunanin wani ya sa min ido ba ko ina ruwan ta da zaman mu a tare ko yaushe? Ban ce komai ba na yi murmushin yaqe na wuce, dan ni kunya ma ta bani. Ko da na koma bangare na se nake sanar da Yah Maheer me Maman Ameerah ta ce, gyaran murya ya yi sannan ya ce, "Haka suke min ko a waje, da an idar da sallah za su hau faɗin na zauna a yi hira mana ni Ko da yaushe na tare a gindin mace, ba zan shiga cikin maza 'yan uwa na ba a yi hira, ni kuwa nakan ce musu matata ta fi ku iya hira me zan zauna na yi cikin maza ina da mata a gida? Dole su kyale ni na dawo gida, banda hirar banza da wofi ba abinda ake yi a taron da ma yawancin majalisu, haka zaki ji su na hirar matan su da bai dace wani ya sani ba,to fa shi za su yi ta yi a wajen,majalisi indai ba na ambaton Allah bane to tabbas se an saɓa wa Allah a cikin shi, ni kuma a kullum ina neman tsari da irin wuraren nan" Tsabar jin daɗin maganganun shi kawai se na tura qofar d'akin mu na ce, "Bari in zo mu ambaci Allah mu samu lada ko ba haka ba?" Dariya muka yi a tare, na kuwa janyo mana qur'anin mu da ke gefen gadon mu a ko da yaushe na kwanta a jikin shi muka hau karantawa har se da na fara hamma alamar ina jin bacci, sannan muka yi addu'a na ajiye a gefen gadon inda na dauka mu ka hau hira da tsare tsaren tafiya, a lissafin da mu ka yi ya kama nan da kwana biyar za mu tafi gida. Ana sauran kwana uku mu tafi gida Yah Maheer ya bani kuɗi ya ce na je na yi mana siyayya ai kuwa ban b'ata lokaci ba muka shirya tsaf muka tafi kasuwa ni da Suwaidatu, muka hau siyayya,kusan rabi da kwatan kuɗin akan ta ya qare, dan kuwa ita ce yarinya duk inda muka je ita zata yi representing din mu, in ta fito fesss mun fito, in batai fess ba to mu ma haka, ban ji komai ba na kyashi ko qin kashe mata kuɗi a matsayin ta na qanwar miji na kuma Yayana sannan ita ma ta wani bangaren qanwata. Tinda muka dawo na nuna wa Yah Maheer me na siyo na ga ya na murmushin jin dad'i,godiya ya yi min sannan na kwashe kayan na hau haɗa mana su a akwati,cikin mamaki ya ce, "Kaiii Baby na tun yau za a fara haɗa kayan?" Dan haɗe fuska na yi sannan na ce, "Da se yaushe to? Ko ka manta ni in Zan tafiya na fi so na hada komai da wuri dan haka a sa min ayis kawai" "Tom an sa maki" Takardun shi ya ɗauka ya ci gaba da marking, lokaci zuwa lokaci ina watsa masa hira ya na taya ni. Ranar kuwa da za mu tafi na yi wa Maman Ameerah sallama da yaran muka ɗauki hanya da duku duku dan a ranar Yah Maheer ke son mu isa Bauchin Yakubu. Cikin ikon Allah kuwa bamu jima a hanya ba muka isa Kano,dan kuwa ana kiran azahar muka isa, (Ya Allah ka dawo mana da kwanciyar hankali a qasar nan ya Rahman) ko gida bamu biya ba muka wuce Bauchi,da isar mu ba mu tsaya a gidan kowa ba muka wuce LK, ranar ko kukan ma kasawa na yi tsabar gajiya, Yah Maheer kuwa wani irin haushin shi da takaicin shi na ji ya kama ni, na qin tsayawa a huta a hanya da be ba. Ya na kula da hakan, dan haka shima sai ya ɗauke kai be kula ni ba ai ba ni kaɗai na gaji ba in haka ne. Lale maraba aka dinga yi mana a gidan kowa ya yi murna da ganin mu sosai, su Maman Ummeeta da Umman Muhibbah murna a wajen su kamar su goya mu, yaran ma sun yi matuqar farin cikin ganin mu,nan da nan sashen su Yah Maheer ya cika da yara,sai Suwaidatu ta ɓace a cikin 'yan uwan ta, sannan ne na samu fuskata ta washe da murmushi, dan ganin yanda kowa ke nan nan da ita da kuma ni, se ta zama abar sha'awa a cikin yara sa'annin ta har ma da wanda suka d'ara ta. Baba kuwa banda fara'a da farin cikin ganin mu ba abinda yake yi, a haka muka zauna bayan na gaida kowa mu ka hau hira da shi,Baba na matuqar so na ni ma kuma ina son shi dan ban taɓa ganin ya sake da surukan shi ba yanda muke yi da shi, komai nawa na da mahimmanci a wajen shi. Baba baya barin kowa ya masa sharar qofar d'akin shi da d'akin nashi ma kan shi, shi zai tattara ya sharo abinshi, ko an masa sai ya sake, inda kowa ya gasgata cewar Baba na so na kenan,dan kuwa ni nakan Yi masa Shara har ya shimfid'a carpet a wajen ya zauna ba tare da ya sake sharewa ba. Washegari bayan mun huta muka shirya mu ka tafi gaishe gaishe da Ummeeta daga gidan gwaggonayen Yah Maheer, har gidan 'yan uwan Babana na kusa, zuwa gidan qanwar shi, se muka biya gidan 'yar Babbar yayar shi mai suna Rasheedah, Rasheedah kusan sa'ata ce, kuma duk zuwan da zan yi Liman Katagum sai na je gidan ta gaishe ta kamar wata uwar miji na, dan haka wannan karon ma mun je, ta kawo mana ruwan randa, ina gani yaran na jagwalgwalo a jiki, na kuwa qi sha na ce na qoshi, a haka muka gama gaida su mu ka tafi gidan iyayen ta, wato gidan Yayar Yah Maheer ɗin......... 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 22: A can mu ka qarasa yinin ranar har na samu yin baccin rana, bayan na tashi ne na ci shinkafa da wake da ta ji man quli shanana da yaji me dad'i,naa ɗauki yayar shi kamar uwa saboda babbar mata ce sosai ɗan ta na fari ma ya na mata har biyu, ta na da jikoki, dan haka ba qaramar mata bace babbar mata ce, akwai 'yar kunya a tsakanin mu, duk so na da qauna ta da wake da shinkafa ban zage na ci gaba ɗaya ba, bayan mun yi sallar la'asar ne muka yi mata sallama mu ka tafi. A hanyar mu ta koma wa ne muka shiga gidan qanwar Babana Goggo Talatu da gidan cousin ɗin Yah Maheer wato Umman Bello,tinda a hanya suke mu ka gaishe su daga nan muka faɗa gidan Addah Ummuna,anan na baje komai nawa mu ka ci mu ka sha muka yi hira sosai, bamu bar gidan ba sai bayan magariba,sannan muka tafi gida. Ko da mu ka koma gida Ummeeta ta yi sashen su nima na wuce namu, zaune na tadda Baba ya na ta jan carbi su Ummah kuwa sun tasa tuwo a gaba za su ci, gaishe su na yi sannan na samu waje na zauna ina jiran Baba ya idar na gaishe shi,se na kula Isha'i yake jira dan haka ba zai magana ba se ya kammala abinda yake se na miqe zan shiga d'aki, ban kula da sababbin takalman da ke a bakin qofa ba sai da na shiga ciki na tadda matar Abubakar wato amarya Mommy, cikin washe baki na ce, "Ahhh mutanen Bauchi yaushe ku ka zo?" "Tin dazu muka zo ku na can ku na yawo" Kalmar yawo ta sa na shiga tunanin wannan ta san yawan dangin mu kuwa? Anya wannan ta iya magana kuwa? To ko zancen akai ta yi a gidan cewa na tafi yawo? Zan gani a fuskar Baba bari ya gama lazimi na gaishe shi, dan shi baya boye min komai,duk da be taɓa min faɗa ba amma in be ji dad'in abu ba ina ganewa. Tinda na kula Mommy kamar bata iya magana ba a hirar da muka ɗan fara da ita, se na fara iya baki na saboda ina da wani hali, na tsani a cab'a min magana, kuma bana son mutum ya dinga magana da raini a ciki yanzu raina zai ɓaci, amma in na kiyaye jan doguwar hira da mutum sai a zauna lafiya ban hasala ba ballantana na faɗa wa mutum ba dad'i nima. Abinci na na gani a gefe, shafa ciki na na yi da yake a cike maqil da shinkafa da Miya da lettuce da tumaturi da albasa, Se soyayyan kifi wanda na ci a gidan Addah Ummuna, duk so na da tuwo haka na kalla na kyale dan ba zan iya ci ba, ina nan zaune aka kira Isha'i nan da nan kuwa Baba ya tashi ya fara sallah, (Ba ya zuwa Masallaci saboda bashi da lafiya)Nima fita na yi na yi alwala na dawo d'akin Mommy na kwance ta na danna 'yar qaramar wayar ta, sallah na tada nima na yi qasaru, ina idarwa na samu waje na zauna ina tasbihi ga Allah, a sannan ne ta tashi ta je ta yi alwala ta dawo ta yi sallah itama,ina nan zaune na ji muryar Baba ya na faɗin. "Kun dawo?" Da sauri na je bakin qofar dakin na durqusa na gaishe shi ya amsa min cikin sakewa da fara'a, ji na yi raina fesss ba abinda ya dame ni tinda kowa ya sauya min a gidan shi kaɗai ne be sauya min ba dan haka nima ba zan damu da fushin kowa ba sai nashi. Mu na nan zaune Yah Maheer ya dawo, direct dakin Baba ya shige Abubakar kuma ya shigo inda muke, nan fa suka fara wani wasanni da Mommy a raina dariya kamar zan yi yaya, saboda abun se ya min wani banbarakwaiii,yi na yi kamar ban gan su ba na buɗe jaka ta na dakko littafi na da biro na hau rubuce rubuce na da na saba,sun kula da cewa gaba ɗaya hankali na baya kan su, domin da gaske ina fara rubutu hankali na ya bar kan kowa a gidan,saboda ni in na sa rubutu na a gaba to fa shi ne a gaban nawa, gajiya suka yi da wasannin nasu ya samu waje a kujera ya zauna suka ci gaba da hira, ba jimawa Yah Maheer ya min waya, na duba jaka ta na zaro wayar, ina ganin sunan shi a jiki na yi murmushi, a raina na ce, 'Dan Baba se yanzu za a kira ni kenan' Da sallama na ɗauki wayar shima ya amsa min ta can bangaren,a hankali ya ce, 'Baby na i miss You wallahi' Yi na yi kamar ban ji ba, se na ce, "Uhummm? Ka ce me?" Da alama tashi zaune ya yi, wanda ina leqa dakin Baban se na hango shi ya na leqawa ya ga shin Baba na jin shi ko kuwa, dariya ce ta kama ni na sake nuna masa ni fa ban ji me ya ce ba, cikin qasa da Muryar shi ya sake cewa, 'Cewa na yi na yi kewar ki wallahi,in baki ji ba yanzu ki bari zan faɗa maki gobe, dan na ce gobe a fitar da dika kayan d'akin can a maida naki' "Tabdijam ai kuwa se dai ka riqe kewar nan har Allah ya maida mu Birnin Kebbi," 'Habaaa ke kuwa, ba ki ga yanda sauran mutanen gidan ke yi ba, kowa da d'akin shi da matar shi shi kenan ni se na fita daban a dangi' "Wa ya ce ka fi dangin fari (hasken fata)? Ai dama kai ka fidda kan ka a dangi ba ni ba" Shiru ya ɗan yi sannan ya ce, 'To gobe dai zaki koma d'akin can da ke kallon rijiya kin amince?' "Me zai hana tunda kayana sun dawo gidan da zama, Allah ya kaimu da rai da lafiya" (da muka bar Bauchi se aka dawo da kayan daki na nan liman Katagum da zama) 'Ameen, sai da safe kar a manta a yi alwala, ayi karatun suratul mulk, a yi addu'a a shaaaafe jiki sannan a karkad'e shimfid'a sau uku tare da faɗin bismillahi, a kwanta a hannun dama' "To ɗan albarka yaron Baba, Allah ya maka albarka, Allah ya tashe mu lafiya, hayyakallah" 'Ameeen 'yar yarinya me nauyi kamar na 'yar paper' Buɗe baki na yi zan yi magana ya kashe wayar ya na dariya, ban san sanda na kalli kaina daga sama har qasa ba, yanzu ni za a kira me nauyi kamar na 'yar paper, na ga alama mutumin nan be dai ji nauyin nawa ba ne da kyau amma ba komai, za mu koma gida ne zai ji nauyin da kyau. Shiru dakin ya ɗauka alamun Mommy ta yi bacci ban san sanda Abubakar ya bar dakin ba,dan haka sai na rufe littafi na na yi shirin kwanciya kamar yanda muka saba. Ummah ce ta shiga ta dauki pillow ta mana sai da safe ta yi kwanciyar ta tsakar gida, har na kammala komai na kwanta se na kasa bacci, dabi'ar wankan dare ta riga ta bi jiki na, juyi kawai nake ina kumawa,ido na ya qi bani haɗin kai in rintsa, ga dare ya yi. Ban san ya akai Yah Maheer ya gane na kasa bacci ba sai na ga ya fita ya yi bakin rijiya, ruwa ya ja a bokiti ya kai banɗaki duk ina jin shi, ya na fitowa ya haske dakin da fitila ya kashe ya sake haskewa ya kashe, ni ce a farkon gado dan haka se na tashi na dau kayan wanka na na fita, a bakin qofar banɗakin ya jira ni, na Yi wanka na na koma d'akin, ai kuwa ina kwanciya se tashin numfashi na saboda bacci bugu ɗaya ya yi min. Da asuba bayan mun yi sallah se muka fita ni da Mommy wadda sam bata da qiwa itama muka gyare gidan tasss muka yi wanke wanke, sannan muka dawo muka zauna a qofar dakin da aka ce zai zama nawa,nama muke yankawa wanda aka kawo gidan ban dai san daga ina ba, Baba na qofar dakin shi ya na alwala, a lokacin takwas da rabi ta wuce,da alama alwalar sallar dhuha yake, Mommy ce ta hau yi min complain akan matar Kabeer, yanda ta dinga musu sharri da wulaqancin da ta mata sanda suka je gidan ta,in ban manta ba jiya da dare ma bayan na dawo daga gaishe gaishe se da aka ban labarin nan, menene na maimaita wa? Cikin rashin son ai ta maganar mutane in basa nan na ce, "Mommy ki yi hakuri da abinda ya faru, amma zan baki shawara, kin ga idan irin haka ta faru tsakanin ki da wani, ki na samun wanda ya bata maki rai ki yi masa magana saboda ku fahimci juna a daidaita komai, kinga yawan wane ya min wance ta min dinnan ba qaramin matsala yake jawowa ba,tinda nake a gidan nan ba a taɓa durqusawa a gaban manya ba saboda samun saɓani, dan Allah kar ki sa daga zuwan ki a fara, mu mata mu ne zamu taimaka wa mazan mu

Chapter 17 of 30