ledojin da ya shiga da su fuskar shi bata dena bayyanar da murmushi ba,juyawa nayi na bude ma'adanar kayan da ban san kan abubuwan ba, ban san ina aka ajiye kayan bacci ba, tinawa na yi da Inda yayar mu ta nuna min ta ce in ina da buqatar sauya kayan bacci na duba, da sauri na duqa na kuwa yi arba da kayan bacci na gaba d'aya,na cikin lefe na da wanda na zo da su daga gida, wasu riga da wando light pink na d'auka masu gashi me laushi a qirji da qasan rigar, sai mayafi kalar kayan baccin nawa, ina gama d'auka na rufe na kama hannun qofa zan fita, kallo na ya yi ya ce,
"Ina zaki je?" Cikin sanyin murya na ce,
"Kaya na zan je na saka......kar ka biyo ni bana jin tsoro" na yi saurin qarasa maganar tawa.
Dariya ya yi mai sauti ya ce min,
"To ba zan biyo ki ba, amma ki tafi da key dan na rufe parlourn,"
Key na zare a jikin qofar na fita na bud'e qofar parlour na shiga, ina shiga na maida key na kulle, amma dik da haka sai waige nake ina fatan Allah ya sa kar ya zo, a haka na sauya kayan, masha Allah kayan sun Karb'i jiki na sosai, mayafi na na yafa,na so na qara fesa turare, saboda ni macece da Allah ya d'ora wa son qamshi, tin ina gidan mu in na gama girkin dare sai na yi wanka na feshe jiki na da turare ko da na Mama ne kuwa.
Kyab'e baki na na yi ina ayyana cewar,
'Gwanda ma ki tafi a haka da sauran qamshin ki har yanzu, kafin ya ga ki na fesa turare ya zaci dan shi ki ke yi'
Ina gamawa sai na samu waje a kujer qarama na zauna na yi shiruuu ina kallon yanda iyaye na suka yi qoqari, kamar yanda bana son tarkace Mamana ta sani haka aka had'a min parlour na ba tarkace, ina nan zaune ni ba me tunani ba ni ba me jiran wani abu ba, a hankali ya kwankwasa qofar, cikin sauri kuwa na miqe na je na bud'e,
"Kin yi alwala?"
"Ah ah"
"Muje mu yi to"
A tare muka fita, ya rufe wajen ya sa key a aljihu muka dau butocin mu muka tafi yin alwala,na riga shi idarwa sai na tsaya ya idar sannan muka koma ciki, sallah ya ja mu raka'a biyu, bayan mun idar ya dafa kaina ya min addu'ar da ake yi wa amare a duk daren su na farko,sannan ya hau min tambayoyi game da addini na, da fari har ga Allah na zaci qure ni yake so ya yi, har na dinga tinanin me ya kawo wannan tambayoyi kamar ana islamiyya?
Ya gama tambayoyin shi na bashi amsa, wajen banbance wankan haidha da janaba ne aka samu akasi ban san banbancin su ba, dan haka se da ya min bayani, ya na yi ya na wani kashe murya da lankwasa ta da fitar da makhareej.
Mu na kammalawa ya janyo ledar da ke ta tsinka min yawu, wato ledar kaza, nan fa ya yi bismillah ya yanko wata narkekiyar tsoka ya miqo min, kunya na ji ta kama ni, sai na kasa karb'a, ba yanda Yah Maheer be yi da ni ba akan na ci, na qi cin wannan na farkon da ya miqo min, bakin shi ya kai, nan da nan na had'iyi wani mugun yawu makwat, tsakani na da soyayyar kaza akwai amana da soyayyar juna,nan take na qudurta a raina in ya miqo na biyu zan karb'a dan ba zan jure qamshin ta ba.
Kamar wanda ya karanci tinani na ya kuwa sake yankowa ya miqo min, na kuwa miqa hannu na dan in karba,shi kuma ya qi saki,ba haka yake so ba so yake ya bani a baki, amma ni a waje na hakan shine daidai,yanda ya tsare ni da ido ne ya sa banda zab'in da ya wuce na bud'e baki na, ina bud'ewa kuwa ya sanya min a baki na hau taunawa, wani irin dad'i ne ya ziyarce ni,haka na dinga jin gard'in ta na tsinka yawu na da sa kunne na qaiqayi, amma saboda rashin rabo a wannan daren ina ji ina gani na hakura daga wannan yankan ban sake cin kazar ba, (which i am always regretting kuma duk sanda na so rikici na ce se an biya ni kazar amarci na da ban ci ba) juice din exotic na yi ta korawa ina zare ido, shi d'in ma ajiyewa ya yi da ya ga na miqe na zauna a bakin gado, saboda so nake na kwanta na gaji ga bacci, amma ina tinanin ya za a yi na kwanta gado d'aya da namiji, na mijin ma wanda nake matuqar ganin mutuncin shi, ohh ya Allah ka kawo min komai da sauqi.
Ba tare da na shirya ko na san sanda ya hau bakin gadon ba, na ji ya kama hannu na ya na fad'in,
"Wannan lallen naki ya yi kyau sosai,"
Kai da jin muryar shi da yanda hannun shi ke rawa ka san shima sabon shiga ne,gaba d'aya sai hannuwan mu suka hau rawa a tare...................
........Da misalin qarfe hud'u na asuba Yah Maheer ya fita ya had'a min ruwan wanka, gida ne ba irin gidajen zamani ba, dan haka a bokiti ya saka ruwan wankan sannan ya cika min babbar buta da ruwa me dumi, da kan shi ya had'a risho a daren ya kunna ruwan zafin, sannan ya kai min,fuska ta shab'e shab'e da hawaye na fita ina hararar shi a duhu, na jima a bayin ban fito ba ina mamakin abubuwan da suka faru a wannan dare, haka na gama wankan da ya sake koya min kafin na fito daga d'aki, na bar masa butar da bokin a cewa ta ya d'auke ai dama shi ya kai su.
A bakin qofar band'akin na gan shi kawai se na yi saurin rab'e shi na shige ciki, bokitin ya shiga ya dakko da butar ya had'a nashi ya yi wankan ya koma d'aki , ina tsaye ina mamakin to da ya d'auke bedsheet d'in wa zai saka wani? Dan ni dai ba zan saka wani ba, ba abinda ya min zafi da abinda ya b'ata yanzu, tinda dama shi haka yake ake ganin shi shiru shiru, murgud'a baki na yi na zauna a bakin gadon, kamar me rad'a na ji ya ce,
"Na ga me ki ka yi, ki ka sake sai na yi maganin bakin nan naki"
Maida labb'ana na yi cikin baki na, ina qunquni a zuciya ta, dan ban bari kalma ko sauti d'aya ya fita fili ba, murmushi na ga ya yi ya ja sallaya ya shimfid'a har guda biyu, kamar yanda muka yi da za mu yi nafila.
Tada sallah ya yi, ya hau nafila, bai tsaya ba se da aka fara kiraye kirayen sallah, sannan ya juyo ya ganni zaune ina qudundune jiki na sakamakon wani irin sanyi da nake ji, gashi ba lokaci ne na sanyi ba balle a ce, lokaci ne na zafi, dan haka cikin sauri sai ya miqe ya zo inda nake, ya dafa goshi na, ya ji zafi zauuu, da sauri ya zube guiwowin shi a gaba na ya na sake duba jikin nawa, ni kuma ganin haka kawai se na fashe da kukan da ban yi ba a dazun, saboda bana son jawo mana kunnen maqota duba da irin ginin da muke ciki, a sannan ne na ware murya tare da baje baki ina kuka tin daga qasan raina har labb'ana.
Hankalin shi ya yi mugun tashi ya hau rarrashi na, ni kuma kamar zugani ake, shiruuu ya yi ya na bin kiran sallahn da ya ji ana ta kira a wasu masallatan,dan haka cikin muryar shi mai sauqin sauti ya ce,
"Young lady ki yi hakuri kin ji? Dan Allah taso mu yi sallah in gari ya d'an waye zan siyo maki magani, ko ki na so na kai ki chemist a maki allura?"
Da sauri na girgiza kai alamar Ah ah,
"Ok to ya isa kukan haka, zazzab'in zai qaru ai, taho nan mu yi sallah ko zaki sake alwala?"
Girgiza kai na sake yi alamar Ah ah, ya na ganin haka kawai se ya miqe ya shiga gaba ya tada sallah, ina tsaye ina jin kamar qafafu na ba za su d'auke ni ba saboda zazzab'in da nake ji, amma a haka na daure muka yi sallah.
Mu na idarwa ya d'akko qur'anai na da aka jera min su saman mirror ya miqo min d'aya ya d'auki d'aya, sannan ya ce,
"Young lady ki yi hakuri gari na waye wa zan samo maki magani, ban san zaki zazzab'i haka ba da na siyo magani kafin na zo"
'Mugu kawai dama an ce masu shiru shiru mugaye ne to gashi na ga d'aya'
Ba tare da na amsa shi ba na hau bud'e qur'anin na je bangon fateeha da baqara, na buga a'uziyya ta da basmala na hau karatu, gane cewa ina fushi da shi ne ya sanya shi bina a karatun, muka yi ta yi har sai da na ji zazzabin jiki na na sauka da kan shi, sannan haushin shi da nake ji ya na tafiya a hankali ina bashi uzirin be aikata laifi ba, hakan ba haramun bane, amma mamakin shi na nan daram a zuciya ta.
A hankali muka kammala suratul baqara, sannan muka rufe qur'anan mu muka yi addu'o'i har da azkar d'in safe, kafin mu kammala addu'ar rana ta hudo ta fito kusan har in ce ta kwalle ma, gaishe shi na yi ya amsa cike da nishad'i da walwala da annurin da ban taba gani fuskar shi ba, tashi ya yi ya dakko mug ya had'a min tea me kauri, sannan ya saka Lipton yellow a nashi mug ya saka sugar ya miqon nawa ya d'auki nashi.
Muna tsaka da sha na ji sallamar mace a qofar d'akin namu, juyawa na yi na kalle shi da alamun tambaya a saman fuska ta, shima nuna min ya yi be san wace ba amma na duba na gani mana, haka kuwa aka yi a hankali na bud'e qofar, tsaye na gan ta a bakin qofar ta kafe ni da ido kamar me son ta gano wani abu a tattare da ni........
Makaranta a yi hakuri da wannan...yanzu inshaa Allah za ku samu MAHREEN yanzu a WhatsApp sakamakon kula da na yi wasu ba sa wattpad kuma ana tare ana jin nauyin juna, dan haka inshaa Allah daga nan har na gama za a dinga samu a WhatsApp.
Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love π all.
π
MAHREEN π
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 9
Hannun ta da ta ke miqo min na bi da kallo, da sauri na riqe plate din da ta miqo min,idanun ta na qare min kallo fuskar ta d'auke da murmushi, nima murmushin na mayar mata ta ce,
"Ina kwana amarya?"
"Lafiya qlou alhamdulillah,"
"Masha Allahu, ga wannan ba yawa ku tab'a,"
"Thank you so much, this is more than enough, thank you"
"Ba komai,"
Juyawa ta yi zata koma d'akin ta, na bi bayan ta da kallo, Maimuna mace me mai jiki mai kyau masha Allah, bata da tsayi sannan bata da qiba, mazaunan da take da shi ne suka qarawa surar ta kyau, d'aki na na koma riqe da plate d'in a hannu na, bud'e wa na yi sai na ga indomie ce da kwai da dankalin turawa a gefe.
Ajiye wa na yi a qasa na masa bismillah akan ya sakko mu ci dan ni bana wasa da ciki na musamman in na ga abinda nake so, halin da nake ciki be sani jin ba zan ci abincin ba, kallon plate d'in Yah Maheer ya yi sannan ya ce,
"Ki ci kawai zan ci cincin da dubulan kar ki damu,"
Qoqarin tilasta masa nake ya ci sai ya kalle ni ya ce,
"Kar ki damu young lady i am not hungry, zan fita anjima sai in kawo maki kayan miya ki yi mana girkin rana, tinda kin ga ko mutanen kano ma basu tafi ba zasu sake dawowa, be kamata ace su zo ba abinci ba ko?"
"Hakane, Allah ya kaimu,"
Loma d'aya na kai baki na ina taunawa, dad'in abincin ya sanya ni lumshe ido, a duniya ina masifar son duk.wani abinci da aka sanya wa farin maggi shine dalilin da ya sa yana wahala in ci abincin da aka sanya wa farin maggi ban gane ba,mu gidan mu ba a cin farin maggi,dan haka nake matuqar qaunar cin shi, lokuta da dama abinci ko ba dad'i indai an saka farin maggi bana jin haushin cin shi ko waye ya dafa kuwa.
Hamdala na yi a qasan raina da Yah Maheer be ci ba, haka kawai na zo na yi girki ya ji be kai wannan dad'i ba?
Ina gama ci na miqe na tattare komai na gyara na share, sannan na kai masa ruwa a buta waje saboda zai yi sallar dhuha (walaha) ya na fita na dakko bedsheet d'ina da ya yaye a jiyan na bud'e qofa kamar mara gaskiya ina leqe, na shige kitchen d'ina na kama inda duk na ga be min ba na wanke, na yi masa muguwar matsa na yarfe, sannan na koma cikin d'akin da sauri na sake maida zanin gadon, ko da ya shigo ya ga zanin gadon har zai yi magana sai ya yi shiru ya na ta kallon shi, ni kuma na juya ina gyaran wardrobe na qarya dan komai a gyare yake, ban juyo ba se da na ji ya tada sallah sannan na yi wufff na bar d'akin na koma parlour na kwanta a kujera ta man rest da nake mugun son irin ta, se gashi an yi min ba tare da an san ma zab'i na ba,wannan karon se na ji bata burge ni ba wanda da a da ne na gan ta aka ce wannan taki ce ba qaramin tsallen murna zan yi ba da farin ciki.
Numfashi nake ta fitarwa saboda sabon zazzab'in da ya ke son sake rufe ni, ina kwance na ji sallamar Yah Maheer ya fito cikin shirin fita, ya ce min bari ya je ya dawo, in 'yan kano sun zo na sanar da shi ya dawo su yi sallama zai je ya samu Yaya Babba a samo motar da za su koma har kano a cikin ta, na ce masa to.
Qasan raina kuwa har na gama yanke hukuncin binsu in koma gidan mu na fasa zaman anan ni,bani da lafiya ba zan zauna ba, ni dai kawai kome za a yi sai an koma da ni a wannan ranar.
Ko minti biyar be yi ba da fita sai ga 'yan uwa na sun zo inda daga nan ba inda za suje za a wuce da su kano, cikin murna na je na tarbe su ina ta farin ciki, na shiga d'aki kamar wadda zata d'akko wani abu, na d'auki akwati na madaidaici da aka d'ora a saman wardrobe na zuba kaya na a ciki sannan na zuge, na ajiye a gefe, na dauki ledar kazar da ban ci ba jiya da sauran lemo na fita da shi,sannan na koma na deb'i kayan gara da yawa na sake fita da shi, Goggonaye na ne wato qannen babana ne su uku suka zo daga baya kowaccen su ta ci kwalliya, Goggo Bilki, Aunty Jummai, Aunty Ameenah (matar qanin babana)da Aunty Iyannan, can kitchen d'ina kuma Yayar mu ce da sauran qannen babana su Shafa, ina zaune wajen su Yayar mu ta ce,
"Ki tashi ki je wajen aunties din ki mana ki gaishe su,"
Ta kula da yanda gaba d'aya nake jin jiki dan haka da ido kawai take bi na har na fita parlour na tadda su su na zaune a kujerun da suka cika parlourn, da ido suke bina bayan na gaishe su, ina fidda nishi kad'an kad'an, Aunty Jummai ce ta ce,
"Wannan nishin da ki ke yi kamar kin yi gudu fa?"
Ji na yi ido na ya kawo ruwa, saboda ni kad'ai na san ya nake ji a wannan lokacin, gaba d'aya jiki na ciwo yake, cikin qoqarin daidaita murya ta na ce mata,
"Banda lafiya ne, zazzab'i nake ji"
Kallon junan su suka yi, na ga sun yi murmushi, can se Aunty Bilki ta ce,
"Ai ya kamata ki sha magani, amma ki ta nishi haka se kace wadda tai gudu,ina shi Maheer d'in?"
"Na sha magani....ya fita wajen Yaya Babba,amma ya ce na kira shi in kun zo"
"To shikenan ki je ki kira shi"
Da kyar na miqe na fara takawa zan fita se na ji suna magana qasa qasa, (ehe bana mantawa na ji ku saraiπ) gaba na yi abu na na dakko waya ta na fad'a masa zuwan su, ya sanar da ni cewar sun had'u da Yaya babba gasu ma tare a waje, na kashe wayata.
Ina komawa wajen su Yayata na zauna muna hira can muka jiyo muryar Yaya Babba da Yah Maheer sun shigo, ina jin muryar Yayana na fita da saurin da zan iya na je gare shi ya rungume ni, se hawaye ya balle min Yah Maheer kuwa ciki ya shiga su gaisa da su Goggo da Yayarmu, cikin kukan shagwab'a na ce wa yayan mu,
"Yayah zan bi ku dan Allah mu koma bana son zama anan"
"Subhanallahi ke da aka kawo ki gidan mijin ki gidan da ake fatan mutuwa ce zata raba ku amma kice wai zaki bi mu? Ai ba haka ake yi ba,"
"Ni dai na fasa zama zan bi ku ni na ma had'a kaya na"
"Tirqashi....to kin ga ki yi hakuri ba haka ake yi ba, duk macen da ki ka ga an mata aure an kai ta gidan miji ba a fatan abinda zai raba ta da gidan daga mutuwa sai zuwa unguwa, dan haka ki yi hakuri Allah ya miki albarka ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka, amma saboda hankalin ki ya kwanta ni ina nan a gari zan kai sati d'aya Kafin na koma zan sake zuwa wajen ki, in baki sauya ra'ayin ki ba sai mu koma tare kin ji?"
Hakan da ya fad'a ne ya sanyaya raina, sai na ji hawayena sun rage gudu, kafin ma ya qarasa shiga ciki an fara danna masu horn akan su fita a wuce, fita suka dinga yi muna sallama a bakin hanya, ganin Yayar mu zata fita se na rungume ta ina kuka, cikin dakewa ta ce,
"Ki yi hakuri Mahreen ke da ga ki ga Addah Ummun ki da Addah Firdausn ki? Ki zaman ki lafiya da maqociyar ki me kirki kin ji Allah ya miki albarka"
Ko ameen d'in ma na kasa furtawa, haka qannen babana suma suka wuce dik aka barni ina tsaye a jikin qofar gidan ina hango su a mota, na jima a wajen ban koma ciki ba ina ta kuka, ina juya wa zan koma ciki muka yi ido hud'u da Yah Maheer da ke tsaye ya na kallo na shima cikin tausayawa, hanya ya bani na wuce ina jin matsanancin haushin raba ni da 'yan uwa na da gidammu da ya yi aka kawo ni wata uwa duniya.
D'aki na shige na kwanta ina numfashin zazzab'in da ya sake rufe ni rufff, magani ya sake bani na karb'a da kyar, ina nan zaune ya na ta jera min sannu se ga qanin shi da abokan shi sun zo, shi yake bi wa Yah Maheer d'in, fita ya yi wajen su Palrour suka hau gaisawa, cike da jarumta na fito nima sanye da hijabi, da plate din da na zuba kayan gara akai na je muka gaisa na ajiye masu plate d'in sannan na miqa masu ruwan shan da ke a cikin jug tin wanda na kaiwa su Goggo na.
Godiya suka min na zauna a gefe suna hira ina yaqe,dan bana so zuwan farko su ga ban girmama su ba, se da na ji sun fara personal hirar gida na tashi na basu waje na koma d'aki na kwanta.
Da daren ranar ma Addah ce ta bamu abinci bayan na cika leda da kayan gara na miqa mata, sannan na deb'i mafitai da plates da qananan cups da aka raba a biki da yayar mu ta min dabarar zuwa da su ta ce ina ba wa baqi in sun zo, dikkan su an saka sticker na auren mu jiki,ta yi min godiya sosai sannan na fad'a mata suna na ta fad'an nata ta ce amma an fi kiran ta da Addah.
********************************
Cikin kwanaki uku na samu wata iriyar kulawa da lele da shagwab'awa wajen Yah Maheer ta yanda da ana tauna ruwa na tabbata da zai tauna min tsabar yanda yake lele na,a sannan kuma na gano Yaya Babba wayo ya yi min ya gudu ba sake dawowa ze yi ba, a lokacin ne nima na ga matuqar wautata da shirme na, dama ta yaya iyaye na za su b'ata lokacin su su aurar da ni a kawo ni sannan a maida ni kamar auren 'yar tsana?
Tini na fawwala wa Allah lamura na na saki zuciya ta na hau bautar aure, a rana ta hud'u Yah Maheer ya aiki qanin shi mai suna Kabeer ya yo mana siyayya, inda ya had'o min da farin maggi, murna a waje na kamar na taka rawa, irin gani yau a gidana ni kad'ai zan amfani da farin Maggi da Baba ke hanawa.
Yah Maheer kuwa d'an gidan Baba ne, ko a hira ya ji Baba baya son abu, har yanzu da muke tare shekara da shekaru to fa ba za a yi wannan abun ba,dan haka ko da ya kyalla ido ya ga Ajino Moto sai ya d'auke shi cikin kayan ya ce banda wannan kar a sake siyowa da shi, duk naci da magiya da shagwab'a ta be sa ya bar min ba, qarshe sai na karba na ce to ya bani na ba wa Maimunah tinda su suna amfani da shi.
Wannan shine dalilin da ya sa ya nesanta da cin abincin da suka kawo, ni kuma se ya zame mani blessing, dan kuwa Maimuna gwana ce wajen iya girki ta yanda ko ba ajino in ta yi girki ya na masifar dad'i,balle kuma ta na saka mutumi na.
Tin ina amarya Yah Maheer da abokan shi da ke zuwa gaishe mu suke yabo da tsananin son girki na, har kyautar kud'i sukan min ko kuma yabo da addu'a.
Zuwan Alhaji Younusa na farko gidan mu na kai masa abinci jellop rice ya so ya qi ci saboda a qoshe ya zo, amma a cewar shi kawai yanda ya ga shinkafar ya yi kyau a plate da qamshin ne ya yi inviting din shi har ya ci, da ya ci kuwa sai da ya hau zuba santi ya na comment akai kamar irin a makarantar nuna bajintar girke girke.
"A gaskiya Maheer ka yi dacen matar aure, gata saliha, gata me kyau, gata me addini, 'yar gidan mutunci sannan ta iya girki, ka san a dafadikan shinkafa ake gane mace ta iya girki ko bata iya ba, ta dafa ta ta yi kyau da dad'i gishiri be yawa ba, maggi be yawa ba, kuma ba a zabga mata mai ko yaji ba, sannan gashi ta dahu daidai bata yi cikin shege ba,(tsimburum-burum) gaskiya dole na ce maki job well done amarya, Allah ya yi albarka"
Wani irin dad'i da farin ciki na dinga ji, kawai se na tuna Babana yanda yake yawan yabon girki na addu'a na yi masa cikin raina sannan na miqe na shige d'aki na bar su tare, kafin na shiga na ji sun yi magana qasa qasa sun tafa an fashe da dariya.
A raina na ce,
'Oho ai dama Yah Maheer d'in nan da ya ga abokan shi sai an yi gulma ta an tafa ake jin dad'i Allah ya shirye ku'
Na murgud'a d'an baki na sannan na yi murmushi na wuce ciki na rufe qofa ta.
Wata na d'aya a gidan aure na ga baqi kala-kala, kar ku manta Bauchi shine inda dangin mahaifi na suke ta b'angaren uba,dan haka ta ko ina ganin baqi nake, b'angare daya kuma muna waya da mutanen gida akai akai, da yayu na da ke cikin garin.
Yau ma kamar kullum ina kwance bayan na kammala aiki na, sanye nake
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 30