Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi/ita, haka abun yake wajen iyayen mu mata, zama kowa ya San ba a rasa samun saba'ni to tabbas muma a gidan mu akwai irin saba'nin da ake samu tsakanin harshen da haqori, in Kuma an samu cikin iKon Allah komai ya na daidaituwa ba tare da an samu rarrabuwar Kai ba. Saboda tsananin yanda yake tsaida adalci a cikin iyalan shi kowa abin so ne a wajen shi, dan haka ni MAHREEN Ina bada wannan labarin ne da kwatankwacin soyayyar da Baba da Mama suka nuna min. Tin Ina qarama ta iyaye na ke fama da d'awainiya ta na kasance an haife ni da nakasa ta gurgantaka, inda qafafuna suke da matsala ta yanda ba na iya tafiya d'aya biyu ba tare da na fad'i ba, wannan abu ya d'aga hankalin iyaye na a wannan lokacin da duk Wani masoyin su, iyaye na basu huta ba har sai da suka yi shige da fice har aka yi min aiki a qafafu na dika biyun a nan garin kano, Dr. Shaban shine sunan likitan da ya yi min aiki mutumin qasar India,na sha Jin labari a wajen iyaye na yanda likitan da matar shi ke nuna soyayyar su a gare ni da yaba kyau na a Koda yaushe. Ba a bar 'yan uwa na a baya ba wajen dawainiya da ni musamman babbar yayar mu, a haka har aka gama jinya ta na samu lafiya, nake takawa kamar kowanne d'a Mai cikakkiyar lafiya. Na taso yarinya Mai kazar kazar da shiga ran mutane duk Wanda ya ganni sai ya ji dama wannan 'yata ce ko qanwa ta ko Kuma dai ya zamana Ina tare da su, saboda chubby yaro na da ban sha'awa a ko Ina. Hakan ne ya yi sanadiyyar zama na a gidan qanwar Babana da nake kira da Goggo, Goggo na ta na so na hakan ne ya sa ta roqi Baba da ya bata ni ta riqe ni,duba da cewa Allah bai azurta ta da haihuwa ba a lokacin nan, dan haka ba tare da Wani tunani ba ya shawarci mama ta tattara min kaya na aka Maida ni gidan Goggo na da zama, mijin Goggo na Alhaji Nafi'u mutumin kirki ne Wanda ke son Yara Allah bai nufa zai samu nashi na kan shi ba, Goggo na na da kishiya wadda muke Kira da Baaba, Allah ya yi masa rufin asiri a wannan lokacin ya na riqon Yara uku a gaban shi kafin na je na zama ta hud'u, duk Wani Jin dad'in duniya daidai arziqin shi, Alhaji ya na wadata mu da duk abinda muke so, musamman ni da nake Qarama a gidan, na taso wajen Goggo na cikin kulawa, kishiyar ta da Kuma mijin ta Suna so na matuqa, inda ta bangaren Goggona kuwa kwata-kwata bana Jin dad'in zama da ita, a cikin zuciyar ta na tabbata akwai soyayya ta, amma a halayen ta da ayyukan ta babu wannan soyayyar, kowa ya shaida cewa ni yarinya ce ba mai qiriniya ko rashin ji ba, bana manta wa saboda haka kaka ta Hajiya Innah ke Kira na da Salihar baiwa,amma dik da haka ban samu tarairayar Goggona yanda ya Kamata ba, duk da cewa ba a rasa wasu lokutan da take kula da ni amma rashin kulawar shi ya fi yawa,ana haka muka samu matsala mai girma har ta Kai ga ta karya min hannu na na dama, mahaifi na ya yi kawaici dik da ran shi ya yi masifar b'aci, ya bar ni ta ci gaba da riqo na be karb'e ni ba, kwatsam da Allah ya kawo rabuwar mu da kan ta ta d'auke ni ta Maida ni gidan mu, wajen mahaifiya ta wadda ta cire rai da yakice soyayyar da take min duba da cewa bana gaban ta, ana Maida ni gidan kuwa ta sa hannu bibbiyu ta rungume ni na ci gaba da zama cikin 'yan uwa na cikin farin ciki da so da qauna. Ba a jima ba Kaka ta ta wajen Uwa wadda muke Kira da Hajiya Innah (Allah ya miki rahama ya sa kina cikin ni'imar shi) ta d'auki riqo na itama, na taso a wajen ta cikin tsananin gata da kulawa, bata so ta ga b'acin raina ko kad'an, gatan da ta bani bai sa tarbiyya ta ta gurb'ata ba, domin ita macece Mai kula da tarbiyyar yaran unguwa ma balle nata, zama na da Hajiya Innah zama ne da na yi shi Mai aminci har na gama makarantar primary ta islamiyya da mahaifin mu ke Saka mu wadda take a Fagge Mai Suna Simarul qur'an, a lokacin da iyaye na da kaka ta suka ga Ina ta girma bana zuwa makarantar boko sai suka yanke shawarar na koma gidan mu da zama inda za a Sanya ni a makarantar bokon da 'yan uwa na ke zuwa, wannan shi ne dalilin dawowa ta gidan mu da zama, kafin a Sanya ni makaranta sai Allah ya kawo wa babbar yayar mu miji ta yi aure a Lagos muka sha bikin Addah Babba suka wuce ita da mijin ta, bayan an kwana biyu da yin auren ne ta roqi mahaifin mu da ya bata ni, Babu bata lokaci kuwa Baba ya bata ni na koma wajen ta da zama. Zama na da Addah Babba zama ne Mai 'yanci ba takura, ba musgunawa, zama ne Mai Cike da so da qauna, domin soyayyar uwa ta nuna min sannan ta had'a min da soyayyar Yaya da qanwar ta,mijin ta mutumin kirki ne Wanda ya dauke ni kamar 'yar da ya haifa, na taso cikin gata matuqa, Ina da wata bakwai a wajen Addah Babba, Baba ya kawo mana ziyara,ya ji su na planning Sanya ni a makaranta a Lagos,ya ga yanda Yara ke Saka qananan skirt a aske Kai dik da ni aski ba Wani sabon abu bane a waje na tinda ya zamana ni da kaina ko da yayu na in Ina gida muke zuwa wajen masu aski a aske min shi tasss (Kai na baya son kitso quraje yake shi ne dalilin yin aski na) Dan haka ba sabon abu bane amma na dinga yawo tsirara tsirara inaaa ba zai amince ba....shine abinda Baba bai yarda da shi ba, bayan ya koma an d'an kwana biyu ban San ya aka yi ba, Addah Babba na kuka ta had'a ni da wasu amintattun mutanen ta aka dawo da ni gidan mu. Tinda na dawo se na dinga kewar ta Ina Jin kamar na koma, gashi yawan ganin Innata na zuwa ya qara tada min da tsumin zama na da ita, Ina matuqar son Innata ta yanda ba zan iya kwatanta wa ba, zama na shiru a ko da yaushe ba makaranta ya sa iyaye na suka yanke shawarar Sanya ni makarantar boko, aka kuwa Sanya ni aji d'aya da qanne na guda biyu mata kasancewar ni ban fara bokon da wuri ba dole na koma baya kafin na samu na iya wasu abubuwa mahimmai. Dawowa ta gidan mu sai ya zamana ba wata cikakkiyar shaquwa sosai tsakani na da Mahaifiya ta, amma hakan ba Yana nufin bata so na ko Kuma ta na fifita sauran 'yan uwa na a Kai na ba, ni ta b'angare na sai nake ji na kamar ba a nan ya Kamata in zauna ba, gidan mu ya na can inda kaka ta, dan na fi sabawa da ita a duk Wanda na zauna da su, nan gidan mu kuwa Jin shi nake kamar riqo na ake, wajen kaka ta Hajiya Innah shi ne gidan mu, wannan dalilin ne ya Sanya a Koda yaushe na samu hutu ko Kuma a weekends nake zuwa wajen ta, har aka Sanya ni islamiyyar da ke unguwar mu dan ci gaba da karatu na na islamiyyah wadda muke zuwa da weekend sai ya zamana bani da Wani hutu daga boko sai islamiyya,a wannan loacin ne Kuma zuwa na wajen Kakata ya ragu, sai dai ita in ta samu lokaci kamar yanda ta Saba ta na zuwa, duk sanda ta zo ji nake kamar na bi ta, a haka har na Saba da zaman gidan mu, na gane nan ne iyaye na suke da 'yan uwa na, sai na hakura da kwalafucin gidan Innah ta, hakan Kuma be rage son da nake mata ba ko kad'an a zuciya ta. A hankali Ina girma mahaifina tsoron girman jiki na na kama shi, saboda shi ma'aikacin lafiya ne ya San illolin da hakan zai iya haifar min a rayuwa ta anan gaba, musamman da yake Ina da lalurar ciwon qafa, Baba ya tsaya tsayin daka dan ganin na rame, bana mantawa tun Ina da shekara sha d'aya na fara period girman jiki na ya bayyana kamar wadda ke da shekaru sha uku ko sha hud'u, tin a lokacin baba ya dage da nema min maganin slimming da ya ji magani an ce ya na Saka rama ya duba ingancin shi to fa zai siyo min na hau sha,Wani ya sani zawo, Wani in na sha haka zan zauna jiya Iyau ba ya min komai. Watarana qanin baba ya fita qasar waje ya samo Wani magani na slimming ya kawo min har gida, saboda ya San yanda d'an uwan shi ya damu da maganar qiba ta, Ina zaune cikin 'yan uwa na aka kira ni na je, Baba ya miqa min tea din ya ce, "To 'yar baba gashi a je ayi ta sha a rage wannan qibar, tashi ki tsaya na gani," Amsar kwalin tea din na yi sannan na tsaya a tsaye ya kalli qafafu na da ke da matsala, ya ce, "Miqewa nake so ki yi tsaye sosai in gani," Na miqe Iya iyawa ta, sai na ga yanayin fuskar mahaifi na ta sauya, saboda har a lokacin in na tsaya se qafafu na su kwanta ba su tsayawa tsaye sambal yanda ya ke so, qanin shi ya ce min na je na had'a tea na fara sha, na fita Ina murna zan rage qiba. Kafin in fita na ji Suna tattaunawa akan qafata da Baba, qanin shi na kwantar masa da hankali akan inshaa Allahu ba abinda zai faru sai alkhairi. Haka na ci gaba da rayuwa cikin yawan laulayin ciwo, musamman ciwon qafa da ciwon ciki, in suka tashi min ko tafiya da kyar na ke yin ta, hakan na daga dalilin da ya sa iyaye na da 'yan uwa na ke tausaya min, Yayana kuwa da nake bi ko makaranta mu ka je na kasa takawa to fa goya ni zai yi duk nisan dake tsakanin bakin titi da gidan mu baya gani sai mun zo gida zai dire ni, gani da shegen nauyi kamar buhun kwaki. Ina da shekara sha hud'u dik wata sura ta budurwar mace da ke ji da cikar 'yammatanci ta bayyana a gare ni, samari kuwa sai dai in ban fita ba. Ana haka Babana da Babban abokin shi suka yi shawarar qulla zumunci a tsakanin su, inda abokin Baba ya nema wa babban d'an shi aure na,babu b'ata lokaci Baba ya amince da hakan domin zumuncin su ya yi kwari. Lokacin da iyaye na suka Sanar da ni, ba zan iya tantance halin da nake ciki ba babu Wani isasshen wayon sanin ma menene aure a tattare da ni, sannan babu wayon sanin wa ya Kamata in so waye be Kamata na so ba, na dai San kawai mutane musamman maza duk inda na shiga su na nuna min soyayya, su na nuna su na son aure na, dad'in dad'awa ni ba zan ce ga fuskar shi ba a daidai wannan lokaci, misali da bayanin duniya bai sa na tuna shi ba, makarantar islamiyya d'aya muke da shi amma gaba yake da ni sosai a aji, ba Kuma zan iya nuna fuskar shi ba in ce ga yanda yake a wancan lokacin. Magana fa ta tsayu cewar d'an abokin Baba zan aura, manema na ta kunno Kai har abun na bawa iyaye na mamaki dika-dika nawa nake? Ni kaina Ina mamakin yanda masu zuwa neman aure na ke tururuwa ba manya ba ba Yara ba ba tsofaffin ba domin Wani ma ya haife ni,hakan na daga cikin dalilin da ya sa a duniya bana son na sa qafa na fita sai dole Kuma abun ya bini har yanzu da na mallaki hankalin kaina bana son fita sai ta zama dolen dole a gare ni, in fita ta wuce makaranta to b'ata min rai take, saboda Ina takaicin yanda zan ga wasu sun haife ni ma amma za su tsaida ni da sunan su na so na. Ana haka watarana Baba ya dawo daga Jigawa can inda yake aiki, da rana Ina zaune a qasa inda na aje masa jakar shi da na karb'o a hannun shi,mama Kuma na zaune saman gado a bangaren shi na dama, Baba ya ce, "Darling kin ji wata magana wajen Alhaji Idris kuwa, wai a masa lamuni kar a Yi auren yaran nan da wuri a jinkirta har sai Musaddiq ya kammala PHD din shi a can qasar da ya tafi? Gaskiya mun tattauna da iyayen ta (qannen shi kenan yake nufi) hakan ba zai yuwu ba, ki duba ki ga yarinyar nan girman jiki ne da ita ba zan aje ta a gaba na har zuwa tsahon wannan shekarun ba,na bashi hakuri gaskiya na ce Masa in dai ta samu miji zan aurar da ita, ko ya ki ka Gani?" Ban Jira amsar da mama zata bashi ba na zame jiki na cikin yaqe na fad'a toilet, durqusawa na yi na yi shiru Ina sauraron su, ban tab'a Jin Ina son Musaddiq ba a rayuwa ta, amma sau d'aya da na gan shi lokacin da muka je gidan su saukar qannen shi, sai na ji zan iya zama da shi a matsayin miji na, na riga na Saba da Jin Kalmar shi zan aura- shi zan aura kusan tsahon shekara d'aya, na tabbata a wannan lokacin kukan sabon da na yi da Jin cewa shi zai zama miji na nake Yi, shiru na ji iyaye na sun yi daga tattaunawar da suke yi, Wanda ban San dalilin yin shirun nasu ba, bayan na gama kuka na na miqe na cire kaya na na hau wanka, Ina gamawa na fito,Ina Jin saukar idanun su a jiki na, amma ban juya Dan kallon d'aya daga cikin su ba. Tinda ga wannan lokacin ban sake Sanya shi a raina ba, ban sake tunanin shi ba, na manta da shafin rayuwar shi kamar an Yi ruwa an d'auke. Ana cikin wannan yanayin Yah Maheer da ya samu admission a makarantar BUK ya kunno kai cikin rayuwa ta,mahaifin shi da mahaifi na 'yan uwa ne, Mahaifin Yah Maheer shi ne gaba da mahaifi na. Yah Maheer ya na da zubin fulani na asali, ya na da kyau daidai misali, sannan ya na da nutsuwa da Kamala, da fari na zaci d'an uwan Mama ne shi saboda yanda ta d'auke shi kamar nata,sai daga baya na gane cewa dangin Baba ne shi,in suka zauna su na hira da Mama sai mutum ya rantse da d'an cikin ta take hira, a duk sanda zai shigo gidan mu daga makaranta ni ce mutum na farko da yake fara Gani,lokuta da dama ya na gani na ne cikin yanayi na na shiririta ko shagwab'a ko aikin gida, ba tare da na sani ba ashe tin gani na farko da ya min ya kamu da so na,Wanda a tarihin rayuwar shi kafff bai tab'a son wata 'ya mace ba duk kuwa da kalar matan da ke cewa su na son shi, wasu har hotuna suke kaiwa gidan qanwar shi dan ta bashi, wasu har shagon shi suke zuwa su bayyana soyayyar su amma bai tab'a kula kowa ba a cikin su. A cewar shi daga sanda ya d'ora Ido akai na ya ji ya na so na daga ranar ya fara Sanya ni cikin addu'o'in shi na kowacce sallar farillah da nafila, ba shi da burin da ya wuce Allah ya bashi ni a matsayin matar da zai aura,hakan ne ya sa ya yi shiru be Sanar da kowa ba, a lokacin da yake ta nuqu-nuqu ya na ganin Babu Wanda ya gane soyayyar da yake min, a lokacin Baba ya harbo jirgin shi, wannan shi ne dalilin da ya sa duk Wanda na aika da sunan ya na neman aure na sai Baba ya ce ya min miji, lokuta da dama na kan yi tinani na ce, 'Wanene mijin nan ne bayan an fasa had'in aure na da Musaddiq? A Ina yake baba be tab'a nuna min shi ba?' Kamar kullum hakura nake da tunani domin bana samun amsar tambayoyi na, Yah Maheer na nan na ta nuqu-nuqu da soyayya ta a ran shi, samari na ta kawo min hari gabas da yamma kudu da arewa, ni Kuma ta b'angare na bani da wata damuwa da ta wuce karatu na da aikace aikacen gida da wasanni da hira da 'yan uwa na, tinda mu gidan mu ba a zuwa wai a sallama a ce an zo zance wajen wance Sam-sam yayun mu ma sai da Wanda aka zab'a masu da shi suke tsayawa kawai, wasu ma ban San sun je ba sai daga baya zan ji labari. Bana manta wata rana Addah Ummu ta zo da labarin Wani abokin karatun ta ya ga hoto na a saman wayar ta ya yaba ya na so zai aure ni, Babu bata lokaci ta zo gida ta Sanar, bawan Allahn nan har mun fara magana da shi ta aure har gidan mu ya zo an bamu dama mu yi hira da shi, sama ko qasa maganar shi ta tashi, be sake dawowa ba (Ya ji addu'ar bayin Allah...lols) Hakan ya yi daidai da dawowar Yah Maheer daga bautar qasa da daddare shi da abokin shi, Ina parlourn waje Ina guga, shiga ta ce dai a jiki na as usual ta qananan kaya, daga ni sai wata farar vest da skirt Wanda iyakar shi qwauri na, kwankwasa qofar su ne ya sa na tashi Dan zuwa bud'e musu qofa, hakan ya yi daidai da shigar Mama parlourn ta qofar da ke kusa da gareji dan ta ji ni shiru ban koma cikin gida ba, ta na zuwa ta wurga min mayafi, ni Kuma har na murd'a qofa na bud'e wa su Yah Maheer, bana tab'a manta mintsinin da ta gasa min a hannu na saboda ban yafa mayafin da kyau ba,(I swear bana mantawa)har a lokacin ban gama rufe jiki na ba,da sauri na ja mayafin na rufe jiki na, shi kuwa Yah Maheer tinda ya kula da kayan da ke jiki na sai ya babbake qofa baya so abokin shi ya shigo ya ganni haka, Mama ce ta umarce ni da na je na kawo musu ruwa, sannan ta min Umarnin Sanya hijabi kafin na dawo. Ina tafe Ina sosa inda ta manna min mintsini na je na sa hijabi na d'ebo musu ruwan sha, ko da na koma abokin shi na can d'akin samarin gidan Yah Maheer Kuma da Mama su na hira ya na zaune kusa da inda nake guga. Mama ce ta tashi ta shiga ciki Dan sama musu abinda za su ci tinda dare ya yi bana mantawa qarfe sha biyu na dare ta kusa, tambayoyi ya dinga jifa na da su Ina guga, tambayoyin da suka kulle min Kai na kasa gane inda ya dosa.......... Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all. 💅 *MAHREEN* 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 4 Mama ce ta dawo hannun ta d'auke da robar da na dafa fried rice for the first time a rayuwa ta, sai dambu Shima ranar na tab'a yin shi, ko ci ban yi ba, dama na ajiye ne da safe na dumama na ci har na tafi da saura makaranta, bashi ta yi ta ce, "Maheer ga wannan ku tab'a ba Wani yawa ne da shi ba, in ta gama gugar ta dora maku ko taliya ne ku qara da shi,da ka sani tinda ku ka taso sai ka yi waya ka Sanar da zuwan ku a aje maku abinci na musamman, yanzu gashi ka zo da baqo gidan ku ba abinci" "Ahh Mama kar ki Wani damu, ai a qoshe ma muke amma zan Kai mana wannan d'in mu ci ba sai ta yi Wani abincin ba, muna godiya sosai Mama da kulawa, Allah ya Saka da alkhairi," Wani haushi ne ya kama ni har cikin raina ban ji dad'in basu abincin nan da Mama ta yi ba,kallon shi na yi ta qasan Ido na na ga ya na kallo na ya na Murmushi, daure fuska na yi na tura baki na gaba,ai ba wai burge ni ya yi ba dan ya ce kar na yi girki, dama Mama ta Saba in dai ya zo gidan nan daga makaranta haka zata dinga zaqulo abu ta na bashi, gamu a cikin gidan bamu San da Wani abun bama, watarana Kuma miya za ta sa na zauna na soya masa ko cin-cin,gashi ban Isa na Yi miyar yanda na ga dama ba sai ta sani a gaba ta ce, 'Ki bar miya ta soyu ta yi yashi-yashi saboda haka ne zai sa baza ta lalace ba, bankawa miya wuta ba shi ne girki ba, ki sa wuta kad'an ki sa hakuri da nutsuwa a girki sai ya Bada ma'anar da ake so' Ina tsaka da tinani na ji Mama na yi musu sai da safe, shi Kuma ya shige da kwanukan abincin d'akin samarin gidan mu da ba kowa ciki sai baqon shi da tinda su ka gaisa da mama ya koma d'akin, da damar yayu na sun tafi makaranta hakan ne ya sa d'akin ya zama ba kowa a ciki sai su. "Ke har yanzu baki gama gugar ba?" "Na gama Mama" na fad'a Ina tura baki, dan kuwa qiris ya rage na fara zubar da hawaye, ban yi shiru ba kuwa se da na mata magana akan abinci na da ta bawa d'an ta ba tare da an nemi izini na ba, Ina Saka Kai na a pillow zan kwanta cikin duhun da ya gauraye d'akin sakamakon kashe wutar lantarkin da muka yi na ce, "Mama ban fa ci abincin nan ba ko d'and'anawa ban yi ba, Kuma baki ga wahalar da na sha ba gidan Aunty Salamatu kafin na iya dafawa, gashi kin basu abincin dika" "MAHREEN abinda ka bayar shi ne naka, ki yi hakuri gobe zan baki indomie a cikin na makarantar su Sa'eed se ki dafa ki tafi da shi shikenan?" Ba haka na so ba Sam, dan ni na so na ci shinkafar da na dafa wadda ake wa laqabi da fried rice tinda ban tab'a dafa irin ta ba da kaina sai ranar. "Subhanallahi kin ga mun manta ko ruwan sha ba mu basu ba, dazu na ce ki kawo ruwa ki ka Kai a kofin silver nan gashi kafin ma mu tashi sun shanye shi, ki je ki d'ebi Wani ki Kai musu" "Mama tsoro nake ji," "Mu je zan tsaya a soro ki Kai musu" Haka kuwa aka yi, ko da na Kai musu ruwan sun cinye abincin tasss Suna zaune su na hira, Yah Maheer zaune yake daga shi sai gajeran wandon su irin na masu bautar qasa, Jin sallama ta ne ya sanya shi yafa farar rigar a kafad'ar shi, tin da na shiga idanun shi ke Kai na, kamar ba zai d'auke su ba,kwanukan na tattara na tambaye su ko akwai Wani abu da suke buqata? Da kan shi ya min alamar babu, kunyar yanda ya ke kallo na ta had'e baki na gumm waje guda, dan kuwa ban sake magana ba na fita na koma wajen Mama da ke tsaye a bakin qofar shiga gidan mu ta na Jira na, sai da ta sake yin addu'a sannan ta rufe gida muka shiga ciki. Ko da na kwanta na kasa cire tinanin kallon da Yah Maheer ya ke bi na da shi, kallo ne da ban tab'a ganin ya yi min irin shi ba sai watarana da ya shigo cikin gidan d'iban ruwa a bokiti na yi sauri na je na karb'a zan ja mashi daga rijiya, amma ya qi sakin bokitin ya kafe ni da kallo

Chapter 3 of 30