ai uwar gayyar ta ce su ce min uban su na koya musu karatun a gida, ka ga ba za su na ci gaba da zuwa ba ko? Allah ya kyauta"
Da jin haka kawai se ya ja bakin shi ya tsuke, dan kwana biyu ma ina mamakin yanda yake biye min muna maganar su, tunda shi kwata kwata baya son a na maganar duk wani wanda baya wajen, musamman maqota,se ya dinga fadin babu kyau, ko se na gama zuba magana se ya ce 'Allah ya kyauta'
Haka na qarasa ranar raina babu dad'i dan ko fita tsakar gida shan iska ban yi ba a ranar saboda in na fita zan iya confronting din Mama Ameerahn in ji me ya sa ta yi abin da ta yi? D'a ai duk na kowa ne ko? Menene ma'anar abinda ya faru?
Ban sake kula maganar koya musu karatu ba, abinci ma da na ga sun qara rage yawan yanda take zuba musu se na qara yawan wanda nake zuba musu, haka muka ci gaba da rayuwa yaran na son zuwa waje na watarana a hana su, watarana in suka saci jiki suka zo ta zane yaro.
************************
Yau na tashi da ciwon ciki sosai,duk da cewa kullum cikin shi nake amma na ranar ya fi na kullum yawa, ga jini ina zubar wa kusan sati uku be tsaya ba, gaba ɗaya bana jin daɗin jiki na, ni na saba yi mana wanki gaba ɗayan mu, in shanya in sun bushe in goge in aje wa kowa nashi in da ya dace, har yaran kan ce wa Suwaidatu.
"Ke kam kin ji daɗin ki babba da ke amma wanki ake miki, mu kuma kin ga da kanmu muke wanke wa Addah Ameerah ta shanya mana,"
Da na ji su sai na ce,
"Ai kuma dan Mommyn ku bata da lafiya ne, amma ai da ta na maku wanki, ko yanzun ma da ta ji sauqi za ta ci gaba da yi maku"
Murmushi na yi da na tuna hakan, yau kuwa yanda nake jin jiki na ba zan iya ba, fita qofar gida na yi na samo wasu almajirai manya manya, ɗaya sunan shi Anas,sauran biyun ban riqe sunayen su ba, wankin mu na kwaso na basu na haɗa da sabulu da ruwan wanki da komai da ya dace, sannan na koma parlour na kwanta.
Ba su gama wankin nan ba se azahar, Yah Maheer ya dawo daga makaranta ya gan su, se ya kwaso kayan shi da yake so ya bada ya basu ya biya su kuɗin wankin su suka tafi, sannan ya shigo inda nake, kwance ya ganni ina buɗe ido da kyar, sannu ya yi min sannan ya dakko qanqara a fridge ya miqo min, godiya na masa ya wuce daki dan sauya kayan jikin shi.
Ɗora qanqarar na yi a mara ta ko zan samu sauqin azabar da nake ji, se da ya yi wanka ya gama shirin zaman gida tsafff ya duba kitchen ya dakko abincin shi sannan ya taimaka min na zauna, abincin ya so ma ci sannan ya miqo min na ce na qoshi, dan ji na nake kamar banda qarfin tauna abincin,kuma bani da qarfin yin komai, ban dai san ya zan kwatanta irin azabar da nake ji ba a wannan lokacin.
Dama tin kafin ya dawo nake jin yin kuka na daure ban yi ba har Suwaidatu ta tafi islamiyya, ganin shi ne ya sa na ke ta matsar hawaye, da alamun tausaya wa a fuskar shi ya kalle ni ya ce,
"Baby na sannu ko? Ko ki na son cin wani abu ne ki sanar da ni na kawo maki?"
Kad'a masa kai na yi alamar ah ah, ido na nan da nan ya hau ambaliyar hawaye,se kuma shessheqar kuka kamar jira nake dama a bani attention na bare baki.
Da kyar ya iya lallashi na ya bani abincin muka ci muka qoshi sannan ya taimaka min na yi wanka, ina yin wankan se na ji qarfi a jiki na, dan haka se na je na fara ninke kayan da aka shanya mana, ina cikin ninke kayan Baban Ameerah ya shiga gidan,kallo na yake kamar zai ɗauke ni ya boye, nan da nan raina ya hasalo, dama bana son yanda yake kafe ni da ido kamar ya samu wata TV, tsaki na ɗan yi na tura baki na na juya masa baya, daf da zai shige bishiyar da ke gaban shi iccen ya gogi fuskar shi, janye wa ya yi da hannun shi ya ci gaba da tafiya, dake sun yi steps a bakin qofar su saboda yara,mu kuma namu babu steps din, tuntube ya yi da step ɗin farko ai kuwa na buga tsaki da qarfi na bar wajen.
Ko da na koma ciki ina sanar da Yah Maheer se na ga ran shi ya ɓaci amma dake shi ba mutum bane me son tashin hankali se ya ce,
"Dan Allah baby na ki dena maganar mutanen nan, maqotan mu ne fa, ba kyau mutum ya na yawan maganar wanda baya nan"
Baki sake nake kallon shi,in faɗa maka mutum na min kallon qurilla ka ce ina maganar shi a bayan shi? Cikin ɓacin rai na miqe na bar wajen, na koma dakin Suwaidatu na yi zama na.
Ban bar dakin ba se da dare ya yi sosai ina kallon shi ya na shige da fice dan na tabbata zaman ne be masa dad'i shi kadai, Yah Maheer ba mutum bane mai surutu amma ya na so na zauna ina masa hira,ni da shi mun saba da mannewa juna a koda yaushe,dan haka se ya gwammace ya yi ta Safa da marwa tsakanin d'aki,parlour da banɗaki dan na qudurta a raina ma shiga banɗakin ba na gaske bane ba abinda yake yi ko ya shiga,gefe ɗaya kuma ya na can kishi na nuqurqusar shi, madadin ya dau mataki se ya ke ta qoqarin shanye wa, gida ne muke ciki me girma sosai ya na da matuqar fad'i, ina matuqar qoqarin kiyaye mutunci na ta hanyar zama da hijabi, amma watarana gagara hakan yake yi saboda zafi,se na ɗauki matakin dena fita kwata-kwata, duk da cewa hakan takura ne a waje na amma ya fiye min da na fita ai ta kalle ni,amma duk da haka da zarar na samu fita fa muka haɗu be san me ake kira da ɗauke ido akan abinda yake ba halalin ka ba, duk da wannan qoqarin da nake shine zan magana a nuna min ina maganar maqota a bayan idon su,wato gani uwar gulmar unguwa ko?
Ai kuwa na qudirta a raina tunda ka nuna baka damu ba ni kuma zan baka mamaki.
Se da na bari an kwana biyu ya manta da an yi waccan abun, da safe kamar yanda na saba na ci kwalliya na raka shi, har watarana Maman Ameerah ta na cewa,
"Wai ke ba kya gajiya ne da raka miji in zai fita? Bini bini kin rako shi se kace wata bindi"
Dariya kawai na yi, ban ce komai ba,ita mijin ta mota ne ma dashi daɗin rakiya amma bata yi,ni kuma Yah Maheer machine ne da shi a wancan lokacin irin roba robar nan,bana jin komai haka nake raka shi bana barin farfajiyar gidan kuma har se ya bar gidan gaba ɗaya.
Yau ma kamar kullum kwalliya na ci sosai da wata qaramar riga ta ta yadin material na roba mai kyau kalar purple da ratsin pink a jiki, iyakar ta qwauri na ta na da roba a qirjin ta ta matse albarkatun qirjina masu yalwa ta fiddo da su ta sama da kyau, sannan ta bude ta qasa tai fad'i, hannun ta qarami ne sosai, gashi na sassauqa da ban jima da yi masa kitso ba na kwance a wuya na se na dora hula kalar rigar, se tashin qamshin turarukan da na fesa na ke yi,fuska ta na ɗauke da sassauqar kwalliya mai ɗaukan hankali, na biyo bayan shi riqe da jakar shi a hannu na.
Dakata wa na yi da bin shi, se da ya yi gaba sannan na bi bayan shi,aka kuwa yi sa'a Baban Ameerah baya gida ya na waje kamar kullum, dan ni sai in dinga ganin kamar motsa jiki yake fita da sassafe ko dai wani wajen yake zuwa oho.
Yah Maheer na durqushe a qasan machine ya na buɗe makullin,ni kuma ina tsaye ina jan jelar gashin kitso na da ta fito saman kafada ta, ina jijjiga jiki na a hankali daga wannan bangaren na koma wancan.
Tunda ya shigo gidan ya hango ni yake kallo na, gilashin idon shi mai qara qarfin gani na nan maqale a idon shi, qara gyara masa zama ya yi da kyau sannan ya ci gaba da taho wa zai yi sashen su, da gangan na qi barin wajen dan so nake Yah Maheer ya gani da idon shi, ba qarya nake wa maqocin shi ba.
Ta qasan Machine din na hango yanda Yah Maheer ke tafasa da ɓacin rai, murmushi na yi sannan na tattaka na haye dakalin qofar sashen mu na tsaya,ya na gama kunce machine ɗin ya kalle ni,
"Ki koma ciki, ki dena fitowa da wannan kayan da ki ka saka ba hijabi, sannan kar ki sake fitowa waje"
Kallon shi na yi sama da qasa na ce,
"Hijabi kam zan saka tunda kullum dama cikin shi nake, amma fitowa wallahi se na fito ai gidan ba nasu bane su kaɗai da ba ka nuna qarya nake masa ba, ai yanzu ka gani da idon ka'
Sanin hali na na zan ma iya shinfid'a carpet a waje nai zama na ne ya sanya shi sassautawa ya ce,
"Habaaa Baby na, dan Allah ki zaman ki a ciki tunda ba abinda ake a wajen kuma ma baki da lafiya, ki zaman ki a ciki kin ji?"
Yanda ya yi maganar cikin lallashi ne ya sa na zumbura baki sannan na ce,
"Haaaaaaa Allah ya so ka, yasin da zama zan zo na yi anan"
Cikin sakin fuska kaɗan ya ce,
"Ni da na san halin kayana" a hankali ya fadi haka,ni kuwa da qarfi na daga murya na ce,
"Ka ce me?"
"Na ce se na dawo, ki kular min da kan ki,sannan ki shirya gobe zaki koma makaranta tunda cikin ya lafa maki ko?"
Kukan shagwaba na fara ina buga qafa dan har raina bana son zuwa jinin nan na zuba se in ga kamar zai bata waje, tunda da yawa yake zuba a ina zan gyara jiki na kuma in ya ɓaci?
"Ni dai gaskiya ba zan je ba se na warke dika"
Zaro ido waje ya yi sannan ya ce,
"Gaskiya za ki makaranta baby na, kusan satin ki ɗaya fa baki je ba, gashi term din ya yi nisa"
Matsawa kusa da shi na yi na haye bayan machine ɗin na kwantar da jiki na a bayan shi sannan na saqale hannaye na a cikin shi na ce,
"In dai za ka siyo min chocolate da chisee me zai hana ni zuwa makaranta?"
"Babu kam se rashin ji in ya motsa"
Maitsinin cikin shi na yi da qarfi se da ya yi qara sannan na sauka na bata rai na ce,
"Ban ce ka dena cewa bana jin magana ba? Baka san zai tasiri akai na ba na dena jin maganar ka?"
"To ai dama ba ji ki ke ba se kin ga dama? Ba qarya na miki ba ai"
Kai masa duka zan yi ya ja machine ɗin shi ya yi gaba ya na min dariya, na daga murya na ce,
"Za ka dawo ka same ni ne, kuma ka tabbata ka dawo da chocolate da chisee din nan in ba haka ba hummmm"
Hannu ya daga min kamar yanda soja ke yi ko 'yan sanda.
Ina shirin in juya in shiga gida na ji....................
*Na ji na gaji da typing😂*
*Mutanen Wattpad sannun ku da voting da commenting...mutanen wazof sannun ku da karatu ba comments, ba amfanin a karanta abu a yi shiru kamar ba a bi, se in ba ai typing ba ne nake gane yawan masu karantawa, ina ga ba dan sana'ar man kitso na ba ma da na ga sabuwar lamba ba lallai na duba message din ba tunda ba a nuna alamar ana biye da ni a group wai se ta PC dama har yanzu ana wannan abun? To akwai wanda baku son ya ga ku na karatun Novel ne?*
*Kar ku manta littafai na ba na kuɗi bane kyauta ne, comments ɗin ku shine taki na, less comments less typing more comments more typingggg eheee😂*
Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful*
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 24:
"Wai ke irin yarinyar nan ko? A siyo maki sweet da chesee, ba ki gajiya ne kullum se kin raka shi? Ni fa ba zan iya yanda ki ke yi ba ko da yaushe ka yi ta manne wa miji ai se ya gundura da kai"
To ni wace ma amsa zan bata ne? Kallon ta na yi fuska ta ɗauke da murmushin da Yah Maheer ya dasa min, ban ga abinda zai goge min shi ba a wannan lokacin, kawai se na sa kai na shige sashe na na bar ta.
Garin ya qara dinkewa da zafi saboda damina da ke gabatowa dan haka zafi sai ya qara yawa sosai, ba sassauci ko ta ina, in an kunna fan zafi take bayar wa bamu da AC, amma ina da standing fan da kuma ta sama,katifa muka dakko muka saka a tsakiyar parlour muka bubbuɗe windows da qofofi, ta haka ne muke samun iska ta dan ratsa, duk da cewa in zafi ya yi zafi bishhiyoyin ma sai in ga kamar tare iskar suke dan ba sa kad'awa sam.
Ga jarabawa na gabatowa sam bani da hutu bani da sukuni,nan da nan kuwa sai ciwo ya taso min, ga ciwon ciki ga qurajen zafi manya manya ga zubar jini wanda na fi wata guda ina yin shi.
Watarana ina zaune a kujera a parlour na kunna waya ta, ta na da TV na kunna ina kallon KB TV se na ga ana tallar wasu masu maganin Islamic,ina kallo kawai na kau da kai na a raina ina ayyana.
'Kai na gaji da shan magunguna, ba na baturen ba ba na Islamic din ba, in qiyashi za ai daga farkon rayuwa ta zuwa yanzu na sha maganin da bai da adadi bai da iyaka, ana ta kashe kuɗi a banza, ba ma zan faɗa masa maganar me maganin nan ba kar ya ce se mun je' (na manta hali na na bayyana masa komai ko da laifi na aikata kuwa se na fallasa kai na da kai na)
Da sauri na kashe wayar na aje ta gefe na, na kwanta na yi lamoooo ina tunanin yanda rayuwa ta take tafiya,kusan kullum cikin ciwo ko kuma wata lalurar ,nan take na daga hannaye na sama na ce,
"Allah na gode maka akan dukkan baiwar ka da ni'imomin ka da ka yi min,Allah ka yi min baiwa ta jinya Ubangiji ka bani ikon cinye wannan jarabawa ka qara min lafiya da imani, Allah ka qara wa miji na hakuri da juriya game da lalurori na, Allah ka qara masa arziki mai albarka ka jiqan iyayen shi Ameen"
"Ameeen ya mar'atussaliha, Allah ya qara wa Mama da Baba lafiya da nisan kwana me albarka"
Shine abinda Yah Maheer ya ce, wanda ya shigo ya ji ina addu'a a fili,da sauri na tashi na je gare shi, har zan rungume shi na fasa, na tsaya ina mamakin yaushe ya dawo ban ji qarar machine ba?
"A can na ajiye shi yanzu zan fita kasuwa na yi mana 'yar siyayya, na ɗan samu wasu kuɗi ne na ce bari na je kasuwa, ga jaka ta aje can, me da me ya kamata a qaro?"
"Alhamdulillahi, Allah ya qara bud'i mai albarka, zauna ka sha ko ruwa ne mana, ballantana na gama girki ma"
"Ni fa abinda ke burge ni da ke kenan, da an sauke na safe a maida na rana ba a zama da yunwa da mutum ya nema yake samu"
"Ai daga wajen ka ne, da baka ajiye wa me zan dafa?"
"Ke dai ki gode Allah kawai kamar yanda nake gode wa Allah da ya bani ke a matsayin matata, kaiiii gaskiya ni ɗin fa na haɗu, se da na bari duk mazajen nan suka gama haukan su wai su suna son ki, na lallabo na lallabo ta bayan fage na dauke ki"
(Kirarin da yake yi wa kan shi kenan a koda yaushe, musamman in na yi abinda ya burge shi sai ya dinga jin shi kam ya gama yin Sa'a a aduniya, sai ya hau kuranta kan shi akan ya lallabo ya ɗauke ni cikin sauqi ba hayaniya)
"Kai dai ka ci gaba da godewa Allah ɗin dan shi ne ya baka ba wani laben ka ba"
"Ehhh ai shi yasa ni bana wasa da tashi kullum cikin dare ina yi wa iyaye na addu'a in roqa maki rahamar Allah da gafarar shi sannan in gode masa da ya bani ke a matsayin mata"
A duk sanda na ji ya ce ya na tashi na musamman ya yi min addu'a a sallolin shi na dare sai wani dad'i ya kama ni, ya sa in tuna Nana Aysha da Annabi Muhammad, tabbas Yah Maheer masoyin Annabi ne shi yasa yake koyi da rayuwar shi, ina zuba masa abinci ina share kwallar farin ciki, hamdala kuwa na yi ta har ban san iyaka ba.
Nan da nan na qudirta a raina ina so na samu lafiya ko dan shi, ko ba dan kai na ba zan dage da addu'a da neman magani dan na samu lafiya shima ya mori lafiya ta, zan nemi lafiya ko dan shi ma na faranta masa kamar yanda ba shi da burin da ya wuce na ya faranta min duk da cewa shi din ba wani hamshaqin mai kuɗi bane amma alhamdulillahi ba ma cikin matsin rayuwa a wannan lokacin, na san Yah Maheer ya na hakuri kwarai da ni, se mu yi watanni be kusance ni ba saboda jini,ko qurji guda ɗaya azababbe ya hana komai tsakanin mu, ko na ɗauki fushin da ban san daga ina ya zo ba, kuma babu abinda aka min.
Se da na bari ya ci ya sha ya qoshi sannan na ce masa,
"Husband Ina da shawara,da dai gaskiya ban so na yi maka magana akan masu maganin nan ba, amma na yi tunani nima ina so in dinga kyautata maka kamar yanda ka ke min,na ji ana ta bayani akan irin matsalar da nake da shi a wani Islamic center da aka buɗe suna da branches a Kano, Kaduna Katsina da nan Kebbi, da wasu states din, shine na ce ko za mu jaraba ne? Wataqila a dace, shi dama magani baka sanin wanda zai karbe ka se ka gwada"
Shiru ya yi kamar ba zai magana ba sai can ya ce,
"Zan je na fara duba wajen na ga ya yake, kin san a neman maganin wannan ciwon naki dole mu kula saboda kar mu faɗa wa shirka, ko wani sabon Allahn, ina ne wajen?"
Nan fa ɗaya tunda ni ban gama kallo ba ma na kashe,ga shegen surutu na ya sa na faɗa bayan na ce ba zan faɗa ba.
"Se dai fa a kunna TV anan na ga tallan amma ban san ina suke ba, kuma ko na ji ma ba lallai na faɗa daidai ba tunda ba inda na sani a garin nan ka sani daga kasuwa se makaranta"
"Hakane kunna mana TV,"
"Ka manta ba wuta ne? Ga waya ta dai"
Ko da muka kunna shiru ba su yi tallan ba har caji na ya kusan karewa dan ta na jan caji in na kunna TV, dan haka sai na kashe wayar na qara masa bayani akan wajen masu maganin, ya tambaye ni abubuwan da zai qaro a gidan, na faɗa masa ya sake fita.
Suwaidatu da ke bacci a dakin ta na leqa na ga har a lokacin bacci take, se kawai na je na kwashi wankin mu na makaranta na je baya na fara.
Ina wanki Husnah da Muhammad na leqo ni lokaci zuwa lokaci, ba su ce min komai se dai su yi shawagi su koma, murmushi na yi a rai na na ce,
'An hana su kula ni kenan'
Ban ce masu komai ba ni ma se dai murmushin da mu kai ta aika wa juna, daga baya na ji motsi ta wajen su su kuma suka kalli wajen cikin damuwa, cikin sanyin jiki suka bar wajen suka shige gidan, se na ji an ja qofar a hankali za a rufe, na kuwa daga murya na ce,
"Ku ja qofar ku da kyau meye na sand'a ku da gidan ku?"
Kirif na ji an buga an rufe an juya da gudu nan take na gane Ameerah ce, kuma ba zata yi haka ba sai da umarnin uwar ta,ko kuma tsabar koya musu da akai ya sa itama ta zama gwana, nan da nan na ji raina ya fara ɓaci akan abinda take yi, ni fa in ba sa son ma a ga juna tsafff zan iya rayuwa bamu haɗu ba, amma mu musulmai ne dole mu fidda haqqin musulunci akan mu, in ba haka ba zamu sha wahala, dan duk wanda ya take dokar Allah komai qanqatar ta ya na ganin bata da mahimmanci ya ji tsoron sanda Allah zai kama shi, ba dan haka ba ni ina iya mantawa da ita tsafff a rayuwa ta.
Ana haka na kammala wanki na na tashi na shige ciki, raina a b'ace har wannan lokacin, Yah Maheer be dawo ba se yamma sosai, lokacin na yi alwala ina jiran lokacin sallah ya yi, (abinda aka koyar da mu kenan a gida,mutum ya zauna da alwala ya jira lokacin sallah kar ka bari lokacin sallah ya jira ka, a koda yaushe abinda Mama ke faɗa min kenan)
Ana kiran sallah kuwa na yi sallar magariba ta, ni da Suwaidatu mu ka yi azkar mu ka yi karatun qur'ani, sannan muka dakko ledojin da ya shigo da su kan ya wuce masallaci.
Lemo, ayaba, kankana, abarba, kayan miya, nama, mangwaro,kayan qamshin miya garlic da dai tarkacen cefane sosai ya yi mana, sabulun wanka da na wanki, su Omo chocolates, biscuits da sweets, yalo da danyen dabino, duk saida ya siyo mana, addu'a muka yi masa a tare sannan muka cire komai muka aje a inda ya kamata, muka debi wanda za mu ci a nan take da kuma wanda za mu miqa wa Maman Ameerah, ina gamawa na ba wa Suwaidatu na ce ta kai mata, ai kuwa ta na kai mata ta juyo,ban san me ke tsakanin su ba, amma na kula itama yarinyar ta dena wani dokin ta da yaran ta.
Washegari da safe na fere doya na soya mana da kwai na yi miyar jajjagen da ta ji albasa da kayan lambu se na tafasa nama na yanka qanana na soya na watsa a ciki na sake juye ruwan naman a ciki ta ɗan yi romo romo ga qamshin albasa, garlic da kayan qamshi se tashi yake, na yi mana baqin tea da na sanya wa kayan qamshin da na hado tin daga Kano, ya na tafasa na tace na zuba wa kowa.
Tare muka zauna muka karya Suwaidatu ta dauki lunch bag ɗin ta daga kitchen ta kai d'aki ni kuma na faɗa wanka, ban jima ba na gama na fito na shirya, ina gana shiri Bashar na zuwa, sallama mukami da Yah Maheer ya rako mu har bakin qofa sannan muka dale machine muka tafi makaranta.
Da misalin qarfe biyu na rana bayan an tashi Bashar ya je ya maida mu gida, mu na komawa na tarar da Yan Maheer baya nan ya wuce makaranta, duba wa na yi kitchen na ga ya rage mana sauran doya da kwan da na ajiye wanda ko da ya ji yunwa kan ya tafi makaranta zai qara.
Hamdala na yi na dakko dan kuwa a yunwace na koma gidan, se da muka ci muka qoshi muka qara da fruits sannan na yi wanka na yi sallah, na kwanta dan in huta, Ina kwanciya bacci mai daɗi ya ɗauke ni, ban farka ba sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 30