su haɗa kan su, kin ga wannan qananan maganganun shi zai sa zumunci tabuwa kar ki bari haka ta faro asali daga wajen ki"
Ranta be so shawara ta ba domin nan da nan fuskar ta ta saukar da b'acin rai, se na yi kamar ban gan ta ba, ni dai na gama nawa, ba zan iya da kayan tashin hankali ba, duk rashin son faɗa na na iya masifa sosai nima sai dai in ba a taɓa ni ba, a wannan fannin kuma bana so Baba dake ganin mutunci na da daraja ta ya daina gani na da su, ai kowanne ɗa ya na da matsayin sa a wajen iyaye, na tabbata ba zai ji dad'i ba in ya ji muna zagin Kabeer da matar shi, dan haka har muka gama aikin bata sake dakko maganar su ba nima kuma haka.
Muna zaune muna karyawa su Dhahiru da Abdurrahman suka zo da Yah Maheer ɗin suka gyara min d'akin da zan koma, ai kuwa na ji dad'in hakan sosai,har na fita gidan sarki gaishe su ban dena jin farin ciki ba, a qalla nima ina da nawa d'akin zan dena hana Ummah hawa gadon ta.
Da ni da Mommy muka tafi, mu na zaune A'isha ta soya masa mai rai da lafiya ga dad'i ga quli an daka mai shegen dad'i ta yi sallama ta kawo mana, Mommy na daga kwance ta dinga daukar masar ta na ci, kamar daga sama se na ji ta ce,
"Ai dama Abbakar ya ce min ke mutuniyar kirki ce wallahi, in Yi koyi da halin ki,kar na yi koyi da halin Fateemah Sarkin yawo"
Ban san sanda na fara tari ba saboda kwarewa da na yi, na d'aga kai na Kalle ta cike da mamaki sannan na ce,
"Baiwar Allah ko dai batan hanya ki kai ne? Ni Abubakar ya ce wa mutuniyar kirki? Kuma ki yi koyi da halin na?"
"Wallahi shi ya faɗa min haka, ya ce ki na da hakuri, baki taɓa matsa wa Yah Maheer ya miki abinda bai da shi ba, sannan ke fita bata dame ki ba sai da dalili, kuma ya ce ki na da hakuri in akwai a ci in babu a hakura, har se da Allah ya kawo azziqi ku ka bar Bauchi ku ka koma Kebbi"
Dariya na dinga yi da ta na wannan lissafin,se da ta gama sannan na ce mata,
"Lallai duniya sauyi sauyi,ke kin san irin zaman da na yi da Abubakar kuwa? Se yanzu da ki na magana na ke hango irin cin mutuncin da ya dinga min,da zagi na da ya dinga zuwa gidan Habibah su na yi shi da Abidah da yanda yake kallo na a sheqe a wulaqance a cikin gidan nan, ashe ya na kula da cewar ina da waɗannan halayen? To alhamdulillahi na godewa Allah ke kuma sai ki dage ki yi hali na gari dan ki samu yabo me kyau a wajen mijin ki"
Hira muka ci gaba da yi ta na ta ban labaran da Abubakar ya bata a zaman mu, wanda na sha mamaki, ashe duk ya san da haka amma yake zagi na, can sai na gane cewar ya kula da halin matar shi yanda yake shi yasa ya ke bata misali da ni, hamdala na yi a raina a qalla an bada shaida mai kyau a kai na.
Har muka koma gida hira bata qare ba, ciki har da labarin gagarumin laifin da ya taba aikata min wanda ba zan taɓa iya faɗin shi a rubuce ba, mamakin yanda ya iya zama ya ba wa matar shi wannan labari ya gama kashe ni a tsayen da muke tafiya,haka na hadiye na shanye mamaki na har muka isa gida, ranar Yah Maheer se murna yake da rawar kai za mu kwana a d'akin mu, ni Kuma Ina masa dariyar mugunta,dan kuwa be sani ba na yi gayyar yaran gidan kaff 'yan matan da muke shiri sosai za su kwana a d'aki na.
Mama da Ummah sun qi bacci suna jiran in ya dawo su ga na tashi yara na kora su sassan su sai suka ji shiru,daga qarshe da muka gama hira da Mommy na ɗauki pillow a dakin Umman saboda nawa yara sun kwanta akai na musu sai da safe, Mama ce ta Kalle ni baki sake ta ce,
"Iyyy shi kuma Maheer ɗin ya kwanta a ina?"
Daidai Yah Maheer ɗin kuwa ya shigo baki har kunne, na Kalle shi cikin dariyar mugunta na ce,
"Ahh da ba a dakin Baba ya ke kwana ba? Ya je ya ci gaba da kwanciya da baban shi nima na kwanta da qanne na, se da safen ku"
Daskarewa ya yi a wajen, sannan kuma na ga ya daga qafa da rashin kuzari ya qara so inda muke, gaishe shi na yi ya amsa cikin murya me rauni,sannan na masa se da safe na wuce daki,ina shiga na hau dariyar mugunta.
Ban jima da kwanta wa ba na ga message ɗin shi,
'Baby na na gode, ni ki ka yi wa haka ko? Ni fa ban ce wani abu zaki bani ba, kawai na yi kewar kwanciya a jikin ki ne, dan Allah ki kora yaran nan dakunan su na shigo'
'Sam ba zan kori kowa ba, haka kawai dan mune sarakan soyayya se mu kasa hakurin kwana huɗu, kar ka manta jibi sunan Babyn Abidah daga nan za mu wuce se mu tafi wintin Dada duk abinda ka ke so ka jira mu je can'
Ina turawa na kashe wayar gaba ɗaya na mimmiqe a gado na da ke tuna min abubuwa da dama na rayuwar da muka yi a Bauchi,a haka bacci me dad'i ya ɗauke ni,hamdala na yi tare da yi wa Zainab addu'a da ta ja min ruwa na yi wanka, da tini wanda na wa rashin M shi zai jawo min bawan Allah, murmushi na yi sannan na kulle ido na.
********************************
Tin zuwanmu gidan ake ta hada hadar suna, mu na nan mu na ta taya ayyuka,mutanen Bauchi da na Liman Katagum an hallara kowa ka gani ya yi ado daidai shi,mai jego ma ba laifi ta yi gayun ta ta sha kwalliya.
Gani na yi ni ban ba da komai ba, wanda na tabbata Yah Maheer ya bada, amma ai ihsanin kowa daban, dan haka sai na duba 'yar jaka ta na qirga sababbin kudi na se na ga ashe na ragargaje su dika dika be fi saura dubu da ɗari huɗu ba, ɗari shida na ware na shiga dakin mai jego na damqa mata na yi mata fatan alkhairi sannan na fito, tinda na ga wasu nera hamsin ma bayarwa suke.
Da aka tashi kuwa se aka dinga rabon abubuwa ana zagaye ni ni da duk wanda ke kusa da ni, awannan lokacin kwata kwata abun be wani dame ni ba, se da wata a wajen ta yi magana ta ce,
"Kin ga se zagaye mu ake saboda mu bamu kawo komai ba, amma ki duba ki ga wadancan gayyar dake 'yan k'wari ne se basu nama da abun sunan ake mu muna zaune kamar gumaka"
Kula da inda ta kalla ta yi maganar se ya sa nan take na ce mata,
"Baki ga ita aikin da ta sha ba, duk abubuwan nan na sticker ita ce fa ta je ta tsaya tsayin daka se da aka kammala ta dawo ta kuma ɗora dambu,"
"Hummm ke dai baki son a fad'i laifin kowa, amma ai shike nan daɗin abun ma dai shinkafa kowa na cin ta a gidan su"
"Uhmmmm Allah ya kyauta'"
Shine abinda na ce kawai, se daga baya na kula abun da gayya ake mana, a sannan ne na ji raina ya ɓaci, kawai sai na ce zan tafi gidan qanwar sa kuma gidan yayan shi inda muka sauka da biki na.
Ko da na sanar da Yah Maheer se be tambayi dalili ba ya ce to na koma dama ya na nan ya na jira na, na kuwa kashe waya na hau shiri, haka na tafi da yunwa ba wanda ya damu ya ji na ci ko ban ci ba.
Ina komawa wintin dada kuwa na tarar da kishiyar qanwar shi ta gama tuwon dare,ga kuma shinkafar rana nan a ajiye tana jira na, akan shinkafar na dira na ci sai da na qoshi, Yah Maheer ya min tambayar duniya na qi sanar da shi me ya faru, dan a gani na be da amfani, se dai na sa ya ji haushin su ko ya riqe su a rai akan sun bata min,kuma ba iya musu magana zai ba, wanda ko ze yi ɗin zan hana shi tinda sai su ga ya bi baya na.
Tinda na yi bacci na farka se na manta duk wani ɓacin rai,domin kuwa Yah Maheer be barni na kwanta da damuwa ba, tsafff ya ciren duk wata gajiya da damuwa.
Washegari na je gidan Kabeer na gaishe su, na je tsohon gidan mu gidan Maimunah muka gaisa, mun haɗu cike da murna da farin ciki, sannan ta raka ni na samu adaidaita sahu ban tsaya ko ina ba sai gidan Isma'il ya ajiye ni anan muka gaisa a lokacin Zaituna na da cikin Yaron ta na biyu, na taya ta murna sannan na kamo hanya na koma wintin dada.
Washegari kuwa Yah Maheer ya ɗauke ni sai gidan Inna Tabawa qanwar mahaifiyar shi da suke Baba ɗaya, na gaishe su muka sake lula wa gidan Kawu Usman da Baba Aunty, daga nan muka je gidan Addah Firdaus, anan ya bar ni ya koma chemist ɗin Baban Hauwa'u saboda ba su da nisa, se yamma lisss ya zo ya ɗauke ni muka je gidan abokin shi da suka yi quruciya tare, sau ɗari zamu haɗu sau ɗari sai ya yaba mana, ya kan ce,
'A gaskiya Madam ki godewa Allah da dukkan alamu ki na da kyawawan halaye shi yasa Allah ya haɗa ki da Maheer,kin gan shi nan tun muna yara ba ruwan shi da mata, kwatsam mu ka ji zai yi aure, gaskiya ki godewa Allah dan duk wadda Allah ya ba miji na gari kamar Maheer to itama da alama ta gari ce'
Bayan kwana biyar da na yi a Bauchi muka koma Kano daga ni sai Suwaidatu da zummar in na gama ziyara ta se ya zo mu koma kebbi, nan ma ziyarar na kafa yi, daga can gidan kakar je ki wancan gidan Inna da Goggon haka na dinga yi har na ci kwana huɗu.
Watarana ina zaune da Baba a dakin shi muna hira, ya dinga min nasiha da bani tarihin Mama yanda ta taso da hakuri da kawaici da shanye duk wata damuwa, ya ce,
"Gaba ɗaya kin dakko halayen Maman ku MAHREEN, Maman ku mace ce mai tsananin hakuri ta yanda duk wani laifi da zan mata bata taɓa kai ni qara gidan su ba har mahaifin ta ya koma ga Allah yabo na yake be san irin zaman da 'yar shi ke yi da ni ba, MAHREEN ki qara hakuri akan rashin haihuwa da Allah be baki ba dama Allah ya faɗa a cikin Alqur'ani...."
Nan da nan na taya shi jawo ayar muka qarasa a tare mu na dariya, cikin dariya na ce masa,
"Ga ayar aqima nan mun jawo Baba, ai ni Baba na haddace ayar nan tasss akai na saboda yawan karanta ta da ka ke yi, Baba kar ka damu akan komai, ka ganni nan da kai na nake addu'a Baba, idan haihuwa alkhairi ce a gare mu Allah ya bamu idan babu alkhairi Allah ya bar mu haka ya sa mana hakuri da juriya da dangana, beside ga Suwaidatu ta na ɗebe mana kewa sannan ga 'ya'yan 'yan uwa na nan duk inda na juya ido na a dangi, kuma na tabbata ko d'an wa nace ina so za a bani,Allah be hana mu duka ba, in ya ba wa wani to zai hana wani, se ya bawa wani ta wani ɓangaren dan haka alhamdulillahi Baba bani da damuwar komai sai hamdala, Yah Maheer na kula da ni sosai Baba fiye da yanda baka tunani "
"Ahhh alhamdulillahi gashi nan muna ganin shaida, Allah ya jiqan mahaifiyar shi ya ba wa Yayana lafiya, Allah ya sa arzikin shi ya fi haka, ba abinda zan ce wa Maheer Sai godiya"
Baba na da saurin kuka dan kuwa a wajen shi na gado saurin kuka, nan da nan hawaye suka fara zuba a idon shi, saboda a cewar shi kalamai na sun daki zuciyar shi sosai, ta wani fannin kuma tausayi na yake ji, saboda a cewar shi har yanzu quruciya ke damu na ban san daɗin d'a bane shi yasa har cikin raina ban damu da rashin haihuwa ta ba duk da ina kallon 'yan uwa na na ta haihuwa,sanda na qara girma zan fahimci damuwar da yake akai na.
Kuɗi ya bani akan na nemi magunguna na sha ko dan qarin lafiya ta ma, na rabu da ciwon cikin da ke addaba ta, wanda in ba ni na fada ba ba me ganewa,saboda ba ni da halin in kwanta in ta jan jiki dan banda lafiya se dai in ciwo ne ya kayar da ni, a wannan lokacin ni na saba da zafi, na saba da ciwo na saba da rad'ad'i, zan ta harkoki na sai in cikin ya motsa min ne zan dunqule waje ɗaya da ya saki na ci gaba da harkoki na.
Godiya na masa na fita wajen Mama na sanar da ita duk yanda mu ka yi da Baba, godiya ta yi sannan ta ce akwai wani wajen me ruqya da za a kai ni a gani shin ko dai aljanu ke damu na, dan haka washegari da sassafe sai na je, godiya na yi mata na koma cikin daki na cire kaya na na faɗa wanka.
Washegari da safe bayan kowa ya karya Hajiya Tani me wanke wanke ta iso ni da Suwaidatu mun share gidan mun gyara, wanka mu ka yi muka shirya muka hau sabgogin gaban mu domin a da in dai aka yi maganar za a je wajen neman magani se abu ya shiririce,asibiti ne kawai nake zuwa ba wata matsala.
Ranar dai haka na cinye ta a shiririta qarshe aka yi min haɗin magunguna na Islamic ba tare da na je ko ina ba.
Kwana biyu tsakani Yah Maheer ya dawo muka ɗauki hanyar mu mai nisa sai Kebbi.
Mun isa Kebbi bayan la'asar saboda da sassafe muka tashi shi yasa muka isa ido na ganin ido,tsarabar da muka je da ita na dibar wa maqota na na ba wa Suwaidatu ta aika musu, Maman Ameerah na nan da halin ta na yatsina da yin abu kamar ana mata dole, ni dai ba kula ta nake ba tunda ba sa'ata b'ace.
Bayan kwana uku muka hau shirin komawa makaranta, ranar Monday muka koma aka ci gaba da karatu.
Watarana da rana muna zaune na dawo daga makaranta se na ga su Husnah da Ameerah na wasan karatu se na kira su, na ce su zo na koya musu karatun Kur'ani, ai kuwa ba musu suka zo kamar wasa se na fara musu da suratul kahfi, abu fa ya yi gwanin sha'awa,nan da nan yara suka fara ɗaukan karatun da kyau da kuma mahimmanci, ba tare da na sani ba ashe ni laifi nake aikatawa babba.........
*Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful*
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 23:
Mun fara samun shaquwa da su Ameerah sosai ta yanda ko abinci za su ci sai sun dakko sun kawo waje na, ni kuma sai in zuba wa Suwaidatu nata su haɗu su ci, na kan zuba mata da yawa sosai yanda zai ishe su su ci su qoshi su dika,duba da cewa su kaɗan ake zuba masu.
Ban taɓa damuwa ko na ji haushin yawan shigo min da suke yi ba, hasali ma ina jin daɗin zuwan su, ina samu in koyar da su duk wata tarbiyya da aka koyar da ni nima a gidan mu,yaran na da nutsuwa da hankali, musamman Ameerah, ta haddace duk abinda mahaifiyar ta bata so,kuma ya na wahala ta aikata abun nan, a haka na gano yawan hana su zuwa sashe na da ake yi, watarana ko wuce wa na yi zan ganta ta na satar kallo na idanun ta cike da hawaye da na ga haka na san ranar an hana su zuwa kenan se nima na kama kai na, Ameerah yarinya ce fara me kyau ta na da qaramin jiki shi yasa suka kusan yin kai ɗaya da Husnah qanwar ta, shi kuwa Muhammad qaramin yaro ne da ba zai wuce shekara biyu da watanni ba.
Watarana na zuba musu abinci sai na ɗauki namu dan in kai mana mu ci ni da Maman su, Yah Maheer na d'aki ya na cin nashi. (Kun ji babbar wauta, na bar miji na a daki ya na cin abinci shi kaɗai na dauka zan je ci da maqociya, duk zaman lafiyan da mace ke yi da maqociya kamata ya yi a zuba abinci a kai musu kema ki zauna ki ci naki ke da mijin ki).
Ina kaiwa se na ga Maman Ameerah na b'ata rai, sai ban kawo komai a raina ba saboda cikin da ke jikin ta, ga zafi, sannan kusan haka halin ta yake ko da yaushe se tai ta bata rai sai dai in ita ta so ta yi fara'a to fa za ta yi,zama mu ka yi muka jawo abincin ta, taliya ce da miya, ni kuma shinkafa da wake da mai da yaji da cabbage da dai sauran tarkacen da za su qara mata dad'i, gaba ɗaya lissafi na ya bani yanda nake son wake da shi kafa haka kowa ke son shi,bana tunanin cewa kowa fa da favorite food ɗin shi, a cinkishe da fuska muka gama cin abincin nan, bayan kammala ci ne na tattara wanda ya zube, na ɗan zauna hira sannan na koma sashe na.
Ina zuwa se na ga su Suwaidatu sun cinye har ma ta qaro musu, zama na yi ina nazarin bata ran da take ta yi, na menene? Dan dai bata kusa haihuwa ba balle in ce ko cikin ciwon naquda take ko dai na mata wani abu ne da ya bata mata rai? Qudirta wa na yi a raina zan bata hakuri ko in tambaye ta ko na mata wani abu ne, dan ni bana so mutum ya dinga zama da ɓacin raina.
Daki na shiga na tadda Yah Maheer ya ci abinci ya na zaune da wayar shi a hannu, zama na yi kusa da shi na dora kai na a kafadar shi ba tare da mun ce wa juna komai ba,mun jima a haka kamar masu jiran ɗaya ya fara cewa wani abu, a tare mu ka kalli juna muka buɗe baki da niyyar yin magana, dariya muka yi sannan ya tallabe hab'ar shi ya ce min,
"Bismillah.. ladies first"
"Inyeee bature..."
"Suna na, kin san haka Innah Halima ke kira na Balarabe? Saboda tsabar fari da kyau na ina qarami?"
"Yanzu dai na ji amma ban san da hakan ba...ammmm dama kawai ina so na faɗa maka wata magana ne,"
"Game da me fa?"
"Ka ga Maman Ameerah ce se in ga ta na yawan bata rai ko me akai mata oho, ka san na faɗa maka watarana hana su Ameerah zuwa nan take, gashi sai in ga kamar yaran ba sa qoshi watarana har rama suke su yi duhu ina so ina jan su a jiki sosai su saba da ni su sake sosai ina ganin kamar maman su bata so"
Gaba ɗaya ya tattara hankalin shi a kaina ya na ji na ya na sauraro na, kuma ya na fahimta ta sannan ya san hali na ina so in kawo ra'ayi na ya ban shawara ko ba zata min dad'i ba, amma laifin shi ɗaya ya fi bani shawara according to yanda raina ba zai ɓaci ba, se in abu ya kwabe se ya ce kaza ya so ce min amma se ya ga kamar ba zan so ba raina ze ɓaci shi yasa ya fasa ya ce kaza,in na ji haka se kuma in dawo ina jin haushin shi muna faɗa.
"Kawai ki ci gaba da jan yaran a jiki, kuma ki na zuba masu abinci yanda za su na qoshi sosai ba dole sai daidai wanda Suwaidatu zata ci ba, sannan ki rage yawan zuwa wajen Maman Ameerahn"
"To amma Husband tausayin ta nake ji, se in ga kamar ta na cikin kadaici yaran sun zo wajen Suwaidatu miji ya fita se na ga kamar ita kaɗai bata jin daɗin zama"
Ina kawo wannan uzurin kawai se ya biye min, bai tsaya ya yi min bayani dalla dalla yanda zan gane ba na kiyaye, a cewar shi nima ina da hujja, sanda komai ya kwabe ina masifa cewa ya yi ai ya san ba za a taba yin tashin hankalin da zai wani damen sosai ba tunda ina da kyakkyawar niyya akan abinda nake shi yasa be hana ni ba.
Da yamma na mana shinfid'a a bangare na kamar ko da yaushe ta qofar baya dan mu yi karatu, ina nan zaune mun fara da Suwaidatu har ta maimaita na baya na mata qari ba su zo ba, addu'a muka yi muka tashi, ina nad'e tabarmar Husnah ta shigo , daga gani satar fitar ta yo, se sauri take ta na wurga ido, irin abun yaran nan wanda aka hana yin abu.
Zata durqusa ta ɗauki abun wasan ta da ta bari a waje na na kama hannun ta na ja ta gaba na na zauna a qasa, sannan na ce,
"Husnene me ya sa baku zo karatu ba yau?"
Kafin ta bani amsa se ga Ameerah nan ta zo sai raba ido take itama, yanayin ta na kalla na ji be min dad'i ba, nan da nan na gane hana su zuwa akai, zan saki hannun ta kenan yarinyar ta ce,
"Mommyn mu ce ta ce kar mu zo in kin tambaye mu mu ce miki daddyn mu na koya mana karatun a gida"
Gyada kai na yi na ce,
"To Masha Allahu, haka ake so dama ai, Allah ya taimaka,"
A guje suka koma ta qofar gaba saboda Maman su ta fi zama a daki kuma dakin a qofar baya yake,cikin rashin jin dad'in abinda yaran suka sanar da ni na tashi na shige d'aki ina tunanin me ya yi zafi haka? Kai da ake koyar da yaran ka abun azziqi kamar masu koyon garaya ko goge? Da kaina na ba wa kai na shawara cikin bayyananniyar murya na ce,
"Allah ya kyauta, rayuwar nan dama se a hankali, MAHREEN ya kamata ki gane hakan,daga abun azziqi se a hau na tsiya karatu ne fa, na qur'ani ma ba na boko ba balle ta ce ana koya masu yahudanci in ma ba ilimin abun, to Allah ya kyauta"
Aikace aikace na na hau yi, amma abun na nan maqale a zuciya ta, kuma duk sanda ya fado min ina jin rashin dad'i a zuciya ta.
Yah Maheer ne ya dawo daga masallaci bayan sun idar da sallar la'asar ɗin suka tsaya da Baban Ameerahn a qofar gida suke hira.
Ko da ya shigo se ya ganni babu walwala, zama ya yi a bakin gado ya na sake qare min kallo, a hankali ya kau da kai ya yi murmushi sannan ya dakko maganar da ya ke ganin zata faranta min, tunda ya ga ina ta damuwa da maganar Maman Ameerah da yaran ta,
"Yanzu muka rabu da Malam ai, ya ce na maki godiya, ya kula yaran sun sake da ke sosai, rannan ya ji Husnah na karatun qur'ani ya tambayi inda ta iya ta ce kece ke koyar da su,sannan ba laifi su na cin abinci enough a wajen mu, Allah ya saka da alkhairi,sannan ya ce ka san dake cikin nan na ba wa Maman su wahala shi yasa bata girki sosai, Allah ya qara zumunci,na ce Ameen haka ki ke ki na da son kyautata wa duk wanda ki ke tare da shi"
Tagumin da na zabga na cire sannan na yi ajiyar zuciya sosai sannan na ce,
"Hummmmmm to
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 30