gado ta koma bacci dan kuwa kowa ya gaji da zirga zirgar da aka sha da rana, sallah na so yi amma se na rasa ya ake yin sallahr,wasa wasa se na dinga qoqarin manta me nake yi, da zuciya ta na fara addu'a ina neman Allah ya shiga lamari na kar ya bar ni da kai na ba zan iya komai ba sai da shi a rayuwa ta.
Idanu na na zubar da wasu zafafafan hawaye nake wannan addu'ar cikin ikon Allah se gashi hankali na ya dawo jiki na, a gaggauce na yi nafila daidai yanda zan iya, ina idarwa kuwa na samu na yi addu'a cikin kuka na ce,
"Ya Allah ka yi wa Annabi salati da sallama da shi da Sahabban shi da iyalan gidan shi da dukkan wanda suka bi shi da kyautatawa har izuwa ranar qarshe, ya Allah ka shiga lamari na kar ka bar dukkan mai cutarwa cikin dare ko rana ya cutar da ni,Allah ka zama gata na ka bani kariya, Allah ka bani kariya akan dukkan mai qudirin cutar da ni ko wane Allah ka shiga tsakani na da ga sharrin mutane da Aljanu Allah ka shiga lamari na"
Kuka ne ya kwace min se a sannan na ji wani tsananin tsoron abinda zuciya ta ke.raya min, anya ba cinye ni matar nan ke son yi ba, Hasbunallahu wani'imal wakeel na dinga nanatawa a zuciya ta har na fara furta wa a kan harshe na da murya ta, kamar wadda aka tsame daga jikin wuta aka kunna wa fan haka na ji jiki na, nan da nan na koma normal.
Hamdala na dinga yi wa Allah ina kuma wa tare da yi masa kirari, qur'ani na buɗe a waya ta na dinga bi, ina jin wani irin dad'i da annashuwa na shiga ta, ban yi gangancin komawa bacci ba a wannan daren, dan ina ganin da na rufe ido na zan sake ganin ta.
Se da na yi sallar asuba sannan na samu bacci me daɗi ya ɗauke ni, ba kuwa ni na farka ba se tara na safe, ko da na tashi an gama share gida an gyara ga abun karyawa ta nan an ajiye min, Baba na je na gaisar ya min ya jiki, sannan ya yaba min a yanda ya ga jiya na maida hankali wajen neman taimakon Allah sannan ya qara da sanar da ni na riqe azkar da karatun qur'ani da kyau kar na yi wasa da su duk abinda ke damu na da izinin Allah, Allah zai yaye min.
Godiya na yi masa na shiga gaishe da su Ummaah ba se na ji ana min jaje ba, mamaki ya kama ni, ban gama mamaki ba se da na shiga sauran sassan gidan sannan sabon mamaki ya riske ni, jaje aka min na tsallake rijiya da baya da na yi, nan take na tuna a wajen wa suka samu labarin abinda ya same ni, murmushi na yi na gyada kai na furta.
"Ummeeta"
Wajen su na shiga muka zauna da iyayen ta muna maida yanda akai ina sake basu labarin wuyar da na ci da daren, suka ce,
"Dama can ta qulla ke take so shi yasa duk da baki ci kuɗin ta ba ta biyo ki da dare"
"Allah ba zai bata Sa'a ba da yardar shi"
Da yamma se ga dayar da ake zargin itama ta na maitar ta zo gaishe da Baba,ganin tun asali dama ta saba zuwa har Kano gidan mu iyaye na na son ta musamman Baba se nima nake son ta, ga shi ta dai tsufa amma kyau a wajen ta se dai a ce Masha Allah,ta na da zumunci sosai matar,gaishe ta na je na yi ina zumudi Itan ma ta yi murna da gani na, nan take na tuna sanda aka kawo ni a dakin da na sauka a gidan su Hauwa'u anan ta zauna itama har se da aka kai ni gida na ta qi tafiya se da kowa ya tafi sai Kabeer da abokin shi Ibrahim su ka qi tafiya, ta zaunar da ni ta min nasiha akan abubuwa guda uku.
Kar in dinga barin takalma da buta a waje saboda ana sihiri a cikin su.
Kar in dinga zubar da gashi na a ko ina bayan na.yi aski ko na yi tsifa.
Kar in dinga barin sutura ta a waje in dare ya yi ina shiga da ita ciki.
Ta na gama.min nasihar ta tafi, sannan su Kabeer suka tafi suma.
Bata wani jima.ba sosai ta tafi, na koma wajen su Mommy mukai ta hira ina basu labarin matar sanda ta na zuwa gidan mu muna.yara da sanda ta zo tin kafin aure na da yah Maheer.
Haka muka gama kwanakin mu muka dunguma muka koma Bauchin Yakubu, anan ne na haɗu da wata baiwar Allah su na ce mata Inna Sa'a, Inna Sa'a irin distance relative din nan ce ta su Ummaahn su Yah Maheer ta na harkokin siyasa ta na da gida anan unguwar su Kabeer, sun saba da Habibah sosai a wannan qanqanin lokacin, gaishe ta na yi sannan na kama kai na saboda na kula kamar akwai ta da surutu Ni kuma ina da taka tsantsan da mutumin da yake da surutu, na kan ce, Ni surutu ke surutu ai tafiyar ba za ta yi daidai ba, ashe kuwa gwanda da na yi hakan saboda da ban yi ba matsalar da na shiga akan baiwar Allahn nan se ta fi haka............
*Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful*
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 28:
Komawar mu Birnin Kebbi ta yi daidai da komawar su Suwaidatu makaranta, dan haka babu bata lokaci ranar Litinin ta saka wankakku kuma gogaggun kayan ta ta tafi makaranta, tun kafin mu tafi hutu nake wanke mana kayan mu na goge mana na ajiye saboda irin haka, kar ya zamana mutum bashi da lokacin wanki balle guga kuma an koma makaranta.
Maman Zakiyya maqociyar mu ta tashi har an maye gurbin ta da wata amarya mai suna Hauwa'u, ban taɓa had'uwa da Hauwa'u ba, ban taɓa shiga gidan ta ba tun da muka dawo, katangar gidan ta haɗe suke da ta gida na, ban san da zaman ta a unguwar ba sai wata rana na fita backyard ɗin mu zan yi wanke wanke na ji su ita da mijin ta, anan na tabbatar da cewa an yi baquwar amarya,murmushi na yi na musu fatan alkhairi a cikin zuciya ta, na qudurta a raina da an kwana biyu zan shiga mu gaisa na gabatar da kai na a matsayin maqociyar ta.
Har na yi sati ɗaya ciff ban samu na leqa Hauwa'u ba, ina ta hidimar iyali na, domin a wannan lokacin Yah Maheer ya na yawan zama a gida baya fita, ni kuma in dai ya na gida dama sabo na ne ba inda nake zuwa muna tare da junan mu, ko ba za ai hira ba mu na nan manne kamar chewing gum kowa na latsa waya ko shi ya na rubuce rubuce a takardu ni ina manne jikin shi ina latsa waya da dai sauran su.
Wataranar alkhamis ba na mantawa saboda Yah Maheer na azumi ranar na fito qofar parlour na ina share wa, sanye nake da qananan kaya na kamar kullum sai na ɗora wata milk color riga a sama,wadda ta fi dacewa da a kira ta da net, kai na babu dankwali kamar ko yaushe, sai dai wannan karon ya samu kitso manya guda biyu da na kan yi saboda kar ya zauna a hargitse ga quraje ga rashin gyara.
Wata mace na gani fara ta shigo,tun daga nesa na ga ta na min wani kallo wanda iya sani na ban san matar ba, ban taɓa ganin ta ba me zai sa ta na min mugun kallo kamar ta ga wata maqiyyiyar ta? Maida kai na na yi qasa na ci gaba da Shara ta tunda dama ban san ta ba na tabbata wajen maman Ameerah ta zo, kamar daga sama sai na ji Muryar ta ta na faɗin,
"Aunty? Aunty ki na ina?"
Nan take na ɗauki Muryar ta maqociyar nan tawa ce wadda ban shiga gidan ta ba,cikin murmushi na miqe na isa gare ta na gaishe ta, a yatsine ta kalle ni, sannan ta ce,
"Lafiya qlou,ashe ki na kula mutane"
Nan take se na ji ban ji daɗin yanda take min magana ba,
"Ban gane ina kula mutane ba? Da wani ya ce maki bana kula mutane? Ko dake ban yi mamaki ba duba da yanda ake min munafurci a fad'i abinda ban yi ba, Allah ya kyauta,"
Jikin ta ne ya yi sanyi dan ta zaci zata faɗa min magana na yi jugum kamar sokuwa, se ta ji na bata amsa, tun daga nan ni da Hauwa'u sai ya zamana daga gaisuwa in mun haɗu ba ma qarawa ba ma ragewa, a rana ta kan shigo gidan mu sau ba adadi duk sanda ta ga dama zata shigo ta fita.
Anas almajirin mu ma ya dena zuwa waje na sai dai wajen Maman Ameerah, daidai da gaisuwa ba ta haɗa ni da shi, zan iya wucewa ya wuce shima ba tare da ya ce min ci kan ki ba, abun mamaki yake bani matuqa musamman in na duba yanda muka riqe shi da irin kyautatawar da mukai masu shi da abokan shi, me na masa da na cancancin haka a wajen shi? Wata zuciyar ce ta kwabe ni akan saka damuwa akan abubuwan da basu da mahimmanci, ai kuwa nan da nan se na tattara komai na watsar na ba wa iyali na mahimmanci .
A dan zuwa wajen Maman Ameerah da nake yi mu gaisa ne lokaci zuwa lokaci, ta ke nuna min mamakin ta akan halayya ta ta rashin tsoro da tsaya wa kai na a duk inda na ga za a cutar da ni ko a min ba daidai ba, har watarana ta na faɗin.
"Ni fa wallahi gidan hayar da muka fara zama a Bauchi mugun tsoro na suke, su na girmama ni sosai ba wadda ta isa na ce eh ta ce ah ah"
Dariya na yi tare da buga qafa da qarfi, na yi amfani da hannu na na daki qasa sannan na ce,
"Tabbb amma kuwa sun yi asara, ina biyan haya ki na biyan haya sannan na ji tsoron ki? Ai ni nan da ki ka ganni bana tsoron kowa sai Allah, duk wanda ki ka ga na d'aga wa qafa to girman shi ya kama kuma girmama wa ce ba wai tsoro ba, tabbb Allah ya kiyaye na ji tsoron wata qatuwar gidan haya"
Wani irin buɗe baki tai ta na kallo na dan tsananin mamaki na da ya kama ta wanda ya kasa boyuwa a saman fuskar ta,sannan tun daga wannan ranar ta janye min ta dena kowacce irin mu'amala da ni wanda ni ban ma fahimci me take yi ba sai watarana na fita nawa backyard ta fita na ta backyard ɗin ta na jin motsi na ta koma cikin gidan ta da gudu ga ciki,nan da nan tsoro ya kama ni me ya faru? Me aka yi? What if ta je ta buge cikin ta fa? Me yasa da ta ji ni ta gudu?
Ban kyale ta ba se da na bi ta har sashen ta na yi ta sallama na ji shiru, har na yi niyyar na hakura na koma waje na se gata ta fito ta na tura baki ranta a matuqar b'ace ta na ta zabga tsaki, na tsani tsaki amma se na danne na jure sannan na ce mata,
"Lafiya na ji kin fito amma kin koma da gudu?"
Tsaki ta sake ja me qarfi sannan ta ce,
"Ni bacci ma nake ba ni b'ace wataqila yara ne"
Cikin raina na maimaita kalmar 'Yara?' yaran da duk sun tafi makaranta,murmushi kawai na yi na mata fatan alkhairi na fita, nan take na gane da ni ce bata so ta haɗu inshaa Allahu kuwa zan dena shige mata in an haɗu an yi gaisuwa shikenan.
Kame kai na da na yi se ya zama kuma ya shiga wa Maman Ameerah hanci da qudundune, nan suka dasa wani sabon zumunci ita da Hauwa'u a baza tabarma a tsakar gida Anas almajiri na gefe yaron ya girma ya balaga amma haka ake zama da shi daga ita sai daurin qirji a sha hira, a zaton su ko hakan zai bata raina oho, ni basu San bana maraba da irin wannan rayuwar ba, na fi buqatar na baje surutu na inda za a saurare ni da kunnen basira.
Hakan da suka gani ban damu ba sai suka fara qulla yanda za a ci zarafi na idan Yah.Maheer ya fita Masallaci ita da mijin ta, Maman Ameerah da mijin ta sun gama qulla komai lokaci ake jira.
Ina zaune zafi ya yi zafi daga ni sai guntun wando da bra ina ta firfita, a haka Yah Maheer ya fito daga bathroom daure da alwala zai wuce masallaci,
"A tashi a yi sallah"
Shi ne abinda ko da yaushe ya ke faɗa idan zai tafi masallaci ko da kuwa bacci yake na taso shi ya yi alwala, to zai tunatar da ni na tashi na yi sallah haka ma in ya dawo zai tambaye ni ' kin yi sallah?' tun abun na min wani iri ina ganin kamar be yarda da ni ina sallah bane ko ya? Har na gane cewar ya na tambaya ne saboda haqqin shi ne ya tabbatar na tsaida ibada ta yanda ya kamata.
Miqe wa na yi dan na je na yi alwala, ina jin qarar buɗe gate Yah Maheer ya fita Maman Ameerah na shigowa, zama ta yi ta na karanta min wasu maganganun rainin hankali wanda suka hasala ni suka tunzura zuciya ta na miqe ina kallon ta ido cikin ido na ce,
"Ke Maman Ameerah bari fa ki ji dalilin da ya sa nake daga maki qafa a gidan nan, ina daga maki qafa ne kawai saboda Addar mu babba ta san mijin ki ina ganin za ku yi shekaru daya da ita ke ba Sa'a ta bace kin girme ni sosai, ni kuma inda na fito an koya min girmama na gaba da ni, to wallahi ki kiyaye ni, ki fita ido na na rufe, in ba haka ba yanda baki ji kunyar zuwa sashe na ba ki ce za ki min warning din banza da wofi mara asali da tushe ba zan ji kunyar yaga Maki rigar mutunci ba, Ohhh wato fako na kuke Yah Maheer ya tafi masallaci da ke da wancan lusarin mijin naki kun shirya ku zo ku ci mutunci na, to ni ba a halicci mutanen da za su tadan hankali ban miqar da nasu tsaye ba"
Wallahi har yau ina hango yanda tsananin mamaki na ya bayyana a fuskar ta, cikin rashin kwarin jiki ta bar sashe na ta koma nata, Baban Ameerah kuwa tun da ya ji babu nasara a faɗan se ya bar gidan shima,abinda ya faru se ya sa na dena ganin duk wani guntun girma da darajar su da nake gani na fara tata masu rashin M, dan kuwa ko gaishe su sai na ga dama nake yi, shi ma dan babu kyau gaba ne a musulunci, to sun nuna min qiri qiri basu so na ba su qauna ta, miji na kuma da ke so na haushin abun suke ji.
Ko da Yah Maheer ya dawo na sanar da shi abinda ya faru shi ma ya yi mamaki, amma be taba nuna wa Baban Ameerah ba, shi kuma Baban Ameerah ya so a tada maganar ya kare kan shi Yah Maheer ya qi bashi dama, da ya dakko maganar mu zai yi sai Yah Maheer ya ce masa
"Wannan magana ta mata ce a bar ta tsakanin su kawai"
Da haka su Maman Ameerah suka fara neman gidan haya ba tare da na sani ba, su na so su tashi su bar gidan tunda ta kasa mulka ta, ta kasa tankwasa ni ta kasa juya ni.
Kafin su tashi Allah ya sauke ta lafiya ta haifi yarinyar ta mace, suka je ganin gida suka dawo, basu jima da dawowa ba suka samu gida a can qasa da mu sosaiiii, amma still ba wanda ya sanar da ni, kamar idan na sani zan hana su tashi.
Kwatsam se ranar da za su tashi har sun gama kwashe kaya a she da kaɗan da kaɗan ba tare da na sani ba, dan tunda ta shigo ta min haukan nan na yanke zuwa sashen ta amma fa duk muka haɗu zan gaishe ta, in bamu haɗu ba na dena zuwa wajen ta shi ya sa ban ga sun kwashe kayan su ba.
A ranar da za su tashi sai na ga mata ana ta shiga gidan, matan unguwar tamu wasu ma ban san su ba saboda ba gidan kowa nake shiga ba, sauran ma da na sani a gidan Naman Ameenah na san su in sun je siyan abu na je hira ko kitso.
Babbar qawar Maman Ameerah Maman Ruqayyah ce ta zo da motar mijin ta, suka ɗebi wasu kayan su kai gaba, ina nan zaune Maman Ameerah ta shigo ta ke sanar da ni su fa yau za su tashi, cikin hikima da iko na Allah sai ban sanya wani reaction na mamaki ko damuwa ko wani abu a fuska ta ba, gaba ɗaya fuska ta ba wani emotion ɗin da zata gani ta san halin da na shiga na mamakin abinda ta sanar da ni a qurarren lokacin nan, kallon ta na yi na ce,
"Masha Allahu za ku tashi? To alhamdulillahi Allah ya sa Alkhairi ya sa albarka, Allah kuma ya sa inda za ku koma ya fi nan Ameen, bari na shirya mu yi rakiya, Suwaidatuuu !"
Na kwala wa suwaidatu kira, nan da nan se ga ta, qawayen ta da ke tsaye su ga ya zan yi in na ji za su tashi sai suka fashe aka koma sashen ta, dama na yi wanka na na saka atampa fara da ratsin purple da baqi ta bala'in yi min kyau, ina zaune ne zaman jiran dawowar Yah Maheer ta shigo sanar da ni wannan labarin,mayafi na baqi da baqin takalmi na dauka,Suwaidatu ta saka yellow material d'in ta, muka ja qofa mu ka nufi sashen Maman Ameerah inda mata ke zaune ana ta hira, shigar mu wajen se hira ta ragu, da damar su se suka hau harara ta kamar sun ga wata muguwa ko wata maqiyyiyar su, wanda ni ban san su ba ma ban taɓa ganin wasun su ba, Hauwa'u ce ke ta rawar kai ita a dole za ta yi missing ɗin Auntyn ta ana bata baki, duk sai na ji ni na muzanta a cikin su tunda ko magana suke na saka baki se a yi shiru ko a qi Kula ni a hau wata hirar gajiya na yi na gimtse baki na na hau danna waya ta ina so na kunna TV dake jiki.
Horn ɗin mota muka ji an danna da qarfi nan take yara suka fita da gudu sun zaci baban su ne, su na ta ihun kiran Daddy Daddy.
Waya ta ce ta hau ringing nan take na duba se na ga kiran Hafsat Ta/fana, wata diyar wani ɗan siyasa ce a birnin Kebbi mutanen kirki,Hafsat ta nuna min qauna matuqa a garin nan ta yanda ba zan iya bayyana qaunar Da ta nuna min ba a ɗan qaramin page ɗin nan, (in baku manta ba ita ce ke sa drivern su ya dawo da ni gida daga makaranta).
Hafsat fara ce sosai kamar irin baturiyar nan ta ɗauki atampa ta sanya a jikin ta haka Hafsat take, ga kyau ga kuɗi Allah ya hore musu.
"Ki na qofar gida? To ku shigo mana"
Nan take na tashi na fita qofar parlourn Maman Ameerah, kowa kuma se ido ya koma kai na, Suwaidatu na zaune a gefe bata bi ni ba, ina fita se na hango Hafsat da yayar ta Hannatou sun nufo ni, cike da murna da farin ciki kamar mun shekara ɗaya bamu haɗu ba,(Haka Hafsat take ko da mun wuni makaranta tare in zata zo waje na to fa murnar da zata yi kamar mun shekara ne bamu haɗu ba, haka Allah ya yi ta da fara'a da son mutane).
Rungume ni ta yi sosai ta na faɗin ,
"Na yi missing ɗin ki Aunty Mahreen ɗina,"
Ni ma nan take na furta,
" I miss you too my Hafsat, mu shiga daga ciki"
Tun kafin mu shiga ta juya wajen Yayar ta ta ce,
"Aunty Mahreen ga Hannatou na kawo maki har gida, da da Yah Mommy za mu zo amma bata samu zuwa ba"( Yah Mommy ita ce babbar yayar su)
"Allah sarki sannu da zuwa Hannatoun mu yau dai gani ga Hannatou"
Se na lankwasa harshe na yi kamar yanda Hafsah ke kiran ta, dariya mu ka yi duka mu ka faɗa sashe na, nan fa na buɗe fridge na d'akko lemon fata da ruwa na zauna ina yanka musu lemon fatar mu na hira, dake na kan ɗan ba wa Hafsat labarin Maman Ameerah musamman in ta min wani abu da ban ji dad'in shi ba kafin na tafi makaranta se ya zamana to Hafsat ta san ta kuma Hafsat kan kawo min ziyara lokaci zuwa lokaci, nan take ta hau tambaya ta,
"Shin Aunty mi halan na ga mutane?"
"Hummm wai mutuniyar ki ce za su tashi shine ba a sanar da ni ba se yau da za a tashin"
"Yeeeeeeeeeehhh Alhamdulillahi gwanda su tashi wallahi mu...."
Da sauri na katse ta na ce,
"Ki yi a hankali kar su ji mu na murna za su tashi,"
"Ai wallahi wannan abun murna ne dole mu yi murna,Allah ya kai lahiya."
"Bana so na bi su wallahi gashi su na jira na za a je can sabon gidan"
"Ai kuwa ba za ki bi su ba, mu na nan ba yanzu za mu tafi ba"
Dariya na dinga yi saboda murna muna hira, nan take kuwa Hafsat da ta ji mutane sun fita alamar za su tafi, se ta miqe ta ce,
"Tashi mu je waje, Hannatou taso taso"
Waje mu ka je ina biye da su baki na har kunne, Maman Ameerah ta so dasan baqin ciki da tunanin anya banda wani mugun halin da ya sa kowa ke gudu na da nuna min qiyayya? Sai gashi Allah ya wanken zuciya da zuwan Hafsat, hamdala na yi a cikin rai na, se na ji Hafsat na faɗin
"Ni fa dama zuwa na yi ki sa min albarka an sai min mota, gata can waje mu je ki gani"
Hannu na ta ja with so much excitement mu ka ɗauki hanyar waje, Shuraim ne ya gan ta ya tafi da gudu yanda yake yi in ta zo ya dale ta ya na kiran sunan ta, daga shi ta yi ta na masa wasa sannan ta ajiye shi muka fara takawa, mata ne sun kusan biyar a jikin motar maman Ruqayyah se Baban Ameerah da mijin Naman Ruqayyah se Yah Maheer wanda ya dawo shima ake sanar da shi a wannan lokacin, se uncle Inuwa sannan yara qanana ana so a shiga mota a tafi sabon gida.
Ido ne ya zuba a kammu mu kuwa mu ka yi kamar bamu san su na kallon mu ba, Hafsat se magana take cikin murna (halin ta ne wannan she is always jovial)
Mun zo daf wajen su Maman Ameerah Hafsat ta ce,
"Da kyar na iya kawo mu nan, se a hankali zan kware inshaa Allahu,"
"Sosai dama komai a hankali ake iya shi har a kware," na fada ina taya ta murna.
Tsaya wa na yi na ce,
"Tafiya za ku yi? To Allah ya kiyaye Suwaidatu zata bi ku ta ga waje mun zo daga baya, na ga ma ba waje ko da na ce zan bi ku,"
"Haka ne to se kin zo,"
"Mota ta na zo na nuna mata ta sa min albarka," in Ji cewar Hafsat da suka saba gaisa wa da Maman Ameerah in ta zo waje na, na tabbata ko a baya da ta san yanda zata yi ta raba ni da Hafsat da ta yi, amma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 30