Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ban sake ganin kowa ba, a tsorace jiki na na rawa na tashi na kunna fitilar wutar lantarkin da ke d'akin cikin hukuncin Allah har na juya zan koma gado aka kawo wuta Da sauri na bud'e qofa na je parlour na d'akko DVD na wadda ke fitar da sauti ko ba TV, plate d'in CD na saka na karatun al'qurani cikin qira'ar Shaikh Abubakar Shad'iri, suratul baqara na tashi ina jin hankali na na kwanciya, ina nan zaune yanda na ga rana haka na ga dare. Ina nan zaune da safe Addah ta dawo daga gidan Maman Humairah ta yi min sallama sannan tace.......... Na gaji da typing aradu...sakamakon tafiyar da na yi ya sa yanzu bana typing da yamma sai da safe gaba d'aya rubutun ga ya gudu da baccin safe na😭 Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love πŸ’• all. πŸ’… MAHREEN πŸ’… WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 15: "Mahreen kin san yanzu haka daga gidan Maman Humairah nake? Mu na hira take bani labari shine na ce bari na zo na fad'a maki, duk da dai na bata amsa" "Me ya faru Yaayah Maimunah?" Cikin qaguwa da son jin labarin na ke tambayar ta, Maimunah ta gyara zama ta kalle ni sannan ta ce, "Maman Humairah ke tambaya ta wai jiya da daddare da misalin sha d'aya na dare da 'yan mintuna Baban Humairah ya fito zai rufe musu gida ya na tsaye ya na addu'a a jikin qofa se ya hango wata mata da lullub'i durqushe a jikin windown kitchen d'in ki,se ya fara tunanin ko d'aya daga cikin mu ce ta yi fad'a da mijin ta shine ta fito waje? Tinani ya yi ko zai kira Maman Humairah ne ta je ta tambayi matar in ta ji mune kuma matsala aka samu se su shiga a daidaita, ba a bar mace a wannan daren ita kad'ai a waje ba, qifta idon nan da zai yi ya sake bud'e su akan matar se ya ga wayam ba kowa, abun ya yi mugun bashi mamaki, har bud'e qofar ya yi ya ga ko zai hango ta tana shan kwana amma be ga kowa ba, shine na ce mata gaskiya ba mu bane, dan ke mijin ki ma baya nan, ni kuma lafiya qalou muka kwana da Yaya,wataqila wata ce ta tsaya amma ba mu bane," Wani irin abu na ji ya dira akai na me nauyi na tashin hankali, 'To ko dai matar da ya gani bayan ta ga an gan ta shine ta shigo min d'aki na? To wacece? Aljana ce ko mayya ko me?' Nan da nan tsoro ya kama ni, tinanin mafita ya baibaye ni, ya zan yi na kub'uta daga maimaituwar abinda ya faru daren jiya? "Amarya ki na ji na kuwa?" Cikin in ina da saurin baki na amsa ta da, "Uhmm...ehhh...ina jin ki...gaskiya dai ba...baaa mu bane...wataqila wata ce zata wuce se ya gan ta" "Nima dai haka na ce mata," Hira muka ci gaba da yi, wadda fiye da rabin ta hankali na baya kai sam sam. A haka na qarasa satin nan ba wani sukuni, babu bacci, babu nishad'i,kuma na kasa sanar da kowa, na kasa sanar da Yah Maheer saboda kar hankalin shi ya tashi gashi ba a kusa yake ba ya na nesa, na zama kamar wata bugaggiya saboda rashin bacci, qasa da saman ido na ya yi dark circle saboda rashin bacci, gani kullum cikin kasala nake. Ranar juma'a da ta kama ranar dawowar Yah Maheer ban b'ata lokaci ba wajen shiga kitchen na tsara masa abinci daidai qarfin mu, sannan na sha wanka na fesa kwalliya, masha Allah nan da nan se ga Mahreen mara nutsuwa a 'yan kwanakin baya ta d'auki saiti, Maimunah kuwa tsokana ta ta hau yi wai yau Oga ze dawo kenan shine aka sha kwalliya haka. Murmushi kawai na saki a sanda na ji hakan, da misalin qarfe sha d'aya na rana sai ga sallamar Yah Maheer ta karad'e kunnuwammu, cikin tsananin murna da d'okin ganin shi na fita daga parlour na tsaya a bakin qofa ina jifan shi da kallon na yi kewar ka, leben baki na ne ya fara rawa sannan ya kyab'e irin na shagwab'abbun nan masu son yin kuka,lokaci d'aya nan da nan ido na ya cika da hawaye ya fara sintiri a kumatuka na masu yalwa, kai kawai ya ke kad'a min alamar ah ah kar na yi kuka, da sauri na qarasa na rufe tazarar da ke tsakani na da shi, ya kuwa sake jakar shi a qasa ya rungume ni, mun kai mintina biyu zuwa uku a haka kafin na duqa na d'auki jakar tashi mu shiga d'aki,sabuwar maraba Yah Maheer ya karb'a daga waje na, sannan muka zauna a bakin gado, hannu na sanya na cire masa hular shi sannan na b'alle masa mab'allin rigar shi, wuyan shi ya samu sassauci daga matsewar da ya yi. Da kyar Yah Maheer ya barni na tashi na kawo masa ruwa da abinci, babu b'ata lokaci kuwa ya hau ci ya na santi, ya na tsaka da cin abincin su Suwaidatu suka dawo daga makaranta da misalin sha biyu da rabi, gaishe shi suka yi suka shiga suka d'auki kayan su da za su sauya,nan ya dinga tambayar su ya makaranta da bayan rabuwa su kuma suna bashi amsa. Abincin su suka je suka dauka suka hau ci, daga baya suka yi wanka, an kawo wuta suka kunna TV suna kallo,ni kuma ina can wajen Yah Maheer wanda bayan ya kammala komai ne ya je ya yi wanka shima, kafin ya dawo ya tarar ina wani irin baccin da se da ya zauna ya na mamakin irin baccin nan, domin kuwa ni macece da ko iska ce ta kad'a sosai sai na farka balle a dinga hayaniya ko a motsa qofa ko wani abu dai haka amma se gashi har tashi na ya dinga yi akan na je na yi wanka na kasa tashi, kyale ni ya yi ya sake rufa ta da kyau ni kuwa na qara gyara kwanciya ta na ci gaba da bacci na. Abu kamar wasa zan tashi ne qarfe biyu, zan tashi ne uku shiru, Yah Maheer ya gaji da shirun ya sake komawa tashi na nan ma shiru, qarshe da ya dame ni se na saka masa kuka sosai, ina kuka na ce, "Ni ka kyale ni na yi bacci na, tinda ka tafi bana iya bacci da kyau se yau, tsoro nake ji, tsoro ake bani, ina firgita bana so na rufe ido na,ina jin tsoro" Tsananin kukan da nake ne ya sanya jikin shi yin sanyi qalau, nan take ya rungume ni sosai a jikin shi ya na qoqarin hana ni jijjigar da jiki na ke yi saboda kuka da alamar tsoro da nake dauke da shi, da kyar ya samu na lafa da kukan, be ce min komai ba ya ce na je na yi wanka na zo. Ko da na yi wankan na koma d'aki sai na tarar ya gyara gadon ya koma parlour, murmushi kawai na yi na sauya kaya marasa nauyi, na bi shi can muka zauna ana hira ana kallo har lokacin la'asar ya yi muka je mu kai sallah. Da dare kuwa haka na dinga shirgar bacci har da munshari, dan kuwa washegari Maimunah se da ta sanar da ni ta jiyo munshari na abinda bana yi, na ce mata, "Tsabar bana bacci ne kwana biyu, yanzu ya dawo se na ji banda wata damuwa alhamdulillah, kuma tsoron da nake ji da abubuwan da nake gani babu" "Alhamdulillah haka ake so ai" **************************** A kwana a tashi har na kai watanni shida a gidan miji cikin damuwa da tashin hankali tsoro da firgici, domin kuwa da ya sa qafa ya yi tafiya zan dinga gani da jin ana tsorata ni,watarana haka zan ga mage a d'aki na ko a parlour wanda bamu da ita sam sam,sannan ko ina a rufe yake ba ta inda za ta shigo,da na tsorata sai in neme ta in rasa,akwai sanda ni da yaran muka ga magen lokacin ba wuta sun dawo daga deb'o ruwa sakamakon wahalar ruwa da ake,gaba d'ayan mu muka haye kujera muna ihu, ana sake haska fitila muka neme ta muka rasa, jiki na banda rawa ba abinda yake yi tsabar tsoro, dikkan mu mun tabbata ko ina a rufe yake to ta ina ta shigo? Ire-Iren tambayoyin nan ne a cikin zuciya ta a koda yaushe a cikin gidan nan, dan haka nake zama bani da sukuni har se ya dawo. Kar ku ce wai bana addu'a, inaaa, addu'o'in da nake ba kad'an bane, amma se na hakura na sanya wa raina jarabawa ce watarana sai labari. Daddad'an labarin samun cikin Maimunah ya sanya walwala da fara'a da nishad'i a zuciya ta, ta yanda na nemi rabin b'acin raina na rasa, a koda yaushe bamu da burin da ya wuce mu yi ta shan hira ana maganar abinda ke cikin cikin nan. Ta bangare guda ni kuma se na d'auki tsahon watanni ban period ba, dan haka be fi sau biyu na yi period ba tin da aka min aure har tsahon watanni bakwai, na qarshen ma da na yi se da muka je asibiti aka bani magani, na kuwa dinga zubar da jinin har ya so ya yi yawa ma,dan kuwa haka jinin zai balle ya dinga zuba min guda guda kamar wani tuwo, daga qarshe se na dinga tinanin anyaaa wannan jinin haidha ne kuwa? Ga yawan kwanaki da yake d'auka kafin ya tsaya. Watarana Maimunah ta tashi da naquda amma da suka je asibiti aka ce musu false labor ne se suka dawo, haka ta dinga yi a tsattsaye har Allah ya kaimu ranar da abun ya zo mata da gaske, daga qarshe na raka ta asibiti ta haifi yaron ta masha Allah kyakkyawa babba, bayan wasu awannani muka dawo gida, me wanka aka aiko mata daga gida da take kula da mai jego da jariri. Bayan suna da kwana takwas muna kwance da Yah Maheer muna hira, se bacci ya dauke mu, muna tsaka da bacci na ji wani irin ciwon ciki wanda azabar shi da zafin shi ba zai fad'u ko ya misaltu ba domin ba zan iya fad'ar ya na ji ba a lokacin,babban abun mamakin shine wannan azababben ciwon cikin na ji shi ne a qasa da minti d'aya, dan kuwa ina jin ciwon cikin na ji kamar an hankad'o ni qasa na fad'o daga gadon, kafin na d'ago daga duqen da nake Yah Maheer ya iso gare ni dan taimaka min ciwo ya tafi, sai kawai na ji kamar an zare min wani abu a ciki na bana jin komai na ciwo sai zufa da ke karyo min, salati na dinga yi ina tasbihi ga Allah, tsananin mamaki da tsoro duk sun baibaye ni, wannan wanne irin ciwo ne me tsananin azaba da qarancin lokaci? Bayan na bayyana wa Yah Maheer me ya faru sai ya ce na shirya zuwa yamma mu je asibitin Malam Idris na dutsen tanshi, haka kuwa aka yi, bayan kammala duk necessary abubuwan da ake yi kafin a ga likita se muka shiga ganin likita, nan da nan aka hau gwaje gwaje da aune aune aka deb'i jini na wanda na bayar aka d'iba da kyarrrr saboda tsabar tsoron allura da nake yi. Muna zaune aka je akai gwajin ciki, malaria da dai duk abinda suka ga ya dace a yi. Duk gwajin da aka min ba a ga komai ba, dan haka se aka rubuta mana scanning likita yace mu dawo gobe a yi, haka muka sake dawowa washegari aka yi scanning aka gama, nan ma ba a ga wata matsala tattare da ni ba, sai dai kawai likita ya ce akwai matsala na ovulation amma za su bani magani da izinin Allah zai daidaita, da na fara ovulating da kyau duk wata matsala za ta kau kuma in da rabon na haihu Allah zai kawo rabo. Har ga Allah a wannan lokacin kunyar masifa nake ji in ji an ce zan haihu,ga kuma tsoro, se in dinga ganin kamar ba zan iya ba, ni ban kai in haihu ba na yi qarama da yawa, ni kaina har a wannan lokacin Yah Maheer lallab'a ni yake kamar jinjira to ta ina zan fara kula da wani jinjirin? Addu'a na dirfafi yi tin a wancan lokacin, 'Ya Allah idan yara alkhairi ne a gare ni da addini na da miji na Allah ka bani, idan babu alkhairi Allah ka min sauyi mafi alkhairi ka sanya min hakuri da juriya da dangana" Kamar abun wasa har na kai watanni takwas ban tab'a ko da b'ari ba, sai dai wasu lokutan sai in dinga zargin kamar ciki ne da ni, haka sauran mutane ma, dan kuwa duk wani sauyi da masu ciki ke gani a tattare da su ina gani, har kwad'ayi da tsirfar ina son kaza bana son kaza,wani jin wari da qamshi,bana son warin risho, ina son qamshin d'aki na i don't mind spending the whole day in my room, hatta da Yah Maheer wasu lokuta bana son ya zauna kusa da ni, wani lokacin kuma ko motsawa daga inda nake bana so ya yi ballantana ya barni ni kad'ai, na fi so na saka kaina jikin armpit din shi ina shaqar qamshin turaren shi da ya had'e da na jikin shi, ko kuma in shaqi qamshin wuyan shi,haka zan manna kaina a jikin shi ina shaqar qamshin turaren shi na Calliope kamar shine abinda na fi so da qauna a kaf duniyar, lokuta da dama in nayi hakan sai mamaki na ya kama shi, ni kaina mamakin kaina nake, da zarar abu ya yi nisa ciki na ya taso irin na masu ciki muka dunguma zuwa wajen likita a duba sai kawai na dawo ina zubar da jini kamar an kunna pampo,tinda na kula da baqar wahalar da nake sha da Yah Maheer ya ce a je asibiti zan hau kuka ina cewa ni dai ba zani ba, har watarana ya ji haushi ya dinga fad'a ya na cewa, "Waini Babyna da ki ke rantsuwar baza ki sake zuwa asibiti ba ni da ke waye babba?" Cikin tura baki da shagwab'a na ce, "Kai ne mana, amma kafin ka qarasa ni na rantse da Allah ba inda zan sake zuwa na gaji da jagwalgwala ni da ake " "Za kuwa ki je asibiti kin ji na fad'a maki, gwanda ma ki tanadi lokacin yin kaffarar rantsuwar ki" Cikin kuka da buge bugen qafa na miqe na bi shi saman gadon da ya koma na kwanta jikin shi ina ci gaba da kuka da tirje tirje, na ce, "Ni wallahi ba zan je ba, ba inda zan sake zuwa se dai a dauke ni ta qarfin tsiya a kai ni" Kuka nake sosai wanda tun ya na jin haushi na se da ya dawo ya na lallashi na tare da nuna min amfanin zuwa asibitin, ni dai na kafe na ce ba wanda ya isa ya sa na sake zuwa asibiti, haka ya kyale ni ban kuma dena kuka ba se da bacci ya d'auke ni. Ranar litinin da sassafe ya gama shirin komawa qauyen Bura na rako shi har qofar gidan mu, muna tsaye muna hira, daga qarshe muka yi sallama ya kama hanya ya tafi. Ni da Maimunah kuwa muka dasa hira, yaron ta ne ya fara kuka kamar abun wasa sai kashi muka ga ni ya na zuba daga jikin shi kamar ruwa, ba wata alama da take nuna wannan kashi ne da ya wuce jurwaye da rigar ta doguwa kalar milk ta yi. Cikin damuwa na kalle ta na ce, "Lafiya yaron nan ke irin wannan kashin?" "Wallahi bashi da lafiya ina ga ma asibiti zamu kai shi bari na kira Yaya, yaron nan na buqatar cikakkiyar kulawa," Daki ta je ta kira wayar mijin ta, babu bata lokaci kuwa ya dawo suka dunguma asibitin malam idris. Yaro ya samu kulawar da ta dace sai dai duk qoqarin likitan dan neman jijiyar yaro a sa masa ruwa abu ya gagara, gashi yaron ya wahala jikin shi ba kwari, Maimunah ta ci kuka ta qoshi saboda yanda ta ga ana huda mata jikin yaro, da kyar suka sami jijiya akan shi, aka masa aski aka sa masa ruwan ta nan. Ina ta tunanin shin in je ne ko kuwa yaya? Har muka yi waya da Yah Maheer ban sanar da shi maganar ciwon yaron ba ballantana na zuwa wajen su. Washegari kuwa da muka tashi sai na yi tunanin anya ba zan kai musu ko da ruwan zafi bane? Tinda muna da shago Abubakar anan yake zama se in d'an hada da Lipton da sugar, ai kuwa ba tare da doguwar shawara ba na cika flask da ruwan zafi na kwashi kayan tea na d'au hanyar zuwa asibitin Malam Idris wanda bamu da nisa sosai da sosai, amma dai akwai 'yar tafiya a tsakani, ko da na fita babu kowa a hanya, ina tafe ina addu'a saboda tsoron da nake ji,ko da na isa se na tarar da Maimunah duk ta fad'a nan da nan tausayin ta ya kama ni sosai,se na tina sanda ta na da ciki, saboda ganin wahalhalun da ta dinga sha ya sa da na je kano ganin likita a Aminu kano teaching hospital in na ga me ciki se in ji kamar in je in taya ta riqe cikin, wata iriyar sabuwar soyayyar Mama ce ta qara shigata a wannan lokacin, dan haka a yanzu ma da na gan ta se na saje jin wannan yanayin da na shiga a baya. Se da na je na ga yaron ya na kwance gwanin tausayi sannan muka fito muka tsaya a waje ni da ita, ai kuwa muna tsaye muna hira se na ji wani abu me d'umi ya na bin qafata, ina saka hannu na tabo cinya ta dikkammu se muka tsorata, jini ne ke bin jiki na me mugun yawa kamar an kunna tap, nan da nan na yi wa Maimunah sallama na bar asibitin, ko da na fita na fara ganin mutane sama sama, sauri na dinga yi dan isa gida da wuri, iya sauri na iya yanda jinin ke tiltilowa daga jiki na, gefe na samu a hanya na tsaya na waiga ko ina ban ga kowa ba, zanin jiki na na kunce na tare gaba na saboda ya dena zuba a hanya, na sa sauri se gida,Allah ya taimake ni a ranar hijabi baqi har qasa na sanya se d'iban qura yake. A haka na isa gida, ina zuwa na tadda Hauwa'u a tsakar gida ta na wanki, cikin wata iriyar murya da ke son yin kuka a kowanne lokaci na ce, "Kawo min ruwa," Buta ta miqo min, ganin ruwa a buta kuma ni ba anan nake so ba, gashi bana son yin magana saboda damuwar dake raina kawai se na fashe da kuka, na d'aga murya yanda zata jiyo ni na ce, "Dan Allah ki miqo min ruwa a bokiti mana" Da sauri Hauwa'u ta je ta deb'o ruwa sosai a bokiti, ta na miqo min na ce ta dakko min kaya a d'aki na sauya. Kafin ta dawo kawai se na yi tsaye ina ganin ikon Allah, ina kallon yanda jini ke zuba a jiki na kamar a mahauta/mayanka, yanzu wannan jinin da ajiki na yake ai da mutuwa zan yi, nan take na tabbatar da maganar Mama a duk sanda na je gida ganin likita akan matsala ta, takan ce, 'Wannan jinin ba jinin jikin ki bane ba kuma na haidha bane, da jinin jikin ki ne da tini kin rasa ran ki ko ki na kwance ana qara maki jini,' Jinjina kaina na yi ina sake gasgata maganar ta, ganin wani qaton gudan jini ya fad'o, sannan me ruwa ya biyo baya, kuma gani kyammm ba alamar jiri ko wani rashin kwarin jiki balle na ce ko a jikin nawa yake fita. Se da ya yi haukan zuban shi ya tsagaita sannan na gyara jiki na na dauki zanin nawa na cukuikuye na yar ta katanga, domin a lokacin nan banda wani isasshen hankalin rashin ganin dacewar abinda na yi, gani nake kawai ba zan iya wanke wa ba, sannan ruwa bokiti nawa zai ci in na ce zan wanke? Haka na fito na wuce d'aki direct, Hauwa'u na tausaya min, parlour suka koma suka zauna ni Kuma na hau bacci. Ban farka ba sai da na ji muryar mutane a parlour, ko da na duba se na ga ashe baqi muka yi, a hankali na saci jiki na je band'aki na sake gyara jiki na, domin hatta gado na se da ya b'aci da jinin, kwata-kwata bana so na yi baqi in ina a irin wannan halin, haka muka gaisa da su sama sama suka tafi. Zuwa cann yamma sai ga su Maimunah sun dawo an sallamo su, haka muka qarasa jinyar kammu baki d'aya, dan kuwa sai da ta yi zazzab'i dan zaman asibitin da ta yi. Kwana na hud'u jinin nan na zuba sosai, be tsaya ba be ragu ba, mamakin ta inda yake fita duk ya ishe ni ya dami zuciyata, gashi na kasa sanar da Yah Maheer saboda baya gari, ko waya muka yi gida se dai in ce bana jin dad'i amma na kasa sanar da kowa matsala ta. Watarana Addah Firdous ta kawo min ziyara, nan muka sha hira ta kawo min kayan mata da kayayyaki na sa wa na gayu, bata tafi ba sai da akai azahar, na raka ta har bakin qofa na dawo. Kallon maganin matan na yi kawai na yi murmushi saboda na sha gwada shan su amma ba sa min aiki, dan kuwa da na sha yamma ta yi se jini ya balle min, tattara su na yi na ce na bawa masu buqata, amma akwai wata zuma dana d'and'ana na ji zaqi se na maqale na qi ajewa nai ta sha, saboda ina mugun son zaqi ni, ban dire robar ba se da na shanye tasss. Washegari ya kama juma'a ranar Yah Maheer ze dawo, tin da asuba nake gyare gyare da qalqale qalqale hatta da dustbin d'ina se da na wanke da makwashin shara, bokitai da butoci na sai da suka sha wanki na musamman,na taka kujera na goge fan da kwayayen fitilu na, sannan na saka farin tsumma na goge kayan d'aki da parlour na, yana kuwa dama bana barin ta sam-sam a gidan. Bayan na gama gyara d'aki na na kunna turaren wuta na qara da na tsinke,kafin na yi wanka na yi duk wani shaving a inda ya dace na yi wanka qal fes, se na d'aura alwala na koma d'aki, daga cikin kayan da Addah Firdous ta bani na zab'i wata riga pink me santsi, iyakar ta cinyoyi na, na gyara gashin kaina na feshe jiki na da turare na shafa humra, sannan na d'auki sweet na jefa a baki na na zumbula qaton hijabi na fito parlour, Maimunah ce ta yi sallama ta shiga, "Kaiii Amarya ki na kashe mu da qamshi" Maimunah mace ce lamba d'aya wajen tsafta, dan kuwa na koyi abubuwa da dama a wajen ta nima, amma a haka se ta dinga yaba qamshi na da tsafta ta. Ta dan jima muna hira da ita da aka kira sallah se ta tafi, ni kuma na sa yaran suka tashi suka yi sallah, tinda ni dai ban ma san matsayi na ba, jinin da nake zubarwa sam be yi kala ko kama da na haidha ba in any way, kuma ina tsoron in yi sallah ya zama na yi sab'on Allah, rasa yanda zan yi na yi se na ce bari na aje sallah har se Yah Maheer ya dawo ya sama min mafita, haka nan na ji zuciya ta ta karye da na tina irin wahalhalun da nake sha, hawaye na ji ya zuba a ido na, da sauri na hau gyarawa saboda bana so kwalliya ta ta b'aci. Kafin yaran su idar da sallah Yah Maheer ya sallama ya shigo, da murna na tafi na tarbo shi kamar yanda na saba, cikin alamun nuna sauri ya tarbe ni sannan ya ce, "Young Lady had'a min ruwa na yi wanka ban samu na tsaya akai sallah da ni ba," Da sauri na kai masa ruwa ya tafi ya yi wanka, kafin ya dawo

Chapter 12 of 30