da cewa ya zo da baqi se ya koma wajen su ya zauna.
Ba jimawa na shiga parlourn wanda tun shigowar su cikin daga murya da hayya hayya abokin shi ke faɗin ,
"Ina uwar gida kuma amaryar take? Madam Allah ya kashe ya baki ke kam kin gama aure mana abokin mu ba shi iya maganar ki ko a waje ne, Allah ya kashe ya baki Madam ki yi yanda ki ka so da shi"
A zaton su zan fito ina washe baki ina hayaniya ina nuna masu na ji dad'i, ko kuma in kuranta kai na in wasa kai na, ni a dole na mallake miji, sai na basu mamaki ta yanda har abokin shi da ya dage se an zo be boye mamakin shi ba, baki suka buɗe su na kallo na tare da amsa min gaisuwa ta kamar i am the most adorable thing they have ever seen in the world.
Domin kuwa ina buɗe qofar da sallama na buɗe ta muka shiga ni da Suwaidatu tare zubewa muka yi a gefen kujera kai na na qasa ina murmushi na me kyau saboda ba zan qarya ba na ji daɗin yanda abokin shi ke ta yaba ni yake kuma nuna cewa Yah Maheer fa nawa ne ni kaɗai, ji nake kamar na masa kyauta.
Gaishe su mu ka yi cikin nutsuwa da kamala sannan na musu sannu da zuwa na miqe na shige ciki, ban sake komawa ba se na aika Suwaidatu da qarin spoons a qaramin plate saboda ni da hannu nake cin abinci, shi yasa Suwaidatu ma ke ci da hannu ta na kwaikwayo na, Yah Maheer kadai ke cin abinci da cokali.
Abinci suka buɗe suka ci,banda santi ba abinda suke zuba wa, abokin Yah Maheer fad'i yake ya na kuma wa,
"Tabbas dole ka riqe matar ka da daraja da mutuntawa,dan wannan duk inda ta fito ta fito daga gidan mutunci, akwai sanin ya kamata, mace irin wannan ba wadanda za ka je ka na maganar su a waje bane, ai se kishin mu na maza ya motsa wani ya ma qafar baya, Allah ya qara baku zaman lafiya Ya Malam Allah ya albarkaci auren ku ya baku 'ya'ya na gari"
"Ameeen ya Allah, dama na sanar da ku, in dai ku ka gan ta da kan ku sai kun yaba"
"Tabbas mun yaba, ni da ta na da 'yar uwa ma da an bani"
Dariya suka sanya baki ɗaya, sannan suka rage abincin basu cinye duka ka ba kamar sun san shi kadai gare mu, suka ce za su tafi ya kira ni mu yi sallama.
Sake leqawa ya yi zai kira ni se ya ganni na shige ramin da akai na pampo ina ta tsalle da wasan ruwa a ciki, kasa riqe dariyar shi ya yi ya ce,
"Ai se ki fito yayun naki za su tafi,"
Tura baki na yi cike da shagwaba na miqa masa hannu kamar yaron da ya ga maman shi ya na so ta ɗauke shi, girgiza kai ya yi ya na dariya sosai ya qarasa fita inda muke ya fito da ni ya na faɗin,
"Allah ya shirya min Mahreen dita"
"Ameeen Allah ya shirye mu baki daya"
"Ameeen"
Har na saka qafa zan shiga daki na dakko hijabi na se na kula ashe be rufe qofar parlour ba,wata iriyar kunya ce ta kama ni na koma baya da sauri ina jiran ya rufe qofar na wuce tare da fatan Allah ya sa ba su ga qafata ba.
Cikin jin nauyin su na koma dan mu yi sallama daga bakin qofar na tsaya na ce,
"Mun gode da ziyara Allah ya bada lada, a gaida iyali"
Yah Maheer ne ya qunshe dariya sannan ya ce,
"A se dai gaida gado da katifa yayun naki har yanzu searching suke"
"To Ubangiji Allah ya bada abokan zama na gari, ku gaida gida mun gode"
Godiya suka dinga min da yaba min sosai sannan suka ba wa Suwaidatu dubu bibbiyu, suka tafi.
Fitar su ke da wuya na dinga tsalle ina murna ina jin daɗin yabon da suka min, bayan Yah Maheer kuwa ya dawo ya sanar da ni yanda suka dinga yabo na sai na sake jin dad'i ina ganin ashe ni din ma na kai wadda za a yaba wa.
A ranar na je kasuwa da kuɗin nan na qaro mana kayan abinci.
*******************************
Wata ranar Laraba na tashi ban da lafiya, ina jin zazzaɓi da ciwon ciki na so na doje na qi zuwa asibitin da Yah Maheer ke ta nanata min zan je a daren ranar ni ɗaya saboda ya na da lecturen safe,haka ya sa ni dole na tafi asibitin ni daya gashi bana son zuwa asibiti ni daya na riga na saba komai shi yake taya ni yi ban saba yin abubuwa da kai na ba.
Ai kuwa tin da na je na tarar da layi kamar ranar ce ranar Litinin tunda an fi cika ranar Litinin, dan haka layi na dinga bi,ga zazzabin se qaruwa yake yi.
Da kyar na samu na ga likita, daga tambayoyin da ya min se ya ce na je a min wani test wai shi virginal test na kawo masa result yanzu ya na so ya gani kafin ya bani magani.
Ji na yi hankali na ya tashi, ga kuɗin da aka zayyano zan biya bamu da su, ga ciwo na ci na, dan sai na ji kamar an qara min zazzaɓin ne da ciwon cikin, ina kuka sosai na kebe na kira Yah Maheer dan in sanar da shi halin da nake ciki a asibitin.............
*A yi hakuri....an hana ni tsayawa akan gab'ar labari😂ni ɗin ce se a hankali bana jin magana😂💃...Ni fa wallahi comments na min kaɗan, ina so yanda na gaji da dogon rubutu na gaji da karanta comments....to dai ku sani iya comments iya typing less comments a ga dan qundun uban lalaci yasin ah toh...yo shi ne takin marubuta*
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Mai so a sanya ta a group ɗin MAHREEN2 paid book ta min magana ta wannan No 09031416423*
PAGE 34:
Ina nan zaune se na tuna irin wannan abun ya taɓa faruwa da ni a Kano, wata shekarar da kawun Yah Maheer ya rasu(Baba dan Juma Allah ya masa rahama)ana ta'aziyya ciwo ya turniqe ni dole na zame jiki na koma gefe na kira Yah Maheer na sanar da shi zani asibiti, dubu goma sha takwas ya zaro ya bani tare da bani hakurin ba zai samu damar raka ni ba saboda mutane da ke zuwa musu ta'aziyya, nuna masa na yi babu komai amma can qasan rai na a tsorace nake, na riga na saba komai zan yi ya na biye shi ke min jagora bana son yin abu baya nan, se in dinga jin wani tsoro na shiga ta,haka na daure na tafi asibitin na bi dogon layi kafin na ga likita, bayan na gan shi ne ya rubuta min testes da za a min na jini guda uku na masa godiya na fita, wajen da ake biyan kudi na je na tadda mata jingim a wajen se gefe layin maza ne amma ba su da wani yawa,ina nan na bi layi na sakankance kuɗin hannu na zai ishe ni, har aka zo kai na, bayan sun karbi takarda ta su ka sanar da ni kudin dubu goma sha tara zan biya, ji na yi gaba na ya yanke ya fadi, domin kuwa kudin waje na dubu goma sha bakwai da dari takwas ne ya ragu na taɓa na yi kuɗin mota.
Sanye nake da niqabi sai na ji zufa ta wanken fuska, tini na fita daga layi na koma gefe ina tunanin makama, dan na tabbata ko na kira Yah Maheer d'aga masa hankali kawai zan yi,ni ba account No ba a lokacin balle a tura min na cire ta POS wa ma ya san da POS time din, sam ban san da zaman shi ba a duniya,na san ba shi ma da shi tunda na san aljihun shi, tunani na yi dama ni da Yah Shamsu muka saba zuwa Aminu Kano duk sanda na zo shi ke rako ni in dai ba da Yah Maheer ɗin na zo ba, yawancin likitocin ma da nake gani abokan Yah Shamsu ne, nan da nan na kira shi ina daga zaune a gefen wasu flowers, ya na dagawa na ji muryar shi sai kuka ya kama ni, cikin kuka na masa bayani rarrashi na ya yi sannan ya ce,
'Haba Mahreen ga Sadeeq a asibitin me makon ki neme shi ya baki kuɗin se ki zauna ki na kuka?'
Da niqabi na na goge majinar da ke tarara a hanci na saboda kuka na ce,
'Ba zan iya kiran shi ba, ni bani ma da No shi dan Allah ka kira ka faɗa Masa'
'Akan me ba zaki iya faɗa masa ba? Bari na turo maki No shi dole ki masa magana sanda ba na nan wa zai taimaka maki a asibitin da ya wuce shi?'
Ya Shamsu ba mutum ne mai faɗa ba dan haka yanzu ma cikin lallashi yake nuna min Yah Sadeeq din dai ya kamata na nema hakan ne ya fi dacewa.
Wani sabon kukan ne ya kwace min, nan da nan zazzabin da na ke fama da shi ya qaru, a duniya bana son roqon kowa, bana son na nemi taimako wajen kowa in ba Allah ba, ko Yah Maheer da muke tare ban san in ta ce masa bani bani ba, gashi dai ba na sana'a a wancan lokacin, amma duk abinda ya bani alhamdulillah wanda be ban ba ba na tambaya se idan abun amfanin gida ne da dole sai na tambaye shi kamar su Omo sabulu da sauran su, ko ina jin shagwaba na ce ya siyo min kayan zaqi da na ke mutuwar son sha.
Yah Sadeeq Family friend din mu ne,tare suka taso da Yah Shamsu,abokai ne ko na ce aminai ne, iyayen mu maza abokai ne sosai, dan haka mun ɗauke su a matsayin yayun mu, suma gidan su sun dauke mu a matsayin 'yan uwan su,ni dai ban ji wani comfort na in kira shi na tambaye shi dubu biyu ba se nake jin zai ce na yi roqo.
No shi ce ta shigo waya ta Yah Shamsu ya turo min, ina nan zaune ina shawarar ko gida ma zani ne abu na mu riqe sauran kudin zai mana amfani in mun tashi komawa Bauchin tunda koda yaushe matsala daya ake nuna min, kuma an kasa bani maganin da zai min amfani, ina tsaka da tunanin nan se ga kiran Yah Sadeeq ya shigo wayata, ina dauka na yi sallama, ya amsa cikin yanayin saurin maganar shi ya hau min faɗan ashe ban dauke shi yayana ba,yana asibitin ina neman kuɗi se na kira Shamsu da ma baya gari, to shi ze zo ya kawo min kuɗin? Hakuri na bashi sannan ya ce ya hakura, in je bakin kitchen na asibitin na jira shi, na amsa da toh, nan take na tafi ina share hawaye na ta cikin niqabi na samu waje a bakin kitchen na zauna ina ta duban hanya, a zato na daga ward din da yake aiki zai fito ya tadda ni anan, da yake wajen nasu da nisa, ashe already ya na cikin ma kitchen ɗin ya na jira na, ina nan zaune kusan tsahon minti ashirin da wani abu, shiru ni ban kira ba shi be kira ba, can se na ji an buɗe qofar kitchen ɗin na sake kallon wanda zai fito a karo na ba adadi dan tun zamana a wajen na ke kallon masu shige da fice, ga qamshin abinci da chips na ta dukan hanci na, Yah Sadeeq na gani cikin kayan shi na likitoci ya na tsaye ya na kallo na, da sauri na miqe tsaye ya zo inda nake ya sa hannu a aljihun shi ya dakko kudin ya miqa min sannan ya ce,
'Tun d'azu ina zaune ina jiran ki kira ni na zo na baki kuɗin amma shiru ke ki na zaune ashe ki na shan iska abun ki'
Cikin jin kunya na bashi hakuri na ce,
'Ka yi hakuri banda kati ne na zaci in ka zo zaka kira ni se na sanar da kai na zo'
'Its ok, yanzu ki duba dubu biyun ta ishe ki ko?'
'Eh na gode Allah ya saka da alkhairi '
'kin tabbata ta ishe ki?'
'Eh ta ishe ni na gode sosai Yaya'
'Humm matsa nan ai baki ɗauke ni yayan ba, tunda se da aka kira ni ke ba zaki iya fadan matsalar ki ba, ki na da na mota?'
'ka yi hakuri inshaa Allah zan kiyaye, ina da na mota na gode'
Sallama mu ka yi ya wuce nima na koma wajen da na bari lokacin wata arniya ce a gaba na shige gaban ta zan miqa kuɗi ta zaburo za ta hau min masifa akan na wuce layi na daga niqabi na na zuba mata jajayen ido na da suka gaji da kuka ina mata wani mugun kallo, domin na tsani dama yanda arna ke baro qasar su su zo su na mana gadara da masifa a namu qasar, jira nake ta ci gaba da masifar na wanke ta ta uwa ta uba dan a wuya nake, se nurse ta leqo ta ce su barni akan layi nake zuwa na yi na dawo, se arniya ta fara,
'Ohhh sorry Ma'am'
Banza na yi da ita na miqa kuɗi aka bani receipt na tafi wajen diban jinin,ina zuwa na ga wata 'yar uwar mu ke diban jinin wanda ko ita zan iya tambayar kudin ta bani, kawai se muka hau hira ta na ta dariya dan ta san za a yi drama wajen diban jini na se ta hana kowa ya dauka ta zo ta dinga lallashi na da ban hakuri sannan ta diba ina ta sharben kuka abu na,dariya suka dinga min dan duk dakin diban jinin na fi su qiba yan siri siri ne su ba wasu masu qiba ba, daga baya nima kunya ta kama ni, na dake abu na,ana ganawa na wuce gida da sauran canjin dari takwas ɗina.
Har na gama tunanin abinda ya faru a garin Kano Yah Maheer be zo ba, shawara na yanke kawai zan koma gida tunda lokaci ma ya kusan tafiya bana jin za su min test din a yau se dai gobe.
Fitowa na yi ina tattaki da kyar ni kadai na san me nake ji a jiki na a wannan lokacin, ina tafe ina tasbihi ga Allah wanda ya azurta ni da jinya ya ke kankare min zunubai, na yi nisa na kusan zuwa gate se na hango Yah Maheer a dayan bangaren ya na shiga asibitin, komawa na yi dan be kula da ni ba, wajen da ake aje abun hawa na bishi ya na juyowa ya ganni, duk na fita hayyaci na, ido na ya faɗa ya zurma,tausayi na ne ya kama shi idan shi ya kada ya yi jawur, hannu na ya kama ya na bani hakuri, har sai da ya bani mamaki, na ce,
"Wannan hakurin na menene?"
"Na komai ne Baby na, ki qara hakuri Allah ya na tare da masu hakuri kin ji?"
Daga masa kai na yi sannan mu ka tafi inda zai biya kudi,se da ya gama komai sannan ya ce mu je, ina biye da shi ina tambayar shi inda ya sami kuɗi ya na sanar da ni, tausayi ya bani ban ce komai ba a rai na se na dinga yi masa addu'a ina roqon Allah ya bashi ikon biyan bashin da ya ci, a zuciya ta ina ganin duk jinya ta ta hana shi tara abun arziqi a rayuwa ko ɗan filin nan na zamani bashi da shi balle gida.
Har muka isa ina tunani kala kala, ni ce mutum ta ukun qarshe da suka ce za su yi mana a yau saura su yi hakuri se gobe se kuma in an Kawo na emergency.
Yah Maheer ji ya yi an ce ya je ya suyi condom da hand gloves,mamakin me za a yi da condom ya hau yi, amma dai ya wuce ya tafi siyowa, tunda nake ban taɓa ganin Condom ba ido da ido na ga yanda ake bude shi se ranar, sanda za a min test su biyu ne a dakin kawai mace da namiji ba a barin namiji shi kaɗai.
Ba bata lokaci na hau gadon aka hau yi min test din ana yi ina kuka, saboda daga macen har namijin arna ne, tunani nake shin mata basa iya yin wannan test sai maza? Ina matasan mu ne ? Yanzu ba a karatu se dai a hau social media, yanzu ba a maida hankali a yi karatu dan kishin kai da kishin mata sai dan kuɗin da za a samu da dai mutanen mu sun yi qoqari wajen yin karatu dan addini da kishin mata kuma gashi tsufa suke tafiya suke, next generation ya za a yi kenan? tun daga nan na qudirta da yardar Allah se na zama midwife dan in dinga taimakawa mata 'yan uwa na.
Ana gamawa jini ya ɓalle min sai da su kan su suka tsorata, audiga matar ta bani ta ce in saka,nan take na samu audigar na saka ban iya amfani da audiga zalla ba se jinin ya dinga bin qafa ta, hankalin su a tashe matar ta yi min dabara da kan ta ta yanda jinin zai tsaya iya audigar sannan ta ce mu je se ranar Monday za a karbi result.
Ina fitowa muka haɗa ido da Yah Maheer se kuka ya kwace min, nan take na dinga yin shi kuwa ba bata lokaci, da kyar ya iya lallash na muka fita zuwa wajen machine ɗin mu, na hau muka wuce gida.
Daidai da pad da zan amfani da shi babu sai wani qaramin towel da muke goge jiki fari qal na yanka biyu na yi amfani da shi, ranar wuni na yi a daki ina jinyar jiki na da zuciya ta.
Na tabbata qarfin tawakkali ne ya sa ban kira na shiga uku na lalace ba a ranar nan saboda yanda na shiga damuwa da kuma yanda nake jin tsananin ciwo a jiki na.
Haka na dinga fama da jinya har Monday muka je mu ka karbi result mu ka kai wa likita same treatment da aka saba min tun farkon zuwa na asibiti shi aka sake min, na gaji da shan antibiotics kala kala, daga me sani amai, se me saka ni na dena cin abinci saboda warin shi se wanda ko zufa na yi se na ji warin shi, haka na daure na gama shan maganin.
Waya muka yi da mama nake bata labarin abinda ya faru, se ta ce na ɗauki ruwa a cup na karanta Fatiha qafa bakwai na shanye inshaa Allah jinin zai tsaya kuma zan ji sauqi.
Nan take kuwa na ɗauki ruwa a cup na yi addu'a na shanye, na ji daɗin jiki na amma jini be dauke ba, har sai da na jera kwanaki ina yi ba fashi, se Allah ya taimake ni jinin ya ɗauke.
Shawara mama suka yi da Baba akan ya kamata na je Islamic center inda ake ruqya a min ruqya ko akwai matsalar jinnu a lamari na, ban san an yi ba amma sun tsaida shawarar duk sanda na je Kano za a kai ni Islamic center dan neman magani.
Rana ta qarshe da na je ganin likita a wajen zaman jiran shi na sha sanyin AC saboda layi ya zo kai na ni ce daf da AC, dan haka tun anan na fara tari, ban wani damu ba a zato na normal mura zan yi,bayan na gama da ganin likita na tsaya a shago na sayi Tom Tom na wuce gida.
Ina zuwa na tadda Yah Maheer na jira na ya bani kyakkyawan albishir...............
To jama'a na gaji se zuwa gobe ko jibi inshaa Allahu.
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 35:
"Na ga kana fara'a sosai halan ta samu ne? Yeeeehhhh ta samu Alqur'ani da ganin ɗan bakin nan naka kamar tsohuwa za ta ce yuthuufff akwai magana ciki nai"
Dariya ya yi tare da kada kai, a duniya ya na so ya ga ina barkwanci to fa zai ta dariya se da ya gama dariyar ni kuma na gaji da juye juyen rawar sannan na zauna ya kalle ni ya ce,
"Kai jama'a Allah ya maki sauqi, wato ni dai na zama bani da sirri har abinda ke zuciya ta ma se kin zaqulo shi, to zauna ki ji me ke sa ni murna"
Dariya nima na yi na zauna a gefen shi na mimmiqe qafafu na da nake jin su kamar ba a jiki na ba tin daga qugu na har yatsu na, juya wa kadan na yi mu na fuskantar juna Yah Maheer ya ce,
"Alhamdulillahi... Alhamdulillahi..... Alhamdulillahi....wannan shi ne abinda zan fara faɗa kafin na miki albishir, sannan zan gode miki kema saboda hakuri da ki ke yi da ni ki ke jure babu na da kuma samu na, tohh kin san dai gidan nan ba namu bane kuma ko bajima ko ba dad'e za mu bar gidan nan ko? (Kada kai na yi ina sauraron shi) to Allah ya nufa na sama mana gida a can Alieru quarters amma one bedroom, na so na sake samo mana a two bedrooms ban samu ba three bedrooms Kuma kin san kuɗin ya yi yawa, dan haka daga nan zuwa Monday za mu koma can da zama, kin ga mutanen nan sun mana qoqari, kar tun ana ganin mutuncin mu mu saki jiki mu yi ta zama a zo abu na sabani ya shiga tsakani, sun yi mana abinda ba zamu taɓa manta wa da shi ba har abada, dan haka tun yanzu mu yi qoqari a rabu lafiya ko? Shi yasa ki ka ga ina farin ciki"
Har cikin zuciya ta na samu kai na da farin ciki nima, ban damu da one bedroom da ya ce zamu koma ba, dan na san gidajen area ɗin ba masu munin da mutum zai qi su bane,ba laifi iyaka daki ɗaya ne se parlour kitchen da babbar tsakar gida,akwai ruwan pampo suma kuma akwai wuta, dan haka ba wani abu da nake da buqata da ya wuce hakan, cike da murna na rungume shi ina hamdala, sannan na ce,
"Gaskiya ba abinda za mu ce wa Allah sai godiya, su kuma su Bashar Allah Ubangiji ya biya su da babban gida a aljannah ya saka musu da dukkan alkhairan shi, Allah ya raya musu zuri'ar su da imani, dole ne duk sanda suka shigo gari mu zo mu yi godiya ta musamman har gida"
"Kwarai, ni fa in Ina masu addu'a har rasa me zan roqa masu nake saboda iya rufin asiri sun mana shi a sanda bani da gidan da zan saka iyali na, bani da kuɗin da zan nemi gidan da zan saka iyali na, bani da komai zuciya ta na quna ta na cike da rad'ad'in rashi da mu ka yi na muhalli, bawan Allahn nan ya share min hawaye, dan haka ba zan taba dena yi masu addu'ar alkhairi ba inshaa Allah"
"Gaskiya dai kam Bashar mutum ne har ma da qari Allah ya baka ikon kyautata masa kaima "
"Ameeen"
Hira mu ka ci gaba yi, daga baya mu ka koma d'aki dama kayan mu ba a watse suke ba, kowa kayan shi na cikin jakar shi, inda ni da Yah Maheer namu ke a haɗe waje ɗaya Suwaidatu nata ke cikin jaka, dama ba wani kaya ne da mu ba sosai a gidan, a can gidan Maman Ameenah ne mu ke da sauran 'yan tarkacen mu har da fridge da TV na se DVD, dan haka sai mu ka sanya rana dan na je na kwashi kayan nawa mu kai can inda za mu koma.
Washegari na tashi da wani irin tari busasshe in na fara sai na ji kamar numfashi na zai ɗauke, a haka na shirya muka tafi gidan Mama ni da Suwaidatu, mu na zuwa Ameenah ta tarbe mu hannu bibbiyu Mama ma ta ji daɗin ganin mu haka zalika Baba, gaishe su mu ka yi aka zauna hira,anan nake sanar da su zamu dawo nan, amma can bangaren one bedroom, murna suka yi da jin haka a qalla mun dawo kusa, dan ni a garin Kebbi nan ne nake dauka a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 30