gidan mu, domin Baba ya kula da bana qaunar wanke wanke, sai ya tsame ni daga cikin qanne na ya had'a ni da yayu na muke girki dake Ina da girman jiki na kamo yayu na,kowa da ranar girkin ta, ko Kuma lokacin girkin ta, misali in Addah Ummu ta yi da safe ni sai in Yi da rana da dare a duk ranar girkin Mama, Addah Firdous Kuma sai ranar girkin Ummah take nata, baba baya qin cin abincin da muka dafa tin muna koyo komai cab'a shi da muka yi haka zai ci abun shi saboda ya San koyo muke Kuma shi ke bamu kwarin guiwa lokuta da dama in na Kai masa abinci, ni da kaina na San tuwo bai dahu ba amma haka zai ta yabawa, har na zo na iya.
Hakan ne ya bamu damar Iya yin girkin daidai misali, ta yanda ko baqi akai iyayen mu ba sa Jin nauyi ko kunyar Basu abincin da muka dafa.
Ina aiki hankali na ya na kan Yah Maheer, Allah Allah nake in kammala girki na in je Kai masa abincin safe sai na Sanar da shi amsar tambayar shi a gare ni.
Sai dai me? Ina tsaka da kwashe abinci na ji ana maganar wai ya tafi, Wani iri na ji a raina kamar na fashe da kuka dan haushi, to shi haka ake soyayyar? Ina ganin yanda masu cewa su na so na da aure ke naci da dagiya akan samun karb'uwa Daga waje na ko wajen Baba, amma shi ko ya Jira ma ya samu amsa daga baki na ya wuce.
Haka na gama Shirin makaranta Ina ta danne b'acin raina saboda bana so kowa ya ga zaqewa ta, da ga cewa ana son aure na na fara rawar Kai, har a makaranta bani da wata walwala, tunani na be wuce dalilin shi na wucewa ba tare da ya ji amsa ta ba.
Da rana bayan mun dawo daga makaranta na cire uniform na shiga wanka, na ji Mama na waya amma ban gane da wa take magana ba se da na ji ta ce bari ta zo zan had'a ku, nan take tinani na ya bani Yah Maheer ne,duk yanda na so na ji na yi fushi da shi se na kasa, ba wai dan Ina Jin son shi ba, ah ah, akwai Wani irin kwarjini Allah ya yi masa Wanda zai wahala mutum ya ji tsanar shi ko haushin shi.
Ban tsaya b'ata lokaci ba na qarasa wanka na na yi alwala na fito, d'aki na shiga na duba kaya na na d'auki Wanda zan Saka, Wanda yawanci kayana qananan kaya yafi yawa saboda su na fi Sakawa, idan zan fita ne na ke Saka manyan kaya, amma duk sanda nake gida to fa zaka same ni da qananan kaya ko Pakistan wears, ni ba yarinya bace mai tsahon gashi amma ba na cikin Wanda za a kira da marasa gashi, Ina da gashi Mai laushi sosai da duhu, ban cika son d'aura d'ankwali ba duk kuwa da qoqarin da Baba da Mama ke Yi wajen ganin bamu zama ba d'ankwali ni dai Kam na fita zakka wajen qin d'aura d'ankwali, haka na gama shiri na na d'aura zani na Sanya hijabi na gabatar da sallar azahar, bayan na idar na je na d'ebi abinci na fara ci,Mama ce ta shiga d'akin ta miqa min wayar ta ta ce min,
"Gashi tin d'azu Maheer ke Kiran ki, na fad'a masa baki jima da dawowa makaranta ba, ki Kira shi"
"Uhumm, na gode"
Shine abinda na ce bayan na karb'i wayar na danna Kiran shi tare da Kara wayar a kunne na, sai ringing wayar take ba a dauka ba, se da ta katse sannan ya biyo bayan Kiran, d'auka na Yi na Kara a kunne na, daga can bangaren shi na ji sautin muryar shi a kunne na.
"Assalamualaikum "
Shine abinda ya fara fitowa daga bakin shi, ban Saba da hira da saurayi a waya ba ko a zahiri saboda Baba baya bari,Dan haka cikin Jin nauyin shi na bud'e baki na ce,
"Wa'alaikumussalam, Ina wuni, da fatan ka Isa gida lafiya?"
"Lafiya qlou alhamdulillah, Dan Allah ki yi min hakuri kin ga na tafi kamar yanda na saba da sassafe, Ina so na Isa bauchi da wuri ne shi yasa, yanzu gani na zo a bani amsar tambaya ta ta jiya"
Murmushi na yi Mai sauti, tabbas haka Yah Maheer yake tafiya, zai zo da dare ya wuce da asuba tin kan a had'u da shi, ya fi yin haka idan ya gama abinda zai yi a makaranta se ya shigo ya kwana a nan washegari ya wuce bauchi.
"Ba komai, tinda ka Isa lafiya alhamdulillah"
"Uhummm kin amince ki zama uwar 'ya'ya na Kuma abokiyar rayuwa ta ta har abada?"
Fuskar Mansoor ce ta gilma a idanu na, da sauri na rintse su na furzar da iskar baki na wadda na ji ta d'auki zafi,na sani zai wahala Mansoor ya aure ni a wannan lokacin come on makaranta fa Muke da ni da shi, sannan mahaifi na da kan shi ya ba wa Yah Maheer izinin tattaunawa da ni, Wanda ba kowa yake bawa dama kamar haka ba, alama ce ta ya yarda ya amince da Yah Maheer kenan, dan haka duk abinda Baba yake so ba zan tab'a tsallake shi ba, sannan ta Wani fannin in na duba Yah Maheer ba shi da makusa, to me zan tsaya Jira? Cikin sanyin murya da jin nauyin shi na ce.
"Na amince Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Hamdala ya dinga jerowa, sannan kamar abun wasa na ji ya katse Kiran, bud'e baki na yi galalaaa Ina bin qaramar wayar da ke a hannu na da kallo, to shi wannan haka ake yi? Ba sallama ba komai kawai ka kashe wayar?
Ina Iya tunawa clearly yanda masu neman aure na suke zagewa wajen zuba min Kalaman qauna in mun had'u kafin in ce masu su zo wajen Babana,kuma ko duba qananun shekaru na basa yi haka suke bazan Kalaman soyayya,amma shi, shi kamar be Iya soyayya ba? Haka kawai ba Wani Kalaman soyayya ka kashe wayar? nan take Wani danasani ya shige ni anya ban yi saurin amsar proposal d'in shi ba kuwa?
What if be Iya soyayya da tarairayar mace ba?
What if aka yi auren ya dinga min irin abinda mutanen dauri/da ke Yi, namiji se yanda ya ce da mace ta na qasan kujera ya na saman kujera hard'e kamar Wani sarki, possibilities d'in abubuwan da zai faru a nan gaba na dinga hasasowa, a hankali na Kori dikkan Wani tunani na miqa lamura na wajen Allah akan ya yi min zab'in abinda ya fi alkhairi.
Sati biyu tsakani har na cire ran Baba zai min magana akan Yah Maheer, Ina wanki a tsakar gida na ji Mama ta Kira ni, da sauri na wanke hannaye na na kalli qananan kayan da ke jiki na sun yi guntu da yawa na je d'akin baba haka, se na ja qaramin hijabi na na Saka, na yi hanyar d'akin Baba.
A bakin qofa na tsaya kamar yanda yake qa'ida a gidan mu ba ma shiga d'akin iyayen mu direct ba tare da mun Yi sallama tare da neman izinin shiga bq, ko da kuwa muna hango su Suna hango mu ne.
Izinin shiga Baba ya bani na shiga na samu qasan carpet na zauna, fuskar shi d'auke da murmushin da ya Saba a duk sanda ya ke kallon d'aya daga cikin yaran shi,Nima murmushin na yi na gaishe su, suka amsa, Baba ya ce,
"MAHREEN d'in Baba, ya aka yi?"
"Babu komai Baba,"
"Kin ji na yi shiru game da maganar Maheer ko?"
Shiru na yi Ina Murmushi ban amsa ba, ganin ba zan amsa shi ba ne ya sa ya ci gaba da magana,
"Ni na bashi izinin zuwa ya miki magana, saboda ya zo ya same ni da maganar ya na so ya aure ki,ni Kuma na jima Ina jiran wannan ranar saboda ba tin yau ba na kula da cewa ya na son ki, amma be Sanar da kowa ba, na yaba da hankalin shi da addinin shi, shine dalilin da ya sa na bashi dama, idan Kun daidaita ya yi maki shikenan, idan be maki ba ki Sanar da ni, ba zan yi maki auren dole ba, ba zan tab'a Yi wa kowa a yarana auren dole ba, after all Nima auren soyayya na yi, dika iyayen ku ni na gan su Ina so suka yi na'am da ni Suma su na so na na aure su, dan haka ki Sanar da ni gaskiya ki na son shi?"
Shiru na yi Ina Murmushi qasa qasa, har a wannan lokacin ban ji soyayyar Yah Maheer na min yawo a raina ba, amma Kuma maganar zai aure ni ta na min dad'i,ban san dalilin faruwar hakan ba, muryar mama ce ta katse mu ni da Baba.
"Haba Baban su, ai Kai ma ka San indai ka yi wa budurwa irin wannan tambayar ka ga ta na Murmushi ta amince kenan, kunya dai take ji,"
Sake duqar da kaina na yi Ina dariya qasa qasa, Baba ya riga ya sani ni ba yarinya bace me b'oye abinda ke cikin ranta ba, Ina Iya Sanar da su komai, ko da za a ga rashin hankali na, to menene dalilin yin shirun, Mama ta dage akan ya kyale ni alama ta nuna na amince, shi Kuma ya dage se na fad'a da baki na na amince ko ban amince ba, Jin haka ne ya sa na d'aga Kai na kalli Baba na ce Masa,
"Na amince baba,amma makaranta ta fa?"
Domin a lokacin nan Ina ta Jin qishin qishin d'in had'a mu za a yi da su Addah Ummu, su sun kammala makaranta Addah Ummu har ta ci gaba da karatu, amma ni Ina JSS 3 ya za a yi a cire ni a min aure?
"Kar ki damu 'yar baba, inshaa Allahu za ki ci gaba da karatun ki, Allah ya yi maki farin jinin masoya da yawa, kin ga ko wancan satin da na dawo se da bawan Allahn nan ya sake turo min limaman unguwar nan da wakilin Mai unguwa akan a bashi ke,(Allah ya jiqan shi ya gafarta masa domin ya rasu a yanzu) ga mutanen can da kuka had'u a kasuwa su hud'u ba su d'aga qafa ba sai da suka biyo ta family house har suka samu address din gidannan suka zo neman auren ki,sannan kin manta Muhammad? Yaron nan da ya musulunta ya na so na bashi ke, ba zan iya ba, na bashi hakuri na Sanar da shi idan ya musulunta ne domin Allah to ya riqe addinin Allah ya bauta masa da gaskiya, Allah ubangiji zai bashi wadda ta fiki, idan ya musulunta ne dan ya aure ki, a gaskiya ya yi hakuri na maki miji, Ina so ki samu namiji kamar Maheer, Wanda yake da addini, ya ke da sanin ya kamata, wanda zai iya da shagwab'ar ki da shiriritar ki, zai ji tausayin ki saboda lalurorin da Allah ya jarabce ki da su, bana son na aura maki namijin da da an kwana biyu zai wulaqanta min ke, Ina fatan kin gane?"
"Na gane Baba, na gode"
"Yauwaa Allah ya miki albarka,Allah ya Sanya alkhairi da albarka a ciki"
Wannan karon Mama ce ta amsa da,
"Ameen ya Allah, Allah ya sa a yi da mu"
"To aje a ci gaba da aiki ko, amshi wannan safar nawa ki wanke min su"
Karb'a na yi na tafi na qarasa wanki na, tinawa na yi da Muhammad bawan Allah, ashe shi yasa ranar da na je wanki a maqotan mu ya zo waje na, da yake gidan da yake haya a matsayin shi na d'alibi a kusa da gidan da na je wanki yake, Muhammad Inyamuri ne ya musulunta aka Sanya masa wannan Suna Mai daraja, Ina zaune a gidan ya yi sallama, Ina sanye da wata doguwar riga da mama ta bani, na yafa mayafin ta na fita wajen shi,Ina fita da ya ga rigar da ke jiki na, se ya ce na je na Saka hijabi domin ya fi min kyau, na koma na Saka hijabi Ina ayyana wa a Raina,
'ka ji mutum Daga musulunta har ya San tsiraici da rufe jiki'
Bana mantawa a ranar har kuka ya yi ya na bayyana min yanda yake so na, amma dole zai hakura da ni,sannan ya miqa min wata takarda da ya yi rubutu da yaren turanci na soyayya, sai kud'i a tsakiyar takardar Wanda ban San da su ba sai daga baya da na je Ina duba takardar, bana manta yanda idanun shi ke zubar da hawaye a lokacin da yake min sallama,ko da na fad'a wa maqociyar mu budar bakin ta sai cewa ta yi,
'Mahreen Ina tausaya maki sanda Zaki wa d'a namiji kuka a irin yanda ki ke Sanya samari kuka, ki duba ki gani haka wannan yaron da ke zaune a can gidan sutudai (students) ya dinga kuka ya na roqon ki so shi, wa ma yake da suna? Yauwa Bashir, Ina tausaya maki sanda Zaki kuka akan namiji'
'Dan Allah Umma ki Dena min wannan mugun fatan Allah ya raba ni da kowa lafiya'
'Ameen ya Allah's
Tausayin Muhammad ne ya kama ni a daidai wannan lokacin,
'Allah sarki ashe Baba ya riga ya Sanar da shi ba zai bashi ni ba shi yasa ya zo rannan mu Kai sallama, Allah ka bashi wadda ta fini Amin'
Wannan ita ce addu'ar da na Yi masa na d'auki bokitin da na gama wanki na na je shanya.
******************************
Tinda Yah Maheer ya ji amsa ta be sake nema na ba, abun ya na damu na sosai, ga mamakin shi da ya qi bari na na huta, shi haka ake yi? Ka na son yarinya ba tsayawa za ka yi ka kafa kan ka ba, wa ya Sanar da shi Ina son shi? Ba zai tsaya ma shi ya nemi soyayya ta ba kawai se ya tafi hankalin shi kwance ba Kira ba zuwa ba saqo? Lallai ma mutumin nan.
Ina zaune Ina wannan tunanin na ji an yi sallama, Ina dubawa sai na ga qannen Babana ne suka zo da matar qanin Babana wadda take Yaya a wajen Yah Maheer,da yake dangin mu Masha Allah akwai yawa, yawanci auren zumunci ake yi, tashi na yi na Isa gare ta domin Ina Jin ta kamar Mahaifiya ta saboda kirkin ta, rungume ni ta yi kamar yanda ta Saba in mun had'u, na gaishe ta, sannan na fita na deb'o masu ruwa, Mama ta fito suka had'u da Ummah su Kai ta hira mu Kuma Yara muka basu waje bayan kowa ya gaishe su.
A hirar da suke yi ne suka tattauna yanda za a had'a aure na da na su Addah Ummu, da Kuma zuwan da 'yan uwan Yah Maheer za su yi dan kawo lefe tare da kud'in aure a tare, ji na yi gaba d'aya hankali na ya tashi.
Domin magana ta bazu a dangi tin da jimawa, wasu na ganin be Kamata na yi aure a wannan qananan shekarun ba, ga qanne na ajin mu d'aya da su,what if akai auren ya hana ni karatu na zo na tara Yara Ina ji Ina gani qanne na za su zo su zama yayu na in zauna se abinda na roqa suka bani, wasu Kuma suka kawo wa Baba gulmar cewa bashi da aikin yi, dan ya kammala karatu ba shi ne ya ke nufin ya na da aikin da zai riqe ni da shi ba, sana'ar da yake ba wata kwakkwaran sana'a bace, shago Yah Maheer ke da shi a wancan lokacin, Dan haka wasu na ganin ba sana'a bace me kyau da har za a d'auke ni a bashi ni.
Kai na ya cika da wasiwasi da tsoron me zai je ya zo, bayan tafiyar su ne da dare Ina kwance a d'aki babbar yayar mu da ke aure a Lagos ta Kira ni, ta wayar Addah Ummu, bayan mun gaisa da ita ta ce min,
"Ke MAHREEN ki tsaya da kyau ki ji me zan Sanar da ke, na ji duk abubuwan da ke faruwa, kin ga masu son kar ki auri Maheer ba qaunar ki suke ba, 'yan baqin ciki ne kawai, Dan basu samu namiji kamar shi bane, ni na San wanene Maheer na zauna da shi a bauchi mutumi na ne, Ina makaranta ko bani da kud'i wajen shi nake zuwa Kuma ya na bani, mutum ne mai kirki Wanda tinda na Yi zaman bauchi na gama ban tab'a Jin an same shi da Wani aibu ba, sannan na ji labarin wasu na cewa wai ya maki tsufa, to bari ki ji, gwanda ki auri Wanda ya girme ki, ya San ke yarinya ce ta yanda ko kin masa laifi zai kyale ki saboda wannan yarintar taki, auren qaramin yaro lalura ne, be kwab'i kan shi ba balle ya kwab'e ki, Dan haka ki ta addu'a Allah ya zaba abinda ya fi alkhairi "
A wannan lokacin na jima da fara kuka, saboda zama confused da na yi,shin na yarda a Yi wannan auren ne ko na ce bana so?
"Ki na ji na ko?"
"Eh Addah Babba na gode inshaa Allahu zan yi abinda ki ka ce,"
"Yauwaa Allah ya Sanya alkhairi"
"Ameen a gaishe min da Yayana" (Dayake na yi zama a wajen Adda Babba Dan haka na Saba sosai da mijin ta)
"Zai ji, ai na Sanar da shi 'yar gidan shi fa aure ya matso, ya na maki fatan alkhairi ya koma wajen aiki"
"Allah sarki Yayana, to Allah ya taimaka ya dawo da shi lafiya"
"Ameeen ki gaishe da mutanen gidan se anjima"
"Ameeen na gode,"
Gama maganar mu da Addah Babba ke da wuya na miqe na janyo jakar makaranta na, na bud'e na d'auki biro da takarda.
Na hau rubutu kamar haka.
*Assalamualaikum Babana, Baba Dan Allah Ina Neman alfarma a wajen ka, kar a Yi min aure yanzu a bari sai na kammala makaranta, saboda kar na zo ban gama makaranta ba qanne na su zo su zama yayu na a nan gaba. Na gode MAHREEN din Baba*
Na yi amfani da Kalmar da ake fad'a min ta qanne na za su zama yayu na in ban gama karatu ba akai aure na, saboda ta na dukan zuciya ta sosai ba kad'an ba.
Da hannu na na bawa baba takardar na koma d'akin mu na 'yan mata na zauna, a tunani na da ya karanta zai Kira ni, amma se na ji shiru, shirun ya yi yawa har washe gari, na zaci ma fushi baba ya yi amma da muka had'u da shi sai ya nuna min kamar ma be karanta takardar ba.
Ji na yi ban ji dad'i ba da be karanta takardar ba, haka na Yi kwanaki Ina jiran Baba be ce min komai ba game da takardar.
Kwatsam wata ranar lahadi ana washegari zai koma wajen aikin shi tinda dama duk juma'a yake dawowa ya koma Monday da sassafe ya kira ni, jiki na har rawa yake Dan tsoron amsar da zan samu wajen Baba.
Idan ya ce an fasa auren Kuma kwata kwata fa? Zan yi farin ciki ne ko zan Yi baqin ciki? Idan Kuma ya min fad'a fa? Idan Kuma ya amince za a ce su jinkirta fa? Wayyooo Allah na tinani zai tarwatsa min kwakwalwa ta.
Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.
💅 *MAHREEN* 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 3
Zaune na tarar da Baba a bakin gadon shi ya na danna laptop din shi gefen shi takardu ne da yawa, sai Kuma littafin addu'o'i guda d'aya a saman takardun,zama na ke qoqarin Yi a qasan carpet d'in d'akin kafin in gama zaman ya min izinin komawa saman kujerar da ke gefen gado, ban b'ata lokaci ba wajen bin Umarnin shi.
Gaishe shi na yi ya amsa ba tare da ya kalle ni ba, sannan fuskar shi bata nuna min halin da zuciyar shi ke ciki ba, shin ranshi b'ace yake da ni ko Kuma ya ji dad'in fad'ar ra'ayi na da na yi? A dan firgice na kalle shi na Kuma amsa Suna na da ya kira a qoqarin shi na rufe laptop d'in shi da yake.
"Na ga saqon ki, Kuma na gamsu da abinda ki ka rubuta, amma ki sani Maheer yaro ne Mai hankali da mutunci, ban sani ba ko kin samu ana zuga ki ne akan shi? Ba na so tin maza na rububin neman auren ki su zo su na gudun ki, Dan haka nake baki hakuri da ki amince da Maheer, ki maida hankali wajen yin addu'a da yardar Allah, Allah zai maki zab'i mafi alkhairi, ni Ina yi, mahaifiyar ki na yi na tabbata Allah zai amsa ya zaba maki na gari,kin Iya istikhara?"
"Ah ah Baba Ina dai ji ana fad'an sallar istihara"
"Ba istihara ake cewa ba, istikhara ake cewa, Kuma ita wannan sallah ana yin ta ne a Yi addu'ar neman zab'in Allah a cikin ta, karb'i nan"
Littafin hisnul Muslim ya miqa min Mai bango ja, ya riga da ya bud'o page d'in da addu'ar take, se na hau dubawa, Baba ya yi min bayanin yanda zan yi sallar da yanda zan yi addu'ar, ni dai da na gama ji sai na ajiye littafin na kalle shi Cike da shagwab'a ta da ta zame min jiki, na ce,
"Ni dai baba Kai ka yi sallar da addu'ar zata fi karb'uwa"
Cikin zuciya ta kuwa Ina Jin haushin yanda Yah Maheer ya Wani dena kira na a waya balle ya sa qafa ya zo Gani na, to Wani tashin dare zan hau yi ina wahala da Kai na akan shi? Baba murmushi ya yi, ya sake miqa min littafin a karo na biyu, sannan ya ce,
"Tashi ki je ki maida hankali wajen yin abinda na ce maki, inshaa Allahu ni din ma zan yi"
"Na gode Baba"
Na sunkuya na d'auki littafin da kyau na bar d'akin, cikin raina Ina ayyana
'Ai kuwa se dai Kai ka yi sallar nan na kwana bakwai ba abinda zai wahalar da bacci na in ya zo, tinda da alama dan ya ga ya samu nasara ya zubar da duk tarin masoyan da nake da su shi yasa ya ke wa mutane yanga'
Na so na qi yin sallar nan, saboda haushin da nake ji,se dai zuciyata bata bani dama ba, qarfe d'aya da wasu mintunan na tashi na yi alwala na yi sallah da littafi na a hannu saboda ban hardace addu'ar ba, na yi sallah na yi addu'a na samu waje na kwanta.
A taqaice se da na jera kwana uku Ina tashi Ina wannan addu'ar, daga qarshe na watsar na ce Baban da ke son Yah Maheer d'in ya ci gaba ni dai na gama tawa.
*****************************
*Wacece MAHREEN?*
Ni MAHREEN 'ya ce a wajen Alhaji Muhammad Ahmad da Hajiya Raihanatu, Alhaji Muhammad na da mata guda biyu na aure, ya na da Yara guda goma sha uku masu albarka, sun had'u shi da iyalin shi wajen ba wa yaran shi tarbiyya Kuma alhamdulillah kaff yaran shi ba Wanda za a d'aga a Yi Allah Wadai da shi.
Suna na ya samo asali tin Ina cikin mahaifiya ta, 'yan uwa na ke Kira na da sunan, Kuma su ke da yaqinin shi za a Sanya min idan an haife ni,ko safa aka d'aga za a ce ta MAHREEN ce, idan hula mama ta saqa za a ce ta MAHREEN ce, ma'anar sunan MAHREEN kuwa shine, Mai kyau kamar Rana, ko za a iya fassara shi da abun so, wannan dalilin ne ya Sanya bayan an haife ni Baba ya so ya sauya sunan, suka yi shawara da Mama ta ce,in aka sauya sunan ba a Yi wa Yara daidai ba, tinda sun riga sun Saba da sunan, dan haka ranar Suna aka rangad'a min Suna MAHREEN.
Alhaji Muhammad mutum ne shi mai adalci a tsakanin matan shi da yaran shi da qannen shi, mutum ne mai tsananin ladabi da biyayya ga mahaifiyar shi wadda ta rage masa bayan rasuwar mahaifin shi, da zaka tara matan Alhaji Muhammad da 'ya'yan shi a d'akuna daban-daban ka tambaye su shin wa Baban ku ya fi so da qauna ne a cikin ku? Kowannen su zai ce Maka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 30