na sama masa wasu kayan cikin wanda ya ke a gida na fesa masu turare na ajiye, sannan cikin sauri na deb'o masa lemon kankana da abarba da na yi masa a qaramin cup a qalla ya jiqa maqoshin shi kafin ya tafi.
Haka kuwa aka yi kuma ya ji dad'in lemon sosai, ina tsaka da taya shi balle mab'allin rigar shi ya kalle ni, sannan ya yi murmushi ya ce,
"Na ga fa yanzu Baby Na ta iya wanki sosai har ma da gugar 'yan gayu"
Dariya na sanya dan tunawa da irin wankin da nake masa a baya.............
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 16:
Ni Mahreen na taso na tarar da mahaifiya ta ta na yi wa Baban mu wanki,tin muna qanana har muka yi wayau musamman qananan kayan shi ita ke wanke wa sai dai da wata lalura, ko kuma aiki ya mata yawa ko dai wani abu makamancin wannan, domin akwai sanda hannun ta ya samu mummunan rauni, amma ya na fara warkewa ta ci gaba da yi masa wanki ba tare da ma ya san ta ci gaba da wankin ba, manyan kayan shi da wasu daga fararen kayan shi kawai yake bayarwa a yo masa wanki da guga a waje, dan haka sai nima na qudurta cewar da yardar Allah nima ni zan dinga yi wa miji na wanki da guga, dan haka duk randa Yah Maheer ya cire kayan shi zan d'auka in je in jiqa se na tara kamar guda uku a bokiti d'aya sannan zan wanke, haka zan cakud'a fari da blue me duhu ko green me duhu, har su zuba su b'ata farin, sannan wajen guga in na goge su to fa bana iya daidaita kafad'un a karkace a shagid'e nake gogewa.
Bawan Allah duk irin tsaftar shi da iya karin gugar shi haka zai saka wanda na yi masa ya fita, abokan shi su yi ta masa dariya su na fad'in,
'Amma dai wannan gugar/wankin amarya ne ko?'
Se dai ya yi murmushi ba tare da ya amsa su ba,se ya dawo ne zai sanar da ni abinda ya faru, ya had'a da nuna min shi fa he is satisfied with the qoqari da nake wajen kula da kayan shi da tsaftace su, da kaina na zauna na ga rashin dacewar abinda nake yi, dan haka watarana da Isma'il ya zo mana ziyara se na deb'o kayan na kai masa parlour na ce dan Allah ya koya min yanda ake wanke kowanne kaya ba tare da wani ya b'aci ba, sannan ya koya min yanda ake gugar kayan maza me kyau, ba b'ata lokaci kuwa ya koya min da kyau, tin daga ranar Yah Maheer be sake saka kayan da suka samu zubar kala ba, sannan guga take tafiya samb'al.
Ina zaune ina ta tunanin baya ina murmushi na ji sallamar shi ya dawo daga masallaci, sabuwar tarba na masa wadda ta sanya shi shagala da kallon gayu na, gyaran murya ya yi sannan ya ce,
"Baby Na wannan rigar fa? Kin ga yanda ta karb'e ki kamar a jikin ki aka d'inka ta, sai ki ka yi kama da babyn roba irin masu kubul kubul d'in kumatun nan"
Tura baki na yi saboda ya ce min 'yar lukuta, tini na fara qaqalo hawaye ina son na masa kuka, se hawaye ya bayar da ni ya qi zuwa, dariya ya dinga min sannan ya ce,
"Yarinya na san dika tricks d'in ki you can't fool me, zo nan"
Maqe kafad'a ta na yi na qi zuwa, qasan raina ina jin kamar na fasa kuka, akwai tausayin shi fal raina, ya dawo daga tafiya ba zan iya bashi wata nutsuwa gamsasshiya ba, dan haka na qi zuwa dan bana so ya saka ran samun wani abu a waje na a wannan rana.
Duk wani wayo da dabara da yake min se na qi zuwa, qarshe ma tashi na yi na ce,
"Ahhhfff ka ga muna ta shiririta mun manta baka ci abinci ba fa, ina zuwa na kawo maka"
Had'e fuska ya yi, ya kira suna na,
"Mahreen ! Zo waje na"
Jin haka da na yi kawai se na saki kukan da nake ta dannewa a can qarqashin zuciya ta, da gudu na tafi na fad'a jikin shi, ya kuwa sanya hannayen shi dika biyu ya rungume ni da kyau, kuka nake kamar zan shid'e saboda tausayin kaina.
Kun san dai yanayin jikin mai qiba, yawan sanya pant and pad is not easy at all,ballantana ni da pad d'in ma bata isa ta da towel qarami nake qunzugu a rana sai na jiqa towel sama da uku da jini, ina yi ina wanke wa ina shanyawa,dan haka gaba d'aya cinyoyi na a goge suke, sannan na gaji da yawan shiga toilet gyara jiki na, ga toilet na gidan haya wannan ya shiga wancan ya fita,ruwan wanke towels din ma kan shi watarana wahala yake dan kuwa babu, ina cikin damuwa sosai, gashi na riga na san in jinin ya fara zuba yana jimawa kan ya d'auke, yanzu yana iya ya gama weekend ya koma ba wani abu da ya gudana tsakanin mu, gashi ya yi sati d'aya dama baya nan, ji yayi na kasa yin shiru ba tare da na shirya ba se na ji ruwan hawayen shi a baya na, da sauri na d'aga kai na kalle shi,hannu ya sa ya share min hawaye na sannan ya yi qoqari ya taya ni gyara kwanciya ta.
Manne muke da junan mu ina a tsakanin qafar shi fuskata na facing wardrobe d'in mu ina ci gaba da tsiyayar da hawaye, hannayen shi ya sa ya qara riqe qugu na ya dora hab'ar shi a kafad'a ta sannan ya sumbaci kunne na, a hankali kamar me koyon magana ya fara magana,
"Baby na ki yi hakuri, mu yi hakuri da wannan jarabawar da Allah ya yi mana, rayuwar nan da ki ka gani kowa da kalar jarabawar da Allah yake masa,na fahimci menene ya sa baki son zuwa waje na, Baby na ba jikin ki kad'ai nake so ba, ke nake so, i am in love with your soul body and everything, and i can't live without anyone of them, sai dai idan d'aya ya na jinya zan yi ta addu'a Allah ya bashi lafiya, in bashi magani, in kuma bashi kulawa, dan haka kar ki damu ki dena kuka kin ji?"
D'aga masa kai na yi a hankali cikin tsananin jin dad'in kalaman shi, nan take na hau tunanin ashe dama haka Yah Maheer yake? Kafin aure ko 'yar i love you d'in nan ta Zamani babu,amma yanzu tinda muka yi aure ba ranar da zata zo ta fad'i be ce min I love you ba, (Har yanzu hakan take ko a baki ko a rubuce baya fashi, alhamdulillah Allah ya qara kare mu da idon masu hassada da ayyana mugun nufi a zuci Ameen)
Gyara zama na na yi na sake mannewa da shi kamar zan koma cikin shi sannan na ce,
"Na gode Yaya na, Allah ya jiqan Momcyn mu ya qara wa Baba lafiya, Allah ya bani lafiya,...Amma ya akai ka gane bayan baka gani ba?"
Hannu ya nuna min jikin window na da nake shanya pants da towels d'in ya ce,
"Tinda muka shigo na gani kawai se na gane jini ya zo sai kawai na hau yin addu'a Allah ya baki lafiya ya kawo qarshen wannan abun,"
"Allah sarki, yauwaa na manta ban sanar da kai ba randa Babyn Addah bai da lafiya na je asibiti da safe, i am sorry ban tambaye ka ba first, kuma tin daga nan jinin ya fara zuba" nan take na bashi labarin komai.
"Babu komai baby na, in dai abu ya taso na gaggawa ko shiga maqota sada zumunci na baki damar zuwa, amma ina maki nasiha da ki ji tsoron Allah a dik inda ki ke, ki iya bakin ki, kar ki fad'i abinda Allah zai fushi da ke ko ki zubar ma da kan ki da ahalin ki mutunci"
"Inshaa Allahu ba zan yi ko d'aya ba, na gode"
Haka hirar ta ci gaba har dai na zare jiki na na samo masa abinci, qarshe na taya shi ci dan nima se na ji kamar an min yasa.
Muna tsaka da ci aka kira sallar asr, ya fita masallaci be dawo ba se gaf magariba, sai gashi da magunguna irin na Islamic chemist din nan, ya had'a min da kan shi ya bani, ina qi ina qi haka dai na shanye ba dan na so ba.
Se da na jera kwana biyun da ya na nan na dinga sha ba fashi.
Ya na komawa kuwa na dauki robar maganin dake da zuma a ciki na kwankwad'e dika, a raina ina cewa,
'Ni wannan in ban shanye ba se na kasa sha nan gaba, gwanda na gama da ita yanzu kawai'
Sauran magunguna ma haka na musu.
Jini be tashi d'auke wa ba se da ya yi a qalla sati uku, sanda ya cika kwana sha biyar Yah Maheer ya ce in ci gaba da sallah, ya koya min idan zan sallah ina tsaftace jiki na na yi tsarki na yi alwala sannan na yi sallah ko da na ji jinin na zuba kar na damu, watarana in ina sallah na ji jinin na zuba sai in dinga ganin kamar sallah ta batai ba, amma a haka zan danne na hakura na idar na tashi.
A satin da ya dauke Yah Maheer ya rankayo gida ya baro Bura,mu na ta murna gyara da kwalliya ba kalar wanda ban ba daidai iyawa ta a wancan lokacin, a kuma wannan satin Hauwa'u bata nan ta je gidan su, Isma'il ya tafi Liman katagum saboda shirye shiryen nad'in sarauta da za a yi wa Baban su Yah Maheer.
Da magariba Yah Maheer ya iso gida riqe da d'an qunshin naman kazar shi da fruits, se ruwan pure water leda d'aya da kananzir, taya shi ajiye komai na yi inda ya dace, Suwaidatu ta masa sannu da zuwa ta koma parlour, muma can muka nufa bayan ya ajiye ledar da ta rage a hannun shi ban karb'a ba.
Plates da wuqa da roba da ruwa na d'akko, na zauna na wanke lemo ayaba da kankana da abarba, na yayyanka mana, na deb'o abinci na jere, na juye kaza a plate, ko da na ajiye se ya ce na kai masa abincin shi d'aki shi ba yanzu ze ci ba, ya faki idon Suwaidatu ya kashe min ido d'aya,murmushi kawai na yi na kuwa yi yanda ya ce, na ba wa Abubakar da Suwaidatu nasu muka shige d'aki.
Sabon amarci muka shirya ci a ranar,dan haka tare muka ci muka sha muka yi hira tare da tinawa da daren farkon mu, daga tashi na tattare kwanuka se na ji zafi sosai a qasa na, da kyar na qarasa miqewa qarshe shi ya qarasa miqo min sauran kwanukan na firar, da kyar na gyara wajen, na yo alwala kamar yanda ya buqata, dan ya qudurta a ranar nan sai mun tuna da ranar farkon mu.
Nima har cikin raina ina so hakan ta kasance dan ko ba komai bawan Allahn yana da hakuri matuqa, na yi shiri da dikkan qarfi da iyawa ta zan bashi had'in kai,sai gashi ina ganin kamar haqon mu ba zai cimma ruwa ba.
Tin ina dauriya ba sai ga ni ina kuka wiwi da hawaye na ba? Yah Maheer na dubawa se ga qatoton qurjin da ban san daga wacce unguwa ya taho ba ya afka jiki na,kuka nake ina kumawa saboda zafin da nake ji, Yah Maheer na ganin haka se ya hau yi min addu'a ya na lallashi na, ko a fuska ban ga alamar b'acin rai ko qin halin da nake ciki ba da wata manufa sai tsabar tausayi na da soyayya da kulawa da ke dawainiya da shi.
Ina kuka na samu bacci mai dad'i, ban tashi farka wa ba sai tsakiyar dare kowa ya yi bacci gashi ban yi sallar isha'i ba ni.
Da sauri na tashi dan zuwa yin alwala na yi sallah sai na ji babu zafin, nan da nan na kai hannu na dan in ji ko qurjin na nan? Ai kuwa se na ji yana nan, take na yi qoqarin fasa shi wani azababben zafi ya ziyarce ni, na kwalla qara, Yah Maheer da ke bacci neya farka cikin magangin bacci, shiru na yi kamar ba abinda ya faru na kwanta gefen shi, cikin baccin da yake matuqar jin dad'in yin shi ya d'ora hannun shi a kafad'a ta ya hau bugawa a hankali har bacci me nauyi ya sake kwashe shi, a hankali na zare jiki na na bar dakin dan zuwa yin alwala.
Washegari da safe ya kama ranar za mu tafi Liman katagum dan halartar bikin nad'in sarautar Baba, garau na tashi ba inda ke min ciwo,ba qurji ba alamun shi,Yah Maheer dik da hint da na dinga bashi sai ya nuna shi fa be gane ba, haka muka gama shiri ina zumbura baki ni a dole an min wulqanci.
In muka had'a ido da shi se dai ya kad'a kai ya yi murmushi.
Ko da muka isa gida muka tarar da gida ya d'auki harami, ana ta hada hada, dake washegarin ranar za a yi nad'in sarautar, aikin abincin washegari akai ta yi, a haka na dinga bin dangi ana gaisawa, wani waje qungiyar manya ce a ladabce zan tsugunna na gaida su na wuce, wasu yayun mu ne wasu kuma daidai ni suke, da yamma aka kammala komai har had'in masar da za a yi washegari da waken da za a yi qosai komai an gyara, an yo markaden kayan miya da na kunu.
Haka muka kwana surukan gidan ana hira ana waqe waqe irin na qauye da sauran su.
Washegari kuwa haka muka sha wankan mu kowa ta qure adaka, kowa ka gani fuskar shi d'auke da fara'a da walwala.
Ina zaune kusa da Goggonin Yah Maheer muna qulla zob'o da kunun aya da na zaqi, Baba ya fita can fada,ina nan zaune se na ga Umman su Yah Maheer ta fito daga wanka ba tare da ta gama ba, ashe Mama ce ta mata kutse cikin bayin, se ita ta hakura ta fito, ganin haka qanwar Yah Maheer wato Mahaifiyar Hauwa'u sai ta kira ni ta bani wani ruwan ta ce na kai mata d'ayan bayin ta yi wanka Baba ya kusan shigowa gida, haka kuwa aka yi, cike da jin nauyi irin na fulanin asali Umma ta wuce ta yi wankan a wani bayin, ni ko na koma muka ci gaba da qulla abubuwan sha.
Muna tsaka da qulle qullen mu Mama ta fito cikin shirin ta ta sanya atampar ta sabuwa karr, sai d'aga kafad'a take, Goggonayen Yah Maheer ne suka hau yi mata d'an biki akan abun da ta yi,
"Kin dai ji kunya a gaban surukar ki ki ka yi wannan abun kunyar"
Kallo na ta yi da wani irin salon da ya tadan hankali, sannan ta ce,
"Suruka? Ina surukar take? Ai ni bani da suruka a wannan gidan har sai sanda wannan yaron ya yi aure (Isma'il)"
Wata iriyar kunya ce ta kama ni, sai na ji na muzanta na qasqanta,miqewa na fara yi zan bar wajen Goggon Yah Maheer ta riqe ni ta maida ni na zauna sannan ta ce,
"Ki rabu da shirmen ta, haka take, ba kuma da ke take ba da mu take"
Haka aka gama qulla zob'on nan raina ba dad'i,muna tsaka da hirarraki sama sama muka ji bushe buhse irin na sarauta, gida ya dauka da sowa aka dunguma akai bakin zaure, Baba ne ya dawo a saman doki, nan da nan akai ta murna,ana tsaka da murna ba se Baba y fad'o a saman doki ba? Nan fa gida ya kaure da koke koke, qanwar Baban ta hau fad'in,
"Ni dama bana son sarautar nan wallahi, Allah ya sa ba wani mugun abun aka maka ba d'an uwa na"
Qannen shi mata da jikoki da 'ya'ya duk sai aka rikice, a rirriqe aka shigo da shi cikin gida akai d'akin shi da shi aka kwantar nan fa gidan ya dinga raguwa saboda taro ya tashi.
A haka Baba ya fara jinya sosai, wadda ni dai ban san meke damun sa ba, amma dai na san bashi da lafiya kuma iyalan shi sun tsaya tsayin daka wajen ganin ya samu cikakkiyar lafiya.
Kwanan mu biyu muka dawo gida, Yah Maheer kuwa se ya zamana ya raba qafa, baya Bauchi baya Liman katagum wajen Baba,ya yi matuqar damuwa sosai da lalurar da ta samu mahaifin shi nima kuma haka, domin Baba ya nuna min so da qauna wadda ban san iyakar ta ba,ya d'auke ni a matsayin 'yar cikin shi, wannan shi ne dalilin damuwa ta sosai, gashi kuma uba ga miji na me so na da qauna ta.
A haka bashi da lafiya aka yi auren Isma'il inda ya auri wata Zaituna dake da zama anan Bauchi, ranar da za a kai ta gidan miji da ni aka kai ta, domin kuwa duk amaryar da aka aura a gidan se an kawo ta liman katagum ni kad'ai ce aka bari a bauchi, shine dalilin da ya sa ana gama auren muka dawo tare, daga baya aka maida ni gida na muka bar ango da amarya a gidan su.
Tafiyar Isma'il sai ta sauqaqa min wani babban kaso na wahala da ke danqare a kai na, domin ba me sani magana sama da shi, ko yaran ba su sani magana kamar yanda yake sani, basu b'ata min rai kamar yanda yake min, tafiyar shi sai ta zame min nutsuwa da salama.
A tinani na matsala ta ta zo qarshe indai akan dangin Yah Maheer ne, ashe ban sani ba wata matsalar ce zata kunno min kai..........
Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 17
Hidimar bikin Kabeer qanin Yah Maheer da Ke bi masa ce ta kankama ba kama hannun yaro,duk Wani ayyukan girke- girken biki da duk wata hidima da ya kamata ace na sa hannu a ciki ban tsaya wata qiwa ko son jiki ba da ni ake yin komai, kuma ina aiki ne domin Allah ba dan ace wance ta na ta aiki ko ganin ido ba.
Abun da ke matuqar burge Ummahn su da ni kenan, wato rashin gudun aiki ,da rashin qiwa wajen aiki,ko da zan yi in dawo Ina ciwon jiki saboda rashin sabo da aikin yawa kamar nasu ba na qin yi zan shiga a yi komai da ni a tashi.
Bayan kammala biki an Kai amarya gidan ta da ke cikin garin Bauchi Wanda yake da dan tazara da gidammu, amma hakan be hana ni Kai musu ziyara ba bayan kwana biyu da yin bikin nasu.
A hankali muka fara shaquwa da Habibah matar Kabeer wadda ta girme ni a shekaru Kuma ta fini sanin kan duniya, da wannan sanin duniyar da ta fi ni da Kuma girme min da tai a shekaru ta yi amfani wajen Jana a jiki har na sakankance da ita na d'auke ta kamar 'yar uwar da muka fito gida d'aya.
Ta b'angaren Habibah kuwa yanda na É—auke ta Sam ba haka ta É—auke ni ba ashe, kallo na kawai take a matsayin tsanin da zata taka ta cimma burikan ta na mallakar dangin miji da Jan dangin miji a jikin ta, duk wata tambaya da za ta min akan kowa na gidan da zuciya d'aya nake zama na bata amsa, sannan da zuciya d'aya nake hira da ita, har ya zamana ba ma boye wa juna abubuwan da suka shafe mu, watarana naje gidan ta sai muka shirya sallar da zata fara a gidan miji za mu je Liman Katagum tare da ita, cikin sa'a sai ya zamana matar Isma'il ma zata je a lokacin ta na d'auke da tsohon cikin ta na fari.
Ko da na koma gida muna hira da Yah Maheer na sanar da shi sai ya ji dad'i da farin cikin yanda muka had'a kammu ni da matar qanin shi, nasiha ya dinga min akan yanda zan ci gaba da zama da kowa lafiya, sannan ya dinga yaba min akan qoqarin da nake na zama da kowa lafiya da nuna kulawa ta da soyayya ta zuwa ga 'yan uwan shi da iyayen shi, nuna masa na yi ai ba komai, nima ai haka yake son 'yan uwa na da iyaye na kamar nashi, dan haka dole na kula da nashi, muna hira Ina gyara akwatin mu na tafiya har na gama tsaf, kallo na ya yi ya yi murmushi sannan ya ce,
"Baby na ke da ki ke ta had'a kaya tin yauuu Se fa jibi ne tafiyar,ko tsabar kin matsu mu je gida inda zaki shiga dangi ki manta da ni?"
"Habaa ba haka bane, kasan akwai kayan Suwaidatu da zan had'a, shi yasa na fara da nawa, bana son yin abu a qurarren lokaci ka sani"
Langwab'e Kai ya yi kamar wani abun tausayi sannan ya ce,
"Allah sarki ni bawan Allah, yanzu in mun je gidan ma ganin ki wahala zai min, gashi na ce ki min tausa tin d'azu kin qi"
A gaskiyar magana tausa na daga abinda bana so a rayuwa, na farko ni ban San dad'in ta ba in ni ake wa, sannan in ni zan yi wa wani sai in ji ana soken hannaye qashi na Sukata, duk sanda na fad'i haka sai Yah Maheer ya ce Ina fad'a masa magana dan na ga ba shi da qiba, Kar na damu zai yi qiba ne sai ya wuce gori a waje na watarana.
Cikin nuna ni fa bana son yin wata tausa na qarasa gare shi na hau yi masa tausa, abokin shi ne ya kira shi a waya suka hau gaisawa, qarshe suka b'ige da hira,cikin sauri na yi amfani da wannan damar na je parlour na sa Suwaidatu d'ebo kayan ta da na goge mata na fara had'a mata tata jakar, takalman Yah Maheer na kwasa na sa a jaka na tsaya Ina kallon kayan namu Ina nishin gajiya, ta baya na na ji an tab'a wuyana, daga Jin haka ba sai na juya ba na San wanene, dan haka kawai sai na tsaya Ina sauraran me yake cewa haushi na shiga ta.
"Baby na dan Allah ki yi hakuri ki cire min kaya na ba da ni za ku tafi ba akwai wani aiki da ya taso daga baya zan biyo ku, I am so sorry darling Kar ki fushi dan na San ba Kya fushi," ya qarasa maganar shi cike da tsokana.
Cikin fushin kuwa na juya Ina kallon shi sannan na ce,
"Habaa dan Allah Husband sai da na gama had'a kaya kafff na kulle komai tafiya kawai nake Jira sannan zaka ce na warware ga kayan ka ba a sama suke ba ma, gaskiya ni dai ka bari in na je can zan cire Maka, and ni bana son wata darling Baba ma fa haka yake Kiran Mama da shi kana kirana darling kamar wata tsohuwa"
Dariya ya dinga yi sannan ya kama hannu na muka zauna a kujera mai cin mutum biyu, ya ce,
"To Baby na daga yau na dena Kiran ki da darling shi kenan? Kuma ai gani na yi Baba na ce maki darling yaran gidan ku ma wasu darling Mahreen suke ce maki....to yanzu daiii komai ya wuce zan je na cire kaya na in yaso se ki qara gyara inda ya b'aci ko?"
Ni dai ba haka na so ba, na so mun yi tafiyar ne tare fushin da nake kenan,ni bana son abinda zai na raba ni da shi na tsawon lokaci, shine dalilin da ya sa ko Kano zani asibiti yake raka ni, to amma wannan karon da alama hakan ba zata samu ba, dan haka washe baki na yi na nuna masa komai ya wuce zan cire masa kayan nashi sannan na masa addu'a da fatan alkhairi akan abinda za su yu d'in.
A ranar da za mu tafi na dinga jiran Habibah ta min maganar tafiya shiru, dan haka da muka gaji da Jira sai muka nufi tasha ko da muka je ashe su a motar gida za su tafi shi yasa bata min maganar tafiya ba tunda ba motar su bace,da samun labari sai muka shiga motar haya muka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 30