Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuwa ta. Gidan Maman Ameenah aka dinga kai kayan mu da suka rage ajiya,se wani gida wanda ban san shi ba har yau kuma ba su neme ni dan su bani kayana ba . Muna gidan Maman Ameenah Maman Abdurraheem ta dawo dan mijin ta ya riga ta zuwa aka buɗe aka debi wasu kayan nasu, nan gidan Maman Ameenah aka kawo mata ita ma,cikin jimami da kuka a idon ta itama ta shiga muka zauna tare muka jajanta wa junan mu abinda ya faru, Maman Abdurraheem ta Shiga damuwa sosai a wannan lokacin itama, zaune muke ana ta shiga da fita ana mana jaje, se ga Maman Ameerah ta zo ta na kukan tausayin mu, cikin jimantawa ta ke sanar da ni yanda akai ta san gobara ta same mu. Godiya na mata tare da fatan alkhairi, daga qarshe ta mana sallama ta wuce wajen Hauwa'u, ban san ya suka yi ba dai amma qarshe gidan ta Hauwa'u da mijin ta suka koma da zama. Mu kuma a ranar na tafi gidan Maryam ɗin Uncle Inuwa mu ka kwana ni da Suwaidatu, mu na nan abokin Yah Maheer Bashar da ke zama a Abuja ya bamu aron gidan shi da ke unguwar Gesse tunda su ba anan suke zama ba yanzu, Bashar abokin aikin Yah Maheer ne mutanen kirki ne shi da matar shi Rasheedah Alqali, tun Rasheedah na amarya Bashar ya kawo mana ita muna Alieru qtrs, ta na da fara'a sosai kuma wayayyiyar mace ce 'yar boko, Rasheedah bata da matsala sam a mu'amalar ta da mutane haka ma mijin ta Bashar. Mun koma Gesse ba jimawa gida irin ginin zamani mai kyau,nan fa na shiga tsaftace shi da kyau yanda ya kamata, nan da nan waje ya hau ɗaukan ido, daki ɗaya aka bamu me ɗauke da qatuwar katifa jibgegiya se mirror da sauran tarkacen kayan daki ,akwai babban parlour da tsakar gida wanda shima babba ne ba laifi, ga kitchen da store, nayi matuqar qoqari wajen kiyaye taɓa duk wani abu da be zama dole ba, misali,ta na da babban gas cooker Wanda ake amfani da shi da wutar lantarki da gas,ban taɓa tabawa ba da sunan zan girki, na tarar da babban deep freezer Wanda Ke dauke da naman kan rago a ciki ko da Wasa ban buɗe dan na yi amfani da shi ba na buɗe ne dan na gan shi a kunne nake mamakin gida ba kowa kuma a kunna freezer? Ina duba wa se na yi ido biyu da naman kan rago babba,da risho na ke amfani tukwane ma ban taɓa na 'yan gayu ba duk da cewa kafin na yi gobara wanda nake amfani da shi sun fi wannan amma haka na dauke kai na daga taɓa duk wani abu da na san tsautsayi zai iya sawa na lalata musu, kar mu je daga kyautata mana mu kuma mu zaqe. Mutanen gida can Kano da Bauchi da suka ji labari sun jajanta mana ainun, domin ba qaramin jarabawar rayuwa mu ka shiga ba a wannan lokacin. Akwai wasu lokutan da bawa kan shiga jarabawar rayuwa ko ina ya toshe masa, ya rasa inda zai saka ran shi ya ji dad'i,ya dinga ganin kamar mutane na sane da halin da yake ciki na neman taimako amma an qi a taimaka masa, a irin wannan lokacin wasu imanin su ke qaruwa wasu kuma ya ragu ko ma ya tafi gaba ɗaya su rasa shi, Alhamdulillahi halin da muka shiga bai raunata imanin mu ba, hasali ma ba mu ɗora ran cewa wani ne zai fidda mu daga wannan halin da muke ciki ba, mun yarda kuma mun amince sannan mun karbi jarabawar mu da hannu bibbiyu muna ta hamdala da istighfari, mun miqa wuya ga Allah mu na neman ya taimaka mana ya kawo mana mafita mafi alkhairi. Gaba ɗaya kayan da za mu saka ma ba wasu masu yawa bane, domin gobara ta cinye kaso 90% a cikin kayan mu, Allah ya sa Baban Ameenah ya bamu atampa guda biyu shadda ɗaya, sai Malama Sa'a da ke da makarantar islamiyya a unguwar ta bamu atampa ɗaya, sai Maryam matar Uncle Inuwa ta bani kayan bacci guda biyu,to wannan kayan su muka samu wajen mutane, muka ajiye saboda gabatowar bikin Ameenah qanwata da za a yi nan da wasu watanni masu zuwa. Abincin da za mu ci kuwa tun mu na iya affording ɗin siyan kayan miya, se da muka zo mu ka koma cin mai da yaji, har yajin ya qare muke saka mai da maggi da gishiri,Maggi ya qare mu ka koma cin shinkafa da mai da gishiri, mai ya qare mu ka hau duba jarkokin mai da muka tarar a store mu na Kalen man da za mu saka a abincin mu, can qasan zuciya ta ina mamakin dangi na da dangin Yah Maheer kowa shiru ba wani taimako da ya zo mana, daga baya na cire tunanin nan a rai na, na sa wa zuciya ta cewar wannan jarabawa ce daga Allah subhanahu wata'ala, ya toshe mana hanyoyin samun arziqin duniya a yanzu ne domin ya bamu na lahira, se na fara addu'ar rabbana atina fidduniya hasanatan wa fil akheerati hasanatan wa qina adhabannar, ina yi ina qasqantar da kai na wajen mai bayarwa da ya buda mana hanyoyin samu, su ma da da nake saka rai su taimaka mana ban sani ba ko akwai wani abu da ya hana su hakan, ban sani ba ko suma a wanne halin suke ciki, nan da nan na sake kwantar kai na da tunani da kuma jiran taimako daga wajen wasu saboda ba su suka halicce mu ba, wanda ya halicce mu ya san za mu iya jurewa ne shi yasa ya kawo mu wannan matsayin. Yah Maheer ya umarce ni dama tun randa mu ka yi gobarar akan cewa duk wanda ya tambaye ni na ce ba wani sosai bane amma mun samu gidan da za mu koma da zama, haka na dinga faɗa wa 'yan uwa na, da na shi, duk da cewar na tabbata a yanayin yanda suke jin tashin hankali a murya ta da tashi sun san ba qaramar gobara muka yi ba. Yah Maheer ya yi iya qoqarin shi dan ganin ya kwantar min da hankali ya kuma nuna min in har ya samu dama zai maida min duk abinda na rasa da ma mafiyin hakan, a kullum muka zauna se ya yaba min akan yanda nake handling situation din da muke ciki. Ana haka ban san ina ya samo kuɗi ba ya siyo mana kayan abincin da za su kai mu sati ɗaya haka,da mai da maggi da yaji,buɗe freezer ɗin da naman kan da muka tarar a gidan na yi na ajiye kayan miyan da na wanke mana dan mu na diba a hankali kar su lalace. Kallon naman kan na yi a raina ina ayyana wataqila sun ajiye ne in sun dawo ya zamana su na da abinda za su dafa, rufewa na yi na kama hanya na koma kitchen na ci gaba da aiki na. Ina aiki mu ka ji sallamar namiji, hijabi na umarci Suwaidatu da ta miqo min na sanya na fita, wani matashi na gani wanda ke kama da mai gidan da muke ciki,gaishe da juna mu ka yi sannan ya qara da cewa, "Dama Hajiya ce ta aiko ni in taho in Karbi langab'u na kai mata" Tunani na hau yi na menene langab'u kuma ni Mahreen? Kallon shi na yi da nuna alamar tambaya na maimaita masa tambayar da ke cikin zuciya ta ta menene langab'u? "Naman kan rago da ke cikin freezer shi an ka ce na karb'o" Nan take na washe baki na ce, "Auhooo shi ne langab'u?? To ina zuwa," Nan da nan na shiga na samo buhu na ciro naman kan da kyar na miqa masa ya tafi, ina kyautata zaton garin cire naman kan nan ne na lalata musu freezer ba tare da na sani ba, ko kuma wajen wanke freezer ɗin na lalata musu shi dan kuwa ruwa na sa na wanke shi sosai saboda kar ya yi wari, se gashi abu ya dena yi. Na shiga tsananin tashin hankali da damuwa a lokacin nan saboda mutanen nan sun yi mana dukkan halaccin da be kamata a ce tsinke na lalata masu ba,na yi kuka kamar zan yi yaya, har sai da Yah Maheer ya ce zai kira Bashar ya sanar da shi ina ta kuka saboda freezer ya lalace sannan na hakura, amma da na tuna sai na ji cewar na aikata babban laifin da be kamata ace na yi ba. Mu na da wata daya a gidan Kabeer da abokan shi da wani ɗan yayar su Yah Maheer suka taho kawo mana ziyara dan ganin halin da muke ciki, kafin su zo na gyara gidan tasss na yi girki shinkafa da Miya har da lettuce suka samu da nama, Yah Maheer ba dai qoqari ba, nan da nan muka gama mu ka shiga wanka ni da Suwaidatu muka shirya mu na jiran baqin mu. Da azahar suka iso saboda sun kwana a Kano sannan suka d'akko hanya da asuba, shi yasa suka samu zuwa da wuri, zuwan su ya sa na ji dad'i a raina a qalla akwai dangin da suka tuna da mu a wannan matsin rayuwar da muka shiga. Ba su kwana ba aka gaisa suka kama hanya suka koma, kafin su tafi Kabeer ya ce zai shiga bandaki da ya shigo ya ba wa Suwaidatu dubu biyu ya bani dubu uku, dama abinda ya shigar da shi kenan se ya juya ya koma,ina so in masa godiya ma ko kula ni be yi ba ya fice, dan tunda suka zo dama na lura baya wani yi min fara'a se daure fuska yake (ban sani ba ashe ana can ana min zagon qasa a gidan shi). Har bakin motar su Yah Maheer ya raka su ya dawo, nan muke nuna masa abinda aka bamu, qara mana dubu biyar ya yi ya ce mu kai ɗinkin kayan mu da na ce zamu je bikin Ameenah da su, atampopin da shaddar gaba ɗaya masu sauqin kuɗi ne ni Kuma a lokacin nan se na ji haushin rashin sanin wani telan da ke da sauqin yanke kudin dinki dan Yakubu ya gwanance a ɗinki shi yasa aka san shi a garin sosai,dan haka yake tsula kuɗi yanda ya ga dama. Ba dan na so ba haka muka ɗauki ɗinkin mu muka kai masa ya gwada mu muka dawo gida. A wannan lokacin rayuwa ta yi mana zafi,gashi yanda na saba iyaye na su taimaka mana a koda yaushe in muna buqatar taimako shiru ba wanda ya sake neman mu ya ji a wanne hali muke ciki, kowa hankalin shi ya dauku zuwa hidimar biki, mu kuwa daidai da sabon takalmin da za mu saka mu je bikin babu balle sarqa da dankunne ko mayafi da jaka. Wasu lokutan duk saurin kuka na in na keb'e Ina so na yi kuka akan halin da muka shiga sai na daure na hana hawaye na zuba saboda a qasan rai na ina jin kamar in na yi kuka Allah zai fushi da ni, saboda na kasa jure jarabawar da ya yi mana. A haka muke ta gungura rayuwa har lokacin bikin ya zo, aka samu albashi Yah Maheer ya bani dubu ashirin na je na siyo mana takalma har shi,duk da ba da shi zamu ba ya na buqatar takalmi malamin makarantar poly yake be kamata ace ya na zuwa da nakasasshen takalmi ba, ko ba me tsada ba a qalla ya sa me kyau ba wanda ya tsufa ya yage ba, yadi na sai masa mai sauqin kuɗi na ce ya dinka ya sabunta akan suturar da ta yi masa saura, cikin dare na ji ya na kuka a sallah ya na min addu'a tare da yi wa Allah kirari da magiyar ya kawo mana sassauci . Da safe mun gaisa da shi ya miqa min hannu na je gare shi ya rungume ni ya ce, "Baby na Allah ya miki albarka, Allah ya warware mana halin da muke ciki, ki qara hakuri akan wanda ki ke yi, ina kula da ke baki da lafiya amma ki ke jurewa ki ke danne wa kar na gani, inshaa Allahu watarana za ki yi dariya a rayuwar ki, yanzu ki sanar da ni ina da ina ke maki ciwo?" Tunda ya fara magana nake kuka, saboda ni kaɗai na san me nake ji a jiki na, ba zan iya misalta masa me ke min ciwo ba, ban san ina zan nuna takamaimai guda ɗaya na ce nan ne ke min ciwo saboda hatta da fatar saman ido na ciwo take min, na yi dauriyar na yi juriyar har na kasa jurewa dole da asuba na hau kuka a boye, da alama kukan nawa ya gani ya gane banda lafiya. Cikin kuɗin da muke da shi ya dauka ya je ya hado min magunguna dan na yi rantsuwa ba zani asibiti ba, ya kada ya rawa na qi na ce ba zani ba, qarshe ma da ya dame ni se na saka masa kuka dole ya kyale ni, tunani na yi in muka je kullum se an ce za a min scanning dan a ga me ke sa ni ciwon ciki, ga kudin magani gashi ba lallai na gama zirga zirga a rana daya ai se kudin tafiyar tamu ya qare ba kuma a sai abinci ba. Cikin dare kuwa jiki na ya dauki wani irin zafin da bai da misali banda jijjiga ba abinda ya ke yi hawayen tunanin ko dai rasuwa zan yi ne ke ta zuba a idanu na. Se da na yi sati ina jinya sosai bamu san me ke damu na ba, a hankali na warke, na koma normal, cikin satin da za a yi bikin kuwa mu ka shirya dan tafiya bikin Ameenah Kano........... 💅 MAHREEN 💅 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 31: Mun isa garin Kano da misalin uku da rabi na rana, gidan shiru saboda a wannan lokacin 'yan biki basu fara zuwa ba, tunda sauran sati ɗaya da wasu kwanaki ne,kowa na can cikin gida, amarya ta tafi gidan qanwar Mama gyaran jiki can bawo road, sudanis ne sun iya gyaran jiki sosai, a hankali muka ja akwatin mu muka shiga gidan, a zato na bayan an gaisa za a d'akko maganar gobarar da mu kai dan a yi mana jaje, a lokacin na yi niyyar bayyana yanda abun ya faru saboda in da taimakon da za a yi mana a yi mana, amma duk wanda mu ka gaisa a gidan se na ga ba wanda ya damu da ya ji ya abun ya kasance. Kayan jikin mu kawai sun isa shaidar sauyin rayuwar da muka samu, shiru na yi na hadiye abinda nake ji na tausayin kai na a cikin 'yan uwa, nima na faɗa hidimar biki tsundum, dama Yah Maheer ya bani dubu goma gudummawar biki, na bayar na riqe sauran dubu goma da ya ce na riqe a hannu na ko zan buqaci wani abun a ciki na je na yi qunshi aka yi wa Suwaidatu baqi da ja itama . Mu na nan zaune duk wata hidima da za a yi ban ware kai na ba kamar yanda ba wanda ya ware ni, har zuwa ranar da Addah Babba ta zo gidan, na yi murna sosai da ganin ta itama ta yi murna sosai da gani na domin mun jima bamu haɗu ba, sai dai ta zo ba ta da lafiya ni na zauna kusa da ita har ranar da aka fara gudanar da bikin, bikin da ya tara dangi masu dimbin yawa da abokan arziqi, kamar yanda kowa ke kwalliya nima haka na sanya ɗaya daga cikin ɗinkin mu da Yakubu tsara mana, gaba ɗaya fitted gown ya min sai dai yanayin style din kowacce daban ne, se gashi na yi wani irin kyau me ban mamaki kamar wadda ta sanya kaya masu shegen tsada,duk inda na shiga sai an yaba kyan da na yi, ganin dangi da abokan arziqi sai ya mantar da ni duk Wani baqin ciki da damuwa da ke raina, hankali na ya kwanta na wannan lokacin, duk kuma inda amarya take ina nan biye kamar yanda ta min a biki na ta na kusa da ni koda yaushe nima haka na kasance a bikin ta se inda na ga be dace ace yayar amarya na wajen ba se na bar ta da qawayen ta. Ranar da aka yi dinner kuwa na sha kuka musamman da aka sanya Waqar Ameenah Ameenah 'yar Auta Ameenah Tauraruwar mata....na kasa dena kukan farin ciki a wannan lokacin ita kan ta amarya se da ta yi kuka ganin yanda wajen ya cika da dangin ta da masoyan ta. Mu ne har azare mu ka raka amarya d'akin ta, Masha Allah gidan Ameenah ba qaramin kyau ya yi ba alhamdulillahi, kwanan mu ɗaya washegari mu ka kamo hanya mu ka koma Kano, daga nan muka je bauchi ziyara zuwa na gidan su Yah Maheer na ga tarbar da ta min dad'i domin kuwa duk sanda mutum ya maka alkhairi ka faɗa,sun nuna alhini da kuma jajanta min gobarar da mu ka yi sannan sun yi mana addu'ar neman tsari kar Allah ya maimaita mana shiga wannan mummunan hali a gaba, godiya na dinga musu har ina hawaye saboda na ji dad'in yanda su ka tuna kuma su ka jajanta mana ainun, kamar koda yaushe se da na dinga kai ziyara daga wannan gida na shiga na fita wancan ba hutawa, ranar qarshe da zan gama ziyara ne na je gidan Rasheedah babbar 'yar Yayar Yah Maheer wanda duk zuwan da zan yi sai na je gaishe ta kamar ibada, daga qarshe na je gidan Ruqayya qanwar Yah Maheer ɗin da suke Mama ɗaya, sai gidan Cousin din shi Ladidi mutuniyar kirki da son zumunci, bana manta wa ina Bauchi ta na yawan kawo min ziyara ta na so na tsakani da Allah. Da yamma muka koma gida a gajiye,abinci muka ci na yi wanka sannan na sanar da su cewar gobe za mu tafi bauchi daga nan mu koma Kano inshaa Allahu. A cikin daren Ummah ta sa aka je gidan Dada (Yayar su Yah Maheer babba) aka karbo daddawa da kuka da kubewa busasshiya da kanwa se albasa wanda tun zuwanmu ta aika kuɗi aka yi mana wannan dakan, na ji dad'i sosai na samu kayan na killace su a cikin kayan mu, sannan muka yi shirin bacci. Da asuba bayan na yi sallah gari ya waye na yi sharar tsakar gida, na sa yara suka wanke banɗaki sannan muka ci abinci, da misalin tara da rabi na safe mun gama shirin tafiya Bauchi, har tasha yaran gidan suka raka mu, mu ka rabu cikin kewa da qaunar juna. Gidan Husaini muka sauka bayan mun isa, mun samu tarba kadaran kadahan, da yamma lisss na shirya muka wuce gidan Addah Ummu na a can muka kwana washegari mu ka tafi Kano. A hanya ina ta addu'ar samun iyaye na cikin walwalar su da lafiyar su tare da fatan Allah ya sa su nuna min soyayyar su da suke nuna min tun ina qarama, bana son yanda muka koma kamar baqi, ban da dogon burin sai sun taimaka mana dole amma ina da burin ganin mu tare kamar da mu na fara'a da annashuwa da juna musamman Babana,murmushin su da soyayyar su a gare ni ta fi kudi da duk wani abun duniya da zan samu, zan iya hakuri na ci gaba da rayuwa a gidan miji na a cikin halin samu da rashi ni dai su dena daure min fuska. Ina addu'a ina hawaye har se da na rasa abinda zan roqa a wajen Allah sannan na samu hawaye na suka tsaya, ko kafin na isa Kano ido na sun yi luhu luhu, a haka mota ta tsaya a tasha mu ka samu taxi zuwa kabuga daga kabuga muka dau adaidaita sahu har gidan mu. Ina zuwa kuwa na ga fa'idar addu'a nan take na tabbatar da cewa biki ne ya ɗauke min hankalin su ba wai sun daure min bane dan ba su son taimaka min kamar yanda zuciya ta ta raya min, ranar hira na sha a bangaren Baba kamar kar mu rabu, labarai kuwa na sha su har wanda ya na primary se da ya bani. Washegari kuwa muka shirya da ni da shi mu ka dauki hanyar zuwa gaishe da Mahaifiyar shi daga nan mu ka je gidan Innata muka gaishe ta , mu ma je gidan qannen shi da ke danladi na sidi, da gidan Babban abokin shi, mu na tafe mu na hira kamar kar ranar ta qare, Baba ya yi yawo da ni sosai a gari duk kuma inda mu ka je se ya sanar da ni nan fa waje kaza ne, ko ya ce, 'Nan mun taba zuwa ni da wane, nan kuwa kin ga mu na yara daji ne, Ohhhh ki ga wajen nan haka ya dawo? Ikon Allah wato na kula Kano har ka gama rayuwar ka wani wajen ma ba za ka san akwai shi ba' Ire-iren wannan labaran ne ya dinga gudana a tsakanin mu, alhamdulillahi ko da be tambayi maganar gobarar da mu kai ba ya wanke min duk wani quncin zuciya ta, na ji cewar har yanzu iyaye na na so na, ba wai yada ni suka yi ba saboda bani da shi, dama can me nake basu? Me nake da shi har da za su share ni dan ya qare? A koda yaushe a jikin su nake a maqale kamar jinjira, su ke yi min abubuwan da ba za su misaltu ba, tunawa na yi da yarinta ta yanda suka sha jinyar nakasa ta kuma har yanzu da girma na su na shan wahalar jinya ta da aljihun su da zuciyoyin su, tunda in banda lafiya ran su na quna saboda tausayi na. Da leda niqi niqi muka koma gida Baba ya yi siyayyar kayan miya da kayan kwalama. Nan da nan na sake kamar wani abu be taɓa faruwa ba, na yi kyau na murje a 'yan kwanakin, ba jimawa kuma mu ka fara shirin komawa garin Kebbi,inda Baba ya bani dubu ashirin, Mama ta bani biyar,sai Umma ta sai wa Suwaidatu biscuits da sweets, godiya muka dinga musu, washegari da asuba bayan na je gaishe da Baba ya min nasihar shi me ratsa zuciya da kwantar min da hankali tare da dasa min wani irin hakuri da tsoron Allah a cikin rai na,Baba ya sanar da ni cewar, "Mahreen duk jarabawar da ki ka ga ta samu bawa daga Allah ne, ba wanda ya isa ya azurta ka ko ya talauta ka bayan Allah, da zaki san tarihin mahaifiyar ki da irin gidan da na auro ta da kuma wahalar da ta sha a cikin aure na da kin gane cewa ki na cikin ni'imar Allah, tabbas kema ki na d'and'ana jarabawar rayuwa,amma ki sani bayan wuya sai dad'i ki dinga duba ladan da za ki samu in ki ka yi ibadar ki daidai,kar ki duba girman wahalar ki ke sha ki duba girman wanda ki ke wa ibadar da kuma girman sakamakon da zai maki,me yasa na dage na dinga sai maku abinci kala kala? Dawa, gero, shinkafa 'yar Hausa, da sauran su? Duk dan ku koyi zama a kowanne situation ku ka samu kan ku ne, dan haka ki qara hakuri Allah na tare da ke, game da maganar rashin lafiyar ki kuma duk abinda ki ke so in dai na neman lafiyar ki ne ki tambaye ni ko nawa ne in ina da shi zan baki, in bani da shi zan nemi hanyar da ta dace na miki, ki riqe mijin ki da kyautatawa, ya na son ki, ya na ji dake ya na kuma kula da dukkan lamuran ki, dan haka kar ki gaza kema wajen nuna masa soyayyar ki, ki yawaita yi masa murmushin nan naki me kyau, hushiryar nan ta fito sosai, kar ki dinga bata rai ki na shan kunu, (ya gwada yanda nake yi in ina fushi😭😭kuka na ya qi tsayawa tunawa da wannan nasihohin ba zan taɓa manta su ba har abada jin su nake kamar yanzu ne Baba ke yi min su) ki riqe ibada

Chapter 25 of 30