gaf da la'asar,a gurguje na sake watsa ruwa saboda zafi,na yi alwala na yi sallah na faɗa kitchen, wake da shinkafa na yi ina da yaji na me dad'i da aka kawon daga Sokoto, se na yi miya da sauran nama da ya rage na yanka cabbage da lettuce a waje guda, na wanke na goga carrot na yanka cucumber sannan na wanke albasa da tumatur na aje na ce se ya dawo sannan in yanka nashi.
Kankana da abarba na gyara na yi blending na goga citta danya na matse lemon zaqi na haɗa lemo na da shi na sa a babban jug di na na roba na sa a fridge na rage mana a roba ni da Suwaidatu muka mayar cups muka sha.
Ina gama shanye wa na ce wa Suwaidatu ta dauki abincin mu ta kai wajen Maman Ameerah ta ce gani nan zuwa, dan so nake na yi kwalliya kar muna cin abinci ya dawo ban kimtsa ba.
Yarinya na kai abinci duk da cewa na saka kayan lambun nan a ciki da mai da yaji ne, maman Ameerah na gani se ta ja tsaki, sannan ta ce,
"Wai matar nan za ta kashe ni da mai da yaji ne?"
Da jin haka sai Suwaidatu ta taho ta sanar da ni, ji na yi maganar ta dake ni, menene ya kai da kiran zan kashe ta bayan ta fini yin mai da yaji, kusan ko da yaushe taliya da mai da yaji take dafawa, a zato na ma sha'awar mai da yaji take, ni ma kuma ina son mai da yaji shi yasa ban wani damu ba, su yaran da miya na saka masu,in miya take so sai kawai ta ce miya nake so meye wani zan kashe ta.
Nan take da na je kuwa na faɗa mata abinda ke raina na ce,
"Habaa Maman Ameerah wace iriyar magana ce zan kashe ki da mai da yaji? In Miya ki ke so akwai miya dama na zaci kin fi son mai da yajin ne ai tunda na ga ki na yawan yin taliya da mai da yaji"
"Kai yarinyar nan munafuka ce har ta faɗa miki?"
Ta na magana ta na dariya, na kuwa ce,
"Ai ba zancen munafurci se gaskiya, Allah ya baki hakuri kawai zan ce amma banda niyyar kashe ki da mai da yaji"
Na ɗauki abinci na na bar wajen, dama na jima ina son na samu hanyar da za a dena wannan ciyayyar mara amfani ka bar miji ya ci abinci shi kaɗai ka je ci da maqociya.
Tin daga ranar na dena wannan ciyayyar yaran ma suka dena zuwa.
Ba tare da na sani ba ashe wai abinda na yi ya mata zafi,ni kuwa a gani na na sauqaqe mata ne tunda dama so take a dena nima kuma so nake a dena tunda haka ta faru ba shikenan ba kowa se ya dinga cin abinda yake so ya qi cin wanda baya so?
Ban sake bi ta kan su ba, iyaka in na sabunta abincin da na san zai shiga haqqin maqota sai na aika musu, ban damu da se ta bani nasu ba sam.
Ana haka na fara qoqarin zuwa maqotan mu kitso,gidan wata dattijuwar kirki da ake kira da Mama, Mama na da yara biyu mace da namiji, Ameenah ita ce babba, sai Ameenu da ke bi mata, mijin Mama shi ma mutumin kirki ne kwarai, domin ni halayen shi na yi min kama da na Babana har cikin raina se na ji soyayyar mutanen ta kama ni, Ameenah kusan sa'a ta ce shekara ɗaya na bata, se Ameenu da zai yi sa'an Ummussalama qanwa ta da ke bi min.
Ganin mun fara sabawa da mutanen gidan sai Maman Ameerah ta fara jin ba dad'i a hankali ta fara kawo min sukar mutanen, ta na sanar da ni munanan halayen da Mama take da shi wanda qarya ne kawai,ban san dalilin yin hakan ba,har na fara yarda da ita, se na janye jiki na na rage zuwa, daga kitso ba abinda nake qara yi a gidan nake komawa gida na, daga baya ma se na ɗauke qafa ta saboda ni se na yi sama da wata biyar dama ban kitso ba, kusan kullum kai na a gyare yake bana wasa da tsaftar shi amma fa kitso be damen ba dama samu akai nake zuwa, se kawai na dena, shiga maqota ba hali na bane se idan wani abun jaje ko murna ya faru na je, duk irin abubuwan da nake na yau da kullum a cikin gida nake yin sa ba lallai sai na fita ba, jin cewa Maman Ameenah ba ta da halin kwarai duk da na so qulla alaqa da su se na sake d'aure qafafu na a cikin gida na maida hankali wajen karatun Nabteb da za mu yi kafin waec.
*********************************
Jarabawa ta yi jarabawa, in na ce jarabawa ta yi jarabawa ina nufin daga jarabawar makaranta har ta rayuwa ta kowaccen su ta tsananta a gare ni,zuwa makaranta kawai nake amma bani da cikakkiyar lafiya, ji nake kamar in ajiye karatun in ce na fasa ba zan yi ba, ni kaɗai na san abinda nake ji a cikin jiki na tin daga tsokokin jiki na qasusuwa na har fata ta, Mamana ke bani kwarin guiwa da nuna min itama haka ta wahala a lokacin ta na zuwa school of nursing, ga ciki na ga karatu ga kula da iyali,a haka ta ci gaba bata tsaya ba, dan haka in dage in ci gaba ni ma watarana sai dai na bada labari,in an kwana biyu ta aika min da 'yan kuɗaɗe ko wasu abubuwan marmarin ta tashar mota mu karba,ta ɓangaren Baba ma ba a bar shi a baya ba,haka zai ta tura min kuɗi dubu goma dubu ashirin ya ce gashi na sai magani Allah ya bani lafiya in qara hakuri jarabawa ce watarana sai labari, na kan yi kuka sosai har sai na yi wa kai na da kai na faɗa sannan na ke lallashin kai na da cewar idan na rasa wasu abubuwan ai ga babbar kyauta Allah ya yi min, ya bani miji na gari, wanda baya son ya ga damuwa ta bari na qarfafa kai na ko dan nashi farin cikin, haka zan daure na jure duk wani ciwo da nake ji a cikin jiki na.
A haka na ci gaba da zuwa makaranta da dad'i ba dad'i, da ciwo da damuwar guduwa da kuɗin mu da masu Islamic chemist su ka yi,domin kuwa da ciwo ya tsananta a gare ni sai muka nemi Islamic chemist ɗin da na ji ana tallan shi a Kebbi TV, cikin ikon Allah muka fara zuwa da weekend, dama duk weekends suke buɗe wa, ko da muka je sai muka ga wajen ba mutane sosai an dan yi fenti a kangon da ke da dakuna biyu manya ciki da parlour sauran gidan duk jeji ne da ciyayi busassu, ba tare da zargin komai ba tunda mun ji ana tallan wajen a gidan Talabijin se bamu damu da yanayin da muka gan shi a ciki ba.
Nan da nan aka yi cike ciken takardu aka fara min ruqya ban nuna wata alama ta Aljanu ba har aka gama, magunguna aka qulla mana aka ce mu je na yi amfani da su na sati biyu sai mu dawo, Yah Maheer nan take ya aje musu dubu ashirin da uku kuɗin magani da ruqya.
Ko da muka koma gida da kan shi yake taimaka min ya dafa na dafawa ya bani na sha ya shafa min na shafawa, ga qurajen zafi da ke min azaba har cikin kai na, ko hijabi da nake sa wa na je makaranta dan ya zama dole ne, shi ya sa da an gama jarabawar ko Bashar be zo ba nake samun abun hawa na koma gida, Yah Maheer da kan shi yake sama min vest cikin kayana me shara-shara se na saka da wandon makarantar na sa hijabi na tafi.
A haka har magani ya qare ba wani sauqi sai daga wajen Allah madaukakin sarki,a wahale nake zuwa makaranta a wahale nake dawowa kullum, maqociya ta itama ta kan ta take dan kuwa cikin ta ya kai watanni bakwai zuwa takwas a wannan lokacin itama zafin ya ishe ta, sanda na cika sati biyu da gama shan maganin se muka koma wajen masu magani,sai suka ce mu bada dubu sha bakwai za a min haɗin magani wanda yake kankat ne da izinin Allah in na sha zan warke, kusan kuɗin da Yah Maheer ke da shi a wannan lokacin ma ba zai isa ba, dan haka dole sai da ya nemo bashi muka cika muka je aka kai kuɗi,sai cewa suka yi mu je mu dawo ranar alkhamis,ranar alkhamis ban samu zuwa da wuri ba saboda ina da jarabawa da safe sai bayan na taso muka je,ko da muka je sai mu ka ga waje wayam kamar ba a taba zama a wajen ba, se na ce wataqila dan mun makara ne, gobe se na dawo, Yah Maheer ya ce Allah ya kaimu, na haye bayan machine ɗin shi na kwantar da kai a bayan shi,saboda yanda nake ji kamar ana juya ni ga kuma zafin rana ga yunwa ina ji,haka muka koma gida cikin jimamin rashin samun bayin Allahn nan da ba mu yi ba.
In taqaita maku makaranta sai da muka jera sati biyu muna zuwa ba ma samun su, akwai wata rana sai mu ka yanke shawara tunda dama da weekends muke samun su a da me zai hana mu dena zuwa ranar alkhamis din mana mu je ranar asabar kawai, ko da muka je ranar asabar nan ma wajen ba kowa haka muka samu waje muka rakub'e saboda rana, mun fi awa biyu zaune mu na jiran su shiru, sai wani bawan Allah ne ya zo ya mana sallama,ya gaisa da Yah Maheer sannan ya tambaye mu wai wajen wa muke zuwa ya na yawan ganin mu anan, da fatan dai ba wajen macutan nan muka zo ba, ai Yah Maheer na jin an kira macuta hankalin shi ya dawo jikin shi ya gane ashe cutar mu akai, kai ya gyad'a wa mutumin sannan ya ce ba wajen su muka zo ba, sallama suka yi da juna na hau machine muka dawo gida bamu sake komawa wajen ba.
Ranar da za mu gama jarabawar qarshe a makarantar BICE, ita ce ranar da na kasa jure azabar da na ke ji a cikin jiki na,zafin da nake ji na ciwo ya fi qarfin a kira shi da zafin wuta, ji nake kamar ana d'aye min fata ta ana zuba gishiri ko ruwan zafi, na rasa inda zan saka kai na in ji sanyi.
Muna zaune a ajin 'yan primary kawai na miqe tsaye, takalmi na ma ashe guda ɗaya na saka, kai na duk ya sha hodar zafi ya yi fururu har ta goshi na ana iya hangowa, idanu na sun yi jawur saboda azaba, Geography muka rubuta dama abinda ya rage mana map reading ne kawai, tafe nake ina addu'ar Allah ya sanyaya mini ya sassauta min, idan wani laifi nake aikatawa na tuba ya yafe min ba zan sake ba, idan jarabawar rayuwa ta ce haka ya bani hakuri da juriya na cinye jarabawar kar na gaza na yi raki.
Har na isa bakin titi ban fahimci me nake yi ba sai da A'isha Hafiz ta biyo ni da warin takalmi na, ta tsaida ni, ta ce,
"Aunty Ina zaki bamu gama jarabawar ba, sauran mu map reading fa,ga takalmin ki, Aunty are you ok?"
Wasu hawaye ne masu bala'in zafi suka taru a ido na, nan da nan na yi qoqarin maida su na ce,
"A'isha bani da lafiya ba zan iya tsayawa ba,Allah ya sanya wa abinda na rubuta a baya albarka,sai watarana"
"Allah ya baki lafiya aunty,Allah ya sawaqe,"
Ina kallon ta ta juya tana d'an dingisawa saboda ciwon qafa itama da take da shi ta koma makaranta,tawa qafar ce ta harba da nata dad'add'en ciwon, murmushi na yi na sa kai na ci gaba da tafiya, Hafsat T/fana ce ta fad'o min a rai, ba abinda zan ce mata sai godiya, lokuta da dama in ina cikin wannan yanayi na rashin lafiya ita ke maida ni gida ko drivern su in ya zo ɗaukan su ta ce a kai ni gida, ban sani ba ko ta san halin da nake ciki ko bata sani ba kawai taimaka min take, dan bana zama na faɗa wa mutane yanayin da nake ciki, a kullum ina qunshe da lalurori na daga ni sai Allah,miji na, iyaye na da 'yan uwa na.
Juyawa na yi na sake kallon gate ɗin makarantar ban ga Hafsat ta fito ba, sai kawai na ci gaba da tafiya, gashi bani da kuɗin machine, tafiyar da nisa ba zan iya zuwa a qafa ba tafe nake ina nishin wahala idanu na na son zubar da ruwan da ke cikin su amma na danne na hana su fita, wata qara na ji kamar ta hatsarin abun hawa daf da ni a tsorace kuma a kid'ime na kulle ido na ina jiran na ji mota ko machine ko adaidaita sahu ya Shure ni na yi gaba.............
(Tunawa da irin memories ɗin nan is not easy wallahi, za ka yi tunanin ka warke amma ciwon na nan a cikin rai😭)
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 25:
Machine ne ya ci burki a baya na da qarfin gaske, ina buɗe ido na a hankali sai na kula na bar kan hanya na fara hawa titi, mutumin har ya fara masifa sai ya kula da yanayi na, cikin rage faɗan da ya fara min ya ce,
"Ke Wagga lahiya ki ke kuwa?"
Nan da nan kuwa hawayen da nake ta maqalewa suka hau sauka da gudu, zafin su na qona kumatu na na durqusa na ɗauki jaka ta da ta fad'i na ci gaba da tafiya, biyo ni ya yi ya ce na hau ya kai ni gida,Na so na yi musu sai na ga Kabu kabu ne ko banda kuɗi zan iya tsayawa maqota na karba na biya na basu daga baya dan dai nera saba'in in Allah ya yarda ba zan rasa me ara min ba.
Komawa baya na yi na hau a hankali na sanar da shi Alieru qtrs za a kai ni,nan da nan kuwa ya dauki hanya sai unguwar mu, mu na isa na ce ya jira na dakko masa kuɗin shi ya ce min,
"Basshi d'ai" (barshi kawai)
Godiya na masa na shige cikin gida, ina shiga na yi wurgi da hijabi na na kwanta a qasan carpet na kunna standing fan dama ta saman a kunne take, kuka na buɗe baki da qarfi ina yi, saboda ciwon da ko ina na jiki na yake min, na yi kukan da ban taɓa yi ba a rayuwa ta ranar har se da bacci ya ɗauke ni,Ko juyi na yi sai na b'are baki na ci gaba da kuka na kafin wani baccin ya sake ɗauka ta.
Duk abin nan da ake na rashin lafiya ta ban taɓa qin yin girki ba, saboda Yah Maheer baya son cin wani abincin in ba nawa ba sai dai in lalurar hakan ta kama ya zama ba yanda zai yi to zai ci a wani wajen, se kuma in mun je gida, ko maqota ne suka kawo abinci baya ci, tin da na dawo garin ya dena cin abincin kowa.
Wata rana da jima wa ban mantawa mu na hira da Maman Ameerah a game da maza da ke cin abinci a ko ina, se na ke faɗin cewa shi baya da wannan halin gaskiya duk da ya kan ci amma se dole,cikin nuna jin haushi ta ce,
'Wa ya faɗa maki baya cin abincin waje?'
'Ba ina nufin ba ya cin abincin waje kwata kwata ba, in dai Ina nan ba ya cin abincin ko ina ya gwammace ya zauna da yunwa ko ya yi ta shan fruits, shi ya sa sanda ya fara zama a garin nan duk sanda ya je zan ga ya rame'
'Ai kuwa ya na cin nawa, kuma rama da ya yi ai saboda ciwon qodar da ya yi ne baki ga har baqi ya yi ba a lokacin,kuma haka ɗaliban shi mata za su dinga zuwa duba shi har abincin suke kawo masa, na kan ce Allah ya kiyaye kar su masa asiri tunda matan garin nan akwai shegen asiri in suka ga namiji su na so se ki ga budurwa ta kai shi wajen malami an asirice mata shi'
A lokacin nan na ji raina ya ɓaci wato a gaba na ne yake nuna ba ya son cin abincin kowa a bayan ido na se ya hau ci, ko da ya dawo na tare shi da maganar ina ta masifa, be ce min ci kan ki ba se da na gama sannan ya ce,
'Da ta faɗa maki ina cin abincin ta ta taba gani na da idon ta na ci abincin wani waje haka kawai ba dalili? Na tan ma saboda mijin ta na gayyata na ne kuma kin san babu kyau a gayyace ka cin abinci ka qi, ke kin ga shaida ai sanda ku ka zo bread ne se fresh milk da fruits su ne abinci na na kan kuma sai nama haka da kifi soyayye na ci, kuma da take maganar 'yan mata ba ɗalibai na bane, sannan ba sanadin na kwanta jinya suka zo duba ni ba? Yanda suka kai haka suke kwashewa tunda ba iya ci ma nake ba, kaiii wannan matar na rasa me yasa take so dole sai ta ja min masifa ina zaune lafiya da iyali na, sannan in banda abinki Zan zauna da yunwa ne idan na ji ina son cin wani abu ba bread ba ke da kan ki ki ke matsa min se na je na siya na ci, ra'ayi na ne bana so na ci wani abincin in ba naki ba, sannan kamawa take nake cin wani abincin idan ba nakin ba, ai komai dalili ne da shi ko? Dan Allah ki dena ɗaukan maganganun matar nan ba kowanne ne ke da amfani ba"
Yanda ya yi maganar ma ni se ya sanya ni dariya, sannan daga baya na gane ai duk abinda ya faɗa gaskiya ne zai kashe kan shi da yunwa ne in be ci abincin wani wajen ba a sanda bana nan? Hira muka ci gaba da yi ya na sanar da ni yanda zan dinga zama da mutane ba komai ne za a faɗa min in dinga dauka ba, wani burin shi ya hana ka zaman lafiya,a haka dai mukai ta hira kala kala har aka manta da zancen.
Ajiyar zuciya na sauke mai qarfi bayan na gama dogon tunani na,a daddafe na tashi na shiga kitchen na yi girki, taliya ce kawai na dafa dama ina da miya, se na yanka lemo da kankana na ajiye sannan na yi wanka na yi sallar la'asar da ta jima da wuce wa.
Wata riga ta na sanya wadda za a kira ta da net, Dan kuwa Shara Shara ce sosai, sai pant da na saka shi kaɗai, zaune nake ina shan iska Suwaidatu da ta dawo daga boko ina bacci ta yi shirin islamiyya ta tafi, dan ta makara sosai jira take dama na farka ta shirya ta tafi, nan take na tuna cewa BD na fa ya gabato December din nan zan cika shekara sha takwas cif-cif,murmushi ne ya kwace min, na hau murna,ni ma zan zama babba.
Maman Ameerah ce ta fito da daurin qirjin ta kamar kullum, zama ta yi a gefe na mu ka hau hira jefi jefi, cikin zumudi na ke sanar da ita cewar,
"Gobe fa BD dina,"
A d'age ta Kalle ni ta ce,
"Shekara nawa?"
"Inshaa Allahu gobe zan cika shekara sha takwaaaasss"
"Mtssswwwwww, ni na zaci ma kin kai ashirin ashe ke se yanzu ne zaki shekara sha takwas ɗin?"
Wani irin b'acin rai na ji ya kama ni, saboda ina da wani hali na tsani tsaki, ita kuma halin ta kenan, bata iya minti ashirin bata zabga shi ba, ni Ko ba da ni akai tsaki ba se na ji ba daɗi balle ayi da ni, kallon ta na yi ni ma a d'age dan na fara mayar mata martanin rashin kyautatawar ta nima a hankali ba tare da na sani ba ma.
"To ai dama kowa da shekarun shi a duniya nima iya nawa kenan, kuma ina alfahari da hakan na ji dad'i da zan cika shekara sha takwas Alhamdulillahi "
Surutai ta dinga yi ta kama hanya ta shige d'akin ta, mamaki ne ya kama ni menene na faɗa a cika shekara sha takwas? Da kai na na furta,
"Allah ya qara kema, me shegen surutun tsiya, komai se kin faɗa ai gashi nan"
Miqe wa na yi da kyar na shige nawa gidan raina a bace, da dare na zaci Yah Maheer ya manta da BD na, se na hau hira a fakaice ina fadan date of birth ɗina, ya na ji na be ce komai ba, haushi ya kama ni, saboda ni fa na ɗauki cika ta shekara sha takwas babban abu, ni ina ta BD ɗina shi ya na ta lafiya ta, dan rashin lafiyar da nake ba ta boyu a idon shi ba, sannan na sanar da shi ko map reading exam ban tsaya na qarasa ba gida na dawo, dan haka a dame yake, what if na zo ban samu na ci Geography ba da dai sauran tunane tunanen nan su suka haɗe masa suka hana shi kula ni.
Ina nan ina kumbura baki ya wuce masallaci sallahr Isha'i,ko da ya dawo na yi wanka na fito da katifa parlour,na yi readyn yin bacci, ina nan daga kwance mu na ta hirar gida dan kuwa ya ce da sallah can za mu je mu yi sallah,har qarfe sha biyu bacci ya qi dauka ta, kuma yau mu ne zamu kwana ba wuta se asuba a kawo, kamar jira suke kuwa ina kwance kawai se dif an ɗauke wuta, wani irin kuka ne ya tokare min wuta saboda na san yau ba zan bacci ba, banda ma rashin baccin da zan yi ciwon da qurajen nan za su hau yi min ba kaɗan bane domin dama ranar an kod'a rana.
Lallashi na Yah Maheer ya hau yi, ya ja maficin da ke gaba na ya hau yi min firfita, ni dai shiru kawai na yi bahaushe ya ce da babu gwanda ba dad'i amma kam bana wani jin firfitar nan, kula da hakan ne ya sa ya ce min,
"Baby na ki qara hakuri, na san zaki ta jin maqota sun kunna inji mu kuma shiru, ga AC a kowanne gida akwai ta amma mu shiru, inshaa Allahu watarana zan sa maki AC zafi ba zai dinga damun ki ba, zan kuma sai maki gen in ba wuta kawai se mu kunna gen ɗin mu mu kunna Acn mu mu sha ko?"
D'aga masa kai na yi a shagwab'e saboda da salon lallashin yake min magana kamar ana ririta ɗan yaron da ba a so ya yi rikici,a qarshe qofar parlour muka fita muka zauna ya shimfid'a abun sallah ya kwanta, nan da nan kuwa bacci ya ɗauke shi, saboda ya gaji,ni kuma yanda na ga rana haka na ga dare saboda ba ma zan iya baccin ba.
Washegari kuwa bayan Yah Maheer ya dawo daga masallaci sai na ji shiru be min addu'a ba, be taya ni murnar cika shekara sha takwas ba, se na hau fushi ina kumbura baki, nan take na tuna sanda na cika shekara sha bakwai a gidan shi lokacin mu na Bauchi, siyayyar kayan kwalama dangin zaqi da na fi so ya yi min,sannan da sassafe ya tura min message zazzafa da addu'o'i a ciki, me yasa wannan karon be min ba, fushin babu gaira babu dalili na hau yi, ina gama komai qarfe tara da rabi Baba ya kira ni, su na a tare da Mama, Waqar da mama ke min tun ina yarinya ta hau yi min,sannan ta min ta BD sannan ta min addu'a sosai Baba ma ya yi min addu'a sosai na dinga jin dad'i tare da yi musu godiya (Har yau in Mama na nishad'i mu kai waya to fa zata rangad'a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 30