muka tashi baki ɗaya dan zuwa sauke farali, bayan fitar Yah Maheer ne na idar da Sallah sai na ji motsin Maimunah a waje da yara, ai kuwa se na fita nima,na kora su zuwa sallah muka dasa hira da Maimunah,cikin hirar mu ne take sanar da ni mijin ta ya yi mata alqawarin ba zai mata kishiya ba sam, daga jin haka sai na ji ita fa a duniya ta gama more wa,nan da nan na qudirta nima idan Yah Maheer ya dawo zan tambaye shi zai min kishiya ko ba zai min ba.
Murna fal ciki na, dan kuwa na gama yanke irin amsar da zan samu duba da yanda yake masifar so na, muna ta hira sai gashi ya dawo shi da mijin Maimunah da alama ya sanar da shi maganar tafiyar shi, dan na ji ya na ta zabga mana fatan alkhairi, ciki suka shige suka bar mu anan waje, ba jimawa nima na bi Yah Maheer ciki, zaune na gan shi bakin gado da wasu takardu a hannun shi ya na dubawa, ban katse shi ba sai da ya gama ya sanya a jakar shi da yake tafiya da ita sannan ya haye gado da kyau, hannu ya miqa min na kuwa tafi da sauri na kama na haye jikin shi na zauna da kyau a qafafun shi ina kallon cikin idon shi, dan so nake ya ji kunya ta nima ya min irin alqawarin da aka yi wa Addah.
"Baby na da alama akwai magana a wannan cute lips ɗin naki, a hanzarta sanar da ni kafin na fitar da ita da kai na"
Dariya na yi sannan na ce,
"Ba sai ka fitar da ita ba ma zan faɗa maka, tambaya ce nake da ita, ina son dan Allah ka bani amsa ta gaskiya,"
Ja na ya yi jikin shi sosai ya rufe ragowar tazarar dake tsakanin mu, sannan ya hau shafa sassauqan gashin kaina da kullum yake shan gyara,"
"Uhmmmm ina jin ki, ni kuma Allah ya bani ikon amsa maki tambayar ki gaskiya da gaskiya"
"Ameeen na san ma gaskiya za ka faɗa dan ban taɓa kama ka da yi min qarya ba....ammmm Yah Maheer ɗinaaaa uhmmmm na ce dan Allah zaka yi min kishiya?"
Ina faɗin kalmar kishiya se ido na ya kawo hawaye har wani kyalli kyalli yake,
"Me ya sa ki ka kawo wannan maganar baby na?"
Cikin jikin shi na sake shigewa kamar wata mage sannan na hau mutsu mutsun shagwaba ina cewa sai ya amsa ni, gyaran murya ya yi ya ci serious, sannan ya d'aga ni na zauna sosai a gefen shi, shima ya jingina da jikin gado,nan da nan se na ji jiki na ya yi sanyi qalauuuuu, daga wannan 'yar tambayar shine se an yi wannan zaman za a bani amsa?
"Zan fara da tambayar ki in ki ka bani amsa Ni kuma na maki alqawarin zan baki amsa daidai da abinda ki ka tambaye Ni na gaskiya"
"Tom ina jin ka"
"Dan Allah gidan ku mace ɗaya Baba ke aure ko biyu?"
A sanyaye na ce,
"Mata biyu ne"
"Gidan mu fa?"
Wannan karon tura baki na nayi gaba, saboda da alama shima biyun zai yi.
"Biyu"
"Yauwaa, kin ga kenan nima idan Allah ya qaddara min zan yi mata biyu ko ina so ko bana so zan yi,ko bajima ko ba dad'e,komai na hannun Allah,mu yi fatan Allah ya mana zaɓi na alkhairi a komai na rayuwar mu"
Kuka na fashe da shi sosai kamar an ce min wani nawa ya mutu,kukan da sai da ya dinga qoqarin rufe min baki na dan har tsakar gida ana ji na,Yah Maheer ya gigice ya rasa yanda zai lallashe ni dan duk wata hanya da yake bi dan ya lallashe ni in Ina masa rikici ta toshe masa a wannan lokacin qarshe se rungume ni ya yi ya bar ni na shaqi kuka na me rai da lafiya har da su majina ido ya min luhu luhu. Ina jin na dena jin kukan se na goge hawaye na na Kalle Shi na ce,
"Yah Maheer,"
Cikin zaquwa ya ji me zan ce ya amsa ni, na kuwa ɗora da cewa,
"Ka ga kukan nan da na yi? Inshaa Allahu na gama kukan kishiya a rayuwa ta, duk randa zaka qara aure na maka alqawari ni Mahreen ba zan yi kuka ba"
Na murgud'a ɗan baki na na fisge daga riqon da ya min na sauka daga gadon, da sauri ya bi ni ya riqe, ji na yi wasu hawayen na biyo min kunci na, cije leb'e na na yi ina jin kamar na ture shi ya dena taɓa ni,
"Wai me ya kawo duk wannan tambayar ne? Tafiya fa zan yi jibi amma ki ke so ki daga min hankali, ke da ya kamata ki kwantar min da hankali a kwanakin da suka rage min amma ki ke kawo maganar da bata gaba na kwata kwata, haba baby Na wannan ba halin ki bane, dan Allah ki fada min a ina ki ka samo idea ɗin wannan kukan akan hasashen zan maki kishiya nan gaba?"
Nan na kwashe komai na sanar da shi,wato tsabar dariya se da ya kware da tari idon shi suka yi ja saboda hawaye,se zai yi magana se ya kwashe da dariya, nan da nan kuwa na sake b'are baki kamar gyad'a na hau wani sabon kukan, da kyar ya iya controlling kan shi ya dena dariyar.
"Yi hakuri to ni ma ba zan maki kishiya ba se in Allah ya hukunta ta na cikin qaddarar rayuwa ta babyn Maheer shi kaɗai,ke kan ki shaida ne duk duniya ban taɓa jin son wata 'ya mace ba bayan ke,ban taɓa zuwa gidan wata da sunan zance ba bayan ke, yanda nake jin son ki a rai na zai wahala wata ta samu matsuguni a zuciya ta, ke na tabbata ko aure zan qara nan gaba zai wahala na so matar sama da yanda nake son ki, ke ce jinin jiki na fa in babu ke ba zan rayu ba, ki yarda cewa qaddara ce kawai zata sa na qara aure shi yasa ba zan iya maki alqawarin ba zan maki kishiya ba, tinda ban san gobe ba"
Na gamsu kuma na yarda da dukkan abinda ya ce dan haka sai na hakura da qoqarin kwace jiki na da nake a nashi na bar shi ya juyar da ni mu na fuskantar juna ya na ta tsokana ta
Da yamma ya yi wanka ya fita wajen abokan shi dan ya musu sallama, ni kuma ya na fita na debi kayan shi da ya dawo da su daga wajen ɗinki, na hau gogewa tinda da wuta, se na ji haushi ya kama ni da na tuna sanda ya karb'o kayan daga wajen ɗinki ya gwada su a jikin shi dan na gani, a cewar shi ni zan fara ganin su a jikin shi kafin ya tafi Kebbin, kayan sun masa kyau sosai sun karbi farar fatar shi,wani abu nake ji me zafi zafi a raina, yanzu haka zai saka a can 'yammata su yi ta kallon shi wataqila ma a can qaddarar qaro auren ma take, da sauri na hau a'uziyya na ji kamar na je na yi wa Maimunah masifa da ta dasa min wannan mummunan tunanin.
Ban fita daga d'akin ba se da na gama haɗa masa jakar tafiyar shi, dan ni komai zan yi na fi so na yi shi kafin time ɗin da ake buqatar abun, bana so a jira ni, bana son jira, bayan na kammala se na shiga kitchen na ɗora abincin dare jelop din shinkafa ce da wake na yi se alayyahu da na sa a ciki, ina gamawa na je na yi wanka na sanya kaya na qanana masu mugun kyau,a lokacin nan ina ji da qirji na da qugu na dan kuwa ba karamin yaba su Yah Maheer ke yi ba, shi yasa nake ji na kamar na fi kowa kyau duk da na san ba haka bane.
(Advantage din namiji ya dinga yabawa matar shi a koda yaushe a komai ta yi, yana sa ta ji kamar ta fi kowa, wanda hakan shine daidai ya na hana mata qoqarin sai sun nuna wa duniya kyan su, tinda suna samun yabo a wajen wanda suke so ba su da buqatar wani ya yabe su)
Yah Maheer be dawo da wuri ba ranar se tara da rabi da minti shida, 9:36pm, ina nan zaune su Hauwa'u duk sun yi bacci, se ni kaɗai d'aki na na shige na cire hijabi na na kwanta, ina kwanciya ko gama miqe qafa ban ba ya murd'a hannun qofar bakin shi ɗauke da sallama,tashi na yi zaune ina jefa mashi murmushi na da kullum Baba ke ce min...
'Kar ki dena yi wa mijin ki wannan murmushin naki me kyau, ga hushirya Allah ya hore Maki, ko ran Shi ne ya ɓaci ya na kallon fuskar ki zai ji kwanciyar hankali, ki riqe murmushi da kyau ya na tausasa zuciyar me kallo'
Qara murmusawa na yi sannan na karbi ledar hannun shi na ajiye a gaban abincin mu, dan da gani babu tambaya nama ne a ciki,bayan mun gama marabar da nake masa in ya dawo,se muka wuce banɗaki ,na raka shi da ruwan da na riga na zuba a bokiti tin da na fito daga nawa wankan shi kawai nake jira dama, muna shiga na juya zan tafi na barshi ya yi wanka se ya riqe ni, bamu fito ba se da na taya shi wankan sannan muka fita a tare muka koma daki,brush ya dauka ya sake fita, kafin ya dawo na fitar masa da doguwar rigar da na taɓa siyo masa watarana da na je Kano ina dawowa, a hanya na ga ana siyarwa kawai na tsaya na sai masa, (kamar yanda yake yawan yi min kyauta haka Ni ma nake masa dan watarana ma da kuɗin shi zan dauka na sai masa abu ya yi ta murna ya na jin dad'i tare da sanya min albarka)
Turare na fesa mata sannan na zauna na duba naman da ya kawo se na ga qunshi biyu, ina tsaka da buɗe wa ya dawo se ya ce,
"Ki aje musu ɗaya ki juye mana d'ayan mu ci"
"To"
Turare ya fesa sannan ya samu waje ya zauna a saman carpet da na shimfid'a mana,abinci muka ci muka sha ruwa muka qoshi sannan na kwashe kwanukan na mayar kitchen na koma d'aki a gado na gan shi ya min nuni da na kashe fitila na je, hakan na yi kuwa ina kashe fitila na je gare shi.......
Da misalin qarfe sha biyu da rabi na dare muna manne da juna muna hira ba zato ba tsammani na ji Yah Maheer ya yanko min tambayar da ta d'aure min kai ta sa ni tunani da jin tsoron me yake nufi da ni??????
Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba da comments ɗin ku, amma a yi hakuri banda zafafawa domin wannan labari na gaskiya ne kamar yanda na sanar da ku tun farko...Thank you my fiful*
💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 19 :
Kamar daga sama na ji Yah Maheer na min tambayar da ta d'aure min kai,
"Baby na anya kuwa ba family planning ki ke yi ba shi yasa har yanzu ba ki samu ciki ba?"
Ji na yi kamar ya buga min guduma akai na, cikin tsananin mamaki da tunanin ina ma shi ya san wani abu wai shi family planning nake kallon shi, ni kaina dika dika nawa nake da zan san wani planning? A ina zan je a min shi? Sannan ta ina ma zan fara, gaba ɗaya sai na zama speechless.
Ganin irin halin da na shiga ne ya sanya jikin shi yin bala'in sanyi, nan take nadamar yi min wannan tambayar ta bayyana a fuskar shi, juyar da fuska ta ya yi dan na kalle shi da kyau, domin tinda ya mun tambayar na kalle shi ina so na tabbatar shin da ni yake ma wannan tambaya ko mistake ya yi ya kira suna na? Ina tabbatar da cewa da ni yake sai na kau da kai na gefe wasu hawaye masu zafi na dukan kunci na, wato shima rashin haihuwa ta ya fara damun shi har da zai zarge ni da yin planning kenan, ba laifi.
"Baby na Please say something, tambaya kawai na yi, saboda d'azu muna hira da abokai na ake maganar planning ya na sa wasu matan su jinkirta haihuwa, ni dama ba wani abu zan ce maki ba, alfarma zan roqa dan Allah in ki na yi ki dena ki bari ko haihuwa ɗaya ne a qalla mu yi se ki yi ɗin, dan Allah"
Yanayin yanda ya yi maganar se ya sanya ni jin matsanancin tausayin shi da ni kaina, ni dai na san bana planning, ban san a ina ake yi ba, ban san ya za ai na je na ce a min planning ba, ta ina zan fara ban sani ba,Allah shine shaida ta akan hakan,ta ɗayan bangaren kuma sai na ji tausayin shi wataqila zai ga duk abokan shi da qanne matan su na ta haihuwa shi kuma shiru har wannan lokacin,ban ce masa komai ba na miqe na wuce zuwa wanka, shima be tsayar da ni ba, dan ya kasa karantar halin ma da nake ciki balle ya san me zai min.
Ina wanka ina kuka, se da na yi na qoshi sannan na kammala na fito a lokacin qarfe ɗaya na dare ta gota, ko da na shiga dakin sai ya taso ze min magana, doguwar riga ta na ja na zura na sanya hijabi na,na tada sallah ban kula shi ba.
Ina sallah ina hawaye, bayan na idar ne na daga hannaye na ina addu'a, nan da nan jikin shi ya qara yin sanyi, sai ya durqusa ya riqe hannaye na ya sanya su a bakin shi ya na sumbata hawaye na zuba a idon shi, sosai.
(Masu cewa qarya ne namiji baya kuka saboda soyayya, ko dan ya ga matar shi na kuka, ko dan bata da lafiya da sauran su to su ne maqaryata, dan mijin ki baya kuka akan ki na cikin wani hali mara kyau does not mean cewa mijin wata ba zai yi mata kuka dan tana cikin wani mawuyacin hali ba, maza kala kala ne, kamar yanda kowa da halittar shi haka kowa da kalar zuciyar shi, da kuma yanda qarfin soyayyar shi take da qarfin zuciyar shi akan soyayyar nan tashi) kallo na ya yi a raunane sannan ya ce,
"Baby na dan Allah ki dena kuka, ki tsaya ki fahimce ni.....ni ban san ma me zan ce maki ba....amma dan Allah ki manta da maganar da na miki, Allah ya bamu zuri'a mai albarka a lokacin da ya fi alkhairi"
"Ameen"
Shine abinda na ce kawai na ci gaba da addu'a ta sannan na tashi na haye gado na juya masa baya, na matse can qarshen gado,wanka ya fita ya yi ya dawo, ya tarar da ni ina shan majina da alama kuka nake har a wannan lokacin,wanda ni kaina na rasa na menene, kawai na san dai zuciyata ta quntata da tunanin da ya yi na cewa zan iya yin planning ko haihuwar fari ban ba.
Sallah ya yi shima ya hau addu'a kafin ya idar ma na yi bacci,a qa'idar shi in Ina bacci baya tashi na, hasali ma dan kar a tashe ni ya na iya zama a parlour ko wane ke nema na zai ce bacci nake ba zai tashe ni ba, amma se gashi ya kasa hakuri se da ya tada ni cikin marairacewa ya ce,
"My baby dan Allah ki manta da maganar da na yi d'azu, ni kaina se da na faɗa na gane rashin kyautawar da na yi, i am so sorry,ki dena kuka, ina son ki a duk yanda ki ke, ko da haihuwa ko ba haihuwa, Allah shi ne me bayarwa kuma ina nan ina addu'a Allah ya bamu me albarka, a gaskiya na yi wauta da na yarda da maganar su har na yi maki magana akai, wannan na daga dalilin da ya sa bana son zaman majalisa se a sa maka tunanin da baka da niyya....baby na kin yafe min?"
Murmushi na yi, dan ina so ya gane na hakura,
"Ni fa ba wai kuka nake akan rashin haihuwa ba, kuka nake akan zaka iya yarda ni na ma san wajen planning sannan har zaka iya tunkara ta da maganar? To alhamdulillahi da ka gane da kan ka ban taɓa yi ba, ba zan taɓa ba, se idan Allah ya qaddara,ban taɓa kuka akan ban samu ciki ba ko ban haihu ba ba kuma na fata har abada na yi, saboda na sani Allah ne ke bayarwa, wanda ya samu ba dabarar shi bane, wanda be samu ba ba rashin wayon shi bane, ba kuma qiyayya ce daga wajen Allah ba, hasali ma Allah yana jin kunyar wanda be ba wa haihuwa ba, a kullum Baba ya na yi min nasiha akan hakan dan haka ni ban taɓa damuwa ba, dan Ubangiji ya min baiwa kala kala da ni'ima kala kala wanda ban roqe shi ba ma dan haka dan ban samu haihuwa ba ba zan masa butulci ba na hau complain,dan haka har cikin zuciya ta Allah ne shaida ba abinda yake damu na, dan Allah ka dena ɗaukar maganar su ko dan gaba Allah ya sa mu dace"
"Ameeen ya Allah....madalla da samun mace ta gari, mai tawakkali, Allah ya qara maki lafiya da imani Baby na, ina alfahari da ke,"
Sumbatar kunci na ya yi se na sa masa kukan shagwaba, na ce,
"Ni dai dan Allah ka bar ni na yi bacci na hutaaa na gajiiii"
"To sarauniyar kyawawan gidan su Allah ya tashe mu lafiya"
"Ameeen, ka jira su Addah Ummu su ji ka za ka yi bayani"
"To ai su ma sun sani ba sai an tsaya bayani ba"
Dariya kawai na yi, hamma ce me qarfi ta kwace min, cikin qanqanin lokaci ina manne da jikin shi da nake jin zan yi matuqar kewa sakamakon sabo da na yi da shi bacci me daɗi ya ɗauke ni.
********************
Shirye shiryen tafiya Kebbi state sun kammala, da sassafe ya shirya na raka shi bakin qofa motar abokan shi da suka samu aiki a garin na jiran shi,ina kuka ina komai ya tafi ya barni da tsananin kewar shi, shi kan shi idanun shi sun yi jawur ba yanda zai yi haka muka rabu ba dan mun so ba.
Bayan tafiyar su duk suka tsaya Sallah se ya kira ni, in ya ji ina kuka se ya yi ta lallashi na, daga qarshe dai na ji ya ce,
"To Umar ina ga fa kawai ku maida ni gida na hakura da aikin nan Madam ta qi dena kuka, ni kuma duk abinda ze sa ta kuka bana son shi"
Ina jin haka se na had'iye kuka na na yi dif hawaye kawai ke zuba min, a hankali na ce,
"Ni dai kar ka dawo, Allah ya kai ku lafiya ya kiyaye hanya ya sanya albarka a tafiyar ku, kuma kar ka qara ce min Madam bana so"
Murmushin shi na Jiyo me sauti tare da amsawar addu'ar da na masa, sannan ya ce,
"Yauwaa ko ke fa baby na, kin ga yanzu zan ji daɗin tafiya ina me farin cikin baki da damuwa se ta kewa ta, Ni kaina na san se na yi kewar ki ba iyaka, dan haka mu yi ta yi wa juna addu'a tare da fatan Allah ya haɗa mu da alkhairi,a min afuwa mada..... auuuu ashe fa kin ce baki son sunan sorry Ma'am"
Dariya na yi me sauti har haqora na na bayyana sannan na ce,
"Haka ne Ameeen ya Allah, se an jima zan kira ka Allah ya kiyaye"
"Ameeen mar'atussaliha Allah ya miki albarka ki gaida yaran"
"Za su ji inshaa Allahu"
Kashe wayar mu ka yi kowa na jin kewar ɗan uwan shi sosai a ran shi.
Bamu sake waya da Yah Maheer ba se tsakiyar dare wajen biyu da rabi, ido na biyu kyamas wanda dama na san za ai haka, barka da arzikin sauka lafiya na musu sannan na yi masa addu'a sosai, tare da jaddada masa yanda na yi kewar shi a raina, daga baya muka yi sallama ya ce na qoqarta na yi bacci.
Mu na gamawa kuwa na yi addu'ar bacci na shafa a jiki na sannan na kishingid'a dan in yi bacci, ko minti goma ba ai ba da kwantawa ta sai na farka a tsorace, dan kuwa ji na yi kamar an shafi qafata, it was so real na ji an shafan qafa da hannu, ko da menebe oho, zare ido na hau yi a duhu, na kalli qasa inda su Hauwa'u suka yi shinfid'a suke bacci kowaccen su ta ma manta a inda take tsabar bacci, to waye ya taɓa qafata?
Nan da nan fa tsoron da na jima ban ji ba ya mamaye ni, nan da nan kuwa na buɗe qur'ani na na hau karantawa cikin d'aga murya daidai yanda ba zan dami mutane ba,ina tsaka da karantawa a zaune a yanda na riqe qur'anin bacci ya sace ni,ban farka ba sai bayan sallar asuba, a gaggauce na yi alwala na yi sallah, sannan na hau abin karyawa, kafin na gama Yah Maheer ya kira tsokanar shi na dinga yi ina kiran shi da gwauro dariya ya yi sannan ya ce,
"Lallai yarinya bata san wanene gwauro ba ashe...to ya kuke ? Da fatan ba wata matsala kin samu bacci sosai?"
Murmushin yaqe na yi kawai dan kuwa ba na so na sanar da shi abinda ya faru a daren jiyan, Ni kaina na yi qoqarin maida abinda ya faru a jiyan a ba komai bane ni ce nake jin kamar wani abu ne amma ba komai bane.
Ta haka ne na samu natsuwa har zuwa yamma, ban rintsa ba ido na ya yi jawur saboda baccin da nake ji, haka rayuwa ta ci gaba da juya min a bayan tafiyar Yah Maheer, har a wannan lokacin bana period daidai, se ya jima be zo ba, in ya zo se ya jima be ɗauke ba.
Watarana da yamma Maimunah na gidan su mijin ta, muna zaune ni da Suwaidatu Hauwa'u na islamiyyah sai muka ji sallama,ko da muka duba sai mu ka ga ashe Innar Yah Maheer ce da suka dakko ni sanda Ina Amarya me suna Baba Aunty, Baba Aunty mace ce mai kirki sosai, kuma ta na son Yah Maheer ita ɗin cousin ɗin mahaifiyar shi ce, duk da a wannan lokacin ban san asalin relationship din su ba na dai san kawai Innar shi ce, wanda na ma zaci Uwa daya Uba daya suke da ita da mahaifiyar shi sai kawu Usman wanda yake dan uwan Baba Aunty ɗin, suna matuqar son Yah Maheer sosai.
Murna na yi da zuwan ta wanda har raina na ji dad'in ganin ta sosai, ta na zaune a kujera na zauna a qasa cikin girmamawa na gaishe ta Suwaidatu ma ta gaishe ta, sannan muka zauna a qasa mu na taɓa hira, daga qarshe ta mana sallama ta aje mana ledar hannun ta,ta yi shirin tafiya gidan ta, bayan mun raka ta mun dawo na ga ashe quli quli ne me dad'i,kuka, yaji jar kanwa da garin tuwo,se gyad'a ta soyu nan da na kuwa muka hau murna ina ta tiqar rawa irin ta qananan yaran nan Suwaidatu na ta min dariya sosai.
Tinda baiwar Allahn nan ta zo mana ba wanda ya sake waiwayar mu dan ya ji ya nake tinda miji na baya nan,ko kuma yaran, haka muka ci gaba da zama ba tare da wata damuwa ba, har ya yi sati biyu da tafiya.
Wata ranar Lahadi da yamma lisss mu na zaune ana hira a parlour na kawai muka ji sallama, da gudu Suwaidatu ta tafi dan kuwa ta ɗauki Muryar me magana, qanqame ta ta yi ta na murna sosai, fita na yi baki na ɗauke da murmushi kallon Nafeesatu yayar Suwaidatu na yi wadda ke dauke da 'yar qaramar jaka a hannun ta ina tunanin me yake faruwa ne?................
Mutanen kwarai masu albarka in an karanta a dannan min star hilis sannan a yi sharing saboda wanda basu karanta ba su antayo ayi da su..ina maraba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 30