Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ๐Ÿ’… *MAHREEN* ๐Ÿ’… WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 1 *Assalamualaikum makaranta novels d'ina Kuna Ina? ku marmatso ku ji ga sabo ya zo da zafin shi, kar ku bari a yi babu ku, coz I promise you wannan salon daban ne, Kun kuwa San in na ce daban ne daban d'in ne ko? Ki hanzarta kar se an yi nisa ki ce a baki daga farko. Allah ya bani iKon rubuta alkhairi ya baku iKon d'aukan abin alkhairi a rubutun nan mai albarka. Son so fisabillahโค๏ธโœ๏ธ* Kowanne d'an Adam ya na fuskantar jarabawar rayuwa gwargwadon yanda Allah mad'aukakin sarki ya hukunta kuma ya tsara masa,ni MAHREEN na sani Kuma na yi Imani da Allah, na yarda cewa qaddarar rayuwa ta ce ta zo a haka, ba zan iya sauya dik abinda Allah ya hukunta zai same ni ba, sanin haka ne ya sa a kullum nake miqa cikakkiyar godiya ta a gare shi, nake neman taimakon shi akan dikkan wani abu a rayuwa ta komai girman shi, Kuma komai qanqantar shi. Ajiyar zuciya na sauke mai qarfi a daidai lokacin da na gama wanki na a maqotan mu, na tattara robobi na da na d'auraye na had'e su waje guda, tsugunnawa na yi a bakin rijiyar na fara wanke qafata da fuska ta da ruwan da na zuba a buta. Ba zan tab'a manta wannan babbar ranar ba a rayuwa ta, mai d'imbin tarihi, rana ce mai matuqar mahimmancin a gare mu da ni da Yah Maheer d'ina. Yammace sakaliya, garin na kano ya yi dad'i saboda yanayin da muke ciki na sanyi,na jima da dawowa gida inda a can gidan maqotan mu na baro wanki na da basu bushe ba, na taho gida domin na yi wanka na ci abinci na yi kwalliya kamar yanda na saba, fitowa ta daga wanka ba jimawa aka d'auke wutar lantarki, cikin Jin haushin d'auke wutar da aka yi na miqa hannu na janyo 'yar qaramar fitila mai d'auke da batira guda uku, kunna ta na Yi, nan da nan kuwa haske ya gauraye d'akin mahaifiya ta Wanda yake d'auke da makeken gado da duk Wani abu da ake da buqata na yau da kullum kadaran kadahan dai, domin mu ba masu kud'i bane, sannan ba talakawa bane, mu na da rufin asiri daidai misali alhamdulillah. Kallon fuskata na yi a madubi Wani qayataccen Murmushi ya k'wace mini hushirya ta ta bayyana, idanu na masu zara zaran gashin Ido suka qara haske a cikin hasken qaramar fitilar. Hoda na d'auka na shafa sannan na Saka janbaki na goga Kwalli tare da taje gira ta da ke Cike da gashi Mai kyau, ban jima da kammala Kwalliya ta ba na duba wajen window na ga yanda gari ke qara yin duhu, cikin sauri na miqe na d'auki kaya na na Sanya Wanda ya kasance leshi ne ja da adon farar fulawa da fararen dutsina, sai na ja farin mayafi na na yafa, qofar parlourn Mama na zo na ja na tsaya Ina tinanin wa zai raka ni deb'o kaya na a duk fad'in gidan nan? Hayaniya na dinga jiyowa a qofar gida alama ce ta cewa mutanen gidan mu da d'aliban da ke zaune a unguwar mu Wanda ke karatu a makarantar BUK sun hallara Dan yin sallar magariba, yayata na hango Mai Suna Ummul khair wadda muke Kira da Addah Ummu ,wajen ta na nufa cikin karya murya da langwabar da Kai irin na mai neman alfarma na ce, "Addah Ummu Dan Allah ki raka ni na deb'o kayana gidan maman Ihsan, kin San ba zan iya zuwa ni kad'ai ba tsoro nake ji" Yanda na shagwab'e fuska da murya ne ya Sanya ta kallo na Cike da hara ta dungure min goshi sannan ta ce, "Mu je, 'yar rainin hankali, matsoraciyar kawai, kin San ba Zaki Iya zuwa ba ki ka bar wankin naki ya Kai war haka, ko me ma ya Kai ki yin wanki a can oho ga gidan ku se kin je Wani wajen Allah ya shirya ki" Ni dai ban ce mata komai ba duk surutu na, saboda kar ta qi raka ni, se kawai na yi gaba na Jira ta ta shirya ta zo mu wuce, Ina tsaye na ji Yara na murna da Kiran "Yeeehh ga Yah Maheer...ga Yah Maheer" Murmushi na yi, na kauda kai na, Ina hasaso kamalar shi, cikin zuciya ta babu komai banda girmama kirkin shi da mutuncin shi, mutum ne shi mai halaye kyawawa, irin kyawun da sai mutum ya jima ya na bincike kafin ya samu me irin halayyar shi, a Ido idan ka gan shi sai ka ji girman shi da kwarjinin shi sun baibaye ka, balle ya bud'e baki ya yi magana, a Koda yaushe maganar shi Cike take da Kamala,ilimi, wayewa, da Kuma sanin ya Kamata. Tinani na ya katse ne a daidai lokacin da na ji Addah Ummu ta ja hannu na muka kama hanyar fita daga gidan namu, a soron gidan muka tsaya muka ga yanda matasa ke biye da bayan Baban mu su na sallah,bamu fita ba sai da suka yi ruku'u sannan muka lallab'a muka Yi sauri muka fita A hanya Addah Ummu na ta bani labarin Yah Sulaiman mijin da zata aura kenan, Wanda yake d'an uwan mahaifin mu ne, an Sanya ranar auren su ita da Addah Firdous, sai sauraron ta nake Ina Jin yanda soyayya take da dad'i da Sanya nishad'i, se da muka Isa gidan sannan Addah Ummu ta yi shiru da hirar da take min wadda ke jefa ni cikin wata duniya ta mafarki kala kala. Ina zuwa na tadda an ninke min kayana an daure su a d'ankwali na, gaishe da matar gidan kawai na yi na dauka muka fita dan komawa gidan mu, mu na Isa qofar gida muka tarar da har an idar da sallah Yah Maheer na zaune a gaban Baba su na tattaunawa, Ido ya d'aga ya kalle ni cikin sanyin shi, sannan ya mayar kan Addah Ummu,a tare muka gaida shi, ya amsa muka shige gida,Ina shiga qani na Wanda shi ne autan maza yazo da gudu ya kama hannu na, sannan ya ce, "Addah MAHREEN kin San me? Yanzun nan na ji Baba da Yah Maheer Suna magana akan ki, Yah Maheer ya ce ya na son ki, baba Kuma ya ce ya amince ya bashi ke amma da sharad'in ya nemi soyayyar ki,domin baya yi wa yaran shi auren dole" Wani abu na ji Wanda ba zan iya fassara ko menene shi ba,, daga saman Kai na har qafata, jiki na ne ya yi sanyi kamar wata kifin da bai da qashi haka na ke ji na. Da sauri na shige d'akin Mama Addah Ummu kuwa ta wuce d'akin mu na 'yan mata ta tada sallah, zama na yi a bakin gado da kaya na Ina jinjina girman wannan magana da na ji, na rasa me ma zan yi,shin farin ciki zan yi ko baqin ciki da Jin wannan lamarin da ya tinkaro ni ba zato ba tsammani? Ya zan yi idan wannan maganar ta tabbata gaskiya ce? Shine Baba ya bada ni da gaske ba tare da ya ji ra'ayi na ba? Anya yaron nan ya ji me su Baba suka tattauna kuwa? Kaii inaaaa wannan maganar ba gaskiya bane. Ina tsaka da tinani na ji sallamar Yah Maheer, Mama ce ta shigo d'akin ganin parlourn da duhu dindim ya sanya ta kwala min Kira dan kuwa ta na kitchen ta ga dawowar mu da shiga ta d'akin, bani da wajen zama da ya wuce d'akin ta, dik da cewa mu na da d'akin mu na 'yan mata. "MAHREEN ko baki ji bane? Ki kawo mana fitila mana, waje duhu qirin haka" Cikin wata iriyar matsananciyar kunya na d'auki fitilar na nufi hanyar parlour sai dai na kasa qarasawa, Ina nan tsaye a tsakanin parlour da d'aki da Kuma toilet na sake Jin muryar mama na min maganar na qaraso na kawo fitila mana, qafata na ja na qara takun da be fi uku ba, na miqa hannu na na Dora fitilar a saman allon kujera mai cin mutun d'aya ba tare da na fita gaba d'aya na ba, kasa komawa na yi ba tare da na gaishe shi ba. Cikin murya mai matuqar sanyi na ce, "Yah Maheer Ina wuni?" Idanun shi da ke kaina ya lumshe sannan ya saki murmushi ya ce, "Lafiya qalou MAHREEN, da fatan kin wuni lafiya?" "Lafiya qlou" Shine amsar da na bashi na yi saurin fad'awa bayi dan yin alwalar sallar magariba,lokaci ya gama tafiya, Ina shiga na samu waje na sake tsayawa, Ina tinanin maganar wai ni Yah Maheer ke so. A haka na yi alwala na fita na tada sallah, kafin na idar sun gama gaisawa da Mama da d'an tab'a hira kamar yanda suka Saba, ya fita ya koma can bangaren mazan gidan mu. Ko da na idar da sallah na jima Ina addu'a, da tinanin shin wannan maganar da gaske ne ko wasa. Kafff mutanen gidan mu sun tattara sun yi qofar gida, kasancewar unguwar mu sabuwar unguwa ce ba mutane sosai, muka fita mu zauna a waje idan babu wuta mu sha iska gaba d'ayan mu, watarana da iyayen mu, watarana mu kad'ai Yara, tinda alhamdulillah gidan mu muna da d'an yawa ba laifi. Ji na yi zafi ya dame ni Kuma a gaskiya ba zan iya ci gaba da zaman d'aki ba akan maganar da ban gama tabbatar da gaskiya ne ko qarya bane na takura kaina ba, tinda har a wannan loacin Baba be Kira ni ba, ba Wani babban da ya min maganar, dan haka sai kawai na miqe na d'akko rigata ta bacci mai laushi wadda aka yi wa hannun ta ado da farin yadi, iyakar ta qauri na, haka nake Sanya ta na zauna a gidan mu, amma idan da baqi Ina Sanya Wani wando na ja a ciki, Dan haka se na Sanya wannan wando nawa na yafa farin mayafi na, na fita zuwa parlour, zama na Yi a kujera na kasa fita waje, dik da cewa hakan ba baqon abu bane a waje na a fita Shan iska, watarana musamman in da redio nakan yi zamana a cikin gida na kamo freedom redio in ta sauraro , amma yau rashin fitar tawa ya min daban da sauran,sannan na ji cewar Anya ba dan Yah Maheer na qi fita ba? Ban gama wannan tinani ba na ji autar mu da muke Kira da Baby ta shigo da sauri ta zauna kusa da ni, ta ce, "Addah MAHREEN wai ki zo in ji Yah Maheer ya na jiran ki a waje" Ji na yi gaba na ya yi wata iriyar fad'uwar da ban San dalilin ta ba, "To Ina zuwa" Shi ne amsar da na bata, ta fita da gudu ta na tsalle irin na qananan Yara, jiki ba kwari na miqe dan zuwa Kiran da ake mini, domin Yah Maheer ba irin mutanen da za su Kira ka ka jinkirta zuwa Kiran su bane, saboda tsananin kamalar shi da kamewar shi. Zaune yake a saman kujera gefen shi Addah Firdous ce Suna hira, ya na cin tuwo a hankali, ya na bata amsa cikin sanyin shi, a gefen su na zauna nima, cikin tsananin daidaita nutsuwa ta da nuna ban San komai ba na sake gaishe shi, zame hannun shi ya yi a cikin abincin ya kalle ni, sannan ya amsa Cike da kulawa, sannan suka ci gaba da hira da Addah Firdous, a hankali na ga kowa na zamewa ana shigewa cikin gida,har ita Addah Firdous d'in, guri ya rage daga ni sai Yah Maheer, shiru ne ya ratsa wajen kafin daga bisani na ji muryar shi ya na tambaya ta da..... "Ajin ki nawa yanzu ?" "A Islamiyya ajina biyu sunan ajin mu Ibn Katheer almakee, a boko Kuma Ina JSS 3 yanzu" "Masha Allah, izun ki nawa?" "Mun Kai izu arba'in yanzu, Ina da haddar izu goma," "Masha Allah, amma ni na zaci ma fa kin Yi sauka, anyways hakan ma daidai ne, kin ga yanzu ana first term ne na San kafin ku kammala JSS 3 din ma za ku sauke" "Eh inshaa Allahu haka muke fata" Ido na ne ya sauka a saman rigar shi daidai kafad'ar shi, Wani qwaro na gani ya na yawo Wanda ban San menene shi ba, ba tare da tinanin komai ba, na sa hannu na sauke qwaron, kallo na ya yi sannan ya kalli inda qwaron ya bi da gudu, sai da na aikata hakan na ga rashin dacewar abinda na yi da na sani fad'a masa na yi sai ya d'auke da kan shi amma na d'auke masa, cikin sauri na ce, "Ka yi hakuri ban San menene ba kawai...." "Kar ki damu, na gode, barakallahu fiki" "Ameen wa fika barakallah" "Inyeee Ashe dai har larabci kin Iya" Dariya na yi, na sunkuyar da Kai na cikin Jin kunya, a hankali cikin dabara irin ta manyan da suke da wayo da sanin duniya Yah Maheer ya dinga min tambayoyi har da samarin da nake da su, da yanda alaqata take da su, na kuwa saki baki na dinga zuba masa surutu, ko ba komai Allah ya hore min baiwar yawan magana. Hira muke sosai da Yah Maheer na ji ya katse ni da tambayar da ta Sanya dik wata na'ura da ke qara min qaimi wajen yawan surutu ta mace. "MAHREEN yanzu idan na ce Ina son ki, Ina so na aure ki, duk tarin masoyan nan naki, za ki Iya aure na?" Shiru na yi kamar ban tab'a magana ba a duniya, saboda ni na sani Yah Maheer na da babban matsayi a waje na, saboda sabon da muka yi da juna, amma ban tab'a Jin Ina Yi masa so irin na soyayya ba, Yah Maheer namiji ne Mai matsakaicin kyau, fari ne shi tass mai matsakaicin tsaho domin kuwa tsahon mu d'aya da shi, ya na da shekarun da suka ninka nawa, sannan shi mutum ne da yake da hakuri, sanyin hali, da kyawawan d'abi'u, ba macen da ta San me take namiji kamar shi ya ce ya na son ta da aure ita Kuma ta ce bata son shi, tinani ya yi wa kaina yawa na rasa amsar da zan bashi, a hankali na ji maganar shi ya ce, "Kar ki damu, zan baki lokaci zan tafi bauchi gobe idan kin Yi shawara zan sake dawowa dan Jin amsar ki" "To Yah Maheer, Allah ya zab'a mana abinda ya fi zama alkhairi" "Ameen" Da haka na tattara kwanukan da ya ci abinci na d'auki ruwa a buta na zuba masa ya wanke hannun sa da bakin sa, hannayen shi farare masu kyawawan yatsu na kalla, cikin raina Ina ayyana yanda suka fi nawa kyau a matsayi na na mace, Murmushi kawai na yi, na d'ebi kwanukan na Masa sai da safe, ya miqe ya raka ni har cikin gidan ya tsaya daga hanyar da zata sada ni da tsakar gidan mu, tin asali ya San ni yarinya ce Mai tsoron tsiya, dalilin da ya Sanya shi raka ni kenan tin kafin na roqi hakan a wajen shi. Ina shiga na ji ana ta hayaniya a parlourn Ummah, 'yan uwana ne maza da mata Suna ta tattaunawa akan maganar neman aure na da Yah Maheer ya yi, qarar ajiye kwanukan da na yi a wajen wanke wanke ne ya Sanya su yin shiru gaba d'ayan su, can na ji muryar qanwata na Sanar da su zuwa na, shiru parlourn ya sake d'auka. Nima parlourn na nufa na samu waje gefen Addah Firdous na zauna, nan fa suka hau tambaya ta, ya aka yi? Me ya faru? Ban bata lokaci ba kuwa wajen zayyana masu abinda ya faru a tsakanin mu, gaba d'ayan su nuna amincewar su suka yi da maganar da ya zo min da ita, suka bani shawarar na Sanar da shi na amince, Cike da kwarin guiwa kuwa na Sanya a raina first thing da zan fara Yi kenan da safe in Allah ya kaimu. Hira aka ci gaba da yi har Nepa suka kawo wuta kowa ya nemi makwancin shi, ko da muka je bacci ma Addah Ummu ta sake jaddada min mahimmancin bashi amsa da nuna masa amincewa ta, inda ta ke nuna min cewar shi din mutumin kirki ne, a kaff masu zuwa neman aure na wajen baba da yayun mu ba ya shi a kyawun halayen, sannan gashi ya na so na, Kuma ko ba komai zai zamana mu uku muna aure a gari d'aya za mu ji dad'in zaman mu a garin. Hakan da ta fad'a ya qara min kwarin guiwar son amincewa Yah Maheer, a hankali na fara Jin saukar numfashin ta, alamun ta yi bacci, ajiyar zuciya na sauke Ina lumshe ido tare da Kara hannayen na a baki na domin yin addu'ar bacci, Ina gamawa na shafa a jiki na na maida kwanciya ta zuwa bangaren dama. Idan na amincewa Yah Maheer Mansoor fa???????? Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love ๐Ÿ’• all. ๐Ÿ’… *MAHREEN* ๐Ÿ’… WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 2 Ajiyar zuciya na sauke mai qarfi na sake gyara kwanciya ta, Ina tinanin matsayin Mansoor a waje na da zuciya ta. Mansoor na d'aya daga cikin samarin da ke so na a makarantar mu, dik da cewa tinda na shiga makarantar ya ke so na Kuma nima Ina ganin shi ya na burge ni saboda tsarin ado da Kwalliyar shi da kamalar shi, sannan da ajin da yake da shi, amma ban tab'a kula shi ba duk irin qoqarin da ya ke Yi na ganin na kula shi d'in,kamar wasa idan ya zo dole sai ya wuce ta gaban ajin mu ya ganni ya ke Jin dad'i, haka nima duk sanda zai wuce d'in na gan shi zuciya ta na samun nutsuwa da nishad'i,Ina da qanne a makarantar Wanda bana so su dinga kula samarin makarantar, to ta yaya ni da ke son kula da qanne na zan b'ige da yin saurayi a makaranta? A wannan lokacin ba Mansoor ne kawai ke so na ba a makarantar mu, hatta da principal din makarantar tamu wanda yake tsoho ne wai Shima so na yake,a cikin malamai da wasu d'alibai su ma ba a bar su a baya ba wajen qoqarin gwada sa'ar su, Wanda na kula hakan na faruwa ne a duk sanda maza suka kula da macen da bata kula kowa sai su yi ta qoqarin tura kan su dan ganin sun zama na d'aya a wajen ta,musamman in Allah ya mata kyan sura. A hankali na kasa jure irin so da qaunar da Mansoor ke nuna min, na fara qoqarin karya dokoki na da na gidan mu, domin mahaifin mu a Koda yaushe ya na mana nasiha da cewar, 'A duk sanda Wani ya gan ku ya ce ya na son ku, kar ku tsaya kula shi a saman hanya, ku ce Masa ya zo gidan ku ya same ni, saboda ba a ce wa namiji ba a son shi direct Wani Mugu ne,sai ya Iya Yi Maka wata muguntar, Wani Kuma da gaske yake auren ka yake so ya yi, Kun ga idan aka samu na gari Wanda Allah ya nufa da shi za a yi sai mu muyi bincike akan shi,' Wannan dalili ne ya sa duk yawan samarin da nake yi gida nake aika su wajen mahaifi na ko wajen yayana Wanda shi nake bi, he is that type of over protective brothers d'in nan, he loves me so much kamar yanda nima Ina son shi sosai,ya na kula da mu matuqa, baya qaunar ganin Wani saurayi na bin mu a duk lokacin da Baba baya gari shi ke tsayawa ya sa Ido akammu, Kai ba shi kad'ai ba ma gaba d'aya yayun mu su na da qoqarin kulawa da tarbiyyar mu a Koda yaushe. Amma dik da haka na take wadannan dokoki da tsaro na gidan mu na fara kula Mansoor, bai tab'a zuwa gidan mu ba dik yanda ya so ya zo bana bari, qanne na ne kawai suka San da zaman shi a matsayin saurayi na na makaranta, Mansoor na da tarbiyya ta yanda ya ke taya ni kula da mutunci na da qima ta da darajata ta 'ya mace a cikin makaranta,bai tab'a Yi min maganar banza ba, Ina girmama shi kamar yanda ya ke girmama ni. Ina tsaka da tunanin shi na ji bud'e qofar toilet alamar Wani ya shiga, sake juyi na yi na lumshe ido Ina karanto duk wata addu'a da ta zo baki na saboda in samu bacci ya d'auke ni, Ina da wuyar yin bacci, domin tin Ina qarama ta se kowa ya yi bacci ya barni, har yanzu da nake da shekara sha biyar a duniya bata sauya zani ba. Mahaifiyar mu ta koya min cewar a duk sanda na kasa bacci, in Yi ta karanta ayatul kursiyyu, ko In yi ta yin tasbihi ga Allah, nan da nan zan ji bacci ya d'auke ni,dan haka kuwa ba b'ata lokaci na kulle Ido na na hau yin tasbihi ga Allah, ban San sanda bacci ya d'auke ni ba, sai farka wa na yi na ga 'yan uwana ana hada-hadar yin sallar asuba. Cikin hanzari na miqe na shiga toilet na yi uzirin da zan yi sannan na d'aura alwala na fito, na tada sallah, Ina idarwa na bi layin 'yan uwana da ke karatun qur'ani, gari na fara haske kowa ya yi addu'a aka shafa aka hau gyaran gida, masu girki suka nufi kitchen kowa ya kama aikin da zai yi. Ni Ina cikin Wanda suke girki a

Chapter 1 of 30