makoshin nata bushewa
tana jin kamar ta yini bata kurbi ruwa ba. Bata
san ta rufe bakinta ba sai da taji har harshenta
ya bushe. Ta kifta idanuwanta ta sake budewa a
cikin nashi a karo na biyu, zuciyarta tayi yawo a
wajajen da bata san zata iya kaiwa ba a cikin
jikinta.
Kirjinta na budewa daga ciki kamar yana son
sanar da ita zuciyarta tayi nisan kiwo na wucin
gadi, lokacin da ta dawo mazauninta sai ta
zauna mata da zanen fuskar shi tarau. Bakine,
gidan su babu wanda za'a kira da mummuna, a
iya danginsu na kusa ma bata taba ganin
mummuna ba. Ko mai kalar fata irin tashi basu
da shi.
"Bahaushe ne"
Lubna sufyan
Hausabook.com 206
Zuciyarta ta furta mata, tana kasa cire
idanuwanta daga cikin nashi
"Wai me kike kallo inata miki magana?"
Saratu ta fadi tana waigawa, maganar da tayi na
karya wani abu da Yelwa bata san ya gifta a
tsakaninta da matashin Saurayin ba
"Muje"
Yelwa ta fadi muryarta na fitowa daga kasan
makoshi, sake waigawa Saratu tayi tana son
ganin abinda ya dauki hankalin Yelwar har
haka. Amman bata gani ba, shisa ta bita tana
riko mata hannu saboda saurin da taga tana ta
zumbudawa, amman sai ta zame hannunta,
bugun da zuciyarta takeyi na amsawa a duka
gabban jikinta, sai take ganin kamar Saratu
zataji yanda zuciyarta take bugawa ta cikin
hannun nata data riko, tafiya take tana saka
kafafuwanta amman bawai tana da nutsuwar
fahimtar hanyar bane balle kuma inda ta dosa.
Da Saratu ta tsayar da ita gaban wasu masu
rake, tsayawa tayi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 207
Yau Saratu ta bari da cinikin raken, ta nutsu
tana fatan bugun zuciyarta ya koma dai-dai.
Lokacin da ta fara jin alamun hakan lokacin ne
kuma wata murya ta ratsa cikin kunnenta
"Sannun ku, rake zaku siya?"
Ya fadi cikin harshen fulatanci shi da kamar
yana tsoron hada jimlolin karsu kasance ba daidai ba
"Kayi yarenka mana, banson me yasa hausawa
ke saka kansu a wahalar dole sai sun koyi
fulatanci ba, banda bata kalmomin wajen
furtawa babu abinda sukeyi"
Maganar Datti ta dawo mata, yakan shigo da
mitar lokutta da dama, harma yace tayi masa
shiru idan taso fahimtar dashi cewa koyon
yaren da ba naka ba akwai aiki a cikin shi.
Juyawa tayi a hankali, zuciyarta na tsayawa na
dakika kafin ta cigaba da dokawa kamar tana
son fitowa waje. Idanuwan shi take kallo, saida
yake dab da ita taga kankantar su, da tashi
shima don da kadan ya fita tsayi, idanuwan shi
sunyi kankantar da za'ace suna da zurfin nan da
yake fisgarta
Lubna sufyan
Hausabook.com 208
"Sannun ki"
Ya sake furtawa
"Yawwa sannu... Wannan zaiyi zaki kuwa?"
Saratu ta amsa shi, dudduba raken data nuna
yayi, kafin ya mika hannu ya zaro wata sanda
yana cema mai raken
"Yanka musu wannan"
Yelwa tayi tsaye, ta kasa daina bin duk wani
motsin shi da kallo, ta kasa aiwatar da komai
banda wannan, saboda bugun da zuciyarta yake
ya gama cinye duk wani karfinta, jikinta yayi
wani irin sanyi
"Yar uwarki bata magana ne?"
Ya tambaya yana murmushi, gefen kuncin shi na
dama yana lotsawa, idanuwan shi na kara
shigewa ciki
"Tanayi... Yelwa ana magana"
Saratu ta karasa tana zungurinta. Numfashi taja
ta baki a hankali tana fitar dashi ta hancinta
"Yelwa..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 209
Ya kira kamar ya saba kira, kamar bashi bane
karon farko daya lankwasa harshen shi da
sunanta
"Sunana Kabiru"
Ya fada mata yana sake saka idanuwan shi cikin
nata, yanayin nan na sake fusgarta, yanayin nan
da yasata jin kamar akwai zurfi a cikin
idanuwan shi da zata iya ninkaya harma ta
nutse a cikin su
Nan ne mafari
Nan zaren kaddarar zai fara jan su
Ruwan da Julde yayi nufin hadiyewa ne yaji ya
zarce yana bin wata kofar da ba hanyar shi ba,
ya kuma toshe masa wucewar iska, abinda ya
saka shi fara tari babu kakkautawa a lokaci
daya yana kokarin ganin numfashin shi ya saitu,
ruwan ya kara sha yana jan numfashi, tarin ya
fara tsagaitawa amman kamar an zuba masa
borkono cikin makoshin shi, bai daina juyo
muryar Datti ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 210
"Allah ya kiyayeni wallahi, da in haifo da irin
Ado gwara na mutu banga kwaina a duniya ba...
Me ake da lalatacce? Sai an magana ace kaddara,
to ita kaddara bata san inda ya kamata ta fada
bane? Kawai mutane sun kasa tarbiyar yara duk
sun lalace an wani boye bayan kaddara"
Yana juyo
"Allah ya kyauta"
Da Dije ta furta kamar ko da yaushe, yau ko
kokarin fahimtar da shi batayi ba, da alamu
itama akwai abinda yake tata zuciyar tun safe,
ya kula komai da sanyi-sanyi takeyin shi
"Daada bakya jin dadi ne?"
Ya tambaya, dan murmushin da ya karanci na
karfin haline ta dora a fuskarta
"Me ka gani? Lafiyata kalau"
Bai matsa ba, yana dai alakanta abinda yake
damunta din da Bukar. Saboda shi yazo yace
mata yaga Hamman Bukar din jiya. Ya ga kuma
dawowarta da yamma. Dan yana sauri zai fice da
ya tsaya ya tambayeta inda taje, sai yayi mata
Lubna sufyan
Hausabook.com 211
sannu da zuwa kawai yana fita. Ita damuwa tayi
da shirun Bukar, shi ran shine a bace shisa bai
cika so ko zancen Bukar ana masa ba. Bayan
wasu yan watanni yace, amman tashin farko sai
da ya shekara harya kara wata daya akai kafin
ya waiwaye su. Dawowa ta biyu a lissafe Julde
yake, watan Bukar din goma sha biyar
"Ka samu 'yan uwan da suka maye maka gurbin
mu ne halan?"
Tambayar farko daya fara yiwa Bukar kenan, sai
yayi dariya, dariyar nan tashi da ko baka so sai
zuciyarka tayi sanyi, musamman da yayi ta
idanuwan shi cike da ban hakuri
"Ko zan sake wasu 'yan uwan ya zanyi da jinin
dake yawo a jiki na? Kuna raina Hamma, wallahi
kuna raina ko da banzo ba"
Kwanaki bakwai Bukar yayi, sai yaga kamar awa
bakwai ne
"Saura ka shekara biyu wannan karin"
Ya fadi cike da kashedi, dariyar dai Bukar ya
sakeyi, daya tashi saiya tsallake kashedin da
Julden yayi masa harya kara. Saiya barsu da
Lubna sufyan
Hausabook.com 212
tarin kewa da tunanin halin da yake ciki. Da
yaga Hamman Bukar din yaso ya tsaya yayi
magana da shi, saiya kasa. Akwai wani haushin
shi da yake kasan zuciyar shi da ya kasa gogewa.
Shine sanadin komai, shi ya kwadaitawa Bukar
barin su. Shi gashi ya dawo yanzun, Bukar na
can. Wannan laifin na Hamman Bukar ba Julde
kadai yake ganin shi ba, harda Dije. Musamman
bayan tayi amfani da barkar da ta tambayi Datti
fita taje gidan Baabuga, ta samu Hamman shi
zaune akan kujera suna hira da matar da take
tunanin itace mahaifiyar shi cikin nishadi
kamar a duniya kaf basu da wata matsala
"Ina Bukar?"
Ta tambaya a madadin amsa gaisuwar da
Hamman yayi mata, numfashi yaja yana fitarwa
cikin yanayin da yake son nuna kamar ta takura
masa, kamar ta saka shi sake maimaita mata
amsar da ya riga ya fada mata ita a baya
"A cikin maiduguri nake karatu, Bukar na
Borno, garuruwan sun bambanta..."
Wannan karin itace ta sauke numfashi, Bukar ya
fada mata, yace mata makarantar su Hamman
Lubna sufyan
Hausabook.com 213
shi a cike take da dalibai sanda sukaje, yana
cikin tarin wanda aka hada aka tura su Borno
din, makarantar wani dan uwan Malamin,
bayani yayi mata yanda zata fahimta. Amman
kewar danta da takeyi ya shafe mata komai
"Me yasa? Me yasa zaka ja shi ku tafi ka dinga
baro shi?"
Ta karasa hawaye cike da idanuwan shi
"Bangane yaja shi suka tafi ba? Bukar din yaro
ne karami?"
Juyawa Hamma yayi yana katse Innar tashi da
"Inna mana..."
Dije ta numfasa da nufin datsa mata magana
itama wata matashiyar budurwa da zai wahala
takai tsarar Yelwa ta fito daga daki tana gaishe
da ita cikin wata siririyar murya da yanayi da
yasa jikinta mutuwa
"Lafiya lau"
Ta amsa tana kallon fuskar budurwar da ba zata
tunata a cikin yaran Baabuga ba. Sannan
yanayin kyawun jikinta, da tufafinta kamar ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 214
daga Marake take ba, a madadin shigar su ta
fulani da ta mamaye fiye da rabin kauyen. Ba
zatace ga asalin sunan kayan jikin yarinyar ba,
kuma ba riga da zani bane ba, shigarta tayi
kama da ta 'yan binni, tsirarin 'yan binnin da
kan shigo Marake lokaci zuwa lokaci, kuma a
cikin harshen hausa tayi mata magana,
gangariyar Hausar da babu alamun sirkin
fulatanci a cikinta
"Zaizo Daada, zai zo da yardar Allah"
Hamma ya fadi, nauyin da zuciyarta yayi bai sa
ta iya amsa shi ba, juyawa kawai tayi, kafarta
daya ta taka soron gidan tajuyo muryar Innar
shi na fadin
"Mero haka zaki wuni baki saka ma cikinki
komai ba? Ko irin abincin namu ne baiyi miki
ba?"
Kalmomin karshe na tabbatar da hasashen
tunaninta. Matashiyar da aka kira da Mero ba
'yar gidan bace ba, bakuwa ce. Ko da bata fada
ba, a iya sunan ta tsaya Dije zata gane bakuwa
ce. Bukar bai taba ambaton Mero a cikin jerin
'yan uwan shi ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 215
Fita Dije tayi tunanin Bukar na danne mata na
Mero
Mero da bata hango kaddara sake hada hanyar
su ba
Balle kuma ta hango yanda zata zama silar
faruwar komai
Tana da yakinin idan wani abu ya samu Bukar
zataji a jikinta, kaunar da take masa na da
wannan girman. Amman bata da sukuni, tun jiya
bata da wani sukuni, zuciyarta batayi mata dadi.
Idan har yazo zata gwada, ko ba zaiji ba zata
gwada ce masa ya zauna a kusa da ita. Ya hakura
da karatun haka, idan da hali ya karasa a
Marake tunda suma makarantun yanzun sun
fara wadatarsu, ko wani gari da yake kusa dasu.
In da idan ta matsa Datti ba zai amfani da nisan
a matsayin uzurin shi na hanata zuwa wajen
Bukar ba.
Ranakun duk da zaka ga yaran sun ci abinci a
gidanta akwai wata magana da suke sonyi da
Datti, yau ma haka ta kasance, Julde a kwanon
Datti ya saka hannun shi bayan isha'i, suna cin
abincin Datti na bashi labarin da bata cika son ji
Lubna sufyan
Hausabook.com 216
a bakin shi ba. Labaran da suke cike da laifukan
wasu, laifukan da suma basu fi karfin Allah ya
jarabce su da irin su ko fiye da haka ba, bata
saka musu baki ba, bata ma daga kai ta kalle su
ba duk da tana zaune akan tabarma daya da su
"Baba ina son zuwa Ikko har cikin raina. Dan
Allah me yasa baka so kabar ni?"
Duk yanda Julde yake matsawa da yin nisa da
Marake bai taba daga hankalin Dije ba, saboda
tasan Datti, ta san Datti ba zai taba barin shi ba.
Kusan yama fita son ganin su a kusa da shi. Don
a lokuttan da Julde yake zuwa Kano harya dawo
baka raba bakin Datti da mita akan yanda
bayason wannan tafiye-tafiyen, mitar da zaka
karanci babu komai a cikinta sai tsantsar kewar
dan nashi da yayi a kusa da shi. Amman yau
amsar da Datti ya bashi ta sa wani abu kadawa a
cikinta da ya wuce ace hanta ce
"Kayi aure tukunna, ka zama cikakken mutun
inda yafi Ikko ma idan kana son zuwa sai kaje..."
Yaga yara a Marake da yawa da suke tafiya kudu
da sunan neman sana'a, yaran hausawa da na
fulani da baiga me yasa zasu bar tushen su da
Lubna sufyan
Hausabook.com 217
sunan neman kudi ba. Nomar suke gujema? Ko
kiwon? Sana'oi gasu nan kala-kala a cikin
yankin nasu da idan ka kama daya da gaske zai
wahala kaqi samun abinda zaka rufawa kanka
da iyalinka asiri. Gasu nan suna dawo da wata
irin shiga sunyi watsi da al'adunsu, sun dauki na
wasu can sun yafa. Randa yaga Baballe ya dawo
da wani wando da wata yaloluwar riga, ya kama
kugu ya tsuke, harya dawo gida yana bambami
shi kadai da tsine irin wannan dabi'a daya
kwaso yana cikakken bafullatani.
Idan ya tsaya iya shiga ma da sauki, wasu
sanadin lalacewar su kenan
"Ai shisa kaga na yiwa Magaji aure kafin in bari
ya tafi kudun nan tunda ya nace, kasan yaran
nan ka haife sune baka haifi halin su ba, nan sai
kaga ya bijere mun akan zuwa kudun nan"
Baban Magaji ya fadi wani lokaci da suke
tattauna yanda burin yawancin matasan shiyar
ya karkata da barin tsatsonsu da sunan neman
kudi. Da farko maganar bata wani zauna ma
Datti ba, saida aka wayi gari dan gidan Malam
Shitu ya tattara kaya yayi gaba, an neme shi an
Lubna sufyan
Hausabook.com 218
rasa, sai daga baya labari ya bazu cewar ya gudu
kudu ne don neman kudin da mahaifin ya nuna
baya so. Abin ya tsorata shi duk da bai fada ba,
amman kasa runtsawa yayi, inda duk zai rufe
idanuwan shi saiya hango Julde a matsayin dan
gidan Malam Shitu. Sai kuma ya hango irin
matakin da zai dauka.
Randa duk Julde zai zabi duniya a saman ra'ayin
shi zai tsine masa ne yabar sallama shi yabar shi
da duniyar. Hukuncin daya hango kwara daya
da zai iya kenan, amman kafin hakan ya faru
yana da hanyoyin da zaibi duk lokacin da Julden
ya sake bijiro masa da zancen zuwa Ikko. Sai dai
dariyar da Julde ya kwashe da ita da irin amsar
daya bashi ta saka shi murmusawa
"To aini ban shirya ba Baba, kabari in fita
neman kudin in tara sai ayi magana"
Murmushin dai Datti ya sakeyi
"A zancen auren naka ne sai ka fita ka tara kudi?
Baka san dan gidan waye kai ba? Ka manta kaf
Marake babu 'yar wanda zaka nema in dai don
kudine ka kasa samu?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 219
Dariyar dai Julde ya sakeyi, aure, shine zaiyi
aure? Kamar hakan na nufin rayuwa da tilon
mace na wani lokaci koda yana da nufin karo
wata. Ko da zai kara ba zai iya wuce mata hudu
ba, da su kadai zai iya rayuwa. Sauran matan da
zasu wuce su shiga idon shi fa? Yayi yaya? Anya
aure na cikin jerin abinda yake hasasowa kan
shi nan kusa kuwa? Ko zaiyi aure ba yanzun ba
"Anya aure yanzun?"
Maganar da yayi nufin furtawa iya zuciyar shi ta
kubce masa
"Sa'anninka nawa ne har an ajiye musu yara? Ai
ka isa auren"
Datti ya fadi
"In kaga kafarka a Ikko to da aurenka"
Numfashi Julde yaja, har ran shi da zuwa Ikko
yake kwana da shi yake tashi. Da tunanin tarin
matan da yaji labarin su, kalar rayuwar da yake
son jin yanda take. Kallon shi Datti yakeyi yana
ganin yanda yake juyayin maganar auren a ran
shi, kamar baya so. Da farko da yayi masa
zancen hanya ce da zai gusar masa da tunanin
Lubna sufyan
Hausabook.com 220
yin nisa da gida. Amman yanzun da wani
tunanin yazo masa sai yaji baya bukar
amincewar Julde, saboda gatane zai masa. Sauki
da nutsuwar sune duka. Idan yace yanzun da
yaga su Yelwa sai wani sashi a zuciyar shi ya
yanke ya fada can wani waje a cikin kirjin shi da
tunanin sunyi girman da za'a iya musu aure
kowanne lokaci.
Musamman Saratu, sai irin mazan da zasu aura
su rike masa yaran da yake ji har a ruhin shi ya
saka shi jin wani irin firgici na daban. Anya a
cikin matasan da yake gani a Marake akwai
wanda ya cancanci ya dauke su ya bawa? Sai
yanzun yaga wanda ya kamata ya dauka ya ba
Saratu, ga Julde a gaban shi
"Ka auri Saratu"
Datti yayi maganar cikin umarnin da kafin ya
amsa Dije ta riga shi da fadin
"Yau kuma yan zolayar taka ne suka motsa"
Muryarta ta fito da tsantsar tsoron da
maganganun shi suka jefata ciki. Saboda taji da
gaske yake, taji babu alamar wasa a muryar shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 221
ko kadan. Maganar tace bata tunanin auren
yaran dukkan su bata taso ba, tunda sun kawo
lokacin da za'a fara hakan. Amman Saratu?
Akwai mata da yawa a kauyen banda ita, akwai
matan da zata so gani da Julde banda Saratu da
bata da nagartar da kowacce uwa zata so danta
ya rayuwa da su. Daga jikin Hammadi ta fito, a
hannun Abu ta taso amman ko daya a cikin tarin
halayen su bata biyo ba.
Tana zaune da Datti don ta samu damar barin
shi ta sake zabarshi, shi din zabinta ne a karo na
farko da na biyu, saboda data nuna bata son shi
a na farkon Baba ba zai taba mata dole ba, in dai
akan maganar aure ne shawara itace abinda zai
shiga tsakaninka da Baba, sauran zabin naka ne.
Idan aka bata takarda da biro duk zata kwana ta
yini tana zayyana duk wani dalili da auren Datti
ya zame mata kuskure, duk wasu halayen shi da
soyayyar da take masa ta rufe mata ido ta sake
dawo masa a karo na biyu.
"Ba zolayar shi nake ba, da gaske nakeyi aure
zan hada su da Saratu"
Datti ya sake tabbatar musu
Lubna sufyan
Hausabook.com 222
"Baba bana son ta"
Julde yayi maganar kan shi tsaye, duk da idan
ance masa meye so din ma bai sani ba. Idan ta
gifta hakika yana so ya tabata, idan tayi masa
magana yana son jinta a jikinshi, yana son
rabarta yaji bambancin da take dashi da sauran
matan daya raba. Amman bai hango su
karkashin inuwa daya a matsayin ma'aurata ba.
Tun kafin ya rabi mace yasan akwai abubuwan
da ya fiso a jikinta. Saratu bata da wannan
abubuwan, idan ya kalleta bayajin komai daya
wuce sha'awar da yanzun yasan ta wani dan
lokaci ce.
"Ungo nan"
Datti yace yana masa dakuwa
"Kai har soyayya ka sani?"
Hannun shi Julde ya tsame daga cikin abincin da
yake ci
"Akan zuwa Ikko ne ai ko? Na hakura..."
Ya karasa yana mikewa yaje ya dauki buta ya
wanke hannun shi yasa kai ya fice daga gidan.
Lubna sufyan
Hausabook.com 223
"Kina jin shi?"
Datti ya fadi yana murmushi, saboda har ran shi
yasan cewa wannan auren babu wanda ya isa ya
hana ayi shi
"Tunda baya so ai sai abar shi"
Dije ta fadi cikin sanyin murya tunda itama baso
takeyi ba, dalilinta kuma ba zai taba zama dalili
a idon Datti da Saratu bata laifi ba
"Ai ba sai yana so ba, bashi da hankalin da yasan
abinda yake so da wanda baya so. Ko ke bansan
ina son ki ba lokacin da Hamma yazo mun da
zancen auren ki"
Kallon shi tayi cikin ido, shigowar Yelwa na
hanata amsawa
"Yelwa..."
Datti ya kira yana sata fadada murmushinta
"Ya kike ganin idan aka hada auren Hamman ki
da Addar ki?"
Karasawa tayi tana zama kan tabarmar cike da
zumudi
Lubna sufyan
Hausabook.com 224
"Dan Allah da gaske kake Baba? Hamma zai auri
Adda?"
Dariya Datti yayi
"Eh mana"
Wani irin tsalle tayi, ihun murnarta na karade
gidan gabaki daya
"Yaushe? Yaushe za'ayi musu auren? Hamma bai
fadamun ba"
Mikewa Dije tayi tsam tana shigewa daki, Datti
baibi takanta ba, saboda yasan bata son Saratu,
bata taba fada da bakinta ba, amman yanayin
mu'amalarta da Saratun ya nuna haka. Ya nuna
yanda bata son yarinyar. Ba kuma ya bukatar
amincewarta, ita dinma a karkashin shi take
balle kuma su Julde.
"Je ki kiramun ita tukunna"
Mikewar kuwa tayi tana fita suka dawo da
Saratu da tun a hanya take tambayarta menene
amman taki bata amsa har suka shigo gidan, ita
kadai ta zauna ta kalli Yelwa da murmushin da
Lubna sufyan
Hausabook.com 225
yake fuskarta don ita ta kasa zama, da alama
zumudi na cinta
"Baba ka fada mata"
Cewar Yelwa tana saka Datti yin dariya sosai
"Idan na zabar miki miji zaki yarda da zabi na?"
Julde ya gilma ta cikin idanuwanta, sawayen shi
na bayyana a cikin zuciyarta har numfashinta na
mata barazana da ta hada kalmar miji, mijinta ta
hango babu hoton shi a wannan hadin. Lumshe
idanuwanta tayi tana aunawa, soyayyar Datti da
ta taso da ita ko ta Julde data tsinta akan hanya.
Tana jin wani abu da yake karyewa a cikin
kirjinta
"Baba kasan ba zanki zabinka ba, wanda duk ka
zabarmun ina so"
Amsarta ta sanyaya zuciyarshi, ta saka wata
kauna da yake mata tasowa ta shimfidu har a
cikin idanuwan da yake dubanta dasu.
"Kaga 'yarka..."
Da Hammadi kan fada baiyi karya ba. Girman da
ta bashi na taba har ruhinshi
Lubna sufyan
Hausabook.com 226
"Zan hadaki aure da Julde..."
Maganar ta dirar mata, a zaune take, amman sai
ta sakejin kamar ta kara zama, zama daban da
wanda tayi tun shigowarta gidan. Zama da sanin
wahalarta ta kare
"Don ina da yakinin ba zai cutar mun dake ba"
Datti ya fadi da tabbacin da bashi da shi
Yayi kalaman da zaiyi dana sanin su a gaba
Tsaye yake ba don babu wajen zama ba, idan ya
juya a cikin gidan da zai iya kira da nashi
yanzun sai yaji shi a cikin wata duniya ta daban.
Duniyar da kamar idanuwa ya rufe ya bude ga
ganta a ciki. Nisan daya hangone ya hade da shi
kamar almara.
"Ba zabinka na tambaya a maganar auren nan
ba Julde, umarni ne. Idan na isa kenan, idan
kuma ban isa ba saika nuna mun iyakata"
Ko da ya daga ido ya kalli Datti amsar daya
bashi daga farko ita ya sake maimaitawa
Lubna sufyan
Hausabook.com 227
"Bana sonta Baba, bana son Saratu"
Maganar kuma ya sake maimaitawa Dije
"Daada ki fada masa bana sonta ko zai jiki...
Bana son yin aure yanzun"
Kallon shi tayi da wani sanyi a cikin idanuwanta
daya nuna mishi rashin ikonta a cikin maganar,
sanyin daya nuna masa inda tana da zabi ba zai
auri Saratu ba
"Kayi hakuri Julde, watakila kaddararka kenan"
Kai yake girgiza mata
"Kaddara ta rasa ta inda zata dirar mun sai
auren da bana so? Yaushe Baba ya fara mana
dole a cikin al'amuran mu?"
Hakurin dai Dije ta sake bashi, hakurin da bai
tausasa zuciyar shi da yake ji a hargitse ba
"Ki fadawa Baba bana sonki, ki taimaka mana ki
fada masa, zama dani ba zai taba miki dadi ba"
Sai dai idanuwan Saratu sunfi nashi
bushewa, zuciyarta tafi tashi kafewa. Akwai
Lubna sufyan
Hausabook.com 228
wani kyalli na son nuna masa iyakarsa da yake
gani cikin kwayar idanuwanta
"Me yasa? Meye banda shi?"
Kai ya girgiza mata
"Kawai saboda bana son ki, shi kadai ne dalili
na"
Akwai ciwo a murmushinta, wani irin ciwo da
yasa shi jin kamar tausayinta na son kutsa
mishi, sai dai wahala yake takaita mata, wahalar
zama dashi da bai hango mata sauki a cikinta ba
"In dai ba Baba yace mun ya fasa hada auren mu
ba zan aureka Julde, kome zaka fada, kome
zakayi zan jure"
Yayi din, abubuwan duk da yasan zai gujema
aurenta, ya fada, maganganun duk da yake
tunanin zasu harzuka zuciyarta, zasu kure
hakurinta. Ko biye masa batayi, yanajin nauyin
Hammadi, yana ganin kimarshi fiye da yanda
yake zato. Don jikin shi sanyi yayi da yaje
gabanshi da nufin yace masa bayason Saratu
"Julde... Lafiya dai ko?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 229
Ya tambaya cikin sanyin nan nashi da yasa yaji
harshen shi ya nade da kalaman da yai nufin
furtawa, baisan Hammadin ya kula kamar baya
son auren ba, shisa ya cewa Datti
"Datti kar a fara abinda ba zai yiwa kowa dadi
ba, shi Julden ya amince har zuciyar shi? Yaran
yanayin yanda suka taso dabanne da lokacin
mu, a abubuwa da yawa ba'a bamu zabi ba, duk
da an mana zabin da idan aka barmu da namu
zai wahala muyi irin shi. Amman a lokacin
rayuwar mu a bude take, su idan ka kula tunda
suka fara girma suna da wata rayuwar tasu da
bamu san komai game da ita ba, cikin wannan
rayuwar harda ra'ayoyi da hasashe akan irin
wannan abubuwan...watakila akwai kalar matar
da ya hango ma kan shi"
Kamar ko yaushe sai Datti yaki fahimtar shi
"Ban haifi yaron da zai dora zabin shi akan nawa
ba wallahi. Ita Saratun in mata magana ai
amincewa tayi, sai shi dana haifa? Idan kaima
iyakata zaka nuna mun akan Saratu dai kayi
kawai, idan kuma bashi bane dan Allah ka bimu
da fatan alkhairi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 230
Saiya kyale Datti tunda in shekara zasuyi ba zai
taba fahimtar inda ya dosa ba. Karshe ma zai
fassara maganar ne ta yanda zai daure
Hammadi ya kasa cewa komai
"Saratu ke kadai zaki iya tsaida maganar auren
nan, idan kika cewa Datti a hakura zai hakura"
Saboda Hammadi ya kula kamar Datti na ma
Saratun soyayyar da baya yiwa nashi yaran
"Saboda me?"
Ta tambaya
"Saboda kinsan Julde baya son auren, bai
amince ba"
Bakinta ta turo gaba
"Baba ya amince, ko kowa bai amince ba ina so"
Ko da Abu ta sake daga masa maganar haka yace
mata
"Addu'a da fatan alkhairi ne namu, daga ita har
Dattin taurin kansu yafi karfina Abu, bana son
fara janyo abinda banda riba a ciki... Saratu zata
Lubna sufyan
Hausabook.com 231
saurari Datti ne kin sani, kome zan fada mata
sautin Datti zai danne nawa..."
Numfashi kawai ta sauke tana fadin
"Allah ya kyauta"
Saboda tasan gaskiya ta fada
"Kayi hakuri Julde, duk wani abu da zakayi
hakuri a cikin shi mai wucewa ne"
Yace ganin Julden yayi shiru. Wata hirar yaja shi
da ita har saida yaga ya sake kafin suyi sallama
"Me yasa ka saba yi mana duk abinda muke so?
Ka saba mana da bin ra'ayoyin mu idan kasan
hakan ba zai dore ba?"
Julde ya jefi Datti da maganar yanajin yanda
duniyar ta hade masa waje daya. Saboda akan
auren Saratu ya fara sanin wata takura tun
tasowar shi
"Saboda ina tunanin randa na kawo nawa
ra'ayin a cikinku babu wanda zaice mun a'a.
Karka kure hakurina akan zancen nan Julde...
Wallahi zan maka baki idan kace zaka bijire
mun"
Lubna sufyan
Hausabook.com 232
Kalamai ne da Julde ba zai taba mantawa ba,
saboda sun sake rura wutar tsanar Saratu a
ranshi. A wajen Datti kuma sun zama makami,
makamin da zai amfani dashi wajen tsorata
Julde yabi ra'ayinshi. Amman bayan kwanaki
biyu saiya sake daga masa maganar, ranshi
kuma yakai matuka wajen baci. Me yasa Julde
yake da taurin kai? Me yasa ba zai fahimci gata
yayi musu daga shi har Saratu ba? Yasan
asalinta, yasan daga inda jikokin shi zasu fito,
bashi da wata fargabar cakuduwar ahali
"Da nace zan maka baki baka yarda ba kenan?
Gani kake ba zan iya tsine maka kabi duniya
akan maganar nan ba ko Julde?"
Koshi Datti da yake furta kalaman bai hango
zasu faru ba, shisa ya cigaba da hidimar auren
kamar Julde bai fadi ya maimaita cewa baya so
ba.
"Dan Allah Hamma kayi hakuri, ka hakura haka,
kaga Baba ranshi ya baci"
Yelwa ta roke shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 233
"Ni kuma nawa bacin ran fa? Yelwa nawa bacin
ran in kaishi ina? Don shi ya haifeni sai yaimun
auren dole? Shi zai zauna mun da ita?"
Kai ta girgiza masa idanuwanta cike da hawaye
"Nace yayi hakuri abar maganar, baka san me
yace mun ba"
Murmushin takaici me sauti Julde yayi
"Kema ca yayi zai tsine mikin?"
Yanda ta kalle shi ya tabbatar masa da hakan ya
fada. Tsinuwa a bakin Datti ba wani abu mai
wahala bane, tunda suka taso suke jin yana bin
'ya'yan mutane da ita, harma da su kansu
iyayen. Abu kadan da bai masa bane zaisa kajita
a bakin shi yana aika musu kwando-kwando.
Bata taba damun daga shi har Yelwar ba duk da
suna ganin tana damun Daadar su. Tunda suna
jin yanda take masa magana a kai har ta gaji ta
daina. Saboda basu taba hango wannan
tsinuwar zata waiwayo kansu ba.
"Meye a tsinuwar? Cikin wanda yake tsinewa
duk rana wa kikaga ya fasa hidimar shi ta yau da
kullum"
Lubna sufyan
Hausabook.com 234
Hawayenta ne suka zubo
"Ance ta iyaye dabance, haka naji
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 27