kamar kuma ba
daga bakin shi suka fito ba, saboda su duka
biyun suna bukatar jinsu, daya taka ya karasa
yana zama gefen gadon, sai hawayen da suke
yawan kwace ma Julde a cikin kwanakin nan
suka sake kwace masa yau, a karon farko, a
gaban Nawfal. Sai dai ya zaiyi? Ya zai rage
Lubna sufyan
Hausabook.com 532
nauyin da yake danne da zuciyar shi? Ba zai
boye har abada ba ya sani, amman so yake ya
boye, daya fadin nan baiso ya tashi ba, ya sone
ace da suka dauke shi, rami ne suka sauke shi a
ciki suka bi da kasa yanda ba zai sake motsin da
za'ace saiya fuskanci kowanne a cikin su ba.
Amman idan fa akace rami, a matsayin shi na
musulmi kalma ce mai nauyin gaske, kalma ce
da take dauke da tarin ma'anoni, hakan na nufin
a binne shi, idan akayi maganar binnewa ko da
ba'a cika ka'idojin da musulunci yazo dashi ba
kabari bahaushe zai kira inda duk aka zira shi
akabi da kasa, kabarin shi, kuma a cikin yan
kwanakin nan ya fuskanci tarin zunuban da
suke kan shi, ya kuma kara sanin idan shekara
dari aka kara masa ba zai taba jin sun isheshi
aikata aikin alkhairin da za'a binne shi babu
wasi-wasi a zuciyar shi ba, babu taraddadin ko
Allah ya karbi tubanshi ko bai karba ba.
Idan har tunanin fuskantar yaran shi na razana
shi haka, fuskantar su da zunubi kwara daya da
yake tunanin shi kadai suka san yayi kokarin
aikatawa bai san yanda zai fuskanci Allah a filin
qiyama ba, a gaban taron da zai kasance na duk
Lubna sufyan
Hausabook.com 533
wata halitta da aka taba wanzarwa a duniya,
mala'iku, aljanu, mutane da ma halittun da Allah
daya halicce sune yabarwa kanshi sanin
wanzuwar su. Kunyar duniya ce kawai wannan?
A cikin tashi duniyar ma ta mutanen da yasan
zasuyi komai don ganin asirin shi ya rufu? Itace
kadai ta gigita lissafin shi haka? Ta saka
hawayen shi suke ta zuba kamar ba zasu taba
tsayawa ba?
Saboda a cikin shekaru masu yawa, a karon
farko yaji kamar ya dawo cikin hayyacin shi,
kamar abinda yake daure dashi ya sake shi tun
ranar, da ya bude ido ranar, da baiga kukan da
Saratu takeyi ba, da batace masa
"Kamar mata sun kare a duniya Julde? Na waje
basu isheka ba? Idan sun kare a Kano kana da
halin da zaka bisu wajen Kano, baka ga kowa ba,
sai ita? Sai Madina? Sai Madina kamar ba daga
jikin Yelwa ta fito ba? Zunuban da kake dauka
kullum basu isa su binneka ba sai ka kara da
nauyin wannan?"
Zai iya dauka komai ya faru ne a mafarki,
mummunar mafarki da idan akace ya bada
Lubna sufyan
Hausabook.com 534
abinda ya mallaka duka don ya guje ma faruwar
shi a gaske zai mika batare da yayi dogon tunani
ba
"Baka so ka aureni ba nasani, ka fadamun da
bakinka, tun daga ranar dana shiga gidanka
zuwa yau, Julde ka shafe kaso mafi girma na
ranakun wajen tabbatar mun yanda baka so na,
kayi duk wani kokarin ganin ka rabani da kanka
na jure, wannan... Ba zan iya ba... Ba zan iya ba
Julde, so da aurenka ne kaddarata, da yardar
Allah ba zasu zama ajalina ba..."
Ta karasa tana saka hannu ta goge hawayenta
da kamar ta bawa wasu damar fitowa, jikinta na
wata irin kyarma da bata da alaka da zazzabin
tashin hankalin da ya lullubeta kamar bargo,
dakyar ta iya mikewa, ya riko hannunta, saboda
a karon farko a rayuwar shi, a cikin abubuwan
daya samu ya kuma rasa, babu guda daya da
baya tare da Saratu, akwai mutuwa ya sani,
amman ko ita bai taba hasaao zata rabashi da
Saratu ba, saboda a wautar tunani irin tashi zai
rigata tafiya. Itace abu kwara daya da yake da
yakinin babu wani abu da zai faru tabar
bangaren shi. Ko akan yaranshi bashi da
Lubna sufyan
Hausabook.com 535
wannan tabbacin kamar yanda yake dashi
akanta.
Ba dan yana sonta ba, ba don auren soyayya
sukayi ba, amman mutanen duk da yaso din
wanda yaba dalili da wanda bai ba wani dalili ba
haka suka barshi, suka barshi ita tana tare
dashi, shisa yanzun da yaji daga bakinta, ya ga
alama a cikin idanuwanta wani irin kadaici mai
tare da firgici ya daki duniyar shi yana
barazanar ruguza abinda yayi saura
"Ke kadaice Saratu, ke kadaice baki taba guduna
ba duk dalilin dana baki, karki fara yau, karki
fara yau da nake jin na rasa komai, a ciki harda
yardar yara na...idan kika tafi shikenan, bani da
komai... Da gaske komai zai zo mun karshe tare
da tafiyar taki"
Ya karasa cikin wata murya da ta sake karya
mata zuciya, saita koma ta zauna, yana kallonta
tayi kuka kamar ba zata daina ba, tayi kuka har
bacci ya dauketa hannun shi yana cikin nata,
nashi hawayen basu fara zuba ba sai da duhun
dare ya mamaye sauran hasken da yake gari, sai
daya rufe idanuwan shi hoton shi tsaye akan
Lubna sufyan
Hausabook.com 536
Madina da nufin keta duk wata yarda da aminci
da ta dauka ta danka masa, tsallake kallon da
take yi masa na wanda ya maye gurbin mahaifin
da ta rasa ya rusata ta hanyar da ba zata taba
komawa dai-dai ba har karshen rayuwarta, sai
da wannan hoton ya dawo masa yana saka
numfashin sa ya fara yi masa barazana sannan
ya tashi zaune.
Yaja iska ta kasa kai masa inda ya kamata balle
yayi kokarin fito da ita, a tsakanin wannan
kokawar da yakeyine hawaye masu dumi suka
fara saukar masa kafin wani irin wahalllen
gunjin kuka ya kwace masa
"Hamma ina son ka, ka sani aiko?"
Muryar Yelwa ta zabi ta dawo masa a dai-dai
wannan lokacin
"Shisa banda wata damuwa Hamma, saboda
nasan abinda ba zaka mallaka mun ba, abinda
baya karkashin ikonka ne kawai"
Ta takan fada duk idan ta nuna tana son wani
abu ya samo abin nan ya bata shi, ya sani, Yelwa
ta tabbatar masa da haihuwar shi Daada tayi,
Lubna sufyan
Hausabook.com 537
amman idan aka saka soyayyar su a ma'auni
zaiyi wahala wadda take masa batafi ta Daada
yawa ba. Me ya same shi da zai kokarin rusa
gudan jininta? Ko daya saba tsallake halarcin
shi ya rungumi haram da hannayen shi a bude,
ya kamata ace akwai haram din da tafi karfin
shi, akwai layuka ko a haramcin da bai kamata
yayi kokarin tsallakawa ba irin yanda yayi. Sai
yake neman ranar da zuciyar shi ta fara haska
masa Madina a matsayin mace dan ya koma yasa
wuka ya ciro zuciyar ya yarda ita ya huta,
amman ranar saita bace masa a cikin sauran
ranaku.
A cikin ranakun daya shafe awanni yanajin
kamar wani abu yana bibiyar rayuwar shi, wani
abu da idan ya cimmasa komai zai iya zuwa
masa karshe. Ashe da gaskene, gashi nan da
komai yazo karshe sai yake danne shi, da Saratu
ta tashi ta rike shi ma saita sa wani kukan ya
kwace masa, kuka yake kashi-kashi, kuka yake
akan abubuwa da yawa, musamman damar daya
samu a tare da Datti ya kasa zuwa ya zube a
gabanshi ya roki ya yafe masa, ya ianye kalaman
shi akan shi, ya roke shi akan gwiwoyin shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 538
komin tsayin kwanakin da zai dauka har saiya
yafe masa, saiya fada da bakin shi ya yafe masa
sannan. Baiyi haka ba, ya dauka yanda lokaci ya
tafi da Datti zai tafi da duk tsinuwar da ya dinga
yi masa, zai kuma tafi da tasirin bakin shi yabar
holokon kalaman kawai.
Ashe suna nan da nauyin su kamar jiya ya furta
masa su, kunyar da ya nemar masa yaji ta, ya
kunyata a gaban mutanen da suka fi komai
muhimmanci a wajen shi, yaji kunyar da yake da
tabbacin lokaci kawai ba zai tafi da ita ba
"Ka daina boye mana Daddy, ba zai canza komai
ba"
Cewar Nawfal yana kallon shi, kai Julde ya daga
yana saka hannu ya goge hawayen shi. Shi da
kanshi Nawfal ba zaice ga asalin abinda suka
fada ba, ya dai san Julde ya maimaita masa babu
abinda ya faru, kuma ya yarda dashi tun ranar,
ya maimaita masa ya yafe masa fiye da yanda ya
maimaita masa babu abinda ya farun, ya rasa
meya rike masa harshe, meya hana shi yace
masa ya yafe masa, ko dan yafiyar ba abu bane
da zai faru lokaci daya? Watakila sai a hankali,
Lubna sufyan
Hausabook.com 539
tare da ciwon yardarsu da ya karya, yanda bai
koyi kokarin danne zuciyarshi ya nuna mata
abinda take so abune da zai rusa zuciyoyin su
duka ba. Yana kallon shi ya sauka daga kan
gadon ya bude wardrobe din shi, a ciki ya janyo
wata jaka, a cikin jakar ma alamun shi sun nuna
akwai abubuwa da yawa daya bude kafin ya
dauko takardar da take hannun Nawfal din
yanajin nauyinta a duka jikin shi, ya damka
masa ita.
Numfashi yaja yana fitar da iskar ta bakin shi,
jikin shi na rawa ya bude takardar, yana tsintar
kanshi da saka dayan hannun shi ya shafi
rubutun, kafin ya rike da duka hannuwan shi
biyu kamar yana rike da hannayen Bukar da
suka bace a cikin tunanin shi, tayi kama da
wasika, sai dai wasikar duniya duka daya sani,
da wadda aka koya musu a farko babu wadda ta
fara da sunan marubucin ta kamar yanda
wannan ta fara dashi:
Bukar,
Abubuwan da zan fada ji nakeyi sunfi karfin
littafi balle in tattara jimilarsu a yar takarda
Lubna sufyan
Hausabook.com 540
guda daya, banda tabbacin mutum daya da nake
son rubutun nan domin, idan nace abinda na
haifa dole in naqalta jinsi a tare dashi, sai dai
hakan ba zai yiwu ba, 'yata zance ko 'dana tunda
ban kai da ganin su ba. Ina rubutun nan ne
saboda zuciyata na rawa akan abubuwa da
yawa, ciki harda rashin tabbacin zanyi tsayin
ran da zanga abinda yake cikin matata.
Cikakken sunana Bukar Baabuga, dan asalin
kauyen Marake, da ga Dije matar Julde, idan
kaje Marake duka ka tambayi Julden Hammadi
ba za'a rasa wanda suka sanshi ba, idan kuka
same shi zaku samo mahaifiyata, zaku gano
Daada. Na biyo Hamma na da sunan karatu, sai
dai dalili yasa ban tsaya makarantar da yayi ba,
yanzun nake fahimtar a cikin dalilin nan harda
kaddarar haduwa da Kaltume, saboda
mahaifinta ya zabeni satika biyu da zuwana
Borno a cikin tarin almajiran da suke karkashin
Malamin mu, da fadin ya yarda da natsuwata, ya
aminta da cancantata daya daga cikin yaran
gidan shi.
Mahaifin Kaltume bai rikeni a dan aikaceaikacen gidan shi kawai ba, haduwata dashi
Lubna sufyan
Hausabook.com 541
saita kara inganta rayuwata, sai yake jana har
wajen kasuwancin shi, a hankali saina fahimci
babu shiri a tsakanin shi da 'yan uwan shi duk
kuwa kasancewar kowannen su karkashin
kulawar shi, cikin ni'imar tarin dukiyar da Allah
ya azurta shi da ita, yau da gobe na san cewa
mahaifi suka hada, shi kadai mahaifiyar shi ta
haifa kafin rasuwarta, mai rabon ganin badin da
ake fada ce ta kasance akan shi, sai kuma Allah
ya ware shi a cikinsu ya azurta.
Akan dukiya, shine karona na farko da nagani
ba naji labari ba, 'yan uwa na neman rayuwar
dan uwansu, rayuwarshi suke nema amman ni
da nake kusa dashi, da lokaci ya koyawa kaunar
shi ni nakejin tsoro. Yanda yake shi kadai a
wajen mahaifiyar shi, haka Kaltume take ita
kadai a wajen shi. Naje marake, na dawo na
samu rasuwar matarshi mahaifiyar Kaltume, na
same shi yana wani ciwo da rayuwa ba'a
hannuna take ba amman zuciyata na fadamun
ba zai tashi ba, a cikin ciwon ya danka amanar
Kaltume a hannu na, a cikin ciwon ya bukaci
bayason kasa ta rufe idanuwan shi ban amshi
aurenta ba. Daga ni har ita an daura mana aure
Lubna sufyan
Hausabook.com 542
bayan na rana daya bamu taba hango
kasancewa karkashin inuwa daya a matsayin
mata da miji ba
Ba Kaltume kawai ya dankamun amana ba,
harda dukiyarta da tashi ce, saiya rasu, kasar
dai ta rufe idanuwan shi yana barina da
Kaltume, yana barmun nauyin zame mata
abubuwa biyu masu muhimmanci da ta rasa, ya
bar mata gadon arzikin shi, ya barmun na
kiyayyar 'yan uwanshi da gari ya dauki zargin
da sa hannun shi a jinyar da ta zama ajalinsu shi
da matar shi, ni da Kaltume munyi ciwo, munyi
jinya kala-kala muna tashi, kamar yanda ta
roka, nayi yunkuri, nayi duk wani kokari na
mubar Borno zuwa Marake sai wani abu ya
danne ni, sai in kasa. Haka kawai nakejin kamar
cikin jikinta ba zanyi tsayin kwanan ganin shi
ba.
Baya takardar Nawfal ya juya, babu cigaba,
baisan abinda yake ji ba, ya mike tsaye, ya koma
ya zauna, kafin ya murza takardar saboda yaji
alamar kamar guda biyu ce, sai ga dayar ta fito,
yana rike da numfashin shi ya soma bin wasikar
Lubna sufyan
Hausabook.com 543
Bukar,
Da gaske babu abinda addu'a ta bari, a ciki
harda yau da muka hada kayan mu duka, bayan
shekara hudu, yau mun hada kayan mu tsaf da
nufin barin Borno babu wanda ya fita daga
hayyacin shi, tun azahar, ga dare na neman
rabawa, amman daga zuciyata nake jin zamu iya
barin Borno a safiyar gobe da yardar Allah, babu
abinda zai faru, zamuyi nisa da kowa da komai,
zamuyi nisa dasu.
Wannan karin har dayar takardar Nawfal ya
dauko ya sake murzawa, ya zazzaga amman
babu komai, su biyun ne kawai. Bayan Bukar,
suna daya kawai ya karu, sunan mahaifiyar da
ko a tunanin shi ba zai iya tunata ba, Kaltume,
ya dauka takardar dauke take da wasu sirrika,
wasu bayanai da zasu amsa masa tarin
tambayoyin da yake dasu bawai su sake jefa shi
cikin sabon rudani ba
Kwanaki biyu kenan, da Nawfal ya same shi ya
mika masa wasu takardu guda biyu, kamar yaki
karba, kamar ya cewa Nawfal din ya fara fada
Lubna sufyan
Hausabook.com 544
masa abinda yake cikin takardun kafin ya
karba, sai yayi karfin halin mika hannu ya amsa,
ya bude ya karanta, nauyin abinda yake ciki na
kara danne shi tare da sauran abubuwan da
yake fama dasu a cikin kwanakin nan
"Ba zakaje Borno ba, ka sani ai ko?"
Ya fadi yana daga ido ya kalli Nawfal din
"Idan tunanin da yake cikin kanka kenan ka
fitar dashi, ba zakaje Borno ba. Waya baka
wannan ma?"
Kafadu Nawfal din ya dan daga masa batare da
yace komai ba, kamar babu muhimmanci a
sanin wanda ya bashi, tunda dai ya rigada ya
gani
"Bajjo ba wasa nakeyi ba"
Ya fadi yanajin wani abu yayi masa tsaye a waya
da yanayin kallon da Nawfal yake yi masa
"Idan naje Borno ta ina zan fara? Ko ina so inje
bansan ta inda zan fara ba Hamma, ni Marake
zanje...zamuje da Hamma Khalid...kace zakaji da
Madina, mu zamuje Marake"
Lubna sufyan
Hausabook.com 545
Numfashi ya sauke yana jinjina ma Nawfal din
kai, takardun ya karba daga hannun Salim yana
juyawa batare da ya sake cewa komai ba, shima
Salim din ya bude baki amman sai ya rasa
abinda zaice, ya karbi duk lambobin wayar da
yake bukata. Ya kuma gama shirin duk da zaiyi,
asibiti ya samu wanda baiji a muryarsu sun
nuna alamun ya takura su ba daya bukaci su
karbar masa shift din shi, tunda ya sha yi musu
nasu na dare babu adadi. Idan komai ya tafar
masa yanda yake so, kwana daya ya tsara yi a
garin Abuja. Duk da bai daga burin shi akan
komai ya tafi yanda ya tsara ba, dan jikin shi ya
gama yin sanyi da yanayin rayuwa yanzun.
Sai yasha mamaki, yanda komai yazo masa da
sauki, saiya kara mamaki akan wani mamakin
lokacin da idanuwan shi suka sauka akan
Kabiru, kafafuwan shi suka soma yi masa
barazanar kasa daukar sauran gangar jikin shi,
da gaske ne, ana kama, har zakaji wasu na cewa
"Ai kuwa idan wane ya bace to tabbas 'yan uwan
shi da dangin shi duka ba zasu taba yarda ba kai
bane ko kece, saboda yanda kukayi kama"
Lubna sufyan
Hausabook.com 546
Shima wajen mutum nawa ya fada masa ya taba
ganin me kama dashi, amman mutumin da yake
tsaye a gabanshi, ko yayi rantsuwa ba zaiyi
kaffara ba jinin Madina ne, da yayi murmushi
sai Salim yaji zuciyarshi ta doka
"Kullum ina duba hanya, a cikin fuskoki da yawa
ina neman wanda zaiyi shige dana Yelwa ko zan
rike shi in tambayi labarin 'yan uwanta, in samu
in hadata da ahalin dana rabata dasu, yaro nazo
nan cike da taraddadi, nazo nan da zuciyata a
tafin hannu na saboda bansan abinda zan gani
ba. Bayan shekaru masu yawa, a tsakanin
haduwa da fulani kala-kala, yau naga fuslar
Yelwa a cikin taka"
Salim ya bude bakin shi, labbanshi sun
motsa,amman muryar shi bata karasa cikin
kunnuwan shi ba, bai san meya tambaya ba sai
da yaji amsar Kabiru
"Neman wanda ya daura mana aure ne abu na
farko da muka fara yi da Yelwa bayan motar
data dauke mu daga Marake ta sauke mu"
Kabir ya karasa maganar da wani kyalli da
Salim din ba zai iya fassarawa ba kai tsaye a
Lubna sufyan
Hausabook.com 547
cikin idanuwan shi, kyallin yana masa kama da
dana sani, yana masa kama da shekaru cikin
wani ciwo na zuciya da babu wanda zai fahimta,
yana kuma yi masa kama da firgici,
kwatankwacin wanda ya dandana a 'yan
kwanakin nan. Yayi tunani kala-kala, akan
abinda ya tambaya, amman ya kasa tunawa. Ya
dai san amsar Kabiru ta saukaka masa wani abu
daya jima kulle da zuciyar shi, ya sauke
numfashin da baisan yana rike dashi ba tun
randa ya karanta wasikar Yelwa a hannun
Madina.
"Za muzo, zan dauko ta muzo"
Shine kalman karshe da suka hadashi da Kabiru,
suna masa yawo a cikin kanshi ya koma Kano,
suna masa yawo har kwanaki uku da yayi
amfani dasu wajen binne kanshi da aiki a asibiti
dan ya janye hankalin shi daga kiran Kabiru, ya
kuma ji dadi da Madina ma duk wayar da sukayi
bata daga masa maganar ba. A safiyar kwana na
ukun ne da yake jin hakurin shi yana gab da
karewa Kabiru ya kirashi ya fada masa suna
hanya, bai tambayi daga inda zasu taho ba, ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 548
dai cire farar rigar jikin shi, ya kuma dauki
mukullin motar shi ya fita daga asibitin
"Kaci abinci Hamma"
Sakon Madina ya shiga wayar shi lokacin daya
fita daga asibitin, ta saba tuna masa yaci abinci
saboda tasan in dai yana aiki saiya wuni da
yunwa. Yau yana da karfin cin abincin, duka a
kwanakin nan zai amsata ne, amman saiya saka
abincin a gabanshi yaji ko kadan bayaso ya kai
shi baki, idan ya tura abinda zai iya yanayin
hakan ne don jikinshi yana bukatar abincin,
amman baya gane dandanon ko kadan. Sai ya
rasa abinda zai siya, bayason shiga bangaren
Saratu, har yanzun bai shirya ganinta ba, balle
kuma abinda zai hadashi hanya daya da ganin
Julde. Yana cikin wannan tunanin ne yaji
alamun kira ya shigo wayar shi
"Adee"
Ya fada bayan ya daga ya saka wayar a kunnen
shi
"Ka manta kana da kanwa ne Hamma?"
Sai murmushi ya kwace masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 549
"Yanzun na fito daga asibiti, abinda zanci nake
nema Adee"
Ya furta a madadin amsa korafinta
"Fanke zan soya ni, ka biyo ka karba mana to,
ina da Zobo da kunun aya a fridge, jiya nayi, in
kuma da tea zaka hada to"
Numfashi ya sauke
"Yanzun sai nazo har unguwarku saboda fanke
Adee?"
Yanajin dariyarta
"To me kake so sai in dafa maka? Kaji? Dan
Allah kazo, kaga rannan da naje gida baka nan,
banganka ba"
Sai da yayi kamar ba zai amsa ba, saboda
tunanin da yakeyi, yana hango tsayin tafiyar da
zai hada shi da gidan Adee daga inda yake
"Bari in karbi fanken"
Bai amsa surutun da takeyi ba ya kashe wayar.
Ya danyi fama da cunkoso daya juya dayan
hannun, tunda ranar aikice, ga kuma yan
Lubna sufyan
Hausabook.com 550
kasuwa da sauran al'umma da suka fito dan
gudanar da uzurin ranar. Sai yaga komai ya kara
kala a idanuwan shi yau, har iskar da yadan
bude gilashin motar tana shigo masa jinta
yakeyi daban, kamar duk wani abu da zaici karo
dashi yau ya san girman abinda yake shirin
faruwa dasu. Da wannan yanayin ya karasa
gidan Adee, yanda duk tayi dashi ya shiga ciki
yakiya, motar shima a bakin kofa yayi parking
dinta bayan ya juyata hannun da zai fitar dashi
daga unguwar
"Hamma wannan ba zuwa kayi kaganni ba"
Cewar Adee data fito jikinta sanye da hijab, tayi
masa kyau, alamar akwai kwanciyar hankali a
tattare da ita, hakan kuma yayi masa dadi, duk
gidansu idan akwai wanda ya cancanci ya samu
natsuwa fiye da kowa to Adee ce, saboda
nagartattun halayen da take dashi
"Baka fadamun zobo zaka sha ba ko kunun aya,
na dai saka maka duka biyun"
Karbar kwandon da ta mika masa yayi yana
ajiyewa kan kujera a cikin motar
Lubna sufyan
Hausabook.com 551
"Naganki, kinganni nima ina lafiya. Ki gaishe da
mijin ki"
Ya karasa yana murza mukullin motar
"Hamma..."
Ta kira da sauri, sai ya daga ido ya kalleta, duk
ta daburce lokaci daya, kashe motar ya sakeyi
yana kiran sunanta
"Adee"
Numfashi taja ta fitar
"Da naje gida, akwai abinda ya faru ko? Na
tambayi Nanna tace bakomai banda Daddy da
bayajin dadi kuma shima jikin da sauki, naga da
sauki, har hira munyi... Daga Bajjo har Khalid
sunce mun bakomai"
Sosai ya kalleta wannan karin yana ganin
sauran kalaman da bata furta ba kwance akan
fuskarta
"Akwai abinda ya faru, ki yarda dani rashin
saninki yafi muhimmanci"
Lubna sufyan
Hausabook.com 552
Ta dauki wasu dakika, har saida ya fara tunanin
musu ne abinda zai fito daga bakinta sannan
tace
"Abinda ya farun? Ya wuce? Komai ya koma daidai?"
Kai ya girgiza mata
"Amman babu abinda lokaci baya tafiya dashi
right?"
Murmushi tayi tana dan daga masa kai
"Zamuyi waya"
Kan dai ta sake daga masa, sai kuma hannunta
bayan ya rigada yaja motar, ta mudubi ya
hangota tana tsaye har lokacin. Babu ma'aunin
da zai iya daukar girman son da yake yiwa Adee.
Tun suna yara yakejin duk wani abu kafin ya
sameta zai fara wucewa ne ta cikin shi, saboda
ko menene zai same shi tsaye a gabanta, yana
bata duk wata kariya da take karkashin ikon
shi. Waje ya samu yayi parking, ya saka ruwa ya
wanke hannun shi ta murfin motar, sannan ya
bude robar fanken, harda soyayyen nama ta
zuba masa. Yayi mamakin yanda ya kusa cinye,
Lubna sufyan
Hausabook.com 553
dakyar ya rage guda hudu, yanka nama biyu.
Gida ya wuce ya watsa ruwa ya sake kaya,
yadine ya saka bula, Nawfal ne ya sai musu, duk
wani kaya da yake dasu masu kalar yawanci
kyautar Nawfal ce, kamar a duniya babu wata
kala da idanuwan shi suke gani sai ruwan
sararin samaniya.
Saiya wuce gidan Daada, kamar kullum a bakin
kofa ya tsaya ya kira Madina, ta fito, sai da ta
zauna cikin motar tana hamma kamar bacci bai
isheta ba sannan ya kula da wani takalmi mai
kaza da ta sakama kafafuwanta, irin mai gashin
nan, murmushi ya kwace masa
"Ina kwana"
Ta furta kowacce kalma a tsakanin Hammar da
takeyi, tana mika hannu cikin kwandon da
dauke kafin ta zauna, ta kuma ajiye shi akan
cinyarta
"Menene wannan? Ina ka samu zobo mai sanyi
da safen nan?"
Yana kallo ta dauki roba daya tana juyawa, data
kwance ta kurba
Lubna sufyan
Hausabook.com 554
"Adda ta baka?"
Ware idanuwa yayi cikin mamaki
"Kasan zobon Adda fa ba irin shi a garin nan,
dana sha saina gane nata ne, nace ta koyamun
dame-dame take sakawa, nayi amman sai naji
bai dai kai nata ba..."
Komai nata, komai na Madina yayi masa, harda
surutun ta
"Fanke? Ya naga guda hudu?"
Ta karasa tana bude robar ta dauko guda daya
"Rage miki nayi"
Ya furta yana jingina jikin shi sosai da kujerar
motar ya juyar da kai yana kallonta, yanda da
yaganta duk wata gajiya da yake ji, wadda ya
sani da wadda bai sani ba take danne shi yana
bashi mamaki, ko bacci yakeji daya ganta saiya
karu, saboda yana so yayi baccin a kusa da ita,
yanajin kamar duk wani hutu nashi yana jingine
ne da ita
"Kwara hudu Hamma?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 555
Ta fadi tana dariya
"Yayi dadi, dakyar na rage"
Dariya takeyi sosai, ya kuwa yi mata dadin, suna
da sauran shinkafa da miyar data dafa da
daddare, shine ta dumama musu da safen saita
dafa ruwan shayi tunda daga ita sai Daada a
gidan, Murjanatu bata nan, bata tambayi inda
taje ba tun jiya saboda abubuwan da take tunani
sunyi mata yawan da bata da wajen kananun
tambayoyi irin wannan.
"Hamma karkayi bacci a motar nan, ka fito mu
shiga ciki ka kwanta a kujera, Daada ma bacci ta
koma"
Madina ta fadi tana saka shi makale mata
kafada, idan cikim gidan ya shiga, ba zaiji ta a
kusa dashi haka ba, tana ma iya bar masa falon
da taga yayi bacci, shisa ya sake langabewa cikin
kujerar, yace yana sonta, ya fada mata yana
tabbatar da taga duk wani waje da son nata ya
taba a tare dashi, batace komai ba, ta kalle shi,
kamar ta fahimta haka ta kalle shi
"Mug..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 556
Ya kira can kasan makoshi, sai da ta gyara
gilashin fuskarta sannan ta kalle shi
"Bakya so na?"
Tambayar ta fito daga bakin shi tana dukanta,
saboda batayi tsammaninta ba, daga wajen wani
ma balle kuma shi, ya zai dora ayar tambaya
akan son da takeyi masa bayan yana daya daga
kalilan din mazan da suke cikin rayuwarta?
Kuma kamar tunda suka hada jini bata da wani
zabi akan son shi. Kafin kusanci ya gifta musu
tana son shi saboda jinin shi da yake yawo a
jikinta, da tasan wanene shi sai ya tabbatar
mata ko basu hada jini ba zata so shi.
Amman a kalmar so na karshe daya furta mata
sai taga kamar yasha bamban da wanda take
tunani, a kallon da yakeyi mata yanzun sai yake
tabbatar da inda tunaninta yaje anan nashi yake
zaune
"Bakya sona"
Wannan karin ya furta cikin son tabbatar ma
kanshi, saita tsinci kanta da sauran girgiza masa
kai, kaifin kallon shi na ratsawa ta cikin kirjinta
Lubna sufyan
Hausabook.com 557
zuwa zuciyarta, kawai dai kamar bata shirya ba
take ji, ta bude baki batare da tasan amsar da
tayi niyyar bashi ba, karar wayar shi ta katse
musu yanayin, daya duba sai taga yanayin shi ya
canza
"Bari yanzun zan dawo"
Ya furta idanuwan shi na kan wayar da bai daga
ba, dakyar ya rabasu da wayar yana kallonta,
kai ta dan daga masa tana daukar kwandon da
yake kan cinyarta, yanda jikinta yake a sanyaye
sai taji dakyar ta iya fita daga motar, kafin tayi
wani yunkuri ya mika hannu ya rufe murfin yaja
motar yabar wajen. Cikin gida ta koma, da
kwandon a hannunta, saita wuce dashi kitchen,
ta dauki robobin da suka rage ta saka a fridge,
harda zobon data fara sha, sai sauran fanken da
guda biyu taci, ta dauko robar tana fitowa falon,
suka ci karo da Daada a tsakiyar falon inda take
neman zama kan kafet
"Wai Daada laifin me kujera tayi miki?"
Madina data zauna kusa da ita a kasa ta fadi
"Ke da batayiwa laifi ba me kike a kusa dani?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 558
Dariya tayi tana mika mata robar fanken
"Adda ce ta ba Hamma, ci kiji Daada, yayi dadi
sosai, inajin gobe idan Allah ya kaimu shi zanyi
mana"
Murmushi Daada tayi tana daukar guda daya
"Lallai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 27