kadan, taya zata tattara abinda ya
faru a kwanakin nan, ta takaita shi harta sanar
da Julde?
"Babu wata matsala"
Shine amsar da takan bashi duk idan ya
tambaya, saboda babu, matsalar ba irin wadda
yake tunani bace ba. Kuma da yanda yake nuna
akwai uzururruka a gabanshi sai ta zabi barin
shi ya tafi don korar wannan uzurin da yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 394
gabansa. Ba sai da matsala ba, wasu rabakun
labari ne iyaye zasu so su baka, abinda ya faru
dasu na farin ciki, abinda ya faru dasu mai
muhimmanci da akasin hakan, wani abu daban
wanda daga kai harsu dinma baku da alaka
dashi. Babu kalar labaran da baka basu ba, suka
saurara, badon basu da abinda yafi labaran
naka muhimmanci ba a lokacin kuruciya, sai
don soyayyarka data danne komai.
A yayin girmansu, reshen ne yake juyewa, sune
suke bukatar wannan kulawar ko da bata kai
rabin wadda suka bayar ba. Duk halin ko in kula
da Datti yake nunawa akan Julde abin yana
damun shi, yana ci masa rai fiye da yanda zai iya
misaltawa. Dije tace kuskuren nasu ne, nashi
kason yafi na kowa, daga ranar har zuwa yanzun
akwai wani bangare na zuciyar shi da kalamanta
suka zauna suke nukurkusa. Ta saka shi
maimaitawa kanshi tambayoyi da dama. Akan
Yelwa, a batunta da Kabiru, a zancen aurenta da
Modibbo. Baya son amsa ko daya da yake samu,
saboda duka suna kamanceceniya da juna, idan
aka dunkule ma'anarsu zata zagaya ta dawo kan
yanda komai yake laifin shi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 395
Amman akan Julde fa? A ina ya kuskure? A
gadarar da yakeyi ta yafi karfin ya haifi
mazinaci? Yafi karfin dauda irin ta zina ta rabi
ahalin shi? Ko aibata iyaye tare da yaran da suka
tsinci kansu cikin irin halin da yake yanzun? Shi
kam yayi kuskure, Dije ta fada masa yayi
kuskure, sauran iyayen yaran fa? Kuskuren
sukayi suma? Ko kuwa kaddarar da yake ganin
kamar katin gayyata ake bawa marar kyauce ta
yi musu ziyarar gayyar sodi? Me yake faruwa?
Duk da ba ilimi gare shi ba, a kasan zuciyar shi
yasan wasu tambayoyin ko karen hauka ya cije
shi huhun shi ba zai busama sautin shi iskar da
zasu rabo kirjin shi zuwa makoshin shi har
harshen shi ya furta su a matsayin sauti ba.
Saboda hakan zaiyi dai-dai da fitar dashi daga
musulunci. Sai dai shin duk wannan laifin nashi
bai cancanci Julde ya sake bashi hakuri ba? Ya
nemi yafiyar shi tare da kokarin gyara alakarsu
ba? Idan ya gaishe dashi ya dauke kai shikenan?
Bai isa ya sake bashi hakuri ba, bacin rai da
karyewar zuciyar daya ja masa. Ko kuma bai ga
shi kadai ya rage masa bane? Duk da kullum sai
zuciyar shi ta tabbatar masa da cewa duk inda
Lubna sufyan
Hausabook.com 396
Yelwa take tana da rai, babu yanda za'ayi ace
baiji a jikin shi ba idan har ya rasa ta.
"Idan Yelwa ta rasu a wani wajen fa? Idan hakuri
ya kamata mu ba zukatan mu a maimakon
duban hanya fa? Ya zamuyi?"
Dije ta tambaye shi wani dare suna kwance,
hannunta ya laluba ya damtse a cikin nashi
"Su biyu ne dani, su kadai suka rage mun a fadin
duniya kaf da zan kalla in kira nawa Dije... Babu
yanda za'ayi in rasa Yelwa jikina bai bani ba,
zata dawo"
Gyara kwanciya tayi, hannun shi da ta kara
dumtsewa cikin natane kawai shaidar daya
samu cewar taji abinda ya fada, sai kuma
yanayin numfashinta da alamar kuka takeyi.
Amman batace komai ba. Har bacci ya dauketa
tana barin shi da juyayin tambayarta. Shisa wata
asabar din daya tashi ya kwana da zazzabi, ya
sake jera hakan har talata Dije tace masa
"Ba zan aikama Julde sako ba kuwa yazo ya
daukeka zuwa asibiti?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 397
Kai ya girgiza mata, baya so ya furta, baya so ya
fada mata yanda yake jin kamar yana gab da
cike iya kwanakin da aka dibar masa zaiyi a
duniya. Ya sha jin karshen duniyar yazo masa,
akwai dararen daya kwanta yayi mamakin bude
idanuwan shi da safe, saboda bai kwanta da sa
ran zai tashi ba. Yayi rashin lafiya da tafi
wannan zafi, amman yanajin wani sanyi cikin
kasusuwan shi duk da zafin zazzabin da yake
jikin shi. Sannan koya ya mike sai yaga garin
yana jujjuya masa. Ga shi larabar daya kwanta,
alhamis saiya tashi harda ciwon kai. Abinda duk
yaci a yinin ranar saiya dawo. Yanayin daya
daga hankalin Dije ba kadan ba.
Da yammaci likis, yayi kokarin tashi zaune,
bayan ya gama jin yanda take jaddada masa
Julde na zuwa juma'ar asibiti za'a kai shi ko ya
amince ko bai amince ba, tunda har kayan sirace
an samo tayi masa zazzabin bai sauka ba. Baiyi
kokarin musa mata ba, saboda yanaji a jikin shi
bama zai kai juma'ar da take kira ba, duk kuwa
da tsakanin su da juma'ar awanni ne ya rage da
za'a iya kirgawa da yatsun hannu, musu da ita
bashi da wani amfani. Kallonta dai yakeyi, kallo
Lubna sufyan
Hausabook.com 398
cikin sigar daya dauki wasu shekaru baiyi mata
irin shi ba, kallonta yakeyi yanajin kwanakin da
ya rage a tsakanin su, sai yakejin son rike ko da
hannunta ne, ya kara bar mata abubuwan da
zata tuna shi dasu.
"Idan ba Dije ba, babu wanda zai iya zama da kai
Datti"
Ya tuna zancen Hammadi a yau, yana ganin
gaskiyar da ya kasa gani a wancen lokacin. Dije,
matar shi, amanar shi, uwar yaran shi. Yaran da
halin shi ya raba shi dasu amman Dije tana nan
tare dashi, kamar yaran ba daga jikinta suka fito
ba. Dije da take shanye duk wani mugun halin
shi
"Dije..."
Ya tsinci kanshi da kiran sunata, saita dago kai
ta saka idanuwanta cikin nashi
"Hamma ya sha fadamun idan bake ba babu
macen da zata iya hakurin zama dani, da gaske
ne, da ban gani ba, amman yanzun na sani. Ban
taba miki godiya ba ko?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 399
Wani abu ya canza a cikin idanuwanta, ya hangi
fargaba da tsoro a cikin su, amman saiya dake
"Nagode, nagode da yanda kika dinga hakuri
dani duk shekarun nan, duk da halayena sun
kawo mu inda muke yanzun... Idan nace ki yafe
mun duk abinda nayi miki naso kaina da yawa
ko?"
Hawayene cike da idanuwanta wannan karin
"Bana jin kinmun wani abu da na rike ki dashi a
iya zaman mu, amman idan kinyi mun din, ko
menene na yafe miki"
Hawayenta ne ya zubo
"Kaga kukana kashi-kashi Datti, bai isa ba saika
kara sakani wani yau? Waye yace kamun wani
abu dana rike ka? Ka daina maganganun nan
kamar kana mun bankwana, kayi ciwo da yafi
wannan kuma ka tashi, da wa zaka barni ma to
in ka tafi? Ko dai dabara ce aure zaka kara kake
son karya mun zuciya da batun mutuwa?"
Dariya yayi, dariyar daya kwana biyu baiyi ba,
dariyar da sautinta bai gama karade zuciyarta
har tayi dogon nazari kan ranar karshe da taji
Lubna sufyan
Hausabook.com 400
dariyar shi haka ba, muryar da ko da Datti bai
yanke kauna da sake jinta ba, ita kam Dije ta
dauki wannan hanyar tayi musu kutse cikin
tunanin su tana girgiza duk wani bango na
ruhinsu
"Baba..."
Yelwa ta kira muryarta na rawa, idanuwanta
tsaye akan shi, shima ita yake kallo. Yelwa ce,
yar shi, tilon yar shi da duhu da kuma ramar da
tayi bata boye kyawun fuskarta ba. Yar shi ce da
yake da yakinin ko fuska aka canza mata zai
ganeta. Sosai yake kallonta, atamfa ce a jikinta
da wata hijabi da asalin kalarta ya kode kamar
hijabin jikinta. Daga duk inda ta fito rayuwa ta
tara mata gajiyar wasan cikar shekara.
Karasawa tayi, yanajin sautin takunta a cikin
zuciyar shi kamar tambari. Hannunta ta mika da
Datti baiko yi tunani ba ya kama, ta lumshe
idanuwanta, wasu siraran hawaye na zubo mata,
ta bude idanuwanta akan Dije da batama san
hawaye takeyi ba
"Daada... Daada Am"
Lubna sufyan
Hausabook.com 401
Yelwa tayi maganar cikin karyewar murya
kuma a wahalce, har lokacin hannunta na cikin
na Datti. Sai da tayi kokarin zama, yanayin
yanda take yin hakan da dabara, tukunna daga
Dije har Datti suka sake kallonta, kallo fiye da
na mamakin ganinta, kallo daya wuce canjin da
fuskarta tayi, sutturar jikinta da kuma tarin
tambayoyin da suke yawo a kawunan su, kallo
na son gane dalilin da yasa take dabara wajen
zama. Kusan a lokaci daya sakon abinda
idanuwan su ya gani ya karasa har cikin kansu
yana saukowa zuwa zuciyoyin su. Ciki ne a jikin
Yelwa, ciki tsoho, idan Dije bata kuskure ba,
yanayin yanda cikin ya dunkule waje daya ya
kuma yo kasa, ko yanzun ciwon nakuda ya kama
Yelwa babu wanda zaiyi mamaki, saboda ko
meye a cikinta gab yake da fitowa duniya.
Babu jaka ko daya a hannunta, sai yar karamar
leda mai layi layi da take sakale a tsintsiyar
hannunta, har bayan zamanta kuma batayi
kokarin ciro ledar ba balle ta ajiye. Numfashi dai
take ta kokarin saukewa kamar zaman ma
aikine. Ta kuma kara matsawa yanda zata iya
Lubna sufyan
Hausabook.com 402
dora kanta a kafadar Daada tana wani irin
sauke ajiyar zuciya.
"Nayi kuskure Daada... Nayi kuskure mafi girma
a rayuwata"
Ta tsinci kanta da furtawa wasu sababbin
hawayen na saukar mata. Sai dai an rasa wanda
zai fara korar shirun daya biyo bayan
maganarta a tsakanin su. Sai kiran sallar
Magriba daya karade gidan. Har aka dire babu
wanda ya yunkura, sai da Daada taji alamar an
kira sallar tukunna ta iya samun karfin mikewa.
Ita tayi alwala, roba da buta ta kawo ma Datti da
bashi da karfin tashi har inda yake. Yelwa ce ta
karba, ita ta dinga zuba masa ruwan yana
alwalar. Shi yaba Dije damar shiga daki ta dauko
wata tabarmar ta shimfida harta tayar da sallah,
yelwar ma inda Datti yayi alwala tayi tata.
Daga zaune ya gabatar da tashi sallar saboda
yana kara jin sanyin nan ya kara lullube
kasusuwan shi, sai yaga kamar daya idar zai iya
farkawa daga mafarkin da yakeyi na dawowar
Yelwa. Kamar zai ga komai ba gaskiya bane ba,
da idanuwa Datti yake rokon Dije ta rike
Lubna sufyan
Hausabook.com 403
tambayoyinta, shima yana da tarin su, ta dan
basu lokaci zuciyar su ta gama gamsuwa da
cewa Yelwa ce a cikin gidan, Yelwa ce a tare
dasu, kafin wani abu ya sake biyo baya. Suna
zaune shiru kowa da magana a bakin shi amman
yana tsoron ya zamana wanda ya fara korar
shirun. A haka isha'i ta same su suka kuma
gabatar da ita.
"Ki zuba mana abinci muci"
Datti yayi maganar, Dije batayi musu ba, a waje
daya ta hado musu abinci, su duka sunayin
kamar basu kula da duk lomar da Yelwa zata kai
bakinta sai ta kai dayan hannunta ta share
hawayen da suka zubo mata ba. Hawayen da
Datti yakejin zafin su har a zuciyar shi, ko
dandanon abincin baya ganewa, hakama
Dije, sun kasa cire hannaye ne saboda Yelwa,
sai da ta fara cirewa tukunna. Suka wanke
hannuwa suka sha ruwa. Jin da Yelwa tayi
bayanta ya amsa yasa ta kiran sunan Allah
"Lafiya? Me ya faru? Baki da lafiya ne?"
Datti ya riga Dije tambaya. Maimakon amsa
wani irin kuka ne ya sake kwacewa Yelwa,
Lubna sufyan
Hausabook.com 404
kamar ta kwana biyu bata ji wani ya damu da
al'amarinta ba balle ya tambayeta me yake
faruwa da ita
"Ba ku tambayeni daga inda nake ba har yanzun
Baba... Daada baku tambayeni ba"
Kauda kai gefe Dije tayi kamar hakan zai hana
hawayen dake idanuwanta zubowa
"Ki huta Yelwa... Gobe duk sai muyi wannan
maganar... Ki huta yau, kije ki kwanta"
Kai Yelwa ta girgiza tana sake matsawa kusa da
Datti, kamar duk abinda zai sake rabata da shi
ba karamin shiri zaizo dashi ba kafin hakan ya
faru, gefen hijabinta ta saka tana goge fuskarta,
amman hawayenta sunki daina zuba. Shirun da
yake cikin gidan zai zaka iya tattara shi ka rufe
jikinka
"Da alamar hadari a garin nan, mu koma daki
kar ruwa ya sauko"
Dije ta fadi tana mikewa, hannun Datti ta kama
ta taimaka masa ya tashi tana kaishi har daki, ta
dawo ta mikama Yelwa da take kokarin tashi
itama hannu, bata ki ba, ta bari Dije ta taimaka
Lubna sufyan
Hausabook.com 405
mata ta mike, bata jira Dijen ba ta shiga dakin
da Datti ya shiga, a kasa ta zauna gefen gadon da
yake kai tana jingina kanta a jiki, wasu sababbin
hawayen na zubo mata. Dije sai da ta gama kayekayen da takeyi a tsakar gida saboda hadarin
kara haduwa yakeyi, taurari duk sun bace a
cikin shi. Ga iska na kadawa alamar kowanne
lokaci ruwa zai iya saukowa sannan ta shiga
dakin.
Shimfidar da tayiwa Datti ita ta samu waje ta
sakeyi a kasa ta kwanta, wata irin gajiya takeji
tana saukar mata, yawon da tunani da ruhinta
sukeyi ne tun batan Yelwa suka samu tsayawa
yanzun da suka sake kasancewa karkashin rufi
daya. Wata irin gajiya ce da bata da kalaman da
zatayi bayaninta balle ta iya fahimtar da wani. A
tsakanin yawon da tambayoyi suke mata cikin
kai wani irin bacci mai nauyin gaske ya dauketa
Baccin da bata san tashi daga shi zaiyi dai-dai da
tarar da duniyarta a birkice ba
Da tayi yaki dashi bata bari yayi galaba akanta
ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 406
Ba don wani ya fada mata cewar don an haifeta a
marake, ta girma, tayi aure anan zata kare
sauran ranakun ta a cikin kauyen ba. Kawai a
jikinta take jin cewa anan din za'a binneta wata
rana, ko da zata bar Marake sai dai tayi tafiyar
da sunan ziyara, ba wai bari na gabaki daya ba.
Duk wani abu da yake da muhimmanci a
wajenta a ganinta ya fara ne daga Marake, ya
fara daga tsatsonta. Ta gilashin motar take
kallon titi, take ganin bishiyoyin da suketa
wucewa suna kara tazarar da take tsakaninta da
Marake.
Shikenan? Da gaske tabar tsatson ta? Dalilai fiye
da daya sun hade waje daya, a cikin wannan
dalilan harda jinjirar da take rike a hannunta
tana bacci kamar a duniya kaf bata da wata
matsala. Sai take jin tsakanin juma'a da asabar
kamar wata rayuwar ce zuwa wata saboda nisan
da tazo mata dashi. Amman jiya ne, jiya ne
komai ya faru, a daren shekaranjiya daya
kasance na juma'a ne baccin da zata kira dana
asara yayi nasarar dauketa. Saboda ji tayi kamar
bata jima da rufe idanuwanta ba ta budesu da
saukar kalaman Yelwa
Lubna sufyan
Hausabook.com 407
"Na kashe shi Daada... Na kashe Baba... Inalillahi
wa ina ilaihi raji'un... Na kashe Baba Na!"
Tabbas ta mike zaune, ta kuma kama Yelwa da
take wani irin fitar da numfashi kamar tana
tsakanin rayuwa da wata duniya ta daban,
akwai hasken fitilar da ta fara dishewa alamun
batirinta yayi sanyi a cikin dakin, wani
numfashin da Yelwa ta sake fitarwa da damkar
da tayiwa Dije na tabbatar da ciwon nakuda ne
ya kama Yelwar.
"Babaa... Na kashe shi Daada... Na kashe Baaba"
Yelwa take fadi a tsakanin ciwon nakudar da
take yi, sai Dije ta saketa tana mikewa tsaye
gabaki daya zuwa kan gadon Datti, tun kafin ta
tabashi tasan babu rai a tare dashi. Abinda ya
saukar mata wannan karin yayi dai-dai da
ruwan daya sauko. Ya kuma yi dai-dai da wani
irin nishi da Yelwa tayi tare da dirowar 'yar da
bata dauki lokaci wajen sanar da dirowarta
duniya ba ta hanyar karade dakin da kuka. Idan
Dije tace ga inda ta samu karfin halin raba
idonta da gawar Datti ta dawo kan Yelwa da
bata taimakon da take bukata tayi karya. Kafin
Lubna sufyan
Hausabook.com 408
ta gama gyara wajen bayan ta samu ta yanke
cibi, ta kuma ajiye yarinyar kan shimfidar da ta
tashi. Ruwan ya fara tsagaitawa, cikin nuna
alamun asuba tayi. Dije kuma ta sami tabbacin
hakan da rangada kiran sallar farko da akayi.
Saita fita daga dakin zuwa dakin girkinsu, jinta
takeyi kamar ba ita ba, da yayyafin da akeyi ya
sauka jikinta ma sai ta dago hannayenta
karkashin duhun asuba, bata gane komai, bata
gane abinda yake faruwa da ita. Komai dai ya
kara canzawa, ciki harda bugun zuciyarta da
bata juyo alamar shi. Dakin girki ta shiga ta
hada wuta ta dora ruwa a tukunya ta dawo.
Saitayi tsaye, kuka jinjirar takeyi har lokacin,
amman Yelwa bata motsa daga inda ta haihu ba,
kamar ma bata motsi itama. Saita rasa wa zata
fara nufa. Yelwar dai ta sake tsintar kanta da
tunkara. Ta kamata ta dago da ita tana jijjigata
"Yelwa.... Yelwa"
Ta kira cikin wata irin murya, amman bata
motsa ba, sakinta tayi tana fita ta dibo ruwa ta
dawo tana sake dagota hadi da shafa mata
ruwan a fuska, sai da tayi hakan wajen sau
Lubna sufyan
Hausabook.com 409
hudu, tukunna Yelwar taja wani dogon numfashi
ta bude idanuwanta, ta kalli Dije, saita mayar ta
rufe tana mirginawa ta sauka daga jikin Daada
taja jikinta ta dunkule waje daya hadi da sakin
wani kuka da alamu suka nuna daga wani sashi
na zuciyarta yake fitowa, kamar bataso farkawa
ba, kuka takeyi kamar babu abinda ya rage mata
a duniya.
"Ki tashi Yelwa, ki karbeta ki shayar da ita ko
zatayi shiru"
Dije ta fadi, muryarta na komawa cikin
kunnuwanta da wani sauti da ta kasa fahimta.
Amman Yelwa bata ko nuna alamun motsawa
ba, sai da ta sake kamota, ko ina na jikinta bari
yakeyi
"Na kashe shi Daada... Na kashe shi.... Na kashe
shi"
Take fadi tana kara maimaitawa kamar karatu.
Kai kawai Dije ta iya dagawa tana taimaka mata
ta tashi zaune, ta saka mata yarinyar a
hannunta, sai tayi shiru, kamar ta gane inda aka
sakata, kamar tasan a jikin wadda ta kwanta
cikintane tsayin watanni. Sai dai daga yanda ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 410
riketa take bin muryar Dije akan ta shayar da ita
zaka gane duk tanayin hakan ne cikin fitar
hayyaci. Kamar rabi da rabi take cikin duniyar.
Sake fita Daada tayi tana zama dakin girkin,
kamar zazzabi takeji da kuma sanyi da ma wani
abu da bashi da suna duk a waje daya.
Ta kwashe ruwan ta dauka takai bayi ta dawo ta
kara zuba wani. Har taje ta karbi yarinyar daga
hannun Yelwa ta goyata ta kama Yelwar ta fito
da ita bata daina kuka tana maimaita
"Na kashe shi"
Ba, sai dai wannan karin kamar kanta take
fadawa maganar ba Daada ba. Tunda babu itace
da zani Daada tayi amfani taiwa Yelwa wanka,
tana tuna mata lokacin da tayi mata hakan fiye
da yanda za'a iya kirgawa a kuruciyarta, a jinyar
da tayi. Sai dai na yau ya sha bamban da sauran.
Kayanta ne ta daukowa Yelwa ta bata ta saka,
ganin kamar hankalinta yayi nisa da ita yasa
Dijen saka mata kayan da kanta. Jaririyar ta
yiwa wanka itama, tana tunanin abinda zata
saka mata a jikinta. Saita tuna ragowar kayan
Haidar da suke gidanta. Ta bayar da wasu da
Lubna sufyan
Hausabook.com 411
yawa, amman akwai sababbi wajen kala hudu
da tun na lokacin yana jariri ne da basuyi
amfani dasu ba. Watakila Mero ta adana ne, sai
kuma kaddara bata barta da zabin tsayawa
daukar su ba.
Su ta lalubo ta saka mata. Ta mika ma Yelwa da
take zaune ita tana daukar mayafinta ta lulluba
taje ta bude gidan tana fita tayi tsaye a bakin
kofar gidan tana rasa inda zata nufa kowa zata
fadawa, sai Abu ta fado mata a rai, safiyar data
shigo musu bayan rasuwar Hammadi. Mutuwar
ta kadata, sai dai yau ta gane babu abinda taji,
ba kuma ta fahimci komai ba, maraicin da take
ciki na sake danneta. Hakama rashin Abu a kusa
da ita, tana nan tsaye, yayyafin da akeyi na rage
karfi har maza suka fara dawowa daga masallaci
"Dije?"
Makocinsu ya kira cikin son tabbatar da ita din
ce
"Dije lafiya kuwa? Me yake faruwa ne? Ba dai
jikin Dattin bane ba ko?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 412
Da yake yasan bashi da lafiya, bai ganshi ba
kwana biyu yayi sallama, ya kuma shigo bayan
Datti ya bada izinin hakan. Sai taji harshenta
yayi nauyi, dakyar ta iya furta
"Ya rasu... Ya rasu ne"
Inalillahi wa ina ilaihi raji'un din daya furta na
dira kunnuwan ta, wani gashi da batasan da
zaman shi ba a wajaje mabanbanta a jikinta
yana mikewa
"Bari in fadama Audi sai aje a sanar da liman mu
taho tare"
Kai ta iya daga masa. Tana nan tsaye har suka
dawo suka sameta, sannan ta iya motsa
kafafuwanta tana binsu cikin gidan, ta kuma
nuna musu dakin da Datti yake a ciki. Tana kallo
suka shiga don su tabbatar da cewa ya rasun. Ita
ta mika musu ruwan da zasuyu amfani dashi
wajen yiwa Datti wankan shi na karshe. Tana
tsaye bakin kofar, sai dai kafin a gama hadashi
har mata na nan makota sun fara shigowa, su
suka kama Dije da batayi musu ba suka shiga
daki da ita. Idan da mamaki a fuskokin su ganin
Lubna sufyan
Hausabook.com 413
jaririya sabuwar haihuwa da take ta tsallara
kuka basu nuna ba.
Ba kuma suyi yunkurin hana Dije da ta dauketa
ta goya ba, tana samun waje ta zauna. Tun
yarinyar na kuka har tayi luf alamar tayi shiru
ko kuma bacci ya dauketa
"Ki fito kiyi masa addu'a..."
Za'a taimaka mata taji ta mike da kanta, har
dakin ta shiga, ta ganshi shimfide an hada shi.
Tsayin shi na kara fitowa kamar an jashi. Tana
tsinkayo muryar mutane, harda wanda zata iya
kira da abokan Datti na fadin
"A'a matar shi zatayi sallama da shi sai a fito da
gawar"
Tana kuma sake jin wasu sunata kiran "Gawa".
Sunan shi harya bace, wani abu da ya girmi
tsoro ya tsirga mata. Tsugunnawa tayi, kirjinta
kamar zai fado
"Kace zakayi son kai idan ka rokeni gafara Datti.
A iya zaman mu idan ka batamun na yafe maka,
Allah nake roko daya shafe kuskurenka ya yafe
Lubna sufyan
Hausabook.com 414
maka...nagode nima... Nagode da tarin kaunar
ka..."
Sauran kalaman sai suka makale mata, kallon
shi takeyi kamar takai hannu ta yaye likkafanin
ta sake ganin fuskar shi, sai dai ko da bata yaye
ba, zata rantse da Allah idanuwanta sun yaye
mata farin mayafin, fuskar shi take ganin tarau
kamar yana bacci. Sai ta mike, tana jin zaren
dake rike da sauran hankalinta na tare da yanda
zata ja numfashi ta fitar da sanin kowanne a ciki
yana kusantata da tarar da Datti. Basu kawo yau
da sauki ba, sun fuskanci kalubale mai tarin
yawa, akan auren su, a yaran da sukaita
binnewa, a yaran da suka rayu kaddararsu tazo
da nauyi. Sai dai zata zabi Datti, idan aka bata
dama zata sake zabar shi a matsayin mijinta. Ko
da kowa zai mata tambari da mahaukaciya, zata
sake zabar Datti iya adadin da dama zata bata.
Saida ta fito ta kalli liman da yake tsaya yana ce
mata
"Sai hakuri, kowanne mai rai mamaci ne, muma
duk lokaci muke jira... Allah ya jikan shi ya yafe
masa"
Lubna sufyan
Hausabook.com 415
Tana amsa shi da
"Julde na hanya, inda duk yake yana hanya. Don
Allah ku jira shi, da sassafe yake isowa. Yana
hanya duk inda yake"
Abinda duk suke fada baya karasawa
kunnuwanta, rokon su tayi da su jira Julde.
Kamar kuwa ta san yana hanyar. Duka alhamis
din tazo masa da wani irin yanayi, haka ya koma
gida daga kasuwa. Shisa ya biyewa Saratu sukai
tashin hankalin da ta kwana biyu tana nema
akan Nawfal. Yaran da baiga me ya tsare mata ta
dauki karan tsana ta dora masa ba. Sai dai daya
kwanta wasu mafarkai ya dingayi da suka kara
hargitsa shi. Yelwa ya gani a tsugunne tana
kallon filin wajen kamar tana jiran wani abu, ya
bude bakin shi ya kirata amman babu sautin da
yake fitowa. Bai san ya akayi yaga Datti ba, a
tsaye yake shi, idanuwan shi na kan Julden, a
maimakon Yelwa da yaga kamar tana jiran wani
abu, Datti na kallon shine kamar yana jiran shi.
Farkawar da yayi bai iya komawa bacci ba,
zuciyar shi bugawa takeyi kamar wani abu na
shirin faruwa dashi. Shisa tuki ne abu na farko
Lubna sufyan
Hausabook.com 416
daya koya bayan sun koma Kano, sannan
mallakar mota tashi ta kanshi. Ya godewa Allah
ya sake gode masa da wannan ni'imar lokacin
da bai saurari Saratu ba, ko wanka baiyi ba
karfe hudu na safe ya fita daga gida yana kamo
hanyar Marake. Ana ta yayyafi a wasu kauyukan.
Baiyi karfin da zai kasa ganin hanya ba, ji yake
tamkar Maraken ta kara masa wani irin nisa. Da
ya shiga cikin garin sai yaji bugun zuciyar shi ya
karu. Sai ma daya doshi gidansu yaga mutane a
kofar gidan, daga nesa ya ajiye motar ya kasheta
ya fito yana takowa da kafafuwan shi cikin
hanzari.
"Sannu Julde... Sannu kaji"
Wani a cikin taron mutanen ya fadi
"Datti lokaci yayi"
Kalamai uku, kalaman da ba zai taba mantawa
dasu ba, lokacin da zuciyar shi tayo kundunbala
daga cikin kirjin shi tana gangarawa cikin gidan,
ya kuwa bita, bata tsaya ko ina ba sai a bakin
gawar Datti da aka fito da ita tsakar gidan. Ya ji
gwiwoyin shi a kasa, bai dai fahimci ko rarrafe
yayi ya karasa ba. Ya kuma dora kanshi a jikin
Lubna sufyan
Hausabook.com 417
gawar Datti yana jin wani abu na rushewa a tare
dashi
"Yanda ka kunyata ni Julde... Allah ya kunyata
ka a idanuwan mutanen da suka fi komai
muhimmanci a wajenka..."
Kalaman Datti da sune na karshe a tsakanin su
suka dawo masa, suna jijjiga zuciyar shi daga
inda take tana komawa kirjin shi ta zauna da
wani irin karfi. Mikewa yayi yana ratsa duk
matan nan harya tarar da Dije ya kamota yana
fito da ita daga dakin
"Daada bai yafe mun ba, Baba bai janye kalaman
shi a kaina ba... Ya tafi bai yafe mun ba"
Kallon shi Dije takeyi, sai take jin wani abu na
bude mata, kamar ganin Julden na fisgota daga
duniyar fitar hayyacin da ta shiga ne, kamar
yanzun zata dawo ta fuskanci komai
"Ka taho a kama, gawa bata jira fa"
Wani ya fadi, da sabon firgici a fuskar Julde yake
kallon Dije
"Kaje... Kaje ka dawo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 418
Ta iya fadi, idanuwanta sun kankance duk da
babu digon hawaye ko daya a cikinsu. Juyawar
kuwa yayi, tana kallo suka daga munkarar da
Datti yake ciki suka fita dashi daga gidan, suna
tafiya tare da wani sashi mai girma na zuciyarta.
Ta lumshe idanuwanta, kirjinta kamar an hura
wuta a ciki. Bata sake saka Julde a idanuwanta
ba sai dare, bayan mutane duk sun tafi, sai yan
uwanta da suke uba daya, saboda wanda suke
uwa daya matan ba'a cikin marake suke aure ba,
da alama kuma labarin rasuwar bai karasa
musu ba.
"Daada..."
Taji muryar shi, sai ta fita ta same shi yana
tsaye. Kallon shi takeyi
"Daada da gaske Yelwa ta dawo?"
Kai ta daga masa, kiran Yelwa da yayi na bude
wani sashi daya toshe a cikin kanta
"Banganta ba, tun da dafe banganta ba, sai
yarinyar"
Numfashi Julde yaja ya fitar, abinda yaji ana fada
a waje da gaske ne kenan. Anga Yelwa ta shigo
Lubna sufyan
Hausabook.com 419
garin da tsohon ciki, ance ma ta haihu, jinjirar
ko jinjirin ne goye a bayan Dije. A wajen zaman
makokin da Julde baiga amfanin shi ba, saboda
ana dawowa aka fara fito da kokon da baisan
wake da karfin halin sheka shi a yanayin da
suke ciki ba. Hawayen dake ta masa barazana
yake dannewa, saboda yanajin shi da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 27