kudirinta ya
girgiza. Idan ta shigo ta samu rabo ta kore ta,
sanadi kawai zata zama, amman tasan akwai
hakan a kundin kaddararta, akwai rabuwa da
Hammadi, ko da matar da zai aura bata zama
sanadi ba kuwa. Tun shi Hammadin da zai kara
auren yana gujema maganar har nacin Abu yasa
shi karbar hakan. Sai gashi ana masa tayin aure
a cikin garin Marake kamar bashi da wani laluri
na rashin haihuwa. Kwadayin su bayyane a kan
fuskokin su tun kafin ma su furta masa bukatar
su.
Shisa duk yayi watsi da su, ya cigaba da dubawa
Lubna sufyan
Hausabook.com 102
"Bana so in auro wadda zata cutar damu
Abu...ina addu'a kar muyi dana sanin auren nan"
Amman yanayin ta na kara masa karfin gwiwa,
sadaka tunda ya aminta da batun auren duk
rana sai yayi tunda yaji wani Malami daya
ziyarci kauyen nasu yana cewa tana kare
masifu. Cikin ikon Allah ya sauke idanuwan shi
akan Pendo, sai yaji zuciyar shi ta natsu, duk da
yaje neman auren ta wajen Mahaifin ta da sanin
cewa zai iya hana shi, bai hana ba. Daga baya
yaji cewa mahaifiyar Pendo bata so auren ba
saboda rashin haihuwar shi, amman Pendo ta
kafe cewar ita Hammadi yayi mata. Ba'a wani
bata lokaci ba tunda kudi ba matsala bane aka
gama shirya komai.
A cikin gidan shi ya kara gyara dakuna biyu da
zasu kasance na Pendo. Abu bata san haka kishi
yake ba, bata kuma san wata yaudara da cewar
ta shirya ganin Hammadi da wata ba, sai da taga
ana shigowa da kayan Pendo da jerin mutanen
da suke rangada guda da wake-waken murna
irin nasu na Fulani, har wata nama Pendo lakabi
da
Lubna sufyan
Hausabook.com 103
"Amaryar Hammadi, uwar 'ya'yan shi"
Zuciyarta ta tsinke kamar kunun kanwar daya
sha sukari, ruwan ya zubo ta cikin idanuwan ta
a matsayin hawaye. Hawayen da har bayan
kawo Pendo bai tsaya ba, hawayen da ta kasa
boyema Hammadi daya shigo dakin ya zauna
gefen gadon ta kusa da ita
"Dan Allah ki daina kukan nan Abu, kinga baki
da isasshiyar lafiya, kiyi hakuri ki daina kukan
nan kar ya saka miki wani ciwon"
Habar zaninta ta kama tana goge idanuwanta da
suka rine saboda kuka, wanne ciwo kuma? Har
akwai wani ciwo da zata ji fiye da wanda take
ciki a lokacin? Sai ace zafin rashin iyayi yasha
bamban da kowanne, bata karyata ba, amman
ba layin su daya da zafin kishi ba, sam ba wajen
su daya ba. A gurin 'ya mace zafi na kishi kalar
shi daban ne, har abada bashi da abokin
kwatance. Duk tausasan kalaman Hammadi sun
rushe lokacin da taga ya mike yayi mata
bankwana, wani abu da bai taba faruwa ba tun
farkon auren su, sai dai idan basa cikin gida
daya.
Lubna sufyan
Hausabook.com 104
Wannan daren, wannan daren da ba zata taba
mantawa ba, yanda taga ranar shi haka ya wuce
yana zo mata da wayewar gari mai cike sa sabon
lamari. Da fari zama suke da Pendo na lumana
da girmama juna, kafin ma ta yunkura da sunan
wani aiki Pendon ta rigata, idan ba Dije ta shigo
ba, kusan komai tare sukeyi ranar girkinta da
ranar girkin Pendon. Shima Dijen ce yanda duk
Abu ta so ta sakema Pendo ta kasa, bata taba
ganin Dije taki jinin wani babu dalili mai karfi
ba sai akan Pendo. Itama Pendon ta kula, duk in
Dije ta shigo bayan gaisuwa bata sake bi
takanta.
Sai Abu ta hakura ta kyale Dije, musamman
yanzun da itama take cikin tata matsalar ga
daban akan Bukar. Canji ne dai Abu bata daina
jin shi a tare da ita ba, wannan zazzabin na duk
dare kamar anyi ruwan shi an dauke, sai kace
bata tabayin ciwo ba, har jikinta ta fara
mayarwa, fatarta ta murje ta kara haske, har
Hammadi saida ya zolaye ta
"Amarya ce ta goga mun kyallin ta"
Lubna sufyan
Hausabook.com 105
Tace masa tana dariya, tana jin dadin yanda ko
na dakika daya bata taba ganin wani sauyi a tare
da shi don ya kara auren nan ba. Har lokacin da
Pendo ta cika watanni biyu da wasu yan
kwanaki, lokacin da ta fara wani ciwo da duk
alamun shi suka nuna cewa ciki ne da ita. Abu
tayi mata murna, tayi ma Hammadi murna. Ta
kuma shiga daki tayi kuka, kukan daya fito daga
wani lungu na zuciyar ta da ya tabbatar mata da
matsalar rashin haihuwar su ba daga Hammadi
bane itace, tagani, kuma haka kowa zai gani.
Cikin kasa da sati daya maganar ta gewaye garin
tsaf, dangin Pendo kuma suka matsa ma
Hammadi akan suna so ta koma gida ta reni
cikinta har sai yayi kwari tukunna. Da yake ba
mai son hayaniya bane saiya amince musu,
ranar da suka zo daukarta haka sukaita yarda
maganganu, Abu ko fitowa daga daki batayi ba
gudun fitina, ta kuma hana Dije da jikinta ke ciri
jin irin maganganun da sukeyi, har wata na
cewa ai gara su dauketa kafin Abu ta kassara
musu yarinya da abinda ke cikinta. Kamar duk
garin basu san cewa inda Abu bata amince ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 106
Hammadi ba zai taba kallon Pendo da zancen
aure ba.
Yanzun ma auren nata zai iya girgiza idan yaji
gorin da suke yima Abu. Ai kam bayan sun tafi
Dije mikewa tayi tana share hawayen takaici
tabar Abu da ta kwanta kan gado wani abu na
konewa a cikin kirjinta. Abinda ta danne bata
bari Hammadi da yake ta binta da kallo ya gani
ba, baice mata komai ba, amman zuciyar shi a
bayyane take cikin idanuwan shi, tausayinta ya
hana shi murnar cikin Pendo, sai taji soyayyar
shi ta karu a zuciyar ta. Har tana sakata kokarin
maida komai ba komai bane ta kuma cigaba da
hakuri da kaddarar ta kamar yanda ta saba a
tsayin shekarun nan.
Sai dai me, Abu bata da tumbi, tana cikin siraran
matan nan da cikin su yake hade da marar su,
yanzun kuwa gani take yana kumburowa kamar
ana hura mata shi, ba ita kadai ta kula ba. Har
Hammadi saida yayi magana, sannan Dije,
sannan duk wani da zata hadu da shi, kamar
wasa har motsi-motsi taji wani dare, bata iya
komawa bacci ba saboda firgici, gani take kamar
Lubna sufyan
Hausabook.com 107
wata cutar ce ta kamata. Ranar da taje gidan su
ne, Inna ta kalle ta sosai tace
"Abu cikine a jikin ki"
Maganar da ta girgiza duniyar da take tsaye kai
tana matukar kadata har tana rasa bakin
musantawa, ciki, akwai ciki a jikinta tabbas,
amman kamar cikin da Innar take nufi daban ne
da wanda ta sani. A ranar zance yayi zance,
lissafin da Abu ta dainayi na ganin al'adarta ya
tashi yana bayyana watanni har biyar, yana
kuma shafe mamakin rashin bayyanar cikin
saboda na fari ne, idan da tana da jiki ma sai
anyi da gaske za'a kula in dai ta batun girman
cikine. Ko a mafarki bata hango ba balle kuma
faruwar shi a gaske. Shikenan? Rana daya Allah
ya wanke mata gorin juya. Da fari taki yarda, ta
mike, ta koma ta zauna tana tuna yanda babu
wani abu da yafi karfin Allah.
Kuka kuwa na murna babu wani makusanci na
Abu da bai tayata da shi ba. Hammadi kuwa
hannuwa ya dora kan cikin nata yana kasa cewa
komai, a durkushe yake amman ya kasa dagowa,
sai da ta dora nata hannayen kan nashi tukunna,
Lubna sufyan
Hausabook.com 108
hawaye yake, hawayen da bai san yanda akayi
suka fara fitowa ba ballantana ya iya tsayar da
su, hawayen shi da suka bude mata kofar nata
"Abu kinga ikon Allah ko? Kinga munyi garaje?
Munyi gaggawa, da mun hakura..."
Kai take girgiza masa, ba suyi garaje ba, har
kasan ranta take jin auren Pendo da Hammadi
babu garaje a cikin shi, ba kuma kuskure bane
ba. Kallon shi tayi da wani yanayi cikin
idanuwanta
"Ka godema Allah kawai Hammadi Am, mu
godewa Allah da tarin ni'imomin da yayi mana...
Kar muce komai banda godiya"
Kai kuwa ya daga mata, murnar da tayi ba zata
misaltu ba, godiyar ta ga mahaliccinta zata
cigaba dayi tana karawa har tsayawar
numfashin ta, sai dai akwai wani sanyi da
zuciyarta tayi, sanyin da take ji har cikin
kasusuwan ta. Shisa murnar da kowa yake
tayata da murmushi take amsawa. Da yake
labari baya boyuwa, sati bata cika ba aka dawo
da Pendo, dariya ma suka bata, maganganu dai
basu gaji ba, ta kula a jinin dangin Pendon yake.
Lubna sufyan
Hausabook.com 109
"Dan Allah kiyi hakuri da abubuwan da yan
uwana suke ta fada...nayi miki murna har
raina... Allah ya sauke ki lafiya"
Pendo tace mata bayan kowa ya watse ta shiga
tayi mata barka da dawowa. Murmushinta ta
fadada
"Babu komai Pendo, Allah ya sauke mu lafiya
zakici"
Murmushi Pendo tayi a kunyace tana kasa
amsawa, babu komai a tsakanin ta da Abu sai
alkhairi, karamcin matar daban ne. Zama suka
cigaba dayi na aminci har cikin Abu ya cika wata
bakwai, tana zaune tana tukin tuwon da Pendo
take tsaye a kanta saboda taki tashi tabari ta
tuka, taji bayanta ya amsa, amsawa da zata
rantse kashin daya fara daga wuyanta zuwa
kugunta ne ya karye, kafin ta kira sunan Allah
ya sake karyewa a karo na biyu a waje daya,
wannan karin yana hadawa da wasu kasusuwa
cikin mararta da batasan akwai su ba, suma
karyewar taji sunayi.
Pendo ta taimaka mata ta mike tana kiran duk
wani sunan Allah da yazo bakinta ko zata samu
Lubna sufyan
Hausabook.com 110
sauki, har suka karasa daki Pendo na mata
sannu, amman can nesa take jiyo muryar Pendo
kamar basa daki daya saboda ciwo. A daddafe
Pendo ta karasa tukin tana sake leka ta, amman
ciwo kamar gaba yakeyi, ta katangar ta kwala
ma Dije kira ta zagayo. Abu kamar wasa, nakuda
ce ta taho ma Dije gabaki daya, Pendo ce ta saka
mayafinta tana ficewa, dan aike ta samu aka
aikama Hammadi da harda gudu ya hada yana
ganin nisan da gidan shi yayi da gonar.
Zuciyar shi a cikin tafukan kafafun shi lokacin
daya shiga gidan, ya samu cikin yan uwan Abu
mutum biyu sun zo, kasa ce musu komai yayi,
gaisuwar su ma bayajin ya amsa, wani gunjin
ciwo ya juyo daga cikin dakin da yasan daga
Abun shine, gunjin da yasa shi zabura kamar
zaiyi cikin dakin ya rabata da abinda yake
azabtar da ita haka. Dole ya fita daga gidan kar
suga hawayen shi, tsaye yayi a kofar gida, anan
Datti yazo ya same shi, suka tsaya suna jiran
ikon Allah. Har akayo Magriba aka dawo babu
wani canji, gabannin isha'i ta haifo danta da ya
fado babu rai.
Lubna sufyan
Hausabook.com 111
Tun kafin su fada mata taji a jikinta, sanyin da
zuciyarta yayi randa tasan da cikin yasa ta fara
shirya ma zuciyarta karbar kowacce kaddara
tazo mata, saiya zamana dacin da taji takaitacce
ne, tana maye gurbin shi da hamdala, ko yau
mata suke zancen nakuda tana da labarin
bayarwa, ko yau ake zancen haihuwa babu
wanda zai kalleta ya wareta. Idan kyautar iya
haka ta tsaya ta gode, ta kara godewa. Da ta rike
yaron ma addu'a tayi masa, tana kara godema
Allah kafin ta mika musu shi. Aka taimaka mata
ta mike don ta gyara jikinta.
Hammadi ne ya kasa tsaida hawayen shi, a karo
na farko ya dandani abinda Datti yaji, tausayin
Abu na cika zuciyar shi fal, kima ta 'ya mace da
darajar ta na daguwa a idanuwan shi. Haka aka
suturta ta gawar akaje aka binne ta. Ko Pendo
sai da tayi kuka har ya zamana Abu ce take
lallashin ta. Gani take itama abinda yake cikinta
kamar ba rayayye bane ba. Danginta nata hauka
da yarda maganganu, idan kuma dakon gawa
takeyi fa? Kowa mamakin karfin hali irin na Abu
sukeyi, ita kuma mamakin yanda suka karkata
Lubna sufyan
Hausabook.com 112
hankulan su kaf akan rashin da tayi, suka kasa
ganin girman kyautar da Allah yayi mata.
"Bansan me zance miki ba... Na rasa me zance
Abu"
Hammadi ya fadi bayan sun samu kebewa da
juna, murmushi tayi
"Ba sai kace komai ba, ka kara tayani godewa
Allah, hakan kawai ya wadatar"
Numfashi Hammadi ya sauke, kallon ta kawai
yake yana jinjina ma karfin zuciya irin tata. Har
zancen sai da Pendo tayi masa
"Anya akwai irin Adda Abu kuwa? Gaskiya kaf
Marake ban taba ko jin labarin irin ta ba"
Dariyar alfahari yayi, Abu, Abun shi kenan.
*
Duk wata kulawa Pendo na samu daga wajen
Abu har cikinta ya shiga watan haihuwa, inda
aka sake daukarta zuwa gidan da zata haihu
kuma tayi wanka acan. Yanda Abu taji gidan yayi
mata shiru duk sai kewar Pendon ta addabe ta,
kaji motsin mutum ma wani abu ne, musamman
Lubna sufyan
Hausabook.com 113
yanda suke zaman lafiya. Da hakane har a wajen
yan uwan Pendo da taje gida duba ta, to Dije ta
fara mata maganar
"Dan Allah Adda karki ce zakije gidan su Pendo,
kin san ba mutunci gare su ba...suna iya yaba
miki bakaken maganganu"
Ko da Dijen batayi magana bama ba zataje ba,
takan dai tambayi Hammadi, kuma tana cewa ta
gaishe da ita, duk da shi da bakin shi bai taba ce
mata yaje wajen Pendo ko kuma zaije ba. Ta san
ba zai rasa zuwa ya duba su ta ba. Ranar talata
labari yazo ma Abu cewar Pendo na nakuda,
kamar tayi tsuntsuwa taje haka ta dinga ji, sai
dai bata wani dauki lokaci ba, tunda duka
gabannin azahar ne, kafin la'asar ta haifi yarta
mace, Hammadi da kanshi yazo yana fada mata,
saida ta rungume shi don murna. Su duka biyun
sun kasa daina fara'a.
Tare suka koma gidan su Pendo, bata damu da
kallon da aketa mata da maganganu kasa-kasa
ba, kishine suke taya Pendo, bai kuma dameta
ba. Musamman yanda Pendo ta wanke mata
Lubna sufyan
Hausabook.com 114
zuciya da murmushin daya nuna najin dadin
ganinta ne
"Adda Abu nayi kewarki, baki zo kin ganni ba,
yau dinma bani kika zo gani ba"
Dariya Abu tayi, yarinya ce basu bata ba, tana
goye bayan wata kakar Pendo akace wanka
akayi mata tana bacci, ba'a so ana yawan sauke
jinjira haka. Murmushi tayi tana amsawa da
"Allah ya raya mana cikin aminci"
Tayi musu sallama tare da yima Pendo
alkawarin zata dawo ta sake duba su, har takai
kofa ta juyo muryar Pendo
"Adda Abu..."
Juyawa tayi, murmushi Pendo tayi mata
"Nagode da dukkan karamcin ki, nagode"
Kai kawai ta daga mata, da ta san cewar wannan
ce rana ta karshe da zata saka Pendo a
idanuwanta da ta tsaya sun kara hira, da ta
tsaya ko ba zasuyi hira ba tayi ta kallon ta, ta
kara daukar wasu hotuna na Pendon da zata
adana tana dawo dasu tamkar tarihin da Pendo
Lubna sufyan
Hausabook.com 115
ta zama a safiyar sunan 'yarta da ta tashi da
wani irin ciwon ciki. 'Yar da dangin Pendo sun
san cewa kulawar ta zata koma karkashin Abu
ne gabaki daya da basu hanata daukarta a ranar
da aka haifeta ba.
Sai dai wasu kaddarorin sun fi gaban hasashe
Wannan shine tunanin Abu lokacin da take rike
da yarinyar da taci suna Saratu, hawaye fal a
idanuwanta
Kaddara
Kowanne rai da irin tashi
***
Dalilan da suka hanata yi ma maza kudin goro
akan cewa basu da adalci, zuciyoyin da suke
kirjin su bangaren tausayi na wasu da yawa a
mace yake kadan ne, mahaifinta baya cikin
wannan dalilan, saboda shima ya kalle ta yace
"Ki dauki Bukar ki mayar da shi gidan mahaifin
shi Dije, shine kwanciyar hankalin ki, shine
kuma rufin asirin shi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 116
Kasa cewa komai tayi, ta dai daga ido, ta kuma
kalli Baba, ta kalle shi da idanuwan da bata taba
kallon shi da su ba, ta kalle shi a ranar ba'a
matsayin mahaifinta ba, zuciya ta uwa tasa ta
kalle shi ta kuma saka shi a jerin mutane
marassa tausayi, mutanen da suka kasa duba
halin tagayyarar da rayuwar Bukar zata shiga
idan ta dauke shi ta mayar gidan Baabuga. Kowa
ya manta yanda da wahala ka fita baka ci karo
da daya a cikin yaran Baabuga sun gantali akan
hanya ba, yar makarantar allon da ake kokarin
saka yara a kauyen ma su basa cikin wannan
tsarin.
A cikin dalilan ta nakin yiwa maza kudin goro
Hammadi yana cikin su, Hammadi daya fita
daban da sauran mazan da rayuwa ta hada
hanyarta da su. Saboda har cikin zuciyarta tana
da yakinin Hammadi ba zaiki rikema Abu dan da
ta samu batare da shi ba, ko da yafi daya kuwa.
"Ba zan rike dan Baabuga ba, ba zan rike ba
wallahi. Karki fara kawo mun shi cikin gidana,
idan ba zaki mayar masa da shi ba kisan inda
zaki ajiye shi, amman ba cikin gidana ba..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 117
Sune kalaman Datti, kalaman da baiyi kokarin
tausasawa ba, iya gaskiyar shi ce ya fada mata
tasani, amman kai tsaye haka? Ba ana sakaya
wata gaskiyar ba? Ana mata lullubi da bargo mai
taushi yanda in aka jefa dukanta zai isa da sauki
"Dan Allah... Kar ka duba Baabuga, karka duba
Bukar din ma, ka dubani, ka duba halin da
zuciyata take ciki...karkayi saurin yanke
hukunci haka, Bukar ba mai rikici bane ba, zai
zauna cikin gidan nan kamar baya nan"
Tayi maganar cike da roko, zuciyarta a
cunkushe, idanuwanta a cike da hawayen da tun
ranar da aka fara mata magana kan ta mayar da
Bukar gidan mahaifin shi suka soma zuba, ba su
kuma yanke mata ba
"Sai dai zan gan shi...idan na shigo gidana zan
gan shi, zai tuna mun daren da kikace mun shi
kadaine daren da kika rabamun kanki da
Baabuga... Daren dana tsana, Baabuga dana
tsana Dije, abinda daren ya haifar da bana son
ko ji balle in tashi in gani a duk rana... Dan
Allah... Dan Allah karki sake mun maganar
nan..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 118
Yanda ya karasa maganar cikin roko yasa ta
mike tabar masa wajen a wancen lokacin. Ta
kuma turo kofar dakinta harta saka sakata
abinda bata tabayi ba. Babu kalar abinda bata
saka a cikin ranta ba, warwarewar dai ce ta
gagara. Musamman da taga da gaske Datti yake
ba zai rike mata Bukar din ta ba
"Zanma Hamma magana in za'a kai masa
dabbobi a hadamun da guda daya, ya bani kudin
in rike yarona da su"
Lomar tuwon da Datti yakai bakin shi ya tauna,
yanajin ta wuce ta cikin makoshin shi, zafin na
ratsawa ta duk lokon da tuwon ya wuce kafin ya
saukar masa a ciki da wani irin nauyi, kallon ta
yayi, babu alamar wasa a fuskarta, asalima
yanda ta hade girar sama da ta kasa ya nuna
cewa ba shawara tazo suyi ba, gaya masa takeyi,
kawo mata wani zancen kuma zaiyi dai-dai da
neman sabuwar rigimar da bai shirya ma ba. Bai
taba sanin Dije ta iya rigima ba, ko zata iya
kallen idanuwan shi ta mayar masa da magana
haka sai akan Bukar din nan.
Lubna sufyan
Hausabook.com 119
Bukar da ya tsana har kasan ran shi, Bukar da
ko sama da kasa zata hade waje daya ba zai
zauna masa a gida ba.
"Madalla..."
Ya amsa yana cigaba da cin tuwon shi, ta kasan
idanuwa yaga ta mike sannan ya daga kai ya bita
da kallo. Daki ta shige ta turo tana saka sakata.
Murmushi ya tsinci kan shi dayi, in dai akan
maganar Bukar ne ba zai taba biye mata ba, duk
da fushin da ta dauka bashi kadai ya shafa ba, ya
kula harda Julde, hanya daya da tasan tana da
ita da zata iya bakanta masa rai, yanda duk taso
ba zai bari hakan ya faru ba. Shisa idan ya dawo
saiya biya ta gidan Hammadi ya ganshi ya dawo,
can yake barin shi yanzun, saiya dauko shi ya
dawo da shine zatayi abinda zaisa dole ya biye
mata.
Da safe ma saida ya gama shiri zai fita, ya shiga
dakinta don yayi mata sallamar da bata ko daga
kai ta kalle shi ba, ya juya ya tsinkayo muryarta
"Zanje gida"
Lubna sufyan
Hausabook.com 120
Labulen ya saki bai amsata ba, yasan me yaji
lokacin daya rabu da ita, kuskure ne da yayi sau
daya, kuskure ne da zai karasa sauran rayuwar
shi yana kokarin ganin bai maimaita ba, shisa ya
fice batare da yace mata komai ba kafin wata
zuciyar tace masa ya nuna mata yana da iko a
kanta, ya hanata yaga abinda zai faru.
"Sai mutane su dauka ni da Abu bama fada, babu
wani zama da za'ace ba'a samun sabani Datti,
yau da gobe tafi karfin wasa. A zaman aure sai
ana kauda kai, sai kuma ana hakuri, idan kaga
yayi karqo to dole akwai wanda akafi cutama,
dole akwai wanda akafi tauyewa, dole daya na
hakuri da daya fiye da yanda dayan yakeyi,
bansan me yasa tsarin ya kasance haka ba,
amman hakanne, kuma muma haka za mu
cigaba da gudanar da zamantakewar...gata nan,
zama ya sake hadaku a karo na biyu, a naku
zaman ko ba'a fada ba ansan wa yafi hakuri da
wani, kaima saika kai zuciyarka nesa a lokuttan
da ka kure hakurin ta"
Zantukan Hammadi ya dauka anan inda yayi
masa su yabar su kamar ko da yaushe idan ya
samu sabani da wani, Hammadi ya tsaya yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 121
masa nasiha akan zamantakewa da mutane da
kuma amfanin hakuri harma da yawan kauda
kai. Saboda yasan baida wannan zuciyar, hakuri
ba halin shi bane ba. Sai a yan kwanakin nan da
Dije take saka kara tana zungurin duk wani abu
da tasan zai hassala zuciyar shi amman ya
kauda kai, duk da yana saukewa akan duk
wanda ya gifta masa a waje. Hakan ne ma yasa
Hammadi yi masa magana
"Da bacin ranka kake zuwa Datti, idan zaka
dinga hucewa akan wanda basu san hawa ba
basu san sauka ba, ka daina zuwa har saika
warware matsalar ka da matar ka"
Numfasawa yayi
"Saina rike mata yaro, akan naki rike mata yaro
ne take ta tashin hankali"
Ya fadama Hammadi din tunda boyewar bata da
amfani
"Bukar?"
Hammadi ya tambaya, kai ya daga masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 122
"To menene dan ka rike shi? Taimaka mata
zakayi, kuma shima yaron inka duba gidan
Baabuga zaka taimaka masa"
Kai yake girgizawa tunda Hammadi ya fara
magana
"Wallahi ba zan rike wannan dan iskan yaron
ba"
Kallon shi Hammadi yayi yana kada kai kawai
hadi da fadin
"Allah ya rufa asiri"
Tunda yasan hali, abinda duk zai dora bayan
wannan kamar zai kara tunzura Dattin ne.
Akwai lokuttan da shiru shine mafi alkhairi,
komin yanda kake ganin kusancin ka da mutum
kuwa. Hidimar shi ta ranar Hammadi ya cigaba
da gudanarwa, yana jin masifa da tijarar da
Datti yake yiwa mutane. A gefe daya Dije
shiryawa tayi, ko ta gidan Abu bata biya ba,
saboda itama ta kara mata takaicin da take ciki
da kafewar da tayi akan Hammadi ya karo aure.
Tana zaune da mijinta lafiya, bai daga hankalin
Lubna sufyan
Hausabook.com 123
shi akan halin rashin haihuwar su ba, ita ta daga
nata.
Ko tsoron wata tazo ta haihu da Hammadi ta
koreta daga gidan batayi. Idan akayi magana sai
tayi murmushi, murmushin nan da Dije take jin
zafin shi har ranta, kamar Abu tana son fada
musu tasan wani abu da su basu sani ba, tana
hangen abinda kome zasu taka ba zasu taba
ganin shi ba. Har ta shiga gidan su zuciyarta a
cunkushe take, ta daiji dadin ganin Baba bai fita
ba, a cewar Innarta yayi ciwon ciki da dare,
saiya tashi bayajin karfin jikin shi, shisa da ta
same shi bayan sun gaisa ya jiki ta fara yi masa
ya amsa sannan ta dora da
"Akan Bukar ne daman Baba...ni ba zan mayar
da shi gidan Baabuga ba, zanma Hamma magana
yau akama Dabbata a siyar sai in kawo kudin
nan a ajiye a dinga masa hidima a cikin su kafin
muga abinda Allah zaiyi"
Numfashin da Baba ya sauke na korar shirun
daya biyo bayan maganar da tayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 124
"Dije kina tunanin ba nida abinda zan rike
Bukar dashi ne? Shisa nace ki mayar da shi
gidan mahaifin shi?"
Kanta ta sake saddawa kasa saboda bata so yaga
hawayen da suke cike da idanuwanta
"Nace ki mayar dashi ne badan ba zan iya rike
shi ba, sai dan shine abinda ya kamata. Iya gatan
da za'ayi ma rayuwar shi kenan"
Mikewa tayi, hawayenta na zuba, Baba bai
hanata ba, ko da ya hanata bata jin zata iya
tsayawa saboda ko ganin hanya batayi sosai,
hawaye sun mata duhu bayan wanda ya lullube
zuciyarta. Bata bi takan Innar A'i dake mata
magana ba ta sa kai tana ficewa daga gidan
gabaki daya, bata ganin komai sai Bukar da ta
baro kwance dakin Innarta yana bacci, yanzun
sai taga kamar yana baccin ne a nutse sanin ba
zata taba barin komai ya same shi ba. Amman
ina, duk wani kokari da takeyi na ganin ta kare
shin nema yake ya subuce mata.
Gidan Hammadi ta shiga, kuka na kwace mata
tana hada ido da Abu
Lubna sufyan
Hausabook.com 125
"Adda ba zan iya gani sun maida shi gidan nan
ba, wallahi zuciyata ba zata dauka ba...baki
ganshi yau yana kwance ba, kamar duka basu
duba kankantar Bukar, mutuwa zaiyi a gidan
Baabuga, mutuwa zaiyi a irin wannan rayuwar
da sukeyi"
Riketa Abu tayi tana jin zuciyarta na karyewa,
maza akwai ikirarin soyayyar 'ya'ya, a baki zaka
dinga jin ikon su, a wajen jama'a zakaji alfaharin
da sukeyi, musamman idan wannan yaron ya
taka wani mataki ne na nasara
"Dana"
Haka zaka ji su
"Yata ce, yar waje na ce"
Bata dandani zafi na haihuwa ba, amman a
tsakanin laulayi, a cikin fitowar rana da
faduwarta, tana tare da Dije, lokutta
mabanbanta, hannunta yana rike dana Dije a
yayin nakuda, yaran da basu ma zauna ba, a
haihuwar Dije ta uku, a irin wannan wahalar da
taga ta sha saida wani sashi na zuciyar ta ya
numfasa cikin jin dadin yanda jikinta bai taba
Lubna sufyan
Hausabook.com 126
dandana irin wannan wahalar ba. Sai lokaci
daya namiji ya kalli mace yace mata ba zai rike
mata danta ba saboda ba nashi bane ba, ba zai
rike ba saboda baiga wani dalili da zaisa ya rike
ba. Tunda suka fara wannan maganar Abu take
jin kamar ta kama Datti ta girgiza shi.
"Laulayin da ta sha kadai dalili ne, nakudar da
tayi kadai dalili ce"
Haka take so ta fada masa, idan bashida halin
rikewa Bukar zata iya fahimta, duk da har abada
ba zata fahimci kowanne irin dalili da zai raba
uwa da yaranta ba, idan tace kowanne dalili
tana nufin kowanne iri. Me yasa namiji zai auro
mace kuma ta rike masa nashi yaran? Me yasa?
Sai ace shi ba zai rike mata nata ba saboda basu
fito daga jikin shi ba, amman shi ta rike nashi da
basu fito daga nata jikin ba.
"Nayi magana da Inna, tace ko da za'a maida
Bukar din ba yanzun ba, yayi kankanta tunda ko
shekaru biyu bai cika ba, a barshi ya kara ko da
shekara ce nan gaba... Kafin nan mun samu
mafita da yardar Allah"
Lubna sufyan
Hausabook.com 127
Abu ta fadi a tausashe, amman kukan da Dije
takeyi yaki tsayawa, saboda jikinta ya fara
sanyi, zuciyarta ta fara karaya, ji takeyi kamar
an dauki Bukar an mikawa Baabuga ne, abinda
zaiyi dai-dai da tagayyararsu gabaki daya. Tayi
kuka har zazzabi ya rufeta, dakyar Abu ta samu
tayi shiru, anan gidan tayi azahar, sukaci abinci
tare da Abun ta kuma kwanta ana. Abu tace
mata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 27