akan Bukar, akan dan
Lubna sufyan
Hausabook.com 153
Baabuga, ita dinma a wa take? Ko igiyar data
kulle su tare take ganin harta isa ta dinga gaya
masa magana haka, duk fadin Marake da
kewayenta babu wanda ya isa, ko Hammadi ba
zai dinga kallon shi yana datsa masa maganganu
irin haka ba, ko dauka tayi kamar inya rabu da
ita karshen duniyar shine zai zo? Numfashi yaja,
yana sauke shi akan fuskar Hammadi daya mike
yana shiga tsakanin shi da Dijen
"Karka fadi wata magana, idan har na isa, ni
Hammadi na isa ina da wata kima a idanuwanka
karka furta komai, dan Allah karka ce komai"
Hammadi ya karasa cike da roko, jikin shi har
kyarma yake saboda baya son tashin hankali, ba
kuma yason ya zama shaida akan danyen aikin
da zai iya faruwa idan Datti ya furta abinda
Hammadin yake gani kwance cikin idanuwan
shi
"Wallahi ba zan rike mata Bukar ba, ko ita zata
rike danta ba zatayi shi cikin gidana ba, Hamma
gara ka fada mata, bata isa ba, Baabuga bai isa
ba, dan su ma bai isa ba...ka fada mata ba'a
gidana ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 154
Kai Hammadi yake daga masa, so yake ya dan
natsu daga dokin zuciyar da ya hau
"To sai me idan baka rike shi ba? Ba sai in bar
maka gidan ba?"
Dije ta fadi, muryarta na fitowa a raunane
saboda kukan da ya kwace mata, magana Datti
zai sakeyi Hammadi yai saurin katse shi da
"Ban isa ba nima ko? Datti ni dinma ban isa ba
kenan"
Shiru yayi yana wani irin maida numfashi,
tabbas yau da babu Hammadi, da su kadaine a
cikin gidan su, ko zai kora Dije gidansu zaiyi
hakan ne bayan ya nada mata dukan tsiya, dan
makwancin shi da ta gani yasa raini ya shiga
tsakanin su, gara ya nada mata duka ya fara cire
wannan renin kafin ya korata gidan su ita da
Bukar din, in yado taga yanda zaiyi rayuwa shi
da Julde da Yelwa lafiya kalau batare da ita a
ciki ba
"Dije kema biye masa zakiyi? Idan shi ban isa
yaga kimata ba, kema hakan ne ko?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 155
Kai ta girgiza tana share hawayenta da bayan
hannu
"Hamma ni ba zan mayar da shi ba, wallahi
mutuwa zaiyi a gidan Baabuga"
Kai Hammadi ya daga mata
"Ni zan rike shi, zai zauna a gidan nan...ni da Abu
zamu rike shi, shikenan?"
Kai Datti yake girgizawa tunda Hammadin ya
fara magana
"Saboda me? Akan me zaka rike shi?"
Juyawa Hammadi yayi
"Saboda gidana ne, akan na isa inyi abinda nake
so tunda ban isa kai in saka kayi ba"
Takalma Datti ya zira yana ficewa daga gidan,
komawa Hammadi yayi ya zauna yana kallon
Dije
"Idan kin amince ni da Abu bamu da matsala da
rike Bukar, kibar shi anan wajen mu... Dan Allah
karki biyewa Datti kuyi abinda ba zai mana dadi
gabaki daya ba...in dai akan Bukar ne kar inji
Lubna sufyan
Hausabook.com 156
bakin ki ke da Datti... Dan Allah Dije ki zama me
hakurin nan da muka sani"
Kai ta daga mishi, ta kasa magana saboda kukan
da take tayi, duk da wani bangare na zuciyarta
ya nutsu da sanin ko ita ba zata rike Bukar
yanda Abu da Hammadi zasu rike shi ba. In dai a
hannun sune tana da tabbacin matsalarta ta
kare
"Nagode Hamma... Adda Nagode"
Ta fadi can kasan makoshi tana daga kai ta kalli
Abu data share kwallarta, tun baya ita taso ace
sun rike Bukar din
"Ko zamu rikema Dije yaron nan ne Hammadi
Am?"
Shiru yayi yana juya maganar
"Rike mata shi ba matsala bane kinsani, amman
bana son mu shiga maganar tunda yaron bana
Dije bane ita kadai, karmu saka mata rai
Baabuga yaki amincewa, kinga zamu kara
dagula mata lissafi, mu dai cigaba da mata
addu'a... Allah ya kawo mafitar da duka zata
bulle mana"
Lubna sufyan
Hausabook.com 157
Bata sake daga ma Hammadi maganar ba, duk
rikicin da ake tayi, shima kuma bai sake daga
mata maganar ba, taji dadin hukuncin daya
yanke yanzun. Ka samu kyautar yaro amman
rike shi ya zama wahala, su suna nema ido rufe,
wasu sun samu suna watsarwa. Ita tanata kirga
ranakune da taqi ganin saurin su don su cike da
dan lokacin daya rage Hammadi ya dauko
Saratu ta dawo karkashin kulawar su. Ko da ta
wanke fuskarta, ta goya Yelwa zata tafi sai da
Hammadi ya sake ce mata
"Kiyi ta hakuri Dije, kinji, wata rana sai labari"
Kai ta daga masa, zantukan shi na zauna mata.
Sai da ta kalli Bukar da yake bacci, taga Julde
daya kwanta a gefen shi, shima yana baccin,
wani sanyi ya ratsa zuciyarta. Shikenan,
hankalinta ya kwanta, amman data fita daga
gidan tana shiga nata da yake a bude sai taji
nisan nan da take ji a tsakaninta da Bukar ya
dawo, katanga ce kawai ta rabasu, amman jin
shi take can nesa da ita, ko da kafin a maida
auren su da Datti, ga Bukar din a jikinta sai ta
dinga jin shi can nesa da zuciyar shi, wannan
nisan ne yasa ta tunanin ko shidin ba zaiyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 158
tsahon rayuwa ba, ko alamune na cewar ta rike
shi a jikinta iya yawan yanda zata iya.
Ta so shi da dukkan zuciyarta saboda ba zata
samu lokaci mai tsayi tare da shi ba, numfashi
taja tana mayarwa hadi da kauda yanayin daga
ranta, abu daya a lokaci daya, yau dai nasara
tata ce, zata maida hankalinta kan wannan ne
kawai, kan yau kawai, ba zata daga hankalinta
akan goben da bata gani ba.
Sai dai goben cike take da hargitsin da Dije bata
hango ba
Nisan
Nisan nan dai shi Bukar zai mata.
**
Lokutta mabanbanta tana jin ana bada labarai
akan soyayya, idan kafin aurenta da Datti ta
dauka so wani nisantaccen abune da yafi karfin
mutanen karkara, kamar so din nau'i ne najin
dadi da bakowa yake da rabon samun shi ba, da
yawan mutane, cikin su harda wasu a cikin 'yan
Lubna sufyan
Hausabook.com 159
uwanta mata, idan ana bada irin wannan
labaran, ace an kalla a fina-finan hausa a binni,
sai suyita dariya, suna daukar abin a matsayin
shiririta
"So ya wuce a baka ci, sha da suttura da wajen
kwanciya?"
Daya a cikin yayyanta ta taba fada, zantukan da
suka zauna mata, zantukan da ta hasaso ta kuma
gina zamantakewa ta aure a kai, tunda yau da
gobe tasa taga hakan a zaman Baba da kuma su
Innarta, ciyarwa dai-dai karfin shi tsaye yake
akan su, haka ta taso tagan su zaune a mazauni
mai kyau, duk tsananin damuna ko naso rufin
dakin su bayayi, a maimakon yanda takan ji
makwabta na koken dakunan su sun kwana
suna yoyo, har bacci yakan gagara samuwa a
wasu dararen wajen iyaye da kuma yaran su.
Haka tufafi, zaka kirga gidaje goma a bayan su,
ka girka wasu goman a gabansu, haggu da kuma
dama, ba'a samu kwara biyu da zasuyi gogayya
da su wajen saka tufafi ingantattu ba.
Lokacin bikin sallah, sakin da zasu saka yafi na
kowa kyawu da tsada, duk kuwa kasancewar
Lubna sufyan
Hausabook.com 160
Baba bahaushe, in har zasuyi shigar fulani, to
sakine me kyau da saika duba zaka same shi a
gidan wasu. Juma'ar duniya tun da Dije ta fara
hankali, ta kuma fara bambance tsakanin
ranaku Baba bai taba fita ya dawo hannu biyu
ba, saiya riko 'yar tsabarshi. Shisa ta kara
aminta da zantukan duk da taji na cewar so dai
baya wuce irin wanda Baba yake nuna ma su
Inna, baya wuce irin wanda yake nuna musu
sudin ma a matsayin 'ya'yan shi, duk da a nasu
kalar son, a wajen Baba ya bambanta da nasu
Inna, yakan shigo da abu ya basu baiba su Inna
ba, wannan so ne na tsakanin mahaifi da yaran
shi.
Da zama na aure yazo kanta, a cikin yau da
goben da ta tsinci kanta tare da Datti ta samu
wannan soyayyar da akace itace karshe a zaman
aure, da farko ta yarda, babu wani so a zama na
auratayya daya wuce samar da ci, sha, suttura
da makwanci me kyau. Sai Abu da Hammadi
suka jirkita tunaninta, suka canza yardarta,
suka nuna mata a zama na aure, idan har ana
magana ta so, ya wuce duk wani lissafi da
kwakwalwarta tayi. Sai ya zamana tana kallon
Lubna sufyan
Hausabook.com 161
duk wani abu daya danganci zamansu da Datti,
tana dubawa, tana neman irin soyayyar
Hammadi da Abu a ciki.
Ba don ta raina ta Dattin ba, da fari ma bata
ganta ba, bata ga wata soyayya data wuce irin
wadda kowa yake dauka ita kadaice a cikin
zaman aure ba, sai da suka binne yaransu na
biyu, sai da ya riketa a jikin shi a lokacin da suka
rasa na ukku
"Baki ga su Hamma suna nema basu samu ba
Dije? A cikin matattun nan ba za'a rasa rayayye
ba, Allah zai kara bamu wani, wanin da zai rayu"
Sune kalaman daya fada mata bayan ya dagota
daga jikin shi yaga hawayen da ta kasa
tsayarwa. Sai kuma ta ga soyayyar shi da
kaddara ta raba zaman su. Sai ta fahimta, auren
ne abu daya, zaman ya bambanta. Mazan ne
suke amsa suna daya, halayen su ya bambanta,
soyayyar ce sunanta baya canzawa, amman
hanyoyin nunata suna da yawa.
"Kina son Baabuga? Dije kin so Baabuga a
zamanku?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 162
Tambayar ta Datti ta daketa, dukan da ko
tunawa tayi sai ta sake jin zafin shi, da ta daga
idanu ta sauke cikin nashi da nufin amsa mishi
da abinda tasan zai kwana biyu yana jin zafin
shi, sai maganganun suka makale mata. Kishin
da ta gani cikin idanuwan shi nasa ta jin kamar
an watsa mata ruwan kankara, ciwon da yake
zuciyar shi ya bayyana a saman kishin yana sata
bude tata zuciyar dan ta fahimci abinda yakeji,
ta fahimci dalilin da yasa tun daga jin maganar
cikin Bukar zuwa yanzun ya zabi yasa ta dora
ayar tambaya akan duk wata kyautatawa daya
taba mata, duk wata magana ta so daya taba
fada mata.
"Me yasa kika yarda 'dan shi ya zauna gidan
Hamma? In shiga kullum in kalle shi? Me yasa ba
zaki ga bana so ki hakura kibar masa 'dan shi ba
Dije? Me yasa kike nuna mun ni kadai ban isheki
rayuwa ba sai da wani bangare na Baabuga a
kusa dake?"
So take ta fahimce shi, amman da ta fara saiya
fadi wani abu da zai dakushe mata hasken da ta
fara gani
Lubna sufyan
Hausabook.com 163
"Dan Baabuga ne, na sani, dan Allah Datti ka
bude udanuwanka, sau daya kawai, ka bude
idanuwanka ka kalli Bukar, ka kalle shi kaga ba
d'an Baabuga bane kawai, d'ana nima..."
Kai Datti ya ke girgiza mata tun kafin ta k'arasa
zancenta, yana nuna mata ba zai taba kallon
Bukar yaga wani b'angare nata a tare da shi ba,
idan ya kalle shi Baabuga kad'ai zai gani,
Baabuga da baya son tuna zama ya had'ata da
shi, sai Bukar ya zame mishi wata tunasarwa da
ya tsana fiye da komai. Hawayen da suka zubo
mata ta share
"Ya kake so inyi? Me kake so in fada maka?
Yanda duk zance maka ban taba son Baabuga ba
idan nace maka ina son Bukar zaka karyata
hakan. Idan nace maka banyi dana sanin
haihuwar Bukar ba zaka kara cewa dole na so
Baabuga... Ka fadamun abinda kake so inyi ka
yarda dani Datti, ka fadamun"
Cikin idanuwa yake kallonta, yana jira ta sake
goge hawayenta ta kuma kara saka idanuwanta
cikin na shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 164
"Ki mayar masa da d'an shi, ki mayar masa da
shi Dije"
Numfashi taja ta fitar tana kauda kai kawai,
saboda ta sani, zuciyarta ce taso karyata ba
hakan zai bukata ba. Hammadi ya roketa karta
sake biye ma Datti akan maganar Bukar, amman
taya zata iya kauda kai bayan duk rana idan bai
mata maganar ba, idanuwan shi da suke cike da
zancen suna bin duk wani motsinta? Bata da
yanda zatayi ta kauce ma maganar Bukar da
Datti, masalahar da Hammadi yake ganin ya
samar musu bata zauna ma Datti ba, abinda bata
ma sani ba shine Datti ya sami Baabuga
"Ka zo ka dauki d'anka, ka yarda dani idan nace
maka rigima dani ne karshen abinda zaka soyi a
fadin Marake, kazo ka d'auki d'anka"
Ya kuma baro Baabuga da baiba damar amsa shi
ba a tsaye. Washegari a wajen da ake kular
musu da dabbobi ya samu Hammadi, saboda
ranar tayi dai-dai da ranar da za'a tafar musu da
wasu shanu kudu don a siyar, har aka ga ware
su aka saka a mota, Hammadi bai ko amsa
gaisuwar Dattin ba, da ya gama ma, rabashi yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 165
ya wuce, shine yabi bayan shi yana sake masa
magana, sai dai kallon da Hammadi yayi masa
ya saka jikin shi yin sanyi, gwiwoyin shi kamar
an buge masa su da sanda
"Ban isa ba nasani, amman na dauka rashin isar
zai tsayane a tsakanin mu, ba saika tsallaka
waje ka nuna ma kowa ban isa ba Datti... Ka
kyauta, na kuma gode"
Hammadi ya karasa maganar cikin harshen
Hausar da zakaji ta a bakin shi lokaci zuwa
lokaci
"Me nayi kuma Hamma?"
Datti ya tambaya duk da ya hasaso inda
zantukan Hammadin suka dosa
"Tambayata kakeyi? Baka sani ba?"
Sunkuyar da kai kasa yayi saboda bayason irin
kallon da Hammadi yake masa
"Dani ka samu kace in dauki Bukar in mayar
bawai ka samu Baabuga ka fada masa yazo ya
dauki d'an shi ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 166
Kamar Abu tana duba, sai da ta hango musu
wannan matsalar
"Ka samu Baabuga kayi masa maganar Bukar,
kar yazo ya sake birkita mana komai, kaga inda
wata matsala sai mu san yanda zamu shawo
kanta"
Ya kuma aminta, ba Baabuga da ya yarda masa
da rike Bukar ba, har Baba saida yaje ya samu
"Anya Hammadi, anya wannan hukuncin naku
mai bullewa ne? Ita Dijen inace na gaya mata ta
dauke kai akan maganar Bukar, mai rabon
ganin badi fa saiya gani, wahala kuma ai bata
kisa, baga sauran 'yan uwa nashi nan ba suna
rayuwa a gidan"
Cewar Baba, sai dai ko babu kalamai masu
taushi, akwai wani kwarjini a tare da Hammadi
da yake cika idanuwan duk wanda zaije ma da
wata bukata, bai dauki lokaci ba wajen gamsar
da Baban kan zaman Bukar a hannun shi,
lokacin da sukayi sallama, banda fatan alkhairi
babu komai a bakin Baba. Ya dauka ya gama
tufke wannan zaren harya zama igiyar da baiyi
tunanin Datti zaibi ya nemi ya warware ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 167
"Idan ban isa da kai ba, ina ce na isa da kai na
ko? Ina kuma damar da zanyi duk abinda nake
so ciki harda zabina na rike Bukar"
Kallon shi Dattin yayi
"Ko da bana son zabin naka? Hamma ko da rike
Bukar yana nufin kuncin tawa zuciyar? Me yasa
kuke nuna mun yaron nan yafi ni? Yaron
Baabuga, me yasa kuke ta zabar shi a kaina? Me
yasa kuka fi son shi? Harda kai Hamma, me yasa
kaima zaka zabe shi a kai na?"
Fushin da ya dauka baiyi tasiri akan Hammadin
ba, yana gani shima saiya share shi, shariyar da
ta kara kuntata zuciyar shi. Shisa ya dawo wajen
Dije, idan ita tace ma Hammadi zata mayar da
Bukar ba zaiki ba, dole zai hakura, amman
itama yana ganin babu alamar nasara akan
haka. Shisa yanzun da yake kallonta ya kasa
furta mata kalmomin da suka kwana biyu suna
masa yawo a kan shi, a karo na farko a tsayin
wani lokaci da wani abu mai yanayi da tsoro ya
cika kirjin shi
"Ki zabi daya, koni ko Bukar, ki zaba Dije, ko ni
ku Bukar"
Lubna sufyan
Hausabook.com 168
Haka yake so yace mata, sai kalaman suka
makale masa, saboda idan ya taba ganin
soyayyar shi a cikin idanuwanta, a yan
kwanakin nan yaga yanda zata iya jingine komai
akan Bukar, akan yaron nan da baya ko son
gani, yaron da yake jin tsanar shi tun daga kasan
zuciyar shi. Shisa ya mike yabar mata dakin,
yabarta da soyayyar Bukar da ta zaba akan
tashi.
**
Idan akace lokaci kan tafi da komai, sai Dije taji
maganar tayi mata nauyi, idan akace komai, za'a
iya nufin komai kenan? Anya? Anya lokaci kan
tafi da komai? Da sunce lokaci kan tafi da wasu
abubuwan zatafi yarda, saboda taga shaida,
akan girman su Julde take ganin wannan
shaidar, akan yanda rikon Saratu ya dawo
hannun Abu, akan abubuwa da yawa, cikin
abubuwan nan harda cire rai da tayi da samun
wani rabon bayan shekaru goma cir da suka
wuce mata batare da ko batan wata ta sakeyi ba,
iya rabon kenan, ta binne wasu, ga uku nan sun
rayu.
Lubna sufyan
Hausabook.com 169
A cikin abubuwan da lokaci ya kasa tafiya da shi,
shine tsanar da Datti yayi wa Bukar, Bukar din
da wanda duk hanya zata hada da shi a Marake,
babba ko karami sai hankali da karamcin shi
sun tabashi, Bukar da duk wani abu da zai shiga
hannun shi burin shi ya raba tare da wanda
yake ganin sun fishi bukata. Bukar dinta, Bukar
mai sanyin halin nan, Bukar mai taushin zuciyar
da bai tsaya akan mutane ba kawai harda
dabbobi. Bukar da zaka ga ana ruwa ya koro
duk wata kaza da zai gani cikin gida ya saka su a
dakin daya zama nashine a gidan Hammadi, har
sai an gama ruwan sama zai bude ya fito da su,
Bukar da zai hango tsuntsuwa ta makale a sama,
duk fadan da Abu zatayi ba zai samu nutsuwa ba
saiya taka ya warware mata abinda ya daureta.
Bukar da ke son tsuntsaye da dukkan zuciyar
shi
"In sa a kamo maka mana Bukar, duk kalar da
kake so"
Hammadi kance masa idan yana laburta masa
wani kalar tsuntsun da ya gani, yana bashi
labarin na'uin shi da yankin da yaji labari anfi
Lubna sufyan
Hausabook.com 170
samun irin na'in tsuntsun a wajajen, sai dai yayi
dariyar nan, dariyar nan tashi da zakaga
kyallinta har cikin idanuwan shi
"Ai zuciyata ba zata nutsu ba idan na tsare shi a
waje daya, baccin kirki ma ba zan iya ba...koni
da kafafuwana ba kowanne gari zasu iya
daukata su kaini ba zan takura idan aka tsareni
waje daya, balle abinda aka halitta ma fukafukan da zai iya tsallakawa kasashe"
Kafin Dije ta furta Bukar daban ne, halayen shi
sun nuna haka, komai da zaiyi ya bambanta shi
da yara sa'annin shi. Babu yanda za'ayi Bukar ba
zai shiga zuciyar ka ba, sai dai shigar da yayi ma
ta Datti daban ne. Baya iya boye tsanar shi, sau
daya Bukar ya gwada kiran shi da
"Baba"
Kamar yanda yaji su Julde suna kiran shi
"Ni ba babanka bane, karka kara kirana da
Baba, sunana Datti"
Lokacin daya fadama Bukar, su duka sun dauka
yayi yarintar da zai rike maganar, amman kuma
sai ranar ta zama rana ta karshe da Bukar din ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 171
sake kiran shi da wani suna ma gabaki daya.
Yana shiga ya gaishe da Dije, baya zama, yanda
duk zata so baya zama, ko abinci ta zuba masa
zaice mata ya rigada yaci abinci ko kuma
bayajin yunwa. Duk wani abu da zai hada
hanyar shi da Datti tunda ya fara hankali guje
masa yakeyi. Abin mamakin yana cikin
shakuwar da take tsakanin shi da Julde da
Yelwa, saboda shi saita wuni suma bata gansu
ba, suna gidan Abu, sai dai ita ta kulle gidan idan
ta gama abinda takeyi ta shiga can, saboda
kadaici saiya addabeta.
Tana da yakinin duk soyayyar da take yiwa
Bukar ba zatayi masa rikon da Hammadi da Abu
sukeyi masa ba, balle kuma Baabuga. Da a
hannunta yake ba zai taso da irin tarbiyar da
yake da ita ba yanzun, ba ita zata gaza ba, irin
sangartar da Julde ya taso ciki ce zata nakasa
rayuwarshi, kamar yanda take ganin tayiwa ta
Julde harda Yelwa ma. Yaranta, yaran da bata
isa ta tsawatar musu ba saboda makauniyar
soyayyar da Datti ya dauka ya dora akan su, laifi
in har bashi yaga sunyi ba, fada idan har bashi
zai musu ba, babu wanda ya isa. Idanuwan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 172
kullum cikin ganin laifukan yaran wasu yake,
bakin shi kullum cikin aibata yaran wasu yake
da dora ayar tambaya akan irin tarbiyar da suka
samu, tun Dije na magana harta gaji ta saka
masa ido.
Bakin Datti dai akan yaran da ba Julde da Yelwa
ba, kaf Marake sai Saratu ce da ta ciri tuta ta
tsira daga shi, saboda babu wanda ya dauka zai
so wasu yaran da basu fito daga jikin shi ba, sai
ita
"Baba Am"
Takan fadi, Saratu kan kira shi da Babanta,
Saratu kan saka kujera ta zauna a bakin kofa
idan lokacin dawowar su Datti yayi, Saratu zata
ruga wajen Datti ko da shi da Hammadi ne a
tsaye kuma su duka suka bude mata hannayen
su, sai ya zamana kamar gasa ce takeyi da su
Julde, gasar da suka rigada suka bar mata
kambunta akan soyayyar Datti, shakuwar su
Zata baka mamaki. Kara irin na Hammadi, ko na
rana daya bai taba kiran Saratu da tashi ba, sai
dai yace
"Yar Datti"
Lubna sufyan
Hausabook.com 173
Julde na da gaddama, idan ya kafe akan abu,
babu wanda ya isa ya tankwara shi, kuma baisan
ya nemi wani abu ya kasa samu ba, Yelwa na da
yawan fara'a, tana kuma gudun bacin ran kowa,
idan kaga kafiyarta to akan dan uwanta ne, akan
Julde ne da take nuna batada wanda yafi shi a
duka fadin duniya, ciki harda Datti da Dijen da
ko da tana karama idan tana kuka Julde ne yake
lallashinta tayi shiru, idan abu take so sai dai
suji a bakin Julde. Idan har Yelwa ta kafe, to
akan wani abune da Julde yake so Dije ta nemi
hana masa, to su duka biyun zasu hadu su
botsare mata.
Saratu a gefe daya, kowa idan ya kalleta zai
dauka zaiga Hammadi a tare da ita, idanuwan
nashine, har yankansu iri dayane, sai dai idan
Hammadi ya kalleka zaka ga sanyin halayyarsa
da yake cikin su, idan Saratu ta kalleka babu
wannan sanyin a cikin idanuwanta, kamanninta
irin na Pendo ne, in kasan Pendo, Saratu ta gifta
saika san cewar jininta ce. Saboda ta taso a
hannun Abu, saboda yanda Abu take tsaye akan
tarbiyarta zaka dauka kaf Marake saika tona
zaka samu mai nagartattun halaye irin na
Lubna sufyan
Hausabook.com 174
Saratu. Daga jikin Hammadi ta fito, kowa shaida
ne, amman Datti ne mudubinta, idanuwanta
akan Datti da duk wasu halaye nashi yake.
Tana da zafin rai, tana da riko, ko fadan yarinta
idan ya hada su da Julde da yanda duk take
nacin ganinta kusa da shi kuwa, ya kwadeta,
saboda alamu da yawa na nuna yanda nata jinin
ya hadu da nashi, shi din nashi jinin bai hadu da
nata ba, yana zaune zaka ga ta shammace shi ta
kwada masa wani abin. Ko kayanta ne ba'a isa a
bayar dasu a gabanta ba, wuni zatayi tana kuka,
da safe tana tashi zakaga ta sake saka wani
sabon kukan, sai tayi kwanaki tana wannan
tashin hankalin da idan Datti yaji zai goyi da
bayanta
"Ku daina bayar mata da kaya tunda bata so,
koni bana so in saka kaya in cire su in bayar,
garama in dinka maka sabo wanda bai kai nawa
ba"
Kai kawai Abu takan girgiza kaine, bata kara
furta komai, saboda idan halayen Datti takalma
ne, basu Saratu ta saka ba, inda ya dauke
kafafuwan shine take saka nata, sawayen shine
Lubna sufyan
Hausabook.com 175
take takawa suna shigewa ta cikin kafafuwanta
suna rabuwa tsakanin zuciyarta da kanta
"Haka kawai sai zuciyata ta dinga tsinkewa idan
ina duban yaran nan, halayen su na zauna mun a
zuciya, wani lokacin kuma sai su bani tsoro,
tunanin ya goben su zata kasance kan hanani
bacci a wasu dararen"
Dije ta fadama Abu lokacin da Julde ya shigo
gidan batare da sallama ba balle ma su saka ran
zai gaishe su, a zuciyar shi ya gaishe su da safe,
baya bukatar ya sake musu wata gaisuwar,
murmushi Abu tayi, idan tace tsoron nan babu
shi a tare da ita zatayi karya
"Allah dai ya raya ya shirya mana"
Ta iya furtawa, Amin din Dije na tsayawa a iya
zuciyarta saboda nisan da tunaninta yayi. Yelwa
da Saratu take kallo, tana juyo dariyar Yelwa
daga inda take, kafin ta Saratu ta ratsa cikin
tunaninta.
A cikin dariyarsu zakaji yanda basu da wata
matsala
Lubna sufyan
Hausabook.com 176
A cikin dariyarsu zakaji yanda basu san wata
kaddara ba balle abinda ta tanadar musu.
Hannu tasa tana share hawayen da ya zubo
mata, wani irin zafi zuciyarta takeyi da ta manta
lokacin da taji irin shi, filin da Bukar yabari na
kara yi mata girma kamar babu kowa a
duniyarta sai shi kadai
"Dan Allah kiyi hakuri Dije, addu'a zaki bishi da
ita, Allah ya tsare shi duk inda zai shiga"
Idan wutace take ci a cikin kirjinta, maganganun
Abu sai suka zama kamar ta kara zuba mata
itace ne a ciki
"Me yasa Adda? Me yasa tunda na haifi Bukar
babu abinda yake so sai nisanta da ni?"
Numfashi Abu ta sauke cike da neman kalaman
daya kamata tayi amfani dasu wajen tausar
Dijen ko zata samu sauki
"Ji nakeyi kamar tunda na haifeshi ban huta ba,
tunda na haife shi nake kokawa da ya zauna
Lubna sufyan
Hausabook.com 177
kusa dani, saboda ina ganin kamar hakanne
kawai gatan da zan iya bashi..."
Kafin yayi wannan girman sai take jin bashida
zabi a duk wani abu daya danganci rayuwar shi,
shisa take kokarin ganin ta zabar masa. Shisa
tun farko bata son yana rabar gidan Baabuga
"Ina so inje wajen su Madu"
Da wannan ya fara, da wannan kalaman ya fara,
ta so ta hana, har a kasan zuciyarta ta so ta
rabashi da 'yan uwan da jini ya hadasu
"Um um Dije, karki fara, karkice zaki rabashi da
su, yaron nan yana da hankalin daya girmi
shekarun shi, duk yanda bakyaso Baabuga ne
baban shi, yanda duk zanyi kokarin maye masa
wannan gurbin ba zai goge hakan ba, Bukar
yasan Baabuga ne baban shi, hana shi rabar
gidan zai jefa masa wasu tambayoyi a zuciyar
shi da zasu rikita tunanin shi"
Haka Hammadi yace mata, shisa tabari, shisa
tabar Bukar yana zuwa gidan Baabuga, tunanin
Bukar da Hammadi ya hango zai rikice idan ta
hanashi rabar gidan Baabuga shine ya faru,
Lubna sufyan
Hausabook.com 178
kuma zata dora laifin a kanta ne kawai. Saboda
duk zuwan da zaiyi ya dawo yakan zo mata da
labarai mabanbanta, a bakin shi tasan kaf
sunayen yaran Baabuga har wani lokacin tana
kokarin dora fuskoki akan irin labaran su da
Bukar yake bata. Tana so taga ko zata gane su
adan zaman da tayi a gidan, amman sai ta kasa.
"Hamma ya dawo Daada"
Hamma, Hamman shi da ko yazo ko baizo ba,
baka raba bakin shi da ambaton shi
"Baka da wani Hamma daya wuce ni, idan zaka
kira wani da Hamman ka, nine Bukar"
Julde ya taba fada da yaji yana bata labarin
Hamman shi kamar bashida wani mudubi na
dubawa daya wuce wannan Hamman. Dan
Julden ya bata dariya, ta dauka Saratu kawai
take da kishi irin na Datti, don ko kaya bata so
ayi mata iri daya da kowa, cikin wannan kowan
harda Yelwa kuwa. Komai nata tafi son shi ita
kadai. Julde bai damu ba, ba zakaga kishin shi ya
nuna ba sai idan kaso ka nuna kamar kafi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 27