akai zata bi, kome ita ta hango a sama
in dai shi bai ganshi ba bata da ikon sake hanya.
Tayi kokarin magana, tama yi maganar, ita da
Modibbo akan titin nan ba abu bane da take so,
Lubna sufyan
Hausabook.com 315
amman yaki bari duk maganarta ta wuce
kunnuwan shi balle ya fahimceta harta canza
kudirin da yake zuciyarshi
Yaki fahimtarta kamar yanda yake tunanin taki
fahimtar shi, taki gane duk wani zabinshi akanta
gatane yake tunanin yayi mata. Mahaifin
Modibbo da ma Modibbon a karkashin shi suke
samun rufin asiri, shisa mahaifinshi baiki ba da
yayi masa tayin fadada alakarsu. Ko bayan
bashida rai Modibbo da ahalin shi basu isa su
wulakantata ba, basu da wannan karsashin
saboda zata gaji kaso mai girma a cikin abinda
zai bari, kason da yasan Julde zai kular mata
dashi har numfashin shi na karshe, tana da
arzikin da tafi karfin wulakanci kowanne namiji
a fadin marake. Gashi dadin dadawa shi
Modibbon bafullatani ne gaba da baya. Me take
so bayan wannan? Menene abinki a tare da
Modibbo?
"Daada shirunki na cutar damu, shirunki a
abubuwa da yawa ya taimaka wajen kawomu
inda muke yau, kiyi masa magana, dan Allah ki
bude baki kiyi masa magana. Ki fada masa wani
Lubna sufyan
Hausabook.com 316
abu zai mutu a tare dani daga ranar da ya
auramun Modibbo"
Yelwa ta karasa maganar wasu irin hawaye
masu zafi na zubo mata, shirun dai Dije ta
sakeyi, shirun da ta fara koyan shi akan
lamurransu daya hada da Datti bayan taga
yanda maganarta batada amfani indai akansu
ne. Tun suna kananansu kuwa, su suka kara
taimaka masa wajen dishe muryarta a duk wasu
lokutta da zata shata musu layin da take tunanin
zai amfani gobensu, Datti ya goge musu shi su
tsallaka. Idan kudi ya dauka ya basu take
tunanin sunyi yawa ta kwace, zasu fita ko me
zatayi kuwa, zasu same shi, zai dauki wanda
suka ninkasu yawa.
"Ubansu mai kudine, su yaran mai kudine Dije.
Ki barmun yara suyi abinda suke so tunda ina
da halin da zasuyi hakan..."
Idan fada tayi musu, a gabansu zaiyi mata
wanda sai ta shiga daki tayi kuka. Shima irin yau
din ta dinga hango masa, da duk wata tsinuwa
da zaibi yaran wasu dashi, da duk lokuttan da
yake ganin shine ya isa akan tarbiyar su, dama
Lubna sufyan
Hausabook.com 317
lokuttan da yake ganin duk idan yaro yayi wani
abu da bai kamata ba to laifin na iyayenshi ne,
sune suka gaza a wani bigire na tarbiya, ikon
canza kaddarar yaransu a hannun su take, sai
Dije tayi kokarin fahimtar dashi. Yaran duk da
suka kasance nagartattu, bayan kokarin
iyayensu akwai addu'a, akwai addu'a da itace
mataki da kuma jigon komai.
Sosai taso ta fahimtar dashi tarbiya abune mai
matukar wahala, bayan godiya lokacin da Allah
yayi maka kyautar samun da, ya kamata tsoro
ya cika zuciyarka, mutum ma ya baka amana
kana taraddadin karka kasance cikin wanda
zasu kasa sauke wannan amanar, ya kamata
tsoro ya cika zuciyarka sanin Allah ne ya baka
amana, amanar yaran da kai dasu zaku tsaya a
gabanshi ya tambayeka akan wannan amanar.
Idan kayi iya kokarinka wajen ganin ka sauke
amanar nan, saika hada da addu'a, ka hada da
sadaka don karesu daga abinda idanuwanka ba
zasu taba hangowa ba. Idan kaga wani ya gaza a
tashi tarbiyar ka bishi da addu'a, ka godewa
Allah da baisa ka gaza ba, idan ba zaka iya ba
kayi shiru, ka kiyaye harshenka.
Lubna sufyan
Hausabook.com 318
Idan yarane ka gani suna abinda bai kamata ba,
kayi musu nasiha idan zaka iya, ka bisu da
addu'a bayan nasihar, ko ka tsaya da addu'ar
kawai, kana da zabi kala-kala, a ciki harda mai
sauki, kaja bakinka kayi shiru. Karka aibatasu,
karka bisu da mugun baki, karkai tir da
halayensu, karka dora laifin lalacewar su akan
iyayensu, watakila sunyi iya kokarinsu, kaddara
ce ta rinjayi wannan kokarin. Idan ma sun
taimaka wajen wannan lalacewar baka da
hurumin da zaka nuna musu yatsa. Allah daya
zabeka, Allah daya baka ikon sauke amanar
daya baka, shi ya basu amanar, a karkashin Ikon
shi suka kasa saukewa. Babu wanda yafi karfin
kaddara, kowacce iri ce.
Amman Datti yaki fahimtar yaren duk da
fulatanci tayi masa ba hausa ba. Sai hakanma ya
dinga ja mata fadanshi da idan ya fara baisan
yayi shiru ba. Suma da ta nuna musu makahon
sone Datti yake musu, soyayyar da ta samo asali
da samu da rashin sauran yaran da suka dingayi
a baya. Ta nuna musu lokaci zai iya zuwa da
Datti zai kasa basu duk wani abu da zasu
bukata, zai kasa karesu daga abubuwan da suka
Lubna sufyan
Hausabook.com 319
fi karfin ikon shi, sai suka koma bayan Datti
suka labe, suna nuna mata akwai rauni a tata
soyayyar.
"Kinfi son Bukar, Daada kinfi son Bukar damu"
Julde ya taba fada mata kai tsaye, sai dai tana
ganin a lokacin kamar shekarun shi basu kai ya
fahimci tana sonsu duka ba, tana kaunarsu
gabaki dayansu, wata irin kauna da bata da
misali. Kawai akwai wani rauni a tare da Bukar
da basu dashi, akwai wata kaunarta da Bukar
din yake nunawa da a cikinsu babu mai nuna
mata irinta, bawai tana kishi bane da yanda
suka dinga zabar Datti akanta. Kawai shakuwar
da take tsakaninta da Bukar, ko nisan da yayi
mata ya kasa dishe haskenta. Kowacce uwa tana
son yaranta, tana sonsu dai-dai da junansu,
hanyoyin da take nuna wannan soyayyar ce take
da bambanci.
"Ban fi son Bukar ba, ku duka ina son ku"
Kallonta yayi, kallonta yayi kamar bai yarda da
ita ba, kamar kalamanta basuyi masa tasiri ba.
Amman ya dora kanshi a jikinta, saboda Julde
ne, ko fada tayi masa, ko fada yaja Datti yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 320
mata zai zo ya dora kanshi jikinta, kamar yana
bata hakuri, kamar idan yayi hakan zuciyarshi
na masa sanyi.
"Kiyi masa magana Daada"
Yelwa ta sake rokonta. Tace masa me? Tace
karya aura mata Modibbo? Ta ina zata fara shiga
wannan maganar? Shiru tayi, hakan yasa Yelwa
ta sa bayan hannunta ta share fuskarta tana
ficewa daga dakin. Idan Dije tace tayi niyyar
magana to zatayi karya. Amman da Datti ya
dawo, saita tsinci kanta da fadin
"Ka kyaleta Datti, tunda tace bata son shi ka
kyaleta. Ya kamata daga kai harsu ku fara
saurarar juna ko zaku samu maslaha"
Saiya kalleta, irin kallon da yasata ganin yanda a
cikin yaran duka Bukar ne kadai yayi yanayi da
ita, ko yanayin yanda Julde yake cin abinci irin
na Datti ne, muryar shi ma haka. Akwai
abubuwan da Yelwa zata furta duk da tana mace
sai muryarta tayi mata iri daya da ta Dattin.
"Babu wanda ya isa yasa a fasa auren nan, ko ita
da kanta Yelwar"
Lubna sufyan
Hausabook.com 321
Wani abu Dije taji ya tsirga mata, wani abu da
bashi da kalma, saiya hado mata da tsoro, tsoro
da firgici mai yawa. Yanda suka zo inda suke
yanzun, yanda tarin kaunar da take tsakanin
Datti da su Julde ta birkice tana juyewa zuwa
haka cikin dan lokaci. Sai taji tana son magana
da Abu, ta kudura a ranta washegari wajen Abu
zataje, su tattauna akan yanda babu wani abu da
yake da tabbas a cikin rayuwa. Yanda komai
yake canzawa abin tsoro ne. Jikinta taji ya dauki
dumi cikin wani yanayi da ta kasa fahimta,
kamar zuciyarta na son sanar mata da komai na
gab da birkice musu, kuma babu wanda ya isa ya
hana hakan faruwa.
Sai ace jiki daya gareka, ruhi daya, zuciya daya.
Ba musanta hakan Yelwa take sonyi ba, tarin
tambayoyi ne take dasu kawai, tun daga lokacin
da ta hadu da Kabiru, ta dauka wani kasone mai
girma daga zuciyarta ya mamaye, sai da
rabuwarsu ta risketa cikin yanayin da ta hango,
amman bai sa zafin rabuwar ya rage mata ba. Sai
taji ba mamaye wannan kason mai girma na
zuciyarta Kabiru yayi ba, saboda idan mamaye
Lubna sufyan
Hausabook.com 322
shi yayi zataji alamar shi da basa tare, zata
rantse ko hannunta ta dora akan kirjinta, inda
zuciyarta take tana iya jin fadin filin daya bari,
kason yana tare dashi, da kason ya tafi yana bar
mata filin daya taba zama. Sai kuma sauran
abinda ya rage mata da yake wani irin ciwo,
ciwo da ba zata misalta ba.
Da kason daya tafi dashi, da kuma wanda ya
rage mata, kenan ya hada zuciya kwara daya
kenan a dunkule, meye takeji yana dokawa yan
uwanta? Dame take son Julde? Julde da har
yanzun idan aka raba yar duniyarta kashi uku,
zai kwashe kaso biyu daga ciki, meye yake
dokawa Daadarta? Baban fa? Me ya karya
lokacin daya rabata da Kabiru? Meya karya a
lokacin daya ja mata Allah ya isa yana kara
kaurinta da wasu maganganun marassa dadin
maimaitawa. Meye Baba ya karya lokacin da ya
toshe kunnuwanshi daga duk rokon da take
masa akan karya hadata aure da Modibbo? Ba
zai yiwuwa ace zuciya daya ce take dauke da
duk wannan bangarorin ba, zuciyarta da wani
sashi ce a gabaki daya jikinta.
Lubna sufyan
Hausabook.com 323
Ruhin kuma fa? Sau nawa tana jin fitar shi daga
jikinta ya koma gefe yana kallon abinda yake
faruwa kamar basu da alaka, kuma a lokacin
tana jin shige da ficen numfashinta, alamar
akwai rai a tare da ita. Yanzun kuma fa? Yau
kuma fa? Yau da ta tsallake komai, ta tsallake
kowa, a karo na farko kuma ta saka kafarta a
wajen Marake gabaki dayanta. Yau da tun da ta
dauki mayafinta, tabi ta tsakanin mutane a
taron bikinta, taji tabar wani abu daya girmi
jikinta a cikin dakin nan, bayan kalaman Daada
"Kowanne mai rai da zaki gani da tashi
kaddarar Yelwa, ba ko yaushe bane abinda kake
so yake alkhairi a tare da kai ba, ba kuma ko
yaushe bane abinda kake ki yake sharri a
wajenka, komai yana iya juyewa. Shisa ake so
kaso kadan, ka kuma qi kadan. Kiyi hakuri
tunda har anzo gabar nan. Datti na da taurin kai
na sani, amman yana kaunarku, idan kika ture
sabanin kankanin lokacin nan ke da kanki
kinsan akaf duniyar shi babu kamar ku, yanayi
miki abinda yake ganin shine iya gatan da zai
iya baki..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 324
Tana jin yanda Dije ta kara sauke murya tana
cigaba da fadin
"Idan kinganshi yau, ki kalle shi, ki kalle shi
sosai Yelwa kiga yanda yafi ki jin ciwon wannan
abubuwan da suke faruwa. Dan Allah ki kwantar
da hankalinki"
Kai ta daga kamar ta ji, kamar kalaman sunyi
tasiri a zuciyarta. Kamar bata gama yanke
hukunci tsallake gabaki dayansu ba. Idan tace
tun da aka rabata da Kabiru bata hakura dashi
ba zatayi karya, bata son Modibbo, koma rana
daya batajin zata taba son shi. Bata kara sanin
daura aurenta da Modibbo dai-dai yake da
yanke mata hukuncin kisa ba sai satika biyu
kafin auren da ta fita, ta fita da sunan shiga
wajen Saratu, ta mike hanya batare da tasan
inda ta nufa ba. Iska take nema, so take tayi
numfashi taji yakai mata inda ya kamata ya kai
mata, tayi numfashi batare da taji kamar kanta
zai rabe gida biyu da yanayin da ya cunkushe shi
ba.
A can kasan zuciyarta wata murya na fada mata
Lubna sufyan
Hausabook.com 325
"Idan kika cigaba da tafiya fa shikenan, zaki bar
komai, zaki gujema auren Modibbo, kici gaba da
tafiya karki juya, karki taba juyawa, akwai iska
daban, komai zaiyi sauki in dai baki juya ba,
ciwon da kike ji zai tsaya in dai kika cigaba da
tafiya"
Muryar kamar ta kara mata bugun zuciyarta, ta
kuma karawa kafafuwanta saurin cikin tafiyar
da takeyi, saurin daya sakata yin tuntube
"Yelwa"
Muryar nan ta daki kunnuwanta, muryar shi,
muryar Kabiru. Bawai batajin ta a cikin kanta
bane ba, yau dai sai taji kamar saida ta daki
kunnuwanta ne sannan takaiwa kanta tana
saukowa cikin zuciyarta, ta kada iska a cikin
filin da rashin shi yabar mata
"Yelwa..."
Ya sake kira yana jan sunan cikin sigar da ta
sakata juyawa, ta kuwa sauke idanuwanta cikin
nashi, tana yawatawa dasu kan fuskar shi,
zuciyarta ta dunkule waje daya, ta gangaro daga
Lubna sufyan
Hausabook.com 326
kirjinta tayo kasa tana karasawa inda yake
tsaye kafin ta tarwatse
"Yelwa"
Wannan karin ya kira da wani irin yanayi mai
nauyi, yanayin daya nuna har cikin idanuwanta,
yanayin da yayi dai-dai da kamar ya kwashe
bangarorin zuciyarta data tarwatse, ya riritasu
cikin hannuwan shi ya mika dai-dai kirjinta,
yana mayar mata da ita a mazauninta. Sai taja
wani numfashi, ta sauke shi tare da abubuwa
masu yawa
Ashe karya tayiwa kanta.
Da tace hango zata iya rayuwa babu shi
Yaudarar kanta tayi.
Da ta dauka akwai wata rayuwa mai sauki da
basa karkashin inuwa daya a tare.
"Na kasa Yelwa, nabi zabinsu, na aureta kamar
yanda suka bukata. Ya zanyi? Kullum fuskarki
nake nema a cikin tata, idan tayi kokarin
kyautata mun dake nake son kasancewa ko da
Lubna sufyan
Hausabook.com 327
rashin kirki zakiyi mun... Sai na saketa, na
saketa jiya, kowa ya juyamun baya yau"
Ya karasa yana sauke numfashi hadi da sake
saka idanuwan shi cikin nata
"Ya zanyi? Wanne irin so ne wannan da lokaci
yaki rage zafin shi?"
Kafadu tadan daga masa, wasu hawaye masu
zafi na zubo mata
"Baba ba zai bani ke ba ko?"
Kai ta daga masa, wani abu na tokare mata
makoshi yana hana kalaman da suke cikin kanta
su fito, shima hannuwan shi ya saka yana rufe
fuskar shi dasu, kamar hawaye yake nema,
nashi su zuba kamar yanda nata suke zuba ko
zai samu sauki. Kafin ya dago da idanuwan shi
da suka sake launi lokaci daya.
A wannan ranar
A wannan tsayuwar
A tsakanin hawayenta da bushewar idanuwan
shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 328
Suka yanke hukuncin daya kawosu inda sukw
yau
Su gudu
Su ka gudu
Ya saka hannunshi cikin nata bayan sun zauna a
motar da Yelwa bata cikin nutsuwar da zataji
inda suka nufa. Ya dai biya kudi sun kuma shiga,
tana jin dumin hannun shi da zufa na ratsawa ta
jijiyoyin nata hannun har zuwa zuciyarta da
take cike da wani irin hargitsi. Karo na farko da
ta rike hannun wani namiji da ba muharraminta
ba, dumin sai yayi mata daban, a lokaci daya
kuma yayi mata kama da wani abu, wani abu
kamar zunubi, wani abu kamar kuskuren da
zata iyayin dana sanin shi a gaba, wani abu
kamar kuskuren da lokacin gyara shi ya kure
mata.
*
"Zan kara aure Saratu"
Ya fada mata, saboda ko babu soyayya a
zamansu ta haifa mishi Salim, akwai tsohon
cikin shi a yanzun, tana shirin sake haifo masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 329
na biyu. Tana shirin sake shafe wani daren, ko
wasu kwanakin a dakin da ba zaka juyo komai
banda nishinta ba. A wahalar da tasha, a irin
tashin hankalin daya shiga shi kanshi sai da
zuciyar shi tayo tsalle zuwa makoshin shi ranar
daya ga tana amai. Daga inda yake tsaye cikin
firgici ya kasa karasawa wajenta balle ma yayi
mata sannu yake mata ihu cikin kanshi
"Wani cikin Saratu? Bakya tausayin jikin ki? Ina
kika samo karfin zuciyar sake shafe wasu
awanni cikin ciwo na nakuda?"
Kamar cikin ita ta bawa kanta shi, ita kadai ta
yanke hukuncin samun shi, bashi da wata rawa
daya taka. Sai dai iya laulayin da tayi na wannan
cikin ya daga darajar mace a idanuwan shi ta
wani fanni da sai yanzun zuciyar shi ta bude ya
fahimta. Karfin hali da Allah yayi wa mace mai
girma ne. Ya tabbata inda shi ya sha wahalar da
tasha lokacin haihuwar Salim, da ba shimfida
kawai zasu rababa harda gida.
"Ke na fara fadawa..."
Ya dora kamar hakan ya isa ya wanke mata
ciwon daya dirar mata, wani irin ciwo daya soki
Lubna sufyan
Hausabook.com 330
kahon zuciyarta har abinda yake cikinta ya
amsa. Kishi na ban mamaki nasa har duhu-duhu
take gani. Tasani, duk fitar da zaiyi sai zuciyarta
tayi ciwo, sai tunani daban-daban ya ziyarceta,
dawa yake raba mata kanshi? Wacece shimfida
daya dashi yana nuna mata abinda take dauka
soyayyar shi ce mai tsayawa a zuciya. Waya rike
a jikin shi? Balle kuma taji kamshin shi ya
bambanta, tasan wata ta kwanta a kirjin daya
kamata ya zama wajenta ne ita kadai, hannuwan
shi ita kadai suke yiwa rumfa sai yaran su idan
ya dauke shi, sai sauran da zata haifo masa
saboda ita kadai Hammadi ya haifa, ita kadai
tana da burin cika gidanta da zuri'ar da take
fatan a nade duniyar da wani daga jinin
Hammadi a cikinta.
Yau kuma abinda take takama zata nunawa
sauran matan da yake bi, tayi tinkaho dashi.
Idan hanya ta hadasu ta daga Salim ta nuna
musu, yanda take da wani bangare na Julde da a
cikinsu babu wanda zai taba samu. Yanda jininta
da jininshi suke yawo a jikin Salim din. Ta ajiye
shi a gefe ta fada musu yanda duka Marake
kowa ya shaida auren su, kowa ta wuce zai
Lubna sufyan
Hausabook.com 331
kirata da matar shi, wani abu da babu macen da
zata taba samu. Shine yake fada mata zata raba
da wata? Gidanta, gidansu, wata zai kawo ya
saka a ciki?
"Wacece?"
Ta tambaya a tsakanin numfashi
"Julde wacece? Wa zaka aura?"
Ta karasa tana kallon shi, tana so taji, da wa zai
rabata mata abu daya da ta dauka mallakinta ne
har abada
"Mero...yar uwar Bukar ce"
Batasan dariya ta kubce mata ba, ba kuma
zatace ga daga inda ta fito ba. Daman mana, ta
saba raba abubuwa da Bukar, ciki harda
Hammadi, harda mahaifinta da ta taso ta ga
yana nuna ma Bukar kalar kaunar da bai taba
nuna mata ba, yana cire hannunshi daga kan
abinda yake ci ya tura a gaban Bukar din bayan
tana zaune a gefen shi. Taji yanda uwar rikonta,
yanda Abu bata da sunan da take ambata sai
Bukar. Kamar shine abu mafi kyawu da bashida
wani gurbataccen yanayi a tare dashi da suka
Lubna sufyan
Hausabook.com 332
fara gani a rayuwar su, kamar a idanuwansu
babu yaron da nagartar shi zata isa idanuwan su
balle har su aunata da ta Bukar.
Tunda taga Datti ya tsane shi ta fara tayashi
saboda a wajenta, tsanar da Datti yayi masa
kawai ta isheta, sai ya hada da wani irin kishin
shi da takeyi. Saboda ta tsani raba abubuwan da
take tunanin natane da wasu, ta tsani hakan fiye
da komai a duniya. Da ya yanke hukuncin tafiya
tafi kowa murna, tafi kowa addu'ar idan ya tafi
karya dawo, ya zauna can har abada, ya fita daga
rayuwar su. Sai gashi lokaci zuwa lokaci saiya
dawo, saiya kara tuna mata da yanda ta tsane
shi, ta tsani murmushin shi da kamar baisan
wata damuwa a duniya ba. Son da Julde yake
masa bai isa ba? Bai isa ba sai Julden ya auro
mata yar uwar Bukar? Me yasa babu wani abu
na alkhairi da yake tare da Bukar ne?
Tsanar shi ce ta ninku a zuciyarta kamar shi zai
dauki auren Mero ya bawa Julde.
"Ka fita Julde, ka fita karka dawo na wasu
kwanaki bana son ganinka wallahi"
Ta karasa muryarta na karyewa
Lubna sufyan
Hausabook.com 333
"Saratu..."
Ya kira muryar shi cike da wani irin taushi
"Haukana kake son gani? Kalar haukan da ko a
labarai baka taba cin karo dashi ba? Ka cigaba
da tsaya mun a cikin dakin bayan na baka zabin
da bani dashi!"
Ta karasa cikin wani irin karaji daya saka shi
fita daga dakin, badan yana tsoronta ba, sai don
abu biyu, cikin dake jikinta, da kuma matsayin
daya san tana dashi a wajen Datti, Datti da yake
so ya tsaya masa a wajen neman auren Mero, ba
zaiso ganin haukan da take ikirari ba, wannan
karin babu riba a cikin biye mata. Shisa ya fita
yana bata lokacin data nuna masa tana bukata.
Har zuwa lokacin da Datti yaje nema masa
auren Mero, da ga mamakin su dukansu ba'a
hana masa ba. Abinda basu sani ba su duka
shine babu yanda Musa baiyi da Mero ba. Har
karatun da yasan tana so yayi amfani dashi
"Na hakura da karatun Kawu"
Lubna sufyan
Hausabook.com 334
Tace cikin wata karamar murya, saiya sake
komawa fadan daya bari yana daukar lallashin
daya dauka zaiyi tasiri a kanta.
"Ba zaki sake zuwa Maraken nan ba tunda baki
da hankali Mero"
A daren da yayi wannan furucin, safiyar Mero ta
sulale tabar masa gidan, tana daga masa hankali
tana kuma tuna masa girman amanarta da take
a hannun shi. Saiya biyota har Maraken, saboda
ta tabbatar masa zata zabi Julde ne akansu,
kowanne hukunci zasu dauka akanta ba zaiyi
wani tasiri ba.
"Yaran yanzun tsoro suke bani Musa, rayuwar
mu da tasu ta bambanta, idan suna son abu babu
wanda ya isa ya tankwara su... Yana sonta, da
kaina nayi masa magana yace aurenta zaiyi. Ni
da mai mu godewa Allah da ya ajiye halayen da
muke ganin katanga ne da bashi aurenta a gefe,
ya nemi mallakarta ta hanyar da duka ba
zamuyi dana sani ba..."
A fuskar Musa zakaga ba haka yaso ba, akwai
yaron amintaccen abokin shi da yake ta nuna
alamar yana son Mero, yaro dan boko, Baban ma
Lubna sufyan
Hausabook.com 335
ya fadawa Musa ya samu aikin koyarwa a garin
Kaduna. Wanda ya taso a kauye ya samu cigaba
na barin kauyen zuwa rayuwar da tafi ta cikin
shi inganci abin ayi masa murna ne. Sai ita? Da
ta tashi a birni zata jajibawa kanta zaman
kauye? Kauyenma da yaron da bincike ya nuna
ko ilimin muhammadiya ma bashida wadatar
shi balle kuma na zamanin. Ta kowacce fuska a
ganin Musa, Mero ba sa'ar auren Julde bace ba.
Kasancewar shi dan kauye ma bashi bane abu
mafi girma, halayen shi da basu da kyau sunfi
komai tashin hankali
"Idan bai riketa bafa? Baabuga idan ya
sakkota?"
Musa ya tambaya, jinjina kai Baabuga yayi
"Nayi wannan tunanin, amman ya zamuyi? Sai
mu dauki hakan shima a cikin kaddararta
kamar haduwa dashi, gara komai ya faru
karkashin inuwar aure, idan bai riketa ba, babu
wanda zaiki aurenta, illar da take cikin kin aura
mata shi tafi ta aura mata shi tashin hankali"
Lubna sufyan
Hausabook.com 336
Zabine sukayi mai wahala, daga Baabuga har
Musa, zabin da yake wa iyaye da yawa wahala.
Saboda suna hango abinda yaran basa hangowa,
suna hango musu zaman aure da mutanen da
tsarin rayuwar su gabaki daya basu dorashi a
nagartacciyar hanya ba, a cikin wannan hangen
nesa sai su kasa ganin abinda yake kusa dasu,
yake gab da fuskar su, amman idanuwan su
sunyi nisan kiwo. Zabin na yaran ne, a wannan
matakin nasiha, kokarin fahimtarwa shine na
iyayen, idan har yaran suka cigaba da toshe
kunnuwan su da rufe idanuwan su daga hasken
da ake ta nuna musa. Sai abar su da duhun, sai
abarsu su dandana duk wani firgici da tashin
hankali da yake cikin duhun, da kansu zasu
miko hannuwa suna neman taimakon iyayen da
suka ture daga farko.
Zabi ne da Datti ya kasa, ya kasa akan Yelwa da
Kabiru, ya kasa barinta tayi kuskuren da yake
tunani, ko babu komai kuskuren natane, a wasu
matakai na rayuwa, duk yanda iyaye zasu so,
duk kumajin su, duk shige da ficensu ba zasu iya
kare yaransu daga wani kuskuren ba, sai dai su
tsaya tare dasu bayan aikata kuskuren, su
Lubna sufyan
Hausabook.com 337
tayasu gyara shi idan mai gyaruwa ne, su tayasu
tabbatar da basu sake maimaita irin shi a karo
na biyu ba, ko kuma su tayasu daukar nauyin
kuskuren da suka aikata. Saiya nemi hada
lokacin auren Julden da sauran kwanakin da
suka rage ma na Yelwa.
Sai daren auren yazo ma gabaki dayansu a
birkice. Cike kuma da taraddadin inda Yelwa ta
tafi saboda bayan kayan jikinta da kuma
mayafinta bata dauki ko da allura ba. Daga
yammacin zuwa daren babu inda ba'a duba ba a
cikin kauyen Marake, wanda ma yaganta ba'a
samu ba. Haka suka waye gari cikin wannan
tashin hankalin da bai hana daura auren Julde
da Mero ba, saboda Datti yace a daura, wani abu
ko guda dayane ya tafi akan yanda suka tsara
ranar. Amman yininta ma anyi shine wajen
karade makotan kauyen nasu cikin nema da
kuma cigiyarta. Babu wani labari, haka Datti ya
shigo cikin gidan yana kallon Dije da ta dago
kanta ta kalle shi.
Su duka kaman an ninka musu shekarunsu
saboda tashin hankali, kafafuwan shi na rawa ya
karasa wajenta, ya riko hannunta, hawayen shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 338
na rigan nata zubowa. A karo na farko yana dora
ayar tambaya akan abinda yayi mai zafi haka
"Wanne zunubi na aikata Dije? Me nayi haka?
Soyayyar da nake musu laifi ce?"
Yake fadi numfashin shi na wani irin fita kamar
mai cutar numfashi. Kaf Marake babu wanda zai
taba fahimtar tashin hankalin da suke a lokacin
sai wanda ya taba shiga kwatancin halin da suke
ciki, wanda ya taba rasa yaro ta hanyar mutuwa
ya kuma duba gabas da yamma, kudu da arewa
yana rasa wani yaron, wannan karin ta hanya
mafi wahala. Saboda a tare da mutuwa babu
taraddadi, a tare da mutuwa idan ka kalli kofa
sai dai a wautar tunani, kasan ka fita da gawa,
ka saka a kabari kabi da kasa, ba kuma zata fito
ta dawo ba. Hakuri ba zabi bane ba, dole ne.
Yanzun fa? Ta ina zasu fara? Hakuri ba zabi bane
ba yanzun, babu shima a cikin abinda yake
faruwa dasu. Yelwa ce, ina zataje? Yelwa da a
cikin Marake ma ba ko ina ta taba takawa ba.
Ina zasu fara nemanta?
Sai dai wannan kaddarar da tafiyarta ta fara
Lubna sufyan
Hausabook.com 339
Wadda dawowarta zata dasa tafi wannan.
Gani yake kamar idanuwan shi ya rufe ranar da
Mero ta tako cikin gidan shi a matsayin mata, ya
bude su ya ganta rike da rabon da suka samu, ya
ganta rike da dansu Haidar. Ba akan shi aka fara
masa haihuwa ba, tun da ga Salim, ga kuma
Fadila, ga kuma wani cikin a jikin Saratu, dan
haihuwar gab da gab takeyi. Abubuwa da yawa
sun faru daga ran daren aurensu zuwa yanzun.
A cikin wannan abubuwan akwai batan Yelwa
da har yanzun suke cikin duban hanya don
ganin ta inda zata bullo.
Mutum, ba dabba ba, a wayi gari ace an nema
sama ko kasa an rasa? Kwanaki bakwai bayan
bacewarta, bai san abinda Dije take ji ba,
hakama Datti, ya shiga gidan ya same su zaune
duka suna kuka, babu wanda yake yunkurin
bawa wani hakuri a cikinsu, sai ya juya kawai
batare da yace musu komai ba, shima idan ya
fita da safe hanyoyi kawai ya kebi, inda duk
kafarshi ta dauke shi sai duhu ya farayi tukunna
ya dawo. Yayi tunanin duniya ko a cikin
Lubna sufyan
Hausabook.com 340
hirarrakinsu Yelwa tayi wata magana da zata
saka shi fahimtar inda take, amman ya rasa.
Rabi da kwatar hankalin shi yana kan dokin
ganin Mero ta zama mallakin shine, gata a cikin
gidan shi, su kwana su tashi daki daya, amman
bashida nutsuwar nuna mata tarin kaunar da
yakeyi mata
"Akwai abinda zan maka ka kasa yafe mun
Hamma?"
Ta tambaye shi kwanaki biyu kafin daurin
auren su, cike da mamakin tambayar ya girgiza
mata kai
"Abinda nayi maka wanda ka sani da wanda
baka sani ba, da ma wanda zanyi maka a gaba
duk ka yafe mun?"
Murmushi yayi, yasan bata son Modibbo,
amman a cikin idanuwanta yake ganin wani
yanayi na mika kai, da kuma sallamawa da
cewar bata da wani zabin daya wuce hakuri da
auren
"Auren nan bashi bane karshen duniyar ki
Yelwa, ki kwantar da hankalin ki, nima nayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 341
nawa binciken, Modibbo bashida wani hali
marar kyau"
Murmushin da ta mayar masa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 27