son
wani akan shi, baya so sam, shisa take kokarin
danne yanda take kaunar Bukar dan batason
Lubna sufyan
Hausabook.com 179
wannan kishin na Julde ya gifta tsakanin su.
Bukar dinma a gaban Julde saiya daina bata
labarin Hamman shi
"Daada baki ji karatun da Hamma yake yi ba,
kamar ya sammun wani sashi na kwakwalwar
shi"
A yanayin yanda yake yawan maganar Hamman
shi ne tasan irin girman kaunar dake tsakanin
su. Duk da Bukar ne, kowama so yake, kowa ma
nunawa kauna yake. Amman kaunar da yakeyi
wa Hamman nan nashi daban take, kuma da
alama yana daga cikin manyan 'yaran Baabuga
da yakan tura neman karatu gari-gari, cikin
wanda zamanta bai tsawaita a gidan shi ba balle
ta san su.
"Hamma Am fa ya haddace sittin, rubutawa yake
yi yanzun"
Bukar ya karasa maganar da yanayin nan mai
cike da alfahari, a yanayin yanda yake yawan
maganar Hamman shi ne tasan irin girman
kaunar dake tsakanin su. Duk da Bukar ne,
kowama so yake, kowa ma nunawa kauna yake.
Amman kaunar da yakeyi wa Hamman nan
Lubna sufyan
Hausabook.com 180
nashi daban take, tunda ya fara mata zancen shi
alamu suka nuna yana daga cikin manyan 'yaran
Baabuga da yakan tura neman karatu gari-gari,
cikin wanda zamanta bai tsawaita a gidan shi ba
balle ta san su. Duk wannan kaunar bata dameta
ba, a hankalima sai ta bude ido taji tana taya
Bukar son 'yan uwan shi, son Hamman nan
nashi.
Da ta sani, in da tasan cewa wannan kaunar zata
kawo su inda suke yanzun da tayi komai a
karkashin ikonta ta yanke wannan kaunar
"Ina so zan bi Hamma Maiduguri inda yake
karatu wannan karin Daada, ina burin yin
karatu mai zurfi kamar na shi"
Maganganun Bukar suka daketa, irin duka na
ruwan saman da baka ga haduwar hadarin shi
ba, bakaji yayyafi ba, karfin ruwan daya dirar
maka kawai kaji
"Ke na fara gayawa"
Bukar ya dora kamar hakan ya isa ya dai-dai
jirkitar da yayi ma duniyarta gabaki daya
Lubna sufyan
Hausabook.com 181
"Idan shawarata kake nema bana so kaje, idan
ra'ayina kake son ji babu inda nake so kaje. Idan
kuma gayamun kakeyi saboda ban isa ba Bukar
kayi abinda kake so"
Tace tana mikewa tabar masa wajen. Ta dauka
zai hakura, har kasan zuciyarta ta dauka zai
hakura saboda Bukar na da gudun bacin rai,
nata fiye da na kowa. Amman kaddarar da take
fisgar shi saita rinjayi komai. Da yaga daga
Hammadi har Abu sun kasa shawo masa kanta
saiya nufi Baba, Baba da yayi bata umarni a
maimakon ya tausheta
"Me yasa zaki hana shi tafiya tunda yana so?
Namiji ne, idan karatu baisa yayi nisa da gida ba,
wata rana neman na kan shi zai iya nisanta shi
da gida. Ki godema Allah daya baki yaro mai
hankali irin Bukar, ke in ba rashin hankali ba ai
abin murna ne ace ya dawo da sittin akan shi"
Hawaye takeyi da tun daga ranar har zuwa yau
take jin sun kasa tsagaita mata. Banda nisan
Maiduguri da Marake babu abinda take
hangowa, yanda duk suke labarta mata kaurin
sunan da yankin yayi a wajen ilimin addini mai
Lubna sufyan
Hausabook.com 182
inganci kunnuwanta basa karasawa da zancen
zuwa zuciyarta. Shima Bukar din da yace
"Ida na tafi ba saina gama zan dawo ba Daada,
irin yanda Hamma yakeyi zan dingayi nima. Duk
bayan wasu watanni zanzo gida inyi sati kamar
yanda yakeyi"
Jin shi kawai tayi, nisan da take ji yayi da
zuciyarta na kara tsayi yana barin wani fili da
batasan me zatayi da shi ba
"Dan Allah Daada, bana so in tafi zuciyarki bata
aminta da zuwan ba"
Nan ma babu abinda tace masa, saboda karya
bata taba shiga tsakaninsu ba, bata so ta fara. Ba
zatace masa ta aminta ba, ba zata ce masa zatayi
komai don yabar wannan tafiyar ba. Hankalinta
bai kara tashi ba sai da tagan shi da kullin kayan
shi, da tarkacen da Abu ta hada mishi, duk
abinda take tunanin zai bukata, ita babu wani
abu data tanada, tunanin ma baizo mata ba
saboda tanata addu'ar Allah ya canza mata
zuciyar shi, da kanshi yace ya fasa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 183
"Daada me yasa zai tafi? Dole sai can? Nan babu
makaranta?"
Yelwa ta karasa maganar idanuwanta cike taf da
hawaye
"Shi ka zaba ko Bukar? Bayan nace maka ni
kadai ne Hamman ka"
Murmushi Bukar din yayi yana girgiza ma Julde
kai
"Bashi na zaba ba Hamma, karatu na zaba"
Su duka basa so, zuciyoyin su basu aminta da
tafiyar ba. Babu yanda zasuyi da Bukar ne tunda
ya kafe, suna ji suna gani ya tafi yabar su da
kewar shi da suka fara tun kafin a kwana. Yelwa
ma Saratu ce ta jata suka shige gidan Abu
saboda kukan da takeyi, Julde ko raka Bukar
kinyi yayi daga baya, sai da yaga ya bace mishi,
ya sha kwana sannan ya bishi da gudu, ko ya
dawo ba gidanta ya shigo ba, sai dai in ya shiga
gidan Abu ne.
"Kiyi hakuri Dije, ki taushi zuciyarki tunda yace
duk bayan wasu watanni zai dawo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 184
Yanda Abu ta karasa maganar da wani
nisantaccen yanayi a muryarta yasa Dije dagowa
ta kalleta. Akwai kyallin hawaye a idanuwan
Abu da taketa kokarin dannewa. Bukar ba daga
jikinta ya fito ba, daga farko ma tana son
yaronne saboda ya fito daga jikin Dije, saboda
kaunar da takeyi wa Dije mai girma ce. Amman
daya dawo hannunta sai ya tabbatar mata ko da
Dije, ko babu Dije idan hanya ta hadasu zata
kaunace shi, zata so shi wata irin soyayya da ba
zata kwatantu ba. Rabon da tayi baccin kirki tun
ranar da Bukar yazo mata da maganar yana so
ya bi Hamman shi. Amman sai ta danne nata
ciwon, ta danne nata zafin zuciyar saboda ta
tausashi Dije.
"Adda"
Dije ta kira muryarta a karye, kunyar Abu na
kamata, tunda aka soma maganar tafiyar Bukar
ta manta cewa a hannun Abu yake, tama manta
cewa itama Abu zata iya jin ciwon tafiyar Bukar
din ko da bai kai nata ba.
"Muyi masa addu'a kawai... Allah ya tsare shi ya
taimake shi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 185
Kai Dije ta daga mata, tana sake share hawayen
da suka zubo mata
"Bari inje gida, yamma nayi in dora tuwo"
Kan dai Dije ta sake dagawa, duk da taga
hawayen da Abu tayi saurin daukewa da yatsa.
Gara taje gida tayi nata kukan ko zata samu
sauki itama.
*
Rigar da Datti ya cire bayan ta dawo ta dauke
daga kan gadon tana kokarin ninketa, sai taji
kamar goro a cikin aljihun, hannu tasa ta ciro,
harda dabino ma
"Ina ka samo goro da dabino?"
Ta tambaye shi, tana kallon inda yake zaune
yana kokarin saka zariya a jikin wandon sakin
dake hannun shi. Lokaci ya koya mata gujema
duk wata magana ta Bukar a tsakanin su.
Saboda hakan baya jan komai sai fadan da suke
shafe kwanaki bai kare ba, koma tace Datti yake
shafe kwanaki bai daina ba. Bata da karfin biye
masa, ta kowacce fuska sai da ya tabbatar ta
gane fada ko jayayya dashi babu wata riba. Ko
Lubna sufyan
Hausabook.com 186
na rana daya bai nuna mata yasan Bukar ya tafi
Maiduguri ba, baima nuna ya kula da baya nan
ba, abin yayi mata ciwo na ban mamaki.
Amman a zaman su yana abubuwa da yawa da
suke mata ciwo, abubuwan da ta koyi shanyewa
tunda ko tayi magana a kai ba zai sauya komai
ba. Hammadi da kan shi ya saka su Julde a
makarantar allo, amman Julde sai yayi sati biyu
baije ba, randa Datti yaga sawun Bulala kwance
a damtsen hannun Yelwa yayi tashin hankalin
da har saida Hammadi ya biye masa
"Saratu ce kake son nuna mun ban isa da ita ba,
sai kasa taje makarantar ita, amman ni dai nawa
yaran dana isa dasu sun gama zuwa. Babu katon
banzar da zai kamamun yara yana duka saboda
karatu"
Hammadi kyale shi yayi, sai dai Saratu ta nuna
ma Hammadi cewa abinda Datti yake so itama
shi take so, abinda baya so itama bata so. Ko Abu
ta tirsasa mata tafiya makarantar sai tayi rashin
kunyarta da babu wanda ta cirewa hula banda
Datti, sannan zata tafi, idan ta tafin ma ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 187
makarantar take zuwa ba, waje take samu tayi
zamanta har sai lokacin tashi tukunna
"Mtswww"
Tsakin da Datti yaja ya maida hankalin Dije kan
shi
"Hamma ne fa ya jani auren nan na wajen yar
Dammud'o....lalataccen aure ma irin wannan"
Kallon rashin fahimta Dije tayi masa
"Kad'o fa ya dauka yaba, yana bafullatanin usul
ya dauki yarinya ya hadata da bahaushe, Allah
tsine wannan hadin. Kinga son da nakewa Yelwa
ko? Gara in binneta da in hadata aure da
bahaushe, inyi kuka in hakura"
Wannan karin a tsorace Dije ta kalle shi,
maganganun shi na taba zuciyarta. Tasan baya
son hausawa, wata irin kiyayya yake musu da
batasan tushenta ba. Tunda a iya saninta babu
abinda bahaushe yayi masa banda bambancin
yare, bai kuma taba bata labari ko akwai wani
abu daya taba faruwa tsakanin shi, ko wani
nashi da bahaushe da yasa yayi musu wannan
tsanar ba. Itama zuwa yanzun ta tabbata da bata
Lubna sufyan
Hausabook.com 188
biyo Innarta ba, da batayi kama da fulani ba, da
bai yara mata yaji ta fahimta ba, yaji ta amsa shi,
tun ranar farko daya ganta ba zai taba
amincewa da aurenta ba.
Yaron da yake magana Dije ta tabbata in dai
haihuwa da kuma girman Marake ne zai wahala
ace bayajin fulatanci. Saboda cudanya da juna
tasa har hausawan cikin ma suna yarawa, duk
da kanayi Datti yake gane kai ba bafullatani
bane, yakan ce suna bata wasu kalaman wajen
furtawa
"Bafa yare ake dubawa ba a wajen aure Datti,
kyawun hali ake dubawa"
Daga kai yayi yana dubanta
"Yare zan fara dubawa, ko Julde ba zai auri
bahaushiya ba"
Murmushin takaici tayi
"To ai kai ka auri bahaushiyar, kuma jinin
hausawa na yawo a jikin su Julde"
Shima murmushin yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 189
"Allah ya tsare su, bangarenki na fulani ne
kawai tare da 'ya'ya na Dije, bangarenki na
fulani na aura, da kuma shi kadai nake cudanya"
Sai taji ya bata dariya. Dariyar da shigowar Julde
ta katse mata
"Daada hannuna zai kone, ki fito ki karba"
Yake fadi, don sallama bata cikin abinda yake
yawaita yi don zai shiga waje, musamman idan
yayi daga farko, to a wajen shi ta dauke ta yini
guda ko zai shiga ya fita gidan sau goma
"Ya za'ayi ka rungumo kunu a langa?"
Dije ta fadi tana karbar kwanon daya dauki
mugun zafi daga hannun shi tana ajiyewa a kasa,
baiko saurareta ba ya fice yana komawa inda ya
fito. Harya shiga gidan murza hannuwan shi
yakeyi a jikin rigar shi cikin yanayin da yasa
Saratu fadin
"Me ya sami hannun?"
Tana daukar kosai ta kai bakinta
"Konewa nayi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 190
Ya amsa a takaice, radadin da tafukan shi sukeyi
na shiga har kwanyar shi. Tashi tayi daga inda
take zaune tana karasawa inda yake tsaya,
batare da tace masa komai ba ta kamo hannun
shi guda daya tana ware tafin hadi da saka nata
a ciki ta murza masa. Nata hannun yake bi da
kallo da kuma yatsunta, yatsunta da suke dauke
da farata farare qal, yanayin taushin su a cikin
nashi kamar bata taba aikin wahala ba tunda
take.
"Sannu... Muga dayan"
Ta fadi tana sakin wannan, tsintar kanshi yayi
da mika mata dayan hannun nashi, ta murza
masa kamar dayan, tana cikin yine Yelwa da taje
kai ma su Dije kosai ta dawo
"Me ya same ka?"
Ta fadi tana karasawa ta janye hannun shi daga
cikin na Saratu tana dubawa, sai dai bata ga
komai ba
"Konewa yayi"
Saratu ta amsata, sosai Yelwa take duba hannun
nashi, ko da bai kone ba jar fatar shi tasa bata ga
Lubna sufyan
Hausabook.com 191
wani bambanci ba ita. Daga ido tayi tana kallon
fuskar shi, amman ba ita yake kallo ba,
hannunta yake kallo, a zahirance yafi na Saratu
kyau, yafi shi komai. Amman baiji abinda yaji da
nata yake cikin nashi ba. Shisa ya zare hannun
nashi, so yake ya kara rike na Saratun, yaji ko
yanayin zai kara dawo masa, yaga ko zai gane
dalilin da zaisa yaji abinda yaji a karo na farko
bayan ya tuna lokutta masu yawa da ya rike
hannunta, amman a rijistar kwakwalar shi babu
wannan yanayin.
Babu dumin nan da yaji ya ratsa ta cikin hannun
nashi yakai ko ina na jikin shi. Ya taba hannun
Yelwa yanzun baiji dumin ba. Hakan na nufin a
na Saratu kawai yake kenan? Ji yayi yana so ya
gwada, yana so ya sake jin dumin nan, yana
kuma so yasan idan a hannun Saratu hakan ya
tsaya ko kuma akwai wasu mata da hannuwan
su ke da dumi kamar nata. Jin idan ya tsaya zai
koma inda Saratu take ya riko hannunta yasa
shi juyawa ya fice daga gidan.
Sai dai fitar shi ba zata sake kaddara ba
Fitar shi ba zata sake komai ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 192
Komai da yanzun ne zai fara
Yelwa take kallo, idanuwanta a rufe, Saratu da
take gabanta tana mata kwalliya, ta diga mata
kwallin daya fara tun daga goshinta zuwa karan
hancinta, da alama digon zai dire ne har habarta
cikin kwalliyar su ta fulani, bakinta ma a zane
yake da bakin kwallin daya zauna das yana kara
fito da hasken fatarta da kamar tana girma yana
kara fitowa ne, girman su harya daina bata
mamaki. Ba son kai Dije zatayi ba idan tace kaf
kauyen babu mai kyawun Yelwa, ko da bata fada
ba, mutane da yawa sun fada, ita da kanta wasu
lokuttan gani takeyi kamar ba daga jikinta
Yelwa ta fito ba.
Yanda take yanzun, kyawunta kamar an cirota
daga cikin zane. Kallon ta Saratu ta danyi
"Yawwa an gama"
Bude idanuwa Yelwa tayi tana saka su cikin na
Saratu
"Nayi kyau?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 193
Ta tambaya tana duba gefenta in da ta ajiye dan
mudubin da ta dauka ta haska fuskarta, tana
danyin farr da idanuwa cike da son ganin
yanayin yanda kwallin ya zanu cikin idon nata.
Kayan sakine a jikinta farare da suka sha ado,
sai sarkar su ta fulani shake a wuyanta, ta daura
dankwalin da harya fara soshewa amman son da
take masa yaki bari ta iya bayar dashi, Abu ce ta
bata shi, ta manta ko tun yaushe. Amman tana
son dankwalin, zanen ganye ne a jiki da koren
su ya fito sosai
"Muje?"
Ta fadi tana duban Saratu, ba zaka kirata
mummuna ba, amman idan har tana tare da
Yelwa babu yanda za'ayi ka ga nata kyawun,
bata da hasken fata kamar na su Julde, amman
kuma ba baka bace ba. tana da madaidaicin
tsayi, yanzun da alamun 'yan matanci ya fara
nunawa a jikinta zaka ga kalar cikar halittar da
take da shi, batayi sirantaka irin wadda aka san
akasarin fulani da ita ba. Sai dai kallo daya
zakayi ma yanayin fuskarta da bakinta da bata
cika sauke labban ba, a dage suke kusan ko da
yaushe, alamar dake nuna saurin fushinta da
Lubna sufyan
Hausabook.com 194
yanda take a shirya da ta mayar maka da
magana idan har bukatan hakan ta taso.
"Wai Daada babu abinda za'a siyo miki?"
Yelwa ta sake tambaya a karo na ba adadi tana
mikewa
"Babu fa, kuma yawo ne zai kaiku ba don akwai
abinda zaku siya ba"
Kafin Yelwa ta amsa Saratu data juya
idanuwanta ta karbe zancen
"Ita fa kasuwa baka sanin kana bukatar wani
abin saika shiga"
Numfasawa Daada tayi batace komai ba, lokutta
da yawa bata cewa komai in dai har zancen ya
zamana tsakaninta da Saratu ne, tana da hakuri,
amman bata son raini, tun kafin Saratu tayi
girman da za'a daina amfani da yarinta ana ma
rashin kunyarta uzuri bata cika son yarinyar ba.
Zuciyarta ta kasa natsuwa da ita, sai halayenta
suka hadu suna kara sakawa ta fita harkarta in
ba ta kama dole ba. Ko Abu ta yiwa rashin kunya
kau da kai takeyi. Tunda idan ta shigama babu
Lubna sufyan
Hausabook.com 195
wani abu da hakan zai haifar, saima fadan da
Datti zai rufeta dashi idan yaji.
Akan Saratu sai ya manta wacece Abu, saiya
manta yanda a ko ina ya kamata ace ya kasance
cikin mutanen da zasu iya bada shaidar halayen
Abu, sai ya manta cewar ko Saratu bata fito daga
ciki Abu ba, ko da ba ita take riketa ba ya
kamata ace tafi karfin Saratu ta kalleta ta mayar
mata da magana ko don dattako da cikar
kamalar da suke shimfide a fuskar Abun. Rashin
kunyar Saratu irin ta Datti ce, babu wanda ya
wuce ta a wajen su muddin tunaninsu ya basu
cewa anbi takan sune. da farko Dije ta dauka
Abu kadai take yiwa, sai a hankali ta kula da har
Hammadi ma bai wuce ta mayar masa da
magana ba, baifi ta hade rai tana surutai kasakasa idan yayi mata fada akan wani abu ba
"Allah ya shiryeki Saratu, Allah ya shiryeki"
Ya kan fadi cike da wani yanayi a muryar shi,
komai. Banda fatan shiriya babu wani abu da
zaka iya bin Saratu da shi. Sai kuma ido, kamar
yanda ta bisu da shi daga ita har Yelwa har suka
fice daga cikin gidan hannuwan su cikin na juna,
Lubna sufyan
Hausabook.com 196
bambanci shekarun su bai rage shakuwar da
take tsakanin su ba, duk da kowa yasan kauda
kan Yelwa na daya daga cikin abinda yasa ba'a
yawan jin kansu. Suna karya kwanar gidan suna
hango Julde, zuciyar Saratu ta doka a cikin
kirjinta, dokawar da ganin shi kawai kan sa
hakan ta faru. Tun kafin ya karaso yake musu
murmushi, ko tace yake yiwa Yelwa murmushi.
Farin wandone a jikin shi da rigar saki, ya tara
suma a tsakiyar kan shi, yayi kitso dai-dai a
kowanne gefe na kan shi da ya saka sauran
sumar a tsakiya, sai sarka ta wuri da take daure
a wuyan shi. Banda kwallin da yake idanuwan
shi babu zanen komai
"Kai ba bororo bane ba..."
Datti yace masa ranar farko da yayi kitso, kujera
yaja ya zaunar da shi, yasa almakashi yana saita
masa sumar da ya tara ta daga gaba tafi sauran
cika, ba kamar sumar Bukar da take luf ba, tashi
a cunkushe take, kuma yafi sonta a hakan. Idan
ya kalli sa'annin shi a Marake, ya kalli
fuskokinsu yaga tsagun fulani reras saiya kara
Lubna sufyan
Hausabook.com 197
godewa Datti da bai musu wannan zanen a fuska
ba. Daya taba tambaya haka yace masa
"Da muna da tsage na gado da na ganshi a fuskar
Babana, ko ta Inna ta, da kuma anyi mana
kagani a fuskata... Fulanin yankin da muka fito
daga shi sukanyi adon sune da kaloli daban
daban a fuska a maimakon tsagar... Idan kana so
sai in koya maka"
Dariya kawai yayi, bayason komai banda kwalli
a fuskar shi, wani lokacin Yelwa da ita take
masa kitson kan saka masa wuri guda biyu ko
hudu a jikin kowanne kitso, bashi da zuciyar da
zai hanata
"Hamma Am"
Yelwa ta kira shi tana fadada murmushin ta,
tana kallon shi kamar duka duniya bata da
wanda yafi mata shi. Shima murmushin yake
mata, tilon kanwar shi da zai iya komai dominta
"Ina zaki je?"
Ya tambaya kamar baiga Saratu tare ita ba,
abinda yayi mata ciwo har kasan ranta. Da zata
iya da ta dinga share shi irin yanda yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 198
shareta, da tayi watsi da lamurran shi kamar
yanda yakeyi da nata. Da ta ganshi taki ganin
shi, ta ji shi taki jin shi. Amman ta kasa, idan ta
gan shi babu abinda take so irin ya kulata, idan
bai kulata ba zata kula shi ko da ba zai amsa ba.
Ta taso tana jin labarin soyayyar dake tsakanin
Hammadi da Abu, da ta fara hankalin fahimtar
wannan soyayyar da bata boyuwa ga kowa sai
taji tana son kwatankwacinta tare da Julde.
Tana hankali tana kara rage abubuwa da yawa
da suke kawo musu rashin jituwa tsakanin su,
sai dai yana nuna mata kamar lokaci ya kure.
Yanzun fiye da lokuttan baya, yana tsaye a
gabanta kamar yau din sai ta dinga jin tamkae
idan ta kai hannunta zata iya dangwalo nisan da
yake tsakanin su, nisan da kan sata farkawa
cikin dare ta kasa komawa bacci. Yanda duk
zatayi tunanin aure, tunanin kwana da tashi a
gida daya da wani namiji, hoton Julde ne a
wannan tunanin. Hoton da girman shi ya hana
mata ganin duk wani matashi dake kauyen,
wadanda suke son samun dama a wajenta da
wanda ma bata gabansu.
Lubna sufyan
Hausabook.com 199
Wani zare ta hango a gefen wuyan Julde da
batasan lokacin da ta mika hannunta da nufin
cire masa ba, ta gefen idon shi ya ganta yayi
saurin rike hannunta yana saukewa hadi da
kallonta, wani irin kallo da yasa tsikar jikinta
mikewa tanajin kamar an buge mata
gwiwoyinta ta baya saboda sanyin da sukayi. Ya
sha kallonta, ba zata iya kirga adadin lokuttan
da idanuwansu suka sarke dana juna ba, amman
bai tana mata kallon da yake mata ba yanzun.
Numfashi yaja ya mayar a hankali yana sakin
hannunta, yanajin yanda sakin hannun nata
shine karshen abinda yake son yi. Me yasa
zatayi kokarin taba shi? Ko dan bata san yanda
yake kokawa da kan shi a duk rana ba yanzun
na ganin bata shiga cikin jerin matan da yake
tabawa ba?
Saboda ita ce, saboda tabata zaiyi dai-dai da
tonuwar sirrin da yayi shekaru hudu yana
binnewa yanzun. Sirrin da babu wanda ya sani
"Ba fa zaka bi motar Ikko ba Julde, ba zakayi
wannan nisan ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 200
Datti ya fadi cike da yanayin da yasan bashida
wajen musu. Yanzun ana kai musu amfanin gona
da dabbobi har garin Kano, nacin daya dinga yi
sai da suka hadu shi da Hammadi sannan suka
shawo kan Datti ya bar shi ya fara bin motar
Kano din, amman ba ko da yaushe ba, saboda in
sunje din anayin har sati daya ba'a dawo ba, su
kuma duk bayan watanni biyune ake kai musu
kayan Kano. A garin Kano, iyakacin su Miltara
da Dawanau. Zuwan shi na biyune ya shiga gari
yawo shi da wani yaron babbar mota da suka
hadu anan Miltara da ake kira da Danjuma. Yace
ma Julde shi dan asalin Zamfara ne wani kauye
da Julde ba zai tuna sunan shi ba.
Almajiranci aka turo shi kauyen Badume, fadi
tashi yasa shi fara neman na kanshi harya soma
bin motocin dake zuwa kudu, a haka ya zama
yaron mota, da suke daukar kayan masarufi
daga nan Miltara zuwa Legas da sauran jihohin
kudu. Cikin irin wannan hirarrakin da suketa ba
Julde mamaki har ya fara bashi labarin kauyen
Tafa da yanda sukan yada zango anan idan zasu
je Lagos ko garin Lokoja. Anan yaji labaran da
tunanin shi bai taba kai shi ba, tare da Danjuma
Lubna sufyan
Hausabook.com 201
suka soma shiga sabon gari, Danjuma ya rike
hannun shi ya hada dana Ladi a cikin sabon gari.
Ladi da yake tunanin zai wahala idan bata girmi
Daadar shi ba.
Sai dai tarin shekarun nan ta ajiye a gefe ta bude
masa ido da wata irin rayuwa da ta amsa masa
tarin tambayoyin da suka dade suna masa yawo
a kai, suna kuma bude masa wani shafin guda na
sababbin tambayoyin da ya kosa da yasan amsar
su a lokacin. Duka matane kamar Ladi? Ko suna
da bambanci? Da duk komawar da zaiyi Kano da
yanda yake samun amsar tambayoyin shi. Sai
dai kalubalen na tare da yanda yake son Datti
yabar shi yabi masu zuwa Ikko, saboda ya leka
yaga ya rayuwa a can yake, idanuwan shi su
gane masa labaran da Danjuma yake ta bashi.
A cikin Marake kawai akwai mutane
mabanbanta, haka ma yanda suke gudanar da
rayuwar su. Amman idan ka duba akwai
kamanceceniya saboda duka kauyen nasu da
mutanen ciki bayajin sun kai yawan al'ummar
daya gani a sabon gari. Idan kana waje daya
babu abinda zaka gani, tun randa ya shiga mota
suka hau titi zuciyar shi take gaya masa an haife
Lubna sufyan
Hausabook.com 202
shi a Marake, ya girma a Marake, amman
dawwama a cikin Marake ba nashi bane ba.
Saboda idan duk yabar kauyen babu wani abu
da yake kewa banda 'yan uwan shi da iyayen shi.
Idan zai dauke su subar Marake yana da yakinin
ko na rana daya ba zai taba kewar komai daya
danganci Marake ba.
Sai dai yanzun ba zuwa Ikko bane babban
kalubalen shi, yanda zaiyi da sabuwar rayuwar
da ya koya. Yanda yake tashi da safe yaji babu
abinda yake so daya wuce ya rabi mace. Macen
da tafi kusanci dashi itace Saratu. Duk idan ya
ganta sai yaji kamar tana kara hura masa wutar
da take cine a cikin jikin shi. Shisa ya rage shiga
gidansu, amman idan shi bai shiga ba ita tana
shigowa nasu gidan. Yana ganin giccinta, ko bai
mata magana ba zatayi masa ita, muryarta na
fitowa a hankali kamar a tsorace take saboda
bata da tabbacin zai amsata ko ba zai amsata ba
"Julde"
Takan kira wasu lokuttan, dan tun lokacin
yarinta yasha buge mata baki akan ta kira sunan
shi gatsau kamar shidin sa'anta ne, rashin
Lubna sufyan
Hausabook.com 203
kunyarta da son ganin ta kular dashine yasa ta
cigaba har ta fara sabawa, kafin tace masa
Hamma ana daukar lokaci. Idan ta kira sunan
shi da wannan muryar sai yaji yana so ta
maimaita, yana so yaji ta kara maimaitawa
kamar yanda yake jin mata da yawa sun
maimaita a lokutta mabanbanta a yanayi iri
daya amman cikin muryoyi daban-daban.
"Hamma..."
Muryar Yelwa ta kutsa cikin tunanin shi
"Kuje abinku... Karku dade amman"
Kai ta daga masa tana riko hannun Saratu da ta
daga ido ta kalli Julde, sai taga kamar launin
idanuwan shi sun canza, kamar akwai wani abu
a cikin su da ya girmi fahimtar ta. Yelwa da take
janta tabi suna nufar hanyar kasuwar. Har
lokacin tana jin jikinta a sanyaye, hirar da Yelwa
take janta da itace tasa harta dan warware kafin
su karasa kasuwar da aketa hada-hada. Da yake
sanyi ya fara zuwa ga sabuwar goruba nan da
magarya kamar ba'aso
"Yelwa kinga magarya"
Lubna sufyan
Hausabook.com 204
Cewar Saratu don tana so, duk da tana da sauran
wadda Datti ya kawo mata, wannan din sai taji
ta shigar mata ido
"Wai dan Allah dadin me kikeji a abin nan? Nifa
na tsani ki shata cikin daki wallahi, duk saiya
gume da wari kamar an bude daddawa"
Dariya Saratu tayi
"Magaryar ce take warin daddawa? Saboda
bakya so? To sai na siya"
Saratu ta karasa wajen mai magaryar daya
bajeta a cikin buhu
"Aifa sai kiyita siya. Da rake ma muka karasa
mukai cinikin sanda aka yayyanka mana muka
tafi gida da yafi wannan magaryar"
Saida ta siyi magaryar tukunna ta dago tana
duban Yelwa dake tsaye tana ta bata fuska
"In dai rake ne mu zagaya a duba me kyau mu
siya... Daga shigowar mu harkin fara mu tafi
gida kamar bake kika damu da muzo ba"
Sake bata fuska Yelwa tayi, ita duk yanda zataji
tana son shigowa kasuwa, da ta tako kafarta
Lubna sufyan
Hausabook.com 205
taga mutane cunkushe sai taji hayaniyar na
shigar mata har tsakiyar kai. Bata cika son shiga
mutane da yawa haka ba. Baki ta bude da nufin
yin magana, abinda bai taba faruwa da ita ba ya
faru lokacin da idanuwanta suka gifta ta gefen
kan Saratu suna sauka cikin nashi, kalaman ta
fara ji sun koma mata cikin makoshi tare da
wata irin iska da tasa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 27