Gwaggo ta
taba fada, ba'a so iyaye su tsinewa 'ya'yan su
lalacewa sukeyi"
Wannan karin dariya Julde yayi. In dai a cikin
lalacewa akwai bin mata, ya rigada ya faru dashi
tun kafin Datti ya tsine masa. Shaye-shayen da
ake magana akai, wanda ya gani wasu sunayi bai
taba burge shi ba, saboda bayason ya taba
kusantar abinda zai rabashi da hankalinshi. To
bayan wannan biyun akwai wata lalacewa ne?
Sai ma ta tirsasa shi yayi auren da baya so, idan
ya auri Saratu ba zai daina bin matan daya fara
ba. Ba zai daina ba, shisa baiga amfanin auren
ba. Hankalin Yelwa da bayason gani a tashe yasa
shi nuna mata zaiyi kokarin ganin komai ya
wuce masa, yayi hakuri da maganar.
Amman kayanshi ya hada da nufin barin gidan
da asuba kafin kowa ya fito. Saida yakai kofa ya
fara tunanin inda zai nufa. Sai ya hango Daadar
shi da halin da zata shiga, sai ya hasaso tashin
hankalin da zai saka Yelwa. To ya gudu ma yaje
ina? Saiya dawo, ya kuma ci karo da Datti a
Lubna sufyan
Hausabook.com 235
tsakar gidan, Datti daya kafe shi da ido ta cikin
hasken alfijir daya fara ketowa
"Gudu zakayi?"
Ya tambaya cikin wata irin murya
"Allah ya kwashe maka albarka idan ka fasa
tafiya!"
Ya fadi yana daukar buta ya nufi bayi kamar
yanda yayi niyya. Kamar kuma bai fadi kalaman
da suka saka jikin Julde mutuwa likis ba. Sai yaji
kamar kalaman da suka dira a kunnuwan shi
sun zagaya ko ina na jikin shi suna bin jijiyoyin
shi sannan suka kwanta luf a wani wajen da
suka fi karfin ganin idanuwa. Sai yake jin zaman
nasu kamar wani iri ne na itaciyar da yake jira
ya fara tsiro ya kafa rassa a tare da shi. Lokaci
daya wani irin tsoro ya cika zuciyar shi, tsikar
jikin shi ta mike kamar mai shirin zazzabi. Saiya
koma daki, sallah ma sai da gari ya waye
tangaran tukunna yayita.
Daga ranar ne kuma bai sake daga maganar
cewa baya son Saratu ba. Hidimar bikin duk da
ake tayi da idanuwa yake binsu. Haka Datti ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 236
fita daga lamarin shi gabaki daya, wani abu daya
zame masa sabo. Bayan gaisuwa saiya rasa
abinda zaice mishi, sabanin da, abincin dare ma
kusan ko yaushe tare suke ci sai dai idan a gidan
Hammadi yaci. Sai har Dije tayi bacci tana juyo
hirar su. Komai ya canza duk akan Saratu, duk
akan aurenta. Da Dattin yace masa yaje yaga
gidan da zasu zauna, magana mai tsayi data
hadasu a cikin wata daya da ake ta hidimar
bikin shi
"In dai yayi maka shikenan ba sai na gani ba"
Bai kuma je din ba sai yanzun da aka rakoshi a
matsayin ango. Har suka gama duk wani abu da
yake al'ada a wajen su jin shi yake wani iri.
Asalima yana jin amsa kuwwar amin din data
daure kaddarar shi da ta Saratu waje daya.
Kallonta yake da fararen kayan saki a jikinta da
suka sha ado irin na amaren fulani. Mayafin
kayan da aka ja aka rufe mata fuska da shi. Ya
rasa abinda yake ji. Dakyar ya iya jan kafafuwan
shi ya karasa inda take ya zauna a bakin gadon
bonon da aka shimfide da sabon zanin gado. Iya
dakin idan ka kalla zaka san Saratu 'yar gata ce,
sannan gidan da ta fido kudi ba matsala bane ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 237
Sai da ya jishi a zaune tukunna wata irin gajiya
ta jiki da zuciya ta saukar mishi tana kashe
masa jiki, kafafuwa yaja kan gadon ya matsa can
karshe ya kwanta. Duk da bata ganin shi taji
kwanciya yayi. Wasu hawaye sirara suka silalo
mata, ta cikin mayafin ta kai hannu ta goge su.
Kafin ta zame mayafin ta ajiye gefe, tana fara
cire tarkacen sarkokinsu dake wuyanta,
goshinta, kunne da hannuwa. Don ita ko
dankunne bata iya kwana dashi komin
kankantar shi sai ta cire, idan ta tashi da safe ta
mayar
"Idan nice kullum saina batar da dankunne"
Yelwa takan fada idan ta ga tana mayarwa da
safe. A saman soyayyar da take yiwa Julde akwai
wani kunci daya dinga kunsa mata tunda aka
fara maganar aurensu da ta dinga shanyewa, sai
ya dunkule ya zauna wani waje cikin kirjinta da
yake mata ciwo
"Har an daura, yanzun na hango su Baba suna
dawowa"
Yelwa ta fada mata cikin farin ciki, tayi
murmushi, amman ba zatace ga daga inda ya fito
Lubna sufyan
Hausabook.com 238
mata ba. Saboda jikinta yai wani irin sanyi da
bata zata ba
"Zama dani ba zai taba miki dadi ba Saratu"
Kalaman da Julde ya dinga jaddada mata suka
dirar mata. Har aka kawota gidan jinta take
kamar mai yawo a saman gajimare. Gashi nan
tun bata kwana ba ya fara nuna mata gaskiyar
kalaman shi. Kasa ta sauka tana shimfida
mayafin da ta cire, ta dawo ta dauki daya daga
cikin filon dake kan gadon ta kwanta. Sai dai
hasken fitilar da take kunne taji cikin idonta
fiye da misali. Jiki taja ta dauki fitilar da mai
batira ce, ta kashe. Duhun da ya mamaye dakin
na ba hawayenta damar sauka, su suka tayata
hira har barawon bacci ya sace ta.
**
Suna zaune cikin gida daya, amman tazarar
dake tsakanin su zatayi daga Marake zuwa
Dutsi. A tsayin satikan hudu ya koyi yin shiru ta
fannin da bai taba hasasowa ba. Yaji dadin
yanda Saratu ta bashi wannan tazarar da yaji
yana bukata. Idan ta gaishe shi da safe bata sake
ce mishi komai. Zatayi girki, zata ajiye masa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 239
Idan ya dawo zai dauka ya ci saboda baida inda
zaije yaci abincin. Kuma ba zai karya ba ta iya
girki, a tsayin sati hudu yana tsintar kanshi da
son komawa gida da cikin shi ya fara ruri
saboda yasan zai sami abinci mai dadi yana jiran
shi. Bayan wannan rayuwa suke a gida daya
amman kowa harkar gabanshi yakeyi, idan dare
yayi zatayi shimfida ta kwanta a kasa, ya kwanta
akan gado.
Ya kanji tana yawan motsi alamar rashin sabo
da kwanciya daga ita sai zannuwan da take
shimfidawa kafin yaji canzawar numfashinta
alamar tayi bacci. Sai yaji kamar bai kyauta
mata ba, amman kwana a kasan zabinta ne
tunda bashi yace ta kwanta ba, gadon yana da
girman da zai ishesu batare da wani ya takura
wani a kai ba.
"Na fita"
Ya furta kamar kullum, addu'ar dawowa lafiya
tayi masa cikin sanyin muryar da bayason ji a
tare da ita. Saboda Saratu ce, sanyi-sanyi baya
cikin halayyarta. Juma'a ce, yasan daga
Hammadi har Datti basa fitowa da wuri, su
Lubna sufyan
Hausabook.com 240
kamar ranar juma'ar ce take zame musu ranar
da sukeyin hutun karshen mako, dan wasu
ranakun juma'ar ma cikinsu babu mai zuwa ko
ina daya danganci kasuwancinsu, sai suyi
amfani da ranar wajen ziyarar abokan arziki da
kuma 'yan uwa. Shisa shima ya fara zabar ya
wuce gidansu ya fara gaisawa da Daada, su
zauna suyi hira da Yelwa. Hirar tasu da Yelwa
bata rasa abinda zata fada da zai rike shi na
tsayin kowacce rana da yakejin shi kamar a
cikin keji.
Yau ma da wannan yanayin ya tashi, ya fara
tashi dashi ne tun safiyar shi ta farko da ya bude
ido da auren Saratu akan shi. Ance idan wani
babban abu zai sameka kana ji a jikinka, ko ka
tashi da rashin kuzari, sanyin zuciya ko wani
yanayi da bai zai misaltu ba. Julde ya yarda da
wannan fadar a baya, ya yarda har lokacin daya
karya kwanar gidansu ya hango cincirin
mutane, saboda yanayin daya tashi da shi ba
bako bane ba. Ya fara sabawa dashi, baisan
kafafuwanshi sun kara sauri ba saida ya ganshi
a kofar gidan
"Rayuwa kenan..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 241
Muryar da baigane mammalakinta ba ta kutsa a
kanshi, amman son shiga cikin gidan Hammadi
da shine farko daga inda ya bullo kafin nasu,
don yaga abinda yake faruwa yasa duk wasu
surutai da akeyi bace masa, Dije ya gani a tsaye,
kafafuwanta babu ko takalma, asalima kallo
daya zakayi mata kaga tashin hankalin da yake
tare da ita. Wajenta ya karasa yana fadin
"Daada me ya faru? Lafiya? Me yasa naga
mutane?"
Ya jera mata tambayoyin zuciyar shi a kan
harshen shi. Yanda ta kalle shi yana sa tsikar
jikinshi tashi saboda ya tabbatar wani abu mai
girma ya fara dasu, girman da zai musu wahalar
dauka. Julde ne a gabanta, kuma da alama
magana yake mata, amman batajin komai sai
muryar Abu
"Lafiya kalau ya dawo sallah Dije, yace mun jikin
shi a mace yake, ni nace masa ya kwanta
watakila daren da muka raba ne muna hira,
bacci ne bai wadace shi ba... Na tashe shi yaki
tashi. Nayi nayi ya tashi yaki tashi... Ina Datti?
Ku zo ko ku zaku tashe shi ya tashi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 242
Har yanzun tanajin hannun Abu data saka cikin
nata tana janta zuwa gidan da Datti da yake biye
dasu cikin rudani. Sai dai yanda Datti ya dago
shi taga ya koma ta kalli Abu, ta kalleta da
zuciyarta a karye saboda tasan baccin da
Hammadi yayi bana tashi bane ba. Ba Abu bace
ta kasa yarda, Datti ne, Datti daya fita ya dinga
zuwa da mutane kala-kala. Tun liman daya ce
musu
"Allah ya karbi abin shi"
Abu ta zame tana zama, ta kuma ja kafafuwanta
ta hade su da jikinta bata sake cewa wani abu
ba. Datti ya kira mutane sunfi ashirin, kana
cewa ya rasu zai sake fita ya kira wani. Yanzun
haka da suke tsaye tashin hankalin da ake ciki
kenan, ya kama Hammadi ya rike a jikinshi
"Hamma ko zaka tafi zaka nuna mun alama,
zakayi rashin lafiya, zaka kwanta jinya. Ba zaka
tafi haka ba, ka tashi ka fada musu ba zaka barni
ba saboda kai kadai ka rage mun"
Ya karasa yana mayar da shi ya kwantar, ya sake
dago shi a karo na biyu
Lubna sufyan
Hausabook.com 243
"Hamma wa zaimun fada? Wa zai gayamun
banyi dai-dai ba? Dan Allah ka tashi..."
Ya karasa cikin wata irin murya da ta shiga
kunnen Julde da wani irin yanayi, saboda
hanyar dakin Hammadi kawai Dije ta iya nuna
masa
"Julde zo kaga Kawunka.. Kayi masa magana ko
zai tashi kai..."
Cikin dakin ya shiga ya kama gawar Hammadi
yana kwantar dashi, ya kuma kamo hannun
Datti da yake kokarin kwacewa
"Karka cemun ka yarda da zancen su, karka
cemun ya rasu"
Yake fadi cikin fitar hayyaci, so yake ya kwace
rikon da Julde yayi masa ya koma jikin
Hammadi
"Baba don Allah"
Julde ya fadi saboda duniyar duka yake jin ta
tashi daga kasan shi ta koma sama kanshi tayi
baya ta fado ta danne shi
"Baba..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 244
Ya sake kira yana saka idanuwan shi cikin na
Datti da sukayi wani irin fayau
"Ya rasu"
Ya fadi, maganar na komawa cikin kunnen shi,
girmanta na zauna masa. A karo na farko yana
dandanar menene zafin mutuwa, yanayin da
yake bako a wajen shi. Sanyin da hannun Datti
yayi a cikin nashi ne yasa ya sake shi. Sake gyara
zama yayi kafin yakai jikin shi kasa gabaki daya
ya dago yana neman numfashin da yai masa
tsaye, dakyar ya fito dashi tare da wani gunjin
kuka daya da hawayen Julde saukowa. Zama
yayi yana kamo Datti daya fada jikin shi yana
kuka kamar karamin yaro, su duka dakyar aka
fito dasu daga dakin. Dije na kamo Abu da babu
digon hawaye ko daya fuskarta suka fito don
bada damar a hada shi.
Zuwa lokacin gidan ya fara cika da mutane,
saida aka fito da gawar, Abu ta hango su sannan
ta zabura ta mike. Dije ta rikota, amman karfin
da take ji ba zai kwatantu ba. Matan duk da suke
gabanta ta dinga tsallakewa saida takai tsakar
gida inda aka shimfide Hammadi cikin sutturar
Lubna sufyan
Hausabook.com 245
da itace zata zamo ta karshe a duniyar kowa.
Ana kokarin shigowa da munkarar da za'a saka
shi ciki
"Hammadi Am"
Ta kira shi a karo na farko sunan na fitowa da
zuciyarta da take da yakinin za'a binne tare da
shi
"Da kace mun hirar jiya bankwana ne, da ka
fadamun sanyin jikinka tabin mutuwa ne. Dana
zauna tare da kai, dana kwanta a gefenka ko
bata dauke mu tare ba inji fitar numfashin ka..."
Ta karasa can kasan makoshi
"Allah ya amsa addu'arka, ban tafi nabarka ba.
Kai kabarni...kai ka fara barina Hammadi..."
Hawayenta suka rike sauran kalaman, a wajen
ta durkusa tanajin karshen duniyarta yazo tare
dana Hammadi. Bata san hannayen suwa ke
kokarin dagata ba
"Kubarni... Dan Allah kubarni"
Lubna sufyan
Hausabook.com 246
Ta roke su, sai suka saketa, amman tanajin su a
gefenta. Har aka saka Hammadi a munkara aka
fita dashi, ihun kukan mata na cika kunnenta
"Allah ya yafe maka Hammadi Am... Allah ya
hadamu a aljannar da kake hango mana tare da
rabon da bamu samu ba anan"
Idan tace bata ji barinta zaiyi a yan kwanakin
nan ba zatayi karya, akwai bankwana a cikin
duk wani abu da sukeyi, sai dai bata hango yau
bane. Da suka sake kamata batayi musu ba,
mikewa tayi suna janta zuwa dakin da ta fito.
Yawan mutanen basu hanata jin wani irin fili da
gidan yayi, har kirjinta take jin wannan filin,
kamar Hammadi ya tafi da komai, a jikin Dije ta
dora kanta tana jin yanda ta lalubi hannunta ta
dumtse kamar tana son fada mata tana nan
gefenta, babu inda zataje. Yanayi ne da bai hana
mata jin kadaicin da zai kasance tare da ita har
karshen rayuwarta ba.
Sai dai mutuwar Hammadi cikar lokaci ce
Akan kowa mutuwa cikar lokaci take jira
Kaddarar su yanzun ne zata fara.
Lubna sufyan
Hausabook.com 247
Daga nesa suke jin labarin mutuwa, a wautar
tunani irin nasa bata hango zumuncin mutuwa
zai biyo takan wanda suka sani nan kusa ba. Sai
dai kamar yanda ake fadine, rai bakon duniya.
Musamman Yelwa da idan gari ya waye ta tashi,
sai ta fito ta taka kafarta gidan sai taji wani abu
a cikin kirjinta ya fadi, saita tuna shikenan, ba
zata ga Hammadi ba, ba zai jata da hirar nan
tashi mai cike da raha ba. Sai taji komai ya tsaya
mata, a tare da kowa tana ganin yanda rashin
Hammadi duk ya taba su, musamman Datti da
yayi wata irin ramewa.
Tashin hankalin su duka ya karu lokacin da Abu
ta gama takaba tace ba zata iya zama a gidan ba,
duk kuwa Julde da Saratu da akasa suka dawo
don kar kadaici ya dameta
"Gidan yayi mun fili Dije, kinsan darare nawa na
rufe idona da fadan kar in bude su? Ko zan tarar
da Hammadi? Banda abinda zan cike ramin da
Hammadi yabar mun. Idan ina cikin gidan nan
babu ranar da mutuwar shi zatayi mun sauki.
Ina bukatar shakar iska daban da wadda ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 248
cudanyu da ta shi ko kirjina zai rage ciwon da
yake mun"
Watakila yanayin yanda tayi maganar ne, ko
kasancewar ranar karo na farko da tayi wata
magana data nuna halin da take ciki. Babu
wanda ya iya hanata komawa gidan dan uwanta
da suka karbeta suna kuma bata daki. Sai
akabar Saratu da Julde a gidan kawai. Julde da
yake jin kamar an dibi wasu shekaru an kara
masa da rasuwar Hammadi saboda yanda
abubuwa da yawa suka koma karkashin
kulawar shi. Saiya zamana duk wani abu da
Hammadi ke kula dashi na daga dukiyar su ya
koma hannun shi, ciki harda gadon Saratu,
tunda Abu an fitar da ita, komai ya koma
karkashin kulawar dan uwanta da ta koma
gidan shi.
Ya dauka girma a hankali yake zuwar ma
mutum, tare da shekaru. Sai nashi ya dira batare
da sallama ba, tare da auren Saratu da zuciyar
shi ta karba a matsayin daya daga cikin
kaddarorin shi duk da ya rasa yanda zaiji
soyayyarta. Rasuwar Hammadi ta canza tsarin
zamansu, batare da sanin dalili ba, ana fitowa da
Lubna sufyan
Hausabook.com 249
gawar sai ta fado mishi a rai, yanda ya
kafafuwan shi suka dauke shi zuwa gidan ba zai
tuna ba. Ya dai dauki mayafinta ya saka mata
bayan ya kama hannunta ya mikar da ita
"Lafiya? Me ya faru?"
Da duka sauran tambayoyin da take jera mishi
muryarta cike da firgici na wucewa ta cikin
kunnuwan shi da wani irin yanayi. Bai tuna ya
rufe gidan ba, ya dai riko hannunta sun taho.
Har yau idan ya kalleta sai yaga rashin tabbacin
da ya bayyana akan fuskarta, kafin wani yanayi
da ba zai taba mantawa ba ya maye mata
gurbinshi hadi da gunjin kukan da zaka san ya
fitone daga lungun zuciyarta. Bai sake sakata a
idanuwanshi ba sai ranar bakwai din Hammadi
"Kaje ka dauki matarka ku koma gida"
Dije ta fada masa, bai musa ba, inda ya saka
kafafuwan shi nan take mayar da nata a duhun
daren da babu hasken komai saina farin wata da
taurari. Sun koma gida, ya tuna hawayen da
suke cike taf da idanuwanta lokacin daya kunna
musu fitila
Lubna sufyan
Hausabook.com 250
"Hakuri zamuyi Saratu"
Ya fada yana ba hawayenta damar zubowa, ya
kama hannunta, ya jata zuwa jikinshi yana
riketa cike da tausayin daya bude masa hanyar
shigar wani yanayin da ya canza akalar daren
nasu. Ta amsa masa tambayoyi da yawa, ta
kuma sake tabbatar masa da abu daya, aurenta
kuskure ne, kuskurene badan bata cika mace
ba, sai dan ita kadai ta masa kadan kamar yanda
ya hanga, irinta guda hudu sun masa kadan. Sai
dai in duk bayan wani lokaci zai sake su ya sake
auren wasu. Bai san ta inda zai fara kauda
idanuwan shi da zuciyar shi daga kan wasu
matan ba.
Kamar akwai wani abu a cikin jikinshi da yake
saka shi jin son kasancewa da duk macen da
zata gifta ta burgeshi. Ranar farko da ya labe a
bayan ganin komai ya tafi dai-dai ya koma Kano,
ya hada shimfida da wata ya tashi sai yaji kamar
an dora masa wani dutse mai nauyi a saman kai,
igiyoyin auren dake kanshi na masa wani irin
dauri da harya dawo Marake bai sake shi ba.
Musamman daya taka cikin gidan daya zama
nasu yanzun, saiya ga kamar Hammadi na
Lubna sufyan
Hausabook.com 251
kallon shi, kamar bai rike amanar daya kamata
ace yana rike da ita ba.
Sai dai akwai abinda yake fisgar shi da nauyin
shi yafi na dutsen da yake ji ya danne shi, daurin
shi ya girmi igiyar auren Saratu
"Yan duniya na binni, kayi harkarka hankali a
kwance baka da tunanin komai"
Ya tuna zancen wani direban babbar mota a irin
hirarrakin su. Shima haka ya dauka, sai da tura
ta kai bango, matsi yayi matsi yanajin yanda
Saratu tayi ma bukatar shi kadan. Lokacin ya
fara abotar sirri da yaran da yake jin Datti na
kwashewa albarka yana kira da 'yan iska. Saiya
fahimci ita lalacewa bata da wani layi a tsakanin
binni da kauye, zabi kawai take bukata, na
kaddarar da tafi karfin iko, ko na kaddarar da
take zuwa da son zuciya. Saboda a cikin Marake
da yake tunanin kowa ya san kowa, sababbin
abokan shi suka tayashi binciko rayuwar da bai
taba tunanin akwaita a kauye ba.
Kowacce rana a cikin tana kara busar masa da
zuciya tana nisanta shi da tsoron kar wani ya
binciko sirrikan da yake boyewa. Ya fara
Lubna sufyan
Hausabook.com 252
ninkayar da baya tsoron nutsewa sam, saboda a
idanuwan Julde bashi kadai bane ba, mutane da
yawa sunayi, wanda aka sani da wanda ma ba'a
sani ba. A cikin wanda aka sani din surutun
wani lokaci ne, musamman shi namiji. Maza
nawane a kauyen aka kama da haura gidaje
kuma maganar ta shude a cikin tarihi? Wasu
sababbin labaran na binneta? Matan da sukayi
cikine ake rabawa da kauyen ba mazan da
sukayi musu cikin ba.
Daya daga cikin dokokin da al'ada ta shimfida
da Julde yake ganin ba zai taba fahimta ba.
Dokar tayi masa, saboda ta fifita zunubin da
yake tunanin girma daya ne, a wani yanayin ma
za'a iya kwashe kusan duka kason a mayar
kacokan akan macen. Laifin da suka aikata da
amincewar junan su zai juya ya koma kamar ita
kadai tayi.
"Kudin shi ta gani ba komai ba"
Wasu zasu ce
"Julde fa dan gidan Datti, ko babu kudi tabi
kyau"
Lubna sufyan
Hausabook.com 253
Ta kowacce fuska idan asirin shi ya tonu yana da
yakinin mutane da yawa zasu nema mishi
uzururrukan da zasu rage girman laifin shi.
Lokaci kuma zai dishe musu hasken laifin har
saiya zamana kamar bai faru ba. Kamar yanda
lokaci ya fara saka shi daina jin nauyin laifukan
shi. Shisa zuwa yanzun bai damu ba, lamurran
shi yakeyi hankali a kwance, a gefe daya yana
gudanar da harkar dukiyar su cikin basirar da
ta dauke hankalin Datti daga sauran lamurran
shi saboda ganin da yakeyi nutsuwar da yake
masa hasashen samu tare da cikar kamalar da a
ganin Dattin inuwar aure kan samar, ta tabbata.
*
Yelwa zata kira sake haduwarta da Kabiru daya
daga cikin abubuwan da suka fi karfinta, irin
barin makauniyar da kaddara take yiwa mutane
batare data duba ta ina takai dukan ba. Idan
tace tunda ta hadu dashi daga farko bai dinga
ziyartar tunaninta ba zatayi karya. Tana
kwance, tana zaune, tana hidimar yau da
kullum. Sai taji shi yana fitowa daga inda yake
cikin dumbin tunaninta yana yo sama, yana
sakata tunanin abinda yake dashi a fuskar shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 254
da bata taba gani tare da kowa ba. Yanayin dake
cikin kananun idanuwan shi da bata taba tunani
ba. Sai mutuwar Hammadi ta binne mata shi har
sai lokacin da ta sake ganin shi, ranar tana
hanyar komawa gida daga aiken da Dije tayi
mata
"Yelwa..."
Ya kira sunanta da murmushin shi, yana tuna
mata da lobawar data kula bari daya na kuncin
shine yakeyi duk idan yayi murmushi, kananan
idanuwan shi na sake shigewa ciki. Bakine don
baki, amman daga inda take tsaye zata iya kula
da murjewar fatar shi da kyallin da yakeyi na
alamar bai tashi cikin wahalar rayuwa ba ko da
ba masu kudi bane, ba zasu rasa rufin asiri ba. A
kasan yanda ya kira sunanta kamar ya santa,
tare da murmushin shi kamar akwai wata alaka
a tsakanin su
"Daga ina haka?"
Ya jefeta da tambayar da tasata ganin karfin
halin shi, har lokacin da murmushi a fuskarshi
"Aikena akayi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 255
Ta amsa tana tsintar kanta da dorawa da
"Zan koma gida..."
Kai ya jinjina
"Zan iya rakaki?"
Kafin ya gama rufe bakin shi ta girgiza masa kai,
kirjinta na wata irin dokawa. Murmushin shi
cike yake da fahimta
"Ki gaida gida. Nagode"
Ya fadi yana juyawa, tabi shi da kallo, kamar
haduwar zata tsaya iya nan. Kamar ba zai samu
wajen zama a zuciyarta ba. Kamar ba zata dinga
neman duk wani uzuri da zaisa ta fita don kawai
ta ganshi ba. Kwanakine suka dinga hadewa
cikin satika har ta bude ido da soyayyar Kabiru
da sanyin halin shi ya dasa mata. Mazan da suke
cikin rayuwarta basu da yawa tun tasowarta.
Datti ta fara dubawa a matsayin mudubi, sai dai
tun kafin tayi hankali Hammadi yasa ta fara
dora ayar tambaya akan halaye da yawa na
mahaifinta, a cikinsu harda rashin hakurin shi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 256
Sai Julde da ya dauki taurin kai irin na Datti,
amman idan ba ka kure hakurin shi ba, zaka
dade baka ga bacin ran shi ba, sannan abinda
duk yaso yi hanashi kan zama rikicin da rayuka
da yawa sai sun baci. Sai Bukar, Bukar bawan
Allah, Bukar da nisa bai sauya komai daga
halayen shi ba. Ziyarar duk da yake kawo musu
sai taga kamar yana kara yin sanyi ne, ko ta dan
tsukun bayan rasuwar Hammadi sai da yanayin
shi ya dawowa da kowa mutuwar sabuwa,
saboda kuka yayi, kuka irin na maraici, kukan
da zakayi zaton daga jikin Hammadi ya fito.
Harya koma duk idan ta ganshi sai taji kwalla ta
cika mata idanuwa, saboda yanda yakeyin
komai da sanyi-sanyi, yanda harya tafi mutuwar
Hammadi bata gama sakin shi ba. Amman a
cikinsu bata ga mai kama da Kabiru ba, bata san
ta inda zata fara ba idan akace ta zayyana
halayen shi. Watakila haka So yake, baka jin
komai, baka ganin komai sai shaukin da kake
ciki. A yanzun idan laifi Kabiru yayi zai wahala
ta gani. A fuskar shi da mutane da yawa zasu
kalla ba adadi kafin su ga abu daya me kyau taga
tarin abubuwan da suka burgeta. Soyayyar da
Lubna sufyan
Hausabook.com 257
take masa ta kara haska mata abubuwa da yawa
tare da shi.
"So banzan abu ne Yelwa"
Saratu ta taba ce mata, kalaman sun bata dariya
a lokacin, bata jin ta fahimce su, a cikin kanta
basu da wata ma'ana. Amman yanzun sai ta
kirga su, banda sunanta, kalmomi hudune suka
tashi jimlar, kalmomi hudun da zata fassara a
cikin shafuka masu yawan gaske
"Nagaji da haduwa dake a wajajen da nake raba
hankalin ki da duban hanya ko wanda kika sani
zai ganmu. Nagaji da boyewa kamar abinda
muke bashi da kyau Yelwa...ina son taka kofar
gidanku..."
Ya fadi yana hargitsa zaman lafiyar da suke ciki,
yana kusanto mata tshin hankalin da take
hangowa daga nesa
"Baba na...Baba na ba zai baka aure na ba"
Ta fadi, kalaman na komawa cikin kunnuwanta
suna sake hargitsa duk wani lissafi da yake tare
da ita. Sai numfashinta ya soma yi mata
barazana, idan ta shaki iskar sai taji bata kaiwa
Lubna sufyan
Hausabook.com 258
har cikinta balle ta karasa ta rarrabu a jikinta.
Duk yanda tasan cewa Datti ba zai bar auren su
da Kabiru ba, bata bar kanta ta hango meye
makomar hakan ba.
"Kibar ni in gwada, ya zaka karaya da yaki tun
bakasan su waye abokan karawarka ba?"
Ya karasa da nufin bata dariya. Sai dai ita da
nishadi sunyi hannun riga a wannan lokacin.
Jininta akan farce yake har juma'ar da Kabiru
yace zai shigo Marake da dan uwan mahaifin shi
kasancewar shi maraya, sai suyi masa jagorar
tambayar aurenta a wajen Datti. Daren juma'ar
na zama na farko data kwatanta sallar daren da
taji ana yawan fadar anayi don neman biyan
bukata, bata san raka'a nawa ya kamata tayi ba,
goma ta fara, sai taga kamar tayi kadan, da ta
fara jerowa saida gwiwoyinta sukayi sanyi. Akan
dardumar ta kwanta, a karo na farko hawaye na
silalo mata. Tana son Kabiru, wani irin so da
bata da kalaman misalta shi.
Da safiyar ranar komai ta kasa ci
"Kinyi zururu, baki da lafiya ne?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 259
Dije ta tambayeta, sai ta matsa jikinta tana
kwanciya akan cinyarta
"Kirjina ciwo yake Daada, kuma kamar zazzabi
na son kamani"
Da yawa zasu iya kiran shakuwar da tayi da
yaranta a matsayin sangarta su, wasu ma suna
ganin bata da kunya. Musamman yanda bata
boye soyayyar da take musu ko a gaban waye.
Har Julde da auren shi zai iya shigowa ya zauna
a tabarma ya zame jikinshi ya dora kanshi a
cinyarta
"Daada nagaji"
Yakan fadi, wasu ranakun zaiyi har bacci. A
cikin su ukun, Bukar ne mai kunya, ko da
kunyar shi bata hana masa kwanciya a jikinta
ba, raunin zuciyar shi zai hana, zaiga kamar yayi
mata nauyi. Tunda tsintsiyar shara bata dagawa
idan har yana cikin gidan. Bukar dinta da kewar
shi take cika zuciyarta lokutta mabanbanta,
tafiyar shi bata taba tsaya mata irin wannan
karin ba, ba don yanda mutuwar Hammadi ta
tabashi ba, wannan yanayine da suma sun shige
shi, ta kuma son a hankali ciwon zai ragu. Sai dai
Lubna sufyan
Hausabook.com 260
kewar tana nan daram, tunda kaunar da take
tsakanin su mai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 27