tayi tana fita daga kitchen
din, wata kujerar Salim yaja ya zauna, saboda
yasan Madina zatayi masa magana idan yaci
kifin a tsaye. Kofi ta samu tana karasa ta bude
fridge ta dauko ruwa ta zuba masa a ciki tana
mika masa
"Nagode"
Ya furta a hankali bayan ya karba, itama taja
kujera ta zauna, kamar hakan wayarta take jira
ta fara ruri, tana dubawa taga Nawfal ne ya
kirata video call. Dagawa tayi tana murmushi
"Hamma..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 449
Ta kira, lokaci daya Salim yaji dandanon kifin da
yake bakinshi ya dauke gabaki daya. Zuciyar shi
tayi nauyi a cikin kirjinshi, bayaso tana kiran
kowa da wannan yanayin banda shi, wannan
murmushin da yake fuskarta ya kamata ace bai
kai haka girma ba tunda bashi take yiwa ba.
Kishine yake damun shi, kishi da bai taba
tunanin yanada irin shi ba, kishin da batama san
yanayi ba
"Kana ina haka? Ina Daada?"
Ta tambaya
"Jaan ta koroni, dole saina fito na sha iska wai,
tana tare da Daada, bacci takeyi sanda na fito
dai... Me kikeyi ke?"
Juya camera din tayi tana haska masa kitchen
din, kafin ta sake dawo da ita zuwa dubanta
"Ina zaune a kitchen ni da Hamma Salim...ni ina
girki, shi kuma yana cin kifi"
Dariya Nawfal yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 450
"Aikin dare yayi ya dawo gida ya kwanta bacci
maimakon ya nemi abinci ya tashi da yunwa
ko?"
Dariya Madina takeyi tana daga masa kai
"Ina zaune a kitchen din Bajjo, ranka kuma zai
baci"
Dariya Nawfal ya sakeyi, Madina ta mikawa
Salim din wayar, ya karba lokacin da ya sake kai
wani kifin bakin shi, Nawfal kuma yana gaishe
dashi, gira Salim ya hade masa a maimakon
amsa gaisuwar yana sakashi sake yin dariya
"Yaushe zaku dawo?"
Salim ya tambaya bayan ya kara jin cewa
Daadar ta samu sauki
"Inajin nan da sati daya haka ko kwanaki goma
idan Allah ya kaimu"
Kai Salim ya jinjina
"Ka kula da kanka..."
Murmushi Nawfal yayi
"Jaan na kula dani"
Lubna sufyan
Hausabook.com 451
Dakuwa Salim yayi masa yana yatsina fuska
cikin yanayin da yasa Nawfal din yin dariya,
yanke kiran yayi kafin ya mikawa Madina
wayar. Karba tayi sai taji zuciyarta kamar batayi
mata dadi da abinda Nawfal din ya fadi, duk da
yayi maganar ne cikin sigar tsokana. Amman
akwai gaskiya a kasan hakan, akwai kuma
yanayin da yake nuna nishadin da fadin
Murjanatu na kula dashi ya samar masa
"Ki duba girkin nan koya totse"
Salim ya fadi ganin tana jujjuya wayar a
hannunta kamar tana jiran Nawfal din ya sake
kiranta, ta kuwa yi masa murmushin nan nata
tana sakashi sauke numfashi. Batayi masa musu
ba ta tashi tana dubawa. Sai ta dauko lettuce din
da ta wanke ta saka shi a kwando dan ruwan ya
tsane ta fara yankawa. Ko da Salim ya gama
cinye kifin shi bai bar kitchen din ba, komawa
yayi ya zauna kan kujerar daya tashi yana
sakata bashi labarin littafin da take karantawa,
idan za'a karbi wukar hannunta a saka masa a
wuya ba zai iya fadin me littafin ya kunsa ba.
Hankalin shi yana kanta, amman kalaman da
take fada basa karasawa kunnuwan shi, yanayin
Lubna sufyan
Hausabook.com 452
yanda labbanta ke motsawa, yanda takeyi da
hannayenta idan tazo wajen da yayi mata dadi a
labarin, da dariyarta sune abinda yake kallo.
Baya ganin komai sai kyanta da ba kowa bane
zai gani farat daya. Yana so rana daya, ya cire
mata gilashin nan, ya rabata da kayan nan, ya
ganta a cikin shigar atamfa, hannuwanta masu
kyan nan da kunshi, ya ganta a cikakkiyar mace
saboda a cikin kanshi daya hasaso tayi kyau,
wani irin kyau mai sanyi. Ko da ta gama girkin
ma sai dakyar ta samu ya bar kitchen din bayan
ta zuba masa. Ta wanke yan kwanonin da ta
bata, ta goge ko ina tana fitowa falon
"Ke ba zaki ci ba?"
Kai ta girgiza masa
"Sai anjima, banajin yunwa ni kam"
Da ya gama cin abincin ma ta kusan mintina sha
biyar tana fama dashi kan yaje ya kwanta
saboda yana bukatar baccin
"Zan kwanta anan"
Kai ta girgiza masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 453
"Anayin kwakkwaran motsi tashi zakayi. Dan
Allah ka kaje ka kwanta Hamma, nima baccin
zanyi"
A fuskar shi baiso ba, saboda ji yake kaman daga
bangaren Saratun zuwa nasu yayi masa wani
irin nisa, nisan da bayaso a tsakaninsu. Amman
da gaskiyarta, ya gaji sosai, yana kuma bukatar
baccin. Yana tafiya ta mike itama zuwa dakin
daya zama nata yanzun a cikin gidan. Kai tsaye
bandaki ta wuce ta watsa ruwa ta fito daure da
towel, sai da ta shafa mai sannan ta saka kaya,
sanin babu wanda zai shigo yasa tabar na
jikinta, tunda lokutta da dama tana amfani
dasune a matsayin na ciki, ta dora wasu akai,
gara ta saka kaya hudu a jikinta komin zafin da
akeyi in har ba zasu fito da wata alama ta
halittarta ba.
Sai dai abinda batayi tsammani bane ba ya faru,
tana tsaye aka murda hannun kofar aka kuma
bude duka cikin abinda bai shige dakika biyu
ba, numfashinta ta dauke lokacin da idanuwanta
suka sauka cikin na Julde. Shi ya fara sauke
nashi yana kallonta, tun dawowarsu daga
airport rakiyar Daada yake jin shi wani iri, yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 454
jin shi kamar yana yawo a cikin wata kwalbane
da baisan yanda zai fito daga cikinta ba. Baccin
kirki baya samu, daya kwanta ya fara bacci sai
yaji ya farka, idan za'a tambaye shi ba zai iya
fadin dalilin farkawar tashi ba.
"Ka kwantar da hankalinka Julde, ance ta samu
sauki. Da yardar Allah babu abinda zai sameta"
Saratu tace masa satin daya fita da ta farka
tsakiyar dare ta ganshi a zaune. Kuma tanata
kokari ya kula tun tafiyar Daadar wajen ganin
ba suyi fada ba, watakila ta kula da yanda baya
cikin hayyacin shi. Sai dai ya kalleta kawai,
tunda baisan ya zai fada mata ba rashin lafiyar
Daada bace kawai matsalar shi. Taya zai fara
fada mata abinda shi da kanshi bai gama sanin
menene ba? Yanajin kamar wani abu na sarke
dashi, ko tuki yake yanajin abin gab dashi, idan
ya sauka yana tafiya da kafarshi saiya waiga yafi
a kirga saboda ji yake kamar abin na biye dashi.
Ga wani irin tsoro da yake cike da zuciyarshi da
baisan daga inda yake tasowa ba.
Yanzun ma yana kasuwa yaji ya nemi yar
nutsuwar da yake tare da ita ya rasa, yayi niyyar
Lubna sufyan
Hausabook.com 455
biyawa wani wajen kafin gida, inda zai samu
wata nutsuwar ta daban, sai ya kasa. Saboda
abinda yake nema yana da tabbacin ba zai samu
a tare da kowacce irin mace bace zata fado
masa. Kamar ya fasa ihu haka yake ji sanda ya
shigo gidan, yaje dakin Saratu ya tura yaganta
kwance tana bacci, sai ya karasa dakin Lukman
ya tura yaji shi a kulle, hakan na tuna masa da
kowacce rana ce, Lukman din yana da
makaranta. Wani abune ya tuna masa Madina na
gidan, kawai so yakeyi yayi magana da wani,
wani wanda yake ji a zuciyar shi watakila ya
samu nutsuwa.
Ko idanuwanshi ya rufe da wahala ya lalubo
hotunan Madina guda uku a cikin kanshi da ta
saka wasu kaya na mata, tunda ta fara hankali
kuma duk ganin da zaiyi mata banda
hannuwanta da fuskarta baya iya tuna yaga
wani abu. Sai yau da baisan yanda zai fara hana
idanuwanshi yawatawa akanta ba. Ganin da
yake mata gajera saiya dauka kamar Adee take
itama, bambancin nasu yana tare da shigarsu da
ta bambanta. Tunanin shine da bai taba yi mata
kallo na biyu ba ko idanuwan shine bai sani ba,
Lubna sufyan
Hausabook.com 456
amman akwai abinda ya kange shi daga hasaso
cewa abinda Madina take boyewa a karkashin
shigarta kenan.
"Daddy..."
Muryarta dake rawa ta kutsa cikin tunaninshi
tana saka shi dakyar ya dago da idanuwan shi ya
kalleta
"Ka dawo? Sannu da zuwa... Inzo in zuba maka
abinci?"
Rashin sanin abinda zai fada yasa shi daga mata
kai
"Barin saka kaya in fito"
Ta furta tana murmushi, haka kawai taji
zuciyarta na mata rawa, taji wani tsoro ya
ratsata irin wanda bata taba tunanin zata jishi
idan Julde yana tsaye a wajen ba. Yanda saida
idanuwan shi suka sake yawatawa a jikinta
kafin ya ja kafafuwanshi ya fita ya saka tsikar
jikinta mikewa cikin yanayi marar dadi, sai taji
kamar wata dauda ta manne mata. Kallo ne da
baiyi mata dadi ba, kallo ne daya sake ninka
tsoron da yake zuciyarta ya kuma raunana
Lubna sufyan
Hausabook.com 457
kallon da take yiwa Julde batare da ta sani
bama. Yana fita jikinta har rawa yakeyi ta
karasa ta kulle kofar tana murza mukulli,
zuciyarta a makoshinta lokacin data gama saka
kaya ta fito tana nufar kitchen. Abincin ta hada
masa tana kai masa dining table, daga nan inda
take tsaye tace masa
"Daddy ga abincin naka"
Tayi nufin komawa dakine sanda taji muryar shi
na fadin
"Ki bani ruwa"
Ta manta da ruwa, kitchen din ta sake komawa
ta dauko kofi da robar ruwa, ta ajiye robar tana
shirin ajiye kofin taga ya mika mata hannu,
batayi tunanin komai ba ta mika masa kofin,
yanda hannunsu ya hadu kadan ya rage kofin ya
subuce mata da Julde bai rike ba, zuciyarta taji
ta sake yin wani tsalle kamar tana kokarin
rabuwa da kirjinta. Da sauri ta juya tana barin
wajen
Lubna sufyan
Hausabook.com 458
"Yanda ka kunyata ni Julde... Allah ya kunyata
ka a idanuwan mutanen da suka fi komai
muhimmanci a wajenka..."
Julde yaji kalaman sun dawo masa lokacin daya
bi bayan Madina da kallo kafin ta bacewa ganin
shi, idanuwan shi ya runtsa ya sake bude su
yanajin jikin shi ya dauki wani irin dumi
Sai dai wata kaddarar yanzun ne shafinta zai
bude...!
Duk labarun tashin hankalin da yake ji basu
taya shi shiryawa zuciyar shi wannan da yake so
wani ya girgiza shi yace masa mummunar
mafarki ne yakeyi ba, ko a tarihi ba zai tuna
kunnuwan shi sun tsinkayo mishi wani yana
bada labari kwatankwacin abinda yake gani
yanzun ba. A tsaye yake akan kafafuwan shi, har
yanzun yana da tabbacin akan kafafuwan shi
yake tsaye saboda yana jin sunyi sanyi. Duniyar
da yake tsaye akanta ne ta birkice dashi tana
nuna masa iyakarsa. Kamar awanni ba kasa da
dakika ba haka yaji tsakanin rufe idanuwan shi
da yayi ya sake bude su kamar yana son wani
Lubna sufyan
Hausabook.com 459
sashi na zuciya ko kwakwalwar shi su karyata
masa abinda yake gani.
Mintina nawa ne daga bangaren su zuwa nan
din, duka anyi awa da fitar shi? Ya za'ayi ace
gabaki daya duniyar ce tayi juyin waina dashi
haka? Yaune fa, dazun nan, ya dawo daga wajen
aiki a gajiye, ya wuce bangarensu kai tsaye yayi
wanka ya sake kaya, maimakon ya kwanta yayi
bacci, da cajar wayarshi da ya dauko danya
makalata sannan ya kwanta ya baro bangaren
su zuwa na Saratu, saboda yana son ganin
Madina, sai dai guga takeyi daya kira wayarta.
Takawa yayi daga falon yana karasawa har
dakinta ya kwankwasa, sai da ta bashi izinin
shiga sannan ya tura kofar. Dakin Adee ne ada,
banda litattafan Madina da suke ajiye kan
durowar gefen gado, kusan dakin yana nan
yanda ya san shi.
Haka kawai sai kewar Adee din ta saukar masa
kamar basa waya kullum. Kusan rabin
rayuwarta ita da Nawfal a makaranta sukayi ta,
saboda itama har sakandire dinta makarantar
kwana ce. Amman dan lokacin da take gida, yayi
kewar wannan lokacin, fadansu saboda bata san
Lubna sufyan
Hausabook.com 460
yanda zatayi abu a hankali ba, ko zaune yake a
falon saiya sani idan itace take wanke wanke,
zai iya rantsewa cokali take dauka tana
kwalawa a jikin kwanoni saboda ta saka shi
magana, ko tafiya zatayi saita dinga jan
kafafuwanta. Idan bai kai mata duka koya
zageta ba batajin dadin. Adee ce duk a cikin
kannen shi zata zauna kan kujerar da yake kai,
ko mai zaman mutum dayace saita zauna a
hannunta.
Har tambayar Saratu yakeyi
"Nanna anya baki haifo Adee bane don kawai ta
takuramun?"
Ko ita Adee din gab da bikinta da ya kai mata
wata masga sai da tace
"Na kusa bar maka gidan Hamma, sai kayi
kewata"
Gani yake kewarta na me zaiyi? Gashi kuwa
yanzun, dakinta kawai ya gani amman zuciyar
shi tayi wata irin matsewa a cikin kirjinshi.
Kewarta yakeyi sosai. A bayan zuciyarshi ya
adana cewar ya kamata ya biya yau ko zuwa
Lubna sufyan
Hausabook.com 461
gobe ya ganta. Tunda kwana biyu bata zo gidan
ba
"Na kusa gamawa... Saura guda biyar"
Madina ta fadi tana masa murmushi, zaune take
bakin gado tana gugar a kai, kofar Salim ya sake
budewa sosai, wannan dokar Saratu ce tuntuni,
in dai wani a cikinsu zai shiga dakin Adee to
kofar a bude za'a barta, sannan kamar yanda
tun suna hade waje daya, ba'a ware musu
bangarensu ba, akwai kujeru a nasu dakunan,
dakin Adee ma akwai. Babu mai hawar mata
gado in dai sun shiga. Da aka ware musu
bangarensu kuma, da hankalin shi dai zai kirga
lokuttan da Adee ta taka bangaren su, sai dai su
suzo na Saratun. Har yanzun kuma akwai
kujerun guda biyu, daya daga ciki yaja yana
zama.
Yanajin yanda zuciyar shi ta nutsu da kusancin
da yake da shi da Madinar
"Bacci ya kamata ace kanayi Hamma"
Kafadarshi daya ya makale mata saboda
bayason yin magana, bayason cewa komai. Da
Lubna sufyan
Hausabook.com 462
zai samu, baccin zaiyi, daki daya da ita. Baccin
da yafi kowanne yi masa dadi da nutsar dashi
shine lokuttan da yayi su a kofar gidan Daada, a
cikin motar shi, sanin tana gefen shi a zaune
tana kallon shi, ko tana danna wayarta, ko tana
karatu. Tana dai gefen shi, koma me ta zabi tayi
kafin ya tashi, awa dayane, wasu ranakun awa
biyu. Amman idan ya tashi sai yaji duk gajiyar
da ya kwaso ya nemeta ya rasa. Madina na da
wannan tasirin a rayuwar shi.
"Ka ci abinci?"
Kai ya daga mata, meatpie ne daya siya da
daddare, guda biyu ya rage, shine ya ci da safen
kafin ya baro asibiti, kuma bayajin yunwa. Kai ta
daga masa, dankali da kwaine da shayi sukayi
da safen, Khalid ma da nashi ya tafi don yace ya
makara, Lukman kuwa a kitchen din ya tsaya
yana ci da sauri-sauri, shima saida tace ta zuba
masa ya tafi dashi ya girgiza mata kai. Ta zauna
kenan a dining table zata karya Julde ya fito,
haka kawai ta tsinci kanta da mikewa bayan ta
fito, ta dauki plate din. Bayan sunanta daya kira
ba zatace ga abinda yake fada ba, saboda yanzun
idan ta ganshi sai taji zuciyarta na mata rawa. Ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 463
dai miko mata wani lemo da ta amsa tana
shigowa daki dashi.
Yanzun ne ma ta hango shi ta mika hannu ta
dauko, robar tayi mata kyau sosai, lemon na
mangwaro ne, ta saka karfinta wajen kwance
murfin, sai taga ya bude kamar a kwance yake
daman, ko dan wasu robobin ba'a datse su da
karfin nan. Kurba tayi
"Wanne irin lemo ne?"
Salim ya tambayeta, sai da ta hadiye ta kara
saboda dandanon yayi mata dadi sannan ta
amsa shi
"Na mangwaro ne, Daddy ya bani dazun... Zaka
sha?"
Kai ya girgiza mata, yana dai kallo harta shanye
duka robar a gefe suna cigaba da hira jefi-jefi
"Bacci kake ji Hamma, kamata yayi ace ka
kwanta"
Ta furta ganin yayi hamma a tsakanin maganar
da sukeyi tafi a kirga, bai amsa ba, kallonta
kawai yayi. Itama kanta take ji kamar an dora
Lubna sufyan
Hausabook.com 464
mata dutse, ga wani lumshewar rashin dalili da
idanuwanta sukeyi mata, ko bashin bacci taci
baya mata haka, balle ta samu wadataccen bacci
"Ke ma baccin kike ji, karatu kika tsaya jiya ko?"
Kai ta girgiza masa, badon bata so ta tsaya
karatun ba, sunyi waya dashi yana asibiti yace
mata ta kwanta tayi bacci saboda tayo masa
korafin kanta yayi mata nauyi. Kuma sai tayi
abinda yace din
"Kai kace in kwanta Hamma"
Tayi maganar kamar bata da wani zabi daya
wuce bin umarnin shi, hakan ya sanyaya wani
bangare a cikin zuciyar shi
"Kawai dai wani baccin ne ya kamani yanzun"
Ta dora da fadi tana kara gyara zamanta. Saiya
mike
"Ki kwanta, nima bari inje in dan samu baccin...
Mu fita yawo anjima?"
Ya karasa maganar da alamun yana jiran
amsarta, kai kawai ta iya daga masa. Shi yaja
mata kofar daya fita daga dakin. Kuma kai tsaye
Lubna sufyan
Hausabook.com 465
bangaren su ya wuce ya kwanta a falo kan
doguwar kujera, bayajin yayi baccin awa daya
yaji ya bude idanuwan shi, dan ya dauki wasu
mintina yana neman dalilin yankewar baccin
nashi ya rasa. Wayar shi daya laluba don ya
duba lokaci yaji bata gefen shi yasa shi tashi
zaune yana tunanin inda ya ajiyeta. Saiya tuna
ya barta dakin Madina, abinda yaso yayi, ya tura
kofar a hankali, ya mika hannu ya dauko wayar
shi, ya rufo mata a hankali, dan duka fatan shi
yana kan ta samu baccin. Shisa har yanzun yake
tuhumar kanshi ko mafarki yakeyi.
Yake addu'a da yakinin da bai taba yi ba tunda
yake a rayuwar shi, abinda yake gani a gabanshi
ya kasance mafarki ne
"Akwai macen da zata gifta ta gabanka baka bita
ba Julde? Kana da wani layi in dai akan mace ne
da ba zaka iya ketarewa ba?"
Maganganun Saratu a wani dare kan fadan da
suka saba ita da Julde suka dawo masa. A
lokacin bai gane abinda take nufi ba, asalima
kalaman sun tsaya masane saboda kamar
basuyi masa dadi ba, kamar tunda yasa
Lubna sufyan
Hausabook.com 466
kafafuwan shi cikin takalmin Julden yake
kokarin fahimtar shi, ya dauka zai tsaya kan
mace dayane, duk sanda zai bi wata zai raya a
zuciyarshi itace ta karshe, sai wani abu ya sake
jan shi, wani abu mai wahalar fassarawa, wani
abu da wanda ya tsinci kanshi cikin yanayin
bukata irin tashi ce kawai zai fahimta. A lokacin
sai yake ganin inda itama Saratun zata saka
kafafuwanta a cikin takalman Julde data yi masa
uzuri ko kadan ne, data gane abinda yakeyi
abune mai wahalar bari, da ta gane akwai
darare mabanbanta daya kudurci cewa shine
daren shi na karshe tare da wata mace da bata
halatta a wajen shi ba, amman saiya kasa. Sai
wani abu ya sake mayar dashi, wani abu mai
girman gaske.
Wannan ne layin da take magana a kai daman?
Layin da komin lalacewar da kayi bai kamata
ace ka tsallaka ba? Ashe haram kala-kala ne?
Girman wani ya kamata ace baka gwada dauka
ba saboda ba danne ka kawai zaiyi ba, harda
makusanta zai hada idan ya tashi.
"Banyi mata komai ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 467
Julde ya sake fadi yana kallon Salim, a gefe daya
kuma yana dawo da Salim din cikin hayyacin shi
yana kuma tabbatar masa da ba mafarki bane
ba, abinda yake gani gaskiya ne. Idanuwan shi
Julde ya raba daga kan Salim yana mayarwa
akan Madina da take kwance da alama batama
san duniyar da take ba. Ya sake mayarwa kan
Salim, jikinshi bari yakeyi, ba kuma waje ba, har
cikin tsokar shi yakejin hakan, zuciyarshi na
wani irin bugu da tun halittarta wannan ne karo
na farko data taba yi masa haka. Ya dade yanajin
shi kamar wanda wani abu yake bibiya, kamar
bacci yake yana mugun mafarki, yanzun kuma
da yaji ya farka saiya taradda mafarkin ya
biyoshi har wannan duniyar ma.
A karo na farko a tsayin lokaci da yaji ya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
A cikin kanshi, yana shirin sake karantowa
sallamar da ta karade falon har suna ji daga
inda suke ta hana shi
"Madina!"
Lubna sufyan
Hausabook.com 468
Khalid ya kira da alamun murmushi a muryar
shi, tun jiya Nawfal yace masa ya zauna cikin
shirin zuwa dauko su daga airport don zasu
kamo hanya a jiyan, zasu tsaya Abuja su kwana
saboda Murjanatu, yau din zasu biyo jirgin
Kano, amman karya fadawa kowa saboda suna
son ba Madina mamaki. Saurin da yakeyi kenan
da safe, ya karasa wajen aiki, akwai takardun da
suke bukatar kulawar shi, ya kuwa gama akan
gaba, dan yana fita daga office, kiran Nawfal din
na shigowa wayar shi, ya kuma ga lambar shice
ta Najeriya, alamar sun karaso.
"Daada kamar dai kinje yawon shakatawa ba
jinya ba, irin wannan karo haske da kiba haka?
Gaskiya da na sani na biku"
Ya furta cikin sigar tsokana, har ranshi yana jin
dadin ganin saukin data samu, dariya kawai
takeyi, da alama murnar dawowa da kuma
ganin shi ta hana tsokanar tashi tasiri, ko da ya
sake cewa
"Bakinki yaki rufuwa Daada, nifa auren nan
bawai inayi bane ba, duk kyan nan da kika kara"
Lubna sufyan
Hausabook.com 469
Hannu takai tana kamo kunnen shi hadi dayin
dariya, shima dariyar yakeyi yana fadin zata
cire masa kunne dan inya tashi kara aure ace ba
za'a bashi ba
"Batare da ita kuke ba?"
Khalid yayi tambayar yana kallon Nawfal
"Ita wa?"
Nawfal ya bukata duk da ya gane cewa
Murjanatu yake tambaya
"Anty na"
Dariya Nawfal yayi
"Tare muke, zata karaso gobe ko jibi In shaa
Allah, kasan ta dade rabonta da nan, to ta tsaya
wajen yan uwanta a Abuja..."
Daada taso su wuce da ita gidanta ne kai tsaye,
Khalid yace
"Daada so kike Madina ta dauki gaba damu? Ai
mu biya mu dauketa kawai sai mu tafi mu sauke
ku tare, bata fa walwala tunda kika tafin nan, sai
kince a cikin bare kika barta ba 'yan uwa ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 470
Murmushi Daada tayi, itama kewar Madinar na
danneta, dan kwanakin nan kullum sai tayi
mafarkinta, ko safiyar yau dan baccin daya
dauketa a cikin jirgi, mafarkin Madina ne ya
farkar da ita, zuciyarta kuma sai tayi mata
nauyi, lokacin daya rage a tsakaninsu take jin
kamar yayi mata nisa fiye da kullum, kamar ba'a
hanyar gida suke ba. Shisa suna shiga cikin
gidan, Khalid ya kwala mata kira Daada taji
kiran har cikin zuciyarta, ganin inda Khalid ya
nufa, Nawfal na rufa masa baya yasa Daada
dinma taji tana so ta karasa don ji tayi ba zata
iya jira har Madina ta fito ba.
"Madi..."
Khalid ya soma, ganin Salim a tsaye yasa
maganar koma masa
"Hamma..."
Ya kira da alamar tambayar me yakeyi a tsaye
haka a wajen a cikin idanuwan shi, fuskar Salim
din Khalid ya kalla yana ganin wani abu a
shimfide akai da yasa karawa bugun zuciyar shi
gudu, haka kawai kafafuwan shi suka soma yi
Lubna sufyan
Hausabook.com 471
masa barazanar kasa daukar shi ta hanyar yin
wani irin sanyi
"Me ya faru? Menene?"
Nawfal yake tambaya yana wuce Khalid ya
karasa inda Salim yake, sai lokacin Salim ya
motsa tun bude dakin da yayi, sai dai ya motsa a
makare dan har Nawfal din ya karasa, ya kuma
ture hannun Salim da yake kokarin hana masa
ganin meye a cikin dakin. Idanuwan shi ya fara
runtsawa yana yo baya kamar an watsa masa
ruwan zafi, yanda zuciyar shi take dokawa na
saka shi neman taimakon bangon wajen don
dai-daita tsayuwar da take neman gagarar shi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ya tsinci kanshi da furtawa, yana sake runtse
idanuwan shi gam, yana maimaitawa cikin
sallamawa ga Ubangiji da neman taimakon Shi
wajen bacewar abinda yagani daga duniyar shi
na har abada
"Hamma"
Khalid ya kira, tsoron da yake cike da zuciyarshi
na bayyana a muryar shi, kai Salim yake girgiza
Lubna sufyan
Hausabook.com 472
masa, ba saiya karaso ba, ba sai yaga abinda zai
canza duniyar shi na har abada ba, amman ya
kasa kin karasawar, cikin dakin ya shiga gabaki
daya, yana kuma yin abinda su duka suka kasa,
karasawa har inda Madina take kwance yaja
mayafin da yake kan gadon ya rufa mata a
jikinta
"Ban mata komai ba..."
Julde ya furta yana kallon Khalid, rigar shi da
take ajiye a gefe Khalid ya dauka ya mika masa,
ganin bai karba ba yasa Khalid kallon shi, wani
abune a cikin idanuwan Julden da ba zai fassaru
ba, kamar shima neman wanda zai tambaya
abinda yakeyi a tsaye a dakin yakeyi, kamar
kuma neman wanda zai jijjiga shi yace masa
mafarki yakeyi yake nema
"Kasa rigarka..."
Khalid ya fadi muryar shi na fitowa a raunane,
karba Julde yayi yana mayarwa, sai yakejin
nauyin rigar tare da wani abu daban na ratsa
shi, tsikar jikinshi ta shiga mikewa, da fankar
dakin ta kada, sai yaji saukar iskar a jikin shi da
wani irin yanayi, kamar tun shigowarshi dakin
Lubna sufyan
Hausabook.com 473
wannan ne karon farko daya san da zaman
fankar, sanyi yakeji, sanyi yakeji har baisan
hakoran shi na haduwa da juna ba balle jikin shi
da yake bari
"Daddy"
Khalid ya kira yana kai hannu ya rike damtsen
hannun Julde dashi, amman yanayin da Julde
yake ji na sanar dashi karshen komai yazo, ga
numfashin shi ya daina kaiwa inda ya kamata,
iskar fanka na kadawa tunda yanajin sanyinta
na kara masa wanda yakeji, amman bata kaiwa
hancin shi balle idan ya shaka ta wadace shi,
rufe idanuwan shi yayi da niyar ya budesu,
amman sai wani duhu na ban mamaki ya lullube
masa komai. Khalid na rike da hannun shi yayi
kasa yanajan har Khalid din da yake kiran
sunan shi a wahalce. Salim na kallon su, yana
kallon Khalid na jijjiga Julden amman ya kasa
motsawa balle ya kai musu wani taimako.
Daada data yi tsaye inda take ma batayi wani
yunkuri ba, jikinta ya bata koma menene ba
abinda zata so bane ba, zuciyarta tayi raunin da
bakowanne tashin hankali zata iya dauka ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 474
yanzun, tana kuma da tabbacin wannan tashin
hankali ne da zai iya karasa abinda yayi saura a
cikin kirjinta. Duk da wasu zasuce wanne dare
ne jemage bai gani ba? Amman ita tasan baiga
daren mutuwar shi ba, wannan kuma dai-dai
yake da hakan a wajenta
"Me yake faruwa ne Daada?"
Saratu da ta shigo gidan take ta sallama harta
karaso babu wanda ya nuna alamar yasan
tanayi ma balle ya amsa ta tambaya, kallonta
kawai Daada tayi da idanuwanta da batama san
sun cika da hawaye ba taji wani tashin hankali
na tasowa tun daga dan yatsan kafarta har
tsakiyar kanta kafin ya tattaro ya samu wajen
zama a cikin kirjinta, sai dai data karasa cikin
dakin bata tsammaci zata ga Julde kwance
kamar gawa ba, bata kuma sake tabbatar da shi
din kacokan ne duniyarta ba sai yanzun da ta
ganshi kwance haka, ba zatace a tsaye ko a
zaune ta rarrafa inda yake ba, ta dai ganta a
kasa, ta kuma ga kanshi a jikinta, hannuwanta
na bin fuskar shi tana son tabbatar da karshen
duniyar ta baizo tare da nashi ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 475
Da gaske ne wani tashin hankalin ya fi gaban
kwatance...
Kallon shi takeyi, sai take ganin kamar ta kalli
mudubi, saboda tana da tabbacin tashin hankali
da ciwon zuciyar da yake tattare da ita ne a tare
dashi, irin abinda take ji ne shimfide a cikin
idanuwan shi, kuma tana da yakinin idan akwai
wanda yasan ciwon Madina bayan ita, to Nawfal
ne, idan akwai wanda yake son Madina kamar
yanda take son ta, Nawfal ne. Wannan tunanin
ne ya bata kwarin gwiwar numfasawa tace masa
"A karo na farko zan roke ka alfarma Bajjo,
shekaru biyu na rayuwar ka zaka aramun duk
da nasan ba'a hannun ka suke ba, ba gabaki
dayansu ba, dan lokaci kadan a cikin kowacce
rana ta shekara biyun, ba asirin Julde zaka
taimaka mun mu rufe ba, ahalina, sauran
ahalina zaka tayani karewa, kar abinda ya rabo
mu da tushen mu ya sake nasara akan mu a karo
na biyu..."
Wani abu ya gilma ta cikin idanuwan Nawfal din
kamar walkiya, yana tabbatar mata da karo na
Lubna sufyan
Hausabook.com 476
farko
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 27