irin sama-sama, bai samu sauki
Lubna sufyan
Hausabook.com 639
ba sai da yaji hannun Murjanatu a cikin nashi, ta
dumtsa kamar ta karanci wani abin yana damun
shi, bata kuma sake shi ba har sai da suka koma
falon, inda Julde, Saratu, Yelwa, Kabiru harma
da Daada suke zaune. Yelwar tayi kyau cikin
farin leshinta mai ratsin ruwan toka a jiki,
fuskarta tayi wani irin fayau, idan baka sani ba,
babu yanda za'ayi kasan tana dauke da ciwon
dake neman rayuwarta. Idan kuma ka santa a
baya, to tabbas zaka gane dalilin da yasa kaf
Marake ake cewa ba'ayi matashiya mai
kyawunta ba. Gefe da gefenta Salim da Madina
suka zauna akayi musu hotuna wajen kala
goma, kafin Salim ya mike yana bari a dauke su
daga ita sai Madina da take ta kyafta idanuwa
alamun tana kokarin maida hawayenta.
Yelwa ba ta da karfin tashi, shisa duk wasu
hotuna da akayi a zaunen tayi su,suka sallami
mai hoton kafin su baje a tsakiyar falon inda
kayan ciye ciye da tarin lemuka suke shirye
cikin farantai masu kyau, kowa ya dauki
kananun filet yana zuba abinda yake marmari,
Salim ne ya zubawa Madina ganin tayi wani irin
sanyi, karba tayi tana daukar samosa daya ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 640
gutsira tana taunawa a hankali badon tana gane
dandanon ba
"Bani ruwa Madina..."
Yelwa ta fadi, da sauri Madina ta dauki robar
ruwa ta bude tana mika mata, ta karba
hannunta na rawa, dakyar ta kai bakinta ta
kurba, ta dawowa da Madina da take nazarin
yanayinta robar, ta karba ta rufe ta ajiye, jingina
bayanta Yelwa tayi da kujerar da take zaune ta
lumshe idanuwanta, taja wani numfashi
"Bansan me yasa ake saka cabbage a abin nan
ba"
Khalid ya fadi yana bata fuska ya hadiye spring
rolls din dakyar, yana kuma saka Madina dauke
idonta daga kan Yelwa ta kalle shi
"Me kake so a saka a ciki to? Alayyahu?"
Cewar Nawfal da ya sake kurbar lemon da yake
hannun shi, don duka abubuwan da suke a baje
a wajen, ba cimar shi bane ba
"Malam ina magana ne da mutane 'yan uwana
da zasu fahimci abinda nake cewa, ina nufin
Lubna sufyan
Hausabook.com 641
tunda ina magana ne kan abincin mu, mu
mutane"
Ruwa Nawfal ya zuba a hannu shi yana yarfawa
Khalid daya kai masa duka yana kaucewa da
sauri, ganin Khalid din na neman wani abu da
zai buga masa yasa shi fadin
"Hamma kayi masa magana..."
Juya idanuwan shi kawai Salim yayi
"Khalid karka dake shi, me yasa baka da hakuri
ne wai?"
Cewar Adee tana kwalawa Khalid din robar
lemon da ta gama shanyewa tana dorawa da
"Magana nake maka..."
Baki a bude Khalid yake kallonta
"Baki ga abinda yayi mun ba? Murjanatu"
Khalid ya karasa yana kallon Murjanatu da tayi
dariya
"Kayi hakuri Hamma, bakina daure yake da
igiyoyin aure"
Lubna sufyan
Hausabook.com 642
Kai Khalid ya jinjina
"Bakin ki suka daure kawai, amman nasan basu
hanaki ganin gaskiya ba, ki rabani da mijinki..."
Dariya takeyi, don ko kafin tazo ta gansu, ta
waya ma da video call shi da Khalid din ba gajiya
sukeyi ba. Idan kagansu daban daban zaka ga
matasan samari masu hankali da cikakkiyar
nutsuwa. Amman idan kagansu tare to zaka ga
yara ne da suke makale a jikin samari, shekarun
da hankalin suke ajiyewa a gefe suna zuba
yarintar da Lukman ma da yake kanin su bayayi.
Wani lokacin sai Salim ya raba musu waje
"Kai Bajjo koma can kujerar"
Amman ba za'ayi minti goma ba zakaji wani a
ciki yana kai kara da cewar dayan yana kallon
shi, karshe sai Salim din ya hada da zagi sannan
zasu natsu. Wani irin shiru ne ya gifta cikin
dakin na dakika, dan kowa a cikinsu zai iya
rantsewa har iskar dake yawo a dakin sai dai ta
tsaya tare da shirun, kafin zuciyar Madina tayi
wata irin dokawa da ta sakata juyawa ta kalli
Yelwa, tayi luf a cikin kujerar, idanuwanta a
lumshe, kallonta Madina takeyi sosai tana so
Lubna sufyan
Hausabook.com 643
taga tayi motsi ko yaya ne. Ganin bata motsa ba
ya sakata tabata tana rasa a cikin jerin sunayen
da ake kiran uwa dasu wanne yafi dacewa ta
kirata dashi kafin harshenta ya iya hada jimlolin
"Ummi..."
Yanayin da ta kira sunan yana saka hankalin
kowa a dakin komawa kan Yelwa, Julde ne ya
taso daga inda yake yana ture har Madina ya
riko hannun Yelwa da kamar hakan take jira ta
sulale akan kujerar, ya kuwa rikota gabaki daya
yana dagota hadi da kallon su Salim cikin neman
taimakon daya kasa furtawa. Salim ne ya tashi
yana kokarin kama hannunta amman Julde ya
hana shi, girgiza masa kai kawai yakeyi
"Daddy dubata zanyi, likita ne ni ka manta"
Sannan Julden ya barshi ya rike hannun Yelwa
da yaji yayi sanyi a cikin nashi. Baisan me yasa
ya fara kallon Daada ba, ya kuma yi dana sanin
hakan, murmushi tayi masa, wani irin
murmushi mai ciwo kafin hawaye su silalo mata,
ta kai hannu ta goge su
"Ta rasu ko? Allah ya karbi ajiyar shi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 644
Ta karasa muryarta na karyewa, sai ta kalli
Julde, tana jin yanda shi kadai ya rage mata
"Bukar"
Wani sashi na zuciyarta ya kira mata sunan shi,
amman yana ina? Julde kadai take dashi, haka
tata kaddarar take, haka Allah ya tsara mata, ta
amsa sunan uwa, a tare da sunan ta fuskanci
kalubale kala-kala, tun daga yaran da suka fito
daga jikinta dan ta amsa sunan uwa kawai, har
kan wanda suka fito suka rayu da ita ta amsa
sunan a aikace, a lokaci daya suka nuna mata
yanda ta gaza a matsayin uwa, shima Julden
wanne tabbaci take dashi na cewar shi zai zuba
mata kasa? Ba ita zata ga fita da gawar shi ba?
"Karka ce mun ta rasu Salim...karka fadamun ta
rasu"
Julde yake fadi yana jin duniyar na jujjuya mishi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Madina ta furta, a zaune take, amman sai taji
kamar ta sake komawa ta zauna, kamar kuma
wani abu ya daki duka ilahirin jikinta
Lubna sufyan
Hausabook.com 645
"Daddy..."
Salim ya kira a tausashe, duk wata alama ta mai
rai tabar jikin Yelwa, sai dai in fuskarta ka kalla,
da siririn murmushin da yake kai, zaka iya
rantsewa bata rasu ba. Sai dakin da yayi shiru
baka jin komai sai sautin kukan Saratu, Adee da
Murjanatu da suke ganin abin kamar almara.
Nawfal kuwa ji yayi kamar an zare masa lakkar
jikin shi, zai iya tuna sau nawa yaje makabarta,
kuma shima tun yana yaro ne, ya kasa dauke
idanuwanshi daga kan Yelwa da yanzun suka
gama hotuna da ita
"Bajjo..."
Ta kira shi kamar ta sanshi, tun ranar daya fara
ganinta taji suna kiranshi haka, itama ta kira
shi, tana kallon shi kamar akwai tarin abinda
take son fada masa, da ta samu dama kalamanta
basu tsawaita ba
"Kayi kama da Hamma Bukar, sai dai baka da
sanyin shi, wannan sanyin da shi kadai yake
dashi...idan kayi dariya kamanninku sunfi
fitowa"
Lubna sufyan
Hausabook.com 646
Murmushi kawai ya iya yi mata zai tuna, saboda
baisan meya kamata yace ba, Bukar din ya bace
a tunanin shi, baisan kamannin shi ba balle ya
hadasu da kalamanta ya auna yaga gaskiyar su.
Yau ma kuma tana ganin shi ta kirashi
"Ina wuni, ya jikinki?"
Ya tambaya, tayi masa murmushi
"Alhamdulillah...gani a zaune"
Sai ya tsinci kanshi da yin dariya
"Allah ya baki lafiya"
Bai tuna ta amsa ko bata amsa ba, Allah dai ya
amsa addu'ar tashi, ga lafiya nan ta samu, ciwon
yazo karshe. Khalid ma ya kasa dauke idanuwan
shi daga kanta. Ashe duk wani labari na mutuwa
da yake ji, duk wani kai gawa da akeyi da shi,
duk tunanin mutuwar shi da yakeyi a kullum,
duk yanda yake fadawa kanshi ba wai sanin
mutuwa kawai yayi ba, har zuciyar shi tasan da
zamanta karyane, bata zo kansu bane shisa yake
ganin haka. Wannan zantukane da yaudarar da
kowanne dan adam yakeyiwa kan shi, daman
haka mutuwar take? Lokaci daya? Ba zaice bata
Lubna sufyan
Hausabook.com 647
nuna alama ba tunda tana ciwo, amman haka
kawai? Yau? Duka suna zagaye da ita suna
labari, suna dariya har ta ratso ta cika umarni ta
fita suna nan zaune basu ji alamunta ba.
Wanne irin zumunci ne wannan? Ba ma ance ko
mutuwa na kunyar idon iyaye ba, ga Daada a
zaune, amman mutuwar bata ki dauke mata
yarinyar da bata jima da dawowa rayuwarta ba.
Kallon komai Khalid yakeyi kamar shirin fim,
musamman yanda Salim yake fama da Julde
daya kamo gawar Yelwa ya kwantar da kanta a
jikinshi yana dan bubbuga fuskarta cikin son ta
bude idanuwan da ta riga da tayi musu rufewar
karshe. A tsakanin kukan su Saratu, hawayen
Mami, da wahalar Julde ta karbar mutuwar tilon
yar uwar shi, haka suka tattara suka fita daga
dakin dan a suturta, haka kuma kukan da sukeyi
bai hana Adee da taimakon Saratu suka shirya
Yelwa suna saka mata kayanta na karshe, ankon
da yake jiran kowanne musulmi.
Haka su kuma da tarin mutanen unguwar su da
suka zo sukayi mata sallah, suka dauki gawar
suka nufi makabarta, a hanya Khalid yake
jinjina Ikon Allah ganin tarin al'ummar da suke
Lubna sufyan
Hausabook.com 648
biye, ganin kuma Yelwar duka yaushe tazo
Kano, waya santa da zaizo dominta? Wanda
suka sansu suka zo donsu din mutanen unguwa
ne, wannan al'ummar kuwa ta wuce mutanen
unguwa, harda masu adaidaita sahu kasancewar
makabartar tsallaken titi, haka suka dinga
parking suna fitowa, can ya tsinkayi muryar
wani yana tambayar
"Wai waya rasu?"
Wani kuma na amsa mishi da
"Bansani ba wallahi, kamar wani yace wata
babbar malama ce, shine nace bari ayi rakiyar
dani, Allah ya yafe mana ya datar damu da
kyakkyawan karshe"
Murmushi Khalid ya tsinci kanshi dayi, Allah
kenan, mai son bayinshi da Rahma, a cikin
alamomi na dacewa dai wannan dimbin jama'ar
da suke raka Yelwa ya nuna cewa tana daga
cikin mutanen da sukayi dacen karshe me kyau.
Ya dauka abinda zaisa Salim hawaye ba karami
bane ba, amman yanda aka gama binne Yelwa,
Kabiru ya mike ya koma ya fadi a gefen kabarin
Lubna sufyan
Hausabook.com 649
suka kamo shi yana hawaye babu wanda bai
karyawa zuciya ba
"Ka sakeni Khalid, dan Allah ku bani yan
mintina, zan tashi, nima ba dadewa zanyi ba,
inaji a jikina ba wani tsayin lokaci zamu dauka a
tsakanin mu ba, ku barni in kara bankwana da
ita kafin in tarar da ita dan Allah..."
Sakin shi sukayi, suka tsaya, ya kusan mintina
biyar kafin ya iya mikewa, su juya suna barin
Yelwa da halayenta duk kuwa tarin soyayyar da
sukeyi mata. Haka suka koma suka shimfida
tabarmi aka kafa rumfa ana karbar gaisuwar
mutuwar da ciwo baisa sun hangota kurkusa
haka ba. Kamar yanda kwanakin suka shiga
wucewa kamar kiftawar idanuwa, daga asabar
din rasuwar har wata asabar din ta zagayo da ta
cika kwanaki bakwai dai-dai, ranar da tayi daidai da ranar da za'a share zaman makokin, suna
zaune da tsirarun mutanen unguwa da kan
tayasu zaman, da kuma Julde da yake a tsakiyar
Khalid da Nawfal, yayi duhu a cikin kwanakin
yayi zuru-zuru dashi, alamar mutuwar ta dake
shi ba kadan ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 650
Kamar daga sama ya tsinkayo wata murya da
lokaci ya fara dishe masa tasirinta na fadin
"Hamma wa na rasa? Na zo a makare ko? Kace
mun ba Daada bace ba, dan Allah kace mun ban
rasa Daada ba?"
Ya kara maganar kafafuwan shi dake masa
barazana na saka shi durkushewa akan
tabarmar kan dole, wata irin iska na kadawa a
lokacin da Julde ya dago idanuwanshi, ya sauke
su akan Bukar, akan fuskar Bukar da take cike
da kasumba, akan fuskar Bukar da yayi wata
irin rama kamar wanda ya tashi daga jinya, akan
fuskar Bukar da hawayen da suke saukar masa,
sai yaji jikinshi ya mutu, yaji kamar bashi da
sauran kalamai, kamar idan yayi kwakkwaran
motsi zai farka yaga mafarki yakeyi, abinda bai
tabayi ba a tsayin shekarun nan, har shakkun
kaunar da yakewa Bukar saida ya darsar masa,
ganin bai taba ko da mafarki dashi ba.
"Daada ce ko Hamma? Na rasata? Kaddarar
haduwar mu ta kare tun a wancen lokacin..."
Kai Julde ya tsinci kanshi da girgizawa
Lubna sufyan
Hausabook.com 651
"Yelwa ce...Daada na cikin gida"
Kai Bukar yake jinjinawa, wasu hawayen na
sake sauko masa da jin mutuwar Yelwar, kafin
ya maida dubanshi kan Nawfal da ya kura masa
ido ko kyaftawa ba yayi. Ya bude baki da nufin
magana Nawfal ya mike, ko takalma bai saka ba
yabar wajen, baiga alamar lafiya a tare da Bukar
ba, Yelwa ta fara dawowa, suka saka rai akanta
gabaki dayansu, sai ta koma, ta tafi inda hakuri
ya zame musu dole tunda ba dawowa zatayi ba,
kwana nawa a tsakani, shikuma zaizo? Duk
shekarun nan? Sai yanzun? Sai yau kamar sun
hada baki da Yelwa.
Duka hayaniyar falon yake jin ta zuqe mishi,
babu wani abu da yake karasawa kunnuwan shi,
kallon su yakeyi daya bayan daya da wani abu
mai kama da alfahari, wani abu da ya girmi so,
ya kuma wuce kauna, yanayi ne da akansu
kawai yasan akwai shi, yake kuma jinshi. Anya
akwai abinda yafi dangi dadi? Akwai abinda yafi
'yan uwa? Sai ya kalli Bukar da ga Kaltume a
zaune a falon amman yana kusa da Daada, yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 652
zaune a kasa kan kafet din dakin a gefenta na
dama, Madina tana gefenta na haggu, Salim
kuma yana gefen Madinar, kallo daya zakayiwa
fuskar shi kagane inda yana da wani zabi bayan
zaman wajen zai dauka. Nawfal ya rufe
idanuwan shi, ya sake budesu akan su Bukar,
shekara daya, ya kamata ace ya saba, zuciyar shi
ta aminta ta yarda da ba mafarki yake ba, su
dinne suka dawo, iyayen shi, kuma duk wani
alamu sun nuna zamansu ba mai karewa bane
nan kusa.
Tunda Bukar din tare suke zuwa kasuwa da
Julde, bayan ya bashi gida mai daki biyu (two
bedroom) daya siya da sunan Lukman, yake
kuma shirin zuba yan haya, sai dai kafin yayi
hakan ne Bukar ya dawo. Zaice ya shafe
kwanaki bakwai bayan dawowar shi yana
kaucewa haduwa dashi, asalima kayanshi ya
hada da kuma matar shi suna tafiya Kaduna
saboda ya fuskanci abubuwan da suke gaban shi
na kasuwancin da ya kafa a garin na Kaduna.
Duk wani sauran kuzari da ya rage masa ya
tattara yana mayarwa akan aikin da fatan ya
dauke masa hankali daga dawowar Bukar, sai
Lubna sufyan
Hausabook.com 653
dai kamar duk wata sa'a da zata wuce da yanda
amon muryar da yake fada masa idan kuma da
gasken Bukar ta leko ta koma zaiyi masa kamar
yanda Yelwa tayiwa Madina fa, yake karuwa. Ko
da ta leko ta koma dinne kamar ya kamata ace
ya tsaya ya samu wani lokacin da zai adana a
zuciyarshi ko dan gaba.
Yaji dadin da Murjanatu bata tayar mishi da
maganar ba, duk yanda yake ganin tana son yin
hakan a lokutta mabanbanta, sai dai idan yaje
jikinta zata kara rike shi, zata sumbace shi a
kunshi ko duk inda labbanta zasu iya kaiwa tana
son fada masa tana tare dashi duk runtsi, idan
kuma yana da bukatar abokiyar tattauna
damuwar shi tana nan, tana nan a kowanne irin
yanayi da hargitsi da zai tsinci kanshi. Ya
godewa Allah, ya godewa Murjanatu, ya godewa
duk wani dalili, karami da babba daya hadu
waje daya ya samar mishi da ita a matsayin
matar aure, saboda yasan ba dabarar shi bace
balle wayon shi. Sai dai kwanakin suka fara yi
masa tsayi, aikin daya ke fatan binne komai a
cikin shi ya daina bashi kariya daga tunanin da
yake ta turewa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 654
A idanuwan shi zaka ga ramar daya fara a tsaye,
idan kuma kasan shi yanda ya zama shiru-shiru
zaka san wani abu yana damun shi, wani abu
mai girma. A ranar wata laraba, ya yanke
shawarar komawa gida wajen sha biyu na rana,
gara yaje ya rabi jikin matar shi ko zai samu
salama a ranshi, ya shigar da motar shi cikin
gidan nasu da Murjanatu ke korafin har yanzun
bai gama yi mata yanda take so ba, ya fito ya ga
maigadin su yana bude gate din da alamun wata
motarce zata shigo, zuciyar shi ta buga, ta kara
bugawa ganin motar Khalid ce, wajen sati kenan
yana gujema duk wani kira da Khalid din yayi
masa a waya saboda yayi masa maganar Bukar.
Bai san dalilin da tunanin awannin dake
tsakanin Kano da Kaduna ba wasu masu yawa
bane balle suyiwa Khalid katanga a tsakanin su,
zuciyar shi ta kara bugawa ganin Bukar ya fara
fitowa daga motar, kafin Khalid ya fito, sai dai
shi bai fara takowa ba, a jikin motar ya tsaya
yana kallon Nawfal kamar yana son gaya mishi
"Ga abinda kake gudu nan na biyoka dashi"
Kamar kuma yana son ce mishi
Lubna sufyan
Hausabook.com 655
"Wannan baya cikin abinda zaka iya gujewa
fuskanta Bajjo"
Ya hadiye wani abu da yaji ya tsaya masa a
wuya, lokaci daya kuma jikin shi ya dauki dumin
da bashi da alaka da zazzabi, kafin numfashin
shi ya fara yi masa barazana ganin Bukar tsaye a
gaban shi. Yadi ne a jikin Bukar din bula mai
haske, sai hula data hau da yadin. Ramar da take
fuskar shi a wancen lokacin babu ita yanzun,
sannan yayi gyaran fuska, farin gashin da ya fara
nuna shekarun shi ya kara masa wani irin
kwarjini na ban mamaki, sanyin halin shi da
kowa yake yawan magana akai shimfide a
fuskar shi
"Na so in baka duk lokacin da kake bukata, sai
dai lokaci abune da yake karanci a ahalin mu
Nawfal, ka yanke mun duk hukuncin da kake so,
amman kayi hakan bayan ka saurare ni, dan
Allah, ba uzuri zan baka ba, bayani zanyi maka,
dalili na kawai zan fada maka..."
Ba zai iya tuna mintina nawa yayi a tsaye inda
yake suna kallon-kallo shi da Bukar din, zai dai
iya tuna Khalid ya karaso, yayi masa maganar da
Lubna sufyan
Hausabook.com 656
ba zai iya tunawa ba, a cikin wannan rudanin
kuma suka shiga falon gidan shi, yanajin shi
kamar bashi ba har lokacin da Murjanatu ta
kawo musu ruwa, lemuka, kayan marmari sai
snacks din da ba'a rabasu dashi saboda tana so,
ta kuma yi wata magana da yasan ba zata wuce
gaisuwa da kuma abincin da zata dora musu ba
tunda basu sanar da zuwan nasu ba. Ruwa ma
Khalid ne ya bude robar ya mika masa, baiyi
musu ba ya karba ya sha yana ajiye robar hadi
da kallon Bukar daya bude bakin shi ya fara
bashi wani labari mai kama da shirin film din
Hausa.
Yace masa sauran kwana daya ranar da suka
shirya barin garin shi da Kaltume ta cika,
hasashenta na faruwar wani babban abu da
rayuwar su ya tabbata, ya dauki Nawfal din sun
fita masallaci sallar Isha'i, aka kuma yi dace an
gayyato wani bakon Malami da ya tsaya yin
wa'azi akan matsalar da ake ta fuskanta ta
yawan mace-macen aure da muhimmanci sauke
hakkin iyali, hakikanin gaskiya zuciyar shi a
wannan lokacin tana gida, tana ga Kaltume,
amman babu wanda yayi kokarin barin
Lubna sufyan
Hausabook.com 657
masallacin, shisa shima baiyi wani yunkuri ba
ya zauna kawai. Har aka gama wajen tara da
rabi, dan Nawfal yayi bacci a jikin shi, sai sabar
shi yayi suka nufi gida, zuciyar shi na tsananta
duka, wani irin yanayi na ziyartar shi,
musamman daya ga gate din gidan a bude, kuma
yasan sun sallami maigadin su tun satin daya
wuce.
Zuciyar shi ta mirgino ta fado kasa inda ta
tarwatse bayan ya shiga gidan ya ganshi anyi
masa dai-dai, kamar ana neman wani abu, kuma
babu Kaltume babu dalilinta. Wani irin firgici da
tsoro suka daki ruhinshi, duka tunanin shi ya
tsaya akan dangin mahaifinta da basu daina
bibiyarsu ba, basu dauke idanuwansu daga
dukiyar da aka bar mata ba, kadarorin da ta
dinga siyarwa tana siyen zinari tana ajiyewa,
wasu kudin kuma ta barsu a cikin asusun
bankin data bude dan hakan kawai.
"Idan zabi ya gifta tsakanin ni da Nawfal ka zabi
yarona, dan Allah kayi nisa dashi yanda dangin
Abba ba zasu cutar mun dashi ba saboda abin
duniya..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 658
Duk wani abu mai muhimmanci yana cikin
mota, sun gama tattara kayan da zasu dauka sun
saka a ciki tunda safe, daya karasa motar cikin
rashin hayyaci, jakar da tafi kowacce
muhimmanci kawai ya iya dauka, daga shi sai
kayan jikin shi da silipas, a kafa ya karasa tasha,
acan suka kwana da safe ya kama hanya. Sai dai
bayan yaje Marake ya ajiyewa Daada Nawfal
batare da bayanin komai ba, juyawa yayi a ranar
ya sake shiga mota dan ya bi bayan Kaltume, ya
kuma sauka cikin rashin sa'ar samun dangin
mahaifinta sun baza neman shi, Kawunta ya kai
rahota ofishin 'yan sanda cewar Bukar din ya
batar da ita, ya gudu da tarin dukiya, yana
komawa ana kama shi.
Bashida wata shaida, Kaltumen da zata zame
mishi shaida baisan inda take ba, yaci wahala a
hannun 'yan sanda a nufinsu na tambayar shi
inda dukiyar Kaltume take, case din daya dauki
wata daya, da Kawunanta suka ga ba zaiyi
magana ba suka maka shi kotu, inda yake da
yakinin cin hanci akayi amfani dashi wajen
garkama shi a gidan yari, laifin shi daya, da
kaddara ta hada shi hanya da Baban Kaltume, ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 659
kuma hadashi aure da ita. Bashi da wata hanya
da 'yan uwanshi zasu san halin da yake ciki. Sai
dai a lokacin da suka garkama shi gidan yari,
Kaltume gidan mahaukata suka kaita suka
lakaba mata ciwon haukan da bata dashi, yanda
take kiran mijinta da danta, suka kuma cewa
likitocin tayi aure, amman mijin da dan duk sun
mutu sakamakon hatsarin da suke tunani shine
ya taba mata kwakwalwa take ta sambatu taki
amsar mutuwar.
Ko da bata hauka, ciwon damuwa da kuma
fargabar halin da mijinta da danta suke ciki ya
taba kwakwalwarta, tun tana yunkurin yakice
zuciyarta harta bar damuwar tayi nasara
akanta, dalilin da yasa asibiti riketa kenan. Da
shekaru suka fara tafiya sai ta amince, ta kuma
fara yarda da cewar watakila da gaske haukan
takeyi. A cikin yaran Kawunanta, yar shi ta
hudu, Hamida ce tayi nasarar jin abinda ya faru
lokacin da ta tsinkaye shi suna tattauna
maganar da dan uwan shi, suna kuma tunanin
inda Bukar da Kaltume suka kai dukiyar da har
a lokacin suka kasa cire ransu daga kanta. Basu
kuma bar zuciya da tunanin ba, saboda su kuma
Lubna sufyan
Hausabook.com 660
ta zabi fannin shari'a, har bayan tayi aure,
shekaru sunja basu bar ranta ba, tana kuma
kallon mahaifinta da zaluncin da bashi da nufin
yin nadama akan shi balle kuma ya tuba.
Ita ta fara nemo Bukar bayan mahaifinta ya
kwanta wata irin cuta da likitoci suka kasa gane
kanta, Allah kuma ya matse shi da ta tayar masa
da zancen su Bukar bai musa ba wajen warware
mata komai, saboda a lokacin babu abinda yake
bukata sai samun salama daga azabar ciwon da
yake fama dashi, duk da mahaifin nata ya shirya
tsaf dan bada shaidar da zata wanke Bukar a
gaban alkalai, shari'ar bata zo da sauki ba,
musamman data hada da ahalin da suka ki bawa
Hamida goyon baya saboda tonon asirin su
gabaki daya. Sai dai bai wani daga burin shi
akan samun nasara ba, ya rigada ya sallamawa
kaddarar da ta fado masa, a zuciyar shi kuma
yayi sallama da kowa nashi, ya dai san duk inda
suke fatan su da addu'o'in su na tare dashi,
musamman Daadar shi.
Sai gashi sunyi nasara, sai gashi ya shaqi iskar
'yanci da ya fitar da rai da ita, sai a lokacin kuma
ya iya tambayar Kaltume, sai lokacin ya bari
Lubna sufyan
Hausabook.com 661
zuciyar shi ta tambayeta, ya kuma yi karo da
labari mai dadi, an fito da ita, asalima ita suka
fara fitowa da ita, tana dai karbar kulawa ne
bisa turbar da ta dace a hannun likitoci saboda
damuwar data taba kwakwalwarta, kuma ana
samun cigaba. Kamar ganin shine babban
maganin da tafi bukata, zaren da zata kama ya
fisgota daga duniyar damuwar da take ciki. Sai
ta samu wani sauki daya ba likitocin mamaki, ya
kuma yiwa Bukar dadi saboda bayason su kara
wasu kwanaki a garin na Borno batare da sun
fice ba, duk wata neman yafiya daga Kawunanta,
da nuna nadama bai taba zuciyar Kaltume ba,
garama Bukar ya bude bakin shi ya furta ya yafe
musu, ko dan darajar Hamida, amman Kaltume
shiru tayi, tunda ko addini ya bata zabin yafewa
ko akasin hakan. Sunyi mata babbar cutar da ba
zata yafu ba a wajenta. Wata shari'ar sai a
lahira.
Haka suka tarkata dan abinda ba'a rasa ba,
bayan tarin godiya da fatan alkhairi suka nufi
Marake. Komai ya kara zuwa masa da sauki
bayan ya nufi gidansu yaga yanda yanda daga na
Datti har na Hammadi suka zama kango saboda
Lubna sufyan
Hausabook.com 662
rashin mutane. Sai yaja Kaltume suka nufi gidan
Baabuga, inda yayi murna da ganinsu, harda
hawayen shi, anan kuma suka samu labari mai
dadi, na zuwan su Nawfal, na ziyarar da suka
sake kawowa a karo na biyu, suka kuma samu
lambar wayar da Khalid ya rubuta yana bawa
Baabuga da nufin ko da wani abin zai taso.
Harda cikakken adireshin inda suke da zama a
jiki, shisa Bukar din bai kira Khalid ba, suka
kwana, washegari suka samu motar Kano, da
kudin hannun shi yayi amfani ya kamawa
Kaltume daki saboda yanda ta nuna alamar
galabaita, ya barta acan da nufin komawa ya
dauketa idan ya gano gidan.
Kallon shi Nawfal yakeyi, tunda ya fara magana,
har wani jiri-jiri yake ji saboda yanda yake so ya
nannade kanshi cikin duk bayanin Bukar da
yake kama da almara ko zai fahimta. Daga
yanda suke kallon shi yasan jira suke yace wani
abu, amman ya kasa ko kwakkwaran motsi balle
ya iya furta wani abu. Kiran sallar azahar shiya
tashe su, tare sukaje masallaci, suka dawo, inda
Murjanatu ta kawo musu shinkafa da sauce din
kifi da tayi da tumatir da albasa, dan ba tattasai
Lubna sufyan
Hausabook.com 663
garesu a gidan ba balle attaruhu, ko nama basu
dashi, idan tayi sha'awa zata fita ta siya ko tayi
order, to a hankalima, saboda Nawfal din
kaunar da takeyiwa nama ta kula kara nisa
takeyi.
Sai salad da tayi musu, da kuma lemuka, ta bar
musu wajen, Khalid ne ya zuba ma Nawfal din da
ya dinga wasa da cokalin shi a cikin abincin har
suka kammala. Suka yi masa sallama suka juya,
ya dai rakasu bakin mota, ya koma ya samu
Murjanatu harta kwashe komai. Kamar kuma ko
da yaushe bata yi masa magana ba, bata
tambaye shi wani abu ba. Shine ma a daren
ranar ya dinga jaddada mata irin son da yakeyi
mata da kuma godiyar da yake yiwa Allah da ta
kasance cikin rayuwar shi. Haka kwanakin suka
dinga zuwa suna wucewa har sati biyu bayan
zuwan su Bukar, yana kwance Murjanatu tazo ta
tsaya akan shi tana girgiza shi cikin wani yanayi
daya saka shi tashi zaune babu shiri.
Kallonta yayi, hawaye ne cike taf da idanuwanta,
ta kasa magana, sai wani abu da bai gama
fahimtar menene ba ta mika masa, baiyi musu
ba ya karba ya duba, sai dai so yake ya tuna inda
Lubna sufyan
Hausabook.com 664
ya taba ganin abinda yake rike dashi, kafin ya
fahimci amfanin shi, zama tayi kusa dashi sosai
tana zagaya hannuwanta ta riko shi jikinta
"Allah ya dubemu..."
Kamar wanda kalamanta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 27